Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a gefen ta, tana d'aga kai sai taga motar Abdul ce, nan take murmushi ya sub'uce mata, lallai maganin bokan nan yana aiki, har ya faɗa tarkon ta da wuri haka? Hamdala tayi a ranta ta buɗe motar ta shiga, babu wanda yace wa kowa komai har suka isa qofar gidan ƊAN LITI, a qofar gida suka tarar da motar Munir suna zaune da shi da Saddiqa suna hira cike da nishad'i tana nuna masa murnar ganin shi da tayi dan kuwa bata zata zai zo ba duba da yanayin aikin shi. Mommy taji daɗin yanda Abdul ya ɗauke kan shi daga kallon su kamar be san su ba, kallon Mommy yayi yace mata, "Sai mun yi waya ko?" Cike da fara'a da jin daɗi tace, "Da yaushe kenan?" "Ina isa gida zan kirawo ki dan ban gaji da jin muryar ki ba," Mommy ji tayi kamar ta rungume shi dan tsananin farin ciki, a guje ta fita daga motar ta yi cikin gida tana ihun murna kamar zata tashi sama, a guje Innoh dake jiran shigar ta gidan ta fito daga d'aki ta damqe wa Mommy baki suka afka d'akin ta dan kar taje tayi b'aram-b'arama a tsakar gida. A can waje kuwa Mommy na fita Abdul yaji kamar ya bi bayan ta, wata iriyar wutar son ta ce ta dinga ruruwa a zuciyar shi, ji yake yi idan bai aure ta ba zai iya rasa ran shi, cikin gaggawa ya bawa driver umarnin ya kai shi gida, Munir kuwa yana nan yana jiran ko ta kwana dan ya ga yanda Abdul ɗin ya dinga kallon masa mata kyale shi kawai yayi dan a cikin taro ne, yanzu kuwa ya shirya karta masa rashin mutunci ba ruwan shi da rawanin sa,sai dai ganin yanda yake yi wa Mommy abun ya d'aure musu kai daga shi har Saddiqan, sai dai babu wanda yace komai a cikin su suka ci gaba da hirar su. A can d'akin Innoh kuwa Mommy ta gama labarta mata komai cike da murna, Ameerah kuwa kuka ta fashe da shi ta hau surutai tana fad'in, "Ai dama ba tun yau nasan baki qauna ta ba Innoh,ni me yasa baki yi min abinda kika yi wa Mommyn ba har Abdul ya fara son ta gashi har yana fad'in zai kira ta, wato ni saboda bana baki kuɗi ko? Ga masoyina can da waccan shegiyar yarinyar a waje ni ina nan zaune kamar mara gata, Innoh kin san yanda nake ji a zuciya ta kuwa? Ji nake yi kamar zan mutu zafi qirji na yake yi min ki taimaka min nima," Cike da tausayawa Innoh tace, "Ameerah dik abinda kika faɗa ba haka bane, yaron nan an kai sunan shi an yi anyi asiri ya ci shi shida matsiyaciyar tsohuwar nan abun ya faskara, shi kanshi Bokan yayi mamaki matuqa, dik da cewa ita kakar tashi an gano k'wank'waman kanta jigajigai ne baza ta tab'u ba, idan muka dage sai an yi mata asirin da zata yarda ya aure ki komai zai iya lalacewa,Ameerah ki yi amfani da jikin ki ki jawo ra'ayin shi idan ba haka ba babu wata hanya da zan iya taimaka maki da ita," "Nima a bani k'walin na gwada mana, idan baiyi ba sai na sake wani salon amma ba wai ki bawa 'yar so ba ni ki hana ni," Cike da fushi Innoh ta karb'i kwallin a hannun mommy ta wurgawa Ameerah tace, "Gashi nan Ameerah Allah ya bada sa'a ki samo zuciyar Manniru kema ya tsani Saddiqa shikenan?" Baabaa da ta doso d'akin hannun ta ɗauke da babban kwano da ta zubo wa Innoh da iyalan ta abinci da soyayyun naman kaji ce taji maganar da Innoh tayi ta qarshe.................   [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 38: Jikin Baabaa ne ya hau wata iriyar jijjiga kamar irin ta qaurayen da ake kad'awa gangi a filin daga, ba tare da ta san sanda ta ajiye abincin ba ta nufi robar dakakken barkonon Innoh na alale ta buɗe ta damqi yaji ta sanya hannun ta a bayan ta ta nufi d'akin Innoh, Sallama tayi ta ce, "Ameerah ke ! zo nan ki ɗauki abincin ku," Duk wanda ya san muryar Baabaa to tabbas ya san an samu sauyi a cikin ta, amma bahaushe yace, mai rabon shan duka sai ya sha, dan haka ba tare da tinanin komai ba Ameerah da ta gama gwagud'a kwallin sihiri ta buɗe labulen d'akin Innoh ta sako kai waje da niyyar karb'ar abinci, suna haɗa ido da Baabaa taji hankalin ta yayi mugun tashi saboda yanda taga jikin Baabaa na tsuma idanun ta sun yi jawur kamar jan yadi,juyawa ta so yi dan guduwa cikin d'aki amma kafin ta ajiye qafarta da ta d'aga Baabaa ta damqo wuyan ta ta matse ta a hammatar ta ta bankawa fuskar ta yajin nan wanda ya shiga har bakin ta da hanci da idanun ta, wani azababben ihu Ameeerah ta saki kafin daga baya jikin ta ya saki ta faɗi yaraf a wajen, Innoh ce ta fito da gudu cike da tashin hankali dan ganin abinda ke faruwa, ido huɗu suka yi da Baabaa dake tsuma tana wata iriyar zufa, katar katar Innoh ta juya da manyan duwaiwaka zata koma d'aki Baabaa ta daka tsalle ta dira a wuyan ta ta shaqe ta ta baɗe fuskar ta da barkono, Mommy da ta ga dik abinda ya faru kuwa tini ta dannawa d'akin sakata ta rufe har window jikin ta na b'ari da fidda zufar tashin hankali. Yare Baabaa ta farayi tana nuna wa Munir da ya shigo shi da Saddiqa Innoh da Ameerah,gaba ɗaya sun kasa gane yaren da take yi dan haka sai suka hau yi mata addu'a dan aljanun nata su lafa, dik yanda Munir yaso d'aga Baabaa ya maida ta d'akin ta kasawa yayi har abun yaso bashi tsoro, Saddiqa kuwa ta duqufa wajen yi wa Baabaa addu'a taji Baabaa ta dawo yin hausa,cikin wata iriyar muryar bafulatanar da bata jin hausa Baabaa tace, "Barni da su....ki barni da su nashe na nuna masu qarfin ikon da god'iyar mu ke dashi," "Ku yi hakuri Allah yana tare da masu hakuri," in ji cewar Saddiqa da ke shafewa Baabaa zufa,cikin kumfar baki da masifa Baabaa tace, "Allah kuma baya tare da azzalumai ba, mu za a yi wa asiri? Ke kin san ko ni washeshe?" "Allah ya baku hakuri, ku yi hakuri dan Allah," Ruwa Munir ya ɗebo a cup ya yi addu'a a ciki ya kafawa Baabaa a baki ta sha sannan ya shafa mata a fuska, atishawa ta dinga jerowa tana kumawa har sai da tayi sama da biyar kafin ta miqe tsaye kamar wata tsuntsuwa, waiqe waige ta farayi tana neman madoki, Saddiqa da Munir ne suka ja ta d'akin ta suna ta bata hakuri, Innoh da Ameerah kuwa na nan sun gigice sun rasa ina za su nufa su sami ruwan wanke idanun su. Cikin kuka Innoh tace, "Yaya kiwa Allah