shagon suka koma cikin gida.
**************************
A cikin watanni bakwai da auren Abdul da Huzaimah,babbar yayar su taje gidan ya fi a ƙirga,kullum taje da kalar sauyin da take gani a tattare da Huzaimah,hakan ke saka ta yi mata tambayoyi masu cike da hikima da dabara dan ta gano dalilin rama da lalacewar ta,ita kuwa Huzaimah dik kalar wayo da dabarar da za a yi mata bata faɗin gaskiyar matsalar ta,daga ƙarshe sai yayar ta ta ɗauka ko ciki ne da ita shi yasa ta lalace haka,domin ba kowa ne cikin fari ke yi masa kyau ba,nan da nan kuwa ta baza magana a dangi,ƴan'uwa da iyayen ta da abokan arziƙi sai suka dinga murna Huzaimah nada juna biyu.
Dik abunnan da ake yi Huzaimah bata san maganar da ake bazawa a dangi ba,sai watarana da Abdul ya kai ta ganin gida,tinda ta je mahaifiyar ta ke nan nan da ita,motsi kaɗan zata tambaye ta ko da abinda take marmari a yi mata? ita kuwa sai ta biye mata ta dinga lissafa dik abinda take so,haka Ummahn ta ta dinga jigilar shiga kitchen da kanta tana samar mata dik abinda ta buƙata,kwanan su huɗu suka baro garin Katsina ta koma ɗakin mijinta.
Tinda ta koma Abdul ke rawar kai kamar wani sabon ango,ba dan komai ba sai dan shan wani maganin gargajiya da Innah Laminde ta aiko masa da shi daga ƙauye ya yi,a hankali yake jin jikin shi yana motsawa,dan haka ya ƙudirta a daren ranar da Huzaimah ta dawo zai ƙara shan maganin ya gwada ko zai samu ci gaba.
Ita kuwa Huzaimah tin da ta dawo take d'aure fuska,gaba ɗaya hirar da suka dinga sha da ƙawayen ta da yayyen ta ne ke yi mata yawo a kwanyar kanta,yanda kowa ta buɗe baki take yabon gwarzantaka da ƙwarewar mijin ta wajen gamsar da ita a gado abun ya burge ta,duk yanda suka so su bugi cikin ta dan itama ta bada nata labarin ƙi tayi,sai dai kawai ta dinga dariya tana sunne kai,babbar yayar su ce ta ce a ƙyale ta,da dikkan alama kunya take ji watarana da kanta zata zo tana basu labari.
Hawaye ne masu zafi suka fara gangaro mata, ba tare da ta damu da zubar su ba ta samu waje ta zauna a bakin gado tana karasa sanya wandon baccin ta,Abdul ne ya shiga ɗakin sai ƙamshi yake bazawa,sanye yake da zallan boxer a jikin shi babu ko vest,ɗaga kai tayi ta kalle shi daga sama har ƙasa,gashi nan dai a ido namiji ne mai ƙirar mazantaka,babu abinda Abdussaboor ya rasa daga kyawun jiki zuwa kyawun fata,sai dai ta inda ya kamata ya nunawa mace shi jarumi ne an kassara wajen,lokuta da dama idan ta fara jin haushin shi sai ta danne zuciyarta ta bashi uziri,tinda ba da kanshi ya illata kanshi ba,sannan ko babu komai ta dalilin zai aure ta ne aka illata shi.
Hawayen ta ne suka ƙaru saboda yanda take ji a jikin ta sakamakon magungunan matan da yayar su ta dinga ɗirka mata,idan ta ƙi sha sai ta hauta da faɗa tana faɗin,
'Ke yanzu haka zaki zauna babu gyara? Kar ki manta fa mijin ki ya taɓa wani auren,kika san ita wanne irin gyara take yi da suna tare? To idan zaki gyara ki gyara,idan ba haka ba akan idon ki zai dawo da ita ko ya sake yin wani auren, tinda baya samun yanda yake so a wajen ki.'
