gaba ɗaya ta faɗa gado tana murna, dan kuwa tayi kewar shamsu sosai tunda tazo sai dai ta ga kowa na jin daɗin shi amma banda ita,ita ko ba za a bata sisi ba kawai ta samu biyan buqatar ta ya wadatar, da wannan tunanin Mommy ta kwanta bacci.
Washegari tun da asuba Hajiya K'waisa ta aika Ruby kiran ta wanda hakan ba qaramin mamaki ya bata ba............
*To nima dai na yi mamaki mutumin da baya tashi domin sallar asuba ya doka wannan uban sammako haka?*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
PAGE 16:
Saida mommy ta yi sallar asuba sannan ta nufi hanyar d'akin da Hajiya k'waisa ke jiranta, ta na shiga ta ga Hajiyan kashingid'e a saman wata royal chair mai hannu ɗaya,ta na sanye da wata had'ad'd'iyar kimono a jikin ta, kanta d'aure da ƙaramin towel kalar kimono ɗin jikin nata, gefe ɗaya Zubaida ce duƙe a saitin ƙafafunta ta na matsa mata su, cikin isa da izza ta miqa hannu ta ɗauki Apple juice ɗin da Ruby ta kai mata, ganin Mommy na shiga d'akin ne ya sanya ta ɗauke kai tare da jan guntun tsaki yace,
"Ai da yanzu nake so na sake aika Sallau ya gano min me kike yi a d'akin da ba za ki zo dan amsa kira na ba,"
"Ki gafarce ni Hajiya, ai na yi zaton tashi na aka yi dan gabatar da sallar asuba shi yasa na yi sallar, ina idarwa Ruby tace min ni kaɗai kike jira shi yasa na zo nan ɗin yanzu"
Kallon Ruby Hajiya K'waisa ta yi, sai yanzu ta gane dalilin jimawar ta ashe sai da ta sake bi ta wajen Mommy ta kirawo ta, fari ya yi da idanun sa sannan ya kur'bi juice ɗin ya mayar kan side table ɗin dake wajen sannan ya tattare rigar shi ya miqe tsaye yana rangwad'a, kallon su Sallau ya yi da Zubaida da ke tsugunne har a wannan lokacin tana jiran Umarnin Hajiyan, tafa hannayen sa ya yi sau uku sannan yace,
"To Zuby, Ruby da Sallau a bamu waje ko?"
"An gama Hajiya"
A tare suka bar wawakeken dressing room ɗin suka bar Mommy da ke jin d'akin ya yi musu kaɗan tsabar yanda take jin ta a takure, kallon Mommy Hajiya k'waisa ta tsaya yi daga sama har qasa, sannan tace,
"To alhamdulillahi komai ya ji baki da matsala a iya inda idanuna suka kalla, amma duk da haka crue ɗin dake yi min gyara na musamman a lokacin da nake da fita ta musamman kamar dai wadda zaki yi a yau za su zo su gyara min ke ciki da waje, za kuma su baki kayan gyara na mata wanda zaki sha ki maida quruciyar ki dan na riga na ji labarin kema 'yar hannu ce,"
Mommy na jin maganar Hajiya k'waisa ta qarshe ta buɗe baki tare da dafe qirji, Hajiyan ma baya ta ja ta yarfa hannu tare da mere baki tace,
"Meye zaki wani buɗe baki kina kallo na kamar na yi miki sharri ko qarya ne ba a gama rabawa gayun qauye ba kafin ki zo nan?"
"Hajiya duk wanda ya faɗa miki haka gaskiya yayi min qarya saboda ni saurayi na ɗaya ne kuma bamu taba yin....uhummm...bamu taba..."
"Dakata min ke ! An faɗa maki dole sai namiji ya kwanta da mace ne budurci ke guduwa? Shi fa budurcin nan ba wani nama bane mai kauri, bashi da k'warin da za ai ta fitar da ruwan jiki kuma ace ba zai tab'u ba, idan har zaki zauna ki yi wasa da jikin ki buqatar ki ta biya to ki sani tabbas budurcin ki yana cikin hatsari, haka zalika idan har zaki na barin namiji ya yi wasanni da ke to tabbas kina taɓa budurcin ki ne, dan haka dole ne a ɗauki matakin gyara dan ba zaki je ki sa naji kunya ba ah toh, bawan Allahn nan kuɗi ya bada wuri na dukan wuri kimanin miliyan biyar akan ki ke kaɗai, babu qaramar karuwar da ta zauna a waje na ta yi darajar ki a fitar farko, dan haka ina so ki gyara jikin ki da kud'in, gyara mai kyau ma kuwa, ke koda dika kud'in ki ka kashe a gyara ba laifi bane saboda gaba zaki samu fiye da haka, mu a bariki kud'in mu wajen gyaran jikin mu suke tafiya kin gane?"
