Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tayi ne? Yunwa take ji kamar taci babu. Tana nan zaune shamsu ya dawo ɗauke da food flask d'in da ta tabbata a wajen mahaifiyar shi ya same shi tinda ita bata da kayan kitchen, ajiyewa yayi a gaban ta yana ɓata rai, bai ce mata komai ba ya samu waje ya zauna ya buɗe,masa ce da miya da nama a ciki, cikin sauri Ameerah ta sauka itama ta saka hannu suka fara ci tare. Tin shamsu na b'ata rai sai ya dawo yana sakar mata fuska, a haka suka gama cin masar nan suka zauna zaman hira, gud'a suka ji an zabga ana yi wa Shamsu da Ameerah kirari irin na yabo saboda kama mutuncin su da suka yi kafin aure. Ameerah ce ta ƙunshe dariya Shamsu ya doka tsaki yace, "Ke fa naga alama baki da hankali,gani kike yi abinda kika aikata ba komai bane ko?" Cikin ɓacin rai ta kalle shi ta qanqance ido tace, "Kasan Allah ka sake kira na mara hankali se na yi maka haukan gaske, da alama baka san wacece ni ba hyi yasa kake ta kira na da mara hankali," Tsaki yayi ya tashi ya fita ya bar gidan gaba ɗaya, yana fita tsakar gida dangin mahaifin shi da na mahaifiyar shi da suka samu halartar gudanar da bikin al'adar tasu ne suka hau tsokanar shi, har d'akin Ameerah suka shiga suka fito da ita aka dasa tabarma da kujera,mayafin ta aka rufa mata aka buɗe mata shi kowa ya shigo ya jefa kud'in shi na taya su murnar kare mutuncin su da suka yi. Nan take wasu mata suka hau ƙusƙus suna faɗin, "Kin ga ana zaton wuta a maƙera sai gashi an same ta a masaƙa, kin ga yayarta da kowa kewa kallon ta Allah itace ta tara mana karuwai da 'yan daudu a ƙauyen nan, tinda aka kai ta shiru kake ji babu wanda ya gudanar da al'ada tinda ai gidan Sarki fulani ne,sai gashi 'yar talla ta kawo mutuncin ta gidan miji," Dayar ce tayi ƙasa da murya tace, "Ai dama haka Allah ke lamarin shi,Allah dai ya basu zaman lafiya," Haka aka dinga jefawa Ameerah Hamsin ɗari, masu bayarwa da yawa ne suka jefa dari biyu, abu kamar wasa sai gashi an tara kuɗi masu tarin yawa. Taro na watsewa Ameerah ta tattara kuɗi cikin ladabi ta kaiwa surukar ta ta durƙusa har ƙasa kamar ta Allah ta miƙa mata tace, "Ummah gashi," Murmushi Ummahn Billy tayi tace, "Ah ah ai wannan naku ne ke da mijin ki, maza tattara ki kai muku Allah yayi muku albarka," "Ameeen" Ameerah tace ta tattare kuɗi tayi gaba dasu zuwa d'akin ta, ƙanwar Billy Faridah da ta san Ameerah sosai sai mamaki take yi da aka ce Ameerah ta kawo mutuncin ta gidan miji lafiya. ************************* A can Australia kuwa Billy ta sha mamakin ganin irin gidan da Amy ta mallaka ba wai haya ba kamar yanda da yawan turawa ke hayar gida da motar hawa da sauran abubuwan more rayuwa, hakan ya nuna mata cewar Amy fa ta kama ƙasa da nerori har da daloli,wani murmushi ta saki dan tunawa da plan ɗin ta.......... [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ *SANARWA !* *Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....* *MAZAUNA GIDA 300* *ƳAN ABUJA 300* *A GARIN MU 300* *KAI NE JARUMI 300* *KUN MAKARO 300* *TAUBASHI 300* *KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻* *IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.