kiyi hakuri kar ki mamaye ni zuciya ta zata buga saboda tsoro ban san ta ina kike ba, ke kuma dan uban ki ba zaki samo min ruwa na wanke ido na ba?" Ta juya inda take jiyo muryar Saddiqa ta faɗa haɗe da daka mata tsawa, a guje Baabaa ta kwace daga riqon da Munir yayi mata ta yi bakin rijiya ta ɗauke guga ta yi d'akin ta ta boye, fitowa tayi hannun ta riqe da wayar ta yau ko wanda zai kira mata Alhaji Baban gidan nata bata nema ba da kanta ta danna wayar, jikokin ta dake tsaye suna kallon ikon Allah sai qunshe dariyar ganin dirircewar Innoh da Ameerah suke yi,dik cikin su babu wanda yayi yunqurin taimaka musu da ruwa. Wayar bata jima tana ringing ba Alhaji Baban gida ya ɗauka cike da fara'a yana taya Baabaa murna akan saukar da Saddiqa tayi, katse shi tayi da faɗin, "Baban gida wace ta haife ka?" Ji yayi gaban shi ya yanke ya faɗi, a tsorace ya furta, "Kece mana Baabaa me ya faru?" "To idan dai ka tabbatar da ni ce uwar da na ɗauki cikin ka watanni tara da kwanaki, na haife ka, sannan na rene ka na shayar da kai mamana to ka tabbata gobe kana cikin qauyen Ba mugu da kud'in auren Manniru da Saddiqa,sannan ka faɗa wa uwar Manniru ta haɗa gagarumin shagalin bikin tarbar surukar ta nan ba da jimawa ba," Baabaa na gama faɗar abinda zata faɗa ta kashe wayar ta ta koma d'akin ta ta zauna ta buga tagumi sai hawaye suka fara zuba a idanun ta na tsananin tausayin Saddiqa da kewar Yadikon Sule,cikin kuka tace, "Inshaa Allahu in dai ina raye 'yar ki ba zata wulaqanta ba, zan tsaya tsayin daka dan na inganta rayuwar ta tinda ubanta bashi da amfani an shanye shi," Saddiqa da ta gama jin maganganun Baabaa sai ta duqa a gaban Baabaa ta kwantar da kan ta a 'yar siririyar cinyar Baabaa tana share hawaye tace, "Baabaa na gode da soyayyar da kike nuna min, yanda kike kula da ni da qanina Allah ya kula da zuri'ar ki kar su yi mummunan qarshe,na gode Baabaa," Munir ne ya shiga yana murmushi yace, "Ah ah, wai me bayin Allahn nan ke yi ne aka ware Munir bawan Allah ? Baabaa yunwa muke ji a zuba mana abinci kwano ɗaya da gimbiya ta mu ci," Share hawaye Baabaa tayi tana murmushi tace, "Anqi zuba maka abinci kwano ɗaya da itan mara kunya kawai," "Ai kuwa gwanda ma ki haɗa mana dan ko baki haɗa ba mu zamu haɗe abun mu ko ya kika ce MANSEEQ ɗina ?" Wani iri Saddiqa taji a jikin ta saboda yanda ya furta sunan da ta tabbata yayi amfani da sunayen su ne ya haɗe su waje ɗaya ya fad'e su, cikin sauri ta miqe ta bar d'akin tana murmushi, tana fita tsakar gida fara'ar ta ta ɗauke dan ganin Ɗan liti a tsakar gida yana zubawa Innoh ruwa ita da Ameerah suna wanke fuskar su suna kuka,suna haɗa ido hantar cikin ta ta kad'a domin kuwa idanun Ɗan liti har wani ja suke yi saboda ɓacin rai, sum-sum-sum ta bi gefen rumfar d'akunan nasu ta shige d'akin Yadikon ta, yana gama zuba musu ruwan Innoh ta d'ebi gishiri ta lasa ta baiwa Ameerah wai ko yajin zai musu sauqi,majina kuwa haka suka dinga tararar da ita kamar an buɗe pampo,cike da b'acin rai Ɗan liti