Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta ga Bilal na dawowa cikin sassarfa,shiru tayi ta hau share hawayen ta ta buɗe rigar ta ta fara shayar da Amir,Bilal na zuwa ya ci karo da Mommy ta buɗe ƙirji babu ko kunya da tunanin rashin dacewar hakan,tsaki ya ja kaɗan sannan ya shiga ya tada motar suka bar asibitin. Sanda suka isa gida a mota ya zauna ya jingina da kujera ya ce su shiga su fito da kayan su zai kai su tasha,babu musu suka wuce ciki mommy na kuka kamar ranta zai fita suka fitar da kayan su,fita Bilal ya yi ya kwashe kayan ya zuba a bayan mota wasu kuma ya zuba su a gefen direba,sai da su Mommy suka shiga motar suka zauna sannan ya je ya kulle gidan ya jefa makullin gidan a aljihun shi. Motar ya shiga ya tada suka nufi tasha,a hanya Mommy ta hau tinanin ranar farko da ta fara zuwa garin kano da sunan aikatau har zuwa ranar da ta sake dawowa domin zaman aure,gashi tin ba a je ko ina ba ta rusa rayuwar auren nata gaba ɗaya da hannun ta,wata mota ce ta gilma ta wuce su fara tass mai baƙin gilashi,Mommy na nan kanta manne da jikin gilashin motar su ta ga motar ta rage gudu ta dawo saitin inda tasu motar take,ba tare da an buɗe gilashin ba motar ta ci gaba da jera gudu da ta su Mommy,har suka isa tasha Mommy na kula da motar. A tasha Bilal ya tsaya ya hau fitar wa da su Mommy da kayan su,masu dako ne suka ɗauka suka kai musu bakin motar da za ta kai su ƙauyen Ba Mugu,Sallau ta gani ya fito daga cikin farar motar nan ya nufi inda suke yana washe baki kamar tin da can sun yi zaman amana da shi,halin da ya ga Mommy a ciki ne ya sanya shi sake son zuwa inda take dan ya ji kanun labarai ya fesawa uwar ɗakin shi K'waisa. Bilal na tsaye yana biyan kud'in motar da zata kai su Mommy tasha ya ga Sallau ya isa gaban Mommy ya ce, "Ahhh Sweet H kece kuwa ko dai ido na ne ke yi min gizo?" Hannu Bilal ya harɗe a ƙirji yana kallon ikon Allah,cikin yaƙe Mommy ta ce, "Sallau daga ina haka? Ya bayan rabuwa kuma? Ya su Zuby?" "Humm ai Zuby a ranar da kika jinyata uwar ɗaki a ranar aka kore ta,ni kaina yanzu ban san ina take ba, kema kuma sai kika yi ɓatan dabo, wannan jinjirin fa?" "Ɗana ne,Allah sarki Zuby yarinyar kirki,na taya ta murna da Allah ya kubutar da ita daga hannun karuwai da ƴan daudu, ku da kuka ga zaku iya zama ai sai kuyi tayi, Allah ya ganar daku, kaga sai anjima tafiya zan yi." "Nima ai na jima rabona da gidan,yanzu dai kina kan hanya bani No ki mayi waya." Babu tunanin komai mommy ta baiwa Sallau lambar ta suka yi sallama ya wuce mota itama ta shiga wadda zata kai su ƙauyen su,Bilal kallon mamaki kawai yake bin Mommy da shi,shi ya rasa ma abinda zai kira lamarin da shi,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Allah ya kyauta ya ƙara shiryar damu hanya madaidaiciya." Sai da motar ta tashi sannan ya bar tashar ya koma asibiti,ko da ya je waje ya samu ya zauna kawai,bashi da niyyar sanar da Abdul abinda ya faru,dan haka sai ya miƙe ya ce, "Bari na je na sama mana abinci, ni sai yanzu ma na fara jin yunwa." "To Bilal,ni dai dan Allah abu mara nauyi za ka kawo min,idan