fara har sai raina ya ɓaci na yi kuka ka ke daina wa"
Hannu ya sanya a aljihun shi ya d'akko ɗari biyu da hamsin ɗin da ya dawo da su ya miqa mata ya ce,
"Amshi sai kilin ki wanke ran naki da na b'ata miki,mu shiga gida ki bani ruwan alwala na yi alwala na je masallaci na ji ma an kusa sallame sallar"
"To Baba"
Suna shiga ta wuce d'akin su ta ajiye ledar kayan ta ta cire mayafin rigar jikin ta ta koma tsakar gidan, ruwa ta ja musu a rijiya suka yi alwala ya fita masallaci ita kuma ta koma d'aki ta yi sallah cikin rashin natsuwa, dan kuwa hankalin ta gaba ɗaya ya na kan wayar ta, ta matsu ta gama abinda take yi ta je ta fara posting hotunan ta a social network, sannan ta duba sauran kayan da aka bata ta gwada su ta ga yanda za su karɓi jikin ta.
Ta na sallame sallar Ameerah ta shiga ta ce,
"Innoh na Kiran ki uwar gantali"
Ko azkar bata tsaya yi ba ta lailaya wa Ameerah ashar ta ce,
"Sa'ar ki ce ni da ki ke kira na uwar gantali? Idan na kama ki sai ran ki ya yi bala'in ɓaci"
"Oho dai ki je ta na Kiran ki"
Tashi ta yi ta jefar da ɗan siririn gyalen ta da take yin sallah da shi ta maida mayafin kayan ta sannan ta ɗauki ledar da ta shiga da ita ta ce wa Ameerah,
"Ai sai mu je ko? Ko a ka aka ce ki kai ni?"
Waje ta yi ta na qunquni, Mommy ta yi amfani da wannan damar ta soke 1500 ɗin ta a bra ta riqe ɗari bakwai da hamsin sannan ta tafi Kiran da Mahaifiyar su ke yi mata.
Ta na shiga ta gan ta zaune daga ita sai ɗaurin qirji,zanin duk ya zazzage zuwa qugun ta, kitson kan ta kamar wanda ya shekara, ta dasa tuwo da miya a gaba ta na miqawa Yayan su Sule nashi,ta na yin ido biyu da Mommy fushin da take yi da ita ya ragu,karkace kai ta yi gefe ta na zuba wa Mommyn miya a nata tuwon ta ce
"Daga ina ki ke tun d'azu ki ka sa ƙafa ki ka bar gida ko sallama baki min ba balle na san inda ki ka tafi?"
"Innoh daga gidan su Billy nake kin ga ma abubuwan da ta bani,ta dawo da himilin tsaraba sai kin gani kawai ke dai,"
Cike da washe baki Innoh ta ce,
"Kai ki bari dan Manzo? Kawo na gani ko da akwai sayiz d'ina?"
Ba musu Mommy ta miqa mata kayan dan kuwa ta san kaff kayan ba me yi mata duba da cewa ita ɗin irin matan nan ne masu jiki ta qasa sosai ta sama kuma ɗan siriri gata kuma da tsaho, ta na gama d'aga kayan ta ce,
"Kashhh ! Gaba ɗaya ba za su yi min ba, karb'i abun ki,amma ina kuɗi na da ki ka ara d'azu?"
"Kin ga ga ɗari bakwai da hamsin ta bani canjin ruwa da muka siya d'azu,na ce bari na kawo maki kud'in ki da na ara na sai katin waya,"
"Shi yasa da kin tambaya nake baki, amma kin ga wannan me kai kamar gidan ungulun? Be kawo ba, bai bada ajiya ba, ya iya Karb'a ya ce zai biya sai dai na gaji na yafe masa,tun dai akan kuɗi ba zan tsine masa ko na yi masa baki ba"
"Hakane kam, bari na je d'aki na ga ko Shamsu ya kira ni ina kyautata tsammanin zai zo yau"
"To a dawo lafiya"
Fita ta yi daga d'akin ta koma nasu d'akin na 'yan mata, a zaune ta tarar da Saddiqa ta na karatun haddar qur'ani da take yi,kullum idan ta je makaranta ta dawo sai ta je wajen Mahaifiyar ta ta sake koya mata sannan ta dawo d'akin su ta yi ta bita, lokuta da dama hayaniyar Mommy da Ameerah ke sanya ta barin d'akin ta koma wajen Yadiko ta yi karatun ta, ko ta je wajen Baabaa dan can ne ba mai takura mata, matsala ɗaya ke hana ta zuwa wajen Baabaa surutu,amma daga baya ta yi maganin abun da yi wa Baabaa wa'azi dan haka yanzu in ta na karatu Baabaa ko motsin azziqi bata yi dan ta riqe wa'azin da Saddiqa ta yi mata akan ba a surutu idan ana ambaton Allah,amma fa da ta gama karatun ta Baabaa za ta sa ta a gaba da qorafin Innoh ta yi mata kaza da kaza,ko kuma yau a gidan qawar ta an yi faɗa da qawarta da surukar ta,haka zata tsare ta da zance har ta rasa inda zata saka kan ta.
