Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta latsa waya yana jiran fitowar su,gefe kuma abokan shi ne mata da maza suna ta hira. Fitowar ta ce ta sanya abokan shi ɗaukan sowa da yabon kyawun da Saddiqa tayi,nan da nan mai hoto ya hau ɗaukan dik wani takun ta da na su Anisah da ƙawayen su dake kewaye da ita suna taku cikin yanga, kafe ta yayi da idanun shi yana jin wani magaɗisun ƙaunar ta na fizgar shi,da kyar ya iya buɗe mata mota ya taimaka mata ta shiga ta zauna sannan ya zagaya cikin sauri ya faɗa gefen ta ya zauna, babban abokin shi mai suna Suhail ya ja motar suka bar gidan sauran motocin abokansa da qawayen Anisah na take musu baya. Basu jima da tafiya ba Ummi da tawagar ta suka shirya suka bi bayan su,basu tsaya a ko ina ba sai a wani babban hall da ake yin biki na masu ido da k'walli, kiɗan da ke ta tashi ne ya sanya Saddiqa fata da addu'ar Allah yasa kar a sanya ta yin rawa a wajen nan dan kuwa ba zata iya ba. Waƙa ce ta fulani saboda Ummi bafulatana ce shi yasa ta shirya fulani dinner saboda a ƙawayen ta ma akwai fulani sosai. Taro yayi taro nera ta koka sosai dan kuwa an watsa ta ma ango da amarya, Saddiqa na gani babu damar magana, tinda ta san dik wannan watsi da kud'in da ake yi haramun ne. Basu tashi daga wajen dinner ba sai bayan magariba, a gajiye kowa ya koma gida cike da kayan ƙwalama da aka raba a wajen biki,dik yanda Hajiya Sa'a taso ganin gazawa ko kasawar wannan bikin ta rasa, ƙarshe ma sai ta hau yiwa Suhail fatan ya samu mace irin Saddiqa kuma a raƙashe ayi wadaƙa da nera kamar yanda aka yi a bikin Munir. Alhaji Baban Gida yayi matuƙar farin ciki da wannan auren dan haka da kan shi ya fito parlour bayan sun dawo sun yi sallah suna hira ya hau gaisawa da mutane yana tsokanar ƙannen shi da suka kawo amarya, a haka suka sha hira har dare yayi Ango ya shigo yana mamakin ganin yanda Ummi ke wani kanainaye masa mata ta hana shi,dan haka ya riga ya ƙudurta idan ba a bashi matar shi ba to fa sai dai ya zauna su ci amarcin a nan gidan dan kuwa babu inda za shi. Amarya ƙawayen Ummi suka shirya ta sha wanka da gayu aka turare ta da turaren wutar HUMKAM banda ƙamshi babu abinda ke tashi a jikin ta, fruit salad Ummi ta sake bata irin haɗin da tayi mata tin farkon zuwan ta ta Karb'a tana sha,sai kawai daɗin shi yasa taji dama da Munir take shan shi dan kuwa yayi mata daɗi sosai,a haka ta gama sha su Hajiya Sa'a sune a gaba-gaba wajen tasa amarya a gaba suka shiga motoci aka kai amarya ɗakin ta. Suna kai ta basu jima ba suka dawo suka baro ta daga ita sai angon ta, domin kuwa ko da suka shirya zasu kai amarya shi kuma har yayi gaba ya riga su isa gidan, tafiyar su ke da wuya Munir ya rufe ko ina sannan ya shiga d'aki kallon Saddiqa yayi dake nad'e a cikin laffaya, wani irin farin ciki ne ya lullub'e shi ya sanya shi durƙusawa a guiwowin shi ya kafa kan shi a ƙasa yana sujjada domin godewa Allah da ya mallaka masa matar aure irin Saddiqa, ga kyau, ga ilimin addini, na bokon ma ta yi dai-dai ita wanda yake fatan nan gaba