"Na gane Hajiya, amma wanne mutumi ne wannan kike magana akai"
"Heeeee ragassss ! Keee yarinya gyara kimtsi mana da fa hajiyar karuwai manyan asshoshi kike magana, ko a zaton ki ban san kina yi min lab'e ba kina ji da ganin duk abinda nake yi a gidan nan?"
Wata iriyar fad'uwa gaban Mommy ya yi, da sauri ta sunkuyar da kan ta qasa ta hau kame-kame da bada hakuri,
"Ki yi haƙuri Hajiya....rashin Billy ne ya sa gidan yi min girma shi yasa nake fitowa, amma inshaa Allahu ba zan sake ba,"
"Be dame ni ba, shi yasa ki ka ga ai ban taɓa kula ki ba, anyways mu koma kan maganar mu, wannan bawan Allahn dai da kuka yi magana ta TikTok shine yake gayyatar ki zuwa resort ɗin shi sabo daya buɗe yana so ya yi weekend da sabon jini,dan haka dan Allah kar ki bani kunya, ki saki jiki ki ci arziqi ki bar arziqi a mazaunin sa, idan ya ji dai-dai ma wataqila ya qara kuɗi kin ga kema daga nan zaki faso gari ko?"
"Hakane Hajiya ina godiya da d'awainiya dani da kike yi,"
Kallon Mommy Hajiya k'waisa ta yi tana murmushi, yarinyar na burge ta da yawan godiya fatan ta Allah ya sa Mommy ta ɗore da biyayya ta kuma zama me riqon amana.
Qarfe tara na safe dai-dai kamfanin da ke zuwa har gida su yi wa Hajiya K'waisa gyara na musamman suka iso, nan take suka hau sama suka shiga dressing room ɗin Hajiya K'waisan, anan suka tadda su suka kwashi gaisuwa dan kuwa sun san shegen son girma irin na ɗan daudun ko dan ya sallame su da kyau dole su saki jiki suma su girmama shi kamar yanda yake so.
Nan take suka bawa Mommy housecoat mai santsi ta saka suka hau mulke mata jiki da kayan gyara kala-kala na zamani,ɗaya daga cikin su ta shiga bathroom ta haɗa ruwan wankan da ya ji kayayyakin gyara da turarukan qamshi kala-kala da flower.
Hajiya K'waisa na zaune tana latse-latse a laptop ɗin ta tana kora juice, Zubaida ce ta shiga wajen da kayan motsa baki ta ajiye, kafin ta fita Hajiya ta kalli ɗaya daga cikin matan tace,
"Ki bi ta kuje kitchen ɗin duk abinda ya dace a dafa mata a dafa a kawo nan taci na ci ta sha na sha dika anan a gabana ina kallo, ba maganar ba daɗi ko da d'aci,"
"To Hajiya, balle ma yanzu kayan namu duk an sake inganta su babu masu bauri a ciki,dik suna da daɗin su"
"Whatever"
Hajiya k'waisa tace tare da yin fari ta ci gaba da danna laptop ɗin ta, a tare ma'aikaciyar suka fita zuwa kitchen da Zubaida, nan ta shiga dafa kaza da sauran tarkacen magungunan mata, ta sa aka haɗa juice kala-kala duk na gyaran jiki ciki da waje tace a kai mata sama gata nan zuwa da sauran.
