Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Bilal a gidan haya yake da zama, dik qarshen wata biyu ko uku yake zuwa gidan su ganin iyayen shi. Watarana suna zaune a masallaci an idar da sallar magrib bayan sun tashi daga aiki, suna fitowa zasu tafi gida Abdussabour ya kirawo Bilal yayi masa tayin komawa gidan shi da zama idan babu damuwa,bayan 'yar jayya da Bilal yayi akan kar ya takura wa Abdul ɗin,daga qarshe dai ya amince ya koma gidan Abdul da zama. A hankali Bilal ya fara gano muguwar dabi'ar Abdul ta neman matan banza da dare, hakan kuwa yayi masifar d'aga hankalin Bilal da sanya shi a cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali har ta kai ya dena cin abinci sosai, baya kuma yiwa Abdul magana daga sallama da gaisuwa shikenan, a wajen aiki kowa yayi harkar gaban sa idan an tashi kafin Abdul yace wa Bilal yaje su tafi Bilal ya wuce, ko kuma ya boye a wani wajen sai Abdul ya tafi ya fito ya b'ata lokaci a waje kafin ya koma gida. Ana haka watarana Abdul ya ritsa Bilal a gida da tambayar dalilin sauyawar halayyar shi da nesanta kanshi da shi Abdul ɗin, bud'ar bakin Bilal sai yace, 'Ka yi hakuri idan nesanta kaina da kai da nayi yana yi maka ciwo, amma zan yi mamaki ace baka san halayyar da kake yi ta neman mata tana nesanta ka bane da Ubangijin da ya halicce ka,ya kaji yanzu a ranka da nake gudun ka?' Cike da jin kunya da gane inda maganar Bilal ta dosa Abdul yace, 'Ina jin babu daɗi a raina, sai nake ganin kamar na yi maka wani laifi ne babba da ya sa kake nesanta kanka dani,' 'To mu 'Yan Adam ma kenan Abdul,kamar yanda na nesanta kaina da kai haka ubangiji ya nesanta da kai har se sanda ka tuba ka dena aikata zina sannan zai kusanta da kai, sannan kamar yanda kake ji a ranka ka yi min laifi ne ya sanya ni nesanta kaina da kai to ya kamata ka dinga ji a ranka cewa neman matan nan da kake yi kana saɓawa Allah, kana fusata shi, idan ya fusata ka san me zai yi maka? Ya baka kuɗi, ya baka gida,ya baka abun hawa, ya baka rai, ya baka lafiya, to me kake nema? Ka tsaya ka bauta masa shi d'ayan ne kake ganin ba zaka iya ba sai ka yi ta saɓa masa da babban zunubin da da an kirawo shirka saɓawa iyaye sai an ce zina? Habaa Abdul nayi zaton ka girmi wannan level ɗin shashancin ashe....' Cike da jin kunyar Bilal Abdul ya tari numfashin shi da cewa, 'Ya isa haka Bilal, na gode sosai da tunatarwar ka a gare ni, tabbas sai yau na fahimci nasihar da mai martaba yake yi min a fakaice, me yasa bai fito fili yayi min nasiha da faɗa sosai yanda kayi min ba? A kullum sai dai ya dinga cewa idan Allah ya baiwa matasa kuɗi su ji tsoron Allah su kashe su ta hanya mai kyau kar su b'arnatar,Bilal wannan dalilin ne ya sanya nake yawan taimaka wa marasa shi,nake kyautatawa iyaye na sosai suke sanya min albarka, a gani na neman matan da nake yi ba wata matsala bace kawai kauda sha'awa ne kafin nayi aure,tinda ai kowa nada sha'awar,' (Da damar matasa idan suka samu kuɗi basu da aure, to fa ba a raba su da d'aya daga cikin abubuwan nan, shaye-shaye,neman mata,caca