Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
taso mu tafi." "Wannan kayan da kika juye a nan fa?" "Akwatin nake da buƙata, Innoh tace kud'in da Shamsu ya bayar na lefe ba zai isa a siyo da akwati ba, shi yasa zamu yi amfani da wannan a zuba mata kayan a ciki," "Mu je an sai mata wasu," Cike da murna Mommy ta maƙale shi tana sumbatar shi, abun ku da tsohuwar hannu tini ta mantar da shi fushin da yake yi na rashin cin abinci da bai ba, cike da so da ƙaunar juna suka rufe gida suka tafi gidan Ɗan liti.......... *Yau rubutun ba yawa saboda abubuwa sun min yawa a karanta da hakuri...masu tambaya daga farko ku min uziri an yi nisa da yawa ba zan iya sake turowa ba daga farko gaskiya,mai son karantawa daga farko dan Allah ta duba page ɗina na Facebook, ko wattpad ko WhatsApp channel d'ina na gode.* [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ *MAHREEN 1K* *MAIDA TSOHUWA YARINYA 1K* *KYAKKYAWAR FAHIMTA* PAGE 55: A shirye Mommy ta tarar da Naja tana cin ɗan waken da ya sha mai da yaji a gidan nasu, babu ko gaisuwa ta zauna tana faɗin, "Washh Allah na, Innoh nima zubo min abincin in ci kafin mu wuce yunwa nake ji ko karyawa banyi ba kafin na fito," Kallon ta suka yi gaba d'ayan su cike da mamaki, yatsina fuska tayi tace, "To ban girka ba, ko rannan ma daga gidan Sarki aka kawo min wanda Sule ya kawo muku, kin dai san ba wani girki na iya ba sosai,jiya ya kawo kayan miya har da su nama da kifi wai ayi girki, haɗe su nayi na jefa a fridge ba zan iya ba," "Kashhh amma dai Mommy an ji jiki, yanzu a kawo miki nama da kifi ki kasa sarrafa wa? To idan baki iya yanzu ba sai yaushe zaki iya? Kin ga muje mu dawo naje gidan naki naga abinda zan iya taimaka maki da shi, ke baki san akan girki ba kaɗai sai ku samu matsala da namiji? Tabdijam, a gaskiya Yaya wannan dik laifin ki ne,habaa yarinya kamar Mommy ace tana fad'ar bata iya sarrafa abinci ba kanta tsaye? Inaaaa ba za a yi haka da ni ba, maza ci ki tashi mu bazama kasuwar mu gama da can mu je gidan naki naga uwar da kike yi," Tura baki Mommy tayi tana ƙunƙuni tana juya ɗan waken da Innoh ta zuba mata, Innoh kuwa gum tayi da bakin ta, dan kuwa bata da abun fad'e, kuskure ne an riga da an tafka shi, yarinyar da take ganin tana baiwa wahala da aikin gida wato Saddiqa babu abinda bata iya girkawa ba sai wanda bata sani ba,idan saddiqa tayi girki har santi take yi, haka Ɗan liti ma har so yake ace Saddiqa ce tayi girki ko Yadikon ta. A gaggauce suka kammala cin abincin su Ameerah ta fito sanye da hijabi da niƙabi wai zata bi su, babu wanda ya hana ta sai suka miƙe suka fita baki d'ayan su, a waje suka tarar da motar Abdul yana kwance ya lumshe ido saboda matsananciyar yunwar da yake ji,nan take Mommy ta saki salati tace, "Laaa ni fa na ma manta tare muke da shi, gashi shima be karya ba," Wani mugun kallo Naja ta sakar wa Mommy sannan ta ja hannun ta ta mintsine ta, ƙara Mommy ta saki tana yarfe hannu, cike da jin haushi tace, "Sokuwar banza kawai, ai sai mu koma ki shigo da