* PAGE 58: Tafe take a makeken gidan dake da sama da ƙasa ko ina a gyare fess kamar da mutane a cikin gidan,tinda Billy ke yawon ta daga gida Nigeria zuwa ƙasashen Africa da ta taɓa zuwa bata taɓa ganin gida mai kyan wannan ba. Komai na gidan kalar brown ne da fari, hatta da kujerun dake gidan kalar brown ne,wani irin ƙamshi ke tashi na musamman wanda ya sanya ta jin wani irin yanayi mai sanya nishad'i,wayar ta ta d'akko tana yi wa kanta da gidan video, a dai-dai jikin table ɗin da aka kunna wasu candles masu kyau ta tsaya, ɗaukan kwalbar tayi ta shinshina, wani irin ƙamshi ne ya ziyarci hancin ta, cikin sauri ta buɗe idanun ta da ta kulle ta hau juya candle ɗin tana mamakin jin ƙamshi na tashi a jikin shi, Amy ce ta fito bayan ta ajiye musu kayan su a bedroom ta samu Billy na mamakin ƙamshin da take ji a jikin candle, cikin sauri ta kashe videon da take ɗauka ta kalli Amy tace, "Kin ga wani magic candle anan me ƙamshi?" Murmushi Amy tayi ta rungume Billy ta baya sannan ta ce, "Ba magic candle bane wannan romantic candle ne,kin san nawa ake siyar da shi kuwa? Wannan na musamman ne, ni da kaina na sa campanin dake kula da gyaran gidan nan su saka min shi, na san zaki so ƙamshin," "Woww ! Ban taɓa sanin kina da wannan capacity ɗin ba, yanzu da gaske kina nufin wannan gidan da motar da aka kawo mu nan dika naki ne?" Murmushi Amy tayi ta saki Billy ta isa gaban makeken fridge ɗin da ke manne a jikin gini irin mai ƙofa biyun nan ta buɗe,tsayawa tayi tana kallon abinda zata d'akko can idanun ta ya sauka akan wata kwalbar lemo, dakkowa tayi ta buɗe locker ta d'akko glass cups guda biyu ta tsiyaya musu ta miƙawa Billy sannan ta kurɓi nata sau biyu ta ajiye, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalli Billy dake jiran jin amsar ta tace, "Billy ba abun mamaki bane dan ina da irin waɗannan kuɗaɗen,a lokacin da na bar gidan k'waisa na fara zaman kai na anan na haɗu da wani Alhaji wanda ya so cutar dani ta hanyar siyar dani ga wata ƙungiyar matan dake yin lesbianism dake a Miami, kuɗi ya samu ba na wasa ba  a lokacin saboda sun yaba da kyawu na da diri na sosai,kin dai ganni kyakkyawar bafulatana ce bani da makusa a jiki na sai dai idan baka ra'ayin irin jiki na ne kawai zaka ga ban yi maka ba. Wannan dalilin ne yasa mata da yawa suka dinga bina a ƙungiyar har daga ƙarshe wata da ta fi kowa kuɗi a cikin su mai suna Arica ta aure ni muka gina gidan mu cike da soyayya mai ƙarfi cike da gaskiya da riƙon amana,Arica na matuƙar sona nima kuma ina son ta sosai,saboda tana kyautata min, ta shagwab'a ni da dukiya sosai komai nake so shi nake samu, kullum cikin saya min gifts take masu tsada,Arica itace shugabar ƙungiyar da aka saida ni,ita ke kula da komai na ƙungiyar, kama daga ci gaban ƙungiyar da fafutukar samarwa da matan dake cikin ta 'yancin kai,a haka muka ci gaba da rayuwa har muka dawo Austaraliya, wannan gidan nata ne da ta siya na musamman saboda ni,rayuwa muke yi cike da so da ƙauna har muka fara shirin adapting yara mu riƙe a matsayin 'ya'yan mu,muna haka kwatsam Arica ta fara rashin lafiya,abu kamar wasa daga ciwon ciki muka je asibiti aka duba ta wai tana da lung cancer,ashe Arica ta jima da sanin tana da wannan ciwon amma bata sanar da kowa ba,wannan dalilin ne yasa muka tattara muka koma asibiti domin bata kulawa kafin lokacin ta yayi. Bayan mutuwar Arica ne na gaji dukiya mai yawa a wajen ta, ciki har da wannan gidan da muke ciki da wani gida dake ƙauyen su amma na barwa iyayen ta shi dan bani da buƙatar shi ni,ina da kuɗi kud'in da suke da matuƙar yawa Billy,daga baya mun dawo muna mutunci da wannan Alhajin sosai wani lokacin ma nakan haɗa shi da yaran da yake ɗauka ya siyar nima ya bani wani abu a ciki, shi yasa kika ga ko a Nigeria bana cikin matsalar kud'ad'e." Baya Amy tayi sannan ta