ta take tsintsiyar hannun Ameerah tace,
"Kin san Allah kina sake magana akan Ummar mu zan kifar dake anan wajen sai dai dik abinda zai faru ya faru,mara mutunci kawai."
"Keee dakata min ! Dakata min ba da ke nake yi ba da me dattin ɗankwali nake yi dan haka matsa ki bani waje."
Dariya sosai Fadila tayi kafin tace,
"Ko ba mai dattin ɗankwali ba? Ai kin baro ta a can GIDAN ƊAN LITI GATSO, kowa ya san Innoh bata wanka sai sati ba kuma ta kitso sai shekara wanki kuwa sai sa'a kin ga kuwa a wajen ta dattin ɗankwali ya ƙare,"
Ameerah na gama jin zagin da ake wa mahaifiyar ta ta yarda tsintsiyar tayi kukan kura ta cafki Fadila suka hau dambe, Ummah ce ta fito da gudu tana faɗin,
"Subhanallahi abun har ya kai haka?"
Cikin haki Ameerah ta k'wace daga riƙon da fadila tayi mata ta zabga wa Ummah harara sannan tace,
"Yama fi haka, ai ke kika turo ta ta yi min rashin kunya, to ki sanar da 'yar ki da tayi kwantai ba mashinshini dik sa'o'in ta na ɗakin miji da yaran su ta fita a sabga ta, idan ba haka ba se na ci uwar da ta kawo ta duni..."
Wani b'arin makauniya Fadila tayi wa Ameerah a fuska na bazata, nan take kuwa Ameerah ta tsaga uban ihu kamar ana zare mata rai,bata gama dawowa hayyacin ta ba Fadila ta yarɓar da ita a ƙasa ta hau kirɓar ta, dik yanda Ummah taso ta janye ta kasawa tayi,a guje suka ga shamsu ya baro shagon shi ya shiga gidan,cikin tashin hankali yayi kan Ameerah yana ƙoƙarin janye Fadila daga kan ta yana faɗin,
"Wannan wanne irin abune Ummah zaku haɗu ku tarar wa yarinya ƙarama ku yi ta duka haka? Ke fadila ɗaga ta ko na kifa maki mari."
Cikin haki Fadila tace,
"Sai dai ka kashe ni, amma tinda ta zagi uwa ta a gaban uwar tawa sai na dake ta na fasa mata wannan shegen ruɓaɓɓen bakin nata idan yaso gobe in ta tashi zagin uwa ta ta tanadi ruwan zafin gasa shi."
Shamsu na jin kalaman Fadila sai ranshi ya ɓaci yace,
"Ummah ta zaga?"
"Eh mana kuma an mata magana take yi wa mutane iskanci har tana min gorin aure, da bamu san yanda aka yi naki auren bane sai ki yi wa mutane gori, a yanda kowa yasan Innoh da shegen asirin tsiya na tabbata kaima asirin aka yi maka,"
Cikin tsawa Ummah tace,
"Fadila na ce ki ɗaga ta ko? Kai kuma ba za ka janye ta ba daga saman matar ka kana gani sai dukan ta take kamar ta samu ganga?"
"Barta Ummah ta koya mata yanda ake yi wa iyayen wasu ladabi,ni na koma shago sai anjima,"
Fita yayi ran shi a matuƙar ɓace, ya jima yana jin haushin yanda Ameerah ta raina mahaifiyar shi,dik sanda yayi mata faɗa sai ta hau fushi, to gwanda ya ƙyale Fadila ta gyara mata zama gobe idan an ce ta zagi mahaifiyar shi zata kiyaye.
A haka ya ci gaba da turawa wasu 'yan mata videos na batsa da ya mayar sana'a,ba ƙaramin samu yake yi ba da wannan sana'ar dan kuwa har maza manya zuwa suke yi su zauna a tura musu ko kunyar Allah basu ji balle ta mutane. Dik daren duniya sai shamsu ya shiga da ɗan ƙunshi gidan na mahaifiyar shi da ƙannen shi daban sannan na Ameerah da shi kan shi daban, yau kuwa ya ƙulla yi mata tsiya tinda ta zagar masa uwa.
