Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na tabbata babu mai aure na saboda abinda kika aikata,Allah ya isa tsakani na dake ba zan taɓa yafe miki ba." Cikin kuka Fadila ta ratsa zata wuce su,Billy da jiri ya ke ɗiban ta saboda gano abinda ke faruwa ta tafi luuu zata faɗi,gefe Fadila ta koma Billy ta faɗi yiiiiff a ƙasa,cikin kuka Fadila tace, "Ki tattara dake da matar taki ku bar mana gida kawai kafin mutanen gari su gane kuna nan,baku da amfani a cikin al'umma tinda kuka ƙetare iyakar Allah irin haka." Cike da tsawa Shamsu ya ce, "Idan baki faɗa min abinda yake faruwa ba kika sake magana sai na tattaka ki anan,haka kawai daga dawowar yarinya ku saka ta a gaba ke da Baba kuna faɗin munanan kalamai akan ta?" Cike da tsawa itama Fadila ta ce, "Dole ne mu faɗi munanan kalamai akan ta saboda abinda ta aikata ya yi muni,Yah Shamsu ina zaune a aji a islamiyya naga an yi group ana magana ƙasa-ƙasa ana kallon wani abu sai a juyo a kalle ni,gajiya nayi da kallon da ake yi mini na leƙa,ina zuwa na ga...ina zuwa naga videon Yah Bilki namiji na amfani da ita ta baya,wani na gaban ta wani na saman kan ta,ban gama kallon wannan ba wata tace,ai tana da video ɗin ta ma wanda take ita da matar ta,yau sati biyu kenan da ta d'akko daga vidmate tana tsoron nunawa mutane,ina duba videon Yah Bilkisu ce da wannan la'ananniyar suna sumbatar juna tare da yin abubuwan da basu dace ba,ki faɗa min shin har yanzu ke musulma ce ko kin fita daga addinin namu shima?" Gaba ɗaya mutanen wajen sun daskare da mamaki da tsoro,Billy kuwa Any ce ta taimaka mata ta tashi,rungume junan su suka yi suna kuka,cikin kuka Billy tace, "Na tuba na daina dik abinda idanun ki suka gane maki Fadila,wannan shine dalilin daya sanya na dawo gida,dan girman Allah ku yafe min...Baba..Baba dan Allah ka tashi ka yafe min,ba zan sake maimaita abinda na yi a baya ba saboda son abun duniya da son zuciya,na tuba ga Allah kuma har abada zan mutu ina neman gafarar Allah,dan girman Allah ku yafe min, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una Anam dan Allah ki faɗa musu mun tuba,hisba ma sun shaida mun tuba." "Mu bamu shaida ba Bilkisu,kin san irin kunyar da kika sa naji yau a kasuwa kuwa? Yaron shagona ke goranta min akan abinda kika aikata saboda ya yi laifi na yi masa faɗa har ta kai ga na kore shi,yana tafiya ya tura min videon ki subhanallahi,gaki nan tsirara maza uku na amfani dake da mata guda biyu,ke karya ce ! Maza har uku akan ki ga mata biyu dik ke kaɗai? Bayan yaron nan ya tura min sai da ya turawa mutanen dik da yake da lambar su a wayar shi, kafin wani ɗan ƙanƙanin lokaci shagona ya cika da mutane ana zagi na,da ƙyar wasu bayin Allah suka kare ni suka ce ai babu laifi na dan kin aikata wannan abun,tinda guduwa kika yi kika bar gida,Bilkisu kin cuce ni,kin cuci zuri'a ta da ke kan ki, yanzu wa zai aure ki tinda kin auri mace ƴar'uwar ki?" Rarrafawa Billy tayi gaban mahaifin ta tana kuka ta kama ƙafar shi ta ce, "Baba dan girman zatin Allah ka yafe min,na tuba ba zan sake ba,Baba ka tausaya min ka yafe mi...." Wani irin gigitaccen mari ne ya sauka a kuncin Billy,bata damu da ta