zan yi bayan gida ji nake kamar zan rasu wajen nishi,ni kaɗai na san irin azabar da nake sha Bilal." Tausayin Abdul ne ya kama abokin nashi,ba tare da ya ce komai ba ya bar ɗakin,Abdul kuwa komawa ya yi ya lafe a jikin pillow yana numfashi sama-sama,har baya so ya kulle idanun shi saboda yanda Mommy ke yi masa gizo a cikin su,Huzaimah ta kira shi tinda abun ya faru yafi sau shurin masaƙi amma ya kasa sanar da ita asalin abinda ke damun shi. Yana so ya sanar da su Innah Laminde me ya same shi nan ma yana tsoron kar magana ta watsu a gari,wasu hawaye ne masu zafi suka fara zubar masa,zuciyar shi na zafi ya furta, "Allah ka shiga lamari na,ban taɓa sanin soyayya zata juye ta koma ƙiyayya ba,me nayi maki a duniya mai muni haka Hadiza da zaki illata ni? Ya Allah kar ka sa na nakasa ta wannan wajen,Allah ka sa Huzaimah ta zauna da ni a yanda ta same ni." Har Bilal ya dawo da abinci ya buɗe masa Abdul bai san shigar shi ba,hankalin shi gaba ɗaya ya tafi wajen tunanin makomar rayuwar shi,Bilal ne ya sauke ajiyar zuciya ya ajiye abincin sannan ya dafe gadon,kanshi ya sunkuyar yana jin zafin ganin abokin shi a cikin mawuyacin hali,da ƙyar ya danne raɗaɗin da yake ji a zuciyar shi ya sake buɗe salad ɗin dankalin turawan da ya ji k'wai da hanta,gefe ɗaya kuma coca-cola drink ya buɗe masa sannan ya ce, "Ka sanyawa zuciyar ka haƙuri Abdul kar ka jawowa kanka wani ciwon kuma na daban,Hadiza dai na saka su a mota shata ma na musu sun kama hanya sun tafi,idan tinanin Amir kake yi babu abinda zai same shi da ikon Allah,ka maida hankali akan lafiyar ka,ka warke ka ci angwancin ka yanda ya kamata,sannan dole ne a yau ba sai gobe ba ka sanar da Huzaimah abinda ke faruwa na gasken-gaske,saboda ba zai yu yarinyar mutane ta zo ta ga saɓanin abinda aka sanar da ita ba,zan kira Innah na sanar da ita ta yanda baza ta ɗaga hankalin ta ba inshaa Allahu,oya riƙe nan ka cinye Allah ya baka lafiya." Karb'ar abincin ya yi yana kallon Bilal da ya ƙi yarda su haɗa ido aboda yanda yake jin ƙwalla na ƙone masa idanu da zafin ta,murmushi Abdul ya yi sannan ya ce, "Na gode ɗan uwa na,domin Bilal ka wuce aboki a waje na,kai amini na ne,kai ɗan uwana ne,ina kaunar ka domin Allah,kuma ina roƙon Allah yasa ko a lahira mu shiga aljannah tare,Allah ya sakawa iyayen ka da alkhairi da suka baka tarbiyya ta gari da nake amfana da ita a tarayyar mu,Allah ya ƙara tsare ka da yin koyi da munanan halaye na,Bilal na gode sosai akan dik abinda kake yi min na alkhairi, sanadin ka ne na dena zina a lokacin da giyar kuɗi take ruɗa ta,sanadinka ne na fara riƙo da addinina yanda ya kamata,madalla da samun aboki na gari kamar ka a rayuwa ta." Hawayen da Bilal ke ta riƙewa ne suka zubo,duka ya kai wa Abdul a kafad'a sannan ya ce, "Dan iskanci se da ka sa na zubar da k'wallar nan da ta nace itama sai ta zubo ko? To film ɗin ya isa haka mu ci abinci yunwa nake ji,kai in ba ma dan tashin hankalin da aka shiga ba yaushe zan kai war haka ban ci komai ba?" Daga nan suka maida hirar tasu ta koma ta barkwanci irin na abokan da suka shaƙu da junan