A cikin gidan kuwa da ƙyar Ummah ta samu ta d'aga Fadila daga saman Ameerah, dik jikin ta yayi futu-futu da ƙura, hancin ta da bakin ta sun fashe sai ɗigar jini suke yi, yawu na tarara ta miƙe tana kuka tace,
"Allah ya isa ban yafe ba matsiyaciya kawai,"
Ganin Fadila ta zabura zata yi kanta sai ta taka da gudu ta shige ɗakin ta, kyacci Fadila tayi tace,
"Matsoraciyar banza mara kunya, da ki tsaya mana ki ga yanda zan yi dake,da na baki mugun mamaki,"
Ameerah zama tayi a bakin gadon ta tana tuna sanda ta daki Saddiqa a soron gidan su bata ji ba bata gani ba,takaici ne ya kama ta ta miƙe da ƙyar ta fita kitchen ta ɗora ruwan zafi a risho, tana gamawa ta juye a bokiti ta shiga wanka.
Bayan ta fito ne ta wuce d'aki ta shirya cikin wani material ɗaya daga cikin na lefen ta da ba a jima da ɗinko mata su ba,kalar material ɗin baƙi mai ratsin green a jiki yayi wa farar fatar ta kyau, turare ta fesa babu shafa mai balle roll on ta koma ta zauna tana ci gaba da kukan bakin cikin shamsu ya ƙi bin bayan ta,ƙwafa tayi tana jiran dare yayi ya zo zata yi maganin shi tinda ta san lagon shi.
Da dare kuwa bayan Shamsu ya dawo taga ya zo da ƙullin leda ya zauna a kujera mai cin mutum ɗaya ya buɗe ledar ya fara cin tsiren shi shi ɗaya ba tare da ya yi mata tayi ko ya zauna inda zata iya zama su ci tare ba,dik yanda taso ta ɗauke kai ta kasa dan haka cikin b'ata rai ta isa gaban shi ta kama ƙugu tace,
"Ina nawa hak'k'in ko ba za a bani bane?"
"Gashi kin faɗa me kuma kike son kiji? Ai in dai zaki zagi uwar da ta kawo ni duniya Ameerah kin gama samun komai daga waje na, ina sane da ƙazantar da kike yi min bakin ki ya dinga wari kamar mushe,hammata tsami,gaban ki wari Ameerah ɗakin ki sai yayi kwana uku baki share ba, sutura babu wanki balle kiyi wanka,dik na hakura na shanye na ji na gani zan zauna dake a haka amma iyaye na basu da mutunci a wajen ki musamman mahaifiya ta,to daga yau an gama irin wannan ɗan iskan zaman a gidan nan kin ji na faɗa maki, dan haka wuce ki bani waje kan na tashi na tattakaki wawuya kawai,"
Kuka ne ya k'wace wa Ameerah ta haye gado kuwa ta dinga rizgar shi, wato a dake ta har a fitar mata da jini a jikin ta amma ya dinga yi mata ihu har da cinye nama ya hana ta? Babu komai Allah zai saka mata ne.
Shamsu kuwa yana gamawa yayi gyatsa me ƙarfi sannan ya nannaɗe ledar ya yar awajen sannan ya cire rigar shi ya haye gado,dama bai dawo gidan ba sai da ya gama kallon fina-finan shi da baya gajiya dan haka a buƙace da ita ya dawo.
Cikin zafi-zafi ya fara taɓa ta saboda yau yaji sauyi, babu wannan mugun warin tayi wanka sai ƙamshin turare ke tashi a jikin ta, cike da tsiwa ta juya zata yi masa rashin mutunci ya samu wannan damar ya rufe mata bakin dan dole ta yi shiru, dik yanda taso ta hana shi kan ta dan ta hukunta shi kasawa tayi da kan ta ta miƙa kai bori ya hau.