Babu ko sallama Mommy ta shiga d'akin ta wurgar da ledar hannun ta ta buga tsaki,
"Ke wai dole ne ki zauna yin karatu anan? Na ga dai Baba yau a d'akin Innoh yake ki je d'akin ku ki yi karatun naki a can mana,salon kawai ki takura wa mutum ya fasa abinda yake da niyyar yi aikin banza kawai"
Da jin haka sai Saddiqa ta tattara littattafan ta a jakar ta ta miqe ba tare da ta ce mata komai ba ta wuce d'akin su, dan ta san halin Mommy da ta amsa ta zata hau masifa wataqila ma ta dake ta Baban su ya zo qarshe a bata rashin gaskiya tun da su ba su bashi kuɗi kamar su Mommy shi yasa baya wani yi da su sosai a gidan da Mahaifiyar su kamar yanda yake bayyana soyayyar shi ga su Mommy a gaban kowa.
"Allah ya so ki yarinya da kin zauna da na daki banza"
Kayan ta ta cire ta samu waje ta zauna daga ita sai under skirt da bra,tuge acucin kan ta ta yi ta baza gashin qeyar ta tare da furzar da iska,sai ta ji jijiyoyin kanta na sakewa a hankali dan kuwa ba k'aramin matsa ta yi wa kan nata ba.
'Yar kwab'irar wayar ta ta d'akko da ta yi full charge a gidan Sarki dan su sola gare su ta cire password ta kunna data sannan ta shiga social media cike da nishad'i da annashuwar son gabatar da qudirin da ke ran ta.....................
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: *GIDAN ƊAN LITI*
RUBUTAWA:HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH)
*PAGE 4:*
Video d'in ta ta sanya a Instagram, sannan ta sanya wasu a status d'in ta na WhatsApp,murmushi ta yi a dai-dai lokacin da take zaɓar sabon hoton take so ta sauya a DP ɗin ta, nan da nan ta tuna wanda ke kai ya fi shekara bata canja shi ba saboda bata yi sabo ba.
Mutane da dama suna ɗaukan Maman Fadwa(Sunan da take amfani da shi a social media) bata son yawan ɗaukan hoto ne, a cewar ta mijin ta ya hana saboda shi ustaz ne ko na Dp ɗin ta ma ya bari ne dan ta dage ta na so ta saka, shine ya umarce ta da sanya face mask dan baya son a gane masa mata.
Dariya ta yi ta buga cinya sannan ta ce,
"Ina ga fa 'yar mu ta farko ni da Yah Shamsu Fadwa za mu sanya mata dan gaskiya idan Sunan nan be bi ni ba ba daraja a lamarin,"
Dariya ta sake bushewa da ita sannan daga qarshe ta miqe ta hau kwala wa Ameerah kira,cike da bata fuska da rashin kunya Ameerahn ta je ta ce mata,
"Gani maye?,"
"Uwar ki ce ! Na ce uwar ki ce, Ameerah kin raina ni ko? Wato saboda kin ga ina zaune ba makaranta ba sana'a ba kuma mijin aure shi yasa na zama sa'ar wasan ki ko? to jeki na fasa aiken naki tunda ke kin zama 'yar matsala zan je da kai na"
Ameerah na jin aike za ta je wa Mommy sai ta hau murna ta na wage baki kamar wawuya,cikin ɗan yake haqora irin na Ɗan liti ta ce,
"To ai Ke ce ki ke ta kwala min kira kamar na yi laifi baki iya magana cikin lumana ba, me za a siyo? Tsire ko balangu ko doya da k'wai ko shayi da burodi da wainar k'wai?"
"Me shegen kwadayin tsiya,zo ki siyo min kifin Tayiragas,ki ce ya kyauta min ya kuma saka yaji"
"Kin san ki na cin kifi sai an san kin kashe kuɗi a gidan nan ko?"