zata ci gaba. Murmushi kawai take ta dokawa a cikin mayafin da take ƙunshe a cikin shi,yana tasowa sai yace, "Ke kin ga tashi ki gani mu yi alwala mu godewa Allah da ya nuna mana wannan rana mai albarka." Babu musu ta miqe tsaye tana gyara mayafin ta cikin muryar da Munir bai taɓa sanin tana da ita ba tace masa, "Ina da alwala sai dai idan kai ne zaka yi sai na jira ka," "Alhamdulillah nima ina da alwala,na tsaya siyan kazar amarci naga suna sallah a wajen sai na tsaya nayi alwala nayi sallah sannan nayo gida." Sallah ya ja su suka yi raka'a biyu sannan ya karanto addu'ar da dikkan ango ya kamata yayi wa amaryar shi a daren farko kamar haka, "Allahumma inni as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha  alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha  alaihi" Yana kammalawa ya zauna kusa da ita ya janyo naman da ya kawo da fresh milk ya buɗe yana tayi mata hira domin ta sake da shi,gaba ɗaya sai yaƙi nuna mata maitar shi a fili saboda baya son ya sa taji ta a takure har ta kasa cin abinci ta ƙoshi yanda ya kamata. Ai kuwa ya samu yanda yake so dan kuwa ta saki jiki suna hira suna cin abinci, banda labarin wajen dinner da yanda ta dinga jin kunyar yin rawa babu abinda suke yi, a haka suka ci suka ƙoshi sosai sannan daga baya suka sha madara, Munir ne ya fara shiga band'aki ya wanke bakin shi sannan itama ta shiga ta wanke nata ta sake tsarkake jikin ta sannan ta koma ɗakin,tana shiga taga baya nan ya tattare ledar da suka ci abinci da kwalin madarar ya fitar da su, sai kawai ta buɗe wardrobe ɗin da ta gani, kallon kayan dake ciki a goge a jere take tayi cike da mamakin wannan dik suturar mutum ɗaya ce? Da kyar ta tsaida idanun ta a kan bangaren kayan bacci ta ɗauki wata maroon rigar bacci mai santsi ta sauya sannan ta ninke wanda ta cire ta saka a can ƙasa inda taga babu komai a wajen ta rufe. Bata jima da shafa Shu'umar Humrar HUMKAM da ta gani a saman madubi ba ta tsaya tana shaƙar ƙamshin tana lumshe idanu tsabar yanda ƙamshin ke ratsa ta,gado ta kad'e sau uku tana bismillah sannan ta buɗe bargo ta shiga tare da zama ta kara hannayen ta a bakin ta tana karanto ayatul kursiyyu uku,ikhlas uku, falaƙ uku, nas uku, sai amanarrasulu uku, tana gamawa ta shafe dika jikin ta ta kwanta ta rufu da bargo, tunawa tayi bata kashe fitila ba sai ta dan yi gajeran tsaki zata sauka tana faɗin, "Kashh na manta ban kashe fitila ba na kwanta," Munir ne ya ziro kanshi ɗakin yace, "Kar ki damu Amaryar Mannirun Baabaa zan taya ki kashewa ke dai ki koma kawai ki kwanta ki jira zuwan angon ki gare ki." Wata iriyar faɗuwa gaban ta yayi nan take ta hau karato addu'o'in samun natsuwar ruhi saboda kar ta bari tsoro ya hana ta sakewa mijin ta da ya jima yana dakon wannan ranar mai mahimmanci a gare su sakewa,cikin wani ɗan ƙanƙanin lokaci Munir ya kashe fitilar tare da kulle ƙofar d'akin yayi duhu dinɗim,ganin haka ne ya sanya ni sake buɗe ƙofar ina ƙunƙuni na kulle su na koma parlour na kunna kallo ina cinye ragowar kazar ango da amarya ina korawa da