**************************
A daren ranar nan Saddiqa bata yi bacci ba sai da ta gyara farar shinkafa ta wanke ta jiƙa saboda tana so tayi sinasir, zob'o ta dafa mai daɗi ta tace ta haɗa ta saka a fridge, Baabaa na ganin ta tana ta murmushin jin daɗi,ta tabbatar da cewa Saddiqa bata baro dik wani kyakkyawan halin Yadiko ba,ta ɗauke su tsaf a kan ta wanda da alama ma za ta iya fin mahaifiyar ta a komai.
Da safe kuwa tinda ta tashi ta saka Saddiq sharar harabar gidan zuwa ƙofar gidan, ita kuma ta hau gyaran gidan, bata samu zama ba sai da ta gama girki ta gyara ko ina tayi wanka sannan ta zauna tana hutawa, Baabaa ce tace,
"Sannu da aiki, Allah yayi maku albarka,Allah kuma ya dawo da shi lafiya,sai dai naga ana ta tuya amma an manta da albasa,"
"Ameen Baaba, amma ban gane me kike nufi ba?"
"Ahhh kin gyara gida tsaff kin yi wanka kin yi kwalliya hannu fari tasss ƙafa fara fat ido babu kwalli,kin kuwa san tasirin yin lalle da sanya kwalli a wajen mace?"
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi, dan kuwa ita a ranta ma har lalle taso taje to nauyin Baabaa ne ya hana ta, kar a ga zaƙewar ta ace ko tarewa bata yi ba tana rawar kai,cikin yin murmushi irin na manya Baabaa tace,
"Koda yake ma gwanda kar ki yi lallen ki jira a yi maki na tafiya ɗakin mijin ki dan na san tinda ya kamo hanya yau ba zai tafi ba sai dake,"
Sake yin ƙasa da kan ta Saddiqa tayi, daga ƙarshe da taji farin cikin yayi mata yawa sai ta miƙe ta bar wajen ta wuce d'akin ta da gudu, a gaban madubi ta tsaya tana kallon shigar ta ta atampa riga da skirt, d'aurin ɗankwalin da ta kafa ya yi dass akan ta kamar an kafa hula, ƙeyar ta kuwa gashin tane irin na Yadikon Sule kwance a dokin wuyan ta ta dunƙule shi waje ɗaya, idanun ta ta kalla taga babu kwalli sai ta buɗe y'ar jakar ta ta zaro kwallin ta shafa har da wani yin style ta saman idanun ta da kwallin,tana gamawa ta kalli kanta sai taga yanda kyawun ta ya fito sosai, sai dai ramar da tayi saboda jarabawa da wahalar makaranta na nan dik ƙashin wuya ya bayyana.
Zama tayi a bakin gado tana nazarin wace iriyar tarba zata yi wa Mijin nata idan ya iso?......
*Ku bawa Saddiqan ku satar amsa.*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA:HAERMEEBRAEH ✍️✨
*SANARWA !*
*Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....*
*MAZAUNA GIDA 300*
*ƳAN ABUJA 300*
*A GARIN MU 300*
*KAI NE JARUMI 300*
*KUN MAKARO 300*
*TAUBASHI 300*
*KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻*
*IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.*
*KAR KU MANTA AKWAI KAYAN GYARAN JIKI A KANO, KADUNA DA KEBBI STATE.*
*FACE OIL*
*SKIN OIL*
*BODY SCRUB*
*HAIR OIL*
*HAIR CREAM*
*HAIR MASK*
*GA MASU SON SIYAN ƊAYA KO SARI SU NEMI WANNAN NO 09031416423*
PAGE 60:
Sadeeq ne ya buɗe wa Munir gate ya shigar da motar shi cikin farfajiyar gidan nasu,cike da maɗaukakin farin ciki ya buɗe murfin motar tashi ya ja Sadeeq dake tsaye yana washe baki jikin shi suka rungume junan su,kallon Sadeeq yayi yace,
"Ina Iyali na?"
