Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙaramar yarinya, akan dole Saddiqa ta buɗe itama ta fita tana ƙoƙarin b'oye kunya da nauyin Ummi dake addabar ta, kafin ta isa Anisah ta fito tana ihun murna,koda ta waiga sai taga Ummi na biye da ita, cikin dai-daita kanta ta nufe su itama tana murnar,nan dai suka dinga taya ta murna da fatan alkhairi, Anisah da Ummi saida suka hau motar suka tuƙa suma suna ta santin motar,a haka Abbah ya dawo ya tarar da su shima ya sanya albarka tare da yi mata fatan Allah ya sauke ta lafiya sannan ya haye sama. Sai bayan magariba Anisah da Khaleesat suka maida Saddiqa gida,ita kuwa sai hamdala take yi da babu wanda ya sake d'aga maganar abinda ya wuce a tsakanin ta da Munir,suna isa gida suka tarar da Munir kwance a doguwar kujera yana kallo,yaci abinci dik ya b'ata wajen kamar wani ƙaramin yaro,kallon su yayi yana murmushi yace, "Sai yanzu kuka ga damar dawo min da matata?" Cikin shagwab'e fuska Khaleesat tace, "Habaa Yah Munir ji yanda ka ɓata wajen nan dan Allah." "Na b'ata ɗin,wani yace ku tafi min da mata bata bani abinci ba?" "Humm gata nan to mun dawo maka da ita ai,sarakan soyayya,mu zamu koma dare yana yi." "Ta yaya zaku koma to bayan babu mota a hannun ku?" "Akwai mota a waje ,Yah Neesah ta bari ne a wajen bamu shigo da ita ba saboda ba jimawa zamu yi ba." Anisah ce ta kalli Saddiqa dake ta bin Munir da kallon so da ƙauna tare da godiya tace, "To Lailah mu zamu wuce a baiwa Majnun kulawa da kyau, Allah ya sanya alkhairi ya tsare." Rufe fuska tayi da hannayen ta dika biyu tana dariya, har suka fice daga gidan bata ce komai ba,Munir ne ya raka su ya dawo ya kulle ko ina sannan ya zauna kallo,zama tayi a gefen shi tana sake yi masa godiya,cikin murmushi yace, "Wai godiyar nan bata isa bane haka?" "Ai dole na yaba maka kuma na gode maka Rouh." Kallon ta yayi yana murmushi tare da kashe idanu yace, "Idan godiya kike so kiyi min muje d'aki ni bana gane me kike faɗa anan." Babu musu kuwa Saddiqa ta miƙe suka shige d'akin su suna dariya,zama nayi dan in ƙarasa kallon film ɗin da ba dani aka fara ba. Da misalin sha biyu na dare suna kwance a saman gadon su manne da junan su Munir sai shafa cikin Saddiqa yake yana hamdala,cikin sake shigewa jikin Munir Saddiqa tace, "Yah Munir ba zan gaji da yi maka godiya ba har abada, saboda ka yi min kyaututtukan da ban taɓa koda mafarkin zan samu irin su ba a duniya,Allah ya saka da alkhairi ya raba ka da iyayen ka da duniya lafiya,Ina so in roƙi wata alfarma a wajen ka, sai dai dan Allah bana so ka ɗauki hakan ta wata fuskar ta daban, ina so ka yi min Kyakkyawar fahimta." Ɗan haɗe girar shi yayi waje guda sannan yace, "Uhumm ina jin ki,Allah ya bani ikon yi maki wannan alfarma da kike nema a waje na." "Yah Munir kaga ni ban iya tuƙa mota ba,amma Babana ya iya,kuma shi ƙaramin direba ne da yake jan adaidaita sahu,ina neman alfarma ka bani dama na mallaka masa motar nan saboda ya sanya min albarka, shi kaɗai nake da shi yanzu Yadiko ta rasu,dan Allah kar ka...." "Babu komai