Kuka ta rushe dashi sannan ta kifa kanta a saman gadon,nan take jikin Abdul ya yi bala'in sanyi,dik wani karsashi da ƙwarin guiwar da ya shiga ɗakin dashi ta kashe masa shi,cikin hanzari ya isa gaban ta ya tsugunna ya kama hannayen ta dika biyu cikin nashi,muryar shi a matuƙar sanyaye ya ce,
"Dan Allah Baby ki tashi zaune ki sanar dani abinda ke damun ki,ko dai na yi maki wani laifin ne ban sani ba?"
Girgiza kai Huzaimah tayi tana zubar da hawaye tare da ajiyar zuciya mai ƙarfi,sake rikicewa Abdul ya yi ya ɗauke ta gaba ɗaya ya ɗora a cinyar shi,a hankali ya ke shafa bayan ta da sigar rarrashi,cikin sauri da zafin nama Huzaimah ta tashi daga jikin shi ta tura shi baya sai da ya kwanta a saman gadon ba tare da ya shiryawa hakan ba,kuka take yi kamar wadda aka yi wa dukan tsiya,cikin kukan ta hau nuna shi tana nuna kanta ta ce,
"Dan girman Allah ka dena taɓa ni,ka dena saka min rai akan abinda ba zan taɓa samu ba, na amince zan yi rayuwar aure da kai,amma ba zan sake yarda ka dinga jagwalgwala ni kamar ka samu mage ba,bana son abinda nake ji a jiki na, bana son abinda kake yi min ka kasa ƙarasawa,ban san yanda ake ji ba,amma zuciya ta na kwaɗaita min abinda ƙawaye na ke faɗa ana ji idan ana mu'amalar auratayya tsakanin miji da mata,dan Allah ka sama min mafita na gaji,na gaji Abdussaboor ba zan iya jurewa ba."
Zubewa tayi a ƙasan wajen ta ci gaba da rusa kuka mai ban tausayi,cikin hawaye Abdul ya miƙe ya bar ɗakin da sauri ya faɗa nashi,wasu zafafan hawaye ne ke kwaranya a idanun shi kamar an kunna famfo,Hadiza ta cutar da shi,me ya yi mata a rayuwa mai muni da zata illata shi haka? Ya so ta a lokacin da kowa ke yi mata kallon ƴar iska,ya rufa mata asiri ya aure ta dik da ya san ita ɗin ba budurwa bace,sannan ta yi yawon karuwanci,shine zata saka masa da nakasa shi irin haka? Yanzu shikenan duk duniya Amir ne kawai ɗan shi? Cikin kuka ya zauna a bakin gadon ɗakin shi ya furta,
"Ban taɓa ganin butulu a duniya sama da ke ba Hadiza,na so ki,na ƙaunace ki,na zauna dake a yanda kike,na kyautata maki a zaman da muka yi,na maida ke sarauniyar mata,babu abinda bana baki kafin ma ki tambaya,ke da kan ki kika sani na ɗaukar maki alƙawari a lokacin da zuciyata bata so,me yasa zaki nakasa ni akan na zaɓi na raya sunnar Annabi dan gujewa zina?"
Rashin samun amsar tambayar shi ne ya sanya shi ɗaukan wayar shi ya kirawo Bilal,Bilal na zaune ya na karatun ƙur'ani bayan ya idar da sallar isha'i ya ga wayar shi na haske,hannu ya miƙa ya ɗauka sannan ya saki murmushi,yana amsawa ya fashe da dariya ya na faɗin,
'Allah ka aurar dani a wannan shekarar na huta da wannan rawar kan da ake min, tin jiya ka ƙi.....subhanallahi kuka kuma? Me yake faruwa? Dan Allah ka dena kuka habaa sai kace ba namiji ba? Me ya yi zafi haka?'
"Bilal bani da amfanin komai a matsayina na ɗa namiji,Bilal ka bani shawara kamar yanda ka saba bani, ya zan yi da matsalar dake tattare da ni akan auren Huzaimah? Yarinyar nan ta yi haƙurin zama dani,a yanzu kuma haƙurin nata ya ƙare,dan Allah ka bani shawara kamar yanda ka saba................."