shi a zuba masa abincin yaci kafin mu wuce, kaiiii ni dai Naja ina ganin tashin hankali yau," Cikin sauri ta ja hannun Ameerah suka koma ciki, a gaggauce ta samo kwano mai kyau aka zuba wa Abdul ɗan wake da mai da yaji aka nemo spoon aka saka masa aka kai soro, tabarma Ameerah ta shimfida sannan ta koma ta samo kwanon silver mai murfi aka zuba masa ruwan randa aka ajiye, Mommy ce ta shigar dashi soron tana ta zumb'ura baki tace masa, "Bismillah, ni na manta baka karya ba sai da muka fito, dan Allah kayi hakuri,anjima zan yi maka girki mai daɗi idan mun dawo na yi alƙawari," Murmushi yayi ya ja kwanon ya bude, ɗanwake ne yayi masa sallama, yaƙe yayi mata dan kuwa baya cin ɗanwake, gudun kar tace ya raina wa gidan su sai ya ɗauki cokalin ya fara kai wa bakin shi da bismillah,yana fara ci a hankali ai ya ji ba irin wanda ya saba ci bane na flour wannan an yi masa had'in wake, dawa, da alabo,santsi da daɗin shi ne ya sa Abdul cinyewa tass ya yi hamdala dan kuwa baya jin zai iya shan wannan ruwan,hamdala yayi ya tashi ya karkad'e jikin shi yace su same shi a mota. Mommy ce ta zauna a gaba Naja na bayan ta, Ameerah kuwa buɗe saitin bayan Abdul tayi ta zauna, da sauri Abdul ya juya yana kallon ta dan ganin me ta shiga dashi iskar motar ta sauya nan take? Gani yayi hannun ta babu komai sai wata ƙaramar baƙar leda, jinjina kai yayi da ya gane tsabar tsagwaron warin jikin tane haka, Naja ta gane dik abinda ke faruwa dan haka sai taji kunya duk ta kama ta, banda harara babu abinda take zabga wa Ameerah har suka isa kasuwa. Bayan fitar Ameerah da Naja ne Abdul ya baiwa Mommy kuɗin da za su sai akwati da nashi gudummawar, godiya ta dinga yi masa sannan ta fita ta same su, Naja tayi wa bayanin komai sannan ta tabbatar mata da tace masa ya jira su su gama siyayya ya maida su gida. Bata gama rufe bakin ta ba Abdul yayi mata waya, murmushi tayi ta dauka ta kara a kunnen ta, cikin wata iriyar murya taji Abdul yace, "Baby zan wuce gida ciki na na juya min, zan aiko Sultan ya ɗauke ku idan kun gama," Kafin ta bashi amsa ya kashe wayar shi saboda yanda cikin shi ke juya masa, tunawa yayi da kodai Ameerah ce tayi sakun ɗan waken da ya ci dazu a gidan surukan nashi? Wani yunƙurin amai ne ya taso masa ya kulle motar ya bata wuta ya bar kasuwar a guje. Abdul bai tsaya a ko ina ba sai a gidan Sarki, yana isa ya tarar da gidan an cika da mata ana ta hira, d'akin shi ya shige ya wuce band'aki ya hau kwarara amai, yana tsaka da amai yaji zawo ya kama shi, da gudu ya cire wandon shi ya hau saman toilet ya hau zazzage cikin shi, ya jima yana zawo da amai kafin ya samu salama ya yi wanka ya gyara wajen ya fito a daddafe,a gado ya kwanta yana maida numfashi,da kyar ya tashi zaune ya janyo first aid kit ɗin shi ya buɗe ya ɗauki maganin amai da gudawa ya sha da ruwan roba sannan ya koma ya kwanta yana numfashi da kyar, bacci ne mai daɗi yayi gaba da shi cikin salama. A can kasuwa kuwa siyayya ta yi siyayya sai Ameerah taga Naja na kwasar turare da tooth paste