sanya hannu ta sosa ba balle ta kare koda wani da yafi wannan zai sauka a fuskar ta ta,duka Ta Annabi ta rufe Billy dashi ko ta ina tana faɗin, "Kin yi asara Bilkisu,kin yi wayon banza,da nasan haka zaki zame mana masifa a rayuwa da kashe ki nayi ko na ɓarar da cikin ki,ku tashi ku fita ku koma inda kuka fito dan uban ku." A gigice Ta Annabi ta ajiyewa Ameerah jaririn ta a ƙasa ta nufi kitchen ta ɗako ƙaton itace ta yo kan su Any a guje zata shirga musu,cikin zafin nama Shamsu ya riƙe ta,ihu ta hau yi tana kuka tana zagin su Billy,da ƙyar Shamsu ya samu nasaarar kai Ta Annabi d'aki sannan ya dawo dan ya taimakawa Mai Dusa ya kai shi ɗaki shima,da ƙyar ya iya ɗaga mahaifin nasu daga ƙasa suka fara takawa zuwa ɗaki,sai da suka gota Billy dake tsugunne tana kuka Mai Dusa ya tsaya ya ce, "Ba za ki zauna min a gidana ba,dan haka ki tabbatar da kafin wayewar gari kin koma inda kika fito,ban damu da ki shiryu ko ki ƙara lalacewa ba,kin riga da kin bar mana tabon da har ƙarshen rayuwar mu zamu yi ta dakon shi." Da sauri Billy ta sha gaban su Shamsu ta tsugunna gaban Mai Dusa ta ce, "Na amince zan koma inda na fito Baba,amma ina roƙon ku kamar yanda na tuba ga Allah,dan Allah kuma ku yafe min,ko bajima ko ba dad'e ina nan zan jira yafiyar ku a gare ni,zan jira ku ku yafe min saboda na sani na cutar da ku." Any na gefe tana ta kiran wayar Man bata shiga,yanzu taya za su bar garin nan ba tare da wata masifar ta sauka akan su ba? Suna murna sun gudo ƙauye daga birni saboda su samu mafaka ashe sun fafake mafakar tasu tun kafin su samu fakewa? Mai Dusa bai kula Billy ba suka wuce ɗaki shi da Shamsu,banda kuka babu abinda Ta Annabi take yi,Ameerah kuwa jikin ta dik ya yi sanyi saboda jin wanda suka fita fitsara,sai jijjiga yaron ta take yi amma ya ƙi shiru,goya shi tayi sannan ta ce, "Bari na kirawo muku babana yazo ya fitar daku daga garin nan,dan kuwa babu makawa mutane idan suka gama hasala za su zo su ɗauki mummunan mataki akan ku,wanda ma bai aikata abinda yakai naku muni ba sun ɗauki mataki akan shi balle ku?" Jiki na rawa ta shiga ɗakin ta ta d'akko wayar ta,dik yanda ta dinga Kiran wayar Ɗan liti bai shiga ba, ƙarshe ma baturiya ce mata tayi wayar a kashe take,cike da tsananin tashin hankali Shamsu ya fita ƙofar gida,ya dawo,ya sake fita ya dawo,ya rasa wacce iriyar shawarar zai yanke,shi me yasa bai samu damar ganin videos ɗin su Billyn ba? Cikin sauri ya kauda wannan tunanin yana son ya sama masu mafitar da za su bar Garin Ba Mugu lafiya. Oda suka dinga ji ana dannawa a ƙofar gida,a zaton su ma Man ne ya dawo ɗaukan su tinda Any ta tura masa saƙo,suna fita da akwatuna niƙi-niƙi sai suka ga Ɗan liti,cikin sauri ya buɗe motar ya ce, "Ku shigo na sauke ku a kano,fusatattun matasan garin nan na can fadar Sarki suna neman izinin a basu dama su ɗauki mataki akan ku dan sun samu labari wai kun shigo gari." A guje Any ta ja hannun Billy dake waiwayen gidan su suka afka motar,Shamsu ne ya buɗe bayan motar ya watsa masu akwatinan su,suna shiga Ɗan liti ya ce, "Maza ku duƙar da kawunan ku ƙasa,kar nima ku jawo min bala'i lalatattun banza,ku rasa iskancin da za kuyi sai