ta san yaron na so. Cike da ladabi Sadeeq ya karɓi kud'in ya tafi shago dan siyowa Mommy abinda ta aike shi.
Kamar yanda ta ƙudirta kuwa washegari da rana bayan ta kammala gyara gidan, ta yiwa Innoh wanka ta sauya mata kaya,sai ta zauna ta bata abinci da maganin ta suka ɗan gwada tafiya a tsakar gidan,suna kammalawa ta kama Innoh suka koma ɗaki,babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta saboda maganin da ta sha da motsa jikin da tayi,tana ganin haka sai ta leƙa tsakar gida taga babu kowa, ledar da aka yo mata siyayyar tsarabar da zata kaiwa Amir ta ɗauka ta duba komai ya yi dai-dai,sai kawai ta fita tsakar gida ta shiga wanka daga nan ta yo alwala sannan ta yi sallar azahar. Tana idarwa ta hau kwalliya sassauƙa ta sanya wani material ɗin ta mai tsada da Abdul ya taɓa siyo mata a zuwan shi kaduna da ya yi saboda aiki,kalar material ɗin ta karb'i farar fatar ta,sai ta yafa mayafin ta ta zira baƙaƙen takalman ta ta ɗauki ledar tsarabar ta ta bar gidan.
Tafe take tana addu'a Allah yasa ta haɗu da Abdussaboor ta sanya shi a idanun ta ko zata ji sanyi a ranta,da wannan tunanin ta isa gidan Sarki. Da Innah Laminde ta fara cin karo a tsakar gidan suna hira da sauran matan gidan,ga goro da chewing gum da alawa nan ana ta ɗaurawa a leda za a kai gida-gida saboda a gayyaci mata auren Abdul ɗin.
Cike da dakiya Mommy ta durƙusa har ƙasa kamar yanda ta saba a baya ta gaishe da Innah Laminde da sauran matan Sarki,kallon ta kowa yake yi kamar sun samu sabuwar halitta,babu wanda ya taɓa tsammanin ganin ta a wannan lokacin,duba da yanda labarin auren Abdul ya karaɗe ƙauyen.
Tana nan duƙe ta jiyo ƙamshin turaren shi kamar a mafarki,kasa tashi tayi daga wajen da take tsugunne sai da Innah Laminde ta miƙe tsaye ta fara takawa ta ce wa Mommyn,
"Shigo ciki ku gaisa da ɗan naki mana."
Sarai Mommy ta gane Innah Laminde bata son Mommyn ta haɗu da Abdussaboor dake shirin shiga cikin gidan ne shi yasa ta yi mata tayin shiga ciki,dan haka tana miƙewa sai ta yi dabarar sakin ledar hannun ta a ƙasa har abun ciki ya watse a ƙasa,cikin wani irin salo Mommy ta duƙa tana kwashe biscuits da chocolates ɗin da suka zube tana mayarwa ledar su,Abdul kuwa da shigar shi gidan kenan idanun shi suka sauka akan Mommy wadda ta juya bayan ta tana kwashe abu a kasa.
Wani irin yawu ya had'iya sai da maƙoshin sa ya yi sama da kasa a fili kafin ya hau ƙyafta idanu da sauri da sauri kamar wanda yake son ya farka daga mafarkin da yake ciki. Mommy kuwa na gama kwashe komai sai ta yi gaba ba tare da ta juya ta kalli inda Abdul ɗin yake ba,tana shiga ɗakin Innah Laminde sai ta zauna a ƙasa tana wani sunne kai,murmushi Innah Laminde ta yi dan kuwa taga dik abinda ya faru,har da halin rikicewar da Abdul ɗin ta ya shiga akan ganin Mommy,gaisawa suka sake yi sannan ta k'wala wa mai aiki kira aka karɓo Abdul a wajen Baban shi aka kawowa Mommy.
Koda ta ɗauke shi ta zaci zai manta da ita ko kuma ya yi mata ƙiwa,sai taga yana ta shafa fuskar ta yana surutai irin na yara. Wasu irin zafafan hawaye ne suka dinga sauka a idanun ta wanda suka yi matuƙar karya zuciyar Innah Laminde har ta ji rashin kyautawar ta akan kaiwa Mommy ɗan ta da bata yi ba har na tsawon watanni masu yawa haka.