da brush, murmushi tayi tace, "Kamar kin san kuwa se da Shamsu yace a sai turare da yawa," Tsaki Naja tayi ta banka mata harara tace, "To ba dole ba Ameerah, kin kuwa ji warin da kike yi? Ban taɓa jin irin warin nan ba tinda uwa ta ta kawo ni duniya, haba Ameerah, me yasa kike yin abu kamar ba mace ba? Ki duba ki ga yanda Mommy ke zuba gayu, dik inda ta zauna sai ƙamshi ya kama wajen, ko abu ta riƙe sai kin ji ƙamshi a jikin shi,gaskiya yanzu ne na san Yaya ta tafka kuskure, ko me muke so mu zama ko mu samu sai fa mun taimaki kammu," Shiru suka yi gaba d'ayan su dan kuwa daga Naja ta gama da Ameerah sai ta koma kan Mommy, a haka suka gama siyayya wajejen ƙarfe biyu na rana, mommy na kiran Abdul sai taji wayar na ta ringing amma ba a ɗauka ba, ƙarshe har sun yanke shawarar yaran dake musu dako su samo musu adaidaita su hau, sai ga kiran Sultan ya sanar dasu inda yake, Ameerah tafi su sanin kan kasuwar ita ta ja su suka tafi, a daidai wannan lokacin rana ta sake dukan Ameerah ita kanta da kyar take shaƙar jikin ta,gudun tafka abun kunya kar Sultan yaji warin da take yi sai tace su yi gaba akwai inda zata je,Naja ce ta fara faɗa ko kula ta Ameerah bata yi ba ta wuce. Da kuɗin hannun ta ta koma kasuwa ta hau siyayyar banza da wofi kawai dan ganin tana da kuɗi,ba tare da ta yi tunanin adana su ba ko a gaba za su yi mata amfani ta kashe dubu takwas sannan ta ɗauki hanyar gida a ƙafa ta lungunan da ta saba bi,samarin ta na da ta dinga gani ta cikin niƙabi tana murmushi ita kaɗai har ta isa gida, a tsakar gida ta tarar da Innoh da su Naja da Mommy da mutanen unguwa an baje lefen ana ta kallo ana yabawa,Innoh da bata da sirri sai da ta sanar da mutanen unguwa kafff yanda aka yi Shamsu ya bada kuɗin lefe, da yanda mijin mommy ya bada na akwati da karin kuɗin da suka ƙaro kayan lefen, takaici ne ya sa Naja jin haushin kanta da ta bawa Innoh labarin abinda ya faru, tashi tayi ta hau haɗe kayan tana faɗin, "To jama'a muna gayyatar ku gobe da yamma za a kai amarya ɗakin ta, duk wadda take so a raka amarya da ita sai ta shiryo tazo," "To Allah ya kaimu, Allah yasa albarka," Haka mata suka yi ta sanya albarka, Ameerah kuwa ta zame ta wuce bangaren Baabaa ta zauna tana ta ciye-ciyen abubuwan da ta siyo a kasuwa, tana duba sauran tarkacen da ta siyo. Bayan tafiyar mutane ne Naja ta kunna Icce ta haɗa ruwan wankan da ta zuba masa ganyen magarya a ciki kamar zata wanke gawa,sai da ruwan nan ya tafasa ya tafarfashe sannan ta kindima a ƙaton baho ta surka tace wa Ameerah ta zo suje ta wanke ta,shaving stick ne a hannun ta da sabulu da soso, sai kwalbar turaren almuski, kuka Ameerah ta fara yi tana faɗin, "Alqur'an ni bana so ki barni nayi wanka na da kaina, haka kawai da girma na da komai ki tasa ni a gaba kice zaki yi min wanka?" "Yasin se na miki wankan dan uwar ki,kin ji warin da kike yi kuwa Ameerah? Ke yanzu ba abun kunya bane namiji da kan shi yace ki sai turare da yawa saboda yana jin wari a jikin ki? Kin san Allah idan baki shige cikin