Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bugawa kafin Mommy ta fito sanye da doguwar riga baqa mai manyan flowers gaba da baya a jiki, sai ta yafa mayafin rigar a kan ta gashin kanta baqi sidiq ya bayyana ta gaban goshin ta, leb'en nan sai ɗaukan ido yake yi saboda man da ta sanya, idon ta kuwa sanye yake da kwallin su na sihiri rambad'ad'au har wani ado tayi dashi a saman idon,cikin takun ta mai ɗaukan hankali ta isa gare shi ta tsaya a jikin qofar gidan su tana jifan shi da wani irin kallo mai sace zuciyar wanda ake  kallon, lumshe idanun shi kawai yayi tare da sauke wata wahalalliyar ajiyar zuciya mai qarfi, jingina yayi da qofar motar shi yana jifan ta da kallon da yake narkar da duk wata gab'a ta jikin ta, cikin sanyin shi da kamewar shi yace, "Anya Hadiza kin san cewa kece nutsuwa ta a yanzu? Sannan kece zaman lafiyar zuciya ta da kwanciyar hankalin gangar jiki da ruhi na, Me yasa kika qi amsa kira na kuma na kira kika kashe wayar ki ko so kike zuciya ta ta buga na rasa raina gaba ɗaya ne?" Cikin wata iriyar murya mai sace zuciyar mai saurare Mommy tace, "Babu caji ne shi yasa ta mutu," Ajiyar zuciya ya sake saukewa dan kuwa muryar ta dama yake so yaji, ya rasa me yake fusgar shi gare ta da yake sanya shi jin kamar zai haukace akan ta, a hankali ya fara takawa zuwa ɗaya gwfen na motar shi ya buɗe mata sannan ya koma mazaunin direba ya shiga yayi mata nuni da ta shiga itama, qin shiga Mommy tayi sai ta samu gefen inda ya zauna ta jingina kawai tana ci gaba da lumshe ido tana ware su akan fuskar shi, dik wani salon da zata yi dan ya kalli cikin idanun ta yi take yi,Abdul fito da qafafun shi yayi yana shaqar wani qamshi na musamman a jikin ta, (qamshin turaren wajen boka ne da aka tsaface dan ya so ta). "Please ki yi magana mana kin barni ina ta surutu ni kaɗai kamar aku, ko baki ji daɗin gani na bane, da alama na takura ki da yawa ko? Hadiza bana jin zan iya bacci idan ban sake ganin ki ba yau," Murmushi tayi ta sunne kai ita a dole taji kunyar shi, a zahiri bata son yin magana saboda kar ta rusa musu plan ɗin su ita da Innoh, amma a cikin ranta tana son ta furta masa kalmar so gwargwadon yanda kunnuwa da zuciyar shi zata iya ɗauka,tana tsaka da tunani taji yace, "Ina fatan dai idan aka zo neman auren ki gobe mutanen gidan ku ba za su ce na yi sauri ba? Domin kuwa da za su taimake ni su bani ke yau ma da babu abinda zai hana ni auren ki Hadiza, ban san yanda zan kwatanta miki yanda nake jin ki a raina ba, amma ni dai na san ina son ki, kuma ba zan iya dena son ki ba har qarshen numfashi na," Murmushi Mommy ta saki sannan tace, "Da gaske kana so na Yah Abdul? Akwai abubuwan fa da baka sani ba a game da ni, idan ka sani daga baya kana ganin zaka iya ci gaba da sona har ka aure ni kayi rayuwar aure dani?" Kallon ta yayi da kyau dan ya bata tabbacin yana son ta yace, "Hadiza ina son ki zan aure ki, kuma ko wanne irin hali gare ki zan jure na zauna dake a haka, Hadiza bazaki gane yanda nake jin ki a raina ba saboda ke baki sona kamar yanda nake son ki shi yasa," "Humm Yah Abdul kenan, ta yaya mace lafiyayya mai hankali zata ga namiji kamar ka tace bata so? Ai idan dai ba ciwon hauka take yi ba ba zata taɓa qin ka ba,balle ni mai hankali, Yah Abdul na fara son ka a ganin farko da na yi maka dik kuwa da irin tashin hankalin da ka riske ni a ciki be hana ni yabawa Ubangiji ba akan Kyakkyawar halittar sa ba" Hamdala Abdussaboor