auren jinsi,kaiii Allah ya wadaran naka ya lalace,jakin dawa ya ga na gida." A guje Ɗan liti ya ja motar shi ya bar garin Ba Mugu da su Billy dake maƙale a motar suna shan faɗa da masifar shi,da ace zai kula da kyau ma da ya hutar da kan shi,dan kuwa basa cikin natsuwar sauraren shi balle su gane me yake faɗa. Bayan tafiyar su da minti goma ne matasa suka yo zuga zuwa gidan Mai Dusa, ihu suka dinga yi tare da faɗin a fito musu da su Billy yau sai sun baƙunci lahira tinda sun ce su ƴan iska ne,ganin kamar raina masu hankali Shamsu yake yi da ya ce basu nan sun gudu da suka samu labarin abinda ke faruwa sai kawai suka afka gidan,duk wani abu mai kyau sai da suka dinga fatali da shi da sunan neman su Billy,wannan abun da suka dinga yi shine ya yi sanadiyyar suman Mai Dusa,ganin halin da ya shiga ne ya sanya Ta Annabi fitowa tana kururuwa ta ce, "Ku taimaka min miji na ya mutu,dan Allah ku fita ku tafi neman su a can waje basa nan,mu kammu mun yi Allah wadai da abinda suka aikata,a cikin jimami muke dan Allah ku barmu muji da abinda ke damun mu, Shamsu ka duba min mahaifin ka baya motsi." Shamsu ya jima da shiga ɗakin tinda ta fito tana kuka ya afka,gani yayi mahaifin nasu na da rai amma ya suma,dan haka sai ya fito ya ɗebi ruwa ya watsa masa ya gyara masa kwanciya,matasan nan kuwa sun fita saboda ganin halin da Ta Annabi ke ciki,Sun tabbata suma a cikin damuwa suke. A can hanya kuwa su Billy basu zauna a kujera ba har sai da suka bar ƙauyen Ba Mugu da wasu ƙauyikan dake kusa da shi sannan suka zauna cike da jimamin abinda ya faru,ko da suka isa kano a tasha Ɗan liti ya sauke su ya bi layi dan yin lodi ya koma ƙauyen su,dik godiyar da su Billy keyi masa bai kula su ba sai ya shige motar shi ya zauna,yana hango su suka samu abun hawa suka bar tashar. Hawaye ne suka hau zarya a kuncin Ɗan liti,yanzu da Mommy bata yi aure ba da tini da ita a wannan badaƙalar,ashe irin wannan soyayyar ta lalacewa Billy take nufin tana yi wa Mommy? ashe dama akwai irin waɗannan mutanen masu auren jinsi da neman maza ta baya bai sani ba? Kanshi ya kwantar a jikin sitiyarin motar ya rushe da kuka. "Kaicon rayuwar mu, kaico na,wace iriyar tarbiyya muka baiwa yaran mu? Me yasa muka biye wa ruɗin duniya da son abun duniya tare da jahilci yaran mu suka lalace? Yanzu ta ina zamu fara gyara tarbiyyar yaran da suka riga suka girma?" Yana tsaka da koka tashin hankalin da ya tunkaro su aka ƙwanƙwasa gilashin motar shi,a cikin dabara ya goge idanun shi sannan ya buɗe ya fita,abokan da ya yi a tashar ne suka hau hira dashi suna bashi labari akan sababbin shugabannin tashar da aka naɗa,wannan labaran ne ya ɗebe masa damuwar dake ran shi har aka zo kan shi ya fara lodi dan komawa ƙauyen Ba Mugu. A gidan Billy motar da ta ɗauke su ta ajiye su,sun jima tsaye suna kallon gidan da ta same shi ta hanyar haramun kafin su kwashi kayan su su buɗe gidan su shiga,suna shiga parlour Billy ta ware murya ta dinga kuka kamar zuciyar ta zata fashe dan baƙin ciki da damuwar da take ciki. Cikin kuka Billy ta ce, "Ya Allah mun tuba,Allah ka yafe mana,ina zamu kai wannan zunubin da muka ɗauka? Mun cutar da kawunan