Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wajen zai rage zafin, ta na sakawa zafin ya haɗe mata ya mata yawa, ga zafin kumburin da kuncin ta ya yi,ga na aboniki,ga kuma na goga tsumma da take yi a wajen, wani nishin wahala ta sauke ta ce, "Kwad'ayi mabud'in wahala,ina zaman zamana a d'aki daga jin za a bada zakka na tashi na hau rawar jiki,gashi nan na ci kud'in zakka da azaba" "Innoh magana ki ke yi ne?" "In ce uwar me to ni ina a wannan halin na tsakanin rayuwa da mutuwa?" Baya Ameerah ta ja ta bar ta a wajen ta na ci gaba da goge muqamuqin ta tare da zuba ruwa mai sanyi a wajen,a haka Yadiko ta wuce madafin su ta hau sharewa dan kuwa ita ce za ta karb'i girki a ranar, duk halin da Innoh ke ciki bai hana ta zabga tsaki ba tare da hararar Yadiko da bata san ma ta na yi ba. Bayan wasu awanni fuskar Innoh ta saɓe daga kumburin da ta yi, shatin kaqoran Baaba ma ya baje, sai zazzaɓi da ciwon kai mai zafi ya rufe ta sakamakon kuka da shiga tashin hankali da damuwa da ta yi,ta na nan kwance ta hau tunanin ya zama dole su bar Mommy tafiya birni aikatau ko babu komai duk wata za ta dinga samun 'yan kud'ad'e irin yanda Mahaifiyar Billy da Baaba ke samu, nan take ta ga wautar ta da ta biye wa Ɗan liti suka hana Mommy tafiya birni, a cewar shi ita mace sai ana saka mata ido, an saka mata ido ma ya ta qare ballantana ba a saka mata ba? A can d'akin Mommy kuwa ta riga da ta gama sanar da Billy amincewar iyayen ta game da tafiyar su tare,nan take suka dinga murna,wani videon da suka yi a gidan mai gari Billy ta yi posting a status d'in ta a qasa ta rubuta (Gidan grandma akwai daɗi amma hutu ya qare, guys ina nan dawowa Abuja nan da wasu kwanaki, na yi missing ɗin ku qawaye na). Mutanen ta da ta ke zabga wa qaryar ita 'yar sanata ce tuni suka hau yi mata comment, ana yaba wa kyawun da ta yi, wasu har tambayar ta suke yi a wanne gari grandma ɗin ta take ita kuwa ta karkace ta ce a cikin garin Kano take da zama. Albishir ta yi wa Hajiyan ta da zuwan Mommy, nan take ta tura mata dubu hamsin ta account ɗin ta sannan ta ce ta tabbata ta kawo mata Mommy kar a samu wata matsalar da za a ce an fasa zuwa, nan take ta yi mata alqawarin zata kawo mata Mommy har gida. Kayan ta ta gama haɗawa a akwati sannan ta wuce tasha ta ciro kud'in da aka tura mata ta yi gida, mahaifan ta ta baiwa dubu biyar biyar sannan ta ware wasu dubu biyar ɗin da niyyar ta baiwa Mommy ta qara wa iyayen ta dan su yarda ana samun kuɗi ta hanyar aikatau. Da yamma liss ana daf da Kiran magariba ta isa gidan su Billy,a tsakar gida ta tadda Yadiko da ta fito daga wanka Saddiq ya na mata shagwab'ar yunwa yake ji ta yi ta gama girki ta zuba masa miyar da ke ta dahuwa a Saman garwashi a hankali,in dai girki ne Yadiko ta ciri tuta ta wannan fannin fiye da Innoh, dan kuwa in ba alale da dambu ba Innoh bata k'ware a girki ba,hasali ma ita sam bata qaunar yin girki musamman tuwo idan ta tuqa kafin safiya a yi d'umame ya sake, shi yasa lokuta da dama sai dai kowa ya ji da kan shi da safe ranar girkin ta. Billy durqusawa ta yi ta gaishe da Yadiko kamar wata ta Allah, sannan ta ce, "Ina mutuniya ta kuwa ko ana ciki ana sallah?" "Ko ana ciki ana latsa waya ba? Ke yanzu da magaribar nan ana ta Kiran sallah aljanu na ta gilmawa shine ki ka fito a haka ki ka zo gidan su ƙawa? Dibi kayan jikin ki fa ki na d'aga hijabin ki na ga babu wata