Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ita duk abinda ke faruwa, sannan ta ce ta bata mijin nata ta roƙe shi ya barta tazo bikin dan kuwa ita ce uwar amarya,da ƙyar ya amince zai barta tazo tun ana sauran kwana biyu bikin. Da rana ta baiwa Sule ATM ɗin ta bayan ya dawo daga makaranta ya ciro kuɗi,ita da Abbe da Shalele suka shiga kasuwa suka fara siyayyar duk da suke da buƙata. Washegari da safe Ameerah tazo da Fadilah suka hau ɗaura alewa da cingam a leda suna baiwa yaran maƙota suna rabawa gida-gida,cikin ƙanƙanin lokaci gari ya ɗauka mutane suka shaida za a maida auren Hadiza da Abdussabour. A can gidan Sarki ma rabon alewar shagalin bikin Abdul ɗin suke tayi kamar wannan ne auren da ya taɓa yi a duniya. Sadeeq Mommy ta cikawa leda da alewa har da biscuits ta ce ya kaiwa dangin Yadiko dake ruga,dan kuwa sun ji labarin dawowar su,hakan da Mommy ta yi ya sa Sadeeq ya ji matuƙar daɗi a zuciyar shi. Cike da farin ciki ya karb'i kud'in machine ɗin da ta bashi ya tafi kai saƙon. Ameerah da mommy ne ke ta faɗa akan kai alewar gayyata gidan Malam,Mommy tace akai,Ameerah tace ba za su gayyaci iyalin boka sabgar su ba,da kyar Baaba ta shiga maganar Ameerah ta bari aka kai wa Tsahare alewar gayyata. Bayan Abdul ya koma gida da dare ya sanar da Suhailah yanda zaman su zai kasance da Mommy,fatan alkhairi ta yi musu baki ɗaya,dan kuwa ta gama ƙudirtawa a ranta ko nan gidan Mommy tace zata zauna matsawa zata yi ta bata fili,ita ba baƙuwar zafi bace,sai dai tsarin da mommy tazo dashi ya yi matuƙar burge ta itama. ***************************** Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce rana bata ƙarya,sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, ranar alhamis rana ce da mutanen ƙauyen Ba Mugu suka tashi cike da farin ciki,baƙi ne ko ta ina ke zuwa mutan gari an cika a ƙofar gidan Sarki,gidan Ɗan liti kuwa mata ne kawai ke kai komo a tsakanin su,saboda murnar walimar bikin Hadiza da Abdul. Da misalin ƙarfe biyu na rana iyalan Alhaji Baban Gida suka iso ƙauyen, Saddiqa na shiga gidan ta yi arba da ƙanwar Yadikon ta,a bakin ƙofar ta saki jakar ta ta isa gare ta da gudu ta rungume ta ta fashe da kukan farin ciki,sun jima a haka kafin su zauna ta fara gaishe da ɗangin mahaifiyar ta da suka cika gidan saboda kara da sukai wa Innoh. Sai da suka gama gaisawa sannan ta ɗauki jakar ta da Munir ya ajiye mata a gefen ta bayan ya gaishe da surukan nashi ya wuce zuwa ɗakin Baaba, direct ɗakin Innoh Saddiqa ta shiga suka gaisa ta yi mata Allah ya sanya alkhairi,da kallo Innoh ke bin jikin Saddiqa da ya gaji da haɗuwa ko ta ina,kama daga kan fatar ta har zuwa suturar dake jikin ta,jakar da take riƙe da ita ma abun kallo ce,nan take abubuwan da ta dinga yi mata na matsantawa da musgunawa suka dinga dawo mata a kan ta,ba tare da jin nauyi ko kunyar mutanen dake ciki ɗakin ba Innoh ta hau tsiyayar da hawaye ta riƙe hannun Saddiqa,kafin ta yi magana Saddiqa ta gane me zata ce,dan haka cikin sauri ta tari numfashin Innoh ta hanyar faɗin, "Allah ya jiƙan Yadikon Sule,na san kewar ta kike yi,ni kaina ina kewar ta,mu ci gaba da haƙuri sannan mu bita da