Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jijjiga take yi kamar shi taji zai ƙara aure,hannun ta ya kama yana miƙa mata yaron su dake kuka, wata uwar harara ta zabga masa sannan ta kashe wayarta ta zauna ta karb'i yaron ta wurga masa mama a baki,cikin ƙunar rai tace, "Amma dai gidan Sarki sun iya harkar ƙaranta,sun zama ƙananan mutane,yo ƙananan mutane mana,wa yake ƙara aure a wannan zamanin ba tare da ta gida ta sani ba? Na yi rantsuwa da....." "Kar ki rantse sahibata, ni ɗin banza nayi maki kishiya baki sani ba? Ai ko zan ƙara aure da sa hannun ki da amincewar ki zan ƙara shi, ballantana ma ni ke kaɗai kin ishe ni rayuwar duniya dai ba ta ƙiyama ba." "Kai dallah can rufe min baki ! Wanne daɗin baki ne Abdul be yi wa Mommy ba tin a daren su na farkon aure? Yanzu baga shi can auren su za a yi da wata ba?" Shiru Shamsu ya yi bai ce komai ba, daga ƙarshe ya zame ya bar gidan,yana fita ya nufi shagon shi dan ya fara aikin shi na turawa mutane sabbin films ɗin da ya d'akko,gani yayi mutane ba su wani zo ba sosai, masu saka caji ne kawai suka fi zuwa,duk an tattare an koma wajen me sabon turin da ke bakin kasuwa, ƙwafa ya yi yana ayyana yanda zai sabauta sana'ar sabon mai turin,dan kuwa ba ƙaramin samu yake yi ba a sana'ar dik da yanzu ba da ita ya dogara ba, kuɗaɗen da Billy ke turo masa suna da yawa har ya fara tunanin sayan fili ya fara gini. A can garin Kano kuwa Abdul yana ɗakin shi riƙe da waya yana magana da Huzaimah sai shagwab'a take yi masa tana faɗa masa kunya take ji,idan masu kawo kaya sun zo ba lallai su ganta ba,ta tafi gidan wata yayar su,dariya yake yi mata saboda yanda take Shagwab'ar abun na ratsa shi sosai, wani irin shauƙi yake ji na musamman tare da fatan Allah ya gabato da ranar auren su da gaggawa ya samu yanda yake so a wajen ta. Babu zato babu tsammani ya ji an fizge wayar hannun shi an yi wurgi da ita jikin gini ta tarwarse,kaca-kaca screen ɗin wayar ya yi kafin ta yi wani haske ta ɗauke gaba ɗaya, iPhone ce ƴar yayi mai tsadar gaske,cikin sanyin jiki ya kalli Mommy da idanun ta suka kaɗa suka yi wani irin jaa kamar ba ita ba,farar fuskar ta ta sauya ta koma jawur kamar tumatur,hannu biyu ya d'aga sama kamar wanda ƴan sanda suka zo kamawa,cikin dakewa ya buɗe baki zai yi magana muryar shi ta kasa fita,da hannu ya hau nuna mata gefen gado yana yi mata alamun ta zauna ya yi mata bayani,wasu hawaye Mommy ta ji sun fara zuba a kuncin ta masu tsananin zafi,kallon shi ta yi sannan ta nuna kanta cikin kuka tace, "Abdussaboor me kake so na yi maka kafin ka gane bana son kishiya ina so in rayu da kai daga ni sai kai sai ƴaƴan mu? Raina ka ke so in siyar ko jiki da ruhi na? Me kake so nayi maka kafin KA FAHIMCI NA TSANI KISHIYA ZAN IYA KASHE KA AKAN KAYI MIN KISHIYA !" Ta ƙarasa maganar ta cikin ɗaga murya da ƙarar da ta kiɗima Abdussaboor,cikin gigicewa Mommy ta juya ta d'akko wata kwalbar turaren wutar ta dake saman madubin ɗakin,kwalba ce babba mai kauri da nauyi, tana ɗauka ta saita gaban