kawo, an saka ranar laraba ta zama rabar da za a fara aiki, lokacin yaran suna gida ana hutun mako.
*************************
Tinda su Mommy suka tafi da Alhajin ta Billy ke jin matsanancin kishi da quncin rabuwa da Mommyn musamman yanda ta ga an yi mata gyaran jiki kyawun fatar ta ya sake fitowa, cikin dabara ta bar parlourn qasa ta haye sama ta sauya kayan ta ta ɗauki wayoyin ta ta sauka qasa,ba ta tarar da kowa ba dan haka sai ta zari makullin mota ta kira Sallau ta bashi saqo ya sanar da hajiya ta tafi club.
Cikin sanyin dake kad'awa na magaribar take tuqi a cikin unguwar tasu ta masu hannu da shuni ta sanya waqar su Brick&Lace ta Love is wicked, a hankali take bin baitin kamar wata k'wararriya tana yarfa hannu tana gyad'a kai,ana zuwa dai-dai inda suke cewa....
'Running around i can't get through my day...'
(You feel me?)
'Thoughs of you just keep consuming me...'
(Inna me head, Inna me head, okey)
'And i though i could do it but now i see that you are not mine....'
'And i was wrong to think you'd change, Yeah....'
'I wish you could stay with me another day (ay)....'
'I wish i could change your mind and make you stay (stay).....'
'Cause I, I'd give anything to hear you say (say).....'
'I'll be loving you eternally (love you eternally)'
Your love is wicked.......
Wayar tace ta fara ringing hakan yayi sanadiyyar tsayawar waqar da take sha tana rawa cike da kewar Mommy, kallon sunan me kiran tayi ta sanya hannu cikin sanyin jiki ta amsa.......
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
*Masu tambaya daga farko ku yi hakuri ku jira a gama a haɗa document ko kuma ku duba channel d'ina ta nan Whatsapp,ko page d'ina na Facebook mai suna Haermeebraerh's Novels,ko wattpad Haermeebraerh9900 Idan kuka yi following kuna liking zaku fi ganin new update da zarar an dora, ina yi wa masu neman Audio na novels d'ina albishir da cewa inshaa Allahu a cikin shekarar nan ko me zuwa za su fara samun audio ɗin a YouTube Channel d'ina.*
PAGE 25:
"Ina wuni Ummah?"
"Lafiya qlou ke ina kika shiga kwana biyu ba waya ba aike shiru,kin san kuwa yanzu haka danake miki magana ina gidan ƊAN LITI yarinyar nan Hadiza ta sai wa Uwar ta ingin markad'e ta sai wa Uban ta sabon adaidaita sahu gadagal da ledar shi da komai? Kin ga yanda Sulemanu ke kashe nera yana watayawa a qauyen nan kuwa? Anya yarinyar nan aikatau take yi ko dai ta kauce hanya ne Bilkisu?"