kawai yake zubawa yana kallon Mommy, ji yake kamar ya sace ta ya gudu da ita ya b'oye ta a waje mai kyau ya dinga bata kulawa kamar sarauniyar dik duniya. Haka Mommy da Abdul suka wanzu suna bayyana wa junan su irin yanda suke so da qaunar junan su tare da fatan kasancewa a inuwa ɗaya. ****************************** Basu isa cikin garin kano ba sai da aka gabatar da sallar magariba sannan suka isa,bayan driver ya sauke mutane a tasha Billy ta bashi kuɗin da ta yi masa alqawari ta bar tashar, a bakin hanya Man ɗin ta da suke ta waya da chatting ya ɗauke ta sai gidan Hajiya k'waisa, suna isa mai gadi yaqi buɗe musu qofa dan hango Billy a mota da yayi, cike da masifa Billy tace, "Ba zaka buɗe gate ɗin bane ko me? Ko kai makaho ne ko kurma da ka tsaya qiqam kamar icce ka qi budewa?" "Ranki ya dad'e Hajiya ce da kanta tace kar na sake na sake buɗe maku gate ke da wannan me bakin dorinar ruwan," "Ka buɗe min na shigo ko kuma idan na kira ta a waya ta baka tabbacin ta cire dokar ta na kore ka qauyen ku da kai na," Cike da tsoro mai gadi ya wangale gate, nan take Man ya shige da motar shi gidan k'waisa ya ajiye a ma'adanar ajiye motoci, cikin isa Billy ta fito dan kuwa bata son su Sallau su kawo mata raini,buga qofar da zata sada su da cikin gidan suka yi kafin daga baya Zuby ta buɗe musu ta ja ta tsaya a bakin qofar tace, "Hajiya bata nan sun fita da Oga Sam,kuma ta jima da bada umarnin kar a barku ku shigar mata gida ke da Mommy, ban san me yasa aka buɗe muku gate ba ma yanzu," "Lallai ne Zubaidah, wato wuyan ki har yayi kaurin yanka ko? Da kyau bari na kirawo Hajiyan na sanar da ita me kike yi min, a sannan ne zaki gane cewa Uwa bata fushi da ɗan ta sai dai ta ladabtar da shi," Cike da b'acin rai Zubaida ta matsa tana qunquni tace, "Ai kuwa anyi asarar uwa da haihuwar ma baki ɗaya," Da jin Hajiya bata nan Billy ta ja Man suka wuce d'akin ta suka kulle dan ɗebe wa juna kewar da suke tattare da ita kafin Hajiya ta dawo. Kusan awanni uku suka ɗauka a gidan kafin Hajiya ta dawo ita kaɗai,cike da gajiya ta hau kiran Sallau dan ya kawo mata abin sha, cikin sauri Sallau ya tafi cika umarnin ta, kamar abun almara haka Hajiya k'waisa ya d'aga kai sama ya hango Billy da Man ɗin ta na sakkowa daga saman benen ta manne da juna kamar suna cikin gidan su na kan su.............. [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 40: Cike da mamaki Hajiya k'waisa ta miqe tsaye tana ganin ikon Allah, cikin kama hab'a da dafe qugu da hannun hagu yace, "Lale maraba gasasshe kura taga baqin jaki,mata k'urasa dangin shaid'an to ni K'waisan alheri me na ci na asham da zan yi ramuwar azumi kuma yau? Sallauuu! Sallauuu! Je ka kira min mai gadin nan mara amfani ka kuma tattaro min kan ku da kai da su Ruby ku zo nan na ji shegen da ya buɗe musu gida na da ban yi wahala da kowacce tsinanniyar qaramar karuwa na samo abina ba," Har Sallau ya taka da sauri zai fita Billy ta qarasa da sauri gaban Hajiya K'waisa ta fashe da kuka ta dafa qafar ta tana faɗin, "Dan girman Allah'n da kike wa Sallah ki dakatar da shi ki ji uziri na," "Toooo wata sabuwa in ji 'yan caca ! ehh lallai dole na saurare ki dan kuwa maganar ki ta tuna min ko sallar asuba ban ba ga kuma duhu ya riske ni, uhumm ina jin ki, ina son sanin dalilin zuwan ki gida na bayan kun yanke wa kan ku hukuncin aure kun ajiye karuwanci? Sannan kin kawo min 'yar daba ko kuma in ce mayya dangin masu shan jini gida har taso