Cikin kuka Mommy ta fashe da dariya da ta ga Abdul ya tashi yana tafiya sosai da ƙafafun shi har yana haɗawa da gudu zai fita waje,ƙamshin turaren Abdul ne ya tabbatar mata da wanda yaron ya gani har yake son fita waje. Cikin sauri Mommy ta miƙe tsaye tana share hawayen ta ta ajiye ledar tsarabar da ta kawo a gaban Innah Laminde ta ce,
"Ni zan koma,sai kuma watarana,ina fatan za a dinga kawo min shi ina ganin shi ko da sau ɗaya ne a wata dan Allah."
Tausayin ta ne ya kama zuciyar Innah Laminde,cikin sanyin murya ta ce,
"Inshaa Allahu za a dinga kawo miki shi lokaci zuwa lokaci dan ku gaisa,fatan mu shine Allah ya raya shi ya yi masa albarka."
"Amin ya Allah na gode."
Da alamun sauri a tattare da Mommy amma Innah Laminde ta sake tsaida ita ta hanyar tambayar ta jikin Innoh,cikin sauri Mommy ta ce,
"Da sauƙi alhamdulillah,tana ma gida yanzu haka, bamu jima da dawowa daga asibiti bama."
"To ki ɗan tsaya na kawo maki abun gayyatar biki ki kai musu,muna gayyatar ku ai yanzu mun zama ɗaya."
Wani irin yawu Mommy ta haɗiya,tare da kallon yanda Innah Laminde ke magana cikin kwanciyar hankali,ba dan kar a ga rashin kunyar ta ba,to tabbas da ta gaggawa Innah Laminde baƙar magana,taya zata bata abun gayyatar auren namijin da take mutuwar so a ran ta wai ta kai gidan su? Wannan ai cin fuska ne,daurewa Mommy ta yi ta tsaya tana jiran Innah Laminde a tsakar gida,Amir ne ya dawo ya riƙe mata mayafin ta,babu ɓata lokaci ta duƙa ta ɗauke shi,ƙamshin turaren Abdussaboor dik ya cika mata hanci, lumshe idanun ta tayi ta sake rungume yaron tana sumbatar shi. Abdul ne ya fito daga ɗakin shi ya yi hanyar waje riƙe da makullin mota.
A haka Innah Laminde ta sami Mommy ta miƙa mata leda cike da goro da alewa da chewing gum har da biscuits tace ta kai gida, godiya ta yi mata tare da sanya alkhairi a auren ta miƙa mata Amir da ya fara rikicin zai bita ta fita da sauri,tana isa soron gidan ta fashe da wani irin kuka mai cin rai,dik yanda taso ta danne kukan kasawa ta yi,kanta ta fara tambaya a fili tana faɗin,
"Shin wai ni wace wautar ce ma ta sanya ni zuwa ganin Amir a irin wannan lokacin? Tinda na yi haƙurin watanni ban gan shi ba me zai hana na ƙara haƙuri har a gama bikin kafin na zo,yanzu gashi zuwana be amfana min komai ba sai tada min da tsohon mikin dake cikin zuciyata da ya yi."
"Zuwan ki ya yi amfani mana Hadiza ! tinda gashi kin ganewa idanun ki shirye-shiryen aure na,a zaton ki tinda kin nakasa ni kin yi gaba babu wadda zata aure ni ko?"