Cikin sauri Billy tace,
"Haba Ummah,kin ga dalilin da yasa bana sakewa na kashe muku kuɗi sosai ko, to ke da kan ki kin fara zargin samun kuɗin Mommy da muke tare muke wahala da jikin mu mu samo ina ga sauran mutane? Ba fa qananan mutane muke yi wa aiki ba, mutane ne da ke riqe da madafan ikon qasar nan, mu yi wanke-wanke mu yi shara mu goge inda suke takawa, mu gama mu ɗora girki,mu wanke band'akin da suke zuba qazantar su,to yanzu haka aike na aka yi ko sallah ban yi ba, kin ga kuwa dole suma su zage bakin aljihu su biya mu da tsoka tinda ba me yi musu idan ba mu ba, kuma su ma baza su iya yi wa kan su wannan wahalar ba,"
Mahaifiyar Mommy ce ke nuna wa sauran matan wayar hannun Ummahn Billy tana gyad'a kai tana farin ciki da jin kalaman Billy, caraf ta cafe maganar tace,
"Allah dai ya yi muku albarka kin ji Bilkisu? Gwanda da Allah yasa ke aka kirawo kike yin wannan bayanin da Mommy aka kirawo se ace dan 'yata ce, to gashi nan dai kowa ya ji da kunnen sa duk d'an baqin ciki se dai ya mutu,"
Da sauri Mahaifiyar Billy tace,
"To Bilkisu za mu yi waya idan na koma gida, Yayan ki ma yazo yau kwanan shi huɗu amma gobe zai koma saboda wai tafiyar gaggawa ta taso masa,"
Lumshe ido Billy tayi kafin tace,
"Allah sarki a gaishe shi to, sai anjima zan kira ki idan na gama ayyuka na,bari na yi sauri kar a yi ta jira na,"
Kashe wayar suka yi Billy ta kashe motar gaba ɗaya ta dafe kanta, cikin wata iriyar murya tace,
"Wai meke damuna ne? Wace iriyar zuciya gare ni ne ni da bana gane inda na dosa? A gaskiya bana jin son Mommy nake yi sai dai tsananin sha'awar kasancewa da ita dan biyan buqata ta, Yah Abdul shi ne wanda zuciyata ke so da aure,na tabbata a duk sanda na gama more rayuwa ta na koma gida zai aure ni,Allah ka nuna min lokacin da zan yakice bariki a rayuwa ta na koma gida,"
Cikin sanyin jiki ta tada motarta ta bata wuta sosai ta nufi club ɗin nasu da ya tara manyan yaran masu hannu da shuni da madafan iko,banda bushe-bushen kayan maye da shaye-shayen kwayoyi da giya ba abinda ake yi a wajen, mata ne kaca-kaca kusan tsirara wasu na zuba soyayya da samarin su a bainar nasi wasu kuma suna rawa, wasu kuma sun shawu sun bugu ba su iya sarrafa kawunan su.
Haka Billy ta samu ta kutsa ta zauna a saman kujerar dake gaban bar ɗin wajen ta yi bayanin irin had'in kaurin da za a yi mata dan kuwa tana buqatar caji sosai, bata jin daɗin zuciyar ta sam, ta rasa ina zata tsaida tunanin ta da soyayyar ta tana cikin rud'ani, ga kewar Mommy da ta kasa barin ruhin ta ya huta, ana gama yi mata had'in nata bar tender ɗin ya miqa mata qaramin cup ɗin ta d'aga kai ta kwankwad'e abinda ke cikin shi tana yamutsa fuska tare da kakari tana damqe wuyan ta, cikin abinda be fi mintuna biyu ba ta dawo normal ta sake cewa a yi mata irin wannan had'in, kallon ta mutumin ya yi yaga ba wasa a fuskar ta, sai ya Karb'a ya yi mata, ta kuwa d'aga baki ta shanye kamar yanda ta yi wa na farkon,tana gamawa ta tashi da kyar tana layi ta shiga filin rawa ta dinga cashewa, a nan ta haɗu da wani kyakkyawan saurayi ya yi mata tayin kwana da shi ta amince ba domin kud'in ba ma sai domin kyawun fuskar da taga yana da shi.
A can gidan Ɗan liti kuwa bayan Billy ta kashe waya sai shewar mata ta tashi suka dinga taya Innoh murnar samun ingin markad'e nan take tace musu,
"Ai ba markad'e ba kawai har niqa zan dinga yi tinda kun dai san garin nan an fi cin tuwo da kunu ba safai ake yin markad'en kayan miya ba,"
Ummahn Billy ce tace,
"Kin kuwa yi dabara Allah ya taimaka ya tsare mana yaran mu a dik inda suke,"
"Ameeen"
Shine abinda qawayen Innoh da 'yan uwan ta irin su Naja suka dinga faɗa kafin daga baya su fara watsewa kowa ta tafi gidan ta, Baabaa kuwa na gefe tana kallon su bata ce komai ba, cikin ranta tunanin su Saddeqa take ta yi, tana son yau dai ta basu abincin dare ko ta halin qaqa ne sai dai ayi bala'in da za a yi a shirye take amma ta dena barin yaran suna kwana da yunwa,ita ba azzaluma bace.