yace, "Me ya faru a gidan yau kuma? Tinda ku dai kun riqe qur'ani kun yi rantsuwa ba za a zauna lafiya a gidan nan ba, ina can bakin sana'a ta Baban Gida ya kira ni yace na zo gida babu lafiya," Kuka Innoh ta fashe da shi zata hau bayani Baabaa ta riga ta, "Dole gida ya kasance cikin rashin zaman lafiya tinda ka gaza a matsayin ka na miji, ka gaza a matsayin ka na uba, kuma ka gaza a matsayin ka na qanin miji na da na ɗora ran koda bani da 'ya'ya Ɗanli zaka kula da ni har bayan raina ba zaka gajiya ba, sai gashi kana ta nuna min banda mahimmanci a rayuwar ka,ko da yake me zai b'ata raina bayan wanda suka zama wajibin ka ma baka kula da su ba, idan da asiri har da halin ka ma Ɗanli,yau fa yarinyar nan ke saukar alqur'ani amma baka je ba, kowa uban ta yaje uwar ta taje, wadda duk ka ga waɗannan biyun basu je musu ba to fa ɗaya ya mutu a cikin su, amma saboda mace ta bada ruhin ka ma rauhanai sun fitsare shi, shine ka qi zuwa bayan kasan uwar ta ta rasu, da babu ni shikenan sai ya zamo babu wanda zai je taya ta farin cikin wannan ranar kenan?" Jikin Ɗan liti yayi mugun sanyi, shi kan shi yana jin babu daɗi akan yanda yake yi wa su Saddiqa, amma a zahiri ko sunan su baya so a faɗa a gaban shi tsabar tsanar su da yake ji na d'awainiya da shi,Innoh ce ta buɗe baki zata yi magana Baabaa tace, "Wa ya halicce ki Innoh?" Cikin sauri Innoh tace, "Allah," "To idan kin raina mahaliccin ki yau ki yi wata maganar banza anan ki sha mamaki,idan kin saba da shirka da raina mijin ki ni ba zan ɗauka ba ko babu aljanu qarshen ki zan gani cikin salama, kai kuma Ɗanli na kirawo Baban Gida nace yazo gobe, ina so ka shaida a goben za a d'aura wa Manniru da Saddiqa aure idan kuma zaka nuna wa matar ka ni ba kowa bace a wajen ka ban isa da kai ba balle abinda ka haifa bismillah," "Dama wake son haɗa zuri'a dake? In banda Ameerah ma data nace ai kema kin san qarya ne ni da kaina na haɗa zuri'a da dangin aljanu dangin bala'i da masifa," Zabura Baabaa tayi zata yi kan Innoh, Innoh ta bi bayan Ɗan liti ta tsaya tana haki, gaba ɗaya sai ya zama wani ɗan tsurut a gaban ta, kusan ita ta b'oye shi dan kuwa ba shi ya b'oye ta ba. Munir ne ya kama hannun Baabaa yace, "Dan Allah Baabaa ya isa haka, ku wai baku gajiya ne? Ku dinga haƙuri da junan ku please rayuwar nan dika nawa take ne?" "Dubu take dan uwar ka Saliha, nace dubu take sake ni kafin na bige ka kai ma," Dariya yayi ya sake riqe ta suka shiga d'aki tana ta sababi da cin alwashi kala-kala akan Innoh da zuri'ar ta idan basu fita a hanyar ta da Saddiqa ba. Duk wannan tashin hankalin da ake yi Mommy ta gaji da zama a d'akin a waje ɗaya sai ta kwanta a gadon Innoh dan ta huta daga firgici da tsoron da ta shiga a haka bacci ya ɗauke ta cike da mafarkai na tashin hankali da ban tsoro, wayar ta na ta ringing bata san tana yi ba balle ta amsa. *************************** Abdussaboor ne riqe da wayar shi a hannu yana ta kaiwa da komowa a d'akin shi hankali tashe saboda qin amsa wayar shi da