shi da ke sanye da zallan gajeran wando ko vest babu a jikin shi ta wurga masa,wata iriyar gigitacciyar ƙara Abdussaboor ya saki ya fara layi,nan take kwalbar ta faɗi ƙasa ta tarwatse,ta kan kwalaben Mommy ta bi ta ƙara saka hannun ta ta naushe shi a gaban shi, nan take ya baje a saman gado a sume,ƙarfin ta ta saka tana kuka tana ci gaba da dukan shi a wajen tare da faɗin, "Sai na illata ka Abdussaboor sai dai mu zauna da ni da kai bamu amfana da wajen ba, dan na tabbata babu yarinyar da zata zauna da kai baka da kayan aiki." Naja ce ta shiga a guje ta ɗaga Mommy daga saman Abdul da ya suma,Bilal da ya jima zaune a parlour yana jiran hayaniyar da ake ta lafa kafin Aunty Naja ta kira masa Abdul ne ya gaza haƙuri ya jira saboda ƙarar da abokin shi ya saki,direct shima ɗakin ya nufa ya kutsa kai babu neman izini kamar yanda ya saba,ganin ash colour ɗin wandon Abdussaboor na ɗigar da jini ne ya sanya shi ƙarasa shiga ɗakin a guje,yana isa gaban Mommy dake ci gaba da kai wa Abdussabour duka ya ɗauke ta da wani gigitaccen mari ya yi wurgi da ita ƙasa,cikin kwalaben da suka tarwatse a ƙasa ta faɗa,ko jin azabar yankan da ta samu a hannun ta da cinyar ta bata yi ba ta miƙe ta cakumo wuyan Bilal tana ɗura masa ashar,cikin kuka ta ce, "Matsiyaci tsinanne wanda ba zai sadu da rahamar Allah ba kawai,ai kai ne babban munafukin dake taya shi rufe min maganar auren,Abdul baya aikata komai sai da shawarwarin ka, da ka faɗa masa ya sanar dani ko ya ma fasa auren da fasawa zai yi,amma dake kai ɗan zina ne baka ƙaunar Allah sai ka goya masa baya ya ci amana ta,Allah ya isa ba zan taɓa yafe maku ba,sai Allah ya saka min." "Sakar min wuyan riga balama ! Shashasha mara hankali daƙiƙiya kawai,bari ki ji na faɗa maki Hadiza,zan kai aboki na asibiti, idan wani abu ya samu lafiyar shi sai kin ƙare rayuwar ki a gidan yari,ko zan yi yawo tsirara sai na wulaƙanta ki." Yarfe hannayen ta ya yi daga jikin shi ya sungumi Abdussaboor a kafad'ar shi ya nufi hanyar waje, Aunty Naja ce cikin kuka ta ɗauki jallabiyya ta bi bayan Bilal ta miƙa masa sannan tace, "Maza ka kai shi asibiti Allah ya bashi lafiya, kuyi haƙuri, kuyi haƙuri,kuyi hakuri da dik abinda Hadiza ta aikata." Ko kallo Naja bata ishi Bilal ba ya fizge jallabiyya ya sakawa Abdul da ya kwantar a saman kujera a parlour,yana kammala saka masa ya ɗauki ruwa a glass cup ɗin wajen ya sheƙa masa,ko gezau Abdul bai yi ba balle ya farka,ganin haka ne ya sake ɗaga hankalin Naja da Bilal, da sauri ya ɗauki Abdul a kafad'a ya fita waje dashi,da motar Abdul ɗin ya yi amfani wajen kai shi asibiti. Ko da yaje asibiti ya yi wa likita bayanin me ke faruwa cikin sauri suka kai shi emergency room aka fara bashi taimakon gaggawa,jinin dake zuba ne yafi ɗagawa Bilal hankali,likita ya jima yana duba Abdul kafin ya fito,zare gilashin idanun sa ya yi ya kalli Bilal yace, "Biyo ni zuwa office d'ina." Cikin sauri Bilal ya bi bayan shi suka shiga office suka zauna,a hankali likita ya fara magana Bilal na sauraren