Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Abuja da zama saboda ya b'atar da sawu kafin qura ta lafa ya sake shigowa kano ko kuma wani garin da ya tara mata irin su Mommy ya kwasa ya je turai ya siyar ya samu 'yan can jin shi, dan haka rayuwa yake yi ta kashin kuɗi da dukiya gaba ɗaya ya manta da wata Hajiya K'waisa da Mommy da tarkacen su. Billy kuwa tinda ta dawo daga yawon ta da ta samo miliyoyin ta ta yi shirin komawa qauyen Ba Mugu dan kuwa a cewar ta Mommy ta buɗe musu hanyar nuna arziqin su ba tare da fargaba ba, a daren ranar da zata tafi sai da suka kai ruwa rana da Samuel yana yi mata masifa akan kar ta sake duk bala'in da qawarta ta shiga su nuna K'waisan alheri a matsayin wadda ta zama silar shigar su damuwa duba da cewa har yau ba a sami labarin inda Mommy ta shiga ba. Itama cikin rashin kunya da masifa tace masa, "Shi ɗan bariki dama yana da wanda zai riqe a matsayin wanda ya ingiza shi? Ai dik wanda ya yarda ya baro gida shi ya so, dan haka ka dena buɗe min ido kana zare min su kamar wani ubana," Da kyar Hajiya K'waisa da ke cikin jimami da alhinin rashin Mommy na kusan wata guda ta raba faɗan. Lokacin da Billy ta isa qauyen nasu ita da saurayin ta da ya kaita a rantsattsiyar motar shi yara da manya ba abinda suke yi banda bin motar da kallo, manyan dake zaune qasan bishiya suna shan dumi a garwashin da almajirai suka bari na ragowar wutar karatun dare sai miqewa suke yi daga tsugunnon da sukai suna leqa motar su dawo suna faɗin, "Ai kamar yarinyar nan ce Bilkisu 'yar gidan mai dusa,kalli wata iriyar sutura a jikin ta, yarinya sai kace anniya, a gaskiya Mai dusa be godewa Allah ba akan ni'imar da yayi masa, yana ɗaya daga cikin masu kuɗin garin nan amma wai ya bar 'yar cikin shi tafiya birni aikatau, ka duba ka ga yarinya ta isa haifar yara biyar tana yawo a titi tib'i-tib'i tsirara, yo tsirara mana ai wannan kayan na jikin ta da su da babu duk ɗaya ne meye ba a gani ba anan?" "Babu kam, jibi wani uban gashin doki da ta saka yana reto har a saman mazaunan ta, kaiii subhanallahi Allah ka kiyashe mu aikin tab'ewa," "Ameeen ya Allah kai dai, yanzu ina ce 'yar ka Sarai shekaran jiyan nan ta haihu? Ba qanwar bayan ta bace? Itama da ta zauna ta fitar da miji an aurar da ita haka zata faru ne?" "Ina fa," Haka suka ci gaba da hira har Billy ta gama ɗaukan kayan da zata iya ɗauka yara suka taya ta tashigar da sauran ciki, sake dawowa tayi dan tayi sallama da saurayin ta, cikin motar shi mai baqin gilashi suka shige ta zauna a jikin shi suna watsewar su, wani daga cikin dattijan nan ne ya leqa ta gaban motar dai-dai inda babu baqin gilashin ya hango Billy na sauka daga jikin matashin suna raba bakin su da suka haɗe tin shigar ta motar, wani irin salati ya ja ya dafe qirji ya na nuna wa sauran, kafin su gani Billy ta fito tana d'agawa saurayin ta hannu ya bar qofar gidan, juyawa tayi suka yi ido biyu da dattijan da ta ga sanda tsohon nan ya leqa ya ga me suke yi, cikin wani irin taku tana rausaya jikin ta ta isa gaban su ta durqusa kaɗan ta gaishe su. Kaɗan daga cikin su ne suka amsa, sauran kuwa banda harara da surutan kar ta zo ta lalata musu tarbiyyar yara ba abinda suke yi,murmushi tayi ta miqe zata tafi ta ɗan karkace ta buɗe jakar ta ta zaro dubu goma ta miqa musu tace, "Gashi a sanya mana albarka a kuma taya mu addu'a Allah ya shirye mu, shi d'a na kowa ne, idan kaga ɗan wani ya lalace ba aibata shi ya kamata ka yi ba addu'ar shiriya ya kamata kayi masa