Qarshe dai kafin kowa ya gama watse sai da suka sakar wa da Baabaa baqar magana akan tana baqin ciki da samun Innoh, ko kula su bata yi ba suka gama rashin kunyar su wadda Innoh ce ta basu lasisin yi mata hakan suka tafi.
Da yamma liss su Saddeqa suka dawo daga makaranta basu tarar da kowa a tsakar gida ba, dan haka d'akin su ta wuce direct ta fara cire kayan jikin ta ta d'aga katifar Yadiko ta saka kud'in hannun ta a inda take ajiye kud'ad'en ta sannan ta sauya kaya ta fita tsakar gida dan zuwa ta gaishe da mutanen gidan kafin a yi magariba.
D'akin Innoh ta nufa ta yi sallama, Naja ce ta amsa mata sannan cikin dakewa tace,
"Ki shigo ni bana son munafurci dalla,"
Jiki a sanyaye Saddeqa ta d'aga labulen d'akin ta leqa tare da durqusawa ta gaishe da Najar sannan ta gaida Innoh dake ta cika tana batsewa ita a dole ga uwar mai kuɗi, cikin muryar rashin mutunci tace,
"Sannu tinkiya uwar tinb'ele baki san gida ba se an nemo ki,kin ga dama kin dawo? To maza ki je madafi ki qarasa tuqe tuwon nan tasss ki raba kuma ki jiqa tukunyar idan kin gama,"
"To Innoh, amma ba za a yi qanzo ba za a jiqa tukunyar?"
Shewa tayi sannan tace,
"Kin taɓa ganin na yi qanzo ni? Wannan ai se uwar ki da ke qas ita ce ke yin qanzo saboda tsoron babu,ni kuwa kin san tin da can Allah ya rufa min asiri ballantana yanzu da 'yata ke aiko min da damman kuɗi,wuce ki je ni kiyi min abinda na saka ki"
Cike da zubar da hawayen ambaton mahaifiyar ta da Innoh tayi ta bar d'akin dan zuwa gaishe da Baabaa,tana fita Naja tace,
"Kaiii Yaya kin iya cin mutunci,to ba wannan ba, kin san dai Goggo ma na can tana jiran a bata wani abu dan kuwa labarin ya kai mata cewa Mommy na yi miki aiken kuɗi,"
(Goggo yayar mahaifin su ce dake zaune da su tin bayan rasuwar mahaifiyar su, yaran Innoh kaf ita suka sani a matsayin kakar su)
Cikin ɓacin rai Innoh tace,
"Kaiiii jama'a Goggo bazata barni na yi qiba ni kaɗai ba, to babu komai idan zaki tafi na baki ko dubu uku ce ta rage zafi,"
"To ina laifiii? Ai da babu gwanda babu daɗi,"
Hira suka ci gaba dayi kafin ta ji madafin shiru alamar babu kowa ciki, kwalawa Saddeqa kira ta dinga yi amma taji shiru, cike da masifa ta miqe tsaye ta d'aga labule tana fad'in,
"Naja bari maganar Ameerah da yaron nan ba auren ta zai yi ba na san, ko ya aure ta da asiri randa duk ya karye wulaqanta min yarinya za su yi kin ga maganin karna yi kar a soma kenan ko?"
