Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
maki," Sai da ta gama yatsinar ta tana ta zabga tsaki sannan ta sauka daga gado tace, "Dubu ɗari biyu, tabdijam banda su nikam gaskiya,zan dai baka dubu goma gudummawa ta Allah sanya alheri," "Ba komai na gode,sai anjima." Ba tare da ta furta komai ba ta kashe wayar ta tana zabga wa wayar harara kamar tana ganin shamsun,cikin masifa take faɗin, "Wato ga ƴar iska ta tafi sayar da jikin ta ta kawo muku kuɗi ko? Ai wannan karon zaku ga wulaƙanci daga waje na,kowa ya samu ya zuba a rumbun sa kawai," Hannu Amy ta sanya ta ja Billy ta kwantar da ita a saman gado sannan ta yi mata rumfa tana sumbatar ta tace, "Love ke da waye ne kike ta mita kika barni ina jiran ki?" Murmushi Billy tayi sannan tace, "Ba kowa bane, mu ɗora daga inda muka tsaya Sweetheart." Billy na fad'ar haka suka ci gaba da aikata masha'ar su da suke ganin dik duniya babu abinda ya kai musu ita daɗi,Amy na samun ƙololuwar gamsuwa da Billy shine dalilin daya sa ta dage ta manne mata har take wani tunani akan Billyn, ta riga ta ƙudirta sanar da ita abinda ke zuciyar ta game da ita sai dai tana jin tsoron amsar da zata bata. Suna nan manne da junan su bayan sun dawo cikin hayyacin su Amy ta sumbaci Billy a kafad'a tace, "Baby ina so na yi maki wata tambaya, dan Allah ki bani amsa tsakanin ki da Allah,kin ga dai gidana, kin ga motocin da nake da su maza da dama basu da irin su,sannan kin ga yanda nake samun kuɗi ta hanyar Youtube channel d'ina da kasuwanci na, ɓangare ɗaya kuma na nuna maki takardar yarjejeniyar dake tsakani na da turawan da suka ɗauke ni aikin yaɗa wannan ƙungiyar tamu ta auren jinsi, kuɗi suke sakar min manyan da zan iya maida wanda naso mai kuɗi cikin kwana ɗaya,dan haka na tabbata ba zaki yi danasanin kasancewa dani ba idan nace ki aure ni," (channel ɗin littafan batsa ake karantawa shi yasa take da subscribers da yawa a sati daya idan aka yi posting tana samun wanda suka gani sama da mutum dubu dari biyar,abun takaicin kuma akwai channels da ake karanta littattafai masu ma'ana da faɗakarwa mutane basu cika bin su bama balle su saurare su,Channels ɗin malamai kuwa su aka fi rainawa sai idan malami ya kai malami ne yake samun mutane dake kulawa da channel ɗin sa. Allah yasa mu dace mu gane gaskiya mu gyara kurakuren mu) Maganar Amy ta zo wa Billy a bazata,dan haka cikin sauri ta d'aga kai ta kalli Amy dan ta gasgata maganar da ta sanar da ita a yanzu,cikin rawar baki da nuna ita ɗin ashe iskancin nata bai kai ko ina ba ta furta kalmar, "Auren Jinsi fa kenan?............... [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ *MAHREEN 1K* *MAIDA TSOHUWA YARINYA 1K* *KYAKKYAWAR FAHIMTA 500* PAGE 53: Shiru Billy tayi tana tunanin irin daular da ta ga Amy na da shi, kama daga kan motoci, gidaje da tsabar nerori da daloli,ta tabbata dik macen da zata mallaki gida a kasar turawa nata na kanta ba ƙaramar mace bace. Wata zuciyar kuwa Ƙauyen Ba mugu ta hango mata,iyayen ta, ƴan uwan ta da rayuwar da taso tayi bayan ta gama