Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dare da kanshi wai ilimi baya kaɗan,ba ni kaɗai ba hatta mahaifiya ta abun yayi mata daɗi sosai,haka ta taho ƙafa da ƙafa dan yi masa godiya,Baffah kuwa ya nuna mata ai babu komai yiwa kai ne,kula dani ne kawai zai yi ya riƙe zumuncin dake tsakanin shi da Malam. Haka na dinga zuwa makarantar boko da islamiyya,wanda gaba ɗaya nafi bada ƙarfi na akan ilimin islama, wannan shine dalilin da yasa na sake dawowa baya ina tisa haddata dan nima in samu damar shiga gasar musabaƙa da ake yi dik shekara,ina jin daɗi da sha'awar yara ƙanana dake shiga gasar musabaƙa kuma suyi nasara,dan haka sai na maƙale wa wani malamin mu malam Isa ba dan komai ba sai dan yanda yake da tarin ilimin addini, nayi imani da Allah zai taimaka min wajen cikar buri na. Tin daga nan idan an tashi zan ƙara minti goma in bawa Malam Isa hadda ta sannan na koma gida,ana haka watarana da dare mummunan al'amari ya afku akai na,baƙin daren da ba zan taɓa mance shi ba har abada a rayuwa ta, na fito daga Islamiyya bayan mutane sun ragu sosai, sai tsirarun da ba a rasa ba, na kama hanyar komawa gida ina tafe ina muraji'ar karatuna,sai naji an yi sama dani an damƙe min baki na, ƙur'ani na da sauran littattafai na a wajen suka watse,ba a dire ni a ko ina ba sai a wani kango da babu kowa,a wannan baƙin daren mutumin da na baiwa mahimmanci a rayuwa ta ya cire tsoron Allah a ran shi yayi min fyad'e,a wannan daren na rasa budurci na,a wannan daren nayi sallama da farin ciki na faɗa rayuwar baƙin ciki." Kukan da Any bata taɓa zaton zata sake yi ba a rayuwar ta ta fashe dashi,ta jima da sallama rayuwar da ta wuce a baya, ta yanda ko ta tuna bata kokawa, sai gashi a yau zuciyar ta tayi rauni,ta karye har tana zubar da hawaye,cikin share hawaye Billy tace, "Kina nufin Malam Isa shine yayi maki wannan aika-aikar? Lallai duniya babu yarda." Cikin wani irin murmushin takaici Any ta kurɓi juice ɗin dake glass cup ɗin gaban ta,kafin ta ajiye ta miƙe tsaye ta taka zuwa kujerar dake fuskantar Billy ta ce, "Ai da Malam Isa ne yayi min fyad'e da da sauƙi Billy,kin san wanda yayi min fyad'e kuwa Billy?" Girgiza kai Billy tayi alamar bata sani ba,murmushi Any ta sake yi sannan ta ce, "Baffah Ilyasu shine yayi min fyad'e Bilkisu,yana gama abinda zai yi dani sai ya jawo ni ya fito dani tsakiyar hanya ya yar dani,idanu na sun kumbura saboda kukan da na sha,cikin hawayen dake zuba mota tazo wucewa a wannan daren ta haske min Baffah na da suke uwa ɗaya uba ɗaya da Malam mahaifi na yana ƙoƙarin buga machine ɗin shi ya gudu. Kar ki manta fa yana da yara mata sa'anni na da wanda suka girme ni, da wanda na girma,saboda dika yaran shi mata ne bashi da namiji ko ɗaya,ya manta girman zumunci da alaƙar dake tsakanin shi da mahaifi na, ya manta haƙƙin maraici da amanar da mahaifiya ta ta damƙa masa,ina nan kwance cikin mawuyacin hali wata dattijuwa dake a layin mu tazo wucewa ita da jikan ta ta taso daga wajen da take saida kayayyakin ta na tsofaffi irin su daddawa kuka da sauran su,suna tsaka da hira da