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
*Masu tambayar novel daga farko ina mai sake baku haƙuri,ku diba wattpad ko WhatsApp channel d'ina za ku samu,an kai wata kusan uku ana tura maku novel a group ɗin da kuke baku fara bi ba sai yanzu da aka kai page har 95? Ai ko kun san ba zai yu a sake tura maku daga farko ba,ku jira a haɗa document amma fa ba kyauta bane.*
PAGE 95:
Gyara zama Bilal ya yi da kyau kafin ya rufe ƙur'anin dake hannun shi ya mayar dashi ma'ajiyar shi,cike da natsuwa ya ce,
"Abdul ka kwantar da hankalin ka dan Allah,ka yi alwala kayi sallah sannan ka roƙi Allah ya yi maku zaɓin alkhairi a rayuwar auren ku,domin ni kaina yanzu ban san kalar shawarar da zan baka ba, addu'a kawai zan taya ku,Allah zai kawo maku mafita,zuwa da safe zan zo gidan daga nan sai mu wuce office."
"Na gode Bilal,har ka sa na ji sanyi a zuciya ta,inshaa Allahu zan yi yanda ka ce,Allah ya shiga lamuran mu,sai da safen zan jira ka inshaa Allahu."
Da wannan shawarar suka kashe waya,Abdul bai ɓata lokaci ba wajen zuwa ya yi alwala ya tada sallah,sai da ya yi nafila raka'a shida kafin ya zauna ya yi addu'a sosai ya shafa,yana idarwa ya naɗe abun sallah ya ajiye a inda ya dace sannan ya haye gado,ya jima a kwance yana juyi kafin ya samu bacci ya ɗauke shi cike da tunanin Huzaimah.
Tinda ya kwanta bai motsa ba sai takwas da rabi na safe, wayar shi dake ta ƙara saboda kiran da ake zabga masa ya jawo,lamabar Bilal ya gani, cikin sauri ya kalli lokaci,a guje ya sauka daga gadon shi ya faɗa banɗaki brush ya fara yi sannan ya watsa ruwa ya yi alwala ya fito,sai da ya yi sallah sannan ya fita zuwa parlour,a saman dinning table ya tarar da Bilal yana kwasar girki,zama shima ya yi sannan ya gaishe da Bilal tare da bashi haƙuri akan makarar da ya yi, murmushi Bilal ya yi ya ce,
"Ai amarya ta wanke ka fess da soso da sabulu, na zo ina ta sallama na ji shiru shine na haɗa shayi,kamar bazan buɗe wannan food flask ɗin ba,zuciyata ta raya min in buɗe ina bud'ewa kuwa na yi arba da wannan garar, shine na hau zubawa tumbina tinda ku baku ga damar tashi ba."
"Au baku haɗu da ita bama kenan,to ai ka yi kyan kai, da wani ne sai ya tsaya jira sai an ce zauna kaci yana kuma jin yunwa."
"Magana ta gaskiya hakan shine ya dace,baka je gidan jama'a ka hau kwad'ayi kamar ni na haife ka ba,nima rashin kan gado ke damuna shi yasa."
Dariya suka saka a tare sannan Abdul ya kurɓi romon farfesun naman kazar da ya ji kayan ƙamshi,sai da suka ci suka ƙoshi sannan Bilal ya ce,
"Tara fa tayi abokina,kirawo ta mu yi abinda zamu yi sai mu tafi office, a haka ma mun makara ka sani."
Abdul ne ya tashi yana gyara wuyan rigar shi,yana shiga ɗakin Huzaimah idanun shi suka yi masa mugun gamo,domin kuwa kaya ya gani a baje a saman gado,babu babban akwatin ta da mai bi masa,cike da mamaki ya hau k'wala mata kira yana dube-dube,rashin ganin ta a gidan ya gigita Abdul sosai,kiran wayar ta ya soma yi,tana ringing ba a ɗaga ba,ya jima yana kira bata ɗaga ba sai ya fito parlour ya samu Bilal a zaune yana sakace haƙori da tsinken sakace,a kiɗime ya ce masa,
"Ban ganta ba fa Bilal,da ka shigo gidan nan baku haɗu ba?"
Da sauri Bilal ya tashi tsaye ya ce,
"Haram ! Ban gan ta ba ko a hanyar shigowa ta gidan nan kuwa,da na shigo ma ban ganta ba na dai ga abinci a jere da zafin su, alama ta nuna bata jima da barin gidan ba na shigo."