su. ************************** Allah-Allah Sallau yake yi ya kaiwa K'waisa pampas,hand gloves,da sprit tare da sauran Antibiotics ɗin da ya tafi siyowa sannan ya fesa mata labarin da ya samo mata mai ɗumi,tin da ya isa gidan ya ke jin hayaniya na tashi kamar za a ɗaga gidan ga kuma motar Sam a parking space,kukan K'waisa ne ya fi tadawa Sallau hankali,yana ƙarasa shiga ya tarar da Sam tsaye a kan K'waisa shi da wani matashi fari tass da shi kyakkyawa suna zazzagawa K'waisa masifa. "....kin ji na faɗa maki,ko nace ka ji na faɗa maka, ka fita daga harkar fiance ɗina,kar ka sake kiran shi ko ka tura masa text message,in banda jaraba ma irin ta tsohon ɗan daudu an ce ba a yi da kai, ba a yi da kai dole ne? Ka kama kan ka mana ka ci gaba da jinyar takashin ka da tsutsotsi ke fita kamar taliya,to ka sani wannan shine warning na ƙarshe da zan yi maka,next time ka kuskura ka yi abinda ya sa na zo gidan nan da kai na sai na yi ajalin ka." K'waisa babu abinda yake banda kuka da kallon Sam da ke shafa matashin dake masifa kamar zai tashi sama,Sallau ne ya yi wurgi da kayan hannun shi ya tafi a guje ya yi tsalle ya naushi matashin a fuska,nan take haƙorin matashin na gaba ya faɗi ƙasa,wani irin ihu mai haɗe da kururuwa matashin ya saki sannan ya faɗi ƙasa yana birgima, Sam na ganin haka ya kalli Sallau cike da ɓacin rai,gani ya yi babu abinda zai ɗiba a jikin Sallau sai dai ma ya daku,dan haka sai ya tashi saurayin shi yana faɗin, "Ku jira ku ga abinda zai same ku,ku jira ku ga yanda zan wulaƙanta rayuwar ku da ga kai sabon kwarton nata zuwa ita kanta uwar ɗakin naka,shegu tsinannu matsiyatan banza kawai masu yoyon kashi." "Tsinewa ai ta ƙare a kan ka,inshaa Allahu kai kuma ɗan daudun banza sai ka fi Hajiya lalacewa da shiga tashin hankali,ka jira ƙarshen ka ka gani,za ku fita daga gidan ko sai na illata ku?" A gurguje Sam ya kama saurayin shi suka bar gidan suna zage-zage, shi kuwa saurayin Sam suna fita ya kafe Sam da mari sannan ya ce, "Daga yau babu ni babu kai,tinda a gaban ka aka cire min haƙori aka kassara kyau na baka ɗauki matakin komai ba, matsoracin banza kawai, nayi dana sanin fara tarayya da kai a rayuwa ta." Dik yanda Sam yaso ya lallashi saurayin nashi abun ya ci tura,a guje matashin ya fita yana kuka,Sam ma mara masa baya ya yi yana kiran sunan shi,cikin rashin sa'a wani ɗan kabu-kabu ya shawo kwana a guje ya kwashe Sam ya watsar a gefen titi,a kid'ime mai kabu-kabu ya tsaya yana salati,saurayin Sam na ganin Sam kwance a ƙasa baya motsi sai kawai ya ɗale bayan kabu-kabu ya ce, "Dan Allah kai ni unguwa uku biyo ni ya yi zai yi luwaɗi dani dan ya ganni haka,ni ba ɗan iska bane, rayuwa cikin yayuna mata ne ya sa nake a haka,dan Allah ka kaini unguwa uku." Kuka saurayin Sam ya fashe da shi,nan take mai kabu-kabu yaga ai wannan damar shi ce ta ya gudu kawai, dan haka sai ya figi machine ya bar Sam yashe a ƙasa suka bar unguwar gaba ɗaya. Sam na nan kwance har magariba babu wanda ya san da shi balle a taimaka masa. A can gidan k'waisa kuwa Sallau ya gama taimakawa K'waisa ya gyara jikin shi,sannan ya bashi