Sanda Mommy taga kazar nan guda wai kuma ita ɗaya zata cinye, sai wani farin ciki ya kama ta, ga wata jahilar yunwa dama tana ji, nan da nan kuwa ta zauna ta gyara zama ta hau cin kazar nan da sauran kayan madara da juices kala-kala da aka kai mata,tun tana ci ba mai kallon ta har sai da ta ja hankalin Hajiya k'waisa,ya kuwa buɗe baki yana yi mata kallo cike da harara, da ya gaji da kallon yanda mommy ke cin abinci ba aji ya daka mata tsawar da ta firgita ta yace,
"Ke ! Meye haka kike yi kina wani cin abinci se kace balama? Kin gan ki kuwa? A haka ne ki ke so ki zama wata a cikin wannan sana'ar tamu da ke yaye mata masu aji da k'walisa? To bari kiji ba inda zaki je ki kai labari in dai haka zaki dinga cin abinci hayam hayam,mu a sana'ar mu ana so mace ta zama mai aji, mai natsuwa da iya takun ta, ana son mace mai taqama da k'walisa, ana son mace mai juriya mara gazawa wajen biya wa customers buqatun su,ana son mace da bata da rawar kai, mai iya shagwab'a da lank'wasa jikin ta duk inda aka lauya ta,ana son mace wadda ta iya kallo ta iya sarrafa kallon ta, ana son macen da ta iya sarrafa bakin ta ta hanyoyi da dama, shi yasa na faɗa maki bakin ki kadarar ki ce, dan haka ki natsu dan Allah kar ki firgita shi yaga kina gatsa kaza irin haka ya tsorata, ina dalili irin wannan kaftu da kike yi haka kamar kin samu gona?"
Bayan gama yi wa mommy wannan jawabin ne Hajiya k'waisa ta tattare tarkacen ta tace idan sun gama su yi mata magana ba zata iya kallon shirmen Mommy ba, su tabbata sun koya mata duk abinda ya dace sun kuma yi mata duk abinda ya dace.
Mommy ba qaramin muzanta ta yi ba da wannan abun da Hajiya k'waisa ta yi mata, amma dake ta sa wa kan ta tana son yin abun sai ta manta da komai ta maida hankali wajen ɗaukan dika darasin da ake koyar da ita.
A gani na matar aure ce yafi dacewa duk ta iya waɗannan abubuwan, sannan maza yana da kyau duk qarshen wata a baka yi ba ka bawa matar ka dubu biyar idan kana da hali da iko ka bata sama da haka domin ta gyara jikin ta, kar ku manta matan banza fa wasu mazan ke kai wa kud'in dan su gyara su kusance su kusanta ta haramun,sun bar matayen su kyawawa da suka fi karuwan kyau a gida basu gyara su ba sannan basu basu abincin da zai gyara masu jiki ba da an yi magana suce basu da kuɗi, Alhaji idan ka gyara ta gida kai zaka mora ga lada ga morewa rayuwar jin daɗin aure. Ke kuma Ta rasulu dan Allah idan kina da hali da yanda zaki yi ki dinga gyara ba dole sai an baki ba, rashin gyara da kimtsin wasu matan ke bazama maza masu ƙarancin tsoron Allah wajen su Mommy da su billy,maza kar ku manta matan ku na haihuwa su na jinin haidha da na biqi, suna buqatar gyara, ko motace ana yi mata juyen baqin mai balle kuma ɗan Adam,kar ku yi sharar masallaci ku yi ta kasuwa.
Bayan wasu awannin da za su kai huɗu Mommy na gani sanye da wasu irin kaya masu tsananin ɗaukan hankali, riga ce irin mai haɗe da guntun wando kalar orange mai manyan flowers green hannun ta sanye cikin aljuhunan wandon gashin ta da ya sha gyara yana wani rawa yayi sama yayi qasa saboda rolling ɗin shi da aka yi sai reto yake a gaban fuskar ta tana wani maida shi baya.
Qafar ta sanye take da wani dogon takalmi green mai tsinin gaske da wasu igiyoyi da aka d'aura mata su har zuwa qaurin ta, hannu daya ta zaro daga aljihunta ta maida gashin ta baya a lokacin da take juyawa a gaban Hajiya K'waisa, ihu Hajiya k'waisa ta sanya tare da fad'in,
"Wayyooo Allah na ! Ashe wannan halitta zaki yi kyau irin haka iyayen ki suka qunshe ki a qauye ki ke zaune baki fito neman kuɗi da arziqin da Allah ya yi maki ba? Anya ba zan fasa aika ki wannan wajen ba a jira sai bikin new year?"
Murmushi kawai mommy ke zubawa ta na wani lumshe ido da gyara labb'an ta.
"Ke Ruby jeki d'aki na ki d'akko siririyar sarqar zinare da zobunan ta ki kawo min nan,ke cire mata wannan fake sarqar a jikin ta, wannan so nake ta zama International handbag ɗin Alhazai kin ganeee?"
Su kan su wanda suka gyara Mommyn kallon ta kawai suke yi, domin kuwa fatar ta ta koma kamar gilashi tsabar haske da sheqin da take yi, qafar ta ta sha gyara ga wasu farata da aka zuba mata dogaye kalar na hannun ta, ana kawo sarqar Hajiya k'waisa ta isa gaban Mommy da kan ta ta saka mata tayi wurgi da wadda ta cire mata, sannan ta sanya mata zobunan zinare a hannun ta, abinda mommy bata taɓa zato da tsammani ba kenan a rayuwar ta zata saka.