"To sai me ba nawa bane?"
Da jin haka Ameerah ta sassauta muryarta ta ce,
"Dan Allah nima zan sai na ɗari biyu wadda na zara a kuɗin Innoh kar ki faɗa mata,"
"Ke ni surutun ya ishe ni haka karb'i nan sauran ki dad'e har Baba ya baro majalisa ya rufe gida ba zan buɗe ba"
"Alqur'ani kar ki buɗe na cinye kifin kuma gobe ki ka je zance ki ka dad'e har aka rufe gida ko Zaki shekara kukan akuya ba zan buɗe ba"
Murmushi mommy tayi a lokacin da ta tuna duk lokacin da Shamsu ya zo suka bar qofar gidan su suka tafi wani wajen suka jima har aka rufe gida bata dawo ba,to da kukan akuya take tashin Ameerah ta je ta zare sakata su koma d'aki kamar babu abinda ya faru,washegari Mommy sai ta biya da wani abin da Ameerahn ce za ta zab'a da kan ta a biya ta da shi ɗin.
Bayan fitar Ameerah da minti ɗaya Mommy ta shiga group ɗin su da ake tura masu videos, stickers da audio note na littafan batsa har ma da rubuce-rubucen batsa da hotuna kala-kala, ni da ke gefe ina d'akko rahoto sai da hankali na ya tashi dan ganin b'arnar da 'ya'yan musulmi kuma ƙananan yaran da ke gaban iyayen su suke aikatawa a cikin group ɗin,sai da na dinga tunanin anya wadannan basu manta daga wacce al'umma suka zo ba kuwa? Sun manta Allah ya zaɓe su ya karrama su ya fifita su a cikin kowacce al'umma da ya aiko wa Annabi da manzanni daya sanya suka zo a cikin al'ummar Annabi Muhammad? Anya kuwa suna da masaniyar tsinuwa da dawwama a cikin fushin Allah da azabar shi zata tabbata akan duk wanda yake rubuta littafan batsa, ko yake tura videos, stickers da pictures na batsa, ko ya ke zaman jira a turo ya karanta, ko ya tambaya da kan shi a tura Masa ya kalla ko ya karanta? Lallai da alama wadannan basu da masaniyar hakan ko kuma sun sani suke take sani wanda yin hakan shi kan shi wani babban zunubi ne mai zaman kan shi.
Tambaya ta a nan ita ce, shin sun shirya jurewa shiga wutar Allah mai tsananin rad'ad'i da azaba a ranar gobe kiyama akan jin daɗin mintina qalilan ne?
Duk wannan tsoro da tashin hankalin da na shiga tare da k'walla ƙarar da na yi saboda firgita da na yi dan kallon wani mummunan video da Mommy ta buɗe ta na kallo ta na jin daɗi,bai sa mommy ta lura dani ba balle ta b'oye abinda take yi, yanda hankali na ya tashi da jin tsoron lallai fa Allah ya na ganin duk abinda muke aikatawa mala'ikun Allah na rubutawa,ranar gobe kiyama za a kunna wannan faifan videon a filin qiyama, a dai-dai wannan lokacin kuma Mommy ta na can hankalin ta ya kai kololuwa wajen tashi da jin daɗin abinda take kallo.
Ta yi nisa kwarai wayar ta ta ɗauki ringing hannun ta na rawa ta ɗauka ta kara a kunnen ta, cikin wata iriyar murya ta ke fad'in,
"Ka na waje? Gani nan zuwa yanzun nan, dan Allah ka jira ni,yanzu na gama kallon zazzafan videon da ka tura mana group bani da natsuwa yanzu, idan bamu haɗu ba zan iya haukacewa"
Wata Shu'umar dariya ya yi ba dan komai ba sai dan yana yin komai ne tare da amfani da lokaci,ya tabbata yanzu ta gama kallon videon kuma ta na nan ta na buqatar kasancewar shi a kusa da ita,wannan dalilin ne ya sanya shi qara gyara jikin shi ya ɗaukar masu sweet ya tafi gidan su Mommy,dan ba zai iya da warin bakin ta ba, shi yasa yake kai mata sweet duk dare ya yi ta yi mata daɗin baki wajen sanar da ita yanda yake son ta da qaunar ta.