"Ikon Allah ! Bilal taho muje gidan Yayah wataƙila tana can."
Babu ɓata lokaci suka kulle gidan suka nufi gidan babbar yayar su Huzaimah dake a hotoro tsamiyar boka,suna zuwa sai suka tarar da mutanen gidan a babban parlourn gidan,Yayah ta sanya Huzaimah a gaba tana zagin ta,mijin Yayah na ta bata haƙuri,ganin su Abdul bai sa ta dena zagin da take yi ba,dan kuwa tana daga cikin mata irin masu masifar zafin rai ɗin nan.
Kamar magen da aka kama tayi satar kifi haka Abdul ya shiga parlourn jiki a sanyaye,zama suka yi a saman kujerun da ke parlourn,cikin girmamawa suka gaishe da mijin ta da ya ɗan manyanta,sannan suka gaishe ta, ko amsawa bata yi ba ta ce,
"Abdussaboor ashe dama kai munafuki ne? Kai maci amana ne? Ka san da cewa da kai da mace ƴar'uwarta dik ɗaya kuke shine baka sanar da mu ba? To bari kaji na sanar da kai wani abu,ko da boka da malam kake yawo,ko kai ne hogan sarkin karfi sai ka saki Huzaimah,dan ba za ta ci gaba da zama da mace ƴar'uwarta ba."
Cike da ɓacin rai Bilal ya riga Abdul magana ya ce,
"Dakata dan Allah malama ! Ya zaki zauna kina Kiran shi da mace? Dik ba ta dalilin irin rashin hankalin ku na mata ya zama haka ba? Ce maki akai zai dawwama a haka? Haƙuri muka zo mu bata yana nan yana shan magani inshaa Allahu komai ya kusan zuwa karshe,a yanda ya faɗa min ma da jiya ta yi haƙuri wataƙila da wata maganar ma ake ba wannan ba."
A harzuƙe Yayah ta miƙe ta tsaya a saman kan Bilal tana nuna shi da yatsan ta manuni ta ce,
"Kai kuma a wanne matsayi kake a wajen shi da har ina magana zaka shiga?"
Abdul ne ya ɗan sosa ƙeya sannan ya ce,
"A yi haƙuri Yayah,shi ɗin ɗan'uwana ne,dan girman Allah kuyi hakuri da abinda ya faru,na so na sanar daku matsala ta tin kafin aure,ita Huzaimah ita tace zata iya zama dani a haka har na samu sauƙi,sannan ta roƙi kar na sanar da kowa...."
"Dakata min malam ! Da ace wani ƙaton laifin ta aikata da tini ka ɗauki mataki kuma ka sanar da duniya,amma da yake harka ce ta rufa maka asiri shi yasa ka ke ganin ya dace ku ɓoye wannan babbar matsalar ko? To kaji na rantse dai babu inda zaka je sai ka sakar min ƙanwa,tana nan da masoya ba babu ba, tana gama idda zata yi auren ta."
"Huzaimah yanzu ba zaki iya kara haƙuri akan wanda kika yi a baya ba mu ci gaba da..."
Cike da jin kunya Huzaimah ta ce,
"Ba zan iya ba gaskiya, haƙuri na ya ƙare,dan Allah ka sawwaƙe min wannan auren na gaji,dan Allah ba dan ni ba."
Wani irin abu ne mai zafi da maƙaƙi ya tokarewa Abdul a wuya,cikin dakiya ya miƙe tsaye,Bilal na ganin yanda Abdul ya miƙe a zafafe sai ya kama hannun shi ya girgiza masa kai, cikin sanyin murya Bilal ya sassauto ya ce,
"Indai maganata ta ɓata maku rai dan Allah kuyi haƙuri,ina nemawa aboki na alfarmar wata ɗaya,idan bai ji sauƙi ba duk matakin da ya kamata ku ɗauka na raba wannan auren ku ɗauka."
"Ba zai yuwu ba,ba zamu bari ta ƙara kwana ɗaya a gidan azzalumi ba,ya sawwaƙe mata yanzun nan kawai."
