daga burika na shine in samu mazaunai irin naki, ba manya ba, ba qanana ba, masu shape kamar an auna, wannan shine dalilin da yasa sanda na tara kuɗi masu yawa na je aka yi min BBL,"
Baki sake mommy ke kallon Billy da ke shayar da ita mamaki da kalaman ta, cikin tsananin mamaki tace
"Menene kuma BBL ni Hadiza?"
"Brazilian Butt Lift kenan, ana amfani da kitsen sassan jikin mutum ne a qara masa a mazaunan sa, misali, za a iya cire kitsen bayan ki ko cikin ki ko cinyoyin ki duk a tara maki su a mazaunai, shi yasa zaki ga wasu na da irin jikin ki, nan kuwa ba haka Allah ya yi su ba su suka je aka yi musu da kud'in su,kamar dai ni,"
"Yanzu Billy jiki na dama yana da kyawun da har wani zai ji sha'awar dama ya zama nashi?"
"Mommy what are you saying? Baki da ido ne? To me ya sa mazajen garin mu musamman masu kuɗi da 'yan boko ke ta nuna maki soyayya? Ba dan shegen wulaqancin da kika zuba masu ki na kin kula su ba da kin jima da zama mai kud'i tun a qauyen Ba mugu,"
"To amma Billy soyayyar tasu ai ba ta domin Allah bace, jiki na suke so da na yi musu maganar aure suke guduwa qarshe har kowa ya dena sunsuna ta"
Dariya Billy ta yi tace,
"Wai sunsuna kamar wata karya, ke tunda fa ki ka zo kika dena maganar yayana, wato kin ga inda zaki dinga samun nerori kin yada shi ko? Alqawari be ce haka ba fa mommyn Ɗan liti,"
"Ba haka bane Billy, muna gaisawa sosai ma, dan ko jiya da dare sai da muka yi hira da shi kafin na yi bacci, bari ma ki ga wasu zafafa da ya tura min d'azu,"
Wayar ta ta janyo suka kwanta sosai a gadon Billy suka fara kunna videos ɗin da suka rikita musu lissafi cikin qanqanin lokaci, a hankali Billy ta yi amfani da wannan damar ta fara taɓa Mommy, nan take shaid'an ya yi rinjaye suka dulmiya cikin sab'on Allahn da ke girgiza al'arshin Allah, sab'on Allahn da ya fi zina zunubi,sun jima a haka Billy na daf da samun cikar burin ta akan Mommy hankalin mommy ya dawo jikin ta, da sauri ta ture Billy da ke samanta ta na faɗin,
"Meye haka muke yi ne Billy? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una meya same mu haka?"
"Dalla ki tsaya mu qarasa abinda muke yi kin wani tashi kina abu kamar baki son abinda nake yi miki,"
"Ba zan iya wannan ba Billy, ke mace ce fa 'yar uwa ta,wannan ai qazanta ne,"
"Qazanta? Amma kike bari namiji ya taɓa ki? Meye marabar dambe da faɗa?"
"Za a iya yin faɗa ba tare da kokowa ba, amma shi dambe dole sai jiki ya gogi jiki, Billy wannan abun ya yi qazanta da yawa ba zan iya irin wannan ba, wannan ɗin ma da nake yi bana fatan na dawwama a cikin shi,"
Cikin ɓacin rai Billy ta buɗe wa Mommy qofa tace,
"Fita ki tafi d'akin ki sai da safe"
Jiki a mace Mommy ta riqe hannun Billy tace,
"Fushi ki ka yi? Dan Allah ki yi...."