da sauran abubuwa na sab'on Allah, dan haka da ka kula Allah ya ɗaukaka ɗan ka maza ka ja shi a jiki ka nuna masa hanyar da zai bi, ba zaka samu damar jan d'an ka a jiki ba har sai ka bashi tarbiyyar da zaka iya juya shi ko bayan ya girma) Nan dai Bilal yayi tayi wa Abdul nasiha da nuna masa haramcin yin zina har ya samu maganganun sa suka yi tasiri a zuciyar shi yayi alqawarin ba zai sake ba. Bayan shekara ɗaya da daina neman matan da Abdul yake yi, ya koma ga Allah rayuwar shi ta koma daga ibada sai aikin shi, kyautatawa iyayen sa da mutanen da Allah ya sa suna da rabon ya taimaka musu, sai kuma da dare idan ya dawo gida sai ya shiga social media ya shiga facbook ya ga me duniya take ciki, daga nan ya koma shiga Instagram da sauran social media platforms, a hankali shaid'an da shaid'anun mata suka fara jan ra'ayin shi har yake chatting da matan Facebook dake nuna suna son shi, dan kuwa hoton shi ne da ya ɗauka a wani companyn qarafa da suka je Abuja wani aiki a profile ɗin shi,a haka Abdul ya gane soyayyar social media da daɗin da take da ita, dan kuwa yana samun biyan buqata sosai kuma daga nan yake aikawa dik yarinyar da ta gamsar da shi kuɗi ko nawa ta buqata baya jin shakkar yin hakan. Dik wannan abun da yake yi Bilal bai sani ba, dan kuwa bai taɓa bada wata qofar da zai gane abinda yake aikatawar ba, tinda kowa da d'akin shi da band'akin shi a cikin d'akin. Ana haka ya haɗu da wata yarinya kyakkyawa a Facebook mai suna Salwahlove,tinda ya haɗu da Yarinyar nan ta ɗauke hankalin shi ya daina mu'amala da kowacce yarinya sai ita, qarshe dai sai da ya zamana har da rana sai Salwa ta sanya Abdul keb'e kan shi a wani wajen su sha soyayyar su,dik yanda taso su haɗu yaqi yarda gudun kar Bilal ya gane wa'azin shi yaa rushe yayi sabon d'ori. A kwana a tashi Abdul da Salwa sun kai watanni huɗu suna soyayya Kwatsam sai Salwa ta fara turo masa hotunan sassan jikin ta, daga qarshe shima ta dinga hilatar shi har ya fara tura mata nashi, cikin rashin dabara da wayo Abdul idan ya tashi zai tura kafff jikin shi, ita kuma dake mai wayo ce sai ta tura iyakar qirjin ta ko gaban ta ko wani sashe na jikin ta, bata taɓa nuna masa hoton ta ba gaba ɗaya tsirara,sannan bata yarda da video call ko voice call kawai a yi chatting. Watarana Bilal da Abdul na zaune a parlour sun yi order ɗin abincin dare, sai mai abici ya kawo ya buga qofa, kasancewar Abdul na zaune kusa da qofa sai ya miqe yace Bilal yayi zaman shi bari yaje ya dawo, Abdul na fita gate ɗin gidan dan karɓo abinci Salwa ta hau kiran shi a waya, ko da Bilal ya leqa sai yaga an rubuta Salwahlove a jikin sunan, Murmushi kawai yayi ba tare da ya ce komai ba sai ya ɗauka yana ɗauka sai yaji an kashe wayar,a zaton shi ma katsewa wayar tayi, yana ajiye wayar Abdul ya shigo, cike da shaqiyanci irin na abokai Bilal yace, 'Aunty Salwa ta kira ka yanzun nan,amma ina ɗauka dan na ji muryar mai sa'ar da ta sace zuciyar ka har ka qi sanar dani, sai naji ta katse,' Murmushi Abdul yayi yace, 'Ba katsewa kiran yayi ba haka take