Murmushi tayi, Hajiya ta ɗan haɗe fuska tace,
"Ya banji bakin ta na fitar da sirrin qamshi ba irin nawa? Maza a d'akko min turare na na baki a saka mata a jakar ta, an haɗa mata akwatin nata dai ko? Komai an saka yanda ya dace ko?"
"Eh hajiya an saka komai da ya dace a saka,"
"Good"
Ana kawo turaren bakin Hajiya ta sa ta buɗe bakin ta fesa mata ta nuna mata yanda ake yi, nan take mommy ta maimaita kamar yanda taga Hajiyan ta yi, suna nan suna ta gyare gyare Sallau yazo ya duqa ya sanar da baqon Mommy ya iso yana waje yana jiran ta, jujjuya ta Hajiya K'waisa ta sake yi, saida ta tabbatar komai ya ji sannan ta raka ta har waje tana wani yanga,dukan kafad'ar Mommy tayi ta ɗan harare ta nan take mommy ta hau yanga itama tana wani kwarkwasa.
Glass ɗin had'ad'd'iyar motar aka zuge zuwa qasa, nan da nan mutumin ya bayyana, da kallo Mommy ta bishi dan kuwa ba za a kira shi da mummuna ba, kuma ba za a ce masa mai kyau ba,yana da jiki dai-dai misali shi ba mai qiba ba sosai shi ba siriri ba, sai uban gashin baki da ya ajiye kan nan ya sha aski k'wal da shi.
Murmushi ya sakar wa Mommy haqorin makka fari tas ya bayyana,cikin muryar shi mai nuna cikar mazantakar shi yace,
"Hajiyar gayu ashe dai wannan kifin naki babbar tarwad'a ce, masha Allah a zahiri ma tafi kyau,bismillah ko?"
Buɗe mata motar drivern shi ya yi ta shige, Hajiya k'waisa ta dafe glass ɗin motar tace
"To ga amana nan, guda na baka guda zaka dawo min da ita, Allah ya bada sa'a,"
Dariya suka yi shi da Hajiya K'waisan, da sauri ya dafe baki yace,
"Uffararan naa ce Allah bada sa'a kuwa? To koma dai meye kuje lafiya ku dawo lafiya sai na gan ku ranar litinin"
Hannu suka d'aga wa juna kafin motar ta fita ta bar gidan,ajiyar zuciya Hajiya k'waisa ta sauke sannan ta shige gida tana faɗin,
"Zan hau sama na huta kar wanda ya dame ni, baby ne kawai zai zo a bari ya hau bayan shi kar shegen da ya tashe ni, ku kuma zaku ji alert sai watarana"
Yana gama fad'in haka ya haye sama ya bar ma'aikatan dake shirin tafiya a nan suna kwasar kayan su.
***************************
Kusan a tare su Saddiqa suka kammala gyara gidan, suna gamawa Munir ya shiga wanka yace su jira shi ya fito zai maida su gida, haka kuwa aka yi su Saddeqa na nan zaune ya yi wanka ya gama ya sanya wasu riga da wando masu kyau tare da feshe jikinsa da turare masu qamshin gaske sannan ya d'aura agogon shi ya fito sanye da takalmi mara nauyi da makullin mota yace,
"Mu je ko? Na ji ma har an fara kiran sallah,"
Saddeqa kanta na qasa ta miqe ta yi gaba, dan kuwa tinda ya fito ta ga yanda ya yi bala'in yin kyau sumar shi na kyalli ta yi saurin kauda kan ta, bata son yanda zuciyar ta ke lugude idan ta kalle shi, wani irin baqon yanayi take ji akan Munir wanda bata taɓa jin irin shi ba akan kowanne namiji.
A bakin motar tashi ta tsaya tana wasa da hannun ta tana jiran isar su shi da Sadeeq,ba tare da ta san sanda ya isa wajen ba sai ta ji qamshin shi ya daki hancin ta da kyau, ta na d'aga ido idanun shi suka shiga cikin nata, murmushin da ya sakar mata ne ya sanya zuciyar ta yin wani irin tsalle kamar zata fito waje, da sauri ta faɗa cikin motar da ya buɗe mata ta zauna tana damqe saitin zuciyar ta da take jin ta kamar zata yo waje.
