Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Iman bace akwai qarin kayan kanti... "Ah haba ke k'anwatace real ma...,aduniya wanake dashi bayanke...,kuma wanake gani kusa dani bayan ke Iman..,kituna daga ummanah sai ke....,kuma kece kika share hawayenah bazan iya yadakeba..,kuma alqawalina ban changr ba....,zan riqeki amana Iman...,saidai akwai abunda bakisaniba...,kuma hasken sanin hakan zai xo maki nanda lkch kad'an...,lkchn kinga kinsan komai nake nufi....,shiyasa banason ki wahala ynx komai za'a dinga yimaki kinji....,ynx me kikeso nayi.....?" Cikin sigar rarrashi yayimata wannan maganar domin har tasowa yayi yazo gaba sit d'inda take zaune yayi..,amma yakasa koh riqa hannunta..,shifa amanarta at baison yaci..,kuma yasan da ya riqa hannunta komai zai iya rugujewa domin ganinta yakeyi kamar farhace tare dashi....,shiyassa yake kiyaye farkon hakan...,toh bale ynx da yake ganin wannan acuci mazan datake sanyawa....yaqara tambayarta..,abunda takeso yayi ynx..... Iman saida tajuya idanunta datake hawaye dasu takuma turo bakinta takuma juyar da fuskar tace..... "Break d'ina nakeso kaima kaci duk da kace ban iya komaiba sai nangaba...,amma kaci koh kad'an ai sai naji sanyi..., 'ya'yanah ya kula dani...." Murmushi yayi ya juya ga break d'in ya d'auki d'ayar doyar datasha soya kuma aka had'a wani abu gefe..,dagani eggsoup ce..,saidai egg d'in shiyafi yawa ciki...,jabbar ya fara tunanin cin wannan jagwalgwalo...,amma yazaiyi dole yadaure yafara yima Iman abunda takeso koh don amanar dake hannunshi tata....,ya fara kai doyar bakinshi amma saida ya runtse ido donji abunda zaiji shigarta a bakin kuma sai zance yachangr domin ta ratsa bakinshi duka...,nan take ya cenye d'ayar kuma yakoma a tabiyun...,yama mance da yayi gardamar cinta.... Iman nacen gefe tana kallonsa in yajuya kuma sai tayimashi gwalo..,da ya juyo saita koma yanayinta nada....,haka yaci rabin wanda takawo mashi...,tea d'inma yasha.....,mamakin yarinyar nan yakeyi dama ta iya girki...? Amma kuma ai wannan soya ce...,kuma zata ga anayi..,amma dafa abinci waya sani ma..... Juyowa yayi..,yace..... "My k'anwa naci..,nayi abunda kikeso koh...?" Murmushi kawai tayi..,batace komaiba miqewa kawai tayi takwashe kayan a table d'in takai kitchen...,jabbar ya susuce p..,domin salon tafiyar Iman ya changr kuma da gayya tayi tafiyar..,yasaki baki yarinya qarama ke wannan abun.., Inaga babbarta sai suma...,dawowa tayi zata wuce bedroom nata...,sai ya kirawota tadawo..... "Iman dama yau umma zata dawo...,ynx hakan office kawai zan shiga nadawo mud'aukota...,hope zakiji dad'in zama da umma gida d'aya.,saidai kowa danashi part ita waccen shiyar zata zauna domin tadawo kusa damu...,saidai kinga akwai nisa tsakaninmu...." Wani tsalle tabuga tafad'a saman kujerar...,saida qaramar rigarta da d'age sama bata saniba amma shi yagani...,sbd tsoron wata kuwwar murna datayi..... "Yeeeeeh ummanah zata dawo...,dole nayi murna..,zaman kad'aici ya qare Iman...,shikenan sai na kwashe kayana nakoma part d'in umma nasan ita zata soni sosai...." Dasauri yace "Iman baki tsoron kijima kanki ciwo..? Wanna fad'owa hakan... Toh kidaina ke amanace gurina banason abunda zai sameki....,kuma ai nima ina sonki..,kinta'ba ganin wanda yaqi d'an uwanshi....?" "Sai 'ya'ya farha..." Gabanshi yafad'i zuciyarshi ta motsa da ambato sunan datayi...,duk da bayason koh sunan yaji..,amma har ynx akwai sauran d'igon son sunan..,hakan yasa...,ya sauya..,Iman tafahimci hakan..,da sauri tamiqe..,don itama bataji dad'iba.... "Kayi haquri bazan sake abunda nayi ynx ba plx......" Dugowa yayi wannan karon saida ya dafa guwayyunta yace..... "Iman kiyi haquri kinji..,kuma kitayani addu'a Allah yayayeman abunda ke damuwata..,kinji...?" Daga mashi kai kawai tayi tace..... "Dayaushe umman zata dawo don inason na tarota idan tazo...?" "Bada dad'ewaba...idan nashiga office zan d'aukota sbd komai nata ankawo itace kawai ta rage...." "Toh Allah yakawo ita lfy...,naji dad'in ganin umma tare damu Allah yabamu ikon yimata biyayya..." Dasauri