"Ke Ruƙayya meye wai haka kike yi ne? Yanzu ni ban isa na baki haƙuri ki ji ba? Tin kafin yaran nan su zo nake faman bin kan ku amma kina ta cijewa,idan ya sake ta kina da wanda zaki aura mata ne?"
"Ko bani da shi zan nema mata,haka kawai yarinya da ƙuruciyar ta a cuce ta? Zaka sake ta ko baza ka sake ta ba mu haɗu a kotu?"
Cikin ɗacin zuciya Abdul ya ce,
"Allah ya kiyashe ni sake komawa kotu akan matsalar iyali,taje na sake ta saki ɗaya Allah ya haɗa kowa da rabon shi."
Yana gama magana ya bar gidan cikin sauri Bilal na take masa baya,Huzaimah kuwa kuka ta rushe da shi tana leƙen su ta window,Yayah ce ta ɗura mata ashar sannan ta ce,
"Dawo ki zauna sokuwa kawai,haka zaki zauna baki san menene jin daɗin gidan aure ba? Ga ƙawayen ki da ƙannen ki nan na ta haihuwa a dangi,ke haka zaki zauna da masakin namiji ba zai iya yi maki ciki ba balle ki haihu?"
Da gudu Huzaimah ta bar wajen ta wuce ɗakin da take sauka idan tazo gidan yayar tata,gado ta faɗa tana kuka tare da data sanin bata baro ɗakin mijin ta ba ta ƙara haƙuri har ya samu sauƙi,yanzu shikenan ta zama ƙaramar bazawara,babu wanda zai yarda bata taɓa mu'amala da namiji ba,kuka ta sake rushewa da shi ta ƙudindine a cikin bargo.
A can parlour kuwa kaca-kaca Yayah da mijin ta suka yi kafin daga baya ya bar mata gidan,waya ta ɗauka ta kira mahaifiyarsu ta sanar da ita duk abinda ke faruwa,nan take mahaifiyarsu ta dinga masifa itama,sannan ta jinjinawa Yayah akan ƙoƙarin da tayi na raba ƙanwar tata da zaman wahala da ta yi,mahaifin su ma da ya ji abinda ya faru be ji daɗi ba,amma yaso Abdul ya sanar da su iyayen ta baki da baki kafin auren,idan yaso sai su zaɓi su bashi ƴar su ko su hana shi,dik da haka yaso ace auren bai rabu ba an ƙara masa haƙuri a ga zuwa wasu ƴan watanni ko zai sami lafiya,daga karshe fatan alkhairi ya yi sannan ya ce zai aiko a ɗakko Huzaimah ta dawo gaban su ta yi iddar ta.
Abdul kuwa kasa zuwa office ya yi a wannan ranar shida Bilal,daga ƙarshe Bilal ne ya kira ya bada uzirin Abdul baya jin daɗi ba za su samu damar zuwa ba,tinda suka zauna babu wanda ya ce da kowa komai,babu abinda Abdul ke tunawa sai dattako da nagartar Huzaimah,yanzu gashi ya rasa ta dik ta sanadiyyar Hadiza,to shi a duniya me zai ce soyayyar Hadiza ta ƙare shi da shi? Amir ya tuna sai ya lumshe ido ya sake miƙe ƙafa a doguwar kujerar da ya zauna,ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke kafin ya ce,
"Ta ina zan fara sanar da Innah da Mai Martaba na rabu da matata? Me mutane zasu kira ni a yanzu? Wacece zata sake aure na idan wannan maganar ta bazu a gari? Hadiza ta cuce ni,ta nakasa ni Bilal"
Hawaye ne masu mugun zafi suka sirnanowa Abdul daga idanun da zuwa kuncin shi,cike da tausayawa Bilal ya ce,
"Allah yana sane da kai, ba zai bari ka wulaƙanta ba,kar ka damu komai ya yi farko zai yi ƙarshe,ban sani ba wataƙila waɗannan abubuwan da sukai ta faruwa ne ya sanya tin fil azal bana kaunar yarinyar nan, kallon muguwa nake yi mata,amma babu komai mai afkuwa ta riga ta afku,Allah ya kawo mafita mafi alkhairi."