addu'a,bari naje mu gaisa da Baaba." Kafin Innoh ta ce komai Saddiqa ta bar ɗakin,cikin zuciyar ta take jinjina karamci da mutunci irin na yarinyar,lallai yau ta tabbatar da ana gadon mugun hali ko kyakkyawan hali a wajen iyaye. Ta kuma tabbata Saddiqa ta yi gadon kyakkyawan hali a wajen mahaifiyar ta,fatan ta Allah ya yafe mata abubuwan da ta yi a baya,sannan ya ƙara haɗa kan iyalin su. Amarya na can gidan Alhaji Baban Gida da su Aunty Naja Abbe da Shalele da yaran su suna girkin abincin walima,sun share ko ina sun gyara saboda sun san masu gidan na nan tafe dan halartar bikin. Suna tsaka da zuba abinci a take away mai yiwa Mommy kwalliya tazo daga kano,wadda Abdul ne ya ɗauki nauyin hakan,hatta da kayan da zata sanya duk saida ya aiko mata su,banda lefen da aka kawo akwatina biyar kamar ba auren bazawara ba. Suna tsaka da kwalliya Saddiqa ta isa gidan,rungume juna suka yi da Mommy,ita da Ameerah kuwa sai suka yiwa juna murmushi kawai,tinda Ameerah take a duniya bata taɓa jin kunyar wani mahaluƙi ba sama da yanda take jin kunyar Munir,wannan dalilin ne ma yasa da taga ya shigo ɗakin tayi saurin kauda kai ta na yiwa yaron ta wasa,murmushi Munir ya yi bayan ya gaida Mommy ya cewa Ameerah, "Damisar gidan Baba Ɗan Liti ba magana?" Tura baki ta yi ta hau hararar shi tana ƙunshe dariyar ta,dariya kowa ya sanya musamman su Saddiqa da suka san asalin abinda ya sanya shi kiran ta da damisa. Bai wani jima ba ya yiwa Saddiqa alamar yana jin yuwa ta sama masa abinci,ɗakin su ya tafi ya rage kayan jikin shi ya kwanta. Babu jimawa Saddiqa ta shiga ɗakin ɗauke da babban faranti dake ɗauke da abinci da ruwa akai,ajiyewa tayi a saman table sannan ta ce masa, "Bismillah taho ka ci abinci,kaga yaron ka tinda muka zo be kula ni ba, yana can yana tarawa Ummina gajiya ko tausayin ta baya ji." Kallon ta Munir ya yi,yaga tana wani ƙyalli,cike da zolaya ya ce, "Ke zo nan,wai wannan ƙyallin goshin da naga kina yi na meye? Ba makaranta kika ce zaki yi ba?" "Uhumm makaranta nake yi mana me yasa ka faɗi haka?" "Ohh baki gane ba ko? To shikenan matso nan na yi maki bayani da kyau." Nan take ta gane me yake nufi,cikin sauri ta miƙe tsaye tana dariya ta ce, "Ni bani da komai,ka rufa min asiri dan Allah na kammala karatu na lafiya." Fita tayi ta barshi yana yi mata dariya,wanka ta shiga tayi a ɗakin baƙin da su Mommy ke zaune suna bidirin su,sai da ta fito sannan ta zauna aka tsara mata kwalliya itama,Ameerah kuwa duk yanda akai da ita ta bari a yi mata kwalliyar zamani ƙi tayi, tace hoda kawai ta ishe ta,bata son wanna kalolin da gashin idon da aka maƙalawa Mommy ta zama dodo,ana tsaka da yi mata kwalliya Billy ta kira wayar Mommy ta yi mata Allah ya sanya alkhairi,dan kuwa har yanzu tana jin nauyi da kunyar shiga cikin taron mutanen garin nasu saboda gudun surutun jama'a akan ta. Gaba d'ayan su sun shirya cikin kyakkyawar shiga kafin su fara raguwa su tafi gidan Ɗan liti,Mommy kuwa na nan bata fita wajen taron walimar ba sai da Abdul da Bilal suka iso suka ɗauke ta a mota su da Suhailah. Ba ƙaramin mamaki ne ya kama Mommy ba da ta ga Suhailah taje wajen bikin nata fuska a sake kamar dama can sun saba da juna (wayayyiyar mace kenan) itama sakin ranta tayi ta shiga motar Bilal ya ja yana ta janta da hira suka wuce ƙofar GIDAN ƊAN LITI.......... [09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI *LAST PAGE ALHAMDULILLAH!* RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 110: Wajen walima ya cika da mata a zazzaune a kujerun roba farare sai washe baki suke yi. Malam liman ne ya yi wa'azi mai ratsa zuciya akan zamantakewar aure,wanda ba iyakar ma'auratan ne suka bada hankalin su wajen sauraran wa'azin ba,hatta da dattijan mata da mazan da suka samu halartar wajen sun ɗauki manyan darussan da basu taɓa sanin akwai su ba a gidan aure. Sai da aka kusan tashi daga taron ne su Aunty Naja da Ameerah suka dinga bi layi-layi suna rabon abincin da suka zuba a take away har da lemon roba da ruwan leda. Ɓangaren maza kuma Sule da Sadeeq ne ke rabon abinci. Bayan an rufe taron walimar da addu'a ne mutane suka dakawa sauran abincin da ya rage wawa,kowa na kwasar rabon shi,tun Ameerah na zagin su tana kai duka har ta gaji ta sakar masu buhun ta koma gefe tana maida numfashi,Naja ce ta dafa kafad'ar ta ta ce, "Rabu da su su kwasa,ai hakan ma arziƙi ne,duk wanda ya ci ya saka albarka ai mun gode." Cikin ɓacin rai Ameerah ta ce, "Dube su kamar wasu ƴan yunwa,kowa fa an bashi amma dan zalama suke ƙwacen na hannun mutane." Dariya kawai Naja ta yi ta kama hannun Ameerah suka shige gida,masu kwashe kujeru da rumfuna ne suka fara kwashe abun su suna lodawa a mota. Amarya kuwa na cikin motar Ango ta yi lunƙui a bayan mota suna shan hirar su,duk wanda ya wuce suna kallon shi,amma su ba a ganin su,mommy sai magiya take yiwa Abdul akan ya barta ta shiga gida,ta gaji tana buƙatar hutu,wani lagwaɓe kai Abdul ya yi tare da turo baki kamar yaron goye sannan ya ce, "Haba baby yanzu kora ta kike yi?" Murmushi Mommy ta yi mai sauti kafin ta ce, "Ni ba korar ka nake yi ba,ka ga dai ba a d'aura auren nan ba fa,wannan abun da ka ke yi ba zai haifa mana ɗa mai ido ba,mu yi haƙuri mu koma ciki daga gobe jiran zai ƙare." Sake shagwab'e mata ya yi ya ce, "Gobe ne fa kawai,dan Allah ki ɗan yi min abun nannnn." Zaro ido Mommy ta yi waje ta janye jikin ta daga yanayin zaman da suka yi,nan take jikin ta ya hau rawa ta fara tuna rayuwar da ta yi a baya,me yasa Abdul ke neman maida ita ruwa bayan ita a kullum neman tsari take yi da sake aikata zina? Ah zina mana tunda ba a ɗaura musu aure ba har yanzu. Da sauri ta sanya hannu zata buɗe motar,cikin zafin nama Abdul ya riƙe mata hannu,juyawa ta yi ta sauke idanun ta a nashi,shima kallon ta yake yi da idanun shi da suka rine suka sauya kala tsabar yanda yake jin wani irin yanayi game da Mommyn,muryar ta na rawa ta kalle shi ta ce, "Baby ka yi haƙuri ka barni na ci gaba da kare mutunci na har na tsawon awannin da ya rage mana kafin mu mallaki junan mu,ka riga ka sani kai nake so,kai zan aura,to me zai sa mu tsaya aikata abinda Allah zai yi fushi damu,mu ɓata yau saboda goben mu ta lalace? Kar ka manta muna da Amir,aikata wani abu da ya saɓawa Allah a wannan yanayin zai iya shafar rayuwar shi." A hankali Abdul ya saki