jikan ta ta ganni a cikin wannan mugun halin ta taimaka min ita da jikan ta suka kai ni gida. Tinda aka kaini a wannan halin matan Baffah na suke min faɗa da masifa tare da kira na da sunaye kala-kala na karuwanci da bin mazan banza,cikin rashin tsoron Allah Baffah na ya fito daga ɗaki kamar bashi ba, da alama ma yayi wanka ne ya sauya kaya dan kuwa sai ƙamshin man shafi yake ya fito yana muzurai tare da cin alwashin washegari sai na faɗa masa inda naje yawon iskanci. Dik yanda tsohuwar nan taso ta nuna masu fyad'e aka yi min sun ƙi fahimta,banda zagi da cin mutuncin iyaye na babu abinda suke yi, hatta yaran su ba a bar su a baya ba wajen zagi na da zagin iyaye na, tare da faɗin dama Malam ne ke yabo na ba tare da yasan mugun iri ya haifa ba. A cikin daren nan tsohuwar nan ta aika yaro wajen Mamana ya sanar da ita tazo gidan Baffah babu lafiya, cikin abinda bai kai minti ashirin ba ta iso gidan,tinda tayi ido biyu da abinda ya same ni ta yanke jiki ta faɗi bata sake shurawa ba, wannan ne yayi sanadiyyar da ni kaina na suma saboda yanda naji mata sun fasa ihun Mamana ta rasu,ban sake farkawa ba sai washegari a gadon asibiti. Ko da na farfaɗo sai na kula babu kowa akai na, ni kaɗai ce a kwance a asibitin bani da kowa sai Allah na,likitar da ta duba ni ce ta tausaya min sannan tace zasu sallame ni tinda na farfaɗo kuma an yi min ɗinki a kasa na,sai na tafi gida wanda ya kawo ni ya biya kud'in komai,a lokacin da aka sallame ni na fito harabar asibitin Billy kallon dika mazan wajen nake yi a matsayin azzalumai,kallon su nake a matsayin mazinata,kallon su nake yi a matsayin maciya amana,na kasa goge fuskar baffahna a cikin kai na, sai a wannan lokacin nake tuna sanda yake yi min fyad'e da irin kalaman da yayi akan ya jima yana son mahaifiya ta bai samu ba, to yanzu gani nama fi mahaifiyar tawa kyau da komai dan haka shi ya samu wajen hutawa. Kuka na durkushe a wajen ina tayi kafin daga bisani na mike na bar asibitin,na gama yanke hukunci ba zan koma gidan baffah ba, zan shiga duniya na ƙarasa abinda ya fara, ba kuma zan manta da shi ba zan dawo gare shi domin ɗaukan fansa, wannan shine dalilin da ya sa na faɗa bariki,har na haɗu da Hajiya K'waisa a gidan karuwai ta taimaka min,daga ƙarshe da na haɗu da Alhaji ya nuna min hanyar safarar mata da maza zuwa turai da dukiyar da ake samu,sai na bar gidan K'waisa na dawo na kafa tawa daular,kin san da waɗanne mata na fara kasuwanci na na farko Billy?" Gyad'a kai Billy dake ta matsar k'walla tayi alamar bata sani ba, cike da wani irin nishad'i irin na wanda ya ɗauki fansa Any tace, "Da babbar ƴar Baffana na fara samun kuɗin safarar mata,na sace tane a ranar da aka ɗaura auren ta da dare za a kai ta gidan miji,ƙasar Columbia na kai ta na siyar,da suka gaji da ita suka dirka mata ƙwayoyi ta sheƙa ƙiyama,bayan ita sai na sace autar shi,daga ita na sace mai bi wa babbar ƴar shi,a haka sai da na sace yaran shi mata kafff,kuma a shekarar ne aka haifa masa yaro namiji,a shekarar ne na baiwa wani yaro mai shaye-shaye a unguwar kuɗi ya nemi jaririn ta