bayin nan ba na ɗakko iccen can sai na dake ki dashi, kin san hali na ai,lokacin wasa a yi wasa, lokacin da ba na wasa ba a maida hankali a yi abinda ya dace haba," Tin Naja na faɗa sai da ta koma lallashin Ameerah kafin ta yarda suka shiga bandakin,ba ƙaramin daurewa Naja tayi ba wajen wanke Ameerah har tayi mata shaving,wani irin wari take yi mai maƙaƙi a wuya,ita kanta da aka gama yi mata wankan aka yi mata shaving hammata da ƙasan ta sai da taji iska na shigar ta, a bakin ƙofa ta tsaya ruwa na ɗiga daga kanta da ya sha wanki da omo da ruwan toka tsabar dattin da ya haɗiya. Brush sabo Naja ta ciro da toothpaste ta baiwa Ameerah tace ta wanke bakin ta, babu musu ta karba ta wanke bakin ta tasss har tana ji wa kan ta ciwo, tana gamawa ta lakuci toothpaste ɗin ta sha tace, "Aunty Naja wannan makilin ɗin akwai shegen zaƙi kamar an saka masa sikarin," "Ko uwar sikarin aka saka masa ba, dalla bani nan,gashi nan kullum da safe da dare ki dinga wanke bakin ki da shi, da kin ga gashi ya fara fitowa a hammatar ki da gaban ki ki saka irin wannan (shaving stick) ko reza ki aske gashin wajen saboda dik wankan da zaki yi idan da gashi a wuraren nan zaki ji kina bashi musamman idan da damshi a jikin su, Ameerah ko baki yin kitso ki dinga wanke kai kina gyarawa dan Allah, ki duba Mommy ki gani, bata kitso amma saboda gyara gashin ta da take yi gashi nan ya koma kamar na turawa,da da bata waye ba ana saka kumfar lox tana cinye gashin gashi yanzu an waye ana amfani da kayan kamfani ya dawo," Dariya Naja da Ameerah suka hau yi, ita kanta Mommy bata ji haushi ba ta tabbata maganar Naja gaskiya ne, dan dama tana da gashi danƙarewa da cinyewar da ya dinga yi a baya dik ta dalili rashin kulawa mai kyau ce,yanzu da yake samun kulawa gashi nan sai san barka,murmushi ta sake yi tace, "Auntyn mu maganin kukan mu, Allah dai ya kawo miki miji ya mori wannan gayun naki, ni fa ina mantawa da shekarun da ke tsakanin mu dan sai in dinga jin ki kamar wata ƙawa ta Aunty Najancy," "Ehhh tinda ban kai uwar ku girma ba dole ku raina ni mana, da jikin Babar mu nayi bana Baba ba da kun isa ku ganni yar firit haka har ku raina ni?" Innoh kanta ta ji daɗin yanda ƙanwar tata ta gyara mata Ameerah, godiya ta dinga yi mata, suna yin la'asar ta sa Mommy a gaba dan su tafi gidan ta ta ga ita kuma wace uwar take yi a gidan da ta kasa girka komai. Kuɗi Innoh ta baiwa Naja ta ƙi Karb'a tace gudummawar ta kenan a matsayin ta na uwar Ameerah,godiya Ameerah tayi wa Naja wanda yin hakan yayi matuƙar basu mamaki, duba da yanda halin ta yake bata san tace wa kowa na gado ba. Daf za su bar gidan ne suka haɗu da Sule suka gaisa ya wuce gida su kuma suka tafi gidan Mommy. ************************ Kwance take a saman makeken gadon da yake mallakin tane a yanzu in ji Baabaa, dan kuwa abinda yake mallakin Manniru ai na matar Manniru ne a cewar ta, ta yi wanka ta sanya rigar shan iska gaban ta dik littattafai ne da ta gama karantawa ba jimawa,wayar ta ce take ringing tana neman