Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rufe wa Innoh ido taci mata mutunci haka har da gorin haihuwa? Da sauri Sule ya fita ya riƙe jakar Naja dake gursheƙen kuka zata bar gidan,cikin matsanancin tausayi ya hau bata haƙuri,ita kuwa mai gayya mai aikin fitowa tayi idanu sun yi mata mici-mici ta hau borin kunya tana faɗin, "Naja lab'e kika fara yi min a gida na? Ashe har ta kai mu ga haka Naja? To a gaskiya idan dai haka zaki dinga yi ki dinga zaman ki a gida kina kula da Goggo in ba kiran ki nayi ba kar ki zo, irin haka ai sai ki ja mutane su dinga ganin baƙi na dan na faɗi gaskiya,ita dama gaskiya ɗaci gare ta in ji ɗan hausa." Ɗan liti ne ya shigo a hanzarce ya ɗauki buta ya zaga, ba jimawa ya fito yana ƙarasa gyara zariyar wandon shi,kallon Naja yayi dake ta kuka ta kasa magana,cikin damuwa ya ce, "Ke Naja me ya samu Goggon? Mutuwa akai ko me?" "Baba ba mutuwa akai ba, Innoh ce take yi wa Aunty Naja gorin haihuwa dan kawai Yarinyar nan tayi waya tace Aunty Naja taje ta zauna mata har sai ta haihu,shine Innoh tace ba inda Aunty Naja zata je ita zata je ta zauna da ƴarta saboda kawai ana cin daɗi gidan Mommyn." Ɗan liti sakin baki yayi yana kallon Innoh da kunya ta gama baibaye ta,ido ya raina fata, sai a lokacin da Sule ke maimaita abinda ya faru ta gano inda tayi kuskure, Naja ce fa, Naja Ƙanwar ta abokiyar cin mushen ta, Naja dake yi mata aiki da jiki da abinda take dashi na sana'ar ta dan farin cikin ta, Naja dake taya ta kashewa da binnewa. Kallon duk da suke binta da shi ne yayi mugun kashe mata jiki ta hau borin kunya tana faɗin, "To Allah ya baki haƙuri Naja'atuwalle ƙanwata ta kainaaa,ai abun be kai haka ba,ga kuɗin mota da na guzirin hanya Allah ya kiyaye, idan kin je ki gaishe ta,Allah ya raba ƙalau." Wani irin mugun kallon tsana Naja ta wurgawa Innoh,sannan ta hau goge hawayen ta tana shessheƙa irin ta wanda ya ci kuka ya gajin nan,baki na rawa tace, "Idan kika ganni a gidan Hadiza ki tsine min Innoh ! Daga yau babu ni babu zuri'ar ki, ina kike sanda ƴar taki ta kusan kashe auren ta tin a garin nan da ƙazanta da rashin iya girki naje na koya mata? Ina kike sanda ƴar ki Ameerah take zagin uwar mijin ta da yi mata rashin kunya mijin ta ya sanar dani naje har gidan ta na gyara mata zama? Kina ina sanda mijin Ameerah ya kirani akan baƙar ƙazantar da take yi naje na ci mata mutunci har ta gyara yake godiya? Dik baki san an yi wannan ba saboda ni na ɗauke su tamkar ƴaƴana na ciki na shi yasa ban taɓa zama na sanar dake ba ban kuma sanar da kowa ba ciki har da Goggo da nake kwana nake tashi da ita,ina dubin duk ɗaya ne,ashe ke abun duniya zai iya rufe maki ido kiyi min haka,to daga yau babu ni babu ke alaƙar mu ta yanke." "Alaƙar ku zata ƙara ƙarfi da ikon Allah,ku yi hakuri na yi muku katsalandam a maganganun ku,dik abinda ke faruwa ina jin ku, ina Naja? In tambaye ki mana, dik abubuwan nan da kika lissafa kin yi wa yaran ta dan wa kika yi?" Cikin share hawaye Naja tace wa Baabaa, "Dan Allah nayi mana Baabaar Abbe? Da ba dan Allah nayi ba ai da na faɗa duniya ta sani." "To Alhamdulillahi,na