baya ya farke shi ya gudo waje na na aika shi ƙasar waje,yanzu haka ya zama babban yaro na,sai daya girma sosai ya zama gawurtacce na sake aika shi ya yi wa Kawu na dake jinya saboda damuwa da tashin hankalin abinda ke faruwa da rayuwar shi fyad'e,yayi masa kaca-kaca, dake Allah bai yi a lokacin zai rasu ba,sai yayi tsawon rai har sai da naje na same shi a d'aki yana jinya,na cika matan shi da kuɗi da kayan abinci,suka bamu waje na zauna na bashi labarin dik abinda yayi min da irin fansar da na ɗauka akan shi,sannan na tabbatar masa idan har yana raye sai ya yi shaidar ɗauke matan shi biyu da suka rage na sayar da su suma. A wannan lokacin ne ya fara wani irin nishi kamar wanda ake zarewa rai,ina ganin haka nayi musu sallama na wuce,Baffah Iliyasu bai rasu ba Billy sai da ya ƙara wata uku da sati biyu da kwana ɗaya a duniya yana shan azaba. Wannan itace Any Billy,bana jin tsoron kowa,bana shakkar kowa,ina da ilimin addini da na zamani dai-dai misali,ni ba jahila bace na san Allah,na san irin azabar da ya tanadar wa dik wanda ya aikata aiki irin nawa, Allah da kan shi yace kar mu kusanci zina, balle mu aikata ta,ni ban kusance ta ba, jefa ni aka yi cikin ta ta karfi da yaji,dan haka zunubin abinda nake aikatawa zai koma zuwa ga wanda ya jefa ni cikin ta." Ajiyar zuciya Billy ta sauke,cikin sanyin murya tace, "Amma kuma ai kin balaga,kema zaki karb'i naki sakamakon zunubin Any,me yasa kin san irin ayoyi da hadisan da kika dinga jawow waccan baiwar Allah'n kuma kika zama haka? Da ace ni ce nake da ilimin da Allah ya baki da ban kawo haka ba,labarin ki ya taɓa zuciya ta ya sa na fara tunanin shin wai menene ma silar fara nawa karuwancin? Kwad'ayi ko son zuciya? Butulcewa Allah da rashin gode masa ko kuma tsananin sha'awa ce da gasa? Dai-dai misali Allah ya horewa mahaifi na abinda zamu ci,ba a taɓa girki a gidan mu babu nama, musamman a tuwon dare,idan ba a saka nama ba za a saka kifi,ke watarana ma Baba na siyo mana kaza gasasshiya ko tsire ko balangu ko kilishi. Daga zuwa aikatau Hajiya K'waisa ta haɗa ni da Man,daga nan ne rayuwa ta ta sauya na fara bin maza da mata kamar karya,a hankali na dena aiki na zama ta hannun daman Hajiya,iyaye na basu taɓa tambayar dalilin daya sanya kud'in aiki na yin yawa ba,da ace sun bi diddigi a lokacin da sun gano inda matsalar take sun yi wa tufkar hanci,da ace ko sau ɗaya sun wanke ƙafa sun je sun ga gidan da nake aikatau da ban zama international karuwa ba." Kuka sosai Billy keyi wanda za a iya kiran shi da kukan nadama,ganin haka ne ya sanya Any tashi ta faki idon Billy ta jefa mata ƙwaya a lemo,sai da ta hau lallashin ta tana yi mata magana mai daɗi sannan ta bata lemon ta sha,tana gama sha babu jimawa wata iriyar sha'awa ta taso mata,rasa inda zata saka kanta tayi,dik yanda taso ta bijirewa jikin ta dan kar ta komawa babban zunubin da suke aikatawa sai ta kasa, dole ta sake wa Any jiki suka gurji junan su son ran su. Basu suka rabu da junan su ba sai tsakiyar dare,bayan komai ya lafa ne Billy ta tashi daga saman kujerar da suke ta kalli Any da