shi, "Wato da farko dai ina so in sanar da kai cewar kar ka damu jinin nan da ka ga yana zuba ba daga al'aurar ɗan uwan ka bane,ta gefen cinyar shi ne ya yanke da abinda aka dake shi dashi ko aka yanke shi da shi, mun ɗinke masa inshaa Allahu zai warke ba tare da wata matsala ba,sai abu na gaba kuma shine,zamu ɗan yi masa wasu gwaje-gwaje da zarar ya farfaɗo saboda mu gani ko ya samu matsala a gaban nashi,wanda muna fatan Allah ya taƙaita ya sa kar a samu wata matsala." Ajiyar zuciya Bilal ya sauke sannan ya ce, "Na gode likita,dan Allah a kula min da shi sosai,ko nawa ne na yi alƙawarin zan kashe akan ya samu lafiya,fata na kawai a tabbata bai samu matsala a wajen nan ba dan girman Allah." Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo wa Bilal, tsantsar tsana da ƙiyayyar Mommy da ya binne a zuciyar shi ya tono har ya samu damar zuba masu taki suka yi yaɗo suka mamaye ko ina na jiki da ruhin shi,cikin zafin nama ya miƙe ya yi wa likita sallama ya bar asibitin, direct police station ya wuce ya yi ƙarar Mommy akan tana son ta illata mijin ta dan zai ƙara aure,nan take kuwa aka shigar da ƙarar shi,aka haɗa shi da ƴan sanda biyu, mace ɗaya namiji ɗaya suka shiga mota suka nufi gidan Abdul,zaune suka tarar da Mommy Naja na gyara mata inda ta yanke tana yi mata faɗa akan abinda ta aikata, ita kuwa jin zuciyar ta take a bushe a ƙeƙashe,idanun ta sun soye ta ƙure waje ɗaya da kallo sai jijjiga jiki take yi, ganin ƴan sandan nan bai karya guiwa ko zuciyar ta ba,hasali ma miƙewa tayi ta nufi ɗakin ta ta d'akko mayafi da zanin goyo ta goya jaririn ta,hannun ta riƙe da handbag dinta da wayar ta kamar mai shirin zuwa biki ko suna. A shirye take ta je kotun ƙoli akan Abdul yayi mata kishiya,dik laifukan ta da ƴar sandar ke karanta mata be girgiza ta ba sai ma gaba da ta yi suka bi bayan ta,Motar Abdul ta buɗe ta faɗa gaba, Bilal yaso ya hana ta shiga gaban sai kawai ya ƙyale ta, dan baya son ma magana ta haɗa shi da ita saboda kar ya faɗi abinda zai zo ya yi daya sani daga baya. Ko da suka je police station har gaban DPO suka je aka fara gabatar da case, daga ƙarshe ganin tana da ɗanyen goyo sai DPO ya ce zai tura su kotu direct ba sai an tsaya wani tsare ta ba. Shi dai Bilal yana nan ya kasa ya tsare yana so a ɗauki duk matakin da ya dace kafin ma ya sanar da iyayen Abdul,dan baya son wani yace masa kar a hukunta ta akan abinda tayi saboda tana matar Yariman ƙauyen Ba Mugu. Suna kammalawa da station ya wuce asibiti wajen Abdul,kwance ya gan shi idanun shi kulle,amma da alama ba bacci yake yi ba,zama Bilal ya yi a gaban gadon ya yi shiru dan be ma san me zai ce ba,sun jima zaune shiru kamar Abdul ba zai yi magana ba,sai Bilal yaji Abdul ya ce, "Na gode Bilal da ka ceci rayuwa ta,ban zaci zan rayu ba a irin azaba da raɗaɗin da suka ratsa gangar jiki na,yanzu shikenan na nakasa ko Bilal? Likita yace min zai yi wahala na ƙara tashi, wace mace ce zata zauna dani a haka Bilal? Na tsani Hadiza, na tsane ta Bilal, na yi