Mommy tayi ba, nan take zuciyar shi ta bashi wataqila taqi amsawa ne saboda abubuwan da ya yi mata a baya ya nuna baya son ta ba kuma ya qaunar ta zamo matar auren shi,cikin sauri ya ajiye wayar ya sanya rigar shi da ya cire ya zira takalmin shi ya nufi d'akin Innah Laminde. Zaune take a qasa Billy na tsefe mata kai tana so tayi mata kitso a cewar ta kan ya tsufa tana buqatar a wanke mata shi a gyara,cike da jin daɗi Innah Laminde ta amince dan kuwa bata da 'ya mace dika yaran ta maza ne sai yaran kishiyoyin ta mata guda uku. A hargitse ya shiga d'akin cikin damuwa ya furta, "Innah kin ga ina ta kiran wayar ta taqi ɗauka ko? Dan Allah Innah kiyi wa mai martaba magana a aura min ita idan ba haka ba zan iya rasa raina, ina son ta, na amince ina ina qaunar ta Innah," Cike da jin daɗi Innah Laminde ta d'aure kanta da d'ankwalin atampar dake jikin ta ta tashi ta kama hannun Abdul da yake a firgice ta zaunar da shi kusa da ita tace, "Ka ga ka sa ta ji kunya ta wani takure waje ɗaya kamar gaske, ai murna zaki yi ba wai kunya zaki ji ki yi shiru ba, alhamdulillahi, alhamdulillahi, alhamdulillahi,SARAUTA Allah yayi maka albarka ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka, ina alfahari da kai d'ana,banda abinka kuma ai da leqowa kayi ka ce taje tinda bata amsa wayar ba, kai da qanwar ka?" Billy ce ta sake duqar da kai tana murmushi ta kalli Innah Laminde ta sake sunkuyar da kai tana saka hannu a baki ita a dole taji kunyar suruka, kallon su Abdussaboor yayi yace, "Innah ina take? Yaushe tazo gidan ban sani ba? Dan Allah kirawo min ita tazo na gan ta ko zan ji sanyi a rai na,Innah bana son na rasa Hadiza a rayuwa ta ina son ta, na yarda ta yi min qarya ta cutar da zuciya ta, amma na amince da soyayyar ta da ta dasa a raina zan aure ta, soyayyar ta itace qaddara ta, Innah ki yi wa Mai martaba maganar auren mu da Hadizana dan Allah," Wani irin ashar Billy ta saki a gaban su ta yi tsalle ta dire sannan tace, "Lallai kuwa soyayyar ta zata yi ajalin ka, dan kuwa na tabbata Innah Laminde ba zaki yarda ki haɗa zuri'a da karuwa ba, da ka auri Mommy ka barni da dakon son ka gwanda a mutu har liman................* [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 39: D'akin Innah Laminde ta wuce cikin kuka ta ɗauki mayafin ta da jakarta ta fito babu ko sallama ta shuri flat shoes ɗin ta baqaqe masu kyau ta bar gidan, dik kiran da Innah Laminde ke yi mata be sa ta juyo ta saurare ta ba balle ta ansa ta, haka Billy ta sa kai ta bar gidan, ba ta tsaya ko ina ba sai a tasha,tana zuwa ta samu mota babu mutane sosai se ta kirawo driver tace ya zo su tafi a haka za ta biya shi kuɗin har da qari ma tana so ya kaita kano, cike da murna kuwa driver ya yi sallama da abokan shi ya shige mota ya bata wuta suka bar qauyen Ba Mugu. Innah Laminde ce ta kalli Abdul dake ci gaba da yi mata magiya kamar bai ga sanda Billy ta bar wajen cikin kuka ba, shi yanzu baya kallon kowa a gaban shi da idanun zuciyar shi da idanun saman