durƙusa a gaban Billy ta zaro zobe mai ɗauke da dutsen diamond a jiki ta kama hannun Billy dake cikin shock tace, "Billy ina so ki yi min alfarmar zama matata wadda zamu rayu cikin so da ƙaunar juna har mutuwa ta raba mu," Cikin wani irin shauƙi Billy ta hau tsalle ta manta da tunanin da ta fara yi akan Amy da Alhajin da ta bata labari a yanzu sai ta hau cewa, "Na amince zan aure ki," Rungume juna suka yi, Amy ta sake buɗe fridge ta ɗakko musu shampain suka jijjiga tare da buɗe kwalbar nan take kumfar ta hau zuba suna ihu suka zuba a cups suka hau sha. A ranar Billy da Amy sun raya daren cikin nuna wa junan su yanda suke son junan su sosai. Washegari da safe kuwa bayan sun yi wanka sun shirya sai suka wuce restaurant dan cin abinci,sai da suka ci suka ƙoshi ne Amy ta ɗauke su suka wuce wajen aski, suna zuwa Billy taga yanda matan dake askin suka sha wata iriyar kwalliya da shiga kamar ba mutane ba, kawunan wasun su babu gashi, wasu kuma rabi da gashi rabi babu, wasu kuma kan sol babu ko ɗigon gashi,ga piercing sun sha a harshe da kumatu wasu har a leb'unan su,dik yanda Billy ta zaci zata ga turawan sai abun ya wuce tunanin ta, cike da ƙauyanci take bin su da kallo har ma ta kai hannu ta taɓa abinda taga tana da buƙatar tabbatar da ingancin wanzuwar shi a jikin 'yan Adam ɗin dake gaban ta. Wata magazine Amy ta ɗauka ta samu kujera ta zauna tare da yi wa Billy nuni da ta zauna a cinyar ta su zaɓi kalar askin da za a yi wa Amy ɗin,zaman su ke da wuya ɗaya daga cikin masu askin ta kula da zoben dake hannun Billy, cikin ihun murna ta kalli Amy tace, "Oh my God are you two engaged?" Cike da murmushi da nuna farin ciki Amy tace, "Yes we are engaged." "Awwww ! Congratulations." Nan da nan matan dake wajen suka dinga taya su murna, wanda suka yi aure a cikin su da junan su sai suka hau surutai suna sanar da Amy yanda idan suka yi aure za su ji daɗin rayuwar su da sauran surutan da already Amy ta riga da ta san su, wata ce ta zo ta tsaida hirar ta hanyar sanar da su Amy fa ita ce tsohuwar matar Arica,nan take suka dinga mamaki, kowa ta bar wajen suka hau aikin dake gaban su. Wani aski Billy ta zab'a a yi wa Amy wanda za a aske kanta ta baya sosai ta gaba a gyara shi a ƙara masa gashi a d'aure mata shi, babu musu kuwa Amy ta zauna aka hau yi mata gyaran kai ana gamawa aka hau aski,sanda aka gama yi mata Billy sai ta rungume ta suka dinga yiwa junan su hotuna da videos kafin daga baya su sallame su su tafi. Shopping Amy ta kai su suyi na abubuwan da za su buƙata na gida, da siyayyar auren su da suke su suyi shi nan da kwana uku, dan kuwa basa son su jima ba tare da sun mallaki junan su ba ta hanyar aure. Rabbi najjina wa ahluna mimma ya'amaloon, tabbas rayuwar generation ɗin nan namu na cikin babban hatsari, 'yan uwa na kuna yi wa kawunan ku addu'ar neman tsari daga zama cikin ɗaya daga lalatattun wannan zamani da wanda zai zo a gaban mu? Zuri'ar ku fa? Idan kuma kuna yi to ku dage ku ƙara akan nada, sannan a haɗa da dikkan musulmi, Allah ka shirya mu ka yi mana tsari da mummunan farko tsakiya da ƙarshe da bayan rayuwar mu Amin. Haka rayuwar su Billy ta kasance cikin kashe kud'ad'e da jin daɗin rayuwa, Amy tayi wa Billy register da ƙungiyar su ta mata masu auren jinsi da wajen da take zuwa motsa jiki,sun kammala da siyayyar kayan da za su saka ranar auren su har ma sun yi booking wajen da za a d'aura auren nasu wanda mad'aura auren arna ne. (Inda zaku tabbatar abun bana hankali bane sab'on Allah'n