Qarasa fita tayi direct sashen Baabaa taje taga su Sadeeq da Saddeqa na cin abinci cikin sauri, salati ta buga tana tafa hannaye, cike da rashin kunya ta kalli Baabaa tace,
"Sannu haɗa su kasa rabasu gamandi jikar buwa,wato kin zo nan kin tasa yara a gaba kina basu abinci salon ki ja min baqin jini a wajen su su dinga gani na a matsayin muguwa ke kaɗai ke son su ko? to Allah ya fiki, na riga ki karance tabara na tofe jiki na da yasin ta Allah ba taki ba,"
Baabaa ce ta d'aga kai ta kalli Innoh taga yanda take zazzaga mata rashin mutunci ko tsufan ta bata gani, cikin sanyin murya da gajiyawa da yawan faɗa da Innoh Baabaa tace,
"Tafi qofar ki ki bar min nan bana son tashin hankali da yammar subhanahu wata'ala,"
"Idan na qi tafiya me zaki yi min?ke dai kin yi asarar hali Yaya, a kullum baki da burin da ya wuce na ki tozarta ni a idon yaran......"
Wata sufa Baabaa ta yi ta ɗauki wani sungumin icce dake qasan kujerar qofar d'akin ta tayi kan Innoh da shi zata kwad'a mata,ihu Innoh ta zunduma ta fita da gudu dan neman mafaka,Naja ce ta fito tana fad'in,
"Yaya menene? Ko dai gamo kika yi da na almuru? "
"Matsa min na wuce Naja kafin ta sameni da wannan iccen na hannun ta ta illata ni, matsa matsa ba gamo nayi da na almuru ba, da fulanin aljanu nake shirin yin gamo masu baqar zuciya,"
Ganin Baabaa a guje da qaton icce a hannu ne ya sanya Naja ma afkawa d'akin a guje ta shige qasan gadon Innoh me rumfa ta kwanta ta yi shiru ko numfashin arziqi bata fitarwa,Innoh na isa d'akin nata ta yi sauri ta rufe qofar tana son ta saka sakata amma Baabaa ta qi bata wannan damar saboda danna qofar da ta shiga yi tana lafta mata wannan iccen hannun nata dake sanya cikin Naja murd'a wa, nan take Innoh ma ta ji hankalin ta ya yi mummunan tashi ta kurma wani uban ihu tana faɗin,
"Yaya ki wa Allah ki bawa 'yar fulani hakuri ta kyale ni kar ta illata ni,idan kika sake rotse min baya bani da me taimaka min,"
"Kin san da haka kike azabtar da marainiyar Allah, tinda baki tsoron Allah bari ni ki ji tsoro na dan kuwa yau se na ga haqoran ki na malelekuwa a qasa zan kyale ki,ba a baya zan jibga miki wannan iccen ba, a hauren ki zan sauke miki su kin ga gobe idan an ce ki kirani da gamandi jikar buwa bakin qara ba,habaa yarinya kin fitine ni kin addabe ni ko kina ganin kammu ɗaya ne?"
Cikin sa'a Innoh ta samu ta sanya sakata, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta leqa ta ɗan qaramin windown ta ta hau yi wa Baabaa rashin kunya, gani tayi Baabaa ta nufi windown da gudu tana tsalle zata d'ale tagar ta shiga, da gudu Inno ta tura Baabaa baya ta ja qofar ta sa sakata tana nishi, cikin takaicin rashin nasara Baabaa tace,
"Qaramar mara kunya da ki tsaya mana ki ga yanda ake ladabtar da marasa tarbiyya,daga yau kuma ni na ɗauki nauyin ciyar da yaran nan in ga shegen da zai hana,ba zan zauna alhakin marayu ya hana ni kwanciyar qabari ba ah toh,"
Sakamakon rufe qofa da taga da Innoh tayi sai ya zamana tana ta magana amma ba a sanin me take faɗa, a haka Saddeqa dake ta sheqa dariya ta isa gaban Baabaa ta karɓe iccen hannun ta ta kai mata d'aki sannan ta fito ta nufi kitchen ɗin Innoh dan kwashe tuwo.
Saboda tsoro da jigata Naja qin tafiya gida ta yi da wuri sai da ta ji motsin Sule ya dawo sannnan ta fita ya raka ta har gida.