"Fita ki tafi d'akin ki nace, bana son surutu da na hau live a TikTok d'ina zan samu wadda zata maye min gurbin ki har da qari, kema ki yi joining ki sha kallo yarinya ni ba macen da wata mace zata wulaqanta bace,ki duba zaki ga yanda nake da daraja a wajen mata, a biya min buqata kuma a biya ni da nera ke wani lokacin ma har da daloli biyana ake yi, bana nima zan gagara na dena tsoron kowa, zan fito da dukiyar da nake da ita duniya ta shaida, ki je sai da safe"
Gaba ɗaya sai mommy ta ji kamar bata kyauta ba, amma ba yanda ta iya dan kuwa Billy ta hasala da yawa, fita tayi daga d'akin ta na share kwallar da ta fara zuba mata abinda ya faru tsakanin ta da billy na sake bijiro mata a kwanyar ta, wannan ai qazanta ne,kuma abun kyankyami ne hakan a wajen ta,da wannan tunanin ta shiga d'akin ta, wayar ta ta kunna ta shiga TikTok ta ga yanda matan Arewa ke ta yin abubuwa marasa ma'ana da amfani, idan kuma ta duba ta kalli videos na mutanen kudu sai ta ga ko comedy za su yi sai ya ba wa mutum nishad'i da kuma wani saqo a cikin shi, ga kuma masu tallata kayayyakin su da gwanjon su da duk wani abu da suke siyarwa, mu kuwa mutanen Arewa koda zamu tallata kayan ba kowa ne ke tallatawa da kyau yanda ya kamata ba har ya samu alkhairin da ake samu a TikTok din,matan Arewa masu zaman kan su kuwa da damar su sun fi tallata kayan mata da na maza ta yanda za su samu damar tallata kawunan su da kuma kalamai na batsa, a haka suke tara manyan followers saboda yanzu duniyar ta koma idan ka iya kalamai na batsa a yi da kai, idan ka iya sanya vidoes na tsiraici ko hotuna na tsiraici a yi da kai, idan kazo da wa'azi ko duba page ɗinka ba a yi balle a kalla har ayi following, ko da an yi following ana ganin baka yin abinda mutane ke so na kauce hanya sai su yi unfollowing ɗin ka.
Mommy na nan na kallace-kallacen mutanen TikTok kala-kala zuciyar ta na ingizata da ta yi joining live ɗin Billy ta ga me suke yi a ciki, hannunta ta saka ta yi joining ta tsaya tana jiran tsammani.
Ba jimawa kuwa ta gan ta cikin live ɗin tsundum,kunnuwan ta kuwa nan take suka fara jiyo mata kalamai da badaqalar da ake yi a live ɗin, idanunta ta rintse dan ganin wata da ta kunna camera ɗin ta ta na wasu abubuwan da duk mai hankali ba zai tsaya kalla ba, da sauri Mommy ta kashe wayar ta gaba ɗayan ta ta kife ta jikin ta na rawa sosai.
Ashe dama yaran hausawa na irin wannan mummunar rayuwar a social Media? Ita a zaton ta turawa ne kawai ke ire-iren lalacewar nan a ɗauke su a video a dinga tura musu suna gani a groups, ashe-ashe Yaran hausawa kuma musulmai suna aikata wannan lalatar,kamar wadda aka daketa akanta ta yi saurin faɗin,
"Sule...tabbas Sule ma abinda yake yi kenan, ashe shi yasa baya so ko motsi yaji ana yi ta wajen d'akin sa ya dinga fitowa yana masifa kenan ana damun shi yana bacci, tabdijam ! Ya zan yi yanzu to? Na zauna in ci gaba da wannan rayuwar ko kuma in tattara in gudu tun kafin na yi lalacewar da ba zan iya juyawa ba?"