ake so a aikata da gasken-gaske kenan my beautiful fiful) A washegarin ranar d'aurin auren sune Amy ta ɗauki Billy a mota dan ta kai ta saloon domin a yi mata gyaran gashi hannu da kuma ƙafafun ta, a hanyar su ta tafiya ne Billy tayi shiru tana nazarin irin rayuwar da ta taso a cikinta ta talauci, da kuma lokacin da mahaifin su ya fara sana'ar saida dusa har Allah ya sanya wa kasuwancin shi albarka yake iya ciyar da gidan shi har ma ya taimaka wa wasu, dik daren duniya idan za a yi abinci sai an saka nama ko kifi, amma dik da haka ita dai hakan bai yi mata ba tana buƙatar ƙari,a haka ta samu Baban ta ya siya mata waya har ta fara WhatsApp, daga shiga groups na batsa da tura videos na batsa ta haɗu da wata da ta hilace ta ta koya mata yanda ake neman mata har da maza ma,a hankali ta kwad'aita mata zuwa kano dan ta haɗa ta da manyan mutane su dinga bata kuɗi sosai,da wannan ta samu ta yiwa Baban ta ƙaryar da ya barta zuwa kano aikatau. Ranar da ta isa kano a gidan karuwai ta sauka ta fara karuwanci irin na ƙazaman karuwan nan ana biyan ta kuɗi kaɗan har ta haɗu da K'waisa ya ɗauke ta a gidan,tin daga nan ta shigo gari take babbar harka. Man shine saurayin da ta fara jin tana so ba wai iya son bariki ba kawai,saboda tafi jin daɗin mu'amala da shi sannan yana sakar mata kuɗi, daga baya samun shi ya ragu ba kamar da ba amma dai still yana bata dik abinda yake da shi, tana tsaka da tinanin taji mota ta tsaya, kallon wajen da suke tayi sai taga a gefen titi ne basu isa inda za su je ɗin ba,kallon Amy tayi taga damuwa sosai a saman fuskar Amy sai ta saki murmushi ta ce, "Lafiya naga mun tsaya anan?" "Ke zan tambaya lafiya naga kin shiga tunani mai zurfi har ina ta yi maki magana baki sani ba? Are you having second thoughts about this....." "No i am not ! na yarda na amince zan aure ki,idan har kin amince kema zaki biya min dikkan buƙatuna da na nema a wajen ki,kin san menene matsala ta, kuma daga dikkan alamu da yanda kike shagwab'a ni na san ba zan yi dana sanin auren ki ba," Murmushi Amy tayi ta duƙa ta sumbaci Billy sannan ta tada mota suka ci gaba da tafiya, suna isa wata mata gajera siririya fara tass mai dogon gashi ta isa wajen su ta nuna masu inda za su zauna, babu b'ata lokaci ta hau wanke gashin Billy da bashi da tsaho sai cika, cikin awanni biyu da rabi aka gama gyara mata gashi da hannayen ta da ƙafafun ta, kallon ta kawai Amy take yi tana farin cikin samun Billy a matsayin matar da zata aura. Shagwab'e fuska Billy tayi tace yunwa take ji,ba ɓata lokaci Amy ta ja hannun ta suka wuce wajen cin abinci, daga nan suka koma gida suka ci gaba da shirye-shiryen bikin su. Da misalin ƙarfe goma na safe wajen da za a yi bikin nasu a bakin ruwa cike yake da mata kala-kala masu shiga iri-iri,wasu tare suke da matan su wasu kuma 'yammatan su,iskar ruwan dake wajen mai sanyi sai kaɗa gashi da tufafin su yake yi, wajen ya sha kwalliya da fararen furanni, hatta da kujerun wajen farare ne,wata mata ce tsaye a jikin wani ɗan gini tana jiran ma'auratan su ƙarasa ta ɗaura musu auren. Hannayen su sarƙe dana juna suka taho, Amy na sanye da suit farare tas masu matuƙar tsada kan nan ya sha gyara ta d'aure shi a tsakiyar kanta kamar yanda Billy ke so, ƙafafun ta sanye suke da wasu fararen takalma sau ciki masu matuƙar tsada,hannun ta d'aure da agogo rolex sai ɗaukan idanu yake yi,wuyan ta kuwa wasu sarƙoƙi ta saka guda biyu suna ta ɗaukan ido,dik wanda ya ga Amy a wannan yanayin ba zai taɓa ɗauka