magunguna ya sha,kuka kuwa K'waisa ya yi shi har ya ji babu daɗi,wata iriyar nadamar rayuwar da ya yi a baya ce ta dame shi,ya gama saddaƙarwa babu makawa yana daga cikin makamashin wuta a ranar gobe ƙiyama,saboda shi ba mai ilimi bane balle ya gane babu abinda ya cancanci rayuwar shi da ya wuce tuba zuwa ga Allah,shi kanshi Sallau bashi da zurfin ilimin addini balle ya ja K'waisa zuwa tafarkin da ya dace,suna cin abincin dare Sallau ya ce, "Kashhh Hajiya ai na manta ban baki wani labari ba,na dawo da zazzafan labari na ci karo da waɗancan marasa mutuncin." "Sallau ka kira ni da Yusuf d'ina,ni yanzu ba Hajiyar kowa bace,kai a tunanin ka yanzu akwai wanda zan iya miƙawa baya na ya sake lalata min rayuwa? Har abada ba zan sake komawa irin rayuwar dana yi a baya ba, ba kuma zan dena tsinewa wanda ya yi sanadiyyar shiga ta wannan mummunar rayuwar ba,da na sani lokacin da na mallaki hankalin kaina na bi Allah da rayuwa ta bata dawo irin wannan ba." Hawaye ne masu zafi suka zubowa K'waisa,cikin son kawar wa da K'waisan baƙin cikin dake ran shi Sallau ya ce, "Kar ka damu,ina nan tare da kai, ba dan komai ba sai dan irin halaccin da ka yi min a rayuwa ta,ka san labarin da zan baka kuwa?" Girgiza kai kawai K'waisa ya yi,nan take Sallau ya sanar da shi haɗuwar shi da Mommy sannan ya ƙara da cewa, "Yanzu haka ina da No ta,ka ga sai ka baiwa Alhaji ka huta da masifa da bala'in shi da kullum yake addabar ka da shi." "Rabu da matsiyaci Sallau babu lambar da za a bashi,idan yaso ya yi kilishi na ni ya hutar dani ma,na tsani duniyar nan na tsani zaman cikin ta." K'waisa na faɗin haka ya tashi daga saman dinning ɗin ya hau sama,jiki babu ƙwari Sallau ya zabga tagumi yana tunanin me zai yi to ya taimaki K'waisa da rayuwa ta juyawa baya? ************************ A ƙofar gidan Ɗan Liti motar su Mommy ta tsaya,wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zuba a idanun Mommy,cikin sauri ta share su sannan ta miƙawa Naja handbag ɗin ta dake gefen ta dan a fitar da kayan gaba ɗaya,a hankali ta fita daga motar rungume da Amir a kafad'ar ta,kayan driver ya dinga taya su shigarwa gidan kafin ya fito ya yi musu sallama da godiya ya wuce. Sai da Mommy ta tsaya ta ƙarewa ƙofar gidan nasu kallo,dik irin kuɗi da daular da Abdul ya wadata ta da shi bata taɓa tunanin ta gyara gidan su ba,gashi rayuwar zama a gidan ta sake kama ta,cikin sauri ta faɗa soron gidan saboda ganin ƙawar Innoh Ramma na nufato gidan nasu riƙe da bokiti a hannu,Innoh na tsaye a saman akwatinan kayan Mommyn tana ta faɗin, "Lale maraba lale da mutanen birni,ku yanzu baza ku iya barin ku yi arba'in ɗin ba kafin ku zo yawon ganin gida?" Maganar tace ta maƙale a lokacin da ta yi ido huɗu da Hadizan ta da Naja suna shiga cikin gidan........ [09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 89: "Ke Naja lafiya naga fuskar Mommy haka? Me ya same ku kuke kuka? Innalillahi ! ko rasuwa aka yi?" Innoh ta faɗa cike da tsoro da dafe ƙirji kamar wata ƴar daudu,Naja ce ta ce, "Babu wanda ya mutu sai auren Hadiza,Abdul ne ya sake ta saki ɗai-ɗai har uku saboda zai yi mata kishiya ta nuna rashin amincewar ta akan hakan." Wani irin jiri ne ya fara ɗaukan Innoh,da sauri ta dafe gini ta jingina tana bin kayan Mommy da kallo,cikin rawar baki ta ce, "Ban gane ya sake ta saki uku ba Naja? Kuna nufin babu kome fa? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una na shiga uku ni Innoh ina zan kai wannan abun kunyar? Maza shiga ɗaki da kayan nan Naja kafin maƙiya su ji su fara yi mana dariya." Baaba ce ta ƙaraso ta na salati,domin kuwa ta ji shigowar su Mommy sai ta fito tana murna dan ta ga jariri ta ci karo da wannan mugun labarin,Ramma kuwa da ta kawo markaɗen waken awara sai ta samu waje ta zauna a saman bokiti ta rabka salati sannan ta ce, "Abinda da yasa na kawo markaɗe da kai na kenan ban aiko yara ba Innoh,wani mugun labari naji wai Yarima Abdussaboor zai ƙara aure har ma an tafi kai lefe,ashe-ashe ma kun samu labari har an yi ɓatacciya,kaiiii subhanallahi wannan abu beyi daɗi ba sam." Baaba na buɗe baki zata yi magana Innoh ta saki jikin ginin da take a jingine ta ƙanƙance ido sannan ta hau nuna Baaba da yatsa tana faɗin, "Allah ka raba mu da magauta na gida da na waje,ai ke fa yanzu abun farin ciki ya same ki auren Mommy ya mace, to sai ki saka lasifika ki hau turmi ko tsani ko kuma ki bi lungu da saƙo na garin nan ki sanar da wanda be sani ba." Cikin tsananin ɓacin rai Baaba ke bin Innoh da kallo,yau ko babu wata alaƙa a tsakanin ta da Mommy ai ba zata so auren ta ya mutu ba,to menene abun farin ciki a mutuwar auren wani? Kafin Baaba ta baiwa Innoh amsa Sule ya buɗe ɗakin shi ya fito, da ƙyar yake takawa saboda yanda jikin shi ke yi masa ciwo ko ta ina,Innoh ya kalla cike da takaici ya ce, "Ke wai Innoh yaushe zaki gyara ne? Yaushe zaki dena ɗaukan abinda kike ji akan wani ki dage shima haka yake ji akan ki? Innoh yaushe zaki gane mu ƴaƴa ne ba wai kadara ba da zaki dinga tinƙaho damu bayan babu wata tarbiyyar arziƙi da kike bamu? Innoh anya kin san su wanene ƴaƴa kuwa? Kin san haƙƙin ƴaƴa akan uwayen su? Yana daga cikin haƙƙin mu ku sanya mu a makarantar islamiyya har ta zamani ko ku koyar damu addini a gida,ko kin san wannan halin da na shiga dik yana da nasaba da rashin ilimin addini? Innoh me yasa a kullum kike ɗora laifin gazawa akan bamu tarbiyyar da baku yi ba akan Baaba dake yi mana ƙoƙari? Ke kuma Mommy ki shige ciki ki huta zuwa gobe zamu yi magana akan wani abu muhimmi,ki sanyawa ran ki auren nan naki da ya mutu ba ƙarshen duniya bane ya zo,Allah yasa hakan shine ya fi alkhairi." Sule na gama faɗin abinda ke ran shi ya wuce ɗaki,Baaba ma addu'a tayi akan lamarin sannan ta ce, "Kin dai ji abubuwan da ɗan ki yace,ruwan kine ki gyara kuma ruwan ki ne ki ci gaba da tata rashin kunyar ki da kika saba,Mommy Allah ya sa hakan shine yafi zama alkhairi a rayuwar ki." A hankali Mommy ta amsa da "Amin" sannan ta ja ƙaramin akwatin dake gabanta sannan ta wuce ɗakin su na da,tana shiga ta saki akwatin ta rushe da kuka,gani tayi komai ya sake lalacewa buhun gawayi ne ma a ɗakin a jingine,da alama Innoh ce ke saida gawayin,ga katifar ta nan