Murmushi Sadeeq yayi ya kama baki sannan yace,
"Bari naje na cewa Baabaa kace ba ita kake son gani ba matar ka kake kewa ita kazo gani,"
"Ba ƙarya kayi ba yaro, dan kuwa nayi kewar mata ta ba kaɗan ba,na matsu idanu na suyi tozali da kyakkyawar fuskar ta, hannaye na suyi wa kyakkyawan jikin ta tarba ta musamman,ba zaka gane me nake nufi ba saboda kai yaro ne, mu je ciki,"
Murmushi Sadeeq ya sake yi sannan yace,
"Na san ya kake ji mana, a kullum ta Allah idan na tashi daga bacci ina jin tsananin kewar Yadiko, nakan ji cewar dama itace zata tashe ni sallar asuba idan naƙi tashi tayi min dundu, wannan karon ba zan yi kuka ba sai dai in yi dariya in tashi in je in yi sallah, idan na dawo daga makaranta sai in ji dama ace ita zan gani tana girki, ko tana alwala zata shiga ɗaki tayi sallah, sai tace min kana cire kayan ka kayi wanka kayi sallah kazo mu ci abinci,wannan karon ba zan ce mata abinci zan fara ci ba, zan amsa mata a yanda ta bani umarni, Yah Munir ina kewar Yadiko sosai,na sani Baabaa da Yah Sadeeqa suna kyautata min dan kar nayi maraici, amma na kasa hakuri zuciya ta na ciwo idan na tina babu Yadiko, ina jin kamar maraici ya kama mu na rashin iyaye gaba ɗaya saboda Baba baya kula mu,"
Hawaye ne suka wanke fuskar Saddiqa da ta fito ganin abinda ya sa suka jimawa basu shiga gidan ba,Munir kuwa idanun sa fal k'wallar tausayin yaron ya rungume shi tsam a qirjin shi yana jin wani irin son yaron na shigar shi sosai,anya bazai bijirewa maganar Ɗan liti ba ya wuce da yaron Abuja?
Takun komawar Saddiqa cikin gida da gudu ne ya dawo da hankulan su kan hanyar da ta bi ta koma cikin gidan,buɗe mota Munir yayi jiki babu ƙwari ya hau deb'o kayayyakin dake ciki, sai da ya miƙawa Sadeeq jakar kayan shi sannan yace,
"Lallai ka san yanda ake ji idan ana kewar mutum, kar ka damu da yardar Allah Yadiko tana can cikin ni'imar Allah, ta huta da wahalhalun duniyar nan da basu ƙarewa,muma muna fatan a dik sanda za mu mutu mutuwar ta zame mana hutu,na san kai yaro ne mai hankali da nutsuwa tare da tarbiyya, a dik sanda ka tina Yadiko kayi mata addu'a,amfanin yara kenan wajen iyayen su a bayan babu su, ka zama nagari sannan ka yi musu addu'a,shi kuma Baban ku duk sanda ka samu dama ka gaida shi, shima kayi masa addu'a Allah ya dawo da hankalin shi gare ku kaji?"
Gyad'a kai Sadeeq yayi Munir ya ɗauki abubuwan da yazo dasu na tsaraba suka shiga cikin gidan, Baabaa suka tarar tana tsaye a bakin ƙofar d'akin Saddeqa tana yi mata nasiha tare da lallashi, anan suka fahimci ta labartawa Baabaa abinda ya faru, Sadeeq ne ya sunkuyar da kai sai yaji bai ji daɗin yanda ya b'ata yanayin ba, Saddiqa ta ci buri da murnar ganin masoyin ta gashi ya sanya ta kuka, kamar yaje ya bata hakuri yake ji, amma sai yayi tunanin kar maganar shi ta sake b'ata yanayin,dan haka sai ya gwammace yayi shiru da bakin shi kawai, parlourn ya bari baki ɗaya.
Baabaa ce cikin murna ta hau yi wa Munir sannu da zuwa, shi ɗin ma sakin fuska yayi suka zauna suka fara gaisawa, sai dai hankalin shi gaba ɗaya yana kan masoyiyar shi, ya matsu ya tashi yaje gare ta dan ya lallashe ta,suna nan zaune yaga ta fito, fuskar ta ta sha hoda da kwalli da alama gyarawa tayi,wuce su tayi sanye da mayafi ta shiga kitchen, sauran abinda bata kai ba ta d'akko ta jera a saman dinning table sannan ta ɗauki ruwa da lemon kwali ta kai masa parlour, gefe ta samu a kusa da Baabaa ta zauna cikin jin nauyin shi tace,
"Yah Munir ina wuni? Ya ka baro min su Ummi na da su Khairat? Ina fatan Abbah na lafiya shima?"