*To makaranta Mommy na neman shawarar ku*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
PAGE 15:
Tunda aka yi faɗa tsakanin Baabaa da Innoh suka dena yi wa junan su magana, Baabaar ce ma watarana takan leqa daga tsaye idan Yadiko na yi wa Innohn gashin baya tana zunduma ihu ta yi mata sannu tare da faɗin,
"Ohh ni Baabaar Abbe ciwo ya samu masu baki shikenan kuma hayyaroto ya qaru, Allah ya sawaqe to,"
A duk lokacin da Baabaa ta faɗi haka sai dai Innoh ta yi k'wafa kawai dan ita kaɗai ta san me take qullawa a ranta za ta aikata wa Baabaa a duk sanda ta ji sauqi, Yadiko kuwa yau kwana uku kenan da faruwar abun bata gaji da zuwa taimaka wa Innoh ba, domin kuwa a ranar da abun ya faru ma ita ta taimaka mata ta kai ta d'akin ta, ba godi bare na gode daga wajen Innoh amma haka take hidima da Innohn, watarana ma sai dai ta dinga ja mata Allah ya isa dan a cewar ta da gayya take danne mata bayan da ruwan zafi duk bakin su ɗaya da Baabaa so suke yi su ga bayan ta.
A kwana na huɗu da faɗan ne Munir ya zo qauyen Ba mugu, gida kuwa ya cika da murna da farin cikin yara da manya dan kuwa ya zo musu da tsaraba sosai, doya kanta ya kawo ta kai d'auri biyu,ga dankalin turawa cike da qaramin buhu, shinkafa buhu ɗaya taliya da makaroni kowanne kwali d'ai-d'ai, sai katon ɗin maggi ɗaya, motar da ya zo da ita ma abin kallo ce haka yara suka bi suka yanyane ta ana ihun baqon Baabaa na Abuja yazo, wanda jin hakan ba qaramin qona ran Innoh yake yi ba.
Munir yafi kama da Baabaa a kaf jikokin ta,sai dai shi yana da manyan idanu wanda ya d'akko daga wajen mahaifiyar shi, fari ne shi tasss kyakkyawa mai qaramin jiki kuma bashi da tsaho sosai, gashin kan shi irin na fulanin nan ne mai nannad'ewa ya tara shi kuwa sosai kamar a yi masa kitso,sai dogon gemu da ya dace da qaramar fuskar shi, yara sai zuwa suke yi suna kallon shi suna faɗin albarkacin bakin su game da kyawun shi, Sadeeq kuwa tinda Munir ya isa garin da hantsi duk inda ya sanya qafa shima nan yake ajiye tashi, sai aka yi sa'a kuwa tasu ta zo ɗaya da yaron, dan kuwa Munir ya yaba da halin shi da natsuwar shi,yaro ne mara surutu sosai,ko da zai yi magana ma to mai ma'ana yake yi.
Lokacin da Sule ya dawo daga yawon shi ya tarar da had'ad'd'iyar motar Munir a qofar gidan su sai ya samu kan shi da tsayawa ya k'yafe ya dinga ɗaukan hotuna kala-kala ba tare da ya san motar ko ta waye ba.
Yana gamawa ya shiga ciki ya doka sallama, sai ya ga takalma masu kyau da tsada a qofar d'akin Baabaa, Innoh ce zaune a tabarma a tsakar gida ta jinginu da gini sanye da qatuwar rigar sanyi saboda sanyin da aka fara yi na ratsa ta ,a dole aka yi dabarar da aka zura mata riga Yadiko ta kamo ta ta zaunar da ita tsakar gida, dan kuwa tana son ta ga k'wal uwar daka itama sai dai baqin hali ya hana ta sakin ran ta a yi murnar zuwan Munir ɗin da ita.
Sule ne ya ja bokitin qarfe ya zauna a gaban Innoh sannan ya ja kwanon da ke gaban ta ya buɗe, alale ce cikin ragowar kwantan da Ameerah ta dawo da shi daga talla sai kuma tsokokin nama da ta uzzira wa Ɗan liti ya siyo mata, a cewar ta tana da buqatar cin nama kafin bayan ta ya dawo dai-dai.