san ke kina da hankali ba kamar wance da ba a kama sunan ta ba,ki yi wa Allah a yanzun ma ki je ki kula da yarinyar da ta baki matsayi irin na uwa, da ace uwar masu gida bata ɗauke ki da mahimmanci ba da ba zata nemo ki ba, ko ba haka ba Ɗanli?" Da sauri Ɗan liti ya hau gyad'a kai kamar agama lizzad sannan yace, "K'warai kuwa Yaya maganar ki gaskiya ce,sannan ma ni ai babu uban da ya gaya min zashi binni,wato na fita sana'a ina can ina neman nakai sai na dawo naga gida babu kowa, kin tattare kin tafi birni cin arziƙi kin bar ɗan wahala a gida ko? To babu inda zaki je." Cikin borin kunya da hauragiya Innoh ta hau faɗin, "Dama ina zanje tinda suna da ƙanwar uwa a raye? Ni dama nasan wannan abun da ya faru tsakani na da ƴar uwa ta sharrin maƙiya ne ana hassadar zaman amanar dake tsakanin mu, shine ake so ayi mana farraƙu, Naja kiyi hakuri dan Allah ki kama hanya ki je,yo idan baki je ba wa zai je?" Nan dai aka haɗu da Baabaa da Ɗan liti tare da borin kunyar Innoh aka baiwa Naja hakuri har ta hakura,Ɗan liti ne ya kaita tasha ta haye abun hawa ta lula sai Kano. ******************************* Wani babban hall ne dake cikin sannanne kuma ƙayataccen hotel ɗin dake garin Abuja cike da mata da maza da kuma jinsin ƴan daudu marasa alƙibla,wani irin kiɗane ko ta ina da ihun matasa da dattijan dake cikin wajen ke ta tashi,kwalaben giya ne ko ta ina irin masu tsadar nan da kofunan gilashi ke ta gilmawa,dik wanda nashi ya ƙare a sake cika mishi. Hajiya K'waisa na gano cikin wata iriyar shiga ta alfarma hannun ta cikin na Samuel suna rawa sai wani yanga yake yana kwantawa a jikin Sam ɗin,wayar Alhaji dake kallon su Hajiya k'waisa ce ta hau ringing,yana nan zaune a d'akin da aka ajiye computers ɗin dake haska CCTV camera ɗin da aka dasa a wajen taron. Murmushi yayi sanda yaga mai kiran nashi,amsawa yayi ya kara a kunnen shi yace, "Ƴar kunama ga zaƙi ga harbi ya aka yi ne?" 'Alhaji naji shiru shine nace bari na kira naji ya akwai kaya a ƙasa ne? Gobe nake son nakai baby na asibiti akwai wani ɗan aiki da take so a yi mata,ni kaina ina ganin idan an yi mata aikin zamu more shi,fatan mu dai Allah yasa yayi kyau,na tabbata kud'in da zamu samu za su ninku akan na yanzu,kaga kafin ta samu sauƙi sai a sauya ta da wata.' "Amy kin ƙi gane wa har yanzu, na sha faɗa maki duk aikin da za a yi wa yaran nan baya wani tasiri sama da idan mai natural aka samu,kinga yarinyar nan da na taɓa kaiwa Alex ta haɗu,yanzu haka gani ga su K'waisa ina kallo a kwamfuta,da ace zan ɗan matsa su da na ji inda zan sake samo ta,ko da tsiya da bala'i ne sai na mayar musu da ita,kin san saboda abinda tayi har yau na kasa saka ƙafata a ƙasar nan, sun riga sun sanar da mutanen su idon su ido na a ɗauke ni kawai." Dariya Amy tayi kafin tace, "Gwanda ma ka hakura da ita kasa K'waisa ta nemo maka wata, zata iya dan duk wasu manyan karuwai da ƴan daudu a ƙarƙashin ta suke,saboda a labarin da naji wajen baby tace yanzu anyi mata aure da ɗan sarkin garin su." "Ko da uban wa aka yi mata aure tinda ta shiga harkar bariki ta yarda zata saida jikin ta saboda kuɗi na siya da tsada,to fa sai ta koma inda ta fit[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ *Dan Allah masu nema daga farko kuyi hakuri ku duba wattpad, ko Whatsapp channel d'ina mai suna TASKAR HAMIBRAH anyi nisa da yawa ba zai yu na dinga tura pages har 71 ba gaskiya. Dik group ɗin da suka ga bana tura musu, basu yin  comment ne ko reacting shi yasa nake zaton ba a bi.