zuqe mana jinin jijiyar wuya da tsintsiyar hannu har gida, sannan yanzu ki zo ki ce zaki hau yi min kukan da na san na makirci ne irin na karuwa?" Hannu k'waisa ya d'aga wa Sallau yayi masa nuni da yatsan shi mai dogayen farata akan ya koma bakin aikin sa ya bar su da Billy, yana tafiya yayi wa Billy da Man dake tsaye yana jinjina kaidin mace nuni da wajen zama kafin shima ya zauna a kujerar da ya tashi ya harɗe qafa ya dora zaratan hannun shi a saman qafar tashi yana jijjiga su yace, "Uhumm se aka yi yaya?" "Hajiyata na zo ne in baki hakuri akan dikkan abinda ya faru a baya wanda ban taɓa tunanin zai faru ba, na ɗauki hakan a matsayin ɗaya daga cikin qaddarar rayuwar da ta haɗa ni da ke tin farko kika taimaka min a rayuwa ta ita ce ta sa na janyo mommy cikin rayuwar mu dan nima na taimake ta har abubuwan da suka faru suka faru,amma na yi miki alqawarin ba zan sake maimaita kuskuren da na yi a baya ba, ke ce mutum ta farko da ta inganta rayuwa ta irin ingantawar da uwa ce kawai zata baiwa 'yar ta,sannan ubane kawai zai kula da abinda ya haifa irin yanda kike yi min,Hajiya kin sani akan son zama dake da nake na aikata abubuwan da ke da kan ki kika roqe ni kar na shiga tsakanin ki da Mommy wanda da na san rabuwar da za a yi kenan da na yi duk yanda zan yi na raba ta da gidan nan kafin ta kai ga cin amanar ki har ta sanya hannu a jikin ku,cikin adalci da kyautatawar ki Hajiyata naga kin dawo mana da dik abinda muka samu a nan wanda da wata ce ko sisi ba zata bamu ba, dan Allah Hajiya kiyi hakuri ki maida ni matsayi na a wajen ki," Jikin Hajiya K'waisa ne yayi sanyi ganin irin kukan da Billy ke yi da kalaman da ta zuba cike da hikimar sace zuciyar K'waisan ,nan da nan ya tashi ya zauna a kujerar da Billy ke zaune ya rungume ta yana lallashi, dan kuwa yana son Billy yana jin ta kamar qanwar shi,shi yasa kafin ya kore su ma sai da ya daure ya ɗauki zugar Samuel,wanda daga baya ma akan yawan yi wa Samuel zancen Billyn saida suka samu sab'ani yayi tafiya canada yayi kwanaki be nemi K'waisan ba, da k'yar ta shawo kan abun ta suka koma dai-dai. "Ya isa haka na yafe miki sai dai ina da sharad'i, dik da dama ko Mommyn ma nice na dage ki kawo min ita, amma a gaskiya bana so ki sake haɗa ni da kowa a barni da kai na na samu wadda zan raina na maida ita abinda nake so a wannan harkar,sannan dik sanda Baby yazo yana faɗa akan dawowar ki gidan nan ke ko zagin ki yayi dole ne ki jure, idan kuma kin san sa'insa zaku yi da shi tun wuri ki tattara komatsan ki ki koma qauyen ku, dan kuwa ba zan ɗauki raina min masoyi ba," "Na gode na gode sosai Hajiyata dama na san uwa ba zata yi fushi da 'yar ta ba,inshaa Allahu zan kiyaye dik abinda kika yi umarni akai, sai dai ina neman alfarma zan koma qauyen mu na zauna na wata ɗaya kafin na sake shawo kan iyaye na akan su barni na dawo aikatau dan kuwa magana taje har gaban sarkin garin mu yace kar a sake barin kowacce mace a qauyen mu fita aikatau.......uhumm Hajiyata Ina cousin d'ina da na sanar da ke a duk sanda na gama da bariki shi zan aura? To Mommy na can ta kasa ta tsare shi zata aura, d'azu yazo har d'akin mahaifiyar shi yake sanar da mu cewar a taimake shi a aura masa Mommy ko kuma ya mutu, wai ya tsane ni baya son sake gani na ko jin labari na in fitar musu a gida ,shine na fito na yo nan dan na san ke kaɗai ce zaki share min hawaye na,Hajiyata idan ya auri Mommy ni fa?" Kukan da Billy tasan yana d'aga hankalin