da kunya, tinda muke da ita tsawon watanni ban taɓa jin muryar ta ba sai dai muyi chatting,yanzu haka kiran da ka gani sanar dani take yi lokacin tane yanzu,' 'Tooo ikon Allah, ai kuwa yau sai dai tayi haƙuri, nima ina buqatar lokacin ka, mun jima bamu zauna haka mun yi hira ba, ashe ita ce ke janye ka,' Nan da nan kuwa Abdussabour ya sanya wayar shi a silent suka hau hira suna cin abincin su da aka kawo musu,a can facbook kuwa Salwah ta cika tayi famm da baqin ciki da damuwar rashin Abdul domin kuwa ta qudirta a ranta yaune wa'adin soyayyar qaryar su zata qare bayan ta amshi wasu manyan kuɗi a wajen Abdul ɗin. Abdul kuwa bayan sun gama cin abinci da hira da Bilal sai kowa ya tafi makwancin shi, suna komawa d'akunan su Abdul ya kunna data ya hau Facebook dan ya lallashi abar qaunar shi Salwa, yana shiga yayi mummunan gamo da saqon da ya rikita ƙwaƙwalwa da ruhin shi har ya kasa kwanciya ya fito zuwa d'akin Bilal a kid'ime. Bugu ɗaya yayi wa qofar d'akin Bilal ɗin Bilal ya fito sanye da gajeran wando da singileti yace, 'Lafiya kake min irin wannan bugun qofar kamar zaka balle ta? Meya fa...' Maganar shi ce ta katse bayan kiran wayar Abdul da aka yi, cikin hanzari Bilal ya kafe shi da ido yana son sanin abinda ke faruwa,Abdul ne ya amsa wayar ya sanya ta a handsfree nan take muryar gardin qato ta fara magana, 'Baby ya baka turo min kud'in da na tambaya ba? Ko baka gane me magana bane? Salwa ce faaaa, dan Allah ka turo min kud'in na gaji da ganin ka ina so na sauya sheqa na koma wajen wani sabon jinin,' 'Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,dama Salwah ba mace bace namiji ne?' Abdul da Bilal suka faɗa a tare, nan take abubuwan da suka dinga faruwa da Abdul suka dinga dawo masa akan shi,yanda Salwah ke qi sam ta tura hoton ta har fuskar ta,da yanda take qin suyi waya ko suyi audio sai dai shi ya dinga yi ya tura mata, ashe dik ta tara waɗannan abubuwan ne ta ajiye dan su zama abinda zata yi blackmailing ɗin Abdul dasu. Cikin fushi Bilal yace, 'Kai dan uwar ka ka san wa kake yi wa wannan shirmen kuwa? Zamu sa a nemo ka a kamo mana kai dik inda ka shiga mu ci uwar ka' Cikin dariya matashin yace, 'Kafin ku nemo ni ni kuma zan wulaqanta ka domin kuwa nan da awa ashirin da huɗu idan banga million uku a account ɗina ba hotunan tsiraicin ka zai shiga duniya zaɓi yana gare ka, kar ka tsaya dogon nazari ai ko ba komai na ɗebe maka kewa da hotunan budurwa ta da take turo min ka kalla ka ji daɗin ka,nima kuma ka turo min naka ina nan na adana su a waje mai tsaron da babu wanda ya isa ya taɓa su in ba ni ba, da wannan sokiburutsun da kuke yi dama kud'in kuka turo min dan kuwa nasan kafi qarfin su ko babyna? da ka zaci a banza zaka hau social media kaga hoton kyakkyawar mace a profile ka kama soyayya da ita? Komai na duniya yana da price ni kuma na yanka maku nawa dole kuma ku biya,' Yana gama fad'ar haka ya kashe wayar shi ya bar Bilal da Abdul cikin tashin hankali,Bilal kallon Abdul yayi yaga yanda nadama da tashin hankali suka baibaye shi, damuwa da