gudun kar kazo kana aibata na wani naka na can ya fi wannan da kake aibantawar lalacewa baka sani ba," Tana gama faɗa musu haka ta tafi ta bar su a wajen suna rabon kuɗi n da ta basu cike da zalama,tinda ta miqa kuɗin dama masu zagin nata suka yi shiru ba wanda ya sake cewa qala, a haka ta shige gidan su da ake ta murnar dawowar ta. Ko minti goma sha biyar da komawa gidan bata yi ba aka dinga doka sallama kamar za a d'aga kwanon da aka rufe soron gidan nasu dashi.............. [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 30: Innoh ce ta qarasa shiga gidan tana ci gaba da banka sallama,Mahaifiyar Billy ce ta fito daga d'akin Billyn bakin ta a washe kamar gonar audiga tana faɗin, "Lale maraba lale da qawata aminiya ta,irin wannan sallama haka kamar an koro ki? To bismillah shigo," "Ai dole ki ganni da tsakar ranar nan Saude ina banka sallama, ina can zaune na kwashe alale an fita da ita naji labarin 'yata ta dawo nace banga ta zama ba se na zo na ji labarin Mommiyata," Billy ce ta fito d'aure da towel a jikin ta da wata jaka me kyau da ke ɗauke da kayan wankan ta, ba tare da ta kula su Innoh ba ta k'wala wa qanin ta kira tana tambayar shi ya kai mata ruwan wankan? Ya bata ansa da eh ya kai, a sannan ne ta kalli Innoh taga yanda take binta da kallon burgewa, sake gyara jikin ta tayi da kyau tana murmushi tace, "Innohn mu barka da war haka, ya gida ya su Ameerah da Baba?" Cikin washe baki Innoh tace, "Kowa na nan lafiya qlou Bilkisu, ina kika baro min mommyna uwar masu gidaaaa?" Murmushi Billy ta sake yi sannan tace, "Tana nan lafiya qlou alhamdulillahi, ai tana ta cewa a gaishe ku aiki yayi mata yawa da tini da ita za a zo ma ai,amma ta bada saqo na baki kafin ta iso, bani minti goma na watsa ruwa na zo," "Na baki arba'in ma idan zai ishe ki, a fito lafiya," 'Masu shegen son abin duniyar tsiya tinda nake ban taɓa ganin tazo gidan nan ba idan ba haihuwa akai ba se gaisuwar rasuwsr Yabi amma jibe ta yanzu ta bugo qafafu kamar babur ɗin mijin ta ta zo yi min sannu da zuwa, ji yanda jikin ta ke rawa saboda tsabar kwad'ayi,' Billy ta ayyana a ranta a lokacin da take wucewa bandaki domin ta yi wanka,Innoh na nan na sharhi akan al'amuran yau da gobe Billy ta gama shiri ta fito mata da wata atampa da leshi sai takalmi ta ɗora mata dubu goma tace na ɗinki ne wai inji mommy,murna Innoh ta dinga yi tana sanya musu albarka tare da fatan su fi haka arziqi, ba jimawa kuwa ta yi musu sallama ta tafi tinda ta karb'i abinda ya kai ta. ****************************** Abdul, Bilal da Mommy sun samu nasarar dawowa gida Nigeria lafiya ba tare da wata tangard'a ba, a gidan su Abdul ɗin mommy take zaune wanda zama da su ya sanyawa Mommy tsoron Allah duba da yanda suke gudanar da rayuwar su daga aiki sai ibada, sai su ci abinci da dukiyar da Allah ya wadata su da ita ta hanyar halal, sai kuma taimakon marasa shi da suke yawan yi. Koda dai ba wani natsuwa take yi ba a wajen yin sallah yanzu tana samu ta yi su guda biyar ɗin a kan lokacin ta ba tare da an ce tashi ki yi sallah ba, a hankali Bilal ya gane wasu daga halayyar ta na rashin son ibada da son abun duniya amma sam Abdul be gane ba, dik sanda kuma Bilal zai yi masa bayani sai ya nuna masa cewar waye baya son abun duniya dama? Sannan ita mace dama tana da rauni yana daga cikin raunin ta wasa da ibada, amma idan aka tsaya akan ta aka dage da yi mata nasiha zata dena ne ta kama Allah da kyau ta yanda zata bawa wasu tarbiyya itama,da haka