jingine dik ta yi ƙura gefen ta kuwa wani abu ya gwaigwaye ta, wanda take kyautata tsammanin ɓera ne. Wani irin tsoro ne ya kama ta ta rungume jaririn ta da kyau a ƙirjin ta,yanzu a haka zata ci gaba da rayuwa anan kenan? Inaaa ba zata saɓu ba bindiga a ruwa dole ne a sama mata wajen zama mai kyau, dan kuwa ta tabbata idan ta kwana anan zata iya yin zazzaɓi. Ƙarshe waje ta fita ta samu waje ta zauna a saman turmi tana kallon Ramma dake shirin barin gidan,dan kuwa ta kula ko dubu nawa zata bayar a matsayin kud'in niƙa babu wanda zai yi mata,tsaki Mommy ta ja dan kuwa ta san yanzu labari zai baza gari. Naja ce ta shiga kiciniyar gyaran ɗakin kafin ta wuce gidan Kaka,dan kuwa ta san tinda mommy ta fita to fa baza ta gyara ba,ƙurar da ta dinga shaƙa ce ta sanya mata mura irin mai zubar da majinar nan,tana kammalawa tayi musu sallama zata wuce,kafin ta tafi ne ta ce wa Mommy, "Ki kwantar da hankalin ki,idan ya san wata ai bai san wata ba,aure ne sai kin koma shi da izinin Allah, ki bari a kwana biyu abubuwa su lafa ni da kaina zan shige maki gaba ki koma ɗakin ki." Hawaye Mommy ta share kafin tace, "To Aunty Naja na gode da kulawar da kika bani kamar ke kika haife ni,Allah ya saka da alkhairi,dan Allah muje na baki ɗan wani abu ki kai wa Kaka." Ɗaki suka koma Mommy ta bada sabuwar atampa da kuɗi tace a kaiwa Kaka,sannan ta baiwa Naja itama atampa da shadda guda ɗaya, godiya tayi mata kafin ta wuce. Ganin ɗakin ya sha gyara dai-dai misali ne ya sanya Mommy zama gefen katifa tana kafe ɗan ta da kallo tana jinjina ikon Allah. Da dare bayan Ɗan liti ya dawo ya kira Mommy da Innoh,nan fa Mommy ta zauna ta basu labarin kafff abinda ya faru, faɗa sosai Ɗan Liti ya dinga yi mata,kafin ya ce, "Malam Jibo ne ya fara sanar dani maganar sakin ai,wai Ramma ce shima ta kira shi take faɗa masa,yanzu fisabillahi Uwata kin kyauta kenan? Allah ya ɗaukaka ki kina gidan hutu ki dawo nan?" Tura baki Mommy tayi kafin tace, "Ni dai Baba ku dena ganin laifi na,taya za ai ya jajiɓo aure ina matar shi yaƙi sanar dani?" "Ni dai a bar wannan maganar,idan ana tado ta zuciya ta bugawa take da ƙarfi." Sallamar Ameerah ce ta katse masu hirar su,cikin hauragiya da hargowa ta hau masifa tana zagin Abdul tare da aibata shi da dangin su,sai da ta gama zibar gadon rashin mutunci kafin ta gaida iyayen nata,zama suka yi suka ci gaba da tattauna lamarin kafin ta leƙa ɗakin Sule ta yi masa ya jiki, bayan ta fito ko wajen Baaba da ta dawo bata leƙa ba balle ta gaishe ta tayi wa su Innoh sallama ta wuce,su kansu babu wanda ya yi azancin yace ta je ta gaishe da Baabaan. ************************** Dik wani plan da ya kamata Any da Hisbah da kuma Jami'an tsaro su haɗa sun gama haɗawa, Billy na can kwance a asibiti domin kuwa ƙurajen bakin ta sun fito har a gaban ta,likita bai hana ta amfani da magungunan da ta zo dasu ba saboda suna da kyau da inganci,ruwa aka sanya mata tare da ɗura masu alluran da ke ɗauke da strong antibiotics a ciki,bacci mai daɗi ne ya ɗauke ta wanda ta jima ƙwarai bata samu irin shi ba,a nan Any ta bar ta ta wuce gida dan