tayi bacci,ta wuce d'aki zuciyar ta na yi mata saƙe-saƙe kala-kala. Wanka ta fara yi sannan ta haye gado ta jawo wayar ta,direct Facebook ta shiga dan kuwa anan ne take ganin shamsu lokuta da dama,yau ma kuwa ta ci karo da sabon posting ɗin shi shi da babyn su da Ameerah,sun sha kwalliya sun yi kyau sosai abun su, nan take kuka mai tsananin ƙarfi ya ƙwace mata,kuka ta dinga yi har bata san sanda ta nemo No Mahaifin ta ba ta danna masa kira........... [09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 80: "Babaa." Billy ta furta cikin wani irin matsanancin kukan da bata san sanda ya taho mata ba,cikin yanayi na damuwa Mai Dusa ya sauke wayar shi daga kunnen shi ya kalli sababbin lambobin da bai sani ba,sannan ya sake mayarwa kunnen nashi, tabbas muryar Bilkisun shi ce ya jiyo a cikin wayar,cikin sauri ya furta, "Bilkisu ! Bilkisu ke ce ke magana? Bilkisu ina kika shiga? Dan Allah ki dawo gida mun yafe miki dik abinda kika yi,ki dawo ki zauna a cikin dangin ki,ki samu miji kiyi aure Bilkisu, aure shine mutuncin dik wata ƴa mace a duniya da lahira Bilki." Kukan da Billy keyi ne ya tsananta har sai da ta sa mahaifin ta zubar da hawaye shima,cikin kuka ta furta, "Baba ku yafe mini,ku yi hakuri akan dikkan baƙin cikin da kuka ƙunsa ta sanadina,Baba ku taya ni da addu'a Allah ubangiji ya bani ikon dawowa gare ku a raye cikin ƙoshin lafiya, Baba ina cikin wani irin mawuyacin halin da ni na jefa kaina da kai na a cikin shi saboda kwad'ayi da son zuciya, dan...." Cikin sauri Billy ta latse wayar ta sanya ta a flight mood saboda kar a sake kiran ta Any ta ji,hawayen ta ta hau gogewa tare da rufe jikin ta har kan ta, Any ce ta shiga ɗakin ta tsaya tana kallon Billy dake cikin bargo tana goge hawaye, murmushi Any ta saki wanda ita kaɗai ta san ma'anar shi sannan ta shiga banɗaki ta hau wanka. Ta jima tana wanka kafin ta fito ta tarar da gadon wayam babu kowa akai,ba tare da damuwar komai ba ta gama shirin ta sannan ta buɗe wata jaka a ƙasan gado ta ɗauki abubuwan da take buƙata ta bar ɗakin,direct ɗakin karatun ta ta shiga,anan ta tarar da Billy ta haukace tana mata bincike,jingina tayi da bakin ƙofa ta harɗe hannayen ta a ƙirjin ta tana ci gaba da kallon Billy dake dube-dube a tsorace,rashin ganin abinda take nema ne ya sanya ta zama a ƙasa ta haɗe kanta da guiwar ta ta fashe da kuka mai tsanani,tafi Any ta hau yi da hannayen ta,cikin abinda bai fi taku biyar ba ta ƙarasa shiga ɗakin,Billy ce ta miƙe tsaye a tsorace tana ja da baya,wani irin tsoron Any take ji wanda bata taɓa zaton zata ji tsoron wani mahaluƙi a duniya irin haka ba. "Looking for this young lady?" (Wannan kike nema Young lady?) Passport ɗin Billy Any ta d'aga tana kad'awa a gaban fuskar Billyn,cikin azama da zafin nama Billy ta yunƙura zata karɓe passport ɗin nata,wani irin naushi Any ta sakar wa Billy sai da jini yayi tsartuwa ta yi katantanwa kafin ta kife a ƙasa,durkusawa Any tayi a dai-dai fuskar Billy ta zaro bindigar da ta soke a bayan wandon ta ta saita kan Billy da ita, cikin wata iriyar murya ta kece da dariyar