k'waisa ta saki tana lafewa a jikin shi, nan da nan kuwa tsanar Mommy da haushin ta ya mamaye zuciyar shi, cikin masifa ya zame Billy a jikin shi ya hau tafa hannu yana faɗin, "Ai kuwa yanda ya ce ya tsane ki to kuwa itama sai mun sa shi ya tsane ta ta yanda ko inuwar ta ba zai so gani ba ballantana ita kanta, ki share hawayen ki ki kwantar da hankalin ki wanda ya taɓa ki ni ya tab'o," Da jin wannan kalaman daga bakin k'waisan alheri Billy tayi hamdala ta godewa Allah sannan ta ci gaba da zuga Hajiya K'waisa, qarshe dai Man da ya ga an manta da shi ya musu sallama ya tafi da alqawarin gobe da sassafe zai je ya maida Billy gidan su tace masa ba da sassafe zasu tafi ba sai dare dan kuwa so take hankalin kowa ya tashi idan sun neme ta sun rasa. ******************************* Yau babu makaranta su Saddiqa sun samu hutun kwana uku kafin su koma boko a ci gaba da shirin zana jarabawar WAEC da NECO wannan dalilin ne ya sanya Saddiqa komawa baccin safe da nufin bakwai da rabi ta farka ta zo ta yi abun karyawa ta gyara waken alale ta niqa almajirai su tafi talle, Ameerah kuwa daren ranar ta kasa bacci saboda tunanin zuwan Alhaji Baban Gida da maganar auren Munir da Saddiqa da aka yi wanda ita Saddiqa ta ɗauka Baabaa ta faɗa ne kawai saboda aljanun ta da suka tashi ba wai tana nufin hakan ba. Tsakar gidan shiru dan kuwa ko Baabaa ba zata yi qosai ba a ranar saboda ko waken ma bata gyara ba a jiya balle a kai ga maganar niqa, bayan haka ma yau babbar rana ce a wajen ta ta tabbata Baban Gida ba zai tsallake maganar ta ba zai zone a yi maganar auren Saddiqa da Manniru kowa ya huta. Shirun da Ameerah taji ne ya sanya ta tashi ta shiga wanka ta wanke bakinta da brush da toothpaste, sannan ta shirya cikin kayan sallar ta da take ji da su, dik da cewa ta rame ta yi fari fayauu sai uban dogon baki da manyan ido hakan bai hana ta yin kyau ba, d'akin Saddiqa ta shiga cikin sand'a ta buɗe hand bag ɗin Mommy ta ɗauki turaren sihirin da taji Innoh da Mommy na magana akai,ta duba da kyau ta jinjina kai sannan ta ɗauke kwallin sihirin shima ta sake lallab'awa ta bar d'akin, d'akin ta taje ta shafa turaren sannan ta saka kwallin ta koma ta mayar ta ɗauki mayafin Mommy na abayar ta ta zira takalmin Mommy baqi ta bar gidan gaba ɗaya da nufin zata je gidan su Munir ta sace zuciyar shi kamar yanda Mommy tayi wa Abdul. Sauri kawai take ta zubawa a qoqarin ta na isa gidan ba tare da ta haɗu da kowa ba, tin daga nesa idan ta hango namiji ko mace sai ta samu waje ta rab'e ta buya dan bata son tsautsayi ya gitta a samu akasi,tafe take tana fad'in, "....Iyi saboda an ga ni bana kawo kuɗi irin shafaffiya da mai Mommy shi yasa ake ware ni ba a son ci gabana ba kuma a son dik abinda nake so,to ni zan sama wa kaina mafita da farin ciki yau sai dai a d'aura auren nan da ni amma bada waccan munafukar ba,ni ce musu aka yi bana son jin daɗin kenan da za a bawa kowa zaɓin ran shi a hana ni nawa," Karaff taji ta daki mutum cikin sauri ta d'aga kai dan taga waye babu b'ata lokaci kuwa idanun su ya sarqe da na juna, qamshin jikin ta ya daki hancin shi,wani irin lumshe idanu yayi tare da sakar mata murmushi mai tsada. Bakin Ameerah na rawa ta hau nuna shi tana kulle idanun ta tace, "Amma dai shamsu ubangiji Allah ya tsine wa gaba ɗaya dangin ku na nan qauyen da na maqotan shi, Shamsu ka cuce ni ka lalata min rayuwa ta ba zan taɓa yafe maka ba har duniya ta nad'e," Kuka Ameerah take