yawon ta, a baya ta tsara da ta gama bariki zata koma gida ta tuba tayi aure, amma yanzu da ta tina mijin da take so Mommy tayi mata shigar sauri akan shi, sai kawai taji bata da wani burin da ya wuce na ta amincewa Amy da buƙatar ta na su yi aure,ko babu komai zata yi rayuwa ta ƴanci da jin daɗi,abinda take nema na dukiya, suna da ɗaukaka a harkar tasu zata same shi. Juyawa tayi ta maida Amy ƙasan ta ta sumbace ta sannan tace, "Na amince zan aure ki,amma da sharad'i," Murmushi Amy tayi cike da jin daɗin nasarar da ta samu na dulmiyar da Billy da tayi tace, "Ina jin ki my love, ki faɗi sharad'in ki ko menene na ma amince tin kafin na jishi,ke kaɗai nake so a yanzu, bayan ke babu abinda yake da mahimmanci a rayuwa ta a yanzu," Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Billy, dama akwai wanda zai so ta har haka? Wataƙila dan babu Mommy a kusa ne, da tana nan da ta k'wace mata Amy ba yanda za a yi a yi mata irin wannan son Mommy na kusa, lallai rabuwar su ma alkhairi ne a wajen ta,kwantawa tayi a saman gadon ta tallabe kan ta tana fuskantar Amy kafin tace, "Sharad'i na ba wani abu bane mai wahala a wajen ki, ina so idan za a yi wannan auren a yi shi a can ƙasar waje ba a Nigeria ba,sannan ina so idan an yi mana auren na zama ina da wani kaso a cikin dukiyar ki, bayan haka idan mun dawo zaki haɗa mana party da mutanen mu zan kuma gayyato Hajiyata," Tinda Billy ta fara tattab'a sharad'in ta Amy take zabga murmushi tana nuna amincewar ta akan hakan,sanda taji Billy tayi zancen gayyatar Hajiya K'waisa sai ta sauka daga gadon tana fad'in, "Hell no babe ! Ba za mu gayyaci wannan zindiƙin ƙaton ba,ki sauya wani sharad'in amma banda wannan," "Haba Sweetheart ki manta komai mana,ki duba fa ki ga yanda ɗaukaka ta same ki, ai ko dan ki kirawo shi yaga yanda arziki ya mamaye ki kin gayyace shi," Shiru Amy ta yi zuwa wani lokacin tana nazari kafin daga baya tace, "Na amince yanzu yaushe kike so mu tafi a d'aura mana auren? dan ni fa ban ƙi ki ce mu tafi yau ba," "Mu bari zuwa wani satin mai zuwa ina so na gyara passport ɗina," "Ok wani satin then,I love you," Murmushi Billy tayi sannan ta mayar mata da martani da, "I love you too," Hira suka ci gaba da yi da tsare-tsaren yanda za su gudanar da shagalin auren nasu da Allah yayi haramci akai,ya la'anci masu aikatawa, yake tsananin fushi akan wanda suke aikata irin wannan zunubin. ************************ Shamsu ne tsaye wajen masu kayan gado suna ta ciniki, mamaki nake yi shin bayan kayan d'akin da aka yi wa Ameerah me kuma ya kawo shi nan wajen saida kayan d'aki? Ciniki suka gama tsafff tare da alƙawarin gobe za su je suga kayan idan yayi musu a yanda shamsu ke son siyarwa sai su bada kuɗi,idan bai yi musu ba dole ya rage musu wani abu, nan take na gane ashe shamsu ba siya zai yi ba, shi ne zai siyar,sallama yayi musu ya kama hanya ya nufi wajen masu saida tsire ya siyi ƙulli biyu, ɗaya na dubu biyu ɗaya na dubu ɗaya, ana gama ƙulla masa ya wuce shago ya siyo lemon roba na fanta ya sai dangin su sweet da