dana sanin sanin Hadiza a rayuwa ta,Bilal ba zan iya ci gaba da rayuwa da Hadiza ba,idan ta illata ni ne dan ta zauna dani ita kaɗai,to ni kuma na datse igiyar auren mu guda ukun,daga yau ni Abdussabour na datse igiyar aure na dake kan Hadiza Ɗan liti dika ukun." "Alhamdulillahi ! Na ji daɗin wannan hukuncin da ka yanke Abdussabour,da ace baka sake ta ba ma sai na yi yanda na yi ka sake ta,Hadiza ba macen da za a haɗa zuri'a da ita bace, alhamdulillah ma da baku tara zuri'a mai yawa da ita ba,yaro ɗaya Allah ya azurta ku da shi a tare,shi kuwa yaro namiji bashi riƙon tabo kamar ƴa mace,Allah ya baka lafiya,yanzu haka ban zo nan ba sai da aka miƙa maganar ta kotu,ba zan bar yarinyar nan ta numfasa ba ba tare da an yanke mata hukuncin da ya dace da ita ba wannan alƙawari na ɗaukar wa kai na........... [09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 86: Baaba ce zaune a parlour ta yi kicin-kicin da rai,fuskar ta babu alamun fara'a ko walwala a cikin ta,gefe kuwa jakar kayan ta ce a ajiye,mayafin ta ta sake gyarawa a kafad'arta sai ta tura ƙafar ta cikin takalmin roban ta mai kyau, Munir ne ya yi sallama ya shiga gidan hannun shi riƙe da wayar shi da makullin mota,tsayawa ya yi turus yana kallon Baaba da ta yi zumbur ta miƙe tsaye tana jifan shi da wani irin mugun kallo kamar wanda ya kashe mata wani nata,cikin ɓacin rai Baaba tace, "Sannu sarkin zamba cikin aminci,kai dai Manniru baka yi halin azziƙi ba sam,zaton da nake yi maka na mutanen kirki kafff ka goge min shi a zuciya ta,haka muka yi da kai? Nace haka muka yi da kai? Rimi-rimi kuka yaudaro ni kai da uban ka da surukin ka kuka kawo ni garin nan,maida ni kuma sai ya zama aiki? Wanka dai bani ke yi wa matar ka ba uwar ka ke wanke ta ta wanke jariri,to ni zaman uban me nake yi da ba za a maida ni ɗakin miji na ba? So kuke na mutu a bariki...." Wani irin kuka ne ya ƙwacewa Baaba,nan ta samu waje ta zauna tana rera shi kamar wadda aka yiwa wani mugun abun,dariya ce ta kama Munir amma haka ya shanye ta ya ƙarasa shiga cikin parlourn ya zauna a gefen Baaba,jakar ta ya janyo gaban shi sannan ya ce, "Kin shirya tafiya yanzu?" Cikin matsar ƙwalla ta d'aga kai ta kalle shi, tana so ta tabbatar da ba raina mata hankali yake so ya yi ba, dan haka tana ganin babu alamar wasa a fuskar shi ta ce, "Na shirya mana Manniru,dan Allah ku maida ni ɗakin miji na,ni tinda aka aurar dani ina da jajayen sawu na ban taɓa yin nisa da ɗaki na ba ya wannan lokaci." 'Ikon Allah,ita wannan har yanzu tana nan da mentality'n mutanen da na rashin fita,lallai yau idan ba a maida ita ba akwai case,gashi ni kuma ina da aiki sosai a office ban san ma ya zan yi da ita ba,ya Allah ka kawo min mafita.' Baaba ce ta ga Munir ya ƙure jakar ta da kallo yana tunani be ce mata komai ba, sai ta miƙe a fusace ta ce "Dama na san ai ba maida ni za ka yi ba,to bari ku ji,ko mutuwa nayi anan ban yarda a binne ni anan garin ba,ku maida ni ɗakin miji na a wanke ni a can a sallace ni a garin mu,tinda kun kafe