Cikin kuka Mommy ta juya tana kallon Abdussabour da ya harɗe hannayen shi a ƙirjin shi ya tokare ƙafar shi ɗaya a jikin gini yana bin ta da kallo,kallo ne dake huda dika wata sura ta jikin ta yana shigewa cikin jikin ta,da ace suna da aure a wannan lokacin da ta fassara irin kallon da yake yi mata da kallon ƙauna da soyayya,kallon ina son kasancewa dake Hadiza. Sai dai kashh wannan Abdul ɗin dake a gaban ta ba Abdul ɗin da ta sani bane a baya. Ba tare da ta ce komai ba ta ɗauki ledar ta da ta faɗi a ƙasa ta gyara zaman mayafinta zata fita daga soron,cikin sauri ya riƙe mata mayafin ya ce,
"Me yasa kika zo gidan mu a yau? Me yasa kike son ki dawo min da hannun agogo baya? Na tabbata ba ganin Amir bane kaɗai ya kawo ki gidan nan,duk yanda akai kin samu labarin zuwana gari yau shi yasa kika fake da ganin Amir kika zo gani na."
Wata iriyar harara Mommy ta buga masa sannan ta ce,
"Allah ya kiyaye na zo ganin ka Abdussabour,lokacin da na yi begen ka,na so ka aure ni na koma zaman gidan ka saboda ina jin babu daɗi akan abinda na yi maka ya wuce,yanzu sai dai in ce Allah ya baku zaman lafiya da kai da sabuwar amaryar ka."
Cike da ɓacin rai Abdul ya sakar mata hijabi,ita kuma ta sa kai ta fita ta bar gidan cikin sauri ba tare da ta waiwaya ba,rintse idanu Abdul ya yi sannan ya ƙanƙame jikin shi waje ɗaya,wani irin abu yake ji a jikin shi game da Hadiza wanda ya jima be ji ba,ji yake yi wani irin karfi na shigar shi wanda ya jima yana neman irin wannan ƙarfin a tattare da shi tin lokacin auren shi da Huzaimah,a hankali ya shafa jikin shi ya ce,
"Kenan hakan yana nufin na warke? Na dawo cikakke kuma lafiyayyen namiji kamar yanda nake a baya?".............
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 105:
Cikin dabara Abdul ya samu ya bar soron gidan nasu ya shige motar shi yana maida numfashi da ƙyar kamar wanda ya yi gudun ceton rai. Wata iriyar zufa ke karyo masa jikin shi na rawa ya tada motar shi ya wuce gidan shi,tinda ya isa ya hau tina rayuwar su ta baya da shi da Mommy, tsoro ya fara ji yana zargin anya ba asiri ta sake yi mishi ba kamar yanda ya ji labari a wajen Sultan bayan ta auri Malam? Cikin fitar da wata iriyar zazzafar iska daga bakin shi ya ce,
"Hadiza me yasa kike son wahal dani ne? Na zata na rufe babin ki a rayuwa ta sai kawai in sake afkawa cikin tarkon son ki a karo na biyu? Shin anya ma son ta nake yi ba wani abu nake so daga wajen ta ba?"
Rasa wanda zai kira ya sanar da shi halin da yake ciki ya yi,idan ya kira Bilal ya sanar da shi zai zama kamar cin fuska ne a wajen shi,idan ya sanar da Sultan kuma yaron zai iya tona masa asiri har mutanen gidansu su san halin da yake ciki. Hannu ya sa ya shafe zufar dake sake tsattsafo masa,salati ya hau yi ya tashi daga inda yake zaune ya buɗe fridge ya ɗauki ruwa mai sanyi ya buɗe robar ya kafa kai yana sha, be ajiye ba sai da ya ƙarar da ruwan duka. Kasa jure yanayin da yake ciki ya yi a gigice ya ɗauki wayar shi ya kira Bilal,cikin sauke numfashi mai matuƙar wahala ya ce,
"Bilal ka taimaka min a ɗaura aure na da Suhailah gobe mu haɗu a kano,Bilal ina jina kamar zan mutu a yanzu haka ka taimaka min ban san ya zan yi ba."
Wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo masa,cikin dakiya ya ƙanƙame wayar yana labartawa Bilal haɗuwar shi da Mommy,shiru Bilal ya yi kafin daga baya ya ce,
"Abdul na riga da na jima da sanin babu wata mace a cikin zuciyar ka da ta samu babban matsayi bayan mahaifiyar ka da ta wuce Hadiza,ko da sihiri ko babu sihiri Hadizar dai kake so, Alhamdulillah yanzu Hadiza ta gyara abinda ta ɓata,amma ina so in faɗa maka dik maitar ta sai Suhailah ta tare a gidan ta kafin ta samu abinda take nema a wajen ka,yanzu ka jira ina zuwa zan aiko Sultan ya kawo maka abinda zaka sha ka samu sassauci,Allah ya ƙara baka lafiya, congratulations aboki na,Allah yasa a daren ku na farko Amir ya samu ƙani ko ƙanwa."