"Kowa da kowa na lafiya qlou alhamdulillah,da fatan na same ku lafiya kuma?"
"Lafiya ƙalau muke alhamdulillah,"
"To masha Allahu,"
Murmushi Baabaa tayi tace,
"Bari na shiga nayi alwala naji kamar an fara kiran sallah,"
Ƙunshe dariya suka yi dan kuwa babu wani Kiran sallah da Baabaa ta jiyo ta dai basu waje ne kawai,Baabaa na tashi Munir ya ajiye cup ɗin juice ɗin da ya kurb'a ya koma kujerar da Saddiqa ke zaune tana jifan shi da kallo kamar bata son ta kulle ido dan jin tsoron kar ta dena ganin shi.
Hure mata idanun yayi da iskar bakin shi kafin a hankali ya ɗora goshin shi a nata, a tare suka sauke ajiyar zuciya,nan take zuciyar Saddiqa ta ci gaba da bugawa kamar zata fito saboda tsallen da take a ƙirjin ta, duk wani bugun zuciyar ta yana jin shi a kunnuwan shi,a hankali ya ɗauki hannun sa ya ɗora a saitin zuciyar ta, lumshe ido tayi tare da taune leb'en ta na ƙasa tana jin wani kwanciyar hankali na ziyartar ta, a hankali ta furta,
"Yah Munir kar Baabaa ko Sadeeq su gammu a haka fa,"
"To ni ɗin ba mijin ki bane?"
Janye kanta tayi daga nashi ta rintse idanun ta tana murmushi,hannun shi ya ɗora a saman nata yana murza zoben azurfar hannun nata yace,
"Wai keee haka ake tarbar miji da kunya? Anyaa zaki iya sakin jikin ki dani kuwa?"
"Lokaci ne zai faɗa mana hakan dani da kai Yah Munir,"
Tana faɗin haka ta miƙe ta wuce d'aki dan haɗa masa ruwan wanka,tana shiga ya kalli hanyar yace,
"Brohhh this is an invitation sign Bismillah Allah ɗaga surukin Baba Ɗan liti,"
Cike da takun taƙama ya shiga ɗakin, yana shiga ya rufe ƙofar ya barni tsaye sake da baki, domin kuwa da alama Munir baya so na ɗakko maku rahoto,shigar shi da mintuna biyar Saddiqa ta buɗe ƙofar ta fito tana zuba murmushi,rufe ƙofar tayi ta jingina da murfin ƙofar tana maida numfashi kamar wadda tayi tsere,hannun ta ta sanya a leɓen ta tana shafawa a hankali cike da shauƙi,murmushi ta saki sannan ta dafe ƙirjin ta dake bugawa da ƙarfi ta bar wajen ta koma dinning ta haɗa masa abinci kafin ya fito,dik abinda take yi cikin nishad'i take yin shi har ta gama.
Tana zaune a parlour ta dasa TV a gaba tana kallo a zahiri, amma kuma gaba ɗaya hankalin ta na can wajen Munir tana tina abubuwan da yayi mata a lokacin da ya same ta tana haɗa masa ruwan wanka,ba tare da ta ji zuwan shi ba sai iskar bakin shi taji cikin kunnen ta na dama yana faɗin,
"Kina so na kika gudo kika barni a ɗakin ni kaɗai sannan kika zo nan kina tunani na?"