mu da iyayen mu,mun cutar da al'umma da muka aje musu mugun abun kallo,na gaji da rayuwar nan Allah ka ɗauki raina in huta !" Any ce ta isa gaban ta ta hau lallashin ta, ita kanta hawaye ne ke gudu a kuncin ta,bata da kowa da zai kunyata akan abinda ta aikata,amma still kunyar kanta da kanta take ji,yanzu da Malam na raye haka zai ga wannan baƙin cikin? Wata zuciyar ce ta ce mata, 'A yanzu ma da iyayen ki basu raye dik abinda kika yi mai kyau ko mara kyau ana tada su a nuna musu.' Cikin sauri ta miƙe tsaye tana faɗin, "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ! Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una! Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una! Ya Allah ka gafarta mana ka kawo mana mafita mafi alkhairi, Allah mun tuba, Allah kai shaida ne mun tuba." Haka suka dinga kuka har suka gaji suka tashi suka yi sallolin dake kan su,ko abinci basu nema ba haka suka kwanta baccin wahala mai cike da mafarkai kala-kala. **************************** Rayuwar gidan su Abdul rayuwa ce ake yin ta cike da farin ciki da kulawa,Abdul na iyakar ƙoƙarin shi dan ganin ya sauke dikkan haƙƙoƙin Huzaimah dake kan shi,wannan dalilin ne ya sanya ya saba mata da romance,ta haka yake samu ya biya mata buƙata,shi kuwa yana nan a naɗe kamar lagwani dan kuwa baya iya yin komai,watarana har tsoro yake ji idan ya ga babu wani ci gaba da yake samu akan matsalar tashi,likitoci na iyakar ƙoƙarin su akan shi,haka ma masu magungunan gargajiya suma suna nasu ƙoƙarin,dan kuwa na musamman Innah Laminde da Mai Martaba suke samawa gudan jinin nasu magani. A hankali Huzaimah ta fara son wannan soyayyar da suke yi ta wuce matakin da suke kai, kwad'ayi da son haihuwa sun dabaibaye rayuwar ta,dik yanda take dannewa tana jurewa hakan be hana ta shiga damuwa da tashin hankali ba,a hankali ta fara rama kamar me ciwo,dik tambayar da Abdul zai yi mata bata iya bashi amsa,watarana idan ya matsa mata ma kuka take yi,ya sha kiran Bilal gidan dan ya tambayar masa Huzaimah ko akwai abinda ke damun ta,ƙarshe sai tace masa babu komai,a haka suka ci gaba da rayuwa damuwa na cin zuciyar Huzaimah a boye, a zahiri kuwa tana nan tana kula da mijin ta da rainon soyayyar da suke ta ginawa. *********************** Jikin Baaba ya yi sauƙi sosai har ta warware ta koma sana'ar ta ta saida goro da ƙosai,Alhaji Baban Gida ya gaji da roƙo da lallamin Baaba akan ta koma Abuja ko ta koma gidan shi dake nan ƙauyen amma Hajiya Baaba ta ƙeƙasa ƙasa taƙi amincewa,dan haka tinda ya koma Abuja bai sake zuwa ba,sai dai Ummi da Munir sun zo yafi sau uku,watarana ma har da su Anisah suke zuwa. Wataranar lahadi da yamma Mommy na zaune a tsakar gida ita da su Innoh da Amir Naja ta sallama gidan,cike da fara'a Mommy ta miƙe tana yi mata lale maraba,Innoh ma sannu da zuwa tayi mata suka zauna aka dasa hira,waya Naja ta ɗauka ta yiwa Mommy message sannan ta sauke wayar suka ci gaba da hirar su,kallon Naja Mommy tayi a cikin wani irin yanayi na rikici da ɗaurewar kai bayan ta gama karanta saƙon da Naja ta tura mata,murmushi Naja ta sakar mata sannan ta lumshe idanun ta dika biyu ta duƙar da kai kaɗan