Murmushi Abdul ya yi,sannan ya ce,
"Yanzu baka ji haushi na ba Bilal akan abinda na faɗa maka game da Hadiza? Na zaci za ka yi fushi kace kun fasa bani Suhailah shi yasa tin ɗazu na kasa kiran ka."
"Inaaa ai Suhailah da ka gani tana da ilimin addini,kuma alhamdulillahi tana aiki da shi sosai,sannan babu wanda be san labarin Hadiza ba a gidan mu,muna da yaƙinin ko bajima ko ba dad'e idan zama be ƙare ba a tsakanin ku zata dawo ɗakin ta....."
Cikin sauri Abdul ya katse Bilal da cewa,
"Tabbas na sani har yanzu ina son Hadiza,ina kuma tsananin ƙaunar ta,sannan ina son kasancewa da ita musamman a yau da ta zama silar warakata,amma Bilal har abada na haramtawa kaina Hadiza,maganar aure babu ita a tsakanin mu har abada."
Murmushi Bilal kawai ya yi,sannan ya ce,
"To Allah ya zaɓa abinda yake shine mafi alkhairi a tsakanin ku,yanzu bari na aiko Sultan ɗin ko har ka ji sauƙi?"
"Ina fa na ji sauƙi,ni dai dan Allah kar ka sanar dashi halin da nake ciki,shegen surutu ne da yaron nan,sai ya kasa ni a faranti a gidan nan kowa ya ɗauka."
Dariya suka yi kafin Bilal ya kashe waya ya kira Sultan, bayan sun gaisa ne ya sanar dashi dik abubuwan da yake so ya siyo ya kaiwa Abdul a gidan shi.
Bayan wasu awanni Sultan ya isa gidan Abdul da lemon tsami da na zaƙi,har da jar kanwa,shi dai mamakin abinda Abdul zai yi dasu ya sanya shi ƙin tafiya bayan ya bada aiken,hira ya hau yiwa Abdul dake ta tsiyayar da zufa duk sanyin fankar dake kaɗawa a parlourn,ƙarshe da ya gaji da surutun Sultan sai ya kora shi ya rufe gidan shi,daga nan ya wuce kitchen ya haɗa lemon tsami da na zaƙi ya matse a waje ɗaya dan ya ji dad'in sha, gefe ɗaya kuma kanwa ya jiƙa daban ya kafa kai ya shanye ta tas,yana gama sha ya ɗauki cup ɗin da ya matse lemon nan ya shanye shi shima. Ɗaki ya koma ya cire kayan shi ya ɗaura towel ya faɗa wanka,sai da ya jima yana wanka da ruwa mai sanyi kafin ya fito cike da kwanciyar hankali a tattare da shi,a hankali ya furta,
"Alhamdulillah ! Allah na gode maka da ka fitar dani daga wannan musibar da na afka,Allah na gode maka da ka bani ikon tsare dokokin ka ban afkawa zinar da matasa ke yi da hannayen su ba domin biyawa kawunan su buƙata,lallai Allah kaine ke shiryar da dik wanda ka so,Allah ka ƙara shiryar dani,dole ne na gujewa haɗuwa da Hadiza idan ina so na zauna lafiya,idan ta kama ma na bar garin nan ne a gobe bari shi zan yi tinda na wadata su da duk abinda suke buƙata na biki."
A gida ya yi sallar la'asar ya samu waje ya kwanta yana hutawa,bacci ne mai daɗi ya ɗauke shi a wajen har Sultan ya kawo masa abinci be sani ba.