tsoro suka shige shi,tinanin shi bai wuce yanda iyayen shi za su ji ba a duk sanda suka fahimci ya aikata zina ta waya har hotunan shi da videos ɗin shi suka watsu a duniya, me zai sami aikin shi? Wacece zata aure shi anan gaba idan tsiraicin shi ya fita duniya? *Bature yace never judged a book by its cover. Masoyan Abdul a yi hakuri kar a canye ni d'anyaaaa haka labarin yazo, kowa yana da rayuwar shi da ta gabata, walau mai kyau walau mara kyau, fatan kawai shine kar mumini ya dawwama a aikin sab'o.* [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 45 Kamar yanda Abdussabour yayi ƙoƙari yayi gini a garin kano da qauyen su na Ba Mugu, haka ma Bilal yake ƙoƙarin yin gini a can garin su na Bauchi saboda yana so idan ya kammala ya tattara har iyayen shi su bar gidan da suke ciki su koma sabo,kasancewar Iyayen shi ba masu qarfi bane ya sanya d'awainiyar gidan su dik ta rataya akan shi, wannan shine dalilin da ya sanya bai iya baiwa Abdul gudummawar kud'in da za su isa a biya wannan bawan Allah'n da ke neman lalata sunan Abdul a idon duniya. Dik yanda mutum yake komawa idan ya shiga tashin hankali da damuwa to fa Abdul ya koma hakan ko ma fiye da hakan, saboda magana ake ta tsiraicin shi zai watsu ya bazu a duniya,gaba ɗaya abun har mamaki yake bashi yanda hanyoyin samun shi suka toshe, dan kuwa tin ana abun 24 hours sai da aka kai 72 hours Abdul bai haɗa kan million biyu bama balle a kai ga ukun,ganin haka ne ya sanya Bilal shawartar shi da ya je gida wajen iyayen shi musamman mai martaba ya tambaye shi koda aro ne wataqila ba za a rasa ba a wajen su,nan take Abdul yayi na'am da wannan shawarar, da rana tsage-tsage ya shirya ya hau motar shi ya wuce garin Ba Mugu, direct gidan su ya nufa ya tarar da mahaifin shi a fada da mutane ana wani case tsakanin manoma da makiyaya, bai tsaya a fadar ba bayan ya kwashi gaisuwa sai ya shiga cikin gida wajen Innah Laminde wadda ke zaune a kujerar ta ta shan iska suna hira da kishiyoyin ta da yaran su 'yammata cikin nishad'i. Innah Laminde na ɗora idanun ta akan fuskar gudan jinin nata gaban ta yayi mummunan faɗuwa,domin kuwa a cikin kwana biyu Abdussaboor ya rame, idanun shi sun yi zuru-zuru kamar wanda yayi shekara yana jinya, shiru tayi tana bin shi da kallo har ya gama gaishe da iyayen nashi yayi wa qannen shi wasa ya isa gaban ta ya durƙusa ya na gaishe ta, da ido ta kafe shi tana son sanin abinda yake damun shi, nan take idanun shi suka kad'a suka yi jajawur, miqewa yayi ya shiga ɗakin ta ya wuce uwar d'aka,Innah Laminde na ganin haka ta tabbatar da babu lafiya, dan haka cikin sauri ta miqe tabi bayan ɗan nata, a tsaye ta gan shi yana sintiri idanun shi na bayyanar da damuwar shi,kafaɗar shi ta dafa ya juyo, suna haɗa idanu ya saki wata iriyar ajiyar zuciya mai qarfi, zama tayi a bakin gado ta nuna masa gefen ta tace, 'Zauna SARAUTA ka sanar dani abinda ke damun ka,' Cikin jin kunya ya zauna a qasan qafafun ta kan shi a qasa yace, "Innah nayi wa Ubangiji na laifi mai girma,gashi tin a duniya zan fara biyan laifin