* PAGE 71: "A dai bi a sannu Alhaji kar a saka garaje a lamarin." In ji cewar Amy dake bin Billy da kallon ƙasa-ƙasa irin na ƙwararrun ƴan bariki,sun jima suna tattaunawa da Alhajin kafin su kashe wayar. Alhaji kuwa yana ajiye wayar tashi a aljihun rigar shi sai ya ɗauki landline ɗin dake saman table ɗin dake gaban shi yayi kiran waya, bai jima da ajiye wayar ba wasu murɗaɗɗun maza sanye da baƙaƙen kaya suka shiga office ɗin nashi. Tsaye suka yi masa kamar wasu dakaru kowannen su yana ɗauke da bindiga a soke a jikin shi,wani mai baƙin gilashi Alhaji ya kalla yace, "Maza ina so a taho min da K'waisa yanzun nan,bana son a bata damar bijirewa, idan ta bijire ko aka ne ku kawo min ita nan." "An gama Alhajin Allah." Juyawa suka yi a tare kamar waɗan da suka sha horo akan yin hakan suka fita,ta cikin CCTV camera Alhaji ya hango yanda suka taso ƙeyar K'waisan Alheri zuwa ofishin nashi,kafin su iso ya taso yana gyara zaman jacket ɗin dake jikin shi ya jingina da jikin makeken teburin da yake zaune a ofishin nashi. Cike da yanga da magana a natse K'waisa ya isa office ɗin yana yatsina da taunar cingam,kallon sama da ƙasa ya hau yi wa Alhajin kafin ya buga shewa ya daki cinyar shi yace, "Ashe rai kanga rai wai tsohuwa ta ga abun nan da ba a kama suna, kai bawan Allah haka ake rayuwa sai kawai kayi ɓatan dabo?" Murmushi Alhaji yayi sannan yace, "To ai gani na dawo yanzu,baki da masaniyar mune muka yi organizing wannan taron? Shi kanshi Ministern da kika kawowa yarinya ni na bashi labarin ki,amma a ganin ki shaharar ki ce ta haɗa ku ko? Na jima da sanin ki kece baki sanni ba sai ta sanadin TikTok da nake shiga dan haɗuwa da irin su Sweet H da irin ku masu connection da mata irin ta,ammmm ina baby na take? Ina so ki haɗa mu muna da unfinished business da ita." Baki sake K'waisa ke kallon Alhaji, sai da taji an yi maganar Mommy ta yatsine fuska tace, "Kai ni rabani da wannan haihuwar asarar haihuwar rage jinin,ni ina na san inda take yanzu? Ai ni rabona da ita tinda suka kwakushe mu nida tawaga ta muka je ƙwatar wa Billy ƴanci a ƙaucen su karnuka suka raka mu babu azziƙi na cire ta a cikin yarana,kai ƙarshe yarinyar nan fa har gidana tazo ta illata mu nida babyna kaga kuwa ai ni sai dai na nemi tsari da sake ganin ta ko?" "I don't care about how you guys get separated,yanzu zan baka wani aiki ne na musamman, dole ne dik inda take ka nemo min ita, dole ne na kashe auren nan nata na maidawa Alex ita saboda kuɗi ya biya maƙudai masu yawan gaske,da su nake sha'anin dik da kika ga yana gudana anan dama wasu da ba zan iya lissafawa ba,yanzu haka shiga new york ya gagare ni saboda su Alex na nema na ido rufe, ya bada umarnin da an ganni a kashe saboda tsinanniyar