hannun ta ya jinginar da kanshi a jikin kujerar motar,cike da tausayawa halin da yake ciki Mommy ta buɗe marfin motar ta fita,duhun da ta gani ne ya bata tabbacin jimawar da suka yi a tare,godewa Allah ta yi dan kuwa ba lallai mutane su gane ta ba,cikin azama ta afka cikin gidan nasu,Abdul kuwa ya jima zaune a bayan motar kafin ya buɗe ya shiga gaba ya tada motar ya wuce gidan Sarki. Ko da ya shiga gidan ya tarar da ƴan'uwan shi da dangin mahaifin shi da na mahaifiyar shi ana ta zuba hira, mata na ganin shi suka hau guɗa suna yi masa kirarin sarauta da na angwaye,murmushin yaƙe kawai yake yi yana amsa gaisuwar su tare da gaishe da wasu da suka girme shi,Suhailah ya hango tana bin shi da kallo,murmushi ta sakar masa kafin ya yafice ta da hannu,noƙe kafaɗar ta tayi sannan ta kauda kanta daga gare shi tana murmushi. Tsaki ya ja a hankali ya wuce ɗakin shi dake gidan,gado ya faɗa ya kwanta ba tare da ya cewa Bilal da Azizah dake zaune suna hira komai ba,Bilal ne ya ce, "Kai malam meye haka zaka faɗo ɗaki da ma'aurata a ciki babu ko sallama?" Banza Abdul ya yi masa ya sake jan pillow ya na jan tsaki,Azizah na jin haka ta tattara kwanukan abincin da ta kaiwa Bilal zata fita,Bilal ne ya ce, "Noor kawo masa abinci da ruwa please." "Tom yanzu kuwa." Fita ta yi ta bar su dan su tattauna,dan kuwa ta san yayan nata nada damuwa duba da yanda yake ta zabga tsaki. Azizah na fita Bilal ya matsawa Abdul ya sanar dashi damuwar shi,shiru ya yi ya kasa sanar da shi abinda ke ran shi,saboda nauyi da kunyar shi da ta kama shi,karshe dai ba dan yaso ba dole ya haƙura ya saki ran shi,abincin da Azizah ta kawo ya zauna yaci ya ƙoshi. Washegari da safe dangin Mommy suka je gidan ta suka sake gyara mata shi tsab,kowa sai son barka yake yi domin babu abinda Abdul bai saka mata ba a cikin gidan. Dan haka basu wani jima ba suka ɗunguma suka koma gidan Ɗan Liti da mata ke taron yini,dafadikan shinkafa aka dafa da ta ji kayan lambu da nama,wasu na ta tsincewa saboda rashin sabawa da cin ganyayyaki a shinkafa. Ruwa kuwa pure water sai ya zamo kamar wani zam-zam a gare su. Amarya da sauran ƴan'uwanta da suke a matsayin ƙawayen ta na can gidan Alhaji Baban Gida sun sha gayu ana ta kaiwa da komowa. Da misalin ƙarfe biyu na rana bayan an idar da sallahr Juma'a aka ɗaura auren Hadiza da Abdussabour a karo na biyu,bisa sadaki nera na dukan nera har dubu ɗari da hamsin,mutane sai ƙananun maganganu ake yi akan yawan kud'in da Abdul ya bayar a matsayin sadakin bazawara. Tinda aka ɗaura auren Abdul ke ɗauke da mabayyanin farin ciki,sai gaisawa yake da mutane ya na yi musu godiya Maestro cinematography na biye da shi yana ɗaukan shi da mutanensa video saboda tarihi. Gefe ya samu suna tsaye shi da Bilal da Sultan da wasu cousins ɗin shi ya kira Mommy a waya,hayaniyar su Ameerah bai bari ta ji ba,dan haka sai da ya jera mata missed calls biyar sannan ta ɗauki wayar,cikin wata iriyar murya ya ce, "Halalina kina lafiya?" Baki Mommy ta damƙe tana dariya ƙasa-ƙasa ba tare da ta ce komai ba,wani irin farin ciki take ji wanda ko a auren su na farko bata ji irin shi ba,muryar Abdul ta jiyo yana