agaji,cike da murmushi ta sanya hannu ta ɗauka ta amsa kiran tare da karawa a kunnen ta. "Hayyakallah ya ruhee," 'Hayyakillah habibty,ya kike, ya yau? Ina fatan jarabawar yau bata baki wahala ba ko?' "Alhamdulillah Zaujee, komai normal,jarabawa kam tayi sauƙi sosai dan kuwa ban zaci Physics ɗin nan zai min daɗi ba," 'Alhamdulillah power of du'a kenan ake faɗa maki,ko kin manta kalar addu'ar da muka dinga yi?' "Ban manta ba gaskiya, na gode sosai masoyi, ya su Ummina da Abbah da su Hafsat? Ina fatan kowa na lafiya? Ya office?" 'Dik alhamdulillah kowa na lafiya, office kuma babu daɗi,' "Ayyaa ka ƙara hakuri, Allah ya sauƙaƙa lamuran," 'Ameen, amma kam lamura ba wani saukin da za su yi kina nesa dani, na matsu ki gama jarabawar nan,wai ni sauran sati nawa ma ki kammala ne?' Dariya sosai Saddiqa tayi kafin tace, "Sauran wata biyu na kammala," A rikice Munir yace, 'What ! Wata biyu fa? Tabb lallai kuwa zan dawo Ƙauye na zauna har se kin kammala dika,' Dariya ta sake yi sannan tace, "Wasa nake yi maka, sauran sati biyu da kwana biyu inshaa Allah," 'Ai na san tsokana ta kike yi, ko da bamu kai watannin da kika lissafa ba balle yanzu da abubuwan technology ya yawaita,Allah ya bada sa'a my love, i miss you so much,' Lumshe ido Saddiqa tayi tana jin wata iriyar kewar Munir da shauƙin son ganin shi na taso mata a ran ta, hakan ne ya haddasa bugawar zuciyar ta ya ƙaru hawaye suka fito daga idanun ta, cikin murya mai rawa tace, "I miss you too my love,ina son ganin ka sosai Hubby," 'Da gaske kina son gani na? Kashe ki kunna data mu yi video call,' Cike da murna kuwa tayi yanda yace, a lokacin da ta ga Munir kwance a gadon shi na Abuja sai da ta tsorata, tayi zaton ko a ƙasar waje yake, shanye mamakin ta tayi dan kuwa an ce dama Alhaji Baban Gida na da kuɗi sosai, shi kuwa Munir banda kallon surar jikin ta babu abinda yake yi, cikin furzar da iskar bakin shi yace, 'Alhamdulillah ya rab,' "Na'am? Kayi magana ne?" Da sauri yace, 'Ah ah ban ce komai ba, uhumm gani to kin ganni, me zaki yi min?' Murmushi tayi cike da jin kunya sannan tace, "Kallon ka kawai zan yi tayi har sai na ƙoshi," Ba tare da zato ko tsammani ba Baabaa ta afko d'akin tace, "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una Saddiqa ke da wanne aljanin kike magana nake jin muryar ƙato a dakin naki? Na shiga uku ni Baabaar Abbe me zan ce da Manniru idan yaji labarin matar shi tayi gamo da aljani na miji?" Dariyar Munir ce ta karaɗe ɗakin ta sa baba kurma ihu tana salati tare da karanta kulhuwallahu ahad,dariya sosai Saddiqa take yi tana nuna wa Baabaa Munir ta screen ɗin sabuwar wayar tata, a hankali Baabaa ta natsu tace, "Yanzu a haka zan iya ganin Baban Gida Shima?" "Sosai ma, zaki iya ganin duk wanda kike so ta haka Baabaataaa" Saddiqa ta faɗa tana rungume Baabaa da har a daidai wannan lokacin nutsuwa bata gama shigar ta ba, haka suka ci gaba da hira suna ta wayar wa da Baabaa kai game da video call. A can gidan Mommy kuwa...... [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 