tana kumawa tare da zagin shamsu, shi kuwa banda bata hakuri da qoqarin riqe mata hannu babu abinda yake yi, cikin tsananin shauqin soyayyar da ta kama shi a cikin 'yan sakwanni yace, "Kiyi hakuri fitilar zuciya ta,tabbas zuciyata yau tayi gamo da haske mai walqiya da ya haskaka ta daga tsananin duhun da ta jima a cikin shi, Ameerah ki taimake ni ki karb'i soyayya ta idan na rasa ki ban aure ki ba mutuwa zan yi," "Za kuwa a yi jana'izar ka kafin azahar dan uban Mai Dusa, idan ka cika shege ka biyo ni gidan mu hyahyahya kawai,Allah ya saka min rusa min yhiri na da ka yi Allah ya tsinewa zuri'ar gidan Mai dusa," Dika bakin ta ta wage tana rusa kuka ta kama hanya zata koma gida dan kuwa magana ta qare, yanda asirin yake aiki shine idan ka saka turare da kwallin wanda ya fara shaqar qamshi kuma kuka haɗa ido dashi to shi zai maqale maka ya so ka har ya aure ka, ta riga ta san yanzu ko sau dubu zata saka ta rasa Munir dan haka tana jin Shamsu na biye da ita yana mata magiyar ta karb'i soyayyar shi ta masa banza ta yi gaba, suna tsaka da tafiya taga motar Munir ta wuce ta a hankali ta nufi gidan su, wani irin kuka ta sake rusawa ta juya tana neman madokin da zata sheme shamsu da shi ko ya mutu ta huta da baqin ciki, rasa abinda zata kwad'a masa tayi sai kawai ta kwashi gudu ta yi gida, Shamsu ma rufa mata baya yayi suka kasa tsere har gidan Ɗan liti. A tsakar gidan Ɗan liti kuwa Munir ne yake taya Saddiqa hura wutar murhu wadda fitowar ta kenan daga d'aki ta hau hura wuta zata ɗora ruwan zafi, Baabaa na ganin su ta hau washe baki tayi komawar ta d'aki tana fatan Allah ya dawwamar da farin ciki a rayuwar Saddiqa,Saddiqa kuwa gaba ɗaya ta gigice da tsoron kar Innoh ko Baban su ga abinda ke faruwa, ta sani Innoh na ganin haka zata hau kiran ta da sunayen 'yan iska kala-kala. Ameerah ce ta shiga gidan a guje tana kuka, ganin Munir na taya Mommy kunna wuta a murhu ne ya sanya ta a haukace ta je ta d'ebi ruwa a rijiya ba tare da ta kula kowa ba ta na gama jawowa ta sheqa a saman murhun tana huci ta hau zage-zage kamar jikar bamaguje, tsananin ɓacin ran abinda tayi ne ya sanya Munir miqewa tsaye a fusace zai yi mata dukan tsiya Ameerah ta sheqa da gudu d'akin ta tana gunjin kuka ta kulle qofar tana ci gaba da zagin su. Ɗan liti ne ya dawo daga siyo suger ɗin shan kokon safe yaga ta'asar da Ameerah tayi sai ya hau salati, cikin fushi kuwa Munir ya kalle shi yace, "Baba Saddiqa ba zata yi wahalar kunna wutar yin girki ba a gidan nan yau dan ba jaka bace ita, waccan mahaukaciyar da ta kashe wutar ta jiqa murhun ita ya kamata a sa ta kunna wutar ta girka abincin da mutanen gidan za su ci....ke zo nan !" Ya kira Saddiqa dake sanye da riga da zani da mayafi a rakub'e, cikin sauri ta isa zata durqusa ya damqi hannun ta suka bar gidan, Ɗan liti tsaye yayi yana kalle-kalle dan kuwa zuciyar shi a shafe take bata tunanin komai balle ya san ma matakin ɗauka, yana nan tsaye yaga Innoh ta fito yafe da mayafi da zani a qugun ta bata da riga a jikin ta kuma a haka tayi sallar safiya dan ba za a kira ta da sallar asuba ba,gaba ɗaya ana ganin qirjin ta saboda tsofewar mayafin jikin ta ta zubar da yawun da ya cika bakin ta wanda tin tana sallah ta tara shi saboda rashin wanke baki,cike da masifa tace, "Yanzu Malam kana tsaye yaro qarami ya gama yi maka tsiwa ya ja hannun 'yar ka suka bar gidan? To uban waye zai yi abun karin ga niqan waken alale nan dik ta tsallake ta