laban.................. *Cassss ana yi ina jin nayis...albishirin ku mutanen k'warai masu albarka, marasa yin comment ko liking a groups ɗin da nake turawa kuna yi kamar baku ganni ba, aradun Allah aski yazo gaban goshi nima ina shan wahala dama wajen sharing, zan dena sharing duk group ɗin da ba a acknowledging ɗina sai in dinga turawa masu so,kar kuma daga baya na dena turawa group ɗin ku ki bini ta PC kice kina so, zaki biya kuɗi kafin na tura maki daga farko zuwa inda na tsaya tabbas.* [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA:HAERMEEBRAEH ✍️✨ *SANARWA !* *Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....* *MAZAUNA GIDA 300* *ƳAN ABUJA 300* *A GARIN MU 300* *KAI NE JARUMI 300* *KUN MAKARO 300* *TAUBASHI 300* *KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻* *IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.* *KAR KU MANTA AKWAI KAYAN GYARAN JIKI A KANO, KADUNA DA KEBBI STATE.* *FACE OIL* *SKIN OIL* *BODY SCRUB* *HAIR OIL* *HAIR CREAM* *HAIR MASK* *GA MASU SON SIYAN ƊAYA KO SARI SU NEMI WANNAN NO 09031416423* PAGE 63: Washegari da safe Saddiqa ta tashi da wata iriyar shagwab'ar da ni kai na da na san ta tun tana ƙarama ban san ta da ita ba, ko taɓa ta Munir yayi sai ta mere baki alamar zata yi kuka,nan da nan shi kuwa jiki na matuƙar rawa da mazari zai hau ririta ta yana lallashi tare da ban baki, a yanda yake jin ta a cikin zuciya tsokar jiki da ɓargon jikin shi zai iya yi mata komai dan farin cikin ta. Wani irin so yaji yana yi mata tare da girmamawa wanda a baya bai yi mata su ba na musamman,bai taɓa zaton yanda ake ta bada labarin lalacewar Ƴan matan yanzu zai samu Saddiqa a yanda ya same ta daren jiya ba,dik wani sharri da zagi da kiran lalacewa da Innoh ta dinga yi mata ashe dik sharri ne? Nan take yaji ƙaunar Yadiko da ta zuri'arta ta samu masauki a zuciyar shi, addu'a kuwa ranar Saddiqa da iyayen ta sun sha ta babu adadi. Shirye take tsaf cikin wani leshi wanda ta dinga mamakin yanda aka yi kayan suka yi mata dai-dai a jikin ta kamar an auna ta duba da cewa ko ganin ta telan be yi ba, kalar purple ɗin ta karɓe ta saboda kala ce dake yi wa kowacce kalar fata kyau, d'aurin ɗankwali ta yi mai kyau da ta kafa a goshin ta kamar hula, sai gashin kanta dake nad'e a bayan ta ya zauna a dogo cikakken dokin wuyan ta, duk yanda zan misalta maku yanda Saddiqa tayi kyau ba lallai ku gane ba sai idanun ku sun gan ta,Munir kuwa zama yayi ya sanya ta a gaba yana kallo ko ƙiftawa baya son yayi, cike da shagwab'ar da ta tsiro da ita daga sama ta hau karya jikin ta tana wasu 'yan koke-koke dake rikita lissafin Munir tace, "Ni dai dan Allah ka daina kallo na haka, sai in dinga jin kallon ka na fasa ƙirji na yana shiga zuciya ta," Da sauri ya dawo gaban ta ya zauna tare da ɗora hannun sa a saitin zuciyar tata yace, "Dan Allah da gaske kike? Muga iya inda kallon nawa ya tsaya,matso in gani," Da gudu ta tashi ta koma parlour tana dariya, hannun shi zube a cikin aljihun wandon shi mai faɗi wanda ya ɗan tsuke daga ƙasa