56: Idanun Naja akan gajeran wandon Abdul ya fara sauka, cikin sauri ta kauda idanun ta tana salati tare da tafa hannaye ta duba ƙasa inda bireziyar Mommy ke kwance kamar a nan ne ya kamata ace an gan ta, dik irin halin jin kunya da nauyin da Naja ta shiga bai dami Mommy ba dan kuwa cire mayafin ta tayi tare da yin wurgi dashi a ƙasa, sannan ta yarda takalman ta a tsakiyar parlour zata shige kitchen, cikin tsawa Naja tace mata, "Kina shiga kitchen ɗin nan ba tare da kin kwashe kayan nan ba Hadiza zan ci maki mutunci, shashasha mara hankali da tunani kawai, yanzu da ace surukar ki ce tazo gidan nan haka zata yi wannan mummunan gamon?" Cikin rashin fahimta Mommy ta juyo ta kalli Naja dake sababi tace, "Aunty Naja wanne kaya zan kwashe kuma daga zuwan mu? Ki bari na d'akko maki lemo da ruwa ki dan jiƙa maƙoshin ki mana," "Abinda yafi lemo da ruwa zaki ɗakko min, Hadiza ki fita a ido na na rufe fa ! ba zaki wuce yanzu ki kwashe ɗan kamfan mijin ki dake zaune dafi'an bil amanati a saman kujera ba? Dibi rigar maman ki a ƙasa yanzu dik wanda ya shigo ya gani ya san me ya faru? Ke baza ki ji kunya ba ashe?" Wata iriyar dariya Mommy ta kece da ita har tana zama, cikin dariyar ta hau kwashe kayan su ta nufi ɗakin ta ta wurga su a saman gado ta fito tana ci gaba da dariya tace wa Naja, "Gaskiya Aunty Najanmu kina da matsala, to meye dan an ga boxer ɗin shi da bra d'ina a parlour? Naga dai ba mu aka gani tsirara ba ko?" "Na yarda baki da hankali Mommy, abinda zuciya ta ke ta raya min ya tabbata, mu je kitchen ɗin mu fara ɗora abincin idan yaso sai mu dawo a gyara gidan lokaci na tafiya, yanzu ace gida ko sati ba a rufa ba da shigar shi dik kin halaka shi haka? Allah ya kyauta," Cikin ƙanƙanin lokaci Naja ta sa Mommy a gaba dan dole ta nuna mata yanda zata dinga kula da kayan miya da nama idan an kawo, da yanda zata dafa ta soya har ta dafa shinkafa da miya, suna gyaran gidan take koya mata yanda ake yin jalof ɗin taliya da na shinkafa,ta koya mata yanda ake soya dankalin hausa da na bature da yanda ake yin simple abubuwan da ta sani a matsayin ta na wayayyiyar da ta shiga garuruwa ta san abubuwan wayewa, a dik abubuwan da ake koyawa Mommy tafi gane na bedroom, dan bata da sauƙi ta wannan ɓangaren, a kullum so take ta dinga burge Abdul da salo-salon da zai zauna daram a zuciyar shi, gane hakan da Naja tayi ne ya sanya ta sakin murmushi ta samu locker ɗin dake gefen gadon Mommy da ta gama gyarawa ta zauna tace wa Mommy, "Zauna Mommy na sanar dake wani abu da baki sani ba," Waje Mommy ta samu ta zauna ta baza kunnuwa tana son taji wani kayan matan da Naja zata sanar da ita dan ta haɗa ta sha ta gigita Abdul a gado, cike da zumud'i take kallon Naja, cikin kwantar da murya Naja tace, "Hadiza ina so ki san cewa shi aure fa da kike gani ibada ne, ba wai dan kawai muna son mutum yana son mu ba sai kawai mu aure shi saboda wannan soyayyar, ah ah soyayya na da mahimmanci a cikin aure domin tana sawa a yi ibadar ta daɗin rai