"Ajiye shi dan uban ka, kana can kana yawon tazubar uban ka ya siyo min dan na ci na maida komad'a tinda an dage sai an ga baya na a gidan nan,yau da kana nan wata qarmasasshiyar tsohuwa ta isa ta sheme ni ne? Amma kai kullum kana can waje kana yawo, idan ka dawo gida kuma kana d'aki kana baccin asara"
"Yasin se na ci nima wa ya ce ki ajiye baki cinye ba? Naman ma duk ya wani bushe, Innoh waye wai ya zo na ga wata arniyar mota a waje? Ko Yah Munir ɗin ne ya iso?"
"Yaya a gidan uwar ka? Idan na sake jin ka kira shi da Yaya sai na ci maka mutunci, yaron da tun da ya zo sannu bata haɗa shi da kowa ba a gidan yana can wajen kakar shi?"
Yadiko ce ta fito zata hura wutar girkin la'asar ta ce,
"Kaiiii Innoh, har d'aka fa ya shiga ya gaishe ki, da ya gan ki babu lafiya ma sai da ya yi miki ya jiki sannan ya shiga waje na nima muka gaisa ya wuce d'akin kakar shi, sannan menene a ciki dan ya kira shi da yaya be girme shi bane ko me?"
Qanqance ido Innoh tayi sannan tace,
"Sannu guntsi fesa, da ke nake ko da d'ana? Ni fa bana son sa ido sana'ar banza sana'ar da ba uwa ba riba,na kasa dake balle nace ki ɗauka? Mamalam gida duk ya zama gidan 'yan kuci ku bamu, se ki bari idan an kasa doyar se a baki kason ki kin ji daɗin shiga maganar da bata shafe ki ba kwad'ayayyiya kawai"
"Innoh ni ce kwad'ayayyiyar? Dan na faɗi gaskiya shine zaki kirani da kwad'ay....."
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una! Allah Allah Allah ka nuna min ranar da zan shigo gidan nan in ga ana hirar arziqi, kai in gan ku shiru ma kowa na harkar gaban ta ze fi min alkhairi akan wannan tashin hankalin da kuke yi a kullum, habaa ! Ina shi Mannirun yake?"
Yadiko ce ta iya amsa masa da,
"Yana d'akin Baabaa, Sannu da zuwa Malam"
Ko kula ta be yi ba ya wuce d'akin Baabaa da ke zaune ta tasa shalelen jikan ta a gaba da abinci kala-kala da ruwan pure water leda uku a faranti se mangwaro masu zaqin gaske, shi kuwa Munir ya dage yana ta shan mangwaro bayan ya gama cin dambu,Sadeeq na gefen shi yana shan mangwaro shima, Baabaa kuwa na ta zuba masa hira.
Labulen d'akin Ɗan liti ya saki bayan ya shiga ciki ya samu gefen gadon qasar Baabaa da ya sha katifa ya sha lullub'i ya zauna,hannun sa ya zura ya ɗauki mangwaro ɗaya a ƙwarya ya kafa masa haqora sannan ya amsa gaisuwar Munir da ke murmushi yana gaishe shi,
"Lafiya qlou Manniru ka zo lafiya? Ya baban naka da ita Hajiyar? Kuna nan lafiya qlou da sauran 'yan uwan naka dika ko?"
"Lafiya qlou kowa yake Baba, sun ce ma a gaishe ka,"
"Allah sarki ina amsa wa, kai kuma zaman qauye ne yake baka sha'awa ka taho yi mana hutu,mu muna so mu gudu mu hyiga birni kai kana zuwa qauye"
Baabaa ce tace,
"Yo ba dole ba kai kuwa Ɗanli uwar da ta haifi uban sa na qauye ai dole ya kawo ziyara,"
Munir ne yace,
"Ah ah fa tsohuwa ki gyara kalaman ki, kice Babar Baban shi tana qauye, ya daga zuwa na zaki dinga zagi na a fakaice"
Dariya Baabaa da Ɗan liti suka yi, suka ci gaba da hirar su ta yaushe gamo, Ɗan liti bai baro d'akin ba sai da ya ci ya qoshi saboda dama girkin Innoh ne Yadiko ke taimakawa ta yi tunda Innoh dai bazata iya ba, kuma baya son zama a wajen Innoh saboda yawan qorafi da kan qara.