chewing gum har ma da biscuit sannan ya wuce gidan su Ameerah. Yana aikawa a kira ta ta fito tana wani yatsina,tana ganin shi da ledoji a hannu ta washe baki tana yi masa sannu da zuwa sannan ta koma cikin gida ta samo masa tabarma a ɗakin Innoh ta koma soron ta shimfiɗa masa. Gaishe shi tayi sannan tayi shiru tana jiran ya bata abinda ya kai mata, Shamsu kuwa daɗin yanda ta saki jiki dashi ne ya sanya shi miƙa mata ledojin dika bai ware nashi ba, karɓewa tayi ta hau yi masa godiya, kallon ta yayi cike da shauƙi yace, "Gobe iwar haka muna tare da junan mu masoyiya ta,na matsu na gan ki a d'aki na a matsayin mata ta Ameerah," "Hummm" Kawai ta furta tana wani abu kamar mai jin kunya,a haka hirar su ta ci gaba har dai shamsu ya samu damar tattab'a jikin ta ya wuce gida,abinda Shamsu yayi mata yayi matuƙar jan ra'ayin Ameerah, kusan abinda kullum take fatan taga tana aikatawa kenan saboda kallon fina-finan batsa da ya zame mata jiki a yanzu,wata irin buƙatar kasancewa da shamsu ke d'awainiya da ita musamman da yanzu ta rage biyawa kanta buƙata da take yi saboda wahalar da ta sha ta ƙuraje da warin gaba,nan take ta hau addu'ar Allah yasa goben a kai ta gidan mijin ta itama ta ji abinda ake ji a gidan aure. Karo suka yi da Innoh dake jingine a jikin gini tana jiran shigar Ameerahn dan kar ta shammace ta ta shige bata bata komai ba,a tsorace Ameerah ta kurma ihu ta falfala da gudu zuwa ɗakin ta, tana shiga ta rufe ƙofa tana ci gaba da ihun a kawo mata agaji ta dunguri aljani. Cikin tsananin jin haushi Innoh tace, "Ke dan uwar ki Naja buɗe ƙofar nan ba aljani kika dungura ba ni ce,ki fito ki kawo ledar da ya kawo miki mu raba ko nayi miki ba daɗi ,na san halin ki na rowa tsaff shi yasa na lab'e dan in ga me zai kawo miki," A hankali natsuwa ta fara shigar Ameerah haushi da takaici tare da baƙin ciki na maye gurbin tashin hankalin da ta shiga,wannan wace iriyar rayuwa ce haka Innoh ke yi? Yanzu kenan akan idon ta shamsu ya gama jagwalgwala ta har ya biya buƙatar shi? Bata buɗe ƙofar ba sai da ta boye babban ƙunshin me ɗauke da nama, lemo, chewing gum,da sweets sannan ta ɗauki ƙasaramin ƙunshi me lemo ɗaya nama ƙunshi ɗaya, tana bud'ewa Innoh ta afka d'akin tana muzurai tare da zagin Ameerah, cikin fushi Ameerah tace, "Yasin Innoh idan baki dena lab'e ba babu ruwa na idan Allah ya sa ki a wuta,miji da mata ne mu fa ni da shamsu ba wai saurayi da budurwa ba balle ki lab'e ki ga me muke yi,haba Innoh haba Innoh, yanzu kenan fa dik abinda muka yi kin gama gani," (Abun takaicin kuma ɗanta na can na iskanci a d'aki ta waya bata taɓa yi masa lab'e ba dan ta san me yake aikatawa,balle ta yi masa gyara) Kunya ce ta ɗan kama Innoh ta hau susar diddigar kan ta,cikin borin kunya tace, "Haram ! Zuwa na kenan naga ya miƙa miki leda shine na tsaya ki zo a raba ko ki sammin abinda aka kawo miki, sannan ni ba zuwa nayi na musamman dan na leƙa ku ba, b'uruntu naji na zaci awaki ne suka shigo, gudun kar suyi b'arna shine na leƙa,ni dai buɗe muga menene dan na ji ƙamshin