"Amin Bilal."
Lokacin sallar azahar nayi suka yi alwala suka tafi masallaci,daga nan suka tsaya suka siyo abinci suka koma gidan,kwanukan da suka ci na safe Abdul ya kalla ya ce,
"Allah sarki ƴar albarka, bata tafi ba sai da ta ajiye min abinda zan ci,Allah kasa hakan shine yafi zama alkhairi a rayuwar mu baki ɗaya,har abada ba zan manta da soyayyar da Huzaimah ta nuna min ba a rayuwa,ita ɗin ƴar adam ce,dole zata buƙaci namiji dama ko bajima ko ba dad'e,Allah ka zaɓa mata namiji mai nagarta ya aure ta ya bata dikkan kulawar da ta dace, Allah ka bani lafiya nima."
"Amin."
Shine abinda Bilal ya iya amsawa kawai cike da tausayawa,abinci suka zauna suka ci suka ƙoshi kafin daga bisani Bilal ya yiwa Abdul sallama ya tafi gidan shi.
*****************************
Ɗan Liti ya yi mamaki ƙwarai da ya ji wanda Mommy ta tsayar a matsayin wanda zata aura, amma sai ya shanye mamakin shi ya bi ra'ayin ta, ana sakkowa daga sallar azahar ranar asabar aka daura mata aure akan sadaki naira dubu hamsin,cike da farin ciki Sule ya iso gida ya sanar da Hadiza dake ta faman kukan baƙin ciki,ba dan shawarar da Naja ta bata ba babu abinda zai sanya ta auren wannan bawan Allah'n.
Babu ɓata lokacin komai dare na yi Naja da ƙawayen ta suka raka Mommy ɗakin mijin ta, kamar koda yaushe Baaba ta yi bajinta wajen yiwa Mommy gara dik da cewa bazawara ce,a cewar ta ai aure aure ne,dan haka ita kuma wannan shine gudummawar ta.
Saddiƙa taso zuwa sosai amma yanayin karatun da ta fara yi ne ya hana ta zuwa,sai fatan alkhairi da ta yi wa Mommy sannan ta tura mata gudummawar dubu ɗari,Mommy ta yi mata godiya sosai saboda ba karamin daɗin samun kud'in ta ji ba,dik wasu kuɗi da ta mallaka sun ƙare a siyan kayan ɗaki da kud'in aiki da za a yi mata,wanda wannan dik a cikin shawarar da Naja ke bata ne,Ameerah kuwa gargaɗin Mommy ta dinga yi akan wannan plan ɗin da suka haɗa ta dinga yi,Innoh kuwa ta gaji da ganin shige da ficen Mommy a cikin gidan,dan haka auren nata tamkar sauke nauyi ne a kan ta,tinda ko tsinke Mommy bata kauda mata a gidan ita ke yin abun ta,sannan ta yi musu girkin rana da dare, da safe ta hura wuta ta yi d'umame ta dama kunu,ga alalen siyarwa da take yi,gaba ɗaya aiki ya haɗu ya yi mata yawa.
Ba dan Ameerah ta so ba haka ta baro gidan mijin ta akai rakiyar amarya da ita,tin daga soron gidan ta hau yatsina fuska,koda Ɗan liti yake talaka gidan shi yafi wasu gidajen da yawa a cikin garin kyau,Mommy kuwa da ta sanya ƙafa a gidan sai kukan ta ya ƙaru tana jin cewa anya bata kawo kanta gidan tashin hankali gidan bala'i da masifa ba kuwa?............
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 96:
Innoh ce zaune a tsakar gida gaban murhu tana kwasar garwashin da za ta shiga dashi ɗaki,sakamakon sanyin da ake busawa.Baaba kuwa na duƙe tana tattara ƴan komatsan ta da ta yi zaman tsakar gida zata koma ɗaki. Sallama suka ji an rabka tare da faɗin,
"Ranki ya daɗe bismillah."