Tin daga wannan ranar Saddeqa da Sadeeq suke samun cin abinci sau uku a rana,dan kuwa Innoh dena basu abincin gidan uban su tayi tace su je Baabaan ta ciyar da su.
Dik abinnan da ake ta faman yi Ameerah na kwance babu lafiya ko talla bata iya fita saboda ta k'wallafa wa zuciyar ta son Munir gashi Munir ya yi mata nisa, a duk sanda ya kirawo wayar Baabaa yace zai gaisa da Saddeqa idan dai tana wajen sai tayi yanda zata yi da tsiya da tsiyatsiya ta karb'i wayar ta yi masa magana, shi kuwa da yaji muryar ta ce sai ya kashe wayar shi ba ya sake kira.
Tayi nacin tayi kukan, ta yi ban hakurin akan Baabaa ta sanya baki Munir ya aure ta amma Baabaa tace Allah ya tsari jikan ta da auren mugun iri,idan ta dami Innoh kuwa akan zancen shi watarana rufe ido take yi ta manta da maganar rashin lafiyar Ameerahn ta mata duka tana kiran ta mayya.
Ameerah duk tabi ta rame ta shiga tashin hankali da rashin madafa,wannan dalilin ne ya sanya duk drama'r da ake ta tafkawa a gidan bata leqo ba balle ta shigar wa Innoh.
***********************
A can qasar Uganda kuwa Mommy na ta cin karen ta babu babbaka dan kuwa ba qaramin kuɗi ta dinga damqa ba a wajen mazajen da ke nuna suna son ta,Alhajin ta da kan shi yake haɗa ta da mazajen da suka fishi arziqi saboda kar ta san kar ne ai dika yawon barikin suka fito shi yasa baya yi mata baqin ciki idan wani ya nuna yana son ta kuma ya bincika yaga mutumin yana da kuɗi sosai se ya haɗa su, tin tana qi gashi yanzu har ta saba.
Ganin hakane ya sanya Alhaji kiran wayar wani abokin harqallar su yace,
"Man ina fatan komai ya zama ready ko? I think she is ready now,"....................
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
PAGE 26:
"....Eh we are going through lake Victoria because i don't want any problem to happen again.....Ok I think Bukasa is...."
K'wank'wasa d'akin nasu da aka yi ne ya sanya Alhaji kallon Mommy da ta baza kunne tana sauraran wayar da yake yi, ta dai ji yana maganar za a yi tafiya ta lake Victoria saboda baya son matsalar da ta faru ta sake faruwa, to menene Bukasa ɗin? Magana ya sake yi mata kafin ta firgita ta dawo da hankalin ta kanshi ta amsa da,
"Na'am?"
"Baki ji ana buga qofa ba? Room service ne ki je ki buɗe,"
"Ohhh ban ji ba ni fita ma zan yi wajen ruwan can na ɗan sha iska,"
Tana faɗin haka sai ta miqe ta sumbaci kuncin shi ta sauya kayan jikin ta zuwa na shiga ruwa ta fita,alama tayi wa da matashin da ya je dan gyara musu d'akin nasu da ya shiga ta wuce tana juya qugun ta da babu namiji mai lafiyar da zai kalla bata burge shi ba.
Direct swimming pool ɗin da ya sha kwalliya gewaye da wasu duwatsu na wuta ta nufa ta ajiye towel ɗin ta a saman gadon da taga wasu matasan samari sun kwanta suna hutawa,kamar wata 'yar ruwa haka Mommy ta d'aga hannayen ta sama shape ɗin ta ya qara bayyana ta afka cikin ruwan, idanun ta rufe a cikin ruwan me hasken sararin samaniya ta hau tunano yanda suke zuwa rafin qauyen Ba Mugu suna wanka a baya kafin ta zama budurwa, daga baya Ɗan liti ya fara hana ta zuwa,cikin ranta take ayyana.