suturar arziki a haka ki ka banka uban hijabi,yanzu ba kya jin tsoron iska ta d'aga ko wani tsautsayi ya faru a ga jikin ki?" Cikin kosawa da maganganun Yadiko Billy ta ce, "Wanda ya gani shi ya jiyo, ni ba wa'azi na zo ki yi min ba,ki je can ki yi ta zuba wa 'yar ki wa'azin naki wataqila ya yi mata amfani, gata nan kullum cikin hijabi bamu san me take b'oyewa ba, wa ya sani ma ko ta d'akko na shege a waje?" "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, Balkisu daga yi maki nasiha Zaki jefi 'ya ta da wannan mugun alkaba'in? To ba ita ba ma ke kan ki da dikkan musulmi ina nema maku tsari da wannan mummunar jarabawa Allah ya baki hakuri qawar ki na d'aki," "Tun farko da haka ki ka ce min da baki b'ata mana rai ba da ni da ke" "Humm duniya ce ta fi bagaruwa iya jima, Allah ya kyauta" D'akin ta ta shige ta bar Saddiq na kallon Billy kamar ya je ya make ta, ita kuwa d'akin su Mommy ta afka ta na shiga ta gan ta kwance a rufe da zani ta na ta latsar waya,zube wa ta yi a jikin ta ta na d'aka mata duka ta ce, " 'Yar duniya ana can ana sallah ki na nan ki na kallon harkar duniya,mu ga me ki ke kallo,yanzu na haɗu da wannan kishiyar uwar taku mai shegen kinibibi kamar ta fi kowa tsoron Allah a duniya" "Hummmm Yadiko ko? Haka take ai duk ta bi ta ishe ni ko ganin ta bana qaunar yi a gidan nan ita da waɗannan shegun yaran nata" "Humm ai kin kusa tafiya ki basu waje qawata, kin ga ga wannan ki sake qara wa su Innoh gobe da sassafe zamu bar garin nan, ina so mu isa da wuri ido na ganin ido saboda lalacewar hanya" "Tom Allah ya kaimu, na gode sosai qawata akan irin wannan qoqarin da ki ke yi min a gaskiya banda masoyiya kaff garin nan sama da ke" Murmushin gefen baki Billy ta yi sannan ta ce, "Babu komai ai yi wa kai ne" A haka suka kwanta tare babu sallah babu salati suka ci gaba da kallon fina-finan da aka tura masu na turanci wanda anan ne suke qara gogewa da yaren turanci,sai dai kashh kusan rabin film ɗin bashi da kyan gani,amma su ko a jikin su, suna gani suna qarin bayani akan abinda suke kallo. Billy bata bar gidan ba sai bayan isha'i,ta bar gidan ɗauke da kayan Mommy da ba su fi kala bakwai ba wanda a ciki biyu ne kawai na sallahn ta sauran dika Billyn ce ta bata. Billy kuwa ta tafi da su ne a cewar ta ba za a ɗaukar mata jakar buhu a bi ta Kano da shi ba, za ta je ta yi wa kayan waje a akwatin ta tun da ta rage kaya ta babbayar,godiya sosai Mommy ta yi mata sannan ta koma d'aki ta kwanta. Da dare Ɗan liti ya siyo wa kowa tsiren ɗari uku-uku har Baaba,hakan da ya yi ya hasala Innoh ta dinga masifa ta na fad'in ai kowa na da kud'in shi me zai sa shi kashe kuɗi a banza? Bai kula ta ba ya ɗauki nasu shi da Yadiko da yaran ta zai tafi wanda kafin hakan sai da Innoh ta qirga shi tsaff tsoka bayan tsoka dan kuwa a cewar ta kar a yi rashin adalci. D'akin Yadiko ba shi da wadatar kayan d'aki daga gadon ta da sif sai ɗan qaramin madubi shikenan ledar tsakar d'akin ma ta yi yagewar da ta fi rabi amma a haka ta gyare d'akin ta tasss,Saddiqa ce zaune a gaban Mahaifiyar ta ta na jin haddar ta Ɗan liti ya shiga bakin sa ɗauke da sallama, murmushi ya sakarwa Yadiko gaba ɗaya dasorin shi suka bayyana itan ma sai ta sakar masa murmushi sannan ya qarasa shiga ya ajiye leda ɗaya a gaban ta, ya miqa wa Saddiqa nata ya ba wa Saddiq nashi sannan ya ce, "To maza a tashi a je makwanci a kwanta