kun nace sai na zauna daku anan ɗin." A fusace Baaba ta kama hanyar ɗakin ta tana sababi,shi dai Munir lallab'awa ya yi yaje ya ga matar shi da ɗan shi suka gaisa sannan ya leƙa wajen Ummi,sai da suka gaisa sannan Munir ya ce, "A gaskiya Ummi a zo a maida Baaba ƙauyen su kowa ya huta tin kafin ta ja maku Allah ya isa." "Subhanallahi Munir kana da hankali kuwa? Wanne irin ta jawo mana Allah ya isa kuma ana zaune ƙalau?" "Ke kike zaune ƙalau da iyalan ki Ummi amma ita akan ƙaya take ta matsu ta koma garin su,yanzu zuwa na zaune na tarar da ita a parlour tana jiran na zo na maida ita garin su,saboda ta san iwar haka nake shigowa gidan kullum shi yasa ta tare ni,yau idan kika ji kalaman da ta saki zaki tabbatar da gab take da ta zabga maku Allah ya isa saboda aje ta anan da kuka yi against her will." "Ikon Allah,to bari na yi wa Baban ku magana,ni a gani na tana nan ta huta da masifa da bala'in Innoh da yaran ta da basu ragawa kowa,sannan ko babu komai anan zata fi samun kulawa,zaman ƙauye da birni ai ba ɗaya bane." Alhaji Baban Gida ne ya fito daga wanka ɗaure da towel a ƙugun sa ya lullub'e jikin shi da wani babban towel ɗin,waje ya samu ya zauna ya ɗauki mug ɗin da aka haɗa masa shayi ya kurɓa,sai da ya gama sha ne ya amsa gaisuwar Munir yace, "Nima jiya na yi tunanin mayar da ita gida gaskiya,amma tinda abun ya zo da haka gobe inshaa Allahu Munir ka shirya kazo ka maida ita saboda yau ɗin nan kana da aiki da yawa da baka ƙarasa ba a office " "To Abbah inshaa Allahu gobe zan zo na maida ta, kafin nan yau a samu ko su Anisah su kai ta a ɗan yi mata siyayyar komawa,ta haka ne zata kwantar da hankalin ta ta fahimci wannan karon da gaske maidata za a yi." "Hakan ma shawara ce mai kyau, ohh Baaba case kenan,ita dai ta mutu a ɗakin mijin ta,to Allah yasa muyi ƙarshe mai kyau baki ɗaya." "Amin mace ta gari,Allah ya yi miki albarka, Allah ya jiƙan iyayen ki, ina jin daɗin yanda kike son mahaifiya ta ƙwarai kike nuna damuwar ki akan ta,Allah yasa yaran mu su ji ƙan ki fiye da yanda kika yi wa naki iyayen da nawa iyayen." "Amin ya Allah miji na gari." Munir sai murmushi yake yana zaune yana sauraren yanda iyayen nashi ke nuna wa junan su soyayya da ƙauna ba tare da ganin sun tsufa ba,dik irin wannan kaywawan halayen dama a wajen su ya gade shi,shi yasa yake ririta Saddiqa kamar ƙwai. Koda ya fita daga ɗakin direct ɗakin Baaba ya shiga, zaune ya ganta saman abun sallah idanu sun rine mata sun yi jawur,farar fuskar nan ta ta dik ta yamutse ta yi ja,harara ta banka masa ta kau da kai gefe, zama ya yi a gaban ta ya tanƙwashe ƙafa sannan ya ce, "Hajiya Baaba tamu ta gargajiya,yanzu dai nazo maki da albishir mai daɗi a sakar mun fuska dan Allah,na je na lallaɓa su Abbah sun amince gobe zan maida ki ɗakin mijin ki,yau ma ba dan aiki ya yi min yawa ba da yanzu mun ɗauki hanya, ki shirya anjima su Anisah su kai ki siyayyar tsaraba,gobe da ƙarfe tara zamu tafi ƙauyen Ba Mugu inshaa Allahu." Tinda Munir ya fara magana Baaba ke washe