ƙuli," Maida ledar bayan ta Ameerah tayi tace, "Ai kuwa idan dan kin ga sanda ya bani ledar nan kin jima a lab'e,ina fita kema kika biyo ni, dan kuwa ba sai da zai tafi ya bani ba," Cike da borin kunya Innoh ta hau zage-zage ta bar ɗakin tana faɗin, "Shegiya marowaciya, inda Hadiza ta fiki kenan,nan nan abincin gidan ta ta zubo tace a kawo mana mu ci, amma ke gaki a gidan ma an baki kina b'oye wa kar na ci,to gaki ga ƙunshin nan ki ci ke kaɗai kiyi zawo ke kaɗai matsiyaciyar yarinya me shegiyar rowa kawai," Ita dai Ameerah ta ji daɗi da Innoh ta tafi bata karb'i ledar hannun ta ba, kuma ta tabbata gobe ba zata sake yi mata lab'e ba, sai da ta rufe ƙofar ta sannan ta samu waje ta baje dika kayan daɗin da Shamsu ya kawo mata,murmushi tayi da ta tina da abubuwan da yayi mata, nan take taji tana iya zaman aure da Shamsu indai zai dinga faranta mata rai irin haka. Babu b'ata lokaci ta hau lodar nama tana shan lemo,kamar wata mayya haka ta dinga cin naman nan tana zare ido, da ta ji motsin Innoh a tsakar gida sai ta rage taunawa,ita kuwa Innoh tana can tana masifa tare da jiran Ɗan liti ya dawo ko da masifa da bala'i ne sai ta ci tsire zata kwanta bacci. Tana nan tana sintiri a tsakar gida kamar ƴar ƙato da goran unguwa Ɗan liti ya dawo,adaidaita sahun shi ya shigar saman barandar ƙofar gidan ya kulle sannan ya shiga gidan, ya kama ƙofar gidan zai rufe kenan Innoh ta kwasa a guje mazaunai na rinjayar ta ta isa wajen shi tace, "Kar ka kulle gidan nan yanzu Malam !" A tsorace Ɗan liti ya qame a jikin ƙyaure yana zaro ido, ganin ya tsorata da bazatan da tayi masa ne yasa ta sassauta murya tace, "Malam na roƙe ka da Allah ka taimaka ka siyo min ƙunshin tsire, idan ka kawo min zan baka labarin abinda ke faruwa har nace ka siyo tsiren,yanzu lokaci na ƙurewa kar su tashi," "Innoh babu wasu isassun kuɗi a waje na, wannan kuɗin na karin safe ne,idan aka siyo nama ɗari biyar ce zata saura min," Kuka Innoh ta fashe da shi ta wuce cikin gida ba tare da ta ce wa Ɗan liti komai ba, ganin Innoh na kuka ne ya sanya Ɗan liti barin gidan jiki a sab'ule ya wuce bakin kasuwa dan siyo mata tsire. Dariya Innoh ta saki sanda ta koma d'aki ta ji shiru be bi bayan ta ba, ta tabbata ya wuce siyo tsiren kenan, zama tayi tana nazarin yanda zata ci wa Ameerah mutunci zuwa safiya. Tana nan zaune Ɗan liti ya dawo,ledar ya miƙa mata ta Karb'a ta raba musu naman ta zuba masa nasa akan shinkafa da waken da ta dafa musu, naman ta hau ci tana lumshe ido, cikin santi ta labarta wa Ɗan liti abinda ya faru zuwan shamsu, cikin takaici Ɗan liti yace, "Amma dai Innoh kin ji kunya alqur'an,yanzu Ameerah kika koma yiwa lab'e tinda Yadikon Sule ta rasu? Lallai tin yanzu zan fara yi wa Sule addu'ar kar Allah ya sa ya zauna a gidan nan idan yayi aure, Allah ya hore masa yayi gini a wani wajen ya zauna," Cike da ɓacin rai ya ture kwanon abincin ya fita tsakar gida ya wanke hannu da bakin shi, ɗakin Yadikon sule ya kalla yaji wata k'walla na shirin gangarowa daga idanun shi, ba kaɗan ba yayi kewar matar