Hijabin ta kawai ta ɗora a Saman wannan under skirt ɗin nata ta ɗauki wayar ta ta shura takalmin ta tayi waje. Tsaye ta gan shi jikin ginin soron gidan su ta sa hannu ta ja shi ciki suka kara qofar gidan.
A can d'akin Innoh kuwa ta gama kasafin abinci wanda tsabar bala'in rowa ke sanya ta kai miya cikin d'aki musamman idan ta saka naman miya aciki da kuɗin ta,kwance take ta buɗe baki ta na ta sakin munshari kamar ana yanka rago a mayanka, fitilar k'wan da ta kunna ta yi qasa saboda rashin kalanzir saura kaɗan ta mace, Saddiqa ce ta dawo daga wajen karatunta a dakin Baaba ta zo wucewa ta ga fitilar na daff da mutuwa sai ta ɗauketa ta kashe ta ajiye inda suke rataye wa saboda kar lagwanin ya cinye a banza, ta na kashe mata ta koma d'akin su dan ta san yanzu Yadiko da Saddiq sun yi bacci.
Ko da ta shiga d'akin bata ga kowa ba sai kawai ta kad'a kai dan kuwa ta san duk inda suke zuwa gaba ɗayan su, saboda idan faɗa ya kacame masu a d'akin da kan su suke tona wa juna asiri.
Shirin bacci ta yi ta yi addu'a ta karkad'e makwancin ta sannan ta kwanta ta na sake rera haddar alqur'anin ta da a yanzu ta kai izu hamsin da uku, a haka bacci mai daɗi ya ɗauke ta.
Jin motsin tafiyar Ameerah ne ya sanya Shamsu da Mommy rabuwa da junan su suna maida numfarfashi kamar waɗanda suka yi wasan tsere,sake lafewa suka yi a jikin gini ta shige gidan bazar-bazar kamar wata balama, ta na shigewa suka fita qofar gidan nasu suna dariyar samun nasarar kammala komai ba tare da an kama su ba kamar kullum.
Kuɗi ya bata dubu biyu sababbi sak irin wanda Billy ta bata, nan da nan kwad'ayin zuwa aikatau ya taso mata, da alama ba qananun kuɗi ake samu ba idan dai har Billy zata dinga kashe kuɗi haka, sallama suka yi da junan su cike da alqawurran sake kasancewa da junan su ta waya,sannan ta faɗa gida shi kuma ya yi hanyar nasu gidan cike da nishad'i yana fatan watarana ta bashi abinda yake buri daga gare ta gaba daya,ba wai su tsaya a iya wasanni ba.
Ko da ta shiga gidan bata koma d'aki ba sai da ta deb'i ruwa a buta ta shiga band'aki sannan ta fita ta koma d'aki, cikin haɗe gira ta ce,
"Ke ina saqo na ki ka zauna ki ka raba qafa kamar 'yar shayi kina cin kifi kin ga na shigo ba Zaki kula ni ba?"
"Ai idan ni ban zama 'yar hyayi ba ke Zaki zama ne,kin zaci ban gan ku ba ne? Na gan ku to Kyale ku na yi kawai, karɓi nan ni kar ki ihyeni da surutu"
Difff mommy ta yi kamar ruwa ya ci ta ta karɓi saqon ta ta koma gefe, raba kifin biyu ta yi, rabi ta saka a tuwon ta dan kuwa yunwa take ji sosai kuma ta san dole sai ta ci tuwon duba da jimawar da take yi online duk dare, shafa cikin ta ta yi dan kuwa kukan yunwa ya saka kamar yasan an kawo kifi,sai ta ji kamar ma bata ci komai ba tun safe tsabar rarakewar da cikin ta ya yi.