ta haɗa hanya da zuri'ar musulmai ba, babu mai ɗaukan ta a matsayin mace sai dai a kira ta da namiji. Billy ce ta kalli Amy ta saki murmushi, rigar ta fara ta ɗan ja dan ta ƙara sauka dik da cewa ta riga da ta san ba saukar zata yi ba tinda iyakar tsawon ta kenan,gashin ta ne ke ta kad'awa saboda iskar ruwan dake kad'awa a hankali,riga ce guntuwa a jikin ta mara hannu ta fitar da shape ɗin ta da ta kashe miliyoyin kud'ad'e domin samar da shi. Fuskar ta ta sha kwalliya sab'anin ta Amy da hoda kawai aka shafa mata sai man baki da maskara,an yi mata gyaran girar da ya dace da doguwa kuma siririyar fuskar ta. Cikin abinda bai fi minti goma sha biyar ba aka gama d'aura musu abinda suka kira da aure, waje ya kaure da ihun murna da party. Tin daga wannan rana Amy da Billy ke rayuwa kamar mata da miji a ƙasar turai,daga wannan ƙasa su je waccan suna honeymoon ɗin su. *********************** Cikin shirin ta tsaf Saddiqa ta fito parlour ta samu Baabaa da ke zaune sanye da atampa ta yafa mayafi tana jiran ta, Sadeeq ne ke ta b'ata rai yana cin magani shi a dole an takura masa baya son zuwa ko ina, kallon shi Baabaa tayi tace, "Bindiga zaka yi ka fashe sai na san kaji haushi mara kirki kawai, ni shi yasa nafi son Saddiqa akan ka,dan kuwa komai lalacewar uban ta da 'yan uwan ta tana son su, amma kai sai shegen riƙo, na rasa a inda ka ɗakko wannan mugun halin dan ba halin uwar ka bane ba kuma na uban ka ba." "Wai har yanzu b'ata rai yake yi ba za shi ba?" "Iyy wai, rabu da d'annema dole ne kaje ka ga ɗakin 'yar uwar ka ka gaishe ta dik da basu gayyace mu ba,kin rufe ko ina ko?" "Eh Baabaa na rufe, ga makullin da za a rufe gidan na d'akko," "Da kyau to mu je yamma na yi, tinda Allah yasa an gama jarabawa lafiya ai sai aje a sada zumunci gobe-goben nan kina ganin wannan me ƙaton kan ya iso,dan na san kin faɗa masa kin kammala yau," Cike da jin kunya Saddiqa ta hau borin kunya tace, "Ni fa Baabaa ban sanar da shi ba, shi da kan shi yake lissafi d'azu yace zai zo goben,kuma ma nace masa kar ya zo yayi zaman shi shine yaƙi," "Uhumm muje ni kinibabbiya bana son ƙarya,ke ɗin ce zai ce zai zo ki hana?" saddiqa bata sake magana ba suka fita suka rufe gidan suka kama hanya dan zuwa gidan Ameerah su ga gida, wanda Baabaa bata san Saddiqa ta jima tana leƙa Ameerahn ba idan an tashi makaranta, tin tana zuwa tana yi mata rashin mutunci har ta dena zagin ta da yi mata habaici...... *Mutanen k'warai masu albarka a yi min kara a zo a sayi littafai na na kuɗi,kar fa a dinga wasa tare ci banban.....* [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ *SANARWA !* *Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....* *MAZAUNA GIDA 300* *ƳAN ABUJA 300* *A GARIN MU 300* *KAI NE JARUMI 300* *KUN MAKARO 300* *TAUBASHI 300* *KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻* *IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.* *Kar ku manta akwai kayan gyaran jiki kamar su;* *Face oil* *Hair cream/oil* *Hair mask* *Skin oil* *Body scrub* *Domin gyaran jikin ku a wannan lokacin na sanyi.