ko? Sai da safe," "To Baba Allah ya tashe mu lafiya" "Amin" Yaran na fita Yadiko ta fita Itama ta je rijiya ta kindimi ruwa ta kai wa Ɗan liti na wanka, sabulun ta irin koren nan na wanki ta sa a kwandon wanka duk ta kai masa ta cika buta da ruwa ta ajiye ta koma d'aki. "Mata ta 'yar aljannah,shi yasa fa idan mutum ya tashi aure malamai suka ce Annabin rahama ya bada shawara da maza su auri mai addini,yau kwana na biyu rabo na da wanka tun wancan zuwan da na yi na tafi da wanka na sai yau zan sake wani, yo ita kan ta uwar garken wato uwar awaki wajen rashin son wanka ba ta yi ba balle mijin ta ya yi," "Hummmm malam kenan" Shine kawai abinda Yadiko ta ce, dan bata son halin shi na son a d'akko zancen Innoh a yi ta zagin ta, dan kuwa yin hakan ba dai-dai bane,Hakan kuma na tabbatar mata da cewa Shima idan ya koma wajen Innoh suna yi da ita. Jin ba za ta ce masa komai bane ya sanya shi tashi ya na fad'in, "Bari na je na dawo akwai labari, da kuma neman shawara da za ki bani" "To malam Allah ya sa na baka mai amfani da albarka" "Ameen" A haka Ɗan liti ya tafi wanka ya gama ya yi alwala dan kuwa bai yi isha'i ba ya na can wajen me nama aka shiga masallaci ya qi barin abinda yake yi ya tafi sai da aka gama yanka masa sannan ya yi gida. Bayan ya gama shiri har sun ci abinci ya kishingid'a a gefen gado ya ce, "Dama shawara nake nema game da yarinyar nan Mommy, kamar yanda ki ka sani ta jima ta na so ta tafi birni na ke hanawa,to shine d'azu ta zo min da jawabai na gansuwa kuma na gamsu na amince ta tafi, uwar ta ma ta amince amma har yanzu na rasa me ya sa na kasa haƙuri na kwantar da hankali na,ke wace shawara ki ke ganin ya dace a bi?" Gyara zama Yadiko ta yi sosai ta buɗe baki ta ce........... [09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: *GIDAN ƊAN LITI* RUBUTAWA: HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH) PAGE 7: "Malam a zato na mun riga mun gama da wannan shafin tinda jimawa amma kuma na ji yau ka sake d'akko maganar,na riga da na san tinda ka kawo maganar a yau kuma a yanzu to fa tabbas kun gama yanke shawara akan mommy za ta tafi kano aikatau ko na bada shawara ba za ku sauya ra'ayin ku akai ba da kai da mahaifiyar ta da kuma ita kan ta yarinyar, ƙarshe ma zagi zai iya biyo baya a zarge ni da yi musu baƙin ciki da hassada wataqila har a zagi yarana a tsine musu tinda ba yau aka saba irin haka ba,abu ɗaya zan sanar da kai wanda bai wuce na ce maka ka yi k'ok'ari ka fi ƙarfin gidan ka kafin gidan ka ya fi ƙarfin ka,sannan ina so na baka shawara akan yanda ka ke son abin hannun 'ya'yan ka da mu matan ka, idan baka ɗauke ido akan haka ba tabbas ina jiye maka ranar qin dillanci..." Cike da wani irin yanayi mara fassaruwa ya katse ta da fad'in, "Dakata dan Allah Yadikon Sule, ke kuwa daga neman shawara sai ki yi ta surutu irin haka? Me ya kawo maganar qin dillaci kuma? Allah ya raba ni da ganin ranar nan,yanzu dai ba wannan ba miko min ruwan nan na karasa sha, tuwo ya yi daɗi Allah ya biya" "Ameeen" Kawai ta ce ta miƙa masa ruwan shan da ya buqata, ta samu waje ta yi shirin bacci ta yi addu'a ta shafe jikin ta tas ta kwanta ta na ta tunanin irin halin da Ɗan liti yake so ya jefe ƴar shi a ciki, ta jima da sanin wasu daga dabi'un Mommy da sule har ma da Ameerah, ta yi magana akan a gyara aka hau yi wa yaran ta fatan tsiya da tsinewa da masifa da bala'i