baki, hannu ta sa ta daki kafad'ar shi cike da murna tace, "Ko ku fa Uhumm? A ce wai ku ɗakko ni tsofai-tsofai dani na dawo gidan yara na zauna ina da nawa ɗakin mijin ba banda shi ba? Allah ya kaimu goben da rai da lafiya, ni da an bar siyan tsarabar ma abubuwan da aka bani ma duk suna nan na kai wa yaran can su Abbe." "Ah ah Baaba ba an yi haka ba, ki dai samu ki sake yi musu tsarabar,ƙawayen ki ma dik ki saya masu abubuwa a san kin zo Abuja gidan ɗan ki ko ba haka ba?" "To ai shikenan, ni a shirye nake, in sun shirya su taho mu tafi." "To ni bari na je na ci abinci na wuce na ma makara." "Allah ya bada sa'a ya yi albarka Mannirunaaa." Dariya Munir ya yi ya amsa da "Amin Baabataaa" sannan ya fita zuwa dinning area,abinci ya ci sosai sannan ya sake sallama da Saddiqa da babyn su Suhail ya tafi office. Wani irin kyau Saddiqa ta ƙara yi saboda ba kaɗan ba jegon ya karɓe ta,ta cika ta zama babbar mace kamar ba ita ba,yanayin ƙirar jikin su ɗaya da Mommy,sai dai Mommy ta fi ta cika sosai da kyawun diri,ita kuma ta fi Mommy kyawun fuska da dogon gashi, yaron su da alama irin jikin baban shi ya ɗakko,wato ƙaramin jiki,amma kyawun fuskar shi dik na Saddiqa ne. Ba ƙaramar kulawa take samu ba daga mutanen gidan gaba d'ayan su,dik wani motsi da zata yi sai ta samu mai taimaka mata,a ganin ta ma abun kamar ya yi yawa,wannan dalilin ne ya sa bata tare da kewar rashin mahaifiya,a kullum tana yi wa mahaifiyar ta addu'a da mahaifin ta sai kuma su Ummi dake kula da ita kamar su suka haife ta. ****************************** Wani irin duhu ne da d'akin mutum baya ganin koda tafin hannun sa,banda zarni da warin kashi babu abinda ke tashi a wajen,ƙarar buɗe ƙofar ɗakin ce ta sanya Sule dake ɗaure hannu da ƙafa waigawa ya kalli mai shiga ɗakin,hasken waje ne ya haske fuskar Sule har ta sanya shi kare hasken da tafin hannun shi,a tsorace na kalli leɓen Sule da ya kumbura ya yi suntum,haƙorin shi da ya karye sai ya ƙarawa fuskar shi muni ya sauya mata kamannin ta,abinci aka tura masa a irin mazubi mai soson nan na take away,cikin sauri ya ɗauki abincin ya buɗe ya hau ci kamar wanda ya yi shekaru bai gamu da hatsi ba. Loma kawai yake zubawa ko ta kan cinyar kazar dake cikin shinkafa da miyar bai bi ba,sai da ya ci fiye da rabin abincin sannan ya fashe da kuka,cikin kuka ya ce, "Oga dan girman Allah ku min rai ku buɗe ni na fito daga ɗakin nan,ku kai ni duk inda za ku kaini amma bana son zaman nan,da na san inda gidan Hadiza yake dan uwar ta da na nuna maku shi na huta, wannan azabar ta ishe ni haka." Kuka ya ci gaba dayi yana roƙon a fitar da shi,mamakin kafiya da taurin kai irin na Sule ne ya sanya Alhaji ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin,cikin sauri yaron Alhaji da ya kawowa Sule abinci ya matsa gefe ya bashi waje,Alhaji ne ya saka hankicin sa ya toshe hancin shi kafin ya ce, "Kai yanzu da ka nuna mana inda Sweet H take ka gwammace ka ci gaba da azabtuwa ko?" "Yallab'ai ai ban musa maka na gane wa kake magana akai