* PAGE 59: A hanya Baabaa ta baiwa Saddiqa kuɗi ta ce ta shiga shago ta ɗan yi wa Ameerah siyayyar abinda ta san tana so na ƙwalama, dan ta san halin mutuniyar tata kura ce uwar kwad'ayi, dariya Saddiqa tayi ta karb'i kuɗin ta tafi shagon, tana zuwa ta hau saiwa Ameerah tarkacen su biscuits da sweets har da indomie, tana isa inda ta bar su suna jiran ta suka rankaya suka yi gidan Mai Dusa. Sai da suka gaisa da shamsu dake shago sannan suka shiga gidan, da sallama Baabaa ta shiga gidan Ummahn Billy na tsakar gida tana shan iskar maraice ta amsa tare da yi musu marhabun da zuwa,ciki tace su shiga Baabaa tace, "Ah ah nan ma ya isa ba jimawa za muyi ba almuru ya gabato," Gaishe-gaishe suka yi a tsakanin su sannan Saddiqa da Sadeeq ma suka gaishe ta, tinda suka shiga Ameerah taji muryar su ta miƙe ta hau kwashe tilin suturun da ta loda a saman kujera ta watsa a cikin wardrobe ba tare da ta ninke ba, tana tsaka da kwashe kwanikan da ta bari tin na jiya da bata kwashe ba suka sallama ƙofar ta, cikin tura baki ta amsa ta ƙarasa fitar da kwanikan ta koma ta zauna, gaishe da Baabaa tayi taga Baabaan na yatsina fuska,Saddiqa da Sadeeqa ma sun gaishe ta amma sai taƙi amsawa da kyau tace musu, "Ya kuke?" Ɗauke kai Sadeeq yayi sai Saddiqa ce ta amsa mata da, "Muna nan lafiya ƙalu alhamdulillah," Ledar da Ameerah ta ƙyalla idanu ta hango a hannun Saddiqa ne ya sanya ta cewa, "Ya kuka tsaya anan ku shigo ku zauna mana, ko aikin soja za kiyi kin fasa na likitan?" Murmushi Saddiqa tayi sannan ta samu waje a ɗaya daga cikin kujerun da suka fara sauya kala ta zauna,Baabaa ce ta kasa hakuri da yanayin da ta tadda Ameerah na ƙazanta da wari a ciki tace, "Ke yanzu Ameerah uwar ki bata zame miki ishara ba ashe? Ko da yake ai lokacin da uban ku yayi mata kishiya kina ƙarama, Ameerah ke fa amarya ce amma d'akin ki ƙasa lamar ba ki share ba, Allah ma kaɗai ya san iya kwanakin da kika yi babu sharar,ki duba ki ga kaya yanda kika watsa su ko rufewa baki yi ba da alama baki jima da watsa su ba dan kar a gan su a barbaje kika ɗaga, ke yanzu irin rayuwar Innoh zaki yi ko? Kalli kan ki yanda ya tuje kamar ana ball a wajen, ji yanda kike tsamin hammata Ameerah ko kunyar kar mijin ki ya shaƙa baki ji," "Na yi wanka fa na shafa turare ni, kuma ni ki dena zagin uwa ta." "Ashe kin san abinda kike yi bashi da kyau idan har zaki ɗauki gyaran da nake yi maki a matsayin zagi? To dan uwar ki Innoh kar ki fasa yin ƙazanta kina ji kina gani mijin naki zai yi maki irin yanda uban ki yayi wa Innohn taki, ko bai auro kyakkyawar bafulatana irin Yadikon sule ba, da ya auro mai hankali, tsafta da kula da kanta irin Yadikon sule kin koma gida zawarci dan kuwa mazan yanzu ba irin na da bane da yana ganin inda zai more ya tsaya akan ƙazama ballagaza ku ku tashi mu tafi," Ajiye mata ledar da suka kawo mata suka yi suka tafi Baabaa na ci gaba da zagin Ameerah har a tsakar gida dan ta tabbata kowa na ganin abinda take yi amma ba a gyara mata, meye amfanin zama da manya idan ba za a yi wa yaro gyara ba? Har ƙofar d'akin Ummahn Billy ta je tana masifa, da sauri ta fito daga ɗakin tana baiwa Baabaa hakuri,cikin yin ƙasa da murya tace, "Ai Baabaa Ameerah addu'a kawai za a bi ta da ita, bayan ƙazanta lamarin ta har da rashin kunya,kina yi mata gyara a inda tayi kure zata buɗe baki ta faɗa maki mai zafi,shi kanshi mijin ma baya ganin laifin ta, to kai bawa ba sai ka koma gefe ba kayi kallo?" "Kwarai da gaske tinda ba zaka sa mutum yin abinda bai niyya ba dole, ai kuwa zata ci malafar uban ta in dai namiji ne,gata gashi Allah bamu alheri," "To Ameen Baabaa a gaida gida mun gode." Bayan tafiyar su Baabaa ne Ameerah ta hau shara, tana yi tana mita tare da yiwa surukar ta habaici akan abinda taji tana faɗa wa Baabaa,Ummahn Billy na jin ta ta kyale ta, Fadila ce ta gaji da jin yanda take yi wa mahaifiyar su rashin kunya ta fita tsakar gidan

Chapter 38 of 70