'Yau dai gani a wata qasar cikin kaya na alfarma ina iyo a idon duniya ba ma a iya ɗan qaramin qauyen Ba Mugu ba,ita rayuwar nan dama idan wani ya takura maka sai Allah ya kawo maka inda zaka huta,'
(Kun yarda irin wannan rayuwar hutu ce ga mai hankali?)
Mommy bata fito ba sai da ta gaji dan kanta sannan ta fita jikin ta na d'igar da ruwa ko ta ina, gashin dokin dake kan ta wanda duk k'wak'k'wafin mutum ba lallai ya gane ba nata bane sai yarari yake yana zubar da ruwa, cikin wani irin taku na qasaita da jin cewa ta kai macen da bata shakkar bayyana tsiraicin ta a dika duniya ta isa ga towel ɗin ta ta hau tsane gashin kan ta cikin salo zuwa gangar jikin ta da babu komai sai pink bikini, duk abin nan da take yi idanun mutanen wajen duk ya tattara ya koma kan ta, wanda ma be ganta ba da farko ganin kowa na kallon ta sai ya juya shima ya hau kallon ta.
A haka Mommy ta gama tsane jikin ta ta haye kujerar dake wajen doguwa me kamar gado ta kwanta tana so gashin kan ta ya bushe.
Wani matashi ne baqi sidiq me qirar qarfi ya nuface ta yana yi mata yaren su na Swahili tare da miqa mata hannu akan su gaisa, dabarbarcewa Mommy tayi dan kuwa bata iya yaren ba, gane hakan ne ya sanya shi fara zuba mata turanci cike da k'warewa, cikin yaqe haqoran ta ta yi fari da ido ta miqe ta ɗauki towel ɗin ta, dan kuwa ba dika ta fahimci me yake magana akai ba duba da cewa yanayin turancin su na rikita ta dama,namu na Nigeria ɗin ma idan aka yi zurfi barin ta ake yi a hanya balle na wata qasar.
Da ido matasan suka dinga binta har ta b'ace wa ganin su, tafe take tana numfashi cikin gimtse haqoranta tace,
"Wai Allah ! Allah ya so ni na gudo, haka kawai zai zo ya bada ni cikin mutane aji na ya zube,a gaskiya zan yi wa Alhaji magana muna komawa Nigeria a samu me koya min turanci tinda dama Billy ta faɗa min idan baka iya turanci ba a wannan harkar ba zaka ɗaukaka yanda kake so ba,"
Daf zata shiga d'akin nasu taga an buɗe murfin qofar kuma ba a fito ba,kalmar da taji bawan Allah'n dake riqe da hannun qofar na faɗa shi da Alhajin nata sun kid'ima ta sun sanya ta taji kamar ta zura da gudu,cikin dafe qirji ta furta,
"Wa za a siyar ni? Ni za a sayarwa da masu jan kunne a kan waɗannan maqudan kud'in? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un na shiga uku ni Mommy,"
Qoqarin guduwa take yi bawan Allah'n nan ya qarasa fitowa daga d'akin shi da Alhajin nata, suna ganin yanayin ta suka fahimci taji tattaunawar tasu, Alhajin ne ya d'aga hannayen shi sama yana yi mata magana da sigar lallashi saboda ganin ruwan hawaye na zubar wa Mommyn da mugun gudu a fuskar ta.
"Calm down baby,zo ki ji maganar da muke yi, kar ki yi mana muguwar fahimta dan Allah,"
Ja da baya ta sake yi sannan tace,
"Wanne irin na zo na ji? Me zan ji? Ashe I love you ɗin da kullum kake faɗa min qarya ce? Kai ne mutum na farko da na taɓa sakewa jiki na yayi yanda yake so da shi da amincewa ta da kuma son raina ba tare da tsoro ko fargaba ba, ba tare da nuqu-nuqu ko b'oye-b'oye ba, amma dik da haka shine za ka ci amana ta? Ni zaku siyarwa masu jan kunne?"