yarinyar nan,dan haka ki nemo ta dik inda take ko kuma a bakin taki rayuwar." Wani irin zillo K'waisa yayi tare da dafe qirjin shi,idanu mazajen dake zagaye da shi suka hau zaro masa suna gyara zaman bindikar su a jikin su,yawu mai kauri ya had'iya sai da Adam Apple ɗin shi ya motsa, nan take jikin shi ya hau rawa,cikin damuwa da marairacewa yace, "Yau na shiga uku na ni K'waisan alheri,ni dai sanin wannan matsiyaciyar yarinyar be zame min komai ba sai tashin hankali da bala'i da masifa,yanzu ta ina zan fara nemo ta?" Alhaji kafaɗun shi biyu ya d'aga sannan yace, "Ban sani ba,ban kuma damu da yanda zaki yi ki samo ta ba, i just want her back,do what ever it takes and bring her back to me,you can go back to the party and enjoy your self." Miƙewa K'waisa yayi yana sharce zufa yace, "Yo wane enjoyment bayan ka katse min shi? Ashe ƴan kud'ad'en da naci na nan na bibiya ta zan biya su ta hanya mai wuya, na shiga uku ni K'waisan alheri." Haka Hajiya K'waisa ta koma cikin taron mutanen da suka fara buguwa da giya suna ta timɓele da aikata masha'a,Sam ta hango shi da wani saurayi suna magana daf da juna kamar za su shige jikin junan su hannayen Sam na yawo a jikin matashin, kallon shi kawai tayi ranta na ƙuna saboda wani azababben kishi da ya taso mata,kaɗa gashin kanshi yayi ya damƙe ƴar jakar shi ya hau wurga ƙafa zai bar wajen,hankalin Samuel ne ya kai kan k'waisa,cikin sauri ya janye daga jikin saurayin yabi bayan masoyin nashi,kafin ya isa gare ta har ta isa inda motocin mutane ke ajiye ta kunna wadda suka zo a ciki ta tada,da wani azababben gudu ya take motar ya bar harabar wajen,tin a hanya ya fara kuka saboda kishin da yake ji,idan bai manta ba wannan ne karo na biyar yana kama Sam da yunƙurin cin amanar shi,banda text messages da yake gani yana soyayya da wasu mazan,kenan lalurar da ta fara damun shi ce take ƙoƙarin nesanta su? Ashe alƙawarin kasancewa da juna har ƙarshen rayuwa da suka yi wa juna ba zai tabbata ba? A haka ya isa gida yana kuka tare da fatan Sam ya biyo bayan shi dan ya bashi hakuri,sai dai har dare ya raba babu Sam babu dalilin shi,ya rasa da wanda zai tattauna game da matsalar da ta kunno masa kai na nemo Mommy. Kaff cikin sabbin yaran shi babu wanda ya sakewa suka shaƙu balle ya basu labarin abinda ke faruwa dashi,agogon dake manne a jikin bangon ƙaramin parlourn shi ya kalla yaga ƙarfe biyu na dare tayi,tunanin ta inda zai fara nemo Mommy yake wayar shi ta hau ringing, a tunanin shi Sam ne sai yaga baƙuwar lamba, yana ɗauka aka ce masa. 'Kar ka shagala da dogon tunani,muna nan muna bibiyar ka har sai ka kawo wa Alhaji abinda ya buƙata zamu ƙyale rayuwar ka.' A tsorace ya kashe wayar yayi wurgi da ita jiki na masa rawa,cikin tsananin tsoro ya furta, "Na shiga uku ni ƙwaisan alkhairi,wannan mutumi ya zame min masifa da bala'i,na zaci na yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda tinda na rabu da Hadiza da Billy ashe an rabu da bukar ne an haifi habu." Safa da marwa yake tayi kafin yaji ƙasan shi na yi masa ƙaiƙayi, kuka ya fashe dashi sannan ya kwashe wayoyin shi da jakar shi