Qarfe shida da minti goma na yamma Yadiko na madafi ta na kwashe tuwo gefe ɗaya kuma miya na saman wuta tana ci gaba da dahuwa. Saddiqa ce ta dawo daga Islamiyyah a gajiye ta na shiga gidan ta yi sallama ta saqale hijabin ta a igiyar shanya ta ɗauki buta za ta zaga dan kuwa a matse da fitsari ta dawo daga makaranta, cikin saurin da take yi zata shiga band'aki ta yi karo da Munir ya fito hannun shi riqe da buta ya gama kama ruwa, da sauri ta ja da baya ta yarda butar hannun ta sannan ta dafe qirji ta na kiran sunan Allah, dan kuwa bata san da zuwan shi ba, sannan bata taɓa tsammanin ganin shi ba.
"Ya salam kula kar ki faɗi,"
"Waye kai ka shigar mana bayi? Innoh Yadiko ku zo ku ga wani ya shigo mana gida"
Baabaa ce ta zo ta ga abinda ke faruwa cike da washe baki tace,
"Ke Yayan ku ne na Habuja da na ce maki zai zo tun kwanakin baya, ai shine ya zo"
Da sauri Saddiqa ta sake kallon shi da kyau, a sannan ne ta gano kamannin da yake yi da Baabaa, cikin jin kunya ta durqusa ta ɗauki butar da ta faɗi ta mayar gefe ta gudu d'akin su na 'Yanmata, Ameerah ta tarar a kwance ta na ta bacci wanda da dikkan alamu ta jima tana yin baccin babu wanda ya d'aga ta,labulen windown d'akin su ta d'aga dan kuwa kyawun Munir ya burge ta, ta na so ta sake yin ido huɗu da sumar kan shi, ta na buɗewa ta leqa a hankali idanun su ya sarqe a cikin na junan su, murmushi ya sakar mata mai kyau, ita kuwa nan take ta saki labulen ta maqale a jikin ginin d'akin ta na qanqame jikin ta tare da sakin murmushin da bata san tana yi bama, a hargitse cikin hargowa da hayagaga Ameerah ta farka ta na faɗin,
"Wanne ɗan iskan ne ya taka min hannu? Ke Saddiqa uban wa yace ki taka ni ko baki da ido ne?"
Da sauri Saddiqa ta matsa ta na zaro ido dan bata ma san ta taka Ameerah ba,
"Dan Allah Yah Ameerah ki yi hakuri ban san na taka ki ba"
"Sannu balama, ina hankalin ki yake har da zaki taka ni amma kice baki sani ba? Dalla malama matsa ni na wuce"
Tashi Ameerah tayi ta fita tsakar gida ta tsartar da yawu sannan ta yi miqa tare da zabga wani ihu a cikin miqar tata ba Kiran sunan Allah babu komai ta nufi d'akin Innoh dan kuwa yunwa take ji.
Munir da ya koma d'akin Baabaa duk ya ga abubuwan da Ameerah ta yi kafin ta shige d'akin Innoh, cikin magana kamar ta me rad'a yace,
"Ikon Allah, lallai gidan granny ya haɗa mutane kala-kala,Allah yasa na gama ganin mutanen gidan kenan kar daga baya kuma na ci karo da me haqoran zarto"
Cike da dariya Sadeeq da baya magana sosai yace,
"Ai bata nan ta na can birni aikatau ba lallai ku haɗu ba ma,"
"Kana nufin akwai me haqoran zarto a gidan nan?"