ta shirya ta sanar da Alhaji zuwan su Nigeri. Cike da farin ciki Alhaji yace, "Welcome back my dear,akwai fa kaya a ƙasa masu kyau,ba ƙaramin kaya za mu ja ba mutuniyas,yaushe zaki shigo?" "Gaskiya sai na huta,babyna bata da lafiya yanzu haka tana asibiti a kwance,nima zuwa nayi na yi wanka na huta sannan na koma wajen ta." "Ayyaa Allah ya sawaƙe." "Amin,ina ga mu bari zuwa jibi da misalin 12 na dare sai mu haɗu a club ɗin ka ka nuna min kayan ko?" "Hakan ma ya yi, brohhh sai kin gan su, tsala-tsala da su, na tabbata sai kin zaɓi wata a cikin su ko hutawar sati ne kiyi da ita." "Hhhhh to shikenan ba wahala sai mun sake waya," Suna gama waya Any ta kira shugaban ƴan sanda ta sanar da shi abinda suka tattauna da Alhaji sannan ta ƙara da cewa, "Maga ta gaskiya sai kun ƙara Jami'an tsaro, kuma ya zamana kuna da kayan aiki sosai,idan ba haka ba Alhaji da mutanen sa za su iya samun nasara akan ku,yana da mazaje zarata sun kai ashirin ko sama da haka dake aiki a ƙarƙashin shi, kuma dikkanin su suna da makamai kamar yanda na sanar daku tin fari,dan haka dole sai anyi shiri sosai,saboda kar azo ana ɓatacciya suyi galaba akan ku." 'Kar ki damu,kedai ki ci gaba da updating ɗin mu akan dik abinda ke faruwa kawai.' Sallama suka yi Any ta shiga banɗaki domin yin wanka,madubin jikin bango dake a cikin band'akin nata ta kalla,ganin ta tayi kamar namiji,nan take ta tina da rayuwarta ta baya,a baya bata da suturar da ta wuce riga da zani na atampa,sai kuma dogayen riguna na atampa,ko materials ko kuma shadda,kullum idan zata fita kuwa sanye take da hijabi da jiƙabi,me ya sami wannan halittar dake tsaye a gaban ta har ta manta Allah? Me yasa ta san halal da haram amma take takewa? Ina zata kai zunubin da ta ɗauka a baya? "Anya Allah zai gafarta min kuwa? I killed Arica....i killed her, matan da na yi sanadiyyar shigar su bariki fa? Matan da suka rasa rayukan su ta sanadiyyata fa? Anya zan samu rahamar Allah kuwa?" Kuka ne ya ƙwacewa Any nan ta durƙusa a ƙasan band'akin nata da yake wanke fesss saboda gyaran da yasha kafin su iso daga masu aiki,kuka ta dunƙule waje ɗaya tana ci gaba da rizga kamar zata shiɗe,a hankali ta tsaya saboda yanda ta ji zuciyar ta na maimaita mata ayar, 'Lataknaɗu min rahmatillah..........innallha yaghfiruddhunuba jami'a.' Idan hakane tuba ya kamata ta yi tayi har sai Allah ya yafe mata kawai,jiki babu ƙwari ta miƙe ta cire kayan ta dan ta yi wanka, dik wani tattoo da ta zana sai da ta sa hannu tana shafashi,yanzu idan taje lahira Allah be yafe mata ba ko a iya tattoo ɗin nan fa sai ta ji jiki tinda Allah ya haramta. Wanka tayi da kyar ta ɗaura alwalar da ta manta yaushe rabon da ta yi ta,tana kammalawa ta fito d'aure da towel,idanun ta sun kumbura saboda kukan da tasha,muryar ta kuwa ko fita bata yi a haka ta fita ta kirawo mai aikin ta,tana zuwa tace, "Zulfa bani aron hijabin ki,zan baki kuɗi gobe ki je kasuwa ki ɗinko min guda ashirin nawa,sannan a d'inka wa bab..ammm Bilkisu guda ashirin,manya muke so ba ƙanana ba please." Mamaki ne ya kusa kashe wadda aka kirawo da

Chapter 56 of 70