Murmushi Munir ya yi kafin ya zagaya ya shiga motar shi dan kuwa kallon cikin ƙwayar idanun ta ya haifar masa da wani irin sabon yanayin da bai taɓa jin irin sa a wajen kowacce mace.
A baya ya ɗauki mace a matsayin qawa kuma abokiyar shawara dan kuwa yawancin qawayen sa mata ne, wannan dalilin ne ya sanya mahaifinsa ke yi masa kallon mara jin magana, ba kuma ya jin nauyin sanar da shi baya jin magana ko a gaban waye, kalmar baya jin magana da ake yawan danganta shi da ita ke sanya shi yin abubuwan da ma ba halayyar shi bane, saboda ya quntata wa Abban nashi,tinda ko zai shekara yana bayanin baya aikata abinda ake zarginsa da shi ba a yarda da shi, a kullum Ummin sa ce kawai ke yi masa uziri da addu'ar idan ma yana aikata wasu abubuwan munana Allah ya shirya shi yasa ya daina.
Zuciyar shi cike da tunanin rayuwar shi da ya baro a Abuja ya ajiye ta a qofar gida suka wuce masallaci shi da Sadeeq.......
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
PAGE 17:
Bakin ta ɗauke da sallama ta sanya qafar ta cikin soron gidan nasu mai tsananin dubu, babu zato babu tsammani ta ji an cukuikiyi hijabin ta an matse mata wuya da shi an kuma matse kan ta a jikin gini,yunqurin k'wace kan ta take yi tare da tambayar,
"Waye haka? Me na yi muku? Sake min hijabi na ni na shiga gida ban yi sallah ba,"
"Ai kuwa yau sai dai a sallace ki dan uban ki,ba ki isa ki janye min wanda nake so ba har ku fara fita tare da shi a mota,"
Wani irin naushi Ameerah da ke lab'e a duhu tana jiran dawowar Saddeqa ta sakar wa Saddeqan a kunci,azabar zafin da ya ziyarci ƙwaƙwalwar Saddeqa ne ya haifar mata da sanya kuka mara sauti saboda shaqar da ta sha,duk yanda Saddeqa ta so ta k'waci kanta ta kasa saboda qarfin su ba ɗaya bane ba sam, Ameerah irin qirar Innoh gare ta,a dire take ga tsaho ga mazaunai, da kyar Saddeqa ta samu nasarar gartsa wa Ameerah cizo a hannun ta da ta shaqe mata wuya da shi, tinda kuwa ta kafa haqoran ta a hannun Ameerahn sai ta qi saki, ihun Ameerah ne ya jawo hankalin Innoh dake zaune a qofar d'akinta ta d'age labule ta na firfita, Innoh na so ta fita waje taga Ameerah ita da wa take zunduma ihu haka amma babu hali,qarshe dai haka ta dinga jan jiki har sai da ta fito tsakar gida ta hau k'walawa Sule kira, Sule kuwa be san ana yi ba ya na can babu sallah babu salati ya sanya headphone yana ta chatting da 'yan mata a Facebook, da ya gama ya koma TikTok, sai haɗa na datar da zai buɗe Live yake yi da dare, a WhatsApp kuwa aikin shi baya wuce tura stickers na batsa da videos ya ce duk mai so ta tura masa data ko katin waya, a haka yake tara data mai yawa da take isar shi shiga sites ɗin batsa har ya kwaso sababbin videos da aka ɗora.