kaɗan,sai vest da ta manne a jikin shi ya fito yana zuba murmushi yana binta da kallo, "Ai da ki tsaya naga inda kallon nawa yake zuwa, dan sharri yanzu ace kallon ɗan mutum na huda ƙirji ya shige zuciya sai kace wani maye?" "A tsakanin jiya da yau idan aka ce min kana lashe mutane har ɓargon su ba zan yi musu ba," Dariya suka fashe da ita a tare ya sanya hannun shi na dama ya shafi kan shi mai tattausar suma irin ta fulani mai nannad'ewar nan,lashe leb'en bakin shi yayi na ƙasa sannan ya kalle ta yana wani lumshe ido, yanayin da ya ke kallon ta dashi yayi matuƙar tasiri wajen jefa ta cikin ƙaunar shi dumu-dumu fiye da yanda take ji a baya. Da kanta ta tashi daga mazaunin ta ta zauna a saman cinyar shi ta rungume shi, murmushi yayi ya hau shafa bayan ta, a hankali tace, "Ruhina yunwa nake ji," "Yi hakuri Ruhina bari na sama nana abinda zamu ci ko?" A hankali ta miƙe daga jikin shi, shi kuwa ya kamo ta ya riƙe fuskar ta yana sumbatar ta, sai da ya gaji dan kan shi sannan ya sake ta ya tafi da baya da baya zai shiga kitchen yana yi mata dariya, dan kuwa ya shanye lipstick ɗin da ta saka gaba ɗaya. Murmushi itama tayi ta samu waje ta zauna da ƙafafun ta da suka yi sanyi saboda kashe mata jiki da Munir yayi,door bell ɗin gidan ce ta fara bugawa tana zabga sallama, cikin sauri Munir yayi hanyar fita dan ya ga ko wanene ke sallama musu. Da sauri Saddiqa ta sha gaban shi tana cije baki saboda zafin da take ji a jikin ta,mamakin saurin shan gaban shi da tayi Munir yayi, cikin tura baki tace, "A haka zaka fita? What if mace ce mai sallamar fa?" Sunkuyar da kanta tayi ta hau wasa da yatsun ta,wani irin kishin shi ne ya taso mata lokaci ɗaya,shi kuwa Munir ji yayi kamar ya taka rawa saboda murna,rungume ta yayi ya manna mata kiss kafin ya ɗaga murya yace, "Wa'alaikumussalam ! Ana zuwa." D'aki ta shiga da sauri ta ɗakko masa jallabiyya ta sanya masa kamar yanda ya taya ta sanya kayan ta,kallon ta yayi yace, "Zan iya fita yanzu gimbiya?" D'aga kai tayi tana dariya ƙasa-ƙasa tare da noƙe kanta,da sauri ya nufi ƙofar ya buɗe sai yaga drivern gidan su riƙe da basket ɗin abinci, cikin girmamawa ya karɓa tare da gaishe shi, amsawa drivern yayi tare da yi musu fatan zaman lafiya da samun zuri'a mai albarka. Bayan ya koma sai ya ajiye basket ɗin a dinning table sai ya wuce kitchen ya d'akko plates da spoons da serving spoon ya dawo, zaune ya ganta gaban abinci tana buga hannun ta a table ɗin tana faɗin, "Yahhh Munirrr yunwa nake jiiii....Yah Munir zan ci abinciiiii." Murmushi kawai yayi ya buɗe food flask d'in farko dan yaga me zai zuba masu, karo yayi da farfesun naman kan rago, daga ƙamshin dake tashi yasan yaji kayan ƙamshi, amma an saka daddawa kaɗan a ciki ɗaya food flask d'in ya buɗe yaga an soya dankalin bature da ƙwai,sai ɗayan kuma fried rice ce da ta ji kayan lambu da naman rago,kunun gyad'a ne a dogon flask ɗin ruwan zafi ya ji kindirmo fari ƙal da shi. Yawu Saddiqa ta had'iya ta ci gaba da shagwab'ar da ke samun mazauni a zuciyar Munir na musamman ta