Abdul ke kashe bakin Bilal da be gama yarda da Mommy ba. Tinda suka dawo ya ɗauke ta suka je shopping ya sai mata dogayen riguna irin na larabawan nan, ai kuwa Mommy ta yi murna da farin ciki sosai dik da cewa ta so k'warai ya barta ta ci gaba da sanya kayan shi, hakan na sanya ta nishad'i da jin wata iriyar shaquwa ta musamman na shigar ta game da shi, abinda take ji akan Abdul bata taɓa jin shi a kan wani namiji ba,yanda yake lelenta kamar k'wai ta gane tsantsar soyayyar da yake yi mata ba ta wasa bace,wanda lokuta da dama hakan na tada hankalin ta, tana tsoron ranar da zai gano ba itace Saddeqa ba kar ya juya mata baya. Tana girmama shi itama sosai kamar yanda yake yi mata, tana ganin mutunci da qimar shi, sannan tana kunyar shi, ga wani irin yanayi na musamman da take tsintar kan ta a game da shi a duk sanda yake yi mata magana cikin natsuwar shi da kamewar shi. Zaune take a d'akin da suka sauke ta tin dawowar su tana shan chocolate ɗin da ya siyo mata tana ta tunani a ranta, sallamar shi taji tare da k'wank'wasa qofar d'akin nata, cikin sauri ta miqe ta isa bakin qofa ta buɗe masa tare da gaishe shi, haɗe fuska yayi kaɗan yana yi mata kallon nan nashi dake tsunduma ta a kogin qaunar shi a kullum,cikin muryar shi ta cikakkun mazaje masu cikar zati da haiba yace mata, "Saddeqah ba na ce maki ki dinga sanya mayafi ba a dik sanda kika ji ɗaya daga cikin mu? Kar ki manta ba muharraman juna bane mu,sannan mu ɗin 'yan Adam ne masu rauni, Allah yayi haramci da kusantar zina bama aikata ta ba, ah ah kusanci da ita ma an haramta, to ki yi tunanin ya wanda ya aikata ta ko yake aikata ta zai fuskanci hukunci a wajen Allah akan qetare iyakar Allah? Ki qara hakuri na san kin matsu ki koma gida wajen iyayen ki, gashi kun kusan yin sauka ma ko? Dan an gayyace ni bikin saukar taku,dan haka kar ki damu ba zamu wuce sati ɗaya ba  zamu gama abinda muke yi na samu hutu sai mu tafi gida tare,idan kuma kin gaji kina so ki tafi ba tare da an yi bincike akan wanda ya sace ki ba to zan iya baki kuɗin mota ki tafi," Cikin tsananin jin kunya tare da danasanin fitowa yawon karuwanci Mommy ta sunkuyar da kanta hawaye na zuba a idanun ta,ta ina zata fara sanar da shi kafin a kai ga sace ta sai da ta fito yawon karuwanci da kan ta? Ta ina zata sanar da shi nasihar da yake yi mata kullum akan zina ta sha aikatawa? Idan yasan rayuwar ta ta baya ya zai ji ? Shin zai qaunace ta kamar yanda take qaunar shi ko zai tsaneta ne? Ya zai ji a lokacin da ya gano ita ɗin ba Saddeqa bace? Hannun shi ya sanya a gaban fuskar ta yana kad'awa dan ya jawo hankalin ta, da sauri kuwa ta fito daga duniyar tunanin da ta afka tace, "Ka yi hakuri zan kiyaye, ina da yawan mantuwa ne," "Yawan mantuwa ko kuma kina sane, so kike ki ja ra'ayin ɗayan mu mu yi aika-aika Allah ya yi mana luguden azaba to ta Allah ba taki ba in shaa Allahu mata tace zata fara b'are ni a leda," Abdul ne ya juya ya kalli Bilal dake zayyano zance kamar wanda ke jin haushin Mommy, ba tare da ya kula su ba ya amshe makullin motar Abdul ya bar gidan yana mita akan ya kamata Abdul yayi ya ɗauke musu Mommy a gida, yarinya me qira kamar lamba takwas za a ajiye musu a gida a matsayin su na mazaje lafiyayyu? A gaskiya ana cutar shi kuma ta Allah ba tasu ba ba me sashi aikata ba dai-dai ba se yayi aure, murmushi kawai Abdul yayi sannan ya sanya hannu a aljihu ya dakko dubu uku ya bawa Mommy yace, "Ga wannan koda zaki sai abinda zaki ci idan baki son abubuwan dake