"K'warai da gaske Yah Mommy kenan,ta na can kano aikatau ai bata jima da tafiya ba ka zo dan bana jin ta cika sati yanzu da tafiya"
"Allah me iko, to ita waccan beautyn da na gani da uniform fa?"
"Yah Saddeqa kenan,"
"Hummm, tashi muje ka raka ni can gidan na dan watsa ruwa kafin a yi magariba dan na ga lokaci ya kusa,"
Sallama Baabaa ta yi ta shiga ta ajiye masa fura da nono da ya sha damun hannu sannan tace,
"Ga fura fa ko zaka ɗora ka danne abincin da ka ci da ita"
Zaro ido waje Munir ya yi sannan yace,
"What ? No alhamdulillahi na qoshi gaskiya ina ki ke so na zuba ta?"
"A cikin ka mana, ku fa mutanen birni baku son cin abinci shi yasa gaka nan kamar a hure ka ka faɗi,"
"Kar dai ki zagi qaramin jiki na dan kuwa ke na gado,kema da kike ci da yawa baki wuce ni ba ai, gwanda ma ni na fi ki qiba, ba wannan ba ma na ce ina keys ɗin gidan can suke zan je na watsa ruwa"
"Ina me?Kai ni idan zaka yi min yaren da na sani kayi, idan ba zaka yi ba mu sha zaman kurame dani da kai ah toh"
"Yi hakuri Granny ki bani makullin gida zan je na yi wanka an kusa Kiran sallah"
"Yanzu na ji magana,gasu nan, amma ka jira Saddeqa ta sake share maka waje dan tun sanda baban ka yace zaka zo na sa aka share ba a sake bud'ewa ba, Saddeqa ! Saddeqa ke !"
"Na'am !"
"Zo taho da shijabin ki ki share gidan Baban gida yaron nan ya samu ya je ya huta an shawo hanya"
Ameerah ce ta fito tana sud'e hannun ta, Munir ya fito shi da Sadeeq daga d'akin Baabaa, tsayawa ta yi hannu a baki tana kallon Munir ɗin da Innoh ta gama gargad'in su akan kar ta kurkura ko da wasa taga ɗayan su ya kula shi,kallo ɗaya Munir ya yi mata ya wuce ta ya miqa wa Saddeqa keys ɗin gidan, a kunyace ta Karb'a saboda ta kula da kallon da Munir ɗin ke bin ta da shi, har zata fita Munir ya kirawo sunan ta ta tsaya cak, a hankali ya taka wajen ta yace,
"Mu je na ajiye ki a gidan ko? Tunda nima can ɗin zan je, Sadeeq taho ka raka mu ko?"
Suna fita waje Ameerah ta koma d'akin Innoh tace,
"Ke da wancan balaraben kike ta zagi kina d'ebewa albarka kike cewa kar mu kula shi? To alqur'ani ni dai na yi mijin aure anan, ko za a kahye ni ba zan qi kula hyi ba ni hyi zan aure,"
Cikin Fushi Innoh ta ce,
"Ai kuwa se dai ki mutun dan kuwa in dai ina numfashi ba zaki aure shi ba shegiya matsiyaciya, mutanen da ba qaunar mu suke yi ba shine kike so ki jawo min matsala, ki dube ni ki ga yanda kakar shi taso sabauta min baya Allah ya taqaita wahala shine kike maganar kina son jikan ta? To sai dai kuwa ki mutu,"
Cike da rashin kunya da qunquni Ameerah ta bar d'akin ta wuce nasu ta kwanta tana rusa kuka tare da cin alwashin duk rintsi duk wuya sai ta ja ra'ayin Munir ya fara son ta har ma ya aure ta.
************************
A cikin kwanakin da Mommy tayi Billy bata nan duk sai ta ji gidan ya yi mata girma, Hajiya K'waisa na yawan fita bata da lokacin zama a gida sai tsakiyar dare ake dawo da ita watarana,haka zata dawo da damman kuɗi ta shige d'akin ta tana rawa tana shewa,dan haka daga ita sai masu aiki da masu koya mata kwalliya da tafiya,magana da dai duk wani abu da ya kamata ace ta iya.