shi da yaran shi, ya rasa me ke danne masa zuciya da tunanin shi a dik sanda yayi nufin zuwa wajen yaran shi ya gan su,tsayuwa ya gama da tunane-tunane ya koma ɗakin ya haye gado ya kwanta zuciyar shi sam babu daɗi. *********************** Washegari da safe masu siyan gado suka sallama gidan Mai Dusa dan kwashe kayan gadon da Sule ya siyar musu. Tin daren jiya da Sule ya koma gida ya yanka ƙarya akan yayi waya da Billy ita tace ya ɗauki kayan ɗakin ta ya siyar ya haɗa lefe ita bata da kud'in da zata bashi da ya wuce dubu goma. Mahaifiyar ta tayi baƙin ciki sosai kuma ta fusata k'warai saboda ta san dik abinda zai sa Billy ta saida kayan ɗakin da kullum take zuzuta tsada da kyan su to ba dawowa zata yi ba kenan,cikin fushi a daren ta furta, 'Au haka tace? Allah ya bata sa'a,' Tana faɗin haka ta shige d'akin ta ta kwanta tana zubar da hawayen baƙin ciki da nadamar rashin baiwa Bilkisun ta tarbiyyar arziƙi da bata yi ba. Masu siyan gado kuwa sun ji daɗin siyan kayan gadon Billy domin kuwa tabbas masu kyau ne da tsada kamar yanda take yawan faɗa, sai dai shamsu ya caka musu yayi musu tsada, sun so su cuce shi amma ya nuna musu ya san kan kasuwa,a haka suka loda kayan a babbar motar da suka zo da ita suka bashi kud'in shi kimanin dubu ɗari da hamsin suka tafi. Murna shamsu ya dinga yi, ko gida bai shiga ba ya wuce gidan su Ameerah direct......... [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️ ✨ *MAHREEN 1K* *MAIDA TSOHUWA YARINYA 1K* *KYAKKYAWAR FAHIMTA 500* PAGE 54: Kwance take laga-laga a tsakar gida dik jikin ta ya ɓaci da zawo da amai, tin Innoh nayi mata dariya tana faɗin, "Allah ya ƙara marowaciyar banza da wofi, ki rasa wanda zaki yi wa rowa sai uwar da ta haife ki," Har sai da ta dawo tana faɗin, "Ohh ni Innoh matar Ɗan liti anya ba guba yaron nan ya baki ba dan ki ci ki mutu kowa ya huta da halin ki? Allah ya baki lafiya taso na kai ki bayi ki dena ɓata min tsakar gida, ji yanda ƙudaje ke bin ki Ameerah," Dik yanda Innoh taso ta taimaka wa Ameerah ta kasa, ƙarshe tunawa tayi da Baabaa da ta ga jikokin ta na zawo da amai sai ta jiƙa musu kuka ta basu, da izinin Allah suna sha sai ciki ya d'aure ya dawo dai-dai, da gudu Innoh ta afka madafi ta haɗawa Ameerah kuka ta tashe ta ta bata a baki, ta na shanyewa ta koma ta kwanta tana murƙususu. Daren jiya Ameerah gaba ɗaya ta saka naman nan mai ƙuli da farin maggi a gaba ta cinye dika ita kaɗai, ga lemo da ta sha mai zaƙi roba biyu,wannan dalilin ne ya sanya cikin ta lalacewa, Innoh na zaune ta tasa ta a gaba tana ta zabga mata sannu, ta tuna kalmar da ta faɗawa Ameerah a daren ranar, 'Ki ci kiyi zawo,' Nan take ta hau nadama a ranta tana faɗin, 'Allah ka sa yarinyar nan ta warke,wannan zawayi yayi yawa,' Tabbas yau Innoh ta gano kaifin da bakin uwa ke da shi akan yaran ta, wataƙila da bata yi mata mugun fata ba da haka bata faru ba,suna nan zaune Ameerah zawo ya tsaya aman ma ya tsaya sai rashin ƙarfin jiki, Innoh kuwa ta ce ba zata iya wankin kashi ba dan haka jira take yi ta samu ƙwarin