mugunta kafin tace, "Yarinya kin riga da kin siyar min da kan ki da hannun ki,dan haka banga dalilin da zai saka ki neman passport ɗin ki ba,ina kike tunanin guduwa to? Ko kin manta ke matata ce? Kin manta kin saka hannu a takarda kin saida min da kan ki akan maƙudan kud'ad'e masu yawa? Kin manta kin saka hannu a contract ɗin aiki da kamfanin mu na porn? Idan kika gudu babar ki kike so mu ɗakko tayi mana aikin mu? Baki da wajen guduwa a yanzu nan ne madakatar ki, kuɗi kike so ai ko? To ai kin samu,zaki ci mai kyau, zaki sha mai kyau, zaki kwanta a wajen mai kyau kalar wanda kike so,zaki tuƙa mota ko ki hau jirgin da kike so,abinda nake so kawai a wajen ki shine biyan buƙata ta a wajen ki da ta kamfanin mu,kar ki mayar dani mutuniyar banza a ƙungiyar mu ƙarƙashin reshen Arewa mana,ko kin san ni ɗin madubi ce a wajen wasu? A matsayin da na taka a yanzu kina nufin zan bari ki zubar min da mutunci na ne? Da mutunci na ya zube a idon ƙungiyar mu da kamfanin mu gwanda na kashe ki kamar yanda na kashe Arica,ohhh ashe baki san nice na kashe ta ba ko? That is a story for another day baby,now stand up, tashi tsaye nace !" Wata iriyar rawa jikin Billy yake yi,naman jikin ta babu inda baya cirawa saboda shiga tsananin tashin hankali,shin dama takardun da ta dinga rattaɓawa hannu babu karantawa ko gamsasshen bayani akai ashe saida kanta tayi da kanta bata sani ba? Dama Arica tsohuwar matar Any ita ta kashe ta ba mutuwa tayi saboda ciwon cancer ba kamar yanda ta faɗa? Cikin zuciyar ta ta hau ayyana, 'Dama abinda wannan matar ke son ta gargad'e ni akai kenan ban gane ba, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ni bilkisu yau na shiga uku, kwad'ayi da son zuciya da muguwar sha'awa sun kai ni gashi sun bar ni a tubalin dana sani.' Cikin sauri Billy ta zube a gaban Any tana faɗin, "Dan girman Allah kiyi hakuri Baby,na san ni mai laifi ce a wajen ki tinda na fara neman passport ɗina ba da izinin ki ba,na yi haka ne saboda labarin da kika bani ya taɓa zuciya ta,kewar iyaye na ce ta kama ni,ina so naje na gan su,ba hauka nake ba da zan ga dukiya irin wannan sannan na koma rayuwar talauci,labarin rashin da kika yi na iyayen kine ya tuna min da nawa, i just want to see them,dan Allah ki taimaka min,ko sau ɗaya ne na gan su,kuma ina son a cikin abinda zan dinga samu na dinga aika masu da wani abu,ke kin san ina son ki, ba zan bar ki ba saboda wani shirmen dalili,ba zan bar kuma wannan dukiyar da na ke ciki ba saboda wani dalili mara tushe." Da fari Any ta ɗauki kalaman Billy a matsayin yaudara,amma daga ƙarshe Billy tayi amfani da ƙwarewar ta a harkar bariki da tantiranci ta yaudari Any ta bata tabbacin tafi son kuɗi da ita akan ta shiryu ta gudu ta bar ta, kewar iyayen ta kawai take yi,dan haka Any sai ta soke bindigar ta ta hau lallashin Billy tare da yi mata alƙawarin zata san yanda za a yi ko sau ɗaya ne su je Nigeria taga iyayen nata,da jin haka sai Billy ta rungume Any tana ci gaba da faranta mata ta hanyar dulmiyar dasu cikin kogin zunubi mai tsananin muni da mummunar makoma ga masu