hannunta na rawa Mommy ta ɗauki wayar ta ta hau yi wa Naja reply........... [09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 94: Sun jima suna hira kafin daga bisani Aunty Naja ta miƙe tsaye tana karkaɗe jikinta ta ce, "To ni bari na tafi gida, na san yanzu haka Goggo na can tana jirana na je na ɗora tuwon dare,gwanda ku gashi muna zaune har Innoh ta gama komai." "To sai yaushe kuma?" "Ban gane sai yaushe ba? Yaushe rabon ki da gidanmu ? Ai Goggo ma fushi take yi dake idan baki sani ba na sanar dake,ta ce tin sanda ta kori wani gajiyayyen saurayin ki mai kai kamar bushiya kika daina zuwa kwana wajen ta." Dariya suka fashe da ita sannan suka tafa kamar wasu ƙawaye,cikin dariya Mommy ta ce, "Hamzy gaye ne fa na bayan layin nan namu,nu kaina yaron nan mugun takaici yake bani, sa'an fa Ameerah ne wai amma ya zo neman aure na tsabar rashin kunya,ina sane na gayyace shi can ai, dan na san bata ɗaukan shaƙiyanci." Dariya suka sake yi, Mommy ta saɓi mayafinta dan ta raka Naja,sai da suka fita daga gidan suka ɗan yi nisa Mommy ta riƙe hannun naja ta tsaida ita,cikin damuwar da tai ta dannewa ta ce, "Aunty Naja ya haka? Yanzu ke kina nufin idan ban aikata haka ba ba zan iya komawa gidan Abdul ba har abada?" "K'warai da gaske, sharaɗin da malam ya bayar kenan,kina dai ganin wancan satin irin rashin mutuncin da kakar yaron nan ta yi mana saboda ba a kai mata shi ba,da yana gidan ubansa haka zata faru ne? Dan haka idan kina son ayi komai a gama cikin ƙanƙanin lokaci to ki amince da abinda malam ya ce kawai." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Mommy ta sauke,da wannan maganar suka yi sallama da Naja ita kuma ta kama hanyar gida zata koma,tafe take tana tuna irin dokokin da Innah Laminde take gindaya mata akan Amir,wata iriyar tsana Innahr take yi mata kamar bata taɓa zama surukar ta ba a baya,me yasa Innah Laminde ta kasa gane dik abinda tayi akan kishin mijinta ta aikata shi? Zuciyar ta cike da tunani ta koma gida,dole ne ma ta amince da wannan shawarar saboda ta samu ta maida auren ta da Abdul. ******************************* Billy da Any sun maida rayuwar su ta koma abun sha'awa ga dik wanda bai san su ba a baya,domin kuwa sun tattare gaba ɗaya dukiyar su sun kyautar da ita ga gidan marayu,hisbah kuwa ta yi musu ƙoƙari ta basu kyautar kud'ad'e,da jin labarin su kuwa gwamna ya bada kyautar sabon gida da motar hawa,tare da jarin million uku aka basu,sanda wannan kyautar ta riske su sun yi kukan farin ciki kamar ba za su dena ba,a yanzu suka tabbatar da cewa idan bawa ya yi tuba na gaskiya zuwa ga ubangijin shi,to lallai Allah zai musanya masa da abinda yafi saɓon Allah'n da ya bari a baya,a baya Billy ta damu da kyautar zunzurutun kud'ad'en da Any ta bayar masu matuƙar yawa, ga kadarori da gidajen su da suke ciki dik ta haɗa ta bayar wa mabuƙata ta bar su babu komai,Billy gama tunanin shikenan za su afka rayuwar tagayyara da ɗimuwa da talauci,sai Allah ya kawo musu taimako cikin gaggawa. Hukumar hisba da manyan ƙungiyoyin kula da haƙƙin dan Adam na garin kano sun yabawa su Any da Billy akan sadaukarwar da suka yi saboda Allah,ba ƙaramin ƙoƙari