Ɗaga kai Innoh da Baaba suka yi a tare dan son ganin wadda zata shiga gidan nasu,Innah Laminde suka gani tsaye sanye da babban mayafi hannun ta riƙe da carbi tana ja,gefen ta da bayan ta kuwa wasu mata ne guda uku tsaye suna take mata baya,cikin sauri Baaba ta katse shirun da wajen ya ɗauka ta hanyar shimfiɗawa Innah Laminde tabarma sannan ta ce,
"Ranki shi daɗe bismillah ga wajen zama,ke Innoh taho ku gaisa mana."
Sai a wannan lokacin ne giyar mamaki ta saki Innoh,a tarihin garin Ba Mugu kafff babu wanda Innah Laminde ke zuwa gidan shi idan ba gaisuwar rasuwa ko ta ciwon da ya yi fice aka sani ba,sai ko gidan ƙanwar ta wato Ta Annabi shima sai da ƙwaƙƙwaran dalili,wannan shine dalilin da yasa suka shiga cikin mamaki gaba d'ayan su.
Gyaran murya Innah Laminde tayi sannan ta ce,
"An wuni lafiya? Ya aka ji da hidima da taron jama'a?."
Cikin sauri Innoh ta ce,
"Ranki shi daɗe alhamdulillahi mun godewa Allah an yi taro lafiya an gama lafiya,sai dai ina mamakin zuwan da kika yi da kan ki ba aike ba."
"Allah sarki ! To ai kuwa ya kamata in tsamo ki daga rijiyar mamakin da kika afka ta hanyar sanar da ku abinda ya kawo mu,ina taya ku murnar aure da Hadiza ta ɗaura a yau,Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a mai albarka."
"Amin ya Allah,godiya muke yi ranki ya dad'e,ai abun ne yazo babu shiri bagatatan,shi yasa ba kowa aka sanarwa ba."
"Allah sarki, ai babu komai,dama babban abinda ya kawo mu shine tafiya da Amir,tinda dai mahaifiyar shi ta sake ɗaura wani auren to muna da buƙatar jikan mu a kusa damu,uban shi na da wata matar da zata riƙe shi,koda babu wata matar ni zan riƙe shi,sanin kan ku ne ɗan Abdussaboor ba zai yi agolanci a wani gidan ba,wannan abun kunya ne ga masarautar garin nan."
Cike da girmamawa Baaba ta ce,
"Ranki ya daɗe ai tafiya da yaro ba zai zama matsala ba,sai dai muna roƙon a bamu nan da sati biyu zamu kawo shi da kammu har gida."
"To alhamdulillahi tinda an samu maslaha,Allah ya kaimu sati biyun da rai da lafiya,Allah kuma ya baiwa Hadiza zaman lafiya a gidan mijin ta,mu zamu tafi."
Cikin azama Baaba ta shiga ɗakin ta ta d'akko turare da goro ta baiwa ɗaya daga cikin matan da suka rako Innah Laminde, godiya suka yi wa Baaba sannan suka tafi,har suka tafi Baaba ta fara naɗe shimfiɗar ta Innoh na nan shuke kamar shikakkiyar dusa a wajen,sai da Baaba ta ce,
"To kin dai ji abinda Laminde ta ce,sai ki fara haɗa masa kayan sa a wanke su tass dan ba za a kai yaro da dauɗa ba."
Cike da rashin mutunci Innoh ta mirgina ta tashi tana haki,sai da ta kama ƙugu da hannu ɗaya sannan ta ce,
"Wai ni Yaya me yasa kike yi min shisshigi a lamura na ne? Yanzu me yasa zaki ce a bari sai nan da sati biyu za a kai yaro? Ke zaki kula min da shi har tsawon sati biyun ta cika? Taya Allah ya kawo min sauƙi har tsakar gida ki ƙara janyo min wahalar raino kuma?"
Baki Baaba ta saki tana mamakin hali irin na Innoh,cike da nuna tsantsar mamaki Baaba ta ce,
"Shi wannan ɗan tayin ne rainon shi da wahala? Lallai idan haka kike nufi kin yi asara Innoh,wai keee me yasa baki da hankali ne? Yaushe zaki yi hankali ki dena son kan ki ki so mutanen da ke zagaye dake domin Allah? Yarinyar nan Mommy menene bata yi maki ba wanda ƴa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 60 Chapter of 70