Rabin kifin kuwa a ciki ta ɗebar wa Ameerah ta ɗauki kaɗan ta daki qafar Saddiqa da bacci ya fara ɗaukan ta ta ce,
"Munafuka na san idan ki biyu, karɓi kafin gobe ki ce ban baki ba, ko ba komai na san an ce ido guba ne"
"Hummmm Yah Mommy kenan,wato kin san an ce ido guba ne ko? Waye to ya faɗi hakan? Shin baki taɓa jin an ce mutum ya kame kan shi daga aikata Zina da dikkan dangogin ta ba? Allah subhanahu wata'ala da kan shi a cikin alqur'ani mai tsarki da girma ya ce wa muminai mata da maza kar su kusanci zina to me yasa ki ke aikata abinda ki ka san haramun ne? Tabbas ina son cin kifi da ma abinda ya fi kifin daɗi wato nama da kaza da duk wani nau'in abinci mai daɗi, amma ba zan sayar da jiki na da arha dan na ci kifi ba ke da ki ka ga Zaki iya ki bada himma ki yi ta yi"
Madadin nasihar Saddiqa ta shiga jikin su sai maganar ta ta hasala su dika,cikin ɓacin rai Mommy ta nuna kanta da yatsan ta manuni ta na qanqance idanu ta ce,
"Saddiqa ni ki ke kira da mazinaciya? Saddiqa dama sharrin da Zaki yi min kenan? Kallon 'yar iska ki ke yi min dama? Yau ko sai na maki shegen duka kin ga idan ya so gobe in an tambaye ki shaidar zama na 'yar iska sai ki fito da shaida"
Nan take jikin Saddiqa ya yi sanyi ba dan komai ba sai dan ta san cewa tabbas ba ta da shaidar kasancewar Mommy mazinaciya tunda bata taɓa gani da idanun ta ana aikata hakan da ita ba,iya abinda ta sani shine mommyn na kalle-kallen fina-finai da karance-karancen batsa, wani k'warin guiwa ta ji ya zo mata dan kuwa su ma ai zinar ne, cikin d'aure fuska ta ce,
"Eh na faɗa ɗin, duka kuma ai ba yau ki ka fara duka na ba ban yi maki komai ba,"
Ameerah ce ta taso ta ce,
"Wai Mommy b'ata lokacin na maye? Ki mayar mata da baki irin namu tun da dama 'yan d'akin su ne kawai ba su da irin shi,daki bakin yarinya sai jini ya yi tsartuwa"
Kafin Ameerah ta rufe baki kuwa Mommy ta yi wa Saddiqa b'arin makauniya a fuska, nan take ta ga wata wuta mai fatsi-fatsi ta gilma a idanun ta,qara ta buɗe baki zata k'walla, Ameerah ta yi tsalle ta damqe mata bakin Mommy ta ci gaba da dukan ta, motsin k'ofar gidan su suka ji suka yi saurin kashe fitila da rufe qofa, shiru Saddiqa ta yi dan kuwa bata so maganar ma ta fita karshe Mahaifiyar ta da ke bacci za a d'aga wa hankali a banza.
Dukan qofar d'akin nasu Ɗan liti ya yi da qafar shi ya ce,
"Lalatattun banza su na can an hangame uban baki ana bacci,yo an tashi tun safe ana ta jidali ba dole a kwanta da wuri ba? Kai kun sa sakata ko?"
Shiru suka yi ba wanda ya amsa masa, da kan shi ya jijjiga k'ofar ya tabbata sun saka sakata sannan ya yi gaba zuwa d'akin Innoh.
Baabaa na jin motsin shi ta yi tsaki tare da fad'in,
"Kai Misbahu kashe fitila ka rufe qofa wancan mashiriricin ya dawo,"
Duk daren duniya bata iya bacci sai ta ji Ɗan liti ya dawo gida, domin kuwa har a wannan lokacin ta na jin shi kamar qaramin qanin ta da ta raina tun ya na yaro,wannan shi ne dalilin da ya sa ko da jikokin ta suna nan bata rufe qofa sai ta ji ya rufe gida ya shige d'akin da yake da kwana a can sannan Itama take sa haqarqarin ta ta yi bacci mai daɗi.
****************************
Kukan zakaran Baabaa ne ya tashi kowa a gidan,sai yawo yake ya na bi d'aki-d'aki ya na kuka kamar wanda aka sanya aikin tashin mutanen gidan dan su gabatar da sallar asuba.
Saddiqa tun kafin ya fara kuka ta farka ta yi sallar ta tare da karatun qur'ani ta yi azkar ɗin ta ta na kukan zuci,dan kuwa har a wannan lokacin bata daina jin zafin da bakin ta yake yi ba, ta tabbata sun fasa mata baki a jiyan.
Qamshin suyar qosan Baabaa ne ya sanya Ameerah tashi daga bacci,ta na miqewa ta zabga hamma da miqa ta fita daga d'akin ta ɗauki buta ta wanke idon ta da bakin ta ta wuce wajen qosai,gaishe da Baabaa ta yi cikin ladabi sannan ta hau zuba wa mutane ba tare da ta sake magana ba, sai da taga na ciki da aka tsame ya kusan qarewa ta ɗauki uku a tare ta jefa bakin ta,Sule ne ya zo da kud'in shi ɗari biyu ya miqa ya ce,
"Baabaa ni dai ki zuba min da kan ki bana son wannan yarinyar ta zuba min"
"To Sulaimanu mai Sunan Annabin Allah, kawo farantin naka"
Karb'a ta yi ta zuba masa mai yawa direct daga kasko,sannan ta ci gaba da kwashe saura, Ameerah ko kula shi bata yi ba, dan ta san inda take wargin ta, sule baya ɗaukan rainin wayon ta zane ta yake yi tasss shi yasa bata wani dogon zance da shi.
