Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da Sallau,duk ranar Juma'a kuma yana zuwa gidan yari ya kaiwa Alhaji abinci,ba dan komai ba sai dan zaman tare da ya taɓa haɗa su a baya. ******************* Wani babban ɗakin taro ne dake cikin Bayero University Kano cike da mata danƙam suna sauraron wata baiwar Allah da ke zuba bayani,ina karasa shiga wajen na ga Billy riƙe da abun magana tana faɗin, "....Dan haka ƴan'uwana mata ina yi maku nasiha da ku ji tsoron Allah,ina son wannan labarin da na baku na rayuwar mu da ni da ƴar'uwata da muka yi a baya ya zame maku babban darasin da zaku gina rayuwar ku akan tafarkin musulunci,domin bariki ta yi min mummunan tabon da ba zai taɓa gogewa ba,sannan ta sa na rasa ƴan'uwana,da garin mu da duk wani wanda ya sanni, tunda babu mai son a gammu tare dashi,ba komai ya kawo haka ba sai mummunan tabon da na yi wa kaina,jinyar da na yi kuwa kaɗai ta ishi mutum ya ji tsoron faɗawa halaka da saɓon Allah,mu yi ƙoƙari iyakar iyawar mu muyi amfani da social media ta hanya mai kyau,hanyar da zata yi sanadiyyar shigar mu aljannah,ba wuta ba,mu gujewa zinar da ake aikatawa ta cikin wayoyin nan na zamani,saboda tana kai mu ga aikata zinar zahiri,anan zan tsaya saboda lokaci da ake nuna min,ina yi muku fatan alkhairi Allah ya tsare mana imanin mu." Abun magana ta miƙa ta sauka a hankali sanye da dogon hijabin ta da ya rufe cikin da take ɗauke da shi,fuskar ta rufe take kiruf da niƙabi,ta samu gefen da Anam take zaune ta zauna itama. Bayan an kammala taron ne ta shiga mota Any ta sauke ta a gida,daga nan Any sai ta tuƙa motar ta wuce shagon su da customers ke ta yi mata waya da messages suna jiran ta,tana isa bakin shagon taga dandazon mutanen dake jiran ta,sai kawai ta godewa Allah a ran ta sannan ta ce, "Tabbas duk wanda ya yi haƙuri a rayuwa ya bi Allah,to Allah zai azurta shi da halal daga ƙarshe,wanda ya yi gaggawa ya bi hanyar shaiɗan to zai samu duniya ƙarshe ta barshi cikin wuya,ko ban yi aure ba ina godewa Allah da ya bani abinda zai riƙe mutunci na,na yarda da Allah na san komai lokaci ne." Fita tayi ta faɗa shagon nasu ta fara sallamar mutane,fuskar ta ɗauke da mabayyanin farin ciki. Rayuwar GIDAN ƊAN LITI ta ƙayatu ta kuma kyautatu,zaman Baaba da Innoh zama ne na mutunci da mutunta juna,Ɗan liti ya bayar da motar shi haya ana fitar da shi kullum,shi kuwa Saddiqa ta yi amfani da albashin ta da taimakon da Munir ya bata ta buɗe masa shagon saida kayan gyaran mota da saida baƙin mai,a duk sanda sadeeq bashi da lecture yana zama da Ɗan Liti a shago yana taya shi sayar da kayyakin. *Alhamdulillahi! anan na kawo ƙarshen labarin GIDAN ƊAN LITI da ikon Allah,ina fatan zaku yi amfani da darusan dake ciki,saboda ni da ku mu samu lada. Inda na yi kuskure ina roƙon Allah ya yafe min ya shafe shi a rubutu na. Allah ya sada mu da alkhairi Mutanen gidan Uncle Ɗanli zan yi kewar ku sosaiiiii.*🤍 *Ku baza kunnuwan ku masu sauraren na YouTube,sabuwar channel ɗina na nan na dakon soyayyar ku kamar yanda nake nuna maku tawa soyayyar ta hanyar kawo maku daɗaɗan labarai. Kar ku manta na fara karanta labarin GIDAN ƊAN LITI a tasha ta mai suna Hamida Sanusi Channel tare da littafin MAIDA TSOHUWA YARINYA anan gaba ina fatan zan saka wani littafin da zai ƙayatar daku.* *Wanda na yiwa alƙawarin document ku yi haƙuri akwai wasu gyare-gyare da nake yi kafin a haɗa,da zarar an haɗa zan tura maku. Idan kuma kuna sauri ku duba channel ɗina dake WhatsApp ku karanta daga farko ko wattpad.* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 70 of 70