nan da na aikata da farashi mai girma, dan Allah ku taimaka min idan akwai kuɗi a wajen ku koda dubu ɗari biyar ne ku bani in tafi yanzu, rayuwa ta na cikin hatsari," 'Hasbunallahu sa'yu'utinallahu min fadhlihi inna ilallahi raghiboon,Allah ubangiji yayi maka gafarar zunuban ka da mu baki ɗaya, tashi ka zauna anan, ka sanar da mahaifin ka abinda ke faruwa kuwa?' Har ya bud'i baki zai yi magana Sultan ya shiga ya isar da saqon mai martaba akan yana son ganin Abdussaboor a turakar shi, domin kuwa ya kula da halin da gudan jinin nashi ya shiga shi yasa ya sallami kowa ya shigo ciki sannan ya aika a kira masa shi dan ya ji damuwar shi. Abdussaboor na gab da fita Innah Laminde ta tsaida shi tace, 'Kar ka b'oye wa mahaifin ka damuwar ka, domin kuwa shi kaɗai ne zai taya ka kokawa kuma ya sama maka mafita,ka zo ka karb'i dubu dari biyu a waje na kafin ka tafi, Allah ya kyauta ya kiyaye dikkan abin qi, ina mai yi maka nasiha da ka ji tsoron Allah a dik inda kake, sannan a koda yaushe ina sanar da kai ka dinga bin dokokin Allah,' Jinjina kai kawai Abdussaboor yayi yana tunanin ta inda zai fara sanar da mahaifin shi abinda ya aikata a rayuwar shi,cike da damuwa ya isa turakar Mai martaba, a zaune ya gan shi an kawo masa abincin ranar shi ya buɗe ya na kallon kwanikan kawai ba tare da ya sa hannu ya ci ba, Abdussaboor na shiga ya samu waje ya zauna ya sake gaida mahaifin nashi, bayan mai martaba ya amsa ne ya kalle shi cikin kulawa yace, 'Bismillah mu ci abinci kafin ka sanar dani damuwar ka,' Hannu Abdussaboor ya wanke ya matsa jikin kwanikan abincin ya jira saida mahaifin shi ya fara sanya hannu ya ɗebi tuwon farar shinkafa da miyar taushen da ta ji gyad'a da naman rago, sannan shima ya sanya nashi hannun, sun fara cin abincin su ba tare da kowa yace uffan ba wayar Abdussaboor ta hau ringing, nan take gaban shi ya tsinke ya faɗi,cike da damuwa ya zaro wayar ya kalli mai kiran nashi, hannun shi ne ya fara rawa sannan ya kalli mahaifin nashi da yayi kamar be ga halin da yake ciki ba, dan kuwa lomar tuwon shi kawai yake sakawa a bakin shi yana taunawa a nutse. Gefe Abdussabour ya koma ya amsa wayar, cikin yin qasa da murya yace, 'Malam ka jira lokaci ya cika mana idan kaga ban baka kud'in ba sai ka kirani,habaa sai faman damu na kake yi, sannan ba zai yuwu na baka million uku ba dole na rage dubu ɗari biyar dan kuwa ban samu dika ba,' Cikin dariyar shaqiyanci bawan Allah'n nan yace wa Abdussabour, 'Calm down mana, ai tunatarwa bata zama laifi ba ko?' Tsaki Abdussabour yayi sannan ya kashe wayar ya koma ya zauna, kasa ci gaba da cin abincin yayi, shi kuwa Sarki bai daina ci ba har sai da ya qoshi sannan ya wanke hannun shi, Azizah ce ta shiga ta kwashe kwanukan sannan tayi waje, gyara zama Mai Martaba yayi kafin yace, 'Bismillah Babana sanar dani damuwar ka kar ka b'oye min komai,' Cikin in'ina da kame-kame Abdussabour ya labartawa mahaifin shi duk abinda yake faruwa da kuma matsalar da ta kunno masa kai, faɗin yanda ran Sarki ya baci ma ba abu bane mai yuwa, amma