ranar ce nara ta farko da har suka dambace da Innoh ta yi sa'a ta yi wa Innoh jahilin duka tin daga ranar Innoh ke shakkarta sai dai a yi cacar baki amma banda gwada 'yar k'ashi,dan haka dole ne ta ja bakin ta ta yi shiru bazata sake magana akai ba,tinda gashi ya na so ya tabka babban kuskuren barin Mommy ta tafi wata duniyar da sunan aikatau bayan sun gama maganar da ita da shi da jimawa akan mommy baza ta je birni aikatau ba,shine yanzu za su sauya shawara,wanne irin kwad'ayin abun duniya ne wannan ke damun shi? Da wuri mommy ta yi wa shamsu sallama ta waya har da yi mata kukan soyayya na zai yi kewar ta sosai, ita kuwa ta yi masa alqawari da cewa kar ya damu za su kasance tare ta waya a kullum ai kamar basu rabu ba, da haka ta samu ya hakura ya dena koke-koken da yake yi mata suka ajiye waya. Baccin ta kalilan ne domin kuwa tunanin ta duk ya qare ne a kan yanda zata samu garin kano shin ya na da kyau kuwa kamar yanda ake ta zuzuta shi? Ko kuma dai yanda ake kiran akwai mutane da yawa ba wani kyau gare shi ba saboda cunkoso? Anya zata haɗu da had'ad'd'en saurayin da zai aure ta ya cire ta daga qangin babu da wahalar rayuwar da suke ciki ita da iyayenta kuwa kamar yanda take karantawa a littafan hausa? Da ire-iren wannan tunanin ta samu bacci ya ɗauke ta. Da misalin ƙarfe huɗu da rabi na asuba Saddiqa ta farka domin yin ibadun ta kamar yanda ta saba har zuwa a yi sallar asuba sai ta ga mommy ta tashi itama a dai-dai wannan lokacin da bata saba tashi ba, in fact wani lokacin ma a sannan take ajiye wayar ta ta juya ta yi bacci,abun ya bata mamaki sosai amma haka ta danne sai zuciyar ta ta kawo mata cewar wataqila fitsari zata je ta yi ta dawo ta ci gaba da baccin ta dan su basu yin sallar asuba sai rana ta fito rangad'ad'au a sama sannan suke yin ta. Ga mamakin ta sai ta ga mommy ta ɗauki soson wanka da sabulun wankanta ta tatsi toothpaste a brush ɗin ta ta rataya zanin wankanta ta fice daga d'akin, ɗauke kanta ta yi daga kallon ikon Allah ta koma ga ibadar ta tana kyautatawa yayar tata zato. Mommy kuwa wankan minti shabiyar ta yi ta yi brush sannan ta yo alwala ta nufi d'akin su ta na rawar sanyi saboda kad'awar da iska ke yi irin ta yanayin nan na farko-farkon shigar sanyi. Tsane jikin ta ta yi sannan ta shafa mai sosai da turare ta sanya sabuwar doguwar rigar da Billy ta bata sannan ta fara doka sallah cikin gaggawa,tana idarwa ta kalli Saddiqa ta ce, "To qanwa ta a yafi juna ni fa yau zan tafi kano,zani neman kuɗi a sanya ni a addu'a Allah ya bani su masu yawa Allah ya sa daga can na samo mijin nuna wa sa'a na kece raini,ga d'akin nan a yi ta ibada Allah ya sada mu da alheri" Cike da mamaki Saddiqa ta miqe tsaye, kawai sai ta ji idanun ta sun ciko da k'walla, ko da dai ba wani shiri suke yi ba sosai da yayarta ta amma ta na son ta sosai, ta na son 'yan uwan nata matuqa gaya sune kawai suke kyarar ta da gudun ta,cikin murya mai rawa Saddiqa ta ce, "Yanzu idan kin tafi sai yaushe kuma? Dan Allah Yah Mommy kar ki dinga dad'ewa baki dawo ba kamar yanda Yah Balki ta gidan me dusa take yi,Yah Mommy zan yi kewar ki da yawa" Wani irin abu Mommy ta ji ya narkar da zuciyarta game da saddiqa a yau kaɗai a rayuwar ta tun bayan da aka haifi Saddiqar, tun saddiqa na yarinya Mommy ta yi son ta sosai domin kuwa ta girme ta sosai, tashin su da fara zama 'yammata ne ta fara kyarar yarinyar saboda