babu takura kamar auren da aka yi shi na dole. Hadiza ina so ki sani ko da kika ga muna zuwa neman taimako ba wai hankali da tunani muka rasa ba, muna nan muna fatan watarana mu tuba mu dena dan babu bawan dake fatan ya dawwama a zunubi sai wanda bai san wanene Allah ba,idan kasan Allah kasan cewar in ka aikata kyakkyawa zaka haɗu da shi ta fuska kyakkyawa sannan idan ka aikata mummuna zaka haɗu da shi ta mummunar siffa to fa dole ne ka dinga addu'ar kar Allah ya kashe ka a kan hanyar ɓata, dan haka ki buɗe kunnen ki da kyau ki saurare ni, kar ki yi min kallon ban san me nake yi ba. Hadiza ba kwanciyar aure bane kawai jigon aure,kina iya zama macen da tafi kowacce mace gamsar da mijin ta koda mata huɗu gare shi, amma yafi son wata akan ki, amfanin ki a wajen shi kawai shine ki kawar masa da kishin ruwan shi, da ya samu natsuwa dake ya komawa wadda yake asalin so,kin ga kenan ba kwanciyar aure ne kaɗai rayuwar aure ba ko ? tinda ana iya zama da wadda aka san ba za a iya kwanciyar auren da ita ba saboda wata lalura da take da ita, amma sai soyayya ta sa a kasa rabuwa da ita. Mommy ki sani ita rayuwar aure ana so mace ta iya girki dai-dai gwargwado, ko da baki zama ƙwararriya ba kar a same ki sifili a bangaren girki wanda a yanzu a matakin da kike kenan,ba a son ƙazamar mace Hadiza, koda ba a same ki mai tsananin tsafta ta bada misali ba to fa kar a same ki ƙazama, sannan ana son mace mai ladabi da biyayya mai sanin ya kamata,macen da ta iya magana mai daɗi ba a tsaitsaye ba kamar shinkafar da bata dahu ba, sannan ana son macen da ke da kirki ma'ana mara rowa mai yawan fara'a da kamun kai, Hadiza a halayen ki kowa yana yaba maki baki da rowa sam, to dan haka ina so ki haɗe wadannan abubuwan da na sanar dake ki riƙe gam, saboda da su ne zaki juya Abdul koda bamu sake nemo maki taimakon komai ba,wannan Shagwab'ar da naga kina yi masa a mota ɗazu ki riƙe ta da kyau domin kuwa babban makami ce, Hadiza ba a ce sai kin zama 100% ba a gidan mijin ki, ana so dai ki zama kina da kaso 80% a ɓangaren kula da gida da mijin ki. Dan haka ga wani haɗin zan sanar dake ki dage ki dinga yin shi, zaki sha mamakin yanda mijin ki zai gigice wajen son ki musamman in kina kula da cikin shi da tsaftace gidan ku. Kaninfari Citta Minannas Kabewa/kabushe Madarar shanu/Ta gwangwani Dankalin hausa Kwakwa Zuma Dabino Kinga da farko dai zaki samu kayan ƙamshin nan, citta busasshiya ko ɗanya ma idan kina so zaki saka ta ta ma fi ƙamshi da daɗi a wannan haɗin, ki daka kaninfari da minannas ko kuma ki deb'i kadan ki jiƙa dik yanda kika yi dai, sai ki samu kabewa ki mata tafasa ɗaya ki bari ta huce,sai ki fere dankalin hausa ki niƙa ki tace ruwan, ki niƙa kabewa ki zuba mata wannan ruwan dankalin, ki cire wa dabino k'wallo ki jiƙa ki niƙa ki juye a saman kabewar nan,ki zuba zuma,madara da wannan ruwan kayan ƙamshin ko garin nasu,ki samu kwakwa ki goga a ciki ki juya sosai, sai ki zauna ki sha ki ƙoshi,idan kina so kina iya sanyawa a ma'adanar

Chapter 36 of 70