bar gidan? Ka juya kaje ka nemo ta dik inda ta shiga ta dawo ta gama aikin dake gaban ta ," Baabaa ce ta fito tace, "Kin dai san yau ne ranar da nake saka ran auren Saddiqa da Manniru ya faru ko? Sannan wai tsayama ita ce matar gidan ko kuwa ke? Ko baki da 'yan matan da suka girme ta a d'akin ki da su ya kamata suna aikin komai a gidan nan amma saboda qin gaskiya da zalunci kike saka yarinya aikin da kika san yaran ki ba za su yi ba ! Innoh ki kiyayi Allah, kar ya yi maki kamun kazar kuku ki zo ki na ganin hukuncin yayi tsauri da yawa," "Ke dalla busasshiyar tsohuwa ki wa mutane shiru, magana nake da miji na ba ke ba,sannan Manniru ai ke kika damu da jikan ki, Ameerah ta tafi qarfin auren wannan siririn yaron, ni ai kin riga da kin sani ba qaunar haɗa zuri'a dake nake yi ba, dan haka ki kama tsufan ki,aiki kuma babu ruwa na da yaushe ne ranar auren ta, ko minti ɗaya ne ya rage indai tana cikin gidan nan sai tayi shi," "To mu zuba mu gani," Sallamar Shamsu ce ta dawo da Ɗan liti cikin hayyacin shi daga kallon sa'insan da su Innoh ke yi, gaba ɗaya ya rame ya fige ya fita a hayyacin shi,kai da ka gan shi zaka tabbatar da yana cikin damuwa da tashin hankali, abubuwa da dama na cin zuciyar shi amma bashi da iKon yin magana, tunawa yayi da sanda ya dawo ya tadda shamsu a qofar gidan nashi har suka gaisa yace masa wajen Ameerah yazo. **************************** A can Abuja kuwa Alhaji Baban Gida da iyalan shi ne suka shirya tsaf dan zuwa qauyen Ba Mugu Ummeen Munir murna fal zuciyar ta na jin hukuncin da Baabaa ta yanke akan ceto marainiyar Allah daga qangin wahala da bauta. A kanon dabo jirgin nasu ya sauka inda suka tadda Munir da Saddiqa na jiran su su ɗauke su zuwa qauyen Ba mugu su dira a gidan Ɗan liti..........[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨ *Assalamu alaikum dan Allah masu tambayar novel ɗin gidan Ɗan liti daga farko ku yi hakuri ku duba page ɗina dake a facbook mai suna HAERMEEBRAERH'S NOVELS ko a wattpad saboda an yi nisa da yawa ba zan iya koda yaushe in ta tura pages ba gaskiya. Shi yasa nakan ce ko da page ɗin farko bai yi maku ba kuna tarawa maybe gaba in ana comments zaku ji sha'awar karantawa. Idan kuma dik ba ku yin Facebook da wattpad ku yi haƙuri a gama a haɗa document na gode.* *Masu tambayar jiya ba a yi posting ba,to alhamdulillahi an dan binciko file d'ina ne ina fatan Allah ya kankare mana zunuban mu baki ɗaya.* PAGE 41: Ummeen Munir ce ta kalli qafar Saddiqa da ta fito daga gaban mota zata koma baya domin baiwa Abban Munir damar shiga gaban motar taga babu takalmi a qafarta ta cikin mamaki tace, "Ke Saddiqa ina takalmin ki? Ya za a yi gand'amemiyar budurwa dake ki dinga yawo babu takalmi?" Sunkuyar da kanta qasa tayi tana satar kallon Munir da ran shi ya ɓaci bayan tuna abinda ya faru da safe da yayi, sai da suka shiga mota kowa ya natsu Munir ya tada motar suka fara qoqarin barin airport ɗin, nan take Saddiqa ta manta da maganar da Ummee tayi ta ci gaba da kalle-kalle saboda sanda suka taho ma shi take yi dan kuwa bata taɓa barin qauyen Ba mugu ta shigo kano ba sai wannan karon. Ummee ce tace, "Kun yi shiru kun kyale ni ina takalmin ta ko su mutanen garin naku haka suke barin budurwa tayi yawo babu takalmi?" Tsaki Munir ya ɗan ja kaɗan sannan yace, "Ummee ba zaki yarda da abinda zan faɗa maki ba wataqila sai kin je gidan kin ga yanda wannan qatuwar matar ke azabtar da Saddiqa,

Chapter 27 of 70