jikin ta sai ta tashi ta yi wanka da ruwan da Innoh ta zuba mata. Sallamar Shamsu ce ta sanya Ameerah buɗe idanu da sauri tana wurga su zuwa hanyar shiga gidan, fatan ta bai wuce Allah ya sa kar ya shiga gidan ba saboda kar ya ganta a wannan mawuyacin halin da take ciki na amai da gudawa, Innoh ce ta ware murya tace masa, "Kai shigo ciki dan wadda ka zo wajen nata bata da lafiya ba iya fitowa zata yi ba," Rasa inda Ameerah ta samu ƙarfin jiki tayi, tana tashi sai ta sungumi babbar butar da Innoh ta zuba mata ruwa dan shiga bandaki ta gudu bayin,tana shiga ta durƙusa tana maida numfashi, jiki babu ƙwari ta cire kayan ta ta hau wanka da ruwan butar, bata fito ba sai da ta gyara jikin ta tsaf,Innoh ce ta miƙa mata zani da hijabi tana faɗin, "Kiyi sauri ki fito yaron nan na jiran ki," "To" Shine kawai abinda ta furta ta d'aura zani ta sanya hijabi a jikin ta, kayan da ta cire ta d'ebo ta zuba a bokitin ƙarfe ta ja ruwa a rijiya ta zuba musu, Shamsu na zaune a tabarmar da Innoh ta shimfid'a masa, kallon Ameerah yayi yaga ta faɗa masa kamar wadda ta kwana rashin lafiya, maida kanshi ƙasa yayi yana jiran ta gama abinda take yi tazo su gaisa ya wuce kasuwa. Bayan Ameerah ta gama dik abinda take yi ne taje inda Shamsu ke zaune ta ja kujera ƴar tsuguno ta zauna, kallon Inda Innoh ta zauna tayi dan taga ko zata tashi ta basu waje, sai taga Innoh bata da niyyar tashi, cikin ɗan haɗe fuska tace, "Innoh ki ɗan bamu waje mana dan Allah," Washe baki tayi tace, "Kayya ai da kun yi hirar ku hankali na ma na can wata duniyar," Tashi tayi ta shiga d'aki ba dan ta so ba, tana shiga ta maƙale a jikin labule ta kasa kunne dan ta ji me za a ce, Ameerah ta san halin mahaifiyar ta sarai dan haka hannun Shamsu ta kama a hankali suka shige d'akin ta suka rufe ƙofa, da jin haka sai Innoh ta kama baki ta damƙe tare da waro idanu waje,me yaran nan ke shirin aikatawa a gidan? Shamsu kuwa na ganin haka sai ya hau washe baki yana murna, a zaton shi wani abu Ameerah keso su aikata shi yasa ta ja shi d'aki, suna shiga ta samu waje a katifar da mommy ta bari ta zauna tana satar kallon aljihun shi da ta hango damin kuɗi a ciki,gefen katifar ta nuna masa tace ma masa, "Bismillah zauna ka tsaya kamar wani soja,ya kamata fa kayi ka kawo kuɗin lefen nan a samu a gama dik abinda ya dace, na matsu nima na ganni a ɗakin miji na kamar kowacce matar aure," Washe baki Shamsu yayi ya zauna a kusa da ita, wani irin wari yaji ya daki hancin shi, wari ne da ya kasa tantance daga inda yake fita a jikin Ameerah, cikin dabara ya janye jikin shi ya koma gefe yana zaro idanu waje, hannu ya sanya a aljihun shi ya ɗakko dubu ɗari ya miƙa mata yace, "Ga wannan, dubu ɗari ne ki haɗa lefen ki, ni kuma zan yi amfani da kuɗin waje na na gyara shago na na ƙofar gidan mu na haɗa solar a dinga kawo caji ina yi wa mutane turin fina-finai da waƙoƙi saboda mu dinga samun na cefane," "Ai kuwa shawarar nan tayi kyau, dama ko shekaran jiya sai da Yah Sule ya gama mitar baka da aikin yi, to alhamdulillahi ga aiki ya