ya haura sama, band'aki ya shiga ya tub'e kayan shi gaba ɗaya, wani ƙaton pampas ne a jikin shi irin na manyan nan,a hankali ya hau ƙoƙarin cirewa yana toshe hancin shi, dik da ƙoƙarin dunƙule pampas ɗin da yake yi dan kar yaga ƙazantar dake ciki hakan bai hana wasu daga cikin tsutsotsin dake ciki fad'uwa ƙasa ba,cikin kuka ya buɗe trash bin ɗin dake cikin banɗakin ya wurga pampas ɗin ya tara ruwa a bathtub mai dumi ya zuba su Dettol da sauran abubuwan kashe ƙwayoyin cutuka,yana gama haɗa ruwan ne ya hau saman toilet ya zauna,ya jima sosai yana zazzage cikin shi kafin yayi tsarki ya shige cikin ruwan ya zauna. Wata iriyar ajiyar zuciya ya sauke kafin a hankali ya sanya hannun shi yana wanke bayan shi da kyau har sai da ya tabbatar ya wanke wajen da kyau,ruwan ya tsiyaye ya sake haɗa wani ya zauna, Hajiya K'waisa bai samu fitowa daga band'akin ba sai da ya zauna a ruwan zafi sau uku, d'aure da towel ya fito yana jin daɗin yanda ya gasa jikin shi ya fitar da ƙazantar da ta taru masa. Kwance ya tarar da Sam a gado yana surutai irin na bugaggun mashaya,tsaki yaja ya wuce gaban madubi ya shafa mai da turaruka sannan ya maida pampas jikin shi ya saka kayan bacci ya bar d'akin ya koma wani dakin,kwanciyar yayi da tunanin yanda zai nemo Mommy. ******************************** Tsabar murnar ganin Naja ce ta sanya mommy rasa inda zata saka Auntyn nata taji daɗi,hakan da Naja ta gani sai ya wanke mata baƙin cikin da Innoh ta dasa mata a rai kafin tazo,nan take ta maida komai ba komai ba ta rungumi ƴar ƴar'uwar tata da ta gama wulaƙanta ta da yi mata gorin haihuwa. Abinci kuwa gashi nan kala-kala Naja taci ta ƙoshi,tana tsaka da shan fruit salad ne ta kalli Mommy tace, "Wannan ɗin daga hotel aka siyo? Dan dai na san baki iya girki kamar haka ba Hadiza." Dariya Mommy tayi sannan tace, "Habaa Auntyna ai wannan sanin da kika yi min,ai tinda muka dawo garin nan ya saka ni a classes na koyon abinci,banda online classes ɗin da na shiga na koyon girke-girken zamani da na gargajiya,Aunty Naja nafa gane yanzu komai zaka yi wa namiji dan ka riƙe shi idan baka gyara kan ka ba aikin banza ne." Hannu Naja ta baiwa Mommy suka tafa kamar wasu ƙawaye sannan Naja tace, "Amma kuwa ba ƙaramin farin ciki wannan sauyin dana gani a tattare dake ba ya sanya ni, inama waccan sokuwar itama ta fahimci rayuwa ta yanda kika fahimce ta da ta mori zaman gidan miji, dan kuwa yanzu shamsu a kafff matasan ƙauyen Ba Mugu da suka yi aure babu yashi wajen kula da iyalin shi,matsala ɗaya da yake fuskanta shine samun ballagazar mata, kaya duk tsadar shi Ameerah zata kashe shi,abinci dik kyan shi da tsadar kuɗin da aka saka aka siyo shi zata bari ya lalace ko wajen girka wa ta ɓata, dole sai dai a azubar,Allah ya nuna min Ameerah ta zama mutuniyar kirki." "Ohhh kice har yanzu Ameerah na fama da wannan shiriritar?" "Humm ai sai dai addu'a kawai, sauƙin da aka samu yanzu ita kanta warin hammatar da take yi na sata amai cikin jikin ta baya son wari, shine fa ake wanka akai akai,amma banda haka kar ki daɗa kar ki raga tana nan a Ameerahn da kika san ta " "Gaskiya