Ta ɓangaren Mommy kuwa tinda ta isa gida ta sauya tunani akan sake auren Abdussaboor,ta sanyawa ranta ko soyayyar shi zata yi ajalin ta gwanda ta bar duniyar da ta sake auren shi. Jikin ta babu kuzari sam haka ta dinga aikace-aikace a gidan,tana gama girkin dare ta yi wanka ta shige ɗakin ta,Sule ta roƙa ya kula da Innoh dan bata da ƙarfin ɗaukar jikin ta ma balle ta ɗaga Innoh.
Da daddare Ɗan Liti ya dawo musu da karas me yawa ya sa Sadeeq ya wanke aka raba aka baiwa kowa nashi,kallon karas ɗin ta dinga yi tana tina yanda Abdul ke yaba miyar ta idan ta yanka masa karas a ciki ya naɗi kayan ƙamshi da ɗanɗano a jikin shi,murmushi tayi mai ciwo ta sa hannu ta share hawayen da ya zuba a kuncin ta,cikin sassanyar murya ta ce,
"Na haƙura da kai Abdussaboor Allah ya baku zaman lafiya da sabuwar amaryar ka,na barwa Allah komai ya yi min zaɓin alkhairi a rayuwa ta,haka ƙaddarar mu ta zo dole ne mu rungume ta,na san ka dena so na,dan haka nima dole na baiwa zuciya ta haƙuri akan ka."
Kuka ne ya ci ƙarfin ta ta kwantar da kanta a saman pillow ta dinga rera shi a hankali. Sallamar Sadeeq ce ta tashe ta babu shiri tana share hawayen ta,cikin mutuwar jiki ya miƙa mata wayar shi ya ce,
"Yah Saddiqa ce take son ku gaisa,wai ta kirawo ki bata samu ba."
Nan take ta tina yau gaba ɗaya bata saka wayar ta a caji ba,waje ta samu ta zauna da kyau kafin ta karb'i wayar,sai da ta daidaita muryar ta sannan ta amsa sallamar Saddiqa,shiru Saddiqa ta yi kafin ta ce,
'Yah Mommy lafiya kike kuwa na ji muryar ki haka? Ko kina damuwa ne akan rashin lafiyar Innoh?'
Wasu zafafan hawaye ne suka soma tsere daga idanun Mommy zuwa kuncin ta,cikin rawar murya da fashewa da kuka ta ce,
"Na cuci kaina da kaina Saddiqa, ina son Abdul son da ban taɓa yiwa wani namiji ba a duniya,na zalince ki na samu soyayyar shi ta hanyar sihiri a baya,gashi yanzu ko kallo ban ishe shi ba,ba nice a gaban shi ba Saddiqa aure zai yi da ƙanwar Bilal a cikin satin nan."
Kukan da Mommy ke yi har tsakar gida ana ji,bata damu da wanda zai ji ta ba babban burin ta shine ta cire damuwar dake danƙare da zuciyar ta a wannan lokacin. Cike da tausayawa Saddiqa ta ce,
'Yah Mommy dan Allah calm down ok? Tin farko Allah bai nufa Abdul zai zama mijina ba,Yah Munir shine zaɓi na,kuma alhamdulillahi na aure shi ina zaune lafiya da ni da shi da iyayen shi,kinga kenan u don't owe me any apology,Allah ya nufa kece zaki zama uwar ɗan shi tilo Amir,dan haka ki kwantar da hankalin ki,zan ci gaba da taya ki addu'a Allah ya yi maki zaɓin alkhairi.'
"A yau na sake tabbatar da ana gadon kyakkyawan hali,domin kuwa Saddiqa kin yi gadon hali me kyau a wajen Yadiko,Allah ya yi miki albarka ya jiƙan Yadiko,ina son ki ƙanwata kin sa baƙin cikin dake danƙare a raina ya ragu sosai,sai nake ji na kamar na sauke wani ƙaton dutse da ya danne zuciya ta."
Murmushi Saddiqa ta yi sannan ta ce,
'Ga ɗan ki nan ya fara iya surutu,amma fa ba a gane abinda yake cewa sai dai ya cika mana kunne da ihu.'
"Ina Baban nawa yake? Bani shi mu gaisa."