Taku ɗaya bawan Allah'n nan yayi ya cafko hannun ta ya matse ta suka maida ita cikin d'akin,ihu ta dinga yunqurin yi amma muryar ta bata fita sosai saboda shaqar da suka yi mata dika su biyun, qafar ta ta sanya a tsakiyar bawan Allah'n nan ta yi masa harbin jakai nan take ya durqushe a wajen yana malelekuwa a qasa saboda azaba, Alhajin ne ya zira hannu a jakar shi ya dakko wani farin kyalle da wata kwalba ya deb'i ruwan dake cikin kwalbar ya shaqawa Mommy nan take ta suma.
Ajiyar zuciya ya sauke me qarfin gaske kafin ya samu ya taimaka wa abokin shi su miqe tsaye tare,
"D'akko allurar nan ayi mata, idan ba haka ba kafin mu je inda zamu je ta farka ta tona mana asiri,"
Cikin hanzari Alhaji ya sake d'akko wata allura ya haɗa ta ya yi wa Mommy, cikin ran shi babu daɗi saboda ya fara kamuwa da son Mommy amma son kuɗi ya ninka soyayyar da yake yi mata dole ne ya saida ta kamar sauran matan da suka yo safarar su.
Cikin sauri suka hau haɗa kayan su, Alhaji ya sauya wa Mommy kayan ta, sannan ya ɗauke ta kamar wata babyn roba, sanda suka fita waje sai ya hau yi mata surutu yana kai mata sumba kamar idanun ta biyu, a haka suka isa parking space suka hau mota suka bar hotel ɗin suka nufi tashar jirgin ruwa.
Babban jirgi ne wanda idan mutum na bakin tekun zai kalle shi sai ya d'aga kan shi sannan zai gama ganin qarshen shi,jirgin ya qunshi waje kashi-kashi kamar wata unguwa, ko da suka isa sun tarar da sauran 'yan matan da za su yi tafiyar da su a wajen, wasun su sai murna suke yi za a je qasar turai da su,wasun su kuma a tsorace suke da shiga jirgin na ruwa dan haka duk wata murnar da suke tattare da ita ta koma tashin hankali.
Mutane ne kala-kala a wajen har da turawa da larabawa da dai sauran mutanen qasashen africa da turai.
A cikin wani d'aki mai ɗauke da gado da abubuwan more rayuwa Alhaji ya shimfid'e Mommy ya ajiye kayan su ya fita ya kulle ta ta waje, abinci da ruwa ya sake komawa ya kai mata da kan shi sannan ya sake fita ya kulle ta ta waje.
Sai da suka kai wajen awa biyu da minti arba'in kafin jirgin nasu ya tashi zuwa turai,wata iriyar qara ya dinga yi ta yanda idan kana waje sai ka toshe kunnen ka,hakan ce ta sanya sauran matan da aka je da su rikicewa suna ta iface-iface na jin tsoro, wasun su kuma suna ta dariya da shewa tare da ɗaukan hotuna har ma da videos suna jin daɗi.
Sun yi tafiyar da ta kai ta awanni biyar kafin mommy ta farka cike da wata iriyar kasala da mutuwar jiki, da kyar take iya buɗe idanun ta, a hankali ta fara magana kamar wata 'yar maye tana faɗin,
"Ka maida ni gida wajen Hajiya K'waisa, mugu azzalumi kawai, ashe shi yasa ka hana ni yin waya da kowa, ka goge min duk wani social media accounts da nake kai Allah ya isa ba zan yafe maka cin amanata da ka yi ba, ka maida ni gida na koma qauyen mu na fasa neman kud'in aure zan yi,"
Kuka take tana jan majina amma babu me jin ta balle ya kawo mata agaji, ta na nan tana kukan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 70