Cikin sauri ta zabura ta koma gefe tana dariya tace,
"Yah Munir dan Allah kar kasa muji kunya a idon Baabaa da Sadeeq,"
"To naji ga wannan, congratulations my love,Allah yasa yanda kika gama secondary school lafiya ya nuna min kin zama cikakkiyar consultant a bangaren mata, wato ina so ki zamo likitar mata wadda zata kula da dik wani matsalar su,kin ga ta hakane za a samu ƙarin mata musulmai da za su duba matsalar 'yan uwan su ba sai namiji ko kuma arna sun duba su ba ko?"
D'aga kai tayi sannan tace,
"Ameeen My love Allah ya nuna mana lokacin, na gode Allah ya saka maka da alkhairi, amma da ka sani baka kashe kuɗi masu yawa haka ba,kar ka manta ko wayar da nake amfani da ita sabuwa ce baka jima da sai min ita ba,"
"Na sani, ina so ki bawa Sadeeq ta hannun ki sai ki yi amfani da wannan,kin ga dik sanda bamu nan zamu dinga kiran shi muna jin ya yake."
"Na gode masoyi, Allah ya ƙara arziƙi mai albarka, Allah ya faranta maka,"
"Ameeen,"
"Muje ka ci abinci ko?"
Binta yayi a baya har suka je wajen cin abincin, tinda ya fara ci yake yi mata santi,ita kuwa sai dariya take yi tana jin farin ciki na ratsa zuciyar ta, a haka suka gama suka koma parlour suna kallo suna hira, idan ya matsa mata da taɓa ta sai ta ce,
"Sannu da fitowa Baabaa,"
Cikin sauri Munir zai matsa ya kama kan shi,da ya gano ta kawai sai ya dena biye mata,tinda suka fara hirar su ta yaushe gamo sallah kawai ke d'aga su, da sun yi sallar za su dawo su zauna su ci gaba da hirar su, gaba ɗaya Munir ya takura da tazarar da Saddeqa ke basu,ita dai taƙi amince masa ne saboda bata son a ga rashin kunyar ta tinda ba a ɗauke ta an kaita ɗakin shi ba,dik bayanin da zai yi mata dan ya gamsar da ita ita ɗin halal ɗin shi ce ta kasa sakin jiki dashi, dan haka tashi yayi cikin fushi ya wuce d'akin su ya kulle bai sake kula ta ba.
Da dare kuwa tuwon farar shinkafa tayi musu da miyar ɗanyar kuɓewa da busasshen kifi,Munir ƙin fitowa yayi bayan ya dawo daga sallar isha'i dik dan ta sauka daga dokin naƙin ta ta same shi a ɗaki ta lallashe shi yaje cin abinci,ganin shiru har tara da rabi bata je bane ya bashi tabbacin ba zuwa zata yi ba, gashi yunwa dik ta addabe shi musamman da ya ji yanda ƙamshin girkin ya cika gidan,ba dan ya so ba haka ya fito yana wani ɓata rai ya deb'i abincin shi da kan shi ya hau ci,santi yake so yayi amma baya so Saddiqa taga fara'ar shi,hararar ta yayi a lokacin da suka haɗa ido, godiyar da Sadeeq ke yi masa ne ta dawo da shi hayyacin shi daga hararar Saddiqa.
Bayan ya gama cin abincin shi ne ya koma ɗakin yana faɗin,
"Ki kawo min tea da ruwa mai sanyi,"
"To."
Tace sannan ta tashi ta shiga kitchen ta hau haɗa masa shayin,tana gamawa ta kira Sadeeq ta bashi tace ya kai wa Munir, babu musu kuwa ya ɗauka ya tafi ya kai masa, Munir ji yayi kamar ya mayar da yaron yace baya so,haka ya danne ya haƙura ai dai yasan dik abinta a ɗakin zata kwana ko? To za su gauraya ne.
Yana nan zaune zaman jiran Saddiqa baccin gajiya ya ɗauke shi,ita kuwa da taje ɗakin Baabaa zata kwana Baabaa bata hana ta ba sai ta gyara mata waje suka kwanta tare suka yi baccin su.