Gimbiya Mommy kuwa bata tashi daga bacci ba har sai wajejen goma da rabi na safiya, lokacin kowa ya san inda ya dosa Ameerah ma mai tafiya talla ta yi wanka ta shirya,Saddiqa da Sadiq da Misbahu da Faisal sun wuce makarantar boko, Sule ɗan zaman banza ya tafi yawon shi, zuwan Ɗan liti d'akin ya kai sau uku ya na tashin Mommy amma bata san ma ya na yi ba, dan ta Innoh kuwa ko shekara za ta yi ta na bacci ba tashin ta take yi ba.
Ta na farkawa wayar ta ta ja ta ga lokaci, murmushi ta yi da ta tuna daren jiyan har 2 na dare suka kai ita da Yah Shamsu suna hirar su, ya tura mata videos sun kai goma har da data ya saka mata da tace datar ta ta qare,Billy kuwa gori ta dinga yi mata da ta ce mata zata sauka saboda datar ta ta qare, anya ba zata samu baban ta ba yau a yi ta ta qare dangane da zuwan ta birni aikatau?
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH)
PAGE :5
Tin da ta ci abincin safe ta koma d'aki ta kwanta ta na karanta littafan da take bi online, dan kuwa Ɗan litin ya riga ya fita neman na kai bata samu ganawa da shi ba a safiyar, ta na nan kwance ta na karatu dai-dai da d'akin da ta kwanta bata share ba,Baabaa ce ta shiga k'wala mata kira kamar zata tsaga gidan, cike da zumb'ura baki ta fita hannun ta na dama riqe da wayar ta kan ta babu ɗan kwali sai sosa shi take kamar wata mai kwarkwata,sai da ta je inda Baabaa take ta tsaya ta na b'ata fuska ta ce,
"Gani maye ki ke ta kwalan kira kamar Zaki tada gidan"
Cike da murna Baabaa ta washe baki ta ce,
"Wannan yaron ne ya yo aiken zakka da aka saba bayarwa duk shekara,da alama bana manya kowa zai samu dubun shi ashirin, yara kuma kuma goma-goma dan kuwa da kan shi ya kasafta komai kin dai san shi ah toh,shi ne nace bari na Kira ki dan ki je ki ciro mana su a can injin da ke bada kuɗi,ya ce ya turo kud'in ta akawun d'ina da kullum yake min gargad'in kar na baiwa kowa katin da lambobin sai wanda na aminta da shi shi yasa kullum nake yawo da shi a lalita ta,kin san yaran nan idan suka san lambobin sirrin ɗauka za su dinga yi su na zarar kuɗi,to shine na ce bari na kirawo ki ke kaɗai na yarda da ita a gidan nan, dan baki yo halin uwar ki ba wajen son yaki halal yaki haram"
Tabbas Baabaa ba ta yi k'arya ba, bahaushe ya kance laifi duk na kura amma banda satar nama,to fa hakan take a wajen mommy,duk wani rashin jin ta da qiriniyar ta bata ɗaukar abinda ba nata bane, ko kuma ba a ce ɗauki an baki ba,wannan shi ne dalilin da ya sa take son neman na kanta amma fa ta hanyar aikatau,ko kuma ta ci gaba da karatu har ta samu aikin gwamnati ko shamsu da take biyewa ba wai kuɗin da zai bata take yi waba,kawai tsabar qarfin sha'awa ce da rashin aurar da ita da wuri da ba a yi ba shi yasa take biye masa idan ta yi kallace-kallacen ta su keb'e su ɗan yi wasannin su ta samu biyan buƙatar ta,ita Mommy a rayuwar ta ta na son harkar hutu shi yasa aikin ma sai ta zaɓi kalar wanda zata yi,bayan zuwa birni aikatau ko aikin gwamnatin bata jin akwai wata sana'ar da zata yi da zata dinga kawo mata kuɗi,aikatau ɗin ma Billy ta kwad'aita mata cewar ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 70