cikin gida,bari mu je sai mun dawo da yamma ko?" D'aga masa kai Mommy tayi tare da faɗin, "Allah ya kiyaye ya bada nasara da sa'a," Yaji daɗin addu'ar ta sosai dan haka sai ya yi murmushi ya furta, "Ameeen" Sannan ya fita ya ja mata qofar ya rufe, a mota ya tadda Bilal nata mita amma be kula shi ba saboda ya tafi duniyar tunanin yanda zai gabatar da Mommy a wajen iyayen shi, dan kuwa da dikkan alamu har yanzu ba a farga cewa Saddeqa ta b'ata ba tinda Sultan na sanar da shi cewar tana nan lafiya, wataqila suna yin haka ne dan a kwantar masa da hankali,shi kuwa sai biye musu yake yi har kuɗi yake aikawa a sai mata abu a kai mata. A can gidan kuwa suna fita Mommy ta shirya ta sanya facemask kamar yanda ta saba a baya, ta nad'e kanta da mayafin rantsattsiyar abayar da ta sanya ta saka takalmi ta ɗauki wayar ta da kuɗin da Abdul ya bata ta rufe musu gidan ta taka da qafarta zuwa bakin titi, adaidaita sahu ta shiga tayi masa kwatancen inda zai kai ta,zuciyar ta ke tsananin bugawa saboda tsoron abinda zai je ya zo. Suna tsayawa a qofar katafaren gidan da ta kira da gidan 'yan wuta a yanzu ta fita ta cewa me daidaitan ya jira ta zai maida ita inda ya dauko ta. Sai da ta buɗe facemask ɗin ta mai gadi ya gane ta sannan ya wangale mata qofar gidan yana murnar ganin ta tare da sanar da ita Hajiyan na ciki ita da Babyn ta, murmushi ta yi masa sannan ta yi godiya tace kar ya rufe qofar yanzun nan zata fito gaisawa kawai za su yi, sai ta shiga hantar cikin ta na kad'awa, a hankali ta hau buga qofar gidan tana jiran a buɗe mata, ba jimawa kuwa Sallau ya buɗe qofar yana yi mata kallon sani, buɗe facemask ɗin ta tayi ya gan ta ya kuwa buga salati tare da faɗin, "Habaa ni fa in ce kamar na san me irin wannan shigar,ke kuwa ina kika shiga haka Hajiya duk ta damu bata da zance sai naki?" "Za ka buɗe wa baqon da aka yi qofa ya shigo ko sai ka gama tsegumin naka ya tsohon kwarto?" Da sauri Sallau ya bar jikin qofar Mommy ta bayyana a cikin gidan, cikin hanzari Hajiya K'waisa da Samuel suka qarasa sakkowa daga bene suka nufi wajen mommy za su rungumeta mommy kuwa tayi saurin ja da baya tana kallon su ɗaya bayan ɗaya tana zabga musu harara, kallon juna Samuel da Hajiya K'waisa suka yi sannan suka kyab'e baki tare da maida kallon su kan mommy suna kallon ta da alamun tambaya a tattare da su,cikin ɓacin rai Mommy tace, "Banzo wajen nan dan kuyi murna da dawowa ta ba,na zo wajen nan ne dan in sanar da ku na dawo qasata Nigeria lafiya ba tabo ba nakasa idan ma abinda yasa kuka haɗa baki da Alhaji kenan kuka siyar dani wajen baturen da ya dinga haiqe min kamar ya samu katifa,to Allah ya isa tsakani na da ku inshaa Allahu sai kun yi mutuwar wulaqanci, na so na haɗa ku da hukuma amma na san babu abinda za a iya yi min saboda kun fini kuɗi, kuna tare da masu mulki dan haka baza ku tab'u ba,dan....." Cikin tsawa da harare-harare Hajiya K'waisa tace, "Ke qaramar 'yar balaja'u ya haka? Ya haka ana murna kin dawo lafiya ki hau ja min doguwa har da maganar siyarwa da hukuma? Idan ma wani abune ya faru ai zama ya kamata muyi a tattauna akai ko? Haka kawai se ki zo ki hau ja min doguwa salon nafi haka shiga duniya? Me ya faru? Ina kika shiga aka dinga neman ki babu waya babu saqo babu ɗan aike?" Mommy kallon su ta tsaya yi a sheqe dan kuwa ta tabbata rainin hankali ne kawai irin na 'yan daudu za ayi mata,cikin hasala tace, "Ya kake magana kamar baka san abinda kuka yi min ba? Da fari ka nuna baka san Alhaji ba