zauna,yana gama zuba musu ya ja kujera kusa da ita ya hau bata, sai da taji yunwar cikin ta ta lafa sannan itama ta hau d'iba tana bashi a baki, a haka suka gama ciyar da junan su abincin sannan Munir ya tashi zai tattare wajen, murmushi Saddiqa tayi ta kama hannun shi tace, "Ai kai kuma ka gama naka aikin, yanzu nawa zai fara," Sakar mata yayi ya nad'e hannayen shi yana binta da kallo,sai da ta gama kwashe komai zata wuce sai ta kalle shi da wani irin salon jin kunya tace, "Ruhin Saddiqa cire rigar nan ta sama nafi son in dinga ganin ka da irin shigar d'azu," Tana gama faɗin haka ta wuce kitchen da sauri tana dariya, shi kuwa Munir wata ƙara ya saki ra farin ciki ya tashi da sauri ya cire jallabiyyar yayi wurgi da ita saman kujera ya bi bayan ta kitchen yana faɗin, "In dai kuwa haka kike son gani na kin samu Ruhina,dik abinda kike so shi zan yi," Murmushi tayi tana sunne kanta tare da satar kallon shi, a haka ta wanke abinda suka ɓata ta hau kallon kitchen ɗin da yanda aka shirya mata kayan da bata san wanda yayi mata su ba, sai dai tafi bada zargin Abbah ne yayi mata komai da taimakon Ummi,a can gefe ta hango yanda aka jera mata wanda dangin mahaifiyar ta suka yi mata cikin tsari gwanin burgewa, har da su ƙwarya mai zane da fai-fai. Hamdala ta dinga yi a ranta suka koma ɗaki ta sake gyara ko ina ta kunna turaren wutar HUMKAM da ta gani a ɗakin da burner,nan da nan ƙamshin turaren wutar ya dinga saukar musu da wani yanayi na natsuwa da annashuwa na musamman. Parlour suka dawo Saddiqa ta ninke rigar shi ta ajiye a kujera suka samu waje suka zauna ya kunna masu kallo, manne suke da juna kamar su shige jikin junan su saboda so da kulawa, gani nayi ana kallo Munir gaba ɗaya hankalin shi baya kan TV ya koma kan amaryar shi yana bata kulawa ta musamman, tin ina iya kallon su har abun ya girmi tunanin yara sai na basu waje na koma ƙauyen Ba mugu. *********************** Su Abbe sun koma gida cike da arziqi da kayan arziqi kala-kala a washegarin ranar da aka kai Saddiqa d'akin ta, dan kuwa ko sallama basu koma sun yi mata ba Ummi tace ayi hakuri abar ango da amarya su huta duba da cewa kowa yaje yaga gidan bata ga dalilin yi musu sintiri ba da safe,dan haka a gidan Baabaa suka kwana za su koma gidajen su da safe, Baabaa kuwa bata ji ƙyashi ko haushin ɗebar wa su Innoh komai ba, hatta da robobi da aka raba a wajen bikin sai da Baabaa ta ɗebar musu har Ameerah da Mommy,ƙullin Sule kuwa daban ne da na kowa,nan da nan Innoh ta sakko daga dokin rashin kunyar da take zubawa Baabaa ta hau yashe baki. Cikin yada habaici Abbe tace, "Haka dai aka iya, ƙuda wajen ƙwadayi aka mace ai." Ko kula ta Innoh bata yi ba ta kawwame kan kayan ta ta wuce d'akin ta,sai da ta shiga ta ajiye komai sannan ta leƙo da kan ta ta labule tace, "Kan ki ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya yace wanka na nake yi, idan baki san wani abu ba yau ki sani, shi raba arne da makami ibada ne, kuma kayan nan da kuka bamu ai ya zama dole ku bayar ne tinda uban ta ya kashe