faɗin, "Alhamdulillah Baby an ɗaura auren mu,kin zama mallaki na a karo na biyu,wanda nake fatan mutuwa ce zata sake raba mu." Cike da farin ciki Mommy ta ce, 'Alhamdulillah Baby Allah ya bamu zaman lafiya,Allah ya baka ikon tsaida adalci a tsakanin mu." Ihu su Ameerah suka sanya Saddiqa dake tsaye tana yiwa Mommy video ta hau rera waƙa tana faɗin, "Alhamdulillahi ta zama matar Abdul,ta zama d'akko riga,ta zama,ta zama ɗakko wando,ta zama,ta zamma miƙo buta." Gaba ɗaya sai ɗakin ya ɗauki waƙar,har Abdul ya kashe wayar yana dariya basu dena ba,Mommy kuwa kukan farin ciki ta fashe da shi,cikin zuciyar ta take jin ko yanzu rai ya bar gangar jikin ta ta cika burin ta,sallamar Tsahare da su Mero ce ta katse ihu da murnar da su Ameerah ke ta yi, Mommy na ganin Tsahare ta tashi tana share hawaye ta isa gare ta ta rungume ta, cike da murna ta ce, "Iya sai yanzu kuka zo? Ina su Binta? Me yasa baki zo min dasu ba?" "Humm baban su ne ya hana, muma da ƙyar ya barmu muka zo,kin san halin shi da kulle." "Hakane kam,na ko gode da ya barmin ke kika zo,Hajiya Mero babu magana,Asabe barkan ku da zuwa bismillah ku zauna." Bayan sun zauna ne suka hau gaisawa,Ameerah ce ta yatsina fuska ta kalli Mero ta ɗauke kai,Mero ma dake mace ce mai tsiwa sai ta yatsina baki ta kauda kai daga kallon Ameerah,Saddiqa ce ta tashi ta kawo musu abinci,sun jima a gidan kafin su yi sallama tare da fatan alkhairi,Mommy bata barsu haka ba sai da ta sa aka ɗebar masu kayan biki mai yawa sannan ta ce su gaida yaran. Amarya da ƙawayen ta basu bar gidan Alhaji Baban Gida ba sai da yamma sannan suka wuce gidan Ɗan liti,Saddiqa kuwa da misalin ƙarfe biyar suka yiwa kowa sallama suka tafi Abuja ita da Munir ta jirgi. Suhailah ma motar su Bilal tabi suka koma da yamma bayan ta yiwa Abdul da Mommy fatan alkhairi,zuciyar ta cike da matsanancin kishin da ta yi namijin ƙoƙari wajen danne shi suka bar garin,daga dangin Abdul har na Mommy sun jinjinawa Suhailah saboda ƙoƙarin kwantar da hankalin ta da na mijin ta da ta yi,babu wanda zai ce ga kalma ɗaya ko wani aikin rashin arziƙi ko rashin mutunci da ta yi kafin bikin da bayan biki,Abdul kanshi ya yaba mata,kuma ya ɗaukar mata alƙawarin tsaida adalci a tsakanin su kafin su tafi. Da misalin 9:59pm dangin ango suka je suka ɗauki amaryar su kamar yanda al'adar ƙauyen take. Tinda suka kai amarya basu wani jima ba Ta Annabi ta sa kowa ya tattara nashi ya nashi suka bar amarya ita ɗaya daga ita sai halin ta. Bayan tafiyar su Mommy sai ta buɗe fuskar ta dan taga ya ɗakin yake,mamaki ne ya kamata da taga an sauya komai na ɗakin ba kamar yanda suke a da ba,hamdala ta dinga yi a ranta tana jin wani irin farin cikin da bata ji ba a auren su na farko. Abdul bai shiga gidan ba sai goma da rabi na dare,hannun shi ɗauke da manyan ledoji guda uku,ba tare da jin nauyi ko kunya ba Mommy ta yafa mayafin ta da kyau a kanta ta miƙe ta isa gaban shi ta karɓi ledojin suka ƙarasa bakin gado suka zauna a tare,tin kafin ta karasa ajiye ledojin Abdul ya rungume ta tsam a jikin shi yana sauke ajiyar zuciya kamar wani jaririn da ya yi kewar mahaifiyar shi,cikin matsanancin farin ciki murya na