fuskar shi da ya wuce Mommy, cikin ɓacin rai Innah ta kalle shi tace, "Yanzu Abdul abinda ka yi ka kyauta kenan? Yarinya na son tin tana qarama har wa girman ta amma kake wulaqanta ta? Anya Abdul haka ake rayuwa? Kai fa da bakin ka kace ba zaka auri Hadizan baka tsane ta baka ko son ganin ta, to yanzu me ya sauya ra'ayin ka akan ta?" "Ni dai a bar tuna baya a fuskanci gaba dan Allah Innah, koda da nace ba zan auri Hadiza ba ai nace ba zan auri wannan mara kunyar ba ko? Ni fa dama can bata yi min ba, yarinyar nan kwata-kwata bata da tarbiyya ke ce baki ga abubuwan da take yi ba idan ta ganni,yanzu dai Innah in dai farin ciki na nada mahimmanci a wajen ki dan Allah ki shige min gaba a nema min auren Hadiza,Innah taɓa qirji na ki ji yanda yake bugawa (nan take yaja hannun Innah ya ɗora a saitin zuciyar shi), a dik bugun zuciyar dake qirji na ina jin yanda soyayyar Hadiza ke qaruwa a raina," Ajiyar zuciya Innah tayi sannan tace, "Abdul dole na so farin cikin ka domin kuwa a kaff yaran gidan nan kai ne yaron da yafi kowa kyautata mana yake son ganin mu cikin walwala da wadata da farin ciki, ba iya ni da mahaifin ka ba kaɗai, gaba ɗaya iyayen ka na gidan nan da dangin mahaifin ka da nawa duk kana kula da kowa, tin baka da shi har Allah ya azurta ka,dan haka zan yi wa mahaifin ka magana a nemo mahaifin ta a yi maganar aure a tsakanin ku,Allah ubangiji ya sa hakan shine yafi zama alkhairi, Allah ubangiji ya kare dikkan sharrin dake cikin tarayyar ku," Wani irin kwanciyar hankali ce ta ziyarci Abdussaboor wanda ya samu kanshi da murmusawa tare da duqawa a gaban mahaifiyar shi ya hau godiya kamar zai koma cikin ta, tin bata murmushi har sai da ta murmusa ta sanya masa albarka. "Yanzu yanda za a yi ka kira min Azizah tazo ta je gidan Mai dusa ta ga ko Bilkin ta je ta sanar da Ta Annabi tazo ina son ganin ta da gaggawa, saboda bana so maganar nan ta b'ata zumuncin dake tsakani na da qanwata," "To Innah bari na aika ta yanzun nan, to ya zancen yi wa Mai martaba maganar Hadizan?" "Ohhh wannan wutar ciki da kake nunawa na bani mamaki Abdul, ai ka bari washegari da safe sanda yafi karb'ar qorafi ko sauraren duk wata magana mai mahimmanci sai na sanar da shi ko? Kai dai ka dage da addu'ar neman zaɓin Allah alkhairi a game da auren ka," Cikin sauri ya katse Innah Laminde da fad'in, "Hadiza ce alkhairi na Innahr mu," Sultan ne ya shigo ya samu waje ya zauna yana furzar da iskar bakin shi sannan ya gaida Innah Laminde ya kalli Abdul dake cikin shauqin qauna yace, "Yah broth how far na, anything for me?" "Hummm Sultan kenan kai dai kullum baka da magana sai ta anything for you kamar kai nake yi wa neman," Dariya Innah tayi tace, "Ahh toh yaro ka girma amma kullum kana maqale a jikin yayan ka, shi da zama yayi zai kai haka ne?" Suna tsaka da hirar ne wayar Abdussaboor ta yi ringing, har ya kai hannu zai ɗauka ta katse,da sauri ya miqe ya bar d'akin yana fara'a ya sake bin kiran,ba a ɗauka ba har sai da ta katse, gaba ɗaya duk wani