na tausayawa Shamsu yana fama waiiii,idan ban manta ba shamsu fa baya son wari ko kaɗan,uhummm bari dai a bar tuna baya Aunty Allah ya yafe mana,Aunty me kika kawo min neeee." Dariya suka sake yi suka tafa tare da shewa, cikin yin ƙasa da murya sosai Naja tace, "Sai anjima idan na shiga ɗaki ki biyo ni, akwai wani taimako da na amso maki wajen malam,a ruwan sha ake sakawa wannan, yanda yasha ruwan nan haka soyayyar ki zata yi ta ninkuwa a zuciyar shi,ba zai ga kowacce mace a matsayin mace ba bayan ke,na tabbata maki babu ke babu kishiya ko a waje balle a cikin gidan auren ku." "Kaiiii amma Aunty Naja banda kamar ki,kin gama min komai Auntyna Allah ya biya ki, dole ne nayi maki kyauta ta musamman Auntyna." Murmushin jin daɗi Naja tayi sannan suka ci gaba da hirar cikin da ke jikin Mommy da irin tanadin da tayi na suna da kayan da suka fara siyowa. Haka rayuwar gidan su Abdul ta ci gaba da kasancewa cikin farin ciki da nishad'i, sai dai ta ɓangaren shi ya samu tawayar nishad'in da yake tsananin buƙata a tattare da Mommyn tinda cikin ta ya shiga wata takwas,gaba ɗaya Mommy yanzu gudun Abdul take yi bata bashi haɗin kai a duk sanda ya neme ta. Tin suna yin abun nasu su biyu babu wanda ya sani har saida Naja ta sani, ai kuwa babu zancen jin kunya ko nauyi haka ta zaunar da Mommy tayi mata faɗa sosai akan hakan, rimi-rimi ta fara bin umarnin Naja tana daurewa kamar abun zai ɗore,ana haka wata rana da safe ta gaji da dauriyar da take yi ta fara masifa da balai'n yana takura mata yayi hakuri har ta haihu ita baza ta iya da jarabar shi ba. Cikin fushi Abdul ya sanya tufafin shi ya ɗauki makullin motar shi ya bar mata gidan saboda samun natsuwar ranshi,wanda da ace Mommy tasan abinda take aikatawa zai jawo mata shiga damuwa da tashin hankali tabbas da ta haƙura ta jure dikkan buƙatun Abdussaboor ɗin.......... [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ *A yi haƙuri a daina tambayar pages ɗin da akai missing saboda na riga na tura,idan baku gani ba ku duba wattpad ko WhatsApp channel,ko ku jira a gama a haɗa document.* PAGE 72: Tin a mota yake saƙe-saƙen inda zai samu biyan buƙatar shi da matar shi ta halalin shi ta hana masa,mamakin yanda Mommy ke gudun shi yake yi,a baya kafin cikin ta ya tsufa ko al'ada take yi ta san yanda zata yi ta bashi nishad'i har ya samu gamsuwa da ita, amma a yanzu dan cikinta ya kai wata bakwai take gudun shi? Ta san halin da yake shiga kuwa a dik sanda ta nesanta daga gare shi? Me yasa take sanya shi tunanin rayuwar shi ta baya? Dukan sitiyarin motar tashi yayi tare da faɗin, "Baby me yasa kika sauya daga romantic wife zuwa wata mace ta daban da ban sani ba?" Da ire-iren wannan maganganun da tunanin ya isa office ɗin shi, ko da ya isa ya tarar da Bilal da sauran ma'aikatan wajen sun saka sabbin ƴan bautar ƙasa a gaba suna yi musu bayanin abubuwan da ya kamata su sani. Ba tare da ya kula kowa ba ya wuce zuwa office ɗin shi ya buɗe ya shiga ya zauna a kujera,juya kanshi ya dinga yi daga wannan ɓangare zuwa wancan, idanun shi kulle suke saboda yanda yake jin shi a matuƙar buƙace da