ashe bakin ku ɗaya,kun haɗa baki an d'auke ni daga Uganda an siyar a New York wajen bature,to ina roqon Allah yanda ya yi min Allah ya kawo me yi miki irin haka ki ji idan da daɗi," "Tuf Allahumma ba amin ba dan ban san uwar da aka yi miki ba har ya jawo zage-zagen nan da tsinuwa, kai ka ji min 'yar iskar yarinya se jafa'i take jawo min daga taimako? Alhaji dai yanda kika ganshi haka na gan shi haɗuwar social media ne ban san sana'ar shi ba ban san ɗan wanne gari bane, da na san waye shi an faɗa maki da ban nemo ki ba da kaina? Kar fa ki manta ke ɗin tanadin Sanata ce e fa, qarshen shekarar nan za...." "Aiko se dai ki bawa Sanatan uwar ki amma ba ni ba shege gardin banza ɗan asara, Allah ya isa tsinanne kwanan nan zan koma garin mu dani da bawan Allahn da ya kub'utar dani daga sharrin ku, kuma inshaa Allahu shine zai zama miji na na bi Allah na tuba na dena wannan rayuwar ta dabbobi kuma Allah ya shirya ku idan kuna da rabo idan babu kuma Allah ya sa ku wulaqanta matsiya...." Wani irin naushi Samuel ya kai wa bakin mommy sai da jini yayi tsartuwa, K'waisa na gefe tana, "Saɓa min kamannin matsiyaciya, ina ganin ki kamar za a more ki ashe kwalluwar shegiya ce ke? Kama bakin ka yi ta duka sai haqoran ta sun zube a qasa babu kuma abinda za a yi," Kukan kura Mommy tayi ta damqi tozon wuyan Samuel kamar wata zombi ta gartsa masa cizo duk yanda Hajiya K'waisa taso karb'ar babyn ta a hannun Mommy kasawa tayi, banda ihu babu abinda Samuel keyi, mommy na sakin shi ta damqi hannun K'waisa shima ta kafa haqoranta Samuel na ganin haka ya haye saman bene da uban gudu yana ihun a cece shi mayya zata shanye musu jini. Dik abinnan da ake yi akan idon su Ruby ake yin shi,yau ce rana ta farko da Zubaida ta yi dariya a gidan tin da aka kawo ta aiki,ta ji daɗi sosai da Mommy ta bar harkar karuwanci fatan ta Allah ya shirya K'waisa dan kuwa yana da taimako da jin tausayin talaka, amma kuma an sadaukar da rayuwa wajen saɓawa Allah. Hajiya K'waisa bata gama dawowa hayyacin ta ba daga zafin da ke ratsa hannun ta ta ji mommy ta damqi kunnen ta ta gatsa masa cizo, ihu ya k'walla yana tsinewa Samuel da ya gudu d'akin su, jin ihun Hajiya yaqi qarewa ne ya sanya Samuel d'akko wani dogon abun qarfe da suke zuba tokar sigari ya fito daga d'akin tare da kwararo ihu kamar mace zai sakko qasa, mommy na k'yalla ido ta hango shi tafe da makami sai ta saki K'waisa ta taka da gudu, Zubaida dake bakin qofa kuwa ta buɗe mata ta fita a guje, mai gadi na nan tsaye ya wangale qofa yana jiran komawar mommy suyi sallama ya ganta ta keto da gudu iska na kad'a rigar ta. Ganin ta a guje ne ya sanya shi fita daga gidan shima a saba'in, me adaidaita sahu na qoqarin tada ɗan sahun sa ya gudu mommy ta afka tana faɗin, "Taka wuta direba mu je !" Banda haki babu abinda take yi, yana samun nasarar kunna ɗan sahun sa suka danna a guje Samuel na kurin bin bayan ta a mota K'waisa dake dura masa ashar tace, "Sokon banza a gaban ka ta kafa min haqori zata kashe ni amma ka gudu shine yanzu za ka zo kana wani kurin banza," "Haba baby ki duba fa ki ga tozon wuyana yarinyar nan ta kama ta kafa masa haqori kamar ta samu goriba ta hau gaigaya, maza je ki shirya muje asibiti dan dole mu ga likita," Abu kamar wasa kuwa haka suka shirya suka yi asibiti, mommy kuwa na isa unguwar su Abdul ta sallami me adaidaita sahu, sai dai tana komawa ta ga gidan a buɗe, a tsorace ta furta. "Na shiga uku waye kuma a cikin gidan, dan lokacin tashin su daga aiki be yi ba?............."