Saddiqa, ai mota yanzu mallakin ki ce,dan haka sai abinda kike so kiyi da ita zaki yi,ki dena neman alfarma,inshaa Allahu idan na samu kuɗi zan sake saya maki wata saboda ina sha'awar naga kina da taki motar ta kan ki." Da sauri ta tashi zaune ta hau murna tana sake yi masa godiya,Allah-Allah take yi washegari tayi ta kirawo Baban nata da baya wani sake mata a duk sanda za su gaisa. Washegari kuwa tun da asuba suka yi wanka suka shirya, Munir ya wuce masallaci ita kuma ta yi sallar ta a ɗakin ta,bayan ta idar ne tayi azkar da karatun ƙur'ani kamar yanda ta saba, sannan ta tashi ta hau aikace-aikacen da ta saba yi dik safiya. Kallon agogon jikin wayar ta ta dinga yi tana kumawa,a yau sai taga kamar lokacin baya gudu,abincin karin su ta ɗauka ta ajiye a dinning table ta koma parlour ta zauna, wayar Baabaa ta kirawo suka gaisa sannan tace dan Allah a baiwa Sadeeq ya kaiwa Baban nasu,babu musu kuwa Hajiya Baabaa ta bada waya aka kaiwa Ɗan liti tana mamakin me yasa ba a kira shi da wayar shi ba. Koda aka kai masa wayar aka ce masa Saddiqa ce ta kirawo, yaji daɗi a ƙasan ran shi, amma a zahiri sai yace, "Ni bani da waya ne da ba za a kira ni ta waya ta ba sai an kira da ta wasu?" Shiru Sadeeq yayi bai ce komai ba,bai kuma dena miƙa masa wayar ba, a hasale ya karb'i wayar ya hau banbamin faɗa, Saddiqa kuwa hawaye ta hau sharewa tana bashi hakuri,Ɗan liti na matuƙar jin zafin abinda yake yi musu amma ya kasa dena musgunawa yaran nashi da yake tsananin so. Innoh ce ta fito ta tarar da abinda ke faruwa sai ta karɓe wayar da salon makirci ta saka a handsfree ta ce, "Yo ke ƴannan banda abinki me yasa zaki kira shi da wayar makiya? Ko bashi da waya ai akwai ta yayan ku Sule ko? Inda Mommy ta fi ku wayo kenan,ko bata same shi ba bata kiran shi a wayar kowa sai ta yayan ku." 'Ku yi hakuri Baba,dama na kirawo ne aka ce min kashe take sai nayi zaton babu caji ne, kuma Yah Sule a wannan lokacin na san barci yake shi yasa ban kirawo a tashin ba.' "To ya isa haka yanzu dai meye dalilin rangad'a masa wannan sammakon?" Ɗan liti ne ya ƙure wayar da ido kamar zai hango Saddiqa a cikin ta, cikin muryar kuka Saddiqa tace, 'Baba kana ji na? Dama mota ce Yah Munir ya saya min jiya, shine naga ni bai dace na mallaki mota ba kai baka da ita, shine nace bari na aiko maka da ita sai ka dinga jigila da ita.' Wata iriyar guɗa Innoh ta saki ta miƙawa Ɗan liti wayar tana rawa da manyan mazaunan ta,ganin Innoh na murna sai shima ya saki ran shi ya hau murna yana saka albarka, jin farin ciki a muryar mahaifin ta ne ya sanya saddiqa share hawayen ta tana godewa Allah. "To yanzu yaushe za a kawo motar kenan?" 'Inshaa Allahu cikin satin nan za a kawo ta Baba.' "Allah ya yarda a gaida Mannirun a yi mana godiya." 