samu," "Ai dama rayuwar nan komai a hankali ake gina shi, bari na je kasuwa naga yanda hali zai yi,kar ki manta a siyo turare da yawa a kayan lefen nan dan Allah." "To ba zan manta ba Allah ya bada sa'a," Shamsu ne yayi saurin buɗe ƙofa ya shaƙi wata iskar 'yanci,hamdala yayi cikin sauri ya fita ya bar gidan, Ameerah kuwa cikin sauri ta zare dubu ashirin ta b'oye,kafin Innoh ta shiga ɗakin nata ta gama b'oyewa ta miƙe zata fita suka ci karo a hanya, kallon kallo suka hau yi wa juna, Innoh ce tace, "Yanzu Ameerah iskancin naki har ya kai na ki ja namiji ɗa...." Maganar tace ta maƙale a dai-dai lokacin da Ameerah ta zaro maƙudan kuɗi ta miƙawa Innoh, Cikin sauri Innoh tace, "Ko da yake ma mace da mijin ta ai kai bawa ba ka sa musu ido ba, wannan kuma na maye?" "Na lefe na mana, yanzu ni dai dan Allah a kirawo Aunty Naja da Mommy su zo a san ya ake ciki ,na gaji da zaman gidan nan ina so a had'o kaya na dai-dai kud'in nan daga yau zuwa gobe a kai ni d'aki na," "Inshaa Allahu kuwa gobe a d'akin ki zaki kwana,ina zuwa," Waje ta fita ta ɗauki wayar ta ta kirawo Mommy ta kirawo Naja ta sanar da su abinda ke faruwa, alƙawarin zuwa suka yi dan su je kasuwa a had'o kayayyakin da suka sawwaƙa a kai Ameerah d'akin ta. A can gidan Abdussabour kuwa tinda suka farka yake jin yunwa, jiya ya kawo dik wani kayan abinci da ya kamata ace suna da shi, amma da dare sai amsowa yayi a gida,da safe ma gashi bata dafa musu komai ba har tara na safiya yayi,hamma yayi yace, "Baby yanzu ba kiyi mana abincin safe ba kike Maganar zaki je gida had'o lefen Ameerah? Kar fa ki manta ke amarya ce, dika-dika kwanan ki nawa ne da tarewa da zaki dinga fita anyhow? A washegarin ranar da kika zo gidan nan sai da na kai ki gidan ku, me yasa kike haka ne?" Shagwab'e fuska tayi sannan ta kwanta a jikin shi tace, "Haba baby yanzu wa Ameerah take da shi da zai yi mata irin wannan hidimar idan ba ni ba? Na zata kai a waye kake ba zaka damu da surutun mutane ba, sai dai kashhh gashi tin kafin wani ya magantu kai ka fara magana,a mota fa za ka kai ni ba wanda zai gammu," "Hummmm, to yanzu me zan ci idan kin tafi baki dafa min komai ba?" "Idan ka ajiye ni sai ka wuce gida ka ci abinci ni kuma na ci a gidan mu ko?" Tashi tayi ta hau shiri yana kallon ta, ita kuwa tana sane ta hau tub'e wa a gaban shi, dan ta san yanda jikin ta ke da matuƙar tasiri a wajen shi, ba kaɗan ba Abdul ke yabawa da surar Mommy shi yasa ko laifi tayi masa akwai zama na musamman da take yi ya wanke laifin ta, tin da aka yi auren nan kullum cikin ƙorafi yake, dai-dai da wajen da suke bacci bata san ta gyara ba balle ta share, gidan dik ya fara ƙura,'yan kwanukan da yake karb'o abinci a gida dik suna ajiye a sink bata wanke su ba. Tana gama shiryawa tsaf cikin doguwar riga ɗaya daga cikin wanda Abdul ya siya mata wayar ta ta hau ringing, dubawa tayi taga Innoh ce,amsawa tayi ta kara a kunne, tana gama jin saƙon Innoh ta kashe wayar ta zazzage kayan ta dake akwati a saman gado ta ɗauka ta ce masa, "Baby na shirya

Chapter 35 of 70