ta kula da yanda take da iyayin son yi mata nasiha akan duk abinda taga ta na aikatawa mara kyau (girman kai kenan, ba wai mutum ya dinga ganin yafi kowa ba shine girman kai, ah ah mutum ya qi karb'ar gyara daga wanda yake ganin be kai ya yi masa gyaran ba shi ake kira da girman kai a musulunci). Da sauri mommy ta ɗauke kan ta daga barin kallon Saddiqa da ke matsar k'walla ta na ta yi mata addu'a da fatan alkhairi tare da roqon ta kar ta dinga jimawa bata dawo sun ganta ba. Wajen da Ameerah ke kwance kamar gawa Mommyn ta nufa ta sami qafarta ta shalla mata wani mugun duka dan ta san idan zata shekara kiran sunan ta ko tashin ta a hankali ba zata tashi ba, ba ma za ta san ana yi ba, ai kuwa da alama wannan mugun dukan ya shigi Ameerah a hargitse ta farka ta na kara hannyenta gaban fuskar ta kamar wata k'aura ta na fad'in, "Waye ya kawo min farmaki? Waye nan ke mommy d'akko adda b'arayi sun shigo" Harara Mommy ta banka mata duk da cewa har wannan lokacin idanun Ameerah a rufe suke ba gani za ta yi ba, cikin hargowa ta sake shurin ta da qafa ta ce, "Ke banza ni ce nan ba b'arayi ba,ki tashi mu yi sallama lokaci na tafiya zan wuce a yafi juna" Nan take Ameerah ta wartsake dan kuwa ta san da zancen tafiyar, cikin goge wani shafcecen yawun bacci da ya yanko a gefen bakin ta ta ce wa Mommy, "Kai haba da asubar nan zaku tafi kamar wanda ake korar ku? Ina laifi ku bari azahar ta yi? To Allah ya kiyaye kin barmin jakar can taki na dinga amfani da ita?" "Eh na bar maku komai ke da Saddiqa ku raba duk abinda ban ɗauka ba,se watarana" Fita ta tashi yi Saddiqa ta tafi da gudu ta rungume ta ta fashe da kuka, bata janye ta ba a jikin ta sai da ta ɗan jima ta na kuka sannan ta janye ta ta ce, "Meye haka kamar wadda in na tafi na tafi kenan? Ku kula da kan ku sai na dawo," Ganin yanda su Mommy da Saddiqa suka rungumi juna abun sai ya burge Ameerah dan su a garin nan ba su wani saba haka ba, sabon abu ne ma a wajen su wannan rungume-rungumen,tafiya ta yi da azamar ta zata rungumi Mommy, Mommy ta ji wani mugun warin yawun bacci ya dake ta, da gudu ta yi waje ta na dakatar da Ameerah, "K'wal uba ! Ameerah kin ji bakin ki kuwa? Waiii hyadda kenan,ki wa Allah kar ki goga min wannan buhun warin na shiga kano a kasa shaqa ta" Wani takaici ne ya kama Ameerah ta hau masifa da rashin kunya kala-kala, dan ita bakin ta baya shiru sam, suna nan tsaye Billy ta shigo sanye da wani riga da wando masu mugun kyau da matse jiki, sai wani siririn mayafi da ta yafa ta ɗauki irin pillown nan da ake sawa a wuya idan an shiga jirgi ko mota, kan ta ɗauke da gingimemen headphone kalar kayan ta wato dark pink and light pink, takalman qafarta kuwa farare ne fatt sau ciki sai zabga qamshi take yi, cikin yanga da sauya maganar da basu taɓa ji ta yi irin ta ba suka ji ta ce, "Mommy please ki yi sauri mana mu wuce driver guda Hajiya ta aiko mana daga kano dan ya maida mu, kuma ta yi haka ne kawai saboda ke kin ga be kamata mu barshi ya yi ta jira ba ko?" Da sauri Mommy ta nufi d'akin Yadiko dan ta taso Ɗan liti su yi sallama, ta na isa kuwa ta k'wank'wasa qauren d'akin Yadiko ta yi mata gyaran murya alamar sallah take yi, qara k'wank'wasawa ta yi ba jimawa Ɗan litin ya amsa tare da yunk'urawa ya tashi ya sanya kaya a jikin shi da kyau ya fita, a bakin qofa ya coge ya na kallon Billy da ta ci uban wando a matse kamar su ce