aikata shi. Tin daga ranar Billy ta saki jikin ta da Any bata sake yi mata maganar zuwa gida ba, sai dai tana ta yi mata maganar yanda zata tura wa mahaifin ta kuɗi,a hankali Any ta buɗe wa Billy account ta zuba mata kud'ad'e masu tarin yawa a ciki,ita kuwa da wannan tayi amfani ta ci gaba da waya da mahaifin ta a boye tana aika masa da kuɗi,tin Ta Annabi na fushi da ita bata kula ta har tazo tana kula ta,watarana haka za su sha hirar su har tayi tayiwa Billy nasiha da wa'azi,wanda ke ƙara jefa Billy cikin kogin data sani bata jefa kanta a inda fitar ta zai zama sanadin mutuwar ta ba. Ana haka watarana Any ta zo ta ɗauki Billy suka fita aiki a kamfanin su na fina-finan porn, (fina-finan batsa/blue films) tinda suka je Billy ke cikin tashin hankali,wanda da a baya ne taga irin waɗannan mazan da kanta zata kai kanta wajen su, amma a yanzu tsoron su take ji,bata son mu'amala da su, bata son su taɓa ta balle su yi amfani da jikin ta. Dik wani shirye-shirye da ya kamata ayi mata kafin gabatar da wannan shiri an yi mata,magunguna da ƙwayoyin da suka saba dirka mata suka bata tasha tayi tatul,nan da nan taji babu abinda take buƙata da ya wuce ta ganta tare da waɗannan mazajen tare da matan dake nasu shirin dan gabatar da film ɗin nasu,cikin abinda bai fi minti biyar ba aka fara ɗaukan film ɗin,sun jima suna yi kafin su kammala su sallami mutanen wajen su wuce gida. Tinda suka koma gida take fama da ciwon jiki,dik jikin ta ciwo yake yi mata saboda aikatuwar da tayi,Any ce ta zage ta taimaka mata wajen yi mata wanka da ruwa mai zafi,sannan ta yi mata tausa da mayukan dake cire gajiya,bayan ta gama mata ne ta ci abinci tabi lafiyar gado,tinda ta kwanta take fatan bacci ya ɗauke ta,amma ta kasa,idanun ta sun bushe sun ƙeƙashe,banda tinanin mafita babu abinda take yi,shin me zata yi ne Allah ya dube ta da idanun rahama ya kub'utar da ita daga hannun waɗannan mutanen? Kamar wadda tayi tambaya aka bata amsa sai taji zuciyar ta ta raya mata, 'Sallah ! Yaushe rabon ki da ki ɗora goshin ki a ƙasa? Yaushe rabon ki da ki amsa sunan ke musulma ce ta ayyukan ki? Ki koma ga Allah ki nemi gafarar shi,tabbas shi mai yawan gafara ne, kuma mai karb'ar tuban bayin shi ne,zai yafe maki kuma zai kuɓutar dake daga hannun waɗannan mutanen komai daren daɗewa.' Hawaye ne ya zubo mata mai masifar zafi,cikin sauri ta sanya hannun ta ta share shi,tashi tayi ta shiga banɗaki ta yi wankan tsarki sannan ta d'aura towel ta fito,kayan ta ta hau bincikawa anan ta shiga tashin hankali,gaba ɗaya babu hijabi ko mayafi,babu doguwar riga irin tamu ta musulmai ko ɗaya,kuka ta fashe dashi sannan ta hau faɗin, "Allah na tuba, Allah ka gafarta min ba dan hali na ba Allah, Allah kai ne al-wadud kuma al'afuwwu,Allah ka so ni ka yi min afuwar laifuka na." Tana gama addu'ar nan ta samu wata riga da wando da suke rufe ko ina na jikin ta ta sanya,hula ta nema ta saka ta samu waje a ɗakin ta hau yin sallolin da ita kanta bata san adadin su ba. Any ce ta farka ta ganta a wannan yanayin sai ta murza ido, ta sake murzawa, wayar ta ta jawo ta