'Zai ji inshaa Allahu.' Suna kashe wayar Innoh ta dinga murna tana faɗin, "Alhamdulillahi muma mun yi mota Ramman Malam Jibo sai a dena yi min gori,Malam dan Allah da motar nan ta iso ka kaini kasuwa a cikin ta ko ba zan sai komai ba a dai ganni a ciki,har ƙofar gidan Ramma nake so ka kai ni mu gaisa ka dawo dani." Cikin washe baki Ɗan liti yace, "Kar ki ji komai Uwar gidan Ɗan liti,abinda kike so shi za a yi." Lokacin da labarin siyan motar ya riski Baabaa ta sanyawa Saddiqa albarka sosai, amma taso ace ta riƙe motar ta, dan kuwa tana jiyewa Ɗan liti haukan Innoh,fatan alkhairi ta leƙa tayi musu kafin ace baƙin ciki ya hana ta zuwa,ile kuwa tana zuwa ta tarar da Innoh har ta fara yada habaicin baƙin ciki ya hana mutanen gida su zo su taya su murnar samun motar da suka yi, cikin hasala Baabaa tace, "Yo Allah na tuba abinda yayi Baban Gida ai shi Yayi Manniru,da ban haifi uban manniru ba da babu Manniru balle ya auri Saddiqa har ya saya mata motar da zata baiwa ubanta har wasu suce za su yi min gori akai, ni kaina da ina zuwa wani wajen da mota za a ajiye min kamar yanda ake ajiye min duk wani abun buƙata ta na yau da gobe a wadace,gori ai ke za a yi wa mara zuciya, kina ƙin uwar yara da yara amma kina son abun hannun su." Ganin babu ribar da Innoh zata diba a wannan faɗan ne ya sanya ta cewa, "Kin ga dai ban kula ki ba,ni ba dake nake ba ki dena zagi na da faɗa min baƙaƙen maganganu,tammm." "Nima ban kama sunan ki ba ai,ko tsarguwa kika yi?" Innoh bata sake cewa komai ba ta wuce ɗakin Sule ta hau buga masa ƙofa dan ta sanar dashi labari mai dad'in da ya same su da sassafe. ******** Bayan kwana uku da maganar siyan mota aka kawo motar har garin Ba Mugu,yara da manya da tsofaffi ne suka yanyane motar ana ta yabawa tare da fatan alkhairi, cikin farin ciki Ɗan Liti ke washe baki yana amsawa tare da godiya. Malam Jibo babban abokin Ɗan liti ne ya matsa kusa dashi yace, "A gaskiya ya kamata kaima ka fara jigila daga ƙauyen nan namu zuwa wasu ƙauyukan da kuma birane, kai shaida ne akan irin manyan kud'in da nake kamawa a duk tafiya ɗaya da nayi, dan haka idan ka shirya kayi min magana na ɗora ka a hanya kaima a fafata da kai." "Ai kuwa na ji daɗi da wannan shawarar taka, inshaa Allahu ranar Juma'a zan zo mu tattauna akan hakan." A haka Ɗan Liti da malam jubo suka tsaida magana zuwa ranar Juma'a za su haɗu a tattauna, ɗan liti yayi register da tashar su sannan yayi duk abinda ya dace. Haka kuwa aka yi,ranar Juma'a da hantsi Ɗan Liti ya isa tasha ya tarar da Malam Jibo suka gudanar da dik abinda ya dace, cikin sa'a kuwa akwai mutane a ƙasa da yawa babu motoci nan da nan aka fara yi wa Ɗan liti lodin tafiya birni,wanda cikin ranshi ya zaci lodin kauyuka za a yi masa ya fara kafin ya ƙware ya fara zuwa birnin,kafin rana ta take an gama lodi Ɗan liti ya sallami mutanen tasha ya saka kai ya nausa saman titi cike da farin ciki. Wata iriyar hanya ce suke bi mara kyau, dik kwaltar ta farfashe,titi yayi ramuka babu daɗin tafiya,rashin sabo da irin wannan tafiyar da tuƙin kanshi ne ya janyo samuwar hatsarin da motar Ɗan liti ta kusan samu a hanyar, nan take kuwa ta tsaya cakkk mutane suka hau yi masa masifa tare da faɗin ya sauke su su nemi wata motar su hau basu shirya mutuwa ba,cikin damuwa Ɗan liti ya sauka daga motar yana basu hakuri