Hira Mommy ta dinga yiwa yaron kamar yana ganewa kafin daga baya suyi sallama da ƙanwar tata da take jin ƙaunar ta na ratsa ko ina na jikin ta. Murmushi tayi da ta tina Ameerah,da ita ta sanarwa halin da take ciki balbale ta zata yi da masifa sannan ta cusawa Abdul ashar har sai zuciyar ta ta yi sanyi,dariya ta saki tana jin ƙaunar ƙannen nata a ranta.
Sadeeq ne ya sake yin sallama ya karb'i wayar shi ya fita,Hadiza na nan kwance tana tinani Ɗan Liti ya aika kiran ta, Sadeeq na shiga ɗakin ta sakar masa murmushi ta ce,
"Ƙani na ko dai hira kake so mu yi da kai ne yau?"
Murmushi ya sakar mata cike da sakin jikin shi da ita ya ce,
"Zan so hakan Yah Mommy,amma Baba ya riga ni,shi yace na kira masa ke yanzu haka."
"Ok to next time zan gayyace ka hira,amma fita zamu yi mu zaga garin Ba Mugu a ƙafa mu sha iskar maraice da kai,ka amince?"
Cike da murna Sadeeq ya ce,
"Na amince Yah Mommy."
Tashi tayi ta maida doguwar rigar da ta sanya da rana ta nufi ɗakin Innoh,tana shiga ta tarar da Innoh a tsaye da ƙafafun ta tana takawa daga farkon bangon ɗakin zuwa bakin ƙofa,dariya suke ta yi ita da Ɗan Liti suna hira gwanin ban sha'awa,rungume Innoh Mommy ta yi ta ce,
"Alhamdulillah Innoh yaushe kika fara takawa ke kaɗai ban sani ba? Baaba ! Baaba zo ki ga ikon Allah !"
Cikin abinda bai kai minti uku ba Baaba ta bayyana a ɗakin,murna kowa ya hau yi saboda ganin Innoh na takawa da kanta,Sule ma dake waya da yarinyar da yake so ya aura sai da ya katse ya kutsa d'akin dan ganin abinda ake yiwa murna,yana yin arba da Innoh na takawa sai ya hau murna shima, a hankali Innoh ta samu gefen gadon ta ta zauna,cikin tsananin farin ciki ta kalli Baaba dake kukan murna ta ce,
"Yaya mai zuciyar zinare kenan,dik ɗawainiya da kulawar da kike yi dani ina gani kuma ina ji,me yasa Yaya kika ci gaba da kula dani bayan kin san yanda na tsane ki nake yi maki rashin kunya?"
"To yanzu ba gashi kin warke ba mu ɗora daga inda muka tsaya? Innoh idan babu tsiwar ki a gidannan ai gidan ba zai yi armashi ba,ranar da kika faɗa cikin wannan mawuyacin halin kasa bacci nayi...."
Kuka ne ya ci ƙarfin Baaba,Ɗan Liti ne ya ce,
"Dan Allah ku dena koke-koken nan haka,mu godewa Allah da sauƙi ya samu."
Innoh ce ta share hawayen ta tace,
"Na gode Yaya,na gode wa duk wanda ya bani gudummawar kulawa har Allah ya bani lafiya,Mommy Allah ya yi miki albarka ya baki miji na gari,ban taɓa zaton zan tashi ba,na yanke tsammanin ba zan sake moruwa ba koda na rayu,Mommy ina son ki samu farin ciki mai ɗorewa a rayuwar ki,Allah yasa idan kin samu miji anan gaba ya zama mijin ki har a aljannah,Yaya ki gafarce ni,daga yau ba zan sake yi maki musu ba, balle har in faɗa maki baƙar magana."
Ranar a ɗakin Innoh aka dasa hirar dare har sai da kowa ya fara jin bacci sannan suka barta ta kwanta itama dan ta huta.