rawa ya ce, "Alhamdulillah ya Allah na gode maka da ka saukar da ƙaddarar da ta rabani da wannan baiwa taka,sannan ka saukar da ƙaddarar da ta sake haɗamu a inuwa ɗaya,Allah kasa babu wata mummunar ƙaddarar da zata sake raba tsakanin mu har abada sai mutuwa ." A hankali Mommy da hawayen farin ciki ke kwaranya a idanun ta ta furta, "Amin ya Allah,tabbas kai ɗin ƙaddara ta ce,ina son ka Abdussabour,ina matuƙar ƙaunar ka,Allah ya barmin kai na yi ta son ka ina jin daɗi a raina." Rabata da jikin shi ya yi suna fuskantar juna ya ce, "Ni ma kece ƙaddarata Hadiza, ina son ki,ina ƙaunar ki,Allah kar ya kawo dalilin da zai sa na dena son ki,saboda idan haka ta kasance zuciya ta zata yi babban rashi,gangar jiki na zai zamo kamar mutum-mutumi." Murmushi suka sakarwa junan su kafin Abdul ya fara isar mata da saƙon dake neman rikita mata nutsuwar ta,cikin sauri ta zame jikin ta,murya na rawa Abdul ya ce, "Ina zaki je kuma? Jiya kin ƙi yi min abinda zaki faranta min kin ce na bari sai yau,yanzu kuma kina ƙoƙarin ture ni." Murmushi Mommy ta yi ta kama leɓen shi da ya tura kamar irin na yaran nan masu rikici ta ce, "Babyyyy jiyan ma na hana kane saboda ba halalin ka bace ni,amma yau babu abinda zai rabani da kai sai bacci,ina so mu gabatar da Sunnar Annabin rahama ne kafin na faranta maka,domin mun cancanci mu nuna farin cikin mu da godiya ga Allah a wannan daren mai dimbin tarihi." Tashi ya yi tsaye ya sumbaci kuncin ta kafin ya fita ba tare da ya ce mata komai ba,yana fita ta gane ɗayan ɗakin ya tafi,dan haka sai ta tashi ta shiga banɗakin ta ta yi tsarki ta yi alwala sannan ta fito ta sanya musu abun sallah,sallah suka tada suka yi kafin Abdul ya dafa kanta ya yi mata addu'a,ledar da ya shiga da ita ya ja gaban ta ya buɗe musu gasasshiyar kaza da Azizah ta gasa musu kafin su tafi a cikin coil paper a cikin garwashin da akai girki a gidan nasu,daga nan ya buɗe ledar fruits da ya siyo a kasuwa da lemo da madara sai ruwan roba. Zama suka yi suka ci suka ƙoshi suna ta hira,suna kammalawa Mommy ta tashi ta gyara wajen, sannan ta ce masa, "Bari naje na wanke baki na nayi shirin bacci,ya kamata ka kira Suhailah ka ji sun isa gida lafiya?" Nan take ya tuna da Suhailah,sai ya ji rashin kyautawa akan rashin kiran ta da baiyi ba,cikin sauri ya ɗauki wayar shi ya fita daga ɗakin,ɗayan ɗakin ya je ya kira Suhailah,ta jima tana ringing bata ɗauka ba har daga karshe ta mutu, sake kira ya yi,bata ɗauka ba,ƙarshe sai ya yi mata message mai daɗi da sanyaya zuciya,ya ɗan tsaya ya ji ko zata kira shi,shiru bata kira ba bata yi masa reply ba,sake kiranta ya yi har ya cire rai zata ɗauka,ya kai hannu zai kashe kiran kenan ya ga ta ɗauka,cikin sauri ya kara wayar a kunnen shi tare da yi mata sallama,amsawa tayi tana ta ƙoƙarin danne kishin dake nuƙurƙusar zuciyar ta,a hankali Abdul ya ce mata, "My Suhailah na yi kewar ki da ƙamshin ki yau sosai,kin min rowar ganin ki,babu komai zan dawo ne zaki yi min bayanin guduna da kika yi yau,kun isa gida lafiya?" Murmushi ta yi dan kuwa sai taji damuwar da take ciki ta ragu sosai,a hankali ta ce, "Eh mun isa lafiya ƙalau ina ma gidan Yah Bilal,zan