matar tashi har a wannan lokacin,tinani yake anya ba zai koma yayi mata ta ƙarfi ba? Baya so ya komawa zunubin da ya tuba yake fatan har abada ba zai kuma aikatawa ba,to amma ya zai yi? Wani irin sassanyan ƙamshin turare ne ya daki hancin shi,a hankali aka fara buga ƙofar kamar ana jin tsoron bugawar,ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya buɗe jajayen idanun shi yayi gyaran murya, murya na rawa ya furta, "Yes..come in." Tura ƙofar kyakkyawar budurwar tayi ta shiga, idanun ta ta zube fesss a saman fuskar Abdul dake ta ƙoƙarin daidaita natsuwar shi,doguwa ce baƙa mai matuƙar kyau, idanunta masu ɗaukan hankalin mai kallo ta zuba masa, cikin ƙanƙanin lokaci Abdul ya sake rikicewa, leb'en shi na ƙasa ya cije ya kalle ta yace, "Lafiya? Kin shigo kin zuba min idanu baki ce komai ba." Cikin sauri da basar da abinda ta ɗarsawa ranta game da kyakkyawan mutumin dake gaban ta ta isa gaban shi ta miƙa masa takardun dake hannun ta tace, "Sir Bilal ne yace na kawo maka wannan ka saka hannu, sannan nice wadda zan dinga taimaka maka akan dikkan ayyukan ka daga yau inshaa Allahu." "Ok...meye sunan ki?" "Suna na Maimooon Salis Ubaid." "What a nice name...Maimoonnn, ok Maimoon ina fatan an yi maki bayani akan dik wasu abubuwa da muke gudanarwa anan kamfanin ko? Idan ba a yi maki ba zaki min hakuri sai zuwa ko gobe ne na yi maki saboda a gaskiya yau bana cikin yanayi na yin kowanne irin aiki." Cikin yanga da rausaya ta isa gaban table ɗin da yake ta ɗora dika hannayen ta tana wani kashe masa idanun ta kyawawa,harshen ta ta ɗan zaro ta lashe labb'an ta sannan tace, "Yess na kula da hakan tin da ka shigo kamfanin nan,na kula da inda hankalin ka ya karkata Sirrr,idan zaka bani dama zan yi maka kowanne irin aiki kake da buƙata,idan nace kowanne irin aiki ina nufin....ko wanne irin aiki." Tana ƙarasa maganarta sai ta hau kallon shi daga sama har ƙasa sannan ta zube idanun ta a wajen da bai kamata ace ta kalla ba a jikin shi,nan take kuwa Abdul ya fahimci abinda take nufi, wani irin ziga da kururuwa shaid'an ya dinga yi masa yana ingiza shi akan ya kashe ƙishin dake damun shi da wannan tsaleliyar budurwar da ya fara gani a yau,ƙamshin dake tashi a jikin ta da saƙon da take aika masa da idanun ta yafi komai fizgar shi a game da ita,ganin tana neman jan ra'ayin shi ne yayi hanzarin cewa, "Okk to bari mu gwada wani abu mu gani idan zaki iya yin kowanne aiki na saka ki." Kafin ya rufe bakin shi ta zagaya inda yake zaune ta hau shafa kafad'ar shi tana matsawa a hankali,nan take tsikar jikin Abdul ta tashi ya sake dulmiya cikin wani yanayi,a hankali Maimoon ta kai bakin ta saitin kunnen sa tace, "I can do anything for you sir,ka gwada ni ka gani." K'wank'wasa ƙofar da aka yi ne ya sa Maimoon saurin barin inda take tsaye ta dawo gaban table ɗin Abdul ta tsaya tana kafe shi da wani Shu'umin kallo da murmushi,murya a sarƙe Abdul ya amsa wa mai buga ƙofar tashi,Bilal ne ya shiga yana masifar me yasa Maimoon ta jima,Abdul ne ya haɗe fuska yace, "Kai bana son iskanci meye haka zaka hau yi wa ƴar mutane faɗa daga zuwa

Chapter 45 of 70