kamewa irin tashi duk ya zubar a cikin qanqanin lokaci, sake kiran wayar yayi yaji baturiya na sanar da shi wayar da ya kira a kashe take, a kid'ime ya shiga d'akin shi ya shirya cikin manyan kaya yana zabga qamshi ya sanya takalmin shi ya bar gidan riqe da wayoyin shi da makullin motar shi. A qofar gida ya tarar da mutane suna zaune ana hira, suna ganin shi suka hau miqa gaisuwar su gare shi, hannu kawai ya d'aga masu ya faɗa motar shi, nan take wasu suka hau gulmar ya fara girman kai wanda ba halin shi bane, wani mutum ne yace, "Ahh dama zaka rasa basarake da girman kai ne? Ai kai dai kawai ayi sha'ani," Wani bawan Allah dake zaune yana jin hirar su da suke tin ɗazu wadda bata wuce zagin mutane da gulma da annamimanci ba ne ya kalle su yace, " Kuna da abun mamaki gaskiya, me yasa baku yi tunanin ko wani abune yake damun shi ba tinda kun dai san halin shi da fara'a da son mutane, yanzu kai da kake maganar girman kai kasan me kalmar girman kai take nufi a musulunci kuwa? Ana kiran mutum da me girman kai ne idan aka faɗa masa gaskiya yaqi ɗauka saboda yana ganin wanda ya faɗa masa gaskiyar be isa ya faɗa masa ba ya fi shi ɗaukaka ta kuɗi ko matsayi ko kuma ya girme shi,dan haka kaga baka sanya kalmar ma a muhallin da ya dace ba, mu dinga yi wa juna uziri dan Allah, dan kuwa ko babu komai kasha karb'ar 'yan kud'ad'en da yake bayarwa," Cikin dariyar yaqe wanda ya kira Abdul da mai girman kai ya hau cewa, "Ahhh abun kuma ya zama 'yar gori?" Shima bawan Allah'n cikin dariya yace, "Babu maganar gori tinda bani na baka ba, nasiha kawai nayi maka Allah yasa mu dace," Gaba ɗaya sai suka haɗa baki suka furta, Ameen. Abdul na isa qofar gidan su Mommy sai ya kirawo wani yaro dake wasa a qofar gidan ya aike shi yace yaje ya kirawo masa ita, cike da murna da farin ciki yaron ya tafi kiran Mommy dan kuwa ya gane waye Abdul, abun farin ciki da alfaharin shine ace mutum kamar Abdul ya aike shi. Yana shiga ya tadda Ameerah na ta kuka a tsakar gida tana rantsuwa babu wanda ya isa ya aurawa Saddiqa Munir ko za a yi yaqin duniya ne ba baɗe ta da barkono ba, dik wannan mintunan da ta ɗauka tana kuka babu wanda ya kula ta balle yace tayi shiru. Shi kuwa Munir takaicin yanda ma aka yi yarinya mara hankali kamar Ameerah ke son shi yake yi, a ganin shi a jerin mutanen da ya kamata su so shi Ameerah bata cikin lissafin su, dan haka da b'acin ran ta ya koma gidan su shi da Sadeeq da ke cike da murna da farin cikin hukuncin da Baabaa ta yanke. Cikin fara'a yaron yace, "Wai inji Yarima SARAUTA yace a kira masa Hadiza," Cikin takaici Ameerah ta kalli yaron bata ce masa komai ba ta miqe ta zaro iccen dake cikin wuta ta bishi a guje, nan take kuwa yaro ya kwasa da gudu ya bar gidan yana faɗin, "Wayyoo Allah na mahaukaciya 'yar macukule ta biyo ni da wuta," Ko ta kan Abdul be bi ba yayi gidan su da gudu,ganin haka ne ya sanya Abdul zuwa bakin k'ofar gidan ya dinga bugawa yana zabga sallama, ya kai kimanin minti biyar yana

Chapter 26 of 70