yi weekend anan,ranar lahadi da yamma zan koma gida saboda fita aiki. "Da kyau my love ! hakan ma ya yi,saboda bana son ki zauna ke kaɗai bana nan kar ki yi kewa ta da yawa,ina son ki my Suhailah,ki yi bacci mai daɗi kin ji? Allah ya yi miki albarka akan namijin ƙoƙarin da kika yi,sai dai har yanzu ina da ƙorafin ƙin bari na na ganki sosai da kika yi yau." Murmushi ta sake yi na jin matuƙar daɗin kalaman shi kafin ta ce, "Mun fa yi sallama ko ka manta ne?" "Ai ban gaji da kallon ki ba,kin ga kyam da kika yi ne?" "Kar ka damu,idan ka dawo za ka ganni har sai ka gaji" Tana faɗin haka ta kashe wayar ta gaba ɗaya ta kwanta tana murmushi,saɓanin da da take cikin ƙunci da zubar hawaye,Azizah ta ji daɗin ganin farin cikin ta,dan haka sai ta taƙaita yi mata hira ta gudu wajen mijin ta. A can ɗakin Mommy kuwa ko kaɗan daɗewar shi be tada hankalin ta ba,dan tasan idan ita ce tana iya jan hirar ma fiye da haka,koda ya koma ɗakin yana shirin bata haƙuri ta jashi jikin ta ta haɗe tazarar dake tsakanin su,ina ganin haka na ce to dama kinibini ya kawo ni gidan amare. Tin daga wannan daren mai albarka Hadiza da Abdul suka ɗinke suka dawo kamar sabbin ma'auratan da basu taɓa aure ba saboda tsananin soyayyar da suke zubawa. Yana gama kwanakin da ya dace ya yi mata suka je gidan Sarki ta ɗakko Amir da kayan shi ya koma wajen ta da zama,Abdul kuma ya wuce kano saboda komawa bakin aikin shi. ******************** Bayan shekara biyar.... Abubuwa na farin ciki da baƙin ciki sun faru,ciki kuwa harda sake haihuwar yarinya budurwa da Mommy ta yi mai sunan Innah Laminde wato Zainab suna kiran yarinyar da Amirah,Azizah ta haifi takwaran mahaifin Bilal sannan daga baya ta haifi Salma,Sai Ameerah da ta haifi yara biyu mace da namiji,a shekarar da Saddiqa ta kammala karatun ta na zama cikakkiyar likitar fata wato Dermatologist a shekarar ta haifi yaran ta biyu maza kyawawa,wanda sune ƴan biyu da aka fara yi a kaf zuri'ar GIDAN ƊAN LITI. Sule ya auri wata yarinya ɗalibar shi,suna nan zaune a GIDAN ƊAN LITI a daƙin Yadikon Sule,sai ya keɓance wajen shi ya ƙara mata ɗaki da makewayi da madafi,Saddiqa ta matsa masa akan ya karkaɗe takardun shi zata ɗauki nauyin karatun shi ya koma makaranta dan samun ci gaba a rayuwar shi. Suhailah kuwa na ɗauke da ƙaramin cikin da bata san dashi ba har sai da ta kwanta ciwo aka kaita asibiti,gwajin farko aka gano tana da ciki har na tsawon watanni uku,sai ta fara rikici tana shagwab'a tare da kiran bata so,nan take Abdul ya ɓata rai ya ɗakko wayar shi ya ce "To bari na sanar da su Mama abinda kika ce,Allah ya yi mana kyauta su Amirah za su yi lil brother ko sister ke kuma kin ce baki so." Da sauri ta rike wayar tana bashi hakuri. Bayan sun koma gida da sati biyu kuma ta fara jin wata iriyar soyayyar cikin na ratsa ta,har tazo ta fi Abdul so da zumud'i akan cikin ma. Ta ɓangaren k'waisan Alheri kuwa likafa ta ci gaba ya buɗe gidan abinci mai suna HALAL RESTAURANCE a unguwar Jambulo,ya ɗauki masu aiki dake taya shi girke-girke da miƙa abinci,da wannan sana'ar ya sai gida da machine ɗin shi mai kyau. Suna nan suna ci gaba da zumunci shi

Chapter 69 of 70