yace, "Ku yi min aikin gafara ƴan uwa,kun dai ga ba laifi na bane yanayin hanyar ce da bata da kyau, ku zo ku taimaka min a gyara abinda ya sanya ta tsayawa sai mu ci gaba da tafiya tsayuwa a irin dajin nan hatsari ne saboda yanda rayuwa ta lalace." Wani abokin Malam Jibo da tinda suka hawo motar yake taya abokin shi Malam Jibo kishi akan motar da ɗan liti yake da ita ne yace, "Mu taya ka ka gyara me? Da kai baka san kan motar ba ka fara shiga dawa da ita? Babu abinda za mu taya ka, kai matsa sa mana hannu a motar nan me zuwa mu hau mu ware ka ji da shi kai kaɗai,ba dai junan ku gasa da kishi ba? Daga ganin aboki na nada mota yana samun kuɗi kaima ka sayi mota,to gaka ga hanyar ai sai ka gyara kayar ka da kan ka." Kamar waɗanda aka yi wa baki ko dama suna jin haushin Ɗan litin gaba ɗayan su sai suka sanya wa motar dake tafe hannu,suka shige suka bar Ɗan liti shi kaɗai a dajin ilahi. Zufa yake sharewa da hannayen shi bibbiyu saboda ranar da ta ƙwalle a saman kan shi,kallon dajin da yake ciki ya sake yi cikin wani irin yanayin da yake ji kamar ya tsala ihu,ko yayi ta zabga kuka babu ƙaƙƙautawa,ya rasa da wanne suna zai kira wannan yanayin da yake ciki,wannan shi ake kira gaba kura baya sayaƙi,kallon matacciyar hanyar da ya biyo ya sake yi sai yaji kukan da yake ta sha'awar yi ya kufce masa,zama yayi ya jingina da motar shi ya ɗage bakin shi sama ya buɗe dika haƙoran shi ya hau tsaga kuka, cikin kukan da yake yi ya hau faɗin, "Kaico na ! Kaico na ! Yau ina zan saka kai na a wannan dajin na ubangiji? Malam Jibo ya cuce ni ya ci amanata daya bani gurguwar shawarar biyo wannan dajin na ubangiji,nidai na tabbata dai sabuwar mota irin wannan ba za a samu wani gyara a tattare da ita ba,sai dai idan yanayin hanyar ne da bata da kyau da kuma rashin sanin ina zan taɓa ta tashi ne ya jawo min shiga wannan tashin hankalin." Majina ya sharce ya sake shiga cikin motar a karo na biyu tin bayan tafiyar fasinjojin shi da suka gudu, taɓe-taɓe ya fara yi cikin ikon Allah da rashin sanin abinda ya taɓo mota ta tashi,da azama Ɗan liti ya fita ya rufe kowacce ƙofa da aka bar masa a buɗe ya koma ya shige cikin motar shi ya ci gaba da tafiya, nan take ya ƙudirta idan ma mugunta ce ta sanya Malam Jibo bashi shawarar ya shiga birni shi kuwa zai bashi mamaki, ba zai dawo ba har sai ya samo alkhairi daga birnin......... [09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 75: Da misalin takwas da rabi Aunty Naja da Mommy suka kammala dik wani shiri da za su yi,sannan suka rufe gidan suka fito harabar gida suka tsaya, Naja ce ta kalli Mommy cike da tantama da tsoro ta ce, "Anya Hadiza kina ganin satar fita daga wani gari zuwa wani garin zai haifar mana da ɗa mai ido kuwa? Ko dai ki kira mijin naki mu yi wata ƙaryar ya san da fitar tamu?" Mayafi Mommy ta sake gyarawa a saman kafad'un ta sannan taɗora jakar ta a kan mayafin ta kalli Naja ta ce, "Aunty dan Allah mu tafi kafin ƙarfe biyu mun dawo, ba sani zai yi ba in dai ba ke kika sanar da shi ba." Bakin gate suka nufa suna