Ganin kiraye-kirayen ba zai kai ta ko ina bane ya sa ta ci gaba da jan jiki a hankali ta dafa gini ta miqe tana takawa a hankali tare da faɗin,
"Ai mugun hali ne ya sa ana jin yarinya na ihu amma kowa ya maqale a d'aki yaqi fitowa, ihum ji ta can wai karatu take yi, yanzu fisabillahi idan ba munafurci da mugun hali ba ace duk kukan da yarinyar nan take yi ba a ji ba? Ita waccan dama qarmasasshiyar tsohuwar banda son gani na a bala'i ni da yarana bata da wani sauran buri da ya ragewa shekarun ta da ya rage mata a duniya,to ta Allah ba taki ba, se dai ki ga tsinewa da lalacewa akan zuri'ar ki ba dai tawa ba,"
Ta na daf da shiga zauren gidan ne Ameerah ta samu nasarar fizge hannun ta daya sha cizo ta fito daga duhun soron da uban gudu, wani irin juyi Innoh ta yi zata gudu bayan ta ya bada ita ta faɗi warwas a wajen ta na kurma ihu,
"Wayyoooo Allah bayana wayyo na hyiga uku na lalace ni Innoh bayana ya tsage a zo a kai ni gidan Ilu me gyaran qashi,"
Ameerah dake kuka shab'e-shab'e ce ta ja burki ta kalli inda Innoh ta yi warwas a qasa tana kwarmato,cikin kuka tace,
"Innoh ki taimaka min yarinyar nan ta cire min fatar hannu, hannuna tsiko yake yi, wayyoo hannu na Innoh ji nake kamar an bad'e shi da yaji,"
"Wace yarinya ce zata cire miki fatar hannu ni kuma ta yi sanadin tsagewar qashin baya na? Kama ni, kama ni na miqe Ameerah na shiga uku na lalace,"
Ameerah kuka Innoh kuka a haka Ameerah ta duqa dan kama Innoh ta tashi sai dai tun kafin ta iya d'aga hannun Innoh ta faɗa saman Innohn ta sake danna mata bayan nata a qasa, nan take kuwa azaba ta sanya Innoh ɗauke wuta kamar wadda ta suma, Saddeqa na durqushe a soron gidan su tana kukan baqin cikin abinda ya faru da kuma rad'ad'in azabar da wuyan ta yake yi mata Munir ya dawo daga masallaci shi da sadeeq, suna daf za su shiga zauren gidan Munir ya kunna hasken wayar shi nan take haske ya gauraye cikin soron, a tsorace Saddeqa ta miqe zata gudu cikin gida, cikin zafin nama ya riqe mata hijabin ta da ya yage ya yi maqal maqal da dattin hannun Ameerah, banda warin yawun Ameerah ba abinda ke fita daga jikin Saddiƙa,munir kuwa ya san ba haka suka rabu da ita ba ɗazu, ɗan ja da baya ya yi sannan yace,
"What happened here? Who did this to you?"
Kad'a masa kai ta hau yi alamar babu kowa,cikin sauri ya d'aga wuyan ta ya ga yanda wani jan shati ya zanu da kyau a wuyan nata, ga hannun ta da fuskar ta inda aka manna ta da gini duk ta kurje, bakin ta cike da yawu ta kasa cewa komai.
Sadeeq ya yi wa nuni da ya jata su shiga ciki, babu b'ata lokaci kuwa yaron ya riqe hannun ta yana faɗin,
"Mu je ciki, Yah Ameerah ce ta yi miki haka ko Innoh?"
"Wa naji ka ce? Su waye za su yi mata haka, kuma akan me za su yi mata irin wannan cin zarafin?"
Suna qarasa shiga gidan suka tarar da Yadiko ta fito taimakawa Innoh ta shiga d'akin ta har sun kusan isa cikin d'akin,Saddeqa na ganin mahaifiyarta ta zubar da yawun bakin ta mai cike da datti ta fashe da kuka har ta na shid'e wa, cikin sauri Yadiko ta juyo tare da sakin Innoh, da sauri Innoh ta dafe gini ta na kiran,
"Washhh Allah baya na,"
A guje Saddeqa ta isa wajen Yadiko ta faɗa jikin ta tana kuka,cikin tsananin damuwa Yadiko take bin jikin Sadeeqa da kallo a tsorace ta hau kallon yanda aka shaqe mata wuya da kurjewar da ta yi sannan ta kalli fuskar Munir da ke cike da rud'ani, gefe ɗaya ga Sadeeq tsaye da ya fara tsiyayar da ruwan hawayen tausayin yayar tashi.
Wani irin tsoro da fargaba ne suka shiga zuciyar Yadiko nan take ta ji zuciyar ta na yi mata suya da quna, waje ta samu ta zauna ta na juya kan ta tana hawaye, cikin kuka tace,
"Me ya faru? Me ka yi mata ? Ku sanar da ni abinda ya faru kada zuciyata ta buga,"
Tana faɗin haka Munir ya gano me take nufi, cikin sauri ya zube guiwowin shi a qasa a gaban Yadiko yace,
"Na rantse miki babu abinda na aikata wa 'yar ki, kar ki manta Saddeqa qanwata ce ba zan taɓa cutar da ita ba,"
"Qarya yake yi Yadiko kama su na yi a soro yana shaqe ta ya danne ta, shine daga na yi musu magana ya biyo ni nima, shine na yi ihu na gudo,qarya suke yi iskan....."
Wani gigitaccen mari Munir ya sauke wa Ameerah wanda ya sanya ta ganin wata walqiya na gilmawa kafin ta ga wani irin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 70