Washegari da sassafe kuwa Munir ya hau tsume fuska yana faɗin,
"Baabaa dake ne za ayi rakiyar kai amarya ko da su waye ni gobe zan koma bakin aiki,"
"Ah ah ni ba dani za a je ba, su Abbe ne da Khalisatu sune za su raka amarya ɗakin ta, kuma ka yi hakuri ka ƙara koda kwana uku ne mu gyara amarya,"
"Ni babu wani gyaran da za a yi mata tinda dai ba tsohuwa bace irin ki,"
"Ai ko sabon abu yana buƙatar gyara Manniru dan haka ko kana so ko baka so dole a gyara ta,"
Haɗe fuska yayi yace,
"To gaskiya kwana uku yayi yawa,ku dai yi ku gama komai a kwana ɗaya zuwa biyu,"
"Da ban ce maka sati ɗaya ba shine kake neman gindaya mana doka?"
Shiru yayi ya bar wajen dan baya so ya matsa da magana Baabaa ta ja lokaci da yawa ya riga ya san halin ta kaifi ɗaya ce,a daren ranar Baabaa ta kirawo yaran ta ta sanar dasu tafiya fa ta taso, dan kuwa sun gama tsara komai dama,washegari suka fara gyara amarya, amarya ta sha ƙunshi baƙi da ja, ta sha wanka da ruwan magarya da lalle tare da turare mai dad'in ƙamshi da almiski fari.
Dik inda Saddiqa ta gilma ƙamshi ke tashi,a washegarin ranar da su Saddiqa za su tafi Baabaa tasa Abbe ta shirya Saddiqa su kai ta gidan Ɗan liti domin yi masa sallama da sanya mata albarka.
Koda suka isa gidan sun tarar ya dawo yana cin tuwo a tsakar gida Innoh na zaune tana yi masa mitar rashin wadata su da abun miya da baya yi duba da cewa yanzu nauyi ya sauka akan shi sosai, Baabaa bata nan, saddiqa da sadeeq basu nan, ga Ameerah da Hadiza basu nan, su kaɗai ne sai Sule amma ɗan naman miya ko kofi ya gagare su,sallamar su Saddiqa ce ta sanya shi tsayawa da wurga lomar tuwon da ya yanko yace,
"Wa'alaikumussalam,bismillah ku shigo,yau wa nake gani kamar Abbe?"
"Iyy nice Baba,Saddiqa na kawo tayi muku sallama gobe in Allah ya kaimu zamu kaita can ɗakin mijin ta Habuja."
Wani ƙololon baƙin ciki ne ya tokare wa Innoh dake ta washe baki a maƙoshi, nan take ta nemi fara'ar da take yi ta rasa,tsaki ta doka sannan ta miƙe ta shige d'aki tana ta zage-zage,hawaye ne suka wanke fuskar Saddiqa domin tunawa da Yadikon ta da tayi, Sule ne ya leƙo ya taya ta murna sannan yayi mata fatan zaman lafiya da samun zuri'a mai albarka, cikin washe baki yace,
"Ina da wata friend ɗita a Abujar kuwa da rabon watarana idan zan kai mata ziyara na leƙo ki,dan kuwa ina daff da kai mata ziyara,"
Murmushi tayi ta na share hawayen da ya ƙi tsayawa cikin rawar murya da baki tace,
"Na gode Yah Sule Allah ya kaimu lokacin da zaka kawo min ziyara, wataƙila ma naga Auntyn tawa ko?"
Sosa kai yayi ya kalli Abbe dake taɓe baki saboda haushin uwar su da take ji ya shafe su, gani take dik fara'ar da suke yi wa su Saddiqa ba dan Allah bane dan yaji za a kai ta Abuja ne.
Ɗan liti ne ya wanko hannun sa ya zauna ya hau yi wa Saddiqa nasiha, tin tana hawaye sai da ta fara kuka wiwi, dik abinda yake faɗa mata jin shi take kamar Yadiko ce take faɗa mata shi,daga ƙarshe ya fyace majina ya goge da hannun shi ya murje sannan yace,
"Allah ya sawa auren ku albarka ya baki ikon yin koyi da mahaifiyar ki,babu macen da ta fimin mahaifiyar ki a matan aure kaf duniyar nan, bana jin kuma za a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 70