ba ko? Ka ga kuwa ko dan azabar nan da nake ci idan na san gidan ta zan kai ku,ni tinda akai mata aure ban san inda take ba,shi wannan ƙaton ɗan daudun da kuka zo dashi rannan ai shi ya kamata ku sa a gaba ya nemo ta,gidan ta na ƙauyen mu shi kaɗai na sani ko mahaifiyar mu bata san gidan ta dake nan birni ba tinda bata taɓa zuwa ba." "To uban me ya shigo da kai birni kake ikirarin suna kazo?" "Alhaji ƙanwata Saddiqa dake Abuja ce ta haihu shine zan je suna daga nan na haɗu da abokai na a gaisa,idan ƙarya nake Allah ya...." Zalɓe ne ya daka masa tsawa ya ce, "Dalla yiwa mutane shiru." Shiru Alhaji ya yi yana nazarin maganganun Sule,ya jima yana nazari kafin ya juya ya ce, "Zalɓe a buɗe shi,ya yi wanka ku same ni a babban parlour." "To Alhajin Allah an gama." Wani irin daɗi ne ya kama Sule,alƙawari ya yi wa kan shi ko Abuja wajen abokan shi da ya yi niyyar zuwa a yi chilling ya fasa zuwa in har aka sake shi,idan kuwa ya koma ƙauye babu shi babu sake shigowa birni,zai kama kan shi ya ƙarasa rayuwar shi a ƙauyen Ba Mugu,da alama can ne yafi dacewa da shi ba zaman birni ba. Da ƙyar Sule yake iya dirza jikin shi saboda azabar zafi da yake ji a fatar shi,ba ƙaramin duka samudawan mazajen nan suka dinga yi masa ba,wanka yake yana zubar da hawayen azaba,a haka ya gama ya sanya sabon kayan da ya siya shi da Hajiya kafin Alhaji ya kamo shi. Tinda ya fito ya ke kallon tsaruwa da kyawun gidan,cikin zuciyar shi yake tunanin su kuwa wacce iriyar dukiya suke da ita haka? Tafe yake yana bin bayan Zalɓe har suka shiga parlourn da Alhaji yake, nan fa Sule ya sake sakin gandar leb'en shi yana ta'ajibin tsaruwar gidan,a ƙasa ya zauna ya sake gaishe da Alhaji, banza Alhaji ya yi masa ba tare da ya amsa shi ba ya ce, "Ban fito da kai dan na ƙyale ka ka ci gaba da yawo sakaka ba, na fito da kai ne dan ka je kauyen ku ka nemo min inda Sweet H take ka sanar dani,idan ka kuskura ka ƙi sanar dani inda take zan ɗauke iyayen ka da kai kan ka na dawo da kai nan,azabar da zan sa a gana maka sai ta fi wadda ka sha a baya,ka fahimce ni da kyau ko?" Tinda Alhaji ya fara magana Sule ke gyad'a kai alamar yana sauraron dik abinda Alhaji ke faɗi,shi dai babban burin shi bai wuce su sallame shi ya koma gida ba. Akwatin shi Zalɓe ya wurga masa sannan ya damƙi hannun shi ya ɗaure masa idanu da wani farin ƙyalle,tankaɗa ƙeyar shi ya yi suka fara tafiya,sun jima suna tafiya kafin Sule yaji an wurga shi cikin mota shi da akwatin shi,gyara zaman shi ya yi da kyau yana hamdala a cikin ran shi,sai da mazajen suka gama hirar da za su yi sannan suka tada motar suka fige ta. Sule na nan zaune yana ayyana abubuwa da dama cikin ran shi yaji an taka wani wawan burki,motar na gama tsayawa aka buɗe inda yake aka damƙi hannun shi da kayan shi aka wurga su waje,ƙarar tashin motar da kurar da ta buɗe Sule ne ya bashi tabbacin su Zalɓe sun wuce, cikin sauri ya kunce idanun shi ya hau juye-juye,gaba ɗaya bai gane wajen da yake ba tinda dama shi baƙo ne a

Chapter 54 of 70