tattaunawa, Mommy ce ta sanya makulli ta kulle gidan sannan suka fara takawa a ƙafa suna kallon hanya ko Allah zai sa su samu abun hawan da zai kai su tasha. Babu jimawa kuwa wani mai adaidaita sahu ya tsaya a gaban su yana tambayar su ko tafiya za su yi, cikin sauri Naja ta bashi amsa da, "Tafiya zamu yi bawan Allah, tasha zaka kai mu ta rijiyar zaki nawa ne?" "Aunty mu hau dan Allah ko nawa ne zan bashi bana son ɓata lokaci." Murmushi mai adaidaitan yayi da ya ji furucin mommy, ya tabbata yau ranar sa'ar shi ce,dan haka har da kiɗa ya saka musu bayan sun shiga, a guje yake tafiya bisa umarnin Mommy har suka isa tashar, dubu biyu ta bashi suka sauka suka nausa cikin tasha, sai godiya mai adaidaitan yake yi musu tare da fatan Allah ya kaisu dik inda za su je lafiya ya maida su gida lafiya. Tinda suka shiga tashar Mommy ke baza ido tana neman mota mai ƙwari da kyau da zata ɗauka shata ta kaisu garin Ba mugu,idanun ta ne suka sauka akan wata jar mota dake zaune a layin garin nasu, cikin sauri suka nufi wajen suka tsadance da driver, ba jimawa bayan ta biya ya sallami ƴan union na wajen ya dauke su suka bar tashar. Tafiyar awa ɗaya da wasu ƴan mintinan ce ta kai su garin Ba mugu,direct gidan malamin tsubbun da Aunty Naja ke kai su suka nufa,suna isa Naja ta ce wa driver ya jira su ba jimawa za su yi ba. Koda suka shiga sun tarar da malamin tsibbun zaune da kayan aikin shi yana jiran su, dan kuwa tin a daren ranar da za su zo Naja ta sanar da shi zuwan su,kallon su yayi yana wani lashe baki kamar baƙin maye,kallon Mommy ya yi yana wani ƙanƙance ido ya ɗaga hannu yana nuna ya ce, "Ah ah ! Wannan ba ita bace matar yariman garin nan namu wadda mijin ta ke son yi wa kishiya kwanan nan?" Gaban Mommy ne ya yanke ya faɗi,cikin sauri ta zauna a gaban shi kamar zata shiga cikin kayan duban nashi,murya na rawa ta ce, "Dan Allah malam ka tausaya min kamar yanda ka tausaya min da farkon zuwan mu, ko nawa kake buƙata zan baka,bana son kishiya bana son wanda yake son kishiya,ban taɓa sanin ina son miji na haka ba sai da ya sanar dani zai ƙara aure." "Kwantar da hankalin ki, tin a daren jiya da Naja ta sanar dani zuwan ku na hau yi maki aiki, sai dai ban zaci za a zo dake ba shi yasa kika ga ina mamaki,yanzu me kike so ayi wa ita yarinyar da zai aura ɗin? Kina so a haukata ta ne, ko a kashe ta, ko kuma a sa tabi duniya kowa ya manta da ita?" "Ni bana son a yi mata ko ɗaya daga cikin waɗannan malam, so nake kawai a raba su, a sanya musu tsananin ƙiyayyar junan su,ta yanda ko ganin juna baza su sake ƙaunar yi ba har abada balle su auri junan su,ko a sanya mata lalurar da zai guje ta ita kanta taji bata son auren shi saboda lalurar." "In dai wannan ne an gama, sai dai wani hanzari ba gudu ba, a binciken da nayi na gano cewar yariyar a ma'aikatar mijin ki take itama." "Kan uban can ! Dama abokiyar aiki Abdul yayi mace shine bai sanar dani ba? Yaushe ma suka fara yin masu aiki mata a wajen nasu? Malam dan Allah ni so nake ma duk wata mace dake wajen a kora ta,bana son kowacce