da yake mutum ne shi mai shanye damuwar shi, sai yayi shiru bai ce komai ba na tsawon wani lokaci kafin daga baya yace, 'Ina No mai kiran naka take?' Jiki na rawa Abdussaboor ya miqawa mahaifin shi No a wayar shi sannan ya koma gefe, Sarki wayar shi ya ɗauka ya danna kira tare da bada umarnin a nemo masa mai wannan No a duk inda yake, sannan a sanya jami'an tsaro su mamaye shi su kama shi yana so ya b'ata wa masarautar shi suna ta hanyar blackmailing babban ɗan shi. Nan take kuwa wanda Sarki ya kira suka bashi tabbacin za su tsananta bincike ya basu wani ɗan lokaci,bayan ya kashe wayar ne ya ƙurawa Abdussabour ido har sai da Abdul ɗin yaji wani irin tashin hankali da damuwa na mamayar shi a hankali, a hankali Sarki ya fara magana, "ABDUSSABOUR ka bani mamaki, ka karya min yarda ta da amincin da na baka, ka kunyata ni a idon ubangiji na, ba tarbiyyar da na yi maka ba kenan ni da mahaifiyar ka,a zato na a iya ilimin da muka baka idan sha'awa ta dame ka kasan yanda zaka magance ta ba tare da ka kauce hanya ba, Abdussabour ina ka bar aure bayan kana da gidaje har biyu, kana da abun hawa, kana da salary da zai iya riqe maka mata huɗu idan kana so? Abdussabour ina ka bar azumin nafila idan kana ganin baka son kayi aure saboda baka shirya yin auren ba? Abdussabour me ya kai ka buɗe zuciyar ka ma mutanen banza har su hilace ka ka afkawa zina? Abdussabour me ya kai ka kallo da karance-karancen banza da ya kai ka aikata zina da girman ka da qimar ka da mutuncin ka?" Hawaye ne ke zuba sosai a idanun Abdussabour, banda istighfari babu abinda yake yi, hakan da yayi ne ya sanyaya ran mahaifin shi, domin kuwa a qallah Abdussabour ba shi yake baiwa haƙuri ba, yana neman gafara ne daga wajen Allah ya fahimci Allah yayi wa laifi, dan kuwa shi laifin zina haqqi ne na Allah,idan bawa ya aikata shi da zarar ya nemi gafarar Allah shikenan, sai dai kuma mutum idan yana da aure to fa ya haɗa da hak'k'in abokin zaman shi, sai ya san hanyar da zai bi ya nemi yafiya ba tare da ya tona asirin kanshi ba gudun lalacewar auren shi gaba ɗaya. Abdul bai samu damar yin magana ba har sai da mahaifin shi ya gama yi masa nasiha mai ratsa zuciya, sannan ya samu damar cewa, "Tinda abun nan ya faru na gane illa da munin abinda na aikata, na kasance ina mai cike da nadama da danasani tare da kaico akan wannan abu dana aikata,ina neman afuwar Allah sannan ina neman gafarar ku akan kaucewa tarbiyyar da kuka yi min,inshaa Allahu irin haka ba zata sake faruwa ba har abada, zan kuma dage na nemi mata nayi aure," "Allah ya karb'i tuban ka babana, kafin lokacin auren naka ina mai yi maka nasiha da ka riqe azumi da yawan karanta alqur'ani da kuma zama a majalisin da ake koyar da ilimi na addini, Allah ya qara yi wa tarayyar ka da Bilal albarka, tabbas shi ɗin aboki ne na gari wanda za a yi fatan a ƙarasa rayuwa dashi har abada,yanzu ka tashi kaje zan kula da wannan kar ka sake ɗaukan wayar shi,sannan ko ya sauya no ya kira ka da kaji shine kar ka kula shi," Dik da har a wannan lokacin zuciyar shi na