Washegari da sassafe Abdul ya bar ƙauyen Ba Mugu ba tare da sanin kowa ba,tinda ya tafi zuciyar shi ke ganin kamar ya baro wani abu mai mahimmanci a can,a haka ya daure ya koma bakin aikin shi dan ya ɗebe wa kanshi kewa da yawan tinani. Yana cikin wannan yanayin kwanakin ɗaurin auren shi da Suhailah suka gabato, Sultan da dangin mahaifin shi da za su tafi garin Bauchi dan ɗaurin auren su Abdul, tin da asubar fari suka baro ƙauyen Ba Mugu suka shiga Kano,a cikin motoci uku suka tafi garin Bauchin Yakubu.
Suna isa Bilal ya tare su ya kai su masaukin baƙin da aka tanada domin su. Gaba ɗaya tunanin Abdul ya tattara ya koma ranar ɗaurin auren shi da Hadiza da aka ɗaura a fadar mahaifin shi ba tare da an shiryawa hakan ba. A hankali ya tambayi kanshi,
"Shin me yasa nake tuna aure na da Hadiza kamar ita kaɗai ce matar da na taɓa aura a duniya?"
Zuciyar shi ce ta bashi amsa da,
'Saboda har yanzu Hadiza kaɗai ka ke so,itace macen da kayi rayuwar soyayya da nishad'i da ita.'
Lumshe idanun shi ya yi tare da lafewa a kan gado,ya ce,
"Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir."
Tinda ya yi wannan addu'ar sai ya samu natsuwar zuciya,ya tattara dikkan lamuran shi ya miƙa su zuwa ga Allah,dan ya san hakan shine kawai mafita a cikin halin da yake ciki.
Washegari da safe da bidirin ɗaurin auren Suhailah da Abdussaboor aka tashi a garin Bauchi a unguwar dumi. Ango da ƙanin ango tare da babban abokin ango kuma yayan amarya sun sha shadda fara tasss mai farin aiki a jiki,hatta da hulunan da suka sanya iri ɗaya ne, Maestro cinematography suka ɗakko yake ta aikin ɗaukan su videon ɗaurin aure,inda bayan an ɗaura aure suna da walima da za a gudanar,wanda duk shi suke son ya ɗaukar masu video da hotunan auren nasu. A wajen Suhailah suka samu labarin shi dan kuwa shi ya yi aikin Video ɗin bikin aminiyar ta dake Yola,videos ɗin da pictures ɗin sun fito fess kamar an saka a computer tsabar haɗuwa,shi yasa itama ta yi booking ɗin shi ta biya masa kud'in mota ya isa har garin bauchin dan ya gwangwaje nasu auren da basirar shi......
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 106:
Da misalin ƙarfe biyu na dare Abdussaboor ne ya sauka daga saman gado fuskar shi na ɗauke da wani irin murmushi mai ƙayatarwa. Farin cikin da ya tsinci kanshi a ciki a wannan dare ba zai taɓa misaltuwa ba,bai taɓa zaton zai samu lafiya cikakkiya ba bayan abinda ya faru da shi a baya,juyawa ya yi a hankali yana kallon yanda Suhailah ta dunƙule waje ɗaya tana bacci,har a wannan lokacin ajiyar zuciya take saukewa. A hankali ya tashi daga gadon ya taka zuwa bathroom,alwala ya yi sannan ya yi wanka ya sake yin brush ya fito.
Sai da ya shafa mai sannan ya fesa turarukan shi masu tsananin ƙamshi da tsada sannan ya sanya farar jallabiya da dogon wandon ta a jikin shi,carpet ɗin sallah ya shimfiɗa a ƙasa tare da tada sallah dan godewa Allah akan ni'imomin da ya azurta shi da su da ba zai iya lissafawa ba. Suhailah kuwa na ganin ya tada sallah ta miƙe a hankali ta taka da ƙyar ta shige band'aki,ruwa ta tara a kwamin wanka sannan ta shiga ta gasa jikin ta da kyau,duk yanda taso ta ji haushin Abdussabour kasawa ta yi,ƙarshe ma samun kanta tayi tana sakin murmushin jin daɗi dik da baƙar wuyar da ta sha a hannun sa. Ashe ba zaman haƙuri zata yi a gidan miji ba kamar yanda ake ta bata haƙuri? Ashe ya ji sauƙi shine bai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 66 Chapter of 70