mace ta raɓi miji na indai ba muharramar sa bace." "An gama, sai dai zaki saki bakin aljihu sosai saboda wannan aikin babban aiki za a yi maki,saniya za a yanka wa aljanu su sha jini sosai a yi wa almajirai sadaka da naman." "Malam ko nawa ne zan biya ayi aikin nan bani da matsala akai,ni dai dan Allah ina son aikin yafi na baya kyau,na yarda da kai zaka yi ma abinda ya fi hakan,dan haka ka bani No wayar ka da Account no ɗin ka sai na tura maka kud'in." Babu ɓata lokaci ya karantawa Mommy No wayar shi tayi saving, sannan ya bata account No ɗin shi tayi masa transfer ɗin kud'in aikin har ma da ƙari,cike da jin daɗi suka baro ƙauyen Ba mugu ko ziyara bata kai wa su Innoh ba. Koda suka koma gidan su sun tarar da gidan a rufe kamar yanda suka barshi,hakan ne ya baiwa Mommy tabbacin Abdul bai dawo ba, girki ta tashi ta yi mai daɗi tayi amfani da maganin da malamin nasu ya bata,tana gamawa ta wuce d'aki ta sheƙa wanka ta sanya riga da skirt na wani material mai laushi,kalar kayan ta amshi farar fatar ta da ciki yasa ta ƙara yin haske mai kyau,nan da nan gida ya kaure da ƙamshin turaren wuta mai haɗe da maganin sihiri,tafe take tana ƙara hura garwashin da bakin ta a zuciyar ta tana fatan Allah yasa malamin nan ya gama aikin da ya rage a daren yau. Ta bangaren Abdussabour kuwa tinda aka tashi aiki Maimoon ta ja shi suka sake fita,wannan karon zuciyar shi bata son fitar ko kaɗan amma babu yanda zai yi da ita,dama bahaushe yace tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa zai doka,dan haka Abdul ya riga da ya san cewa ya d'akko ruwan dafa kan shi. Hotel ɗin da suka je ranar farko shi suka sake komawa,tin da suka shiga Maimoon ke ƙoƙarin jan ra'ayin Abdul ɗin amma yaƙi bata haɗin kai, cikin fushi ta zaro wayar ta tana wani cika tana batsewa tace, "Tinda na kula ban da amfani a wajen ka, bari kawai na watsa video ɗin mu duniya taga irin abinda kake yiwa yaran mutane,dan kuwa dik wanda ya gani zai tabbatar da ranar farko na fara kusantar namiji,kai kuma me kake da shi da zaka kare kan ka?" "Ya kike so in yi ne Maimoon? Gaba ɗaya gangar jiki na ta ƙi bani had'in kai, kwata-kwata ni bani da wata sha'awar sake kusantar ki." "Au haka ma zaka ce min? To na ji baka da sha'awar sake kusanta ta, ya maganar auren namu yanzu?" Shiru yayi yana roƙon Allah ya kawo masa mafita,yayi nadamar kasa jure sha'awar ɗan ƙanƙanin lokacin da yayi, yanzu gashi biyan buƙatar da yayi na ƴan mintuna na neman sanya shi a nadama har zuwa ƙarshen rayuwar shi. Kamar wadda aka mintsina haka Maimoon ta miƙe tsaye,wani irin nishi tayi sannan ta kama marar ta,cikin gigicewa ta saki wayar dake hannun ta ƙasa ta fasa wani irin ihu,a guje Abdussaboor ya nufi wayar hannun ta jikin shi na wata iriyar rawa,direct videon da take ƙoƙarin watsawa a duniya ya goge daga wayar gaba ɗaya,jakar ta ya hau dubawa ya samo camerar da ta ɗauke shi video a ranar su ta farko,babu tunanin komai ya hau goge dik wani abu dake kan camera ɗin,sannan ya rotsa ta a ƙasa, sai da ya kammala dik wani goge-gogen