duba time,gani tayi asuba ta kusa, sai kawai ta koma ta kwanta ta ci gaba da baccin ta,ita kanta ta san bata kyautawa da rashin sallar da take yi,a cikin zuciyar ta ta ƙudirta zata gyara ko ba yau ba. Billy kuwa bata tashi daga wajen ba sai da ta duba lokaci taga lokacin sallah yayi, sannan ta yi sallar asuba ta tashi ta kwanta,ba jimawa kuwa bacci mai cike da ni'ima da mafarkai barkatai da ta kasa tantance su ya ɗauke ta. ********************** Yau sati ɗaya kenan ake neman inda Sule ya shiga ba a samu ba,magana har ta fara baza gari Sulen gidan Ɗan liti ya ɓace,Ɗan liti tin da ya dawo aka gama sunan yaron Ameerah ya ji labarin ɓatan Sule sai bai baiwa abun mahimmanci ba,ranar da ya cika sati ɗaya cif bai dawo bane ya tafi tasha wajen abokan kasuwancin shi ya labarta musu abinda ke faruwa,nan fa aka hau bashi shawarwari, ciki har da masu cewa ya kai maganar wajen malamai a yi masa duba,ita ce hanya mafi sauki da zai gano inda Sule yake. Ɗan liti tin yana ɗaukan maganar ɓatan sule abun wasa har abu ya kai shi ga kwantawa jinyar kwana biyu,likita Mommy ta ɗauka tin daga kano tayi masa kud'in mota aka bashi masauki a gidan sarki yaje ya duba Ɗan liti,Saddiqa dake can Abuja ma hankalin ta ya tashi saboda ɓatan Yah Sule. Ƙarshe dai Abdul ne ya kai magana gidan redio da talabijin aka bada cigiyar Sule,Mommy kullum kukan ta da damuwar ta bai wuce sai da Sule yaje suna wajen ta sannan ya ɓace ba, ai da can yana shiga kano lafiya ya koma lafiya,me ya faru wannan karon aka rasa shi? ********************* Hajiya K'waisa na zaune a parlour abun duniya ya bi ya ishe ta saboda barazanar da take samu ta wajen Alhaji akan ya nemo masa Mommy,gefe ɗaya kuma ga Sam da ya juya masa baya,hawaye ne suka zubo masa yasa hannu ya share su,Sallau ne ya shiga ya kai masa smoothy dan kuwa yanzu ya dena cin kowanne irin abinci sai wannan,saboda samun sauƙin wahalar da yake sha idan yaje zagawa. Tausayin K'waisa ne ya sanya Sallau zama a ƙasa yace, "Hajiya dan Allah ki dena kukan nan,idan ina ganin hawayen ki zuciya ta na karye wa," Ajiyar zuciya K'waisa ya sauke kafin ya sauke tagumin da ya zabga ya ce, "Humm Sallau ai dole na zabga tagumi tinda ni na gayyato shi da kai na,kana ji kana gani wancan ɗan tijaran tsohon shegen da yazo shekaran jiya ya ƙare min tanadi,yace dole na fito masa da Sweet H,ni yanzu ina zan ganta? Me kama da ita ma ban gani ba balle ita, ya yake so nayi da rai na? Ga matsalar Samuel da ta sako ni a gaba,ya manta halacci da soyayyar da na yi masa a rayuwa,saboda shi bana bin kowa,na kame kai na na ce shi kaɗai nake so,sai yanzu na gane wautar da na tafka,tin ciwon nan yana kaɗan idan zan je asibiti baya raka ni,sai dai ma ya bar ƙasar ko yace naje zai biyo baya na, da na ji sauƙi zai dawo ya sake rarake min baya ya gudu ya bar ni da jinya,yanzu gashi ya yi min muguwar illa ya dena zuwa, ko kasan wai yau ni K'waisan alheri ne zai kira baby baby ya ƙi ɗaukan waya ta? Ko kasan jiya da na kirawo shi wani ne ya amsa wayar yake faɗan wai babyn shi na bacci a dena kira sai ya

Chapter 50 of 70