kud'in shi akan ta,nima kuma dole a bani kaso na na ladan riƙo a matsayi na na matar uban ta." Wani kallo shalele da bata magana ta yiwa Innoh na takaici,cikin saurin maganar da take dashi tace, "Ke mara mutunci ! Ke har kina da abun cewa a bangaren riƙon Saddiqa? Ke wacece a cikin dangin mu kaff? Ki jira ki sha mamakin abinda zai biyo baya akan iskancin nan da kike yi wa mutane, ki rubuta ki ajiye sai mun baki mamaki, koni nan Autar Baabaa na girme ki amma haka kike rufe ido ki dinga zagin uwar mu ko mu kammu,an faɗa maki tsoron ki muke ji? Ki kiyayi zuwa rafi da tulu Innoh saboda ina matuƙar jiye maki fashewar shi baki shirya wa hakan ba." "Kullum ai cikin shan mamakin ku dama nake ni ai? To hali ne aka tsotso kala-kala kunga kuwa dole....." Wata mahangurɓa Shalele ta sakarwa Innoh a baki,ta bi ta a guje d'akin nata tana ihu, Innoh ma kwasa tayi da gudu tana ihu ta na ci gaba da zagin Baabaa,dika yaran Baabaa basu da jiki kamar ta, Alhaji Baban Gida ne kawai yake da ƴar ƙiba irin ta hutu da jin daɗi. Wani irin yare Shalele take yi bakin ta na kumfa tana dukan Innoh a ka,banda salatin Innoh baka jin komai a ɗakin,Abbe na bakin ƙofa tana tiƙar dariya, dama babban burin ta a rayuwa watarana Innoh ta fusata Shalelen Baabaa mara magana da son hayaniya,ta tabbata dik sanda haka ta faru ba da ita za a yi faɗan ba da babarbariyar aljanar ta za a kacame,idan kuwa haka ta faru ko bafulatanar Baabaa bata isa raba wannan faɗan ba sai ta gaji da kanta ta sauka take bari. Baabaa ce ta fito sanye da hijabi hannun ta riƙe da carbi,sallar walaha/dhuha take yi dama sanda suka fito kawowa Innoh kayan, sai kuma taji ana faɗa,Abbe ta kalla dake dariya tana riƙe Sule tare da faɗin, "Kana shiga zata haɗa ku ku dika ta yi ta duka." "Eh ni ki barni na shiga, kina ji ana dukan uwa ta amma kike dariya kin ƙi ki raba su faɗan,wannan wanne irin abu ne dan Allah?" "Shiga Sule, ai shi mai rabon shan duka sai ya sha, maza jeka ka ceci uwar ka hannun barebarin aljanu." Baabaa ce ta kama baki tace, "Wooo me kuma wannan mara kunyar tayi wa Shalelena har barebarin ta suka zo?" "Daga abun arziƙi ne tsiya ta biyo baya har tana haɗawa da zagin ki, kin kuwa san kowanne ɗan halak aka zagi iyayen shi sai ya ɗauki mataki, to fa matakin Shalele ke ɗauka." Sule ne ya fito daga ɗakin a guje bakin shi riqe da hannayen shi bibbiyu, ihu ya kurma saboda ganin jini a hannun shi haƙorin shi ya taɓa ta gaba yaji rabin guda ɗayan ya yanke, a guje ya shiga ɗakin shi ya ɗakko madubi ya kalli bakin shi yaga yanda yayi window, shi ba hushirya ba kuma haƙorin bai gama fita ba yanke wa yayi,kuka ya fashe dashi yana faɗin, "Shikenan na shiga uku na lalace,yanzu ta ya zan kalli baby na da wannan wawulon? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una na shiga uku ni sulemanu." Dariya Abbe ta dinga kwasa, Baabaa kuwa d'akin ta shiga taga Shalelen ta kwance a gefen Innoh da ta suma dan wuya,ita kuwa shalele sai jera atishawa take yi bakin ta zuwa rigar ta duk kumfa ne jiki,da kyar Baabaa ta d'aga ta ta k'wala wa Abbe kira tace ta kai mata ruwa,koda Abbe ta shiga ɗakin sai ta tarar da Innoh yashe a ƙasa babu zani rigar ta ta yage, kanta yayi malulu ko ta ina saboda dukan da ta sha da murfin kwanon langa,bakin ta kuwa sai jini yake fitarwa damatsan ta duk shatin haƙoran Shalele,tausayi Innoh ta dawo tana bata,ruwa suka zuba mata ta farfaɗo,ta jima bata gane a inda take ba kafin ta buɗe ido da kyau ta zuba su akan Baabaa, Abbee da Shalele suna tsaye sun zuba mata na mujiya, nan take kuwa ta koma luuuuuu ta sake sumewa........ *Innoh kika ce ba kya ji?*😂 [09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI RUBUTAWA:HAERMEEBRAEH ✍️✨ *SANARWA !* *Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....* *MAZAUNA GIDA 300* *ƳAN ABUJA 300* *A GARIN MU 300* *KAI NE JARUMI 300* *KUN MAKARO 300* *TAUBASHI 300* *KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻* *IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.* *KAR KU MANTA AKWAI KAYAN GYARAN JIKI A KANO, KADUNA DA KEBBI STATE.* *FACE OIL* *SKIN OIL* *BODY SCRUB* *HAIR OIL* *HAIR CREAM* *HAIR MASK* *GA MASU SON SIYAN ƊAYA KO SARI SU NEMI WANNAN NO 09031416423* PAGE 64: Ruwa Baabaa ta sake shafa wa Innoh a ƙafafun ta ta farka tana lumshe idanu,idanun ta na sake sauka akan Shalele sai ta fashe da kuka mai tsanani har da majina,cikin lasar busasshen leb'en ta dake fitar da wata iriyar azabar zafi saboda fashewar da yayi tace, "Ki yiwa Allah ki yafe min ba zan sake faɗar wata muguwar magana akan yaya ba, dan Allah ki yi hakuri Shalelen sarkin aljanu." Hararar ta Shalele tayi sannan ta miƙe ta bar d'akin ba tare da ta ce komai ba, tana komawa sashen Baabaa sai ta kwanta a gado ta hau bacci abunta kamar babu abinda ya faru. Baabaa da Abbe ne suka yi wa Innoh faɗa akan abubuwan da take yi, hakuri ta basu sannan suka koma d'akin Baabaa a tare, bacci suka tarar da Shalele nayi, Abbe tace, "To ni Baabaa zan wuce gida,gwanda ita bata da nisa da gidan nan ni kuwa kinga tafiya ta da nisa, Allah ya sake sada mu da alkhairi, Allah ya sa wannan aure mutuwa ce zata raba shi, idan Shalele ta farka ayi mata sannu, yau dai aljanun da ake faman su rabu da ita shekara da shekaru sun yi rana." "Ke ina wata rana a wajen aljani kedai Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani kawai, Allah kuma yayi muku albarka ya saka da alkhairi, Allah ya baku ladan sada zumunci." "Ameen Baabaa bari nazo na wuce,nasan mutanen ki anan can ana zuba ido aga ta ina zan ɓullo." Har bakin ƙofar gida Baabaa ta raka Abbe kafin ta koma ɗakin ta, Shalele na can na ci gaba da bacci Baabaa ta haɗa mata nata kayan da alƙawarin tana tashi zata sata a gaba itama ta koma nata gidan. Innoh kuwa da kanta ta haɗa wuta Sule na taya ta suka tafasa ruwan zafi ta gasa jikin ta musamman kanta da yayi ƙololo saboda dukan da ta sha da murfin langar tuwo. Tinda abun nan ya faru har yamma Sule yaƙi buɗe baki balle yayi magana da kowa,ya rasa hanyar da zai bi dan haƙorin shi ya dawo dai-dai,dik wata dabara da yake

Chapter 41 of 70