da yake son yi ne hankalin shi ya kai kan Maimoon dake yashe a ƙasa tana murƙususu kamar wadda ake shirin zarewa rai. Cikin kuka da fitar hayyaci ta miƙa masa hannu tana faɗin, "Ka taimaka min zan mutu,ciki na ciwo yake yi." "Kamar ya in taimaka maki,ina ce yanzu kike neman sanya ni a bala'i? Kin ga tafiya ta, ga wayar ki nan ki kirawo wata a cikin ƙawayen ki ta taimaka maki." "Dan girman Allah Sir ka taimaka min, bana so na mutu yanzu, wayyoo Allah na zan mutu." Tausayin tane ya kama Abdussabour,cikin sauri ya taimaka mata ya ɗaga ta ya ajiye ta a saman gado, gani yayi jinin ya dena zuba amma dik da haka bata daina murƙususun da take yi ba,No wata ƙawarta tace ya kirawo tazo ta maida ita gida,babu b'ata lokaci kuwa ya nemo No ya kara mata a kunne, baya ma so a ji muryar shi a san suna tare,cikin nishi da fitar hayyaci Maimoon ta ce, "Khairi dan Allah...ki zo Royal hotel ki ɗauke ni banda lafiya." Bayan ƙawar Maimoon ta amsa ne Abdul ya kashe wayar ya sake gyara mata kanta ya faɗa banɗaki,sai da ya gyara jikin shi sannan ya fito ya kalle ta,tana nan kwance yanda ya barta sai murƙususun ciwo take yi,cikin sauri ya tattare nashi ya nashi ya bar ɗakin,tinda ya fita yake zuba sauri be tsaya ba sai a bakin motar shi,a guje ya ja motar shi ya bar hotel ɗin ya nufi gida. Tin a hanya yake jin kanshi na yi masa wani irin nauyi,tsananin ƙiyayyar Maimoon yake ji tana ninkuwa a zuciyar shi fiye da ƙin da yake yi mata a baya,hankalin shi gaba ɗaya ya tafi gida, fatan shi kawai ya buɗe idanun shi ya ganshi a gaban Mommy,a yau ya yarda ya amince Mommy itace rayuwar shi,itace farin cikin shi,ba zai taɓa iya ci gaba da rayuwa mai daɗi ba idan babu ita,ba ya jin zai iya yi mata kishiya,furucin da yayi mata na zai ƙara aure ma jin shi yake yi kamar ya aikata babban zunubi, ya zai yi ya wanke kan shi a wajen Mommy ne? Da wannan tunanin ya tsaya a wani super market yayi wa Mommy siyayya,yana fita ya tsaya a wani shahararren wajen gashin kaji ya saya mata har guda biyu ba dan babu a gidan ba,sai dai yayi hakan ne kawai dan yasan tafi son gashin waje,gida ya nufa yana addu'ar Allah yasa ta dena fushi da shi,zai bata haƙuri har sai ta yafe masa, zai bata kulawa fiye da yanda yake bata a baya. Ko da ya isa bakin gate ɗin gidan ji yayi kanshi ya sara da ƙarfi har sai da ya dafe kan da hannu ɗaya,a hankali yaji hankalin shi na dawowa jikin shi, waje ya fita ya buɗe ƙofar gidan ya shiga sannan ya koma ya shigar da motar shi ya kashe,sai da ya fitar da kayan da ya siyo sannan ya koma ya rufe gidan. Tin kafin ya juya baya yaji ƙarar buɗe ƙofar shiga gidan,juyawa yayi a hankali ya hango ta tana tahowa cikin takun ta mai ɗaukan hankalin shi,murmushi ta sakar masa ta lashi leb'en ta na ƙasa tana wani kashe masa idanu,kallon leb'en ta da suka sake kumbura saboda tsufan da cikin ta yayi,shi dai duk duniya baya jin akwai wadda ta kai masa Hadizan shi kyau. Kamar yaron da yayi kewar mahaifiyar shi, haka Abdul ya tafi wajen Mommy da sassarfa ya rungume ta yana sauke

Chapter 47 of 70