Lokuta da dama cikin dare idan ta fito zata tarar ana tsarawa Hajiya k'waisa kwalliya ta garari, ana gamawa za a ɗauke ta hotuna masu kyau ta ɗora a shafukan ta na internet sannan ta yi vidoes nan ma ta yi posting, watarana sai daf ana kiran sallar asuba zata gama abubuwan da take yi ta kashe wi-fi a goge mata kwalliyar ta ta wuce sama, Allah ne masani tana sallah bata sallah take kwantawa bacci sanin gaibu sai Allah.
Kwanan Mommy takwass cif a gidan da dare ta fito daga d'akin ta kamar koda yaushe dan ganin yanda Hajiya K'waisa ke gabatar da lamuran ta cikin dare ta ji Hajiyan na waya da wani wanda bata san ko wanene ba, cikin rausaya da fari kamar wani mace yake faɗin,
"Eh gaskiya she is not ready yet, dan kuwa wannan kifin ba a kowanne ruwa yake rayuwa ba, ka jira idan aka gama bikin new year wataqila ka samu shiga,"
Hajiya K'waisa ta jima ta na sauraron me ake faɗa daga ɗaya bangaren kafin ta tashi zaune da ga kishingid'ar da ta yi ta yarfa hannun ta ɗaya sannan ta mayar ta kama hab'a tace,
"Da gaske zaka iya bata waɗannan maqudan kud'ad'en a lokaci ɗaya? To indai haka ne babu damuwa sai ta fara da kai, kaine first customer ɗin ta kenan, amma kasan ni yarana fa ba kamar saura suke ba, pay before service ne su,ka yarda zaka tura kuɗin ne yanzu ko kuwa?"
Shiru ta sake yi na wasu daqiqu kafin tace,
"An gama na waje na, Heeeee ragassss ! Ni fa shi yasa kake burge ni dan baka wasa, duka d'auka ne kai, Allah dai ya biya na waje na masu kashe kuɗi a sab'on Allah a jefa kaɗan a aikin Allah"
Mommy na jin wannan hirar ta tabbata akan ta ake yin wannan maganar, cikin sand'a kamar yanda ta saba lab'ewa ta kalli Hajiya k'waisa ta koma d'akin ta yau ma haka ta yi, tana shiga d'akin ta maida qofar ta a hankali ta rufe ta na maida numfashi,kallon kanta ta yi a madubin dake gaban ta ta juya jikin ta ta sake, bakin ta da ya sha man leb'e ta kalla taga yanda yake sheqi idanun nan sun sha eyelashes, ga uban gashin doki an saka babu mai cewa ba nata bane saboda yanda ya mannu da kan ta, shape ɗin ta mai kyau cikakke ta kalla ta ga yanda qirjin ta ya sake cika saboda supplements ɗin da ake bata tana sha na gyaran fata da jiki.
"Ohh ni Mommy yanzu da gaske harkar karuwanci zan faɗa tsundum? Ko nawa bawan Allahn nan zai biya akai na kuma oho? To ko dai shine wanda yake ta yi min naci a TikTok d'ina ne?"
Da sauri ta nufi wayar ta ta kunna ta shiga TikTok ɗin ta, Dm ɗin ta ta duba, da messages ɗin mutumin da ya nace mata ta fara cin karo kamar haka.
*Sweet H da alama ni ne na yi nasarar samun ki a matsayin wadda zata taya ni yin hutun weekend*
Sai stickers na banza da ya tura mata kala kala wanda ya sanya ta shiga wani yanayi na tsananin buqatuwa da abinda ya nuna matan, cikin rawar hannu ta shiga wajen yin reply ta danna masa heart ta tura sannan ta kashe wayar ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 70