[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 31: Tsayawa tayi tana tunanin shin ta shiga ne ko ta gudu ta nemo taimako dan kuwa da dikkan alama b'arayi ne suka shiga gidan duba da cewa yanzu ba lokacin tashin su Abdul bane daga aiki, tana nan tsaye tana tunani taji an buɗe qofar a zafafe, Bilal ne ya leqo yana binta da wani irin mugun kallo yace, "Dalla malama idan zaki shigo ki shigo,idan bazaki shigo ba ki kama gaban ki," Mommy na jin haka ta fara tafiya zuwa cikin gidan kamar wadda ake tunkud'awa, tana shiga taga Abdussaboor zaune a saman kujera ya dafe kan shi da hannu biyu yana juya shi cikin wani irin yanayi mai ban tausayi, ba tare da ta san kalar laifin da ta aikata ba ta durqusa a gaban shi tana zubar da hawaye tace, "Yah Abdul dan Allah kayi...." "Tashi daga kusa da shi munafuka, dama ni jiki na ya bani akwai wata manaqisar da kike qullawa, ke ɗin ba mai gaskiya bace,zaki sanar da mu sunan ki da asalin ki ko se na dakko wayar cajin can na yi ta zane ki da ita?" A zafafe Bilal ke magana kamar zai shaqe Mommy, cikin in ina ta hau son tayin magana amma kalma ɗaya ta kasa fita daga bakin ta sai kuka da take yi kamar an aiko mata da labarin mutuwar Ɗan liti. A hankali Abdul ya zaro wayar shi ya cire ta a key ya miqawa Mommy ba tare da ya ce mata komai ba, Karb'a tayi hannun ta na mugun rawa kamar mazari ta hau duba hoton da aka tura masa ta WhatsApp,hoton Saddeqa ne tsaye ta duqar da kan ta tana murmushi tare da wani bafulatanin matashi kyakkyawa,wanda tana ganin shi ta gano kamannin shi da Baabaa da kuma baffan ta wato Alhaji Baban Gida,rubutun qasan ta karanta wanda aka rubuta.... 'Yayah wai dan Allah yaushe zaka zo ne? Yau kwana uku kenan da wannan guy ɗin yazo kullum shi yake kawo Gimbiyar garin Ba mugu makaranta a mota kuma shi yake zuwa ɗaukan ta, da dikkan alamu akwai soyayya da shaquwa a tsakanin su, ka yi sauri ka dawo kar ya riga ka fa!' Tana gama karantawa jikin ta ya qara ɗaukan rawa kukan ta ya qaru, Bilal ne ya karɓe wayar a hannun ta dan kuwa sauran qiris ta sake ta ta faɗi a qasa,cikin tsawa yace mata, "Wacece ke?" Shiru tayi ta qi magana ta ci gaba da kuka sosai kamar ana dukan ta,cikin sanyin murya da gajiya Abdul ya furta, "Wacece ke?" "Yah...Yah....Ab..Ab..Abdu..." "Bilal haɗa mana kayan mu muje gida please," Ba tare da Bilal ya sake cewa komai ba ya wuce cikin d'aki ya bar Mommy da Abdul a parlour, mommy na ta kirb'ar kuka Abdul na kwance a kujera ya kulle idanun shi yana jin yanda zazzaɓin da ya kama shi a lokaci ɗaya yake ragargazar qashi da b'argon jikin shi, ƙwaƙwalwa da zuciyar shi sai zogi suke yi mishi, be taɓa sanin yayi zurfi akan son yarinyar da yayi zaton Saddiqan shi bace sai yanzu da ya ji cewar ba ita bace,wani irin so mara misaltuwa Abdul yake yi wa Mommy wanda a yanzu tunanin yanda zai rayu rayuwa mai kyau da inganci yake yi idan babu ita a cikin tashi rayuwar. Yana nan zaune Bilal ya fito da akwati sannan ya wurga wa Mommy tarkacen kayan da suka siya mata a jaka ya zare mata ido tare da nuna mata qofar waje da hannun shi, ɗaukan jakar tayi ta tsaya taqi fita tana ci gaba da kukan ta, Abdul ne ya tashi zaune da k'yar tare da dafe kan shi da hannu ɗaya ya miqe, jiri ne ya ɗauke shi zai faɗi Mommy tayi saurin kai hannu zata tare shi Bilal ya riga ta, a tare suka sakar mata wani mugun kallon da ya sanya ta ɗaukar jakar ta ta fara yin hanyar waje, zuciyar ta zafi take yi mata sosai, ina

Chapter 21 of 70