cikin tashin hankali amma ya samu natsuwa da salama kaɗan,yana fatan asirin shi ya rufu har abada a samu nasarar yin maganin wannan mutumin dake neman zubar masa da mutunci. Abdussabour bai bar garin Ba Mugu ba sai bayan magariba,a lokacin Mai martaba ya sanar dashi bawan Allah'n nan ya shiga hannu, yana ofishin 'yan sanda dake Yakasai a garin Kano da ya isa ya wuce can a kashe case ɗin,baya so ya aika kowa daga nan saboda baya son kowa yasan me ya faru ciki kuwa har da mahaifiyar shi, godiya Abdussabour ya dinga yi wa mahaifin shi sannan ya yi sallama da iyayen shi mata ya bar garin Ba Mugu ya koma cikin garin Kano, direct Yakasai ya nufa yana zuwa ya tarar da Bilal da yayi wa waya tun a hanya,rungume Bilal yayi cike da farin ciki kamar an ce masa case ɗin ya qare. Ko da aka nuna masa matashin da yayi masa wannan abun sai da ya nemi waje ya zauna saboda shiga damuwa,nan take ya tuna sanda matashin yazo masa shajaran majaran yana neman taimakon abinda zai ci da qanwar shi da mahaifiyar shi kasancewar shi maraya, Abdul ɗin bai yi qasa a guiwa ba wajen taimaka masa da maqudan kud'ad'e sannan ya bashi No shi yace a duk sanda yake da buqatar taimako ya neme shi, tin daga nan yake taimaka wa yaron ba tare da sun sake haɗuwa ba,amma shine ya biyo masa ta wannan hanyar zai cutar dashi. Nan take Bilal yayi tsalle ya falle matashin da mari, dik faɗa da tsoratarwar da hukumar 'yansandan ke yi wa Bilal be hana shi lallasa yaron ba, yana zagin shi, cikin takaici yace, "Matsiyaci dogon banza, dube ka kamar na Allah, ashe ƙwallon shege ne, kai yanzu ka rasa wanda zaka zalunta sai wanda ya taimake ka? Dan Allah ku bari na ci uwassa in yaso ku rufe ni na kwana anan tare dashi," DPOn da ya dena hana Bilal dukan yaron ne ya riqe shi yana dariya yace, 'Aboki na gaka gajere amma sai masifar tsiya, ana hana ka kana qara daka tsalle kana falla masa mari, tin ina jin haushin qin jin maganar mu da kake yi har ka fara bani dariya, to yanzu ba wannan ba dai, a iya binciken da muka fara mun gano qarya yake yi bashi da wani abu daya b'oye na game da abinda ya faɗa akan ka, hasali ma dik maganar da kuka yi dashi goge ta yake yi saboda qanwar shi na amfani da wayar tana assignment shi yasa baya barin komai da zai sanya mata zargi akan yayan nata,iskanci ne kawai irin na ɗan yau, amma dik da haka zamu sake bincikar shi na sati biyu dan tabbatar da bai ajiye wata shaida ba a wani wajen,' Cike da d'imuwa da gigicewa matashin nan yace, 'Sati biyu ! Dan girman Allah kar ku ajiye ni har tsawon wannan lokacin mahaifiya ta zata iya mutuwa dan baqin ciki idan ta neme ni ta rasa aka ce mata ina nan, ba irin tarbiyyar da tayi mana ba kenan, ni kaina tsautsayi ne da rashin godiyar Allah yasa na aikata abinda nayi, dan Allah me gida kayi hakuri ka sa baki a sake ni na koma, yau tin safe bamu ci abinci ba dikan mu har mahaifiyar mu, gashi bata da lafiya tana da ciwo zuciya magungunan ta sun qare,bana so na rasa ta, bana so na rasa ta dan Allah ku taimaka min,' Kuka matashin nan ya

Chapter 30 of 70