suka yi ba har da suka iya barin dukiyar su mai tarin yawa saboda sun san basu same ta ta hanyar halal ba. Tin daga wannan lokacin hukumar take jan su Billy a jiki,dik inda za a je wa'azi za a saka su a gaba a je da su,hakan ba ƙaramin ƙara musu imani yake yi ba,a dik sanda suka je suka dawo daga wa'azi jikin su kan yi sanyi,suna shiga damuwa idan suka tina rayuwar su ta baya,sannan suna godewa Allah da ya basu ikon gane gaskiya kuma suka gyara. Haka rayuwar su take ta gudana kafin daga baya Any ta zaunar da Billy ta kawo musu shawarar fara kasuwanci,a cewar ta zara bata barin dami,idan basu fara kasuwanci ba kud'in hannun su ya ƙare basu da wanda zai ɗauki nauyin lalurorin su na yau da gobe,Billy ta yi na'am da shawarar sai dai sun jima suna saƙa da warwarewa akan wace iriyar sana'a za su yi? Watarana Any na WhatsApp tana duba wani group da bata jima da shiga ba,group ne da ake tura littattafan hausa a cikin shi,sai taci karo da wata baiwar Allah marubuciya tana tallan wani littafin ta da ta rubuta me suna MAIDA TSOHUWA YARINYA tare da No wayar ta a jiki (09031416423), kamar wasa sai ta ɗauki No dake jikin rubutun da matar ta tura ta yi mata magana ta private chat,bayan sun gaisa ne tace mata tana son littafin da taga tana tallatawa na MAIDA TSOHUWA YARINYA,nan take matar ta tura mata account No ta saka dubu ɗayan ta aka bata document ɗin littafin.Billy ta nunawa yanda suka yi da matar,nan take Billy ta yatsina fuska ta ce, "Ke yanzu Any da wannan shirmen ne zamu zuba jari mai yawa mu kama sana'a? Haba dan Allah,ki dinga yin abu da tunani mana please." "Menene abun rashin tunani anan Billy? Kin kuwa ga irin abubuwan dake cikin littafin? Tinda na shiga group ɗin naga matar na tallata kayan gyaran jikin da take siyarwa na san lallai littafin nada amfani,kuma na nuna maki hirar mu ta sanar dani yawancin abinda take siyarwa ɗin nan akwai su a littafin,muma ba sai mu duba muga wanne zamu iya yi a ciki ba?" "Gaskiya ni ba zan tsaya shiririta da wasan yara ba,idan gyaran jikin ne mu je mu siyo na shago mu zuba muyi mu samu kuɗi,kowa fa yanzu ya raja'a akan kayan nan na shafe-shafen zamani,waɗannan abubuwan nata dik wahal da kai ne,ko kuma mu fara saida kayan sawa kamar su leshi,atampa,materials da mayafai,ga kuma jakunkuna da takalma dik ana ya yin siyarwa,shagon ƙofar gida kawai zamu gyara mu watsa komai tinda kan hanya muke ba zamu yi wahalar samun masu saya ba." "Humm ban ƙi shawarar ki ba,amma wannan ɗin ma mu gwada Billy,yanzu ba a zama waje ɗaya,raba ƙafa ake yi saboda zaman banza ba namu bane,kar ki manta wahalar da muka sha a baya muka tara dukiyar haram,idan muka yi haƙuri da wahalar da zamu sha a yanzu watarana sai kiji ana kwatance da mu." Ajiyar zuciya Billy ta sauke sannan ta ce, "To wanne suna zamu sanyawa business ɗin namu yanzu?" "Me zai hana mu saka A&B BEAUTY PALACE?" Kyab'e baki Billy tayi,dan ita har yanzu shawarar amfani da wani ɗan ƙaramin littafi su kafa sana'a bai zauna mata ba,sai dai bata son hakan ya zame musu matsala ita da Any da ta ɗauke ta kamar babbar yayar ta,da taimakon Allah da addu'a duk wata muguwar soyayya da suka ɗora wa