wayyoo Allah a cire mu mun takura,maida kallon shi ya yi wajen Mommy ya ganta sanye da kayan mutunci sai ya ce, "To kuje lafiya ku dawo lafiya da arziki mai yawa, amma ban yarda ki dawo min da irin waccan shigar karuwan ba" A hankali yake magana yanda daga shi sai Mommyn ne za su ji, d'aga kai ta yi ta juya zata fita Yadiko ta fito ta miqa mata leda mai cike da quli-quli mai sugar da kayan qamshi da take siyarwa ta ce, "Allah ya kiyaye ya sa ki je a sa'a Allah ya yi maki tsari da haram komai yawan ta ya haɗa ki da halal komai qanqantar ta, Allah ya kare ki daga sharrin dake cikin zamanin nan ya fito maki da miji na gari mai albarka" Innoh ce ta iso sajen ta na hamma ta na gyara d'aurin qirjin ta tare da tsirtar da yawu sannan ta ce, "Ba amin ba, ji min wata iriyar addu'a dan Allah malam,wannan ai mugunta ce, idan zaki yi mata addu'a Allah ya bata miji na gari da dukiya me yawa ki yi mata idan ba za ki yi ba ki ja bakin ki ki yi shiru dan Allah" Baki Yadiko ta sake dan bata ga laifin da ta aikata ba a addu'ar ta,cikin d'akin ta ta koma ta hau azkar ɗin ta na bayan sallar farilla da bata yi ba ta na yi ta na tuna yanda ta ga idanun Saddiqanta alamar ta sha kuka wanda ta tabbata na rabuwa da Mommy ne, murmushi kawai ta yi da ta tuna yanda Mommyn ta kula da Saddiqa lokacin ta na qarama kafin su girma amma daga baya komai ya sauya, addu'ar alkhairi ta yi musu ta rufe shafin tunanin su gaba ɗaya. Mota ce mai kyau ta zo ɗaukan su gaba ɗayan ta baqin gilasai gare ta kamar ta masu kidimashin, (kidnapping) haka su Mommy suka shige drivern da ke tuqa motar ya ja suka bar qofar gidan, ko da Saddiqa ta juya zata koma ciki dan yin sallar asuba dan kuwa har an riga an yi bata samu ta yi ba ita, sai ta ga bata ga Ameerah ba a masu raka Mommyn kad'a kai ta yi ta shige ciki dan kuwa a tunanin ta yau tunda dai tafiya Mommyn zata yi tafiyar da bata taɓa irin ta ba ko wani a gidan nasu ai ya kamata ta je su raka ta tunda har sule sai da ya fito. Bayan tafiyar mommy ne da kamar awa guda Baaba ta fito suyar qosai Ameerah ta tafi taya ta ko sallah bata yi ba kamar koda yaushe, suna cikin aikin saida qosai ne Ameerah ta nisa ta ce, "Ohhh ko su Mommy sun isa yanzu kuwa ko suna can suna tafiya a wannan luqeqiyar motar sai Allah,ai Baaba baki ga motar da Mommy da Balki suka shiga ba yanda ki ka san jirgi haka motar take" "Keee 'yannan jirgin ki ka taɓa gani ko me? Sannan gidan uwar wa Mommyn za ta je har ta shiga mota ban sani ba ina gidan nan?" "Ai baki sani ba dama ? Ba a faɗa maki Mommy za ta tafi kano aikatau ba? " Wani salati Baabaa ta saki sai da ta firgita yaron da ke kusa da ita zai miqa mata kud'in k'osai kamar zai faɗa cikin mai Ameerah ta yi sauri ta tare shi, kuka Baaba ta fashe da shi har da majina ta miqe ta tafi cikin gidan ta na surutai, a tsakar gida ta tadda Ɗan liti ya na miqa wa Yadiko kuɗin cefane Innoh na qulla qullin alale ta na waqe-waqen habaici da neman fitina, ganin Baaba afujajan ta na rusa kuka ne ya sanya Ɗan liti da Yadiko yin kan ta da sauri dan su ji bahasin kukan nata,cikin tsananin kuka ta ce, "Allah ya jiqan malam, Allah ya lullub'e shi da rahamar shi a kabarin sa, Ɗan liti ka kiyayi zubar hawaye na kar ka sa ya jiqa kabarin miji na a can barzahu yana zaman zaman sa," "Me ya faru kike irin waɗannan maganganun ne Baaba?" "Yo ba dole na yi irin waɗannan

Chapter 5 of 70