zuƙatan su a baya duk ta kau,har kunyar junan su suke ji idan suna tina rayuwar da suka yi a baya. Da wannan shawarar Any da Billy suka fara neman kafinta dan ya gyara masu shago,sai da suka kashe sama da dubu ɗari uku wajen ƙayata shagon nasu ta yanda zai jawo musu kwastomomi,ana gama buga kantoci da sanya wall paper su Any suka zuba kujeru masu kyau, ƙarshe sai da ta dinga shiga internet tana ganin yanda masu shagunan gyaran jiki suke haɗa nasu shagunan,sannan suma suka ƙarasa haɗa nasu,dik wanda ya shiga shagon nan sai ya jima yana mamakin yanda akai matan da basu taɓa saida ɗan kunne ba suka ƙirƙiri irin wannan idea ɗin,a cikin satin Any ta shika kasuwa ta siyo kayan haɗin sabulai da ta ga an koyar,ta siyo na body scrub, da man skin da na gashi,da haɗin dilka da halawa,bata baro kasuwar nan ba sai da ta siyo dik wani kayan haɗin gyaran jikin da taga suna da buƙata,a hankali da taimakon matar da ta sayi littafi a wajen ta ta fara haɗa kayan gyaran jikin,bayan sun gama komai Billy ta dinga murna tana tsalle,cike da farin ciki Billy ta ce, "Ashe dai wannan shawarar mai ɓullewa ce Any,ni fa da dik a tsorace nake kar mu narka kuɗi masu yawa komai ya kwaɓe mana,wa muka ajiye da zai sake ɗora mana jari?" "Kamar yanda bamu san zamu samu wannan ba Allah ya bamu, Allah zai sake bamu wani Bilkisu,kar ki manta a kasuwanci akwai riba da fad'uwa,dole ne mu sa wannan a ran mu kafin kasuwancin mu ya samu ci gaba,dole ne mu sanya a ran mu cewa komai na Allah ne,shine ke azurtawa ba zafin neman mu ba,eh tabbas ana so ka tashi ka nema kafin ka samu,amma mu sani sai Allah ya nufa zamu samu ɗin,dan haka dan Allah Billy mu sa zuciyar mu da jikin mu a kasuwancin nan,da yardar Allah watarana zamu ji daɗi." "Inshaa Allahu zan yi dik abinda kika ce, yanzu kawo robobi na taya ki sanya sticker mu zuba abubuwan da aka gama, gobe da sassafe sai mu je mu jera a shagon,zuwa ranar Juma'a sai mu buɗe shago ko?" "K'warai da gaske, wannan shawarar taki ta yi kyau,Allah yasa mu buɗe a sa'a,zan zauna na tallata mana komai a online idan mun gama,ta hakan ma naga ana samun kwastomomi." Nan da nan suka haɗu suka dinga saka sticker suna zuba kayan sana'ar su a mazubi suna kullewa,kamar yanda suka tsara kuwa washegari suka zuba kaya suka jera a shagon, nan da nan waje ya haska,Any ce ta zauna a kujerar da ke da table a gabanta,Billy na yi mata dariya ta yi mana short video,kamar abun wasa ta ɗora a shafin ta na TikTok da Instagram,sannan ta saka a status ɗin ta,tana tallata shagon nasu,daga nan suka ƙara share wajen suka goge,Any ce ta ce, "Sauran mu mu siyo bokitai da babban mazubin da za ana adana ruwa saboda kinga ba kullum ake samun na famfo ba,ina ganin da ragowar 200k ɗin nan na business mu siyo atampa ko leshi mu ɗan gwada zubawa a gefe mu gani?" "Ah ah yanzu an fi yayin dogayen riguna, ko materials ɗin da ake rigunan dasu sai kig ga mutum ya siya ya kai tela ya dinka masa." "To ai sai mu gwada materials ɗin mu gani ko?" "Allah ya kaimu goben mu je tare,wataƙila ma mu samu wasu abubuwan da zamu siyo." "Amin." Da haka suka ci gaba da gyare-gyaren da za su yi suka rufe

Chapter 59 of 70