ya amsa "ameen my qanwa..." Wani bala'in dad'i yaji..,qaramar yarinya da ita amma akwai hankalin magana mai sanyi....,tatashi tayi d'aki da murnarta tarkonta yafara kama tsuntsuwa...,tanashiga tafad'a saman gado harda murmuje...... "Wooooo nafara bud'e Page's 'ya'ya jabbar yau nasan da mamakin Iman zaka wuni...,kadawo kuma naqaramaka na dare kayi barci dashi...,nafara kenan har sai kafad'i ni ba qwailabace cikakkar macce ce mai hankali...,kuma sai ka daina tunanin 'ya'ya farha gabad'aya zansa kamanta da wata alaqar soyayya ta had'aku...,zanyi yaqin neman soyayyata da qarfin hikimata..,gada nayi biyu babu ba Isham kuma babu biyayyar iyaye....,'ya'ya jabbar mund'aura kenan muga wazaiyi winning......" Bayan shigar Iman d'aki jabbar qofar yaketa kallo har tashige...,ya daskare yakasa tashi.., har wani abu yaji ya soki zuciyarshi..,saidai yasan ba son Iman bane dai haka da wuri..,saidai burgeshin datayi na nuna murnarta ga zama da mahaifiyarshi..,abunda yr uwarta bata amintaba kwatakwata....,lallai Iman yarinya kike amma akwai hankali...,kuma wai wayannan masukkan datake juyawa natane kuwa koh acuci mazane...? Toh nidai gani ganin mamaki...,Allah kaqara tabbatar man da alkhairinka....,jabbar ke nanatawa a zuciyarshi har yakai bed room nashi yashirya yad'aukoh bag d'inshi ta office ya d'auko makulli yafito...,fitowarshi itama tafito yace..... "My qanwa office zan wuce..,me kikeso na sayomaki....?" Tayi murmushi harda juyar da idanunta...,ta matso daga inda yake ta ranqwashe kanta tace a sigar wasa kuma ta ta'be d'an qaramin bakinta tace..... "Banason komai saidai fatana kaje lfy kadawo man da umma tah lfy shine best hope d'ina...,naga nawar naga nakoma cen da zama...." Yabud'e idanunshi baki d'aya..., yace.... "Iman baki rabo da yarinta..,ameen toh yr qanwata saidai zama permanent gurin umma ah ah...,don bazaki barniba dodo yacinyeniba nikad'ai...,ki manne gurin ummah...." Dariya sukayi baki d'ayansu..,yawuce tanamasa bye bye..... Yawuce da farin ciki..har yakai inda zashi...,itakuma tafara shirin taron umma d'in.... Mudai je xuwa...... *Bee Been masoya*๐Ÿ’ž [1/17, 1:38 PM] Bee Been๐Ÿ’ž Masoya: ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ* ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง ยฉยฎ Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ โ˜…TRUE LYF STORYโ˜… โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… *~ADDU'AR NEMAN TSARI DAGA SON ZUCIYA~* *_ุงู„ู„ู‡ู… ุฅู†ูŠ ุฃุนูˆุฐ ุจูƒ ู…ู† ู…ู†ูƒุฑุงุช ุงู„ุฃุฎู„ุงู‚....^ ูˆุงู„ุฃุนู…ุงู„....^ูˆุงู„ุฃู‡ูˆุงุก.....ุŒ_* *ุงู…ูŠู† ูŠุงุงู„ู„ู‡...._*๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป *_WRITTERS INAJI DAKU INA ALFAHARI DAKU MANYA DA QANANAN IRINMUBA๐Ÿค’INAYINKU INA QARAWA...,FA'DINKU ZAI SA NACIKA PAGE 'DINA BAN RUBUTA KOMAIBA....,ALLAH YABARMANKU...,IDAN KINA WRITTER SHAFIN NAKUNE DUKA...., AMBATONKI DOLENE โคFIRDAUSI SODANGIโคALLAH YASA AQARE NEW BUK LFY MAI SUNA ZAMANI...., Bee Been kuce๐Ÿ’ž_* Page... โ˜…1โƒฃ8โƒฃโ˜… ยฎ Sauri kawai takeyi tashirya..,taduba end colour d'inta cikin kayan da Anwar yasayomata..,tabud'a tasamu wata milk colour d'in riga mai bala'in kyau tasaka rigar sama ya matse da wasu igiyoyi jikin rigar da wasu kalar duwatsuna akayi aikin gurin rigar ta bugu....,domin nigeria bance baza a sametaba amma gsky za'a sha wuyar samunta...,farha tayi kwalliya taji da fad'i domin daman ita kwalliyane kawai batayi amma kuma tanason kwalliya kuma tanayimata kyau...,sauri kawai takeyi...,domin gidansu jamila zataje nan Anwar zai d'auketa....,jawo takalmanta tayi wayanda bata ta'ba sanyawaba tasaka...taduba kanta dai2 tayi iya yi domin koh ina chip chip...,gyalen rigar babbane amma bashi xata sakaba domin gada mamar taganota...,jawo hijab d'inta tayi tasaka har kusan gwuiwarta ya rufe ta d'auko hand bag d'inta tariqa agefen hannunta amma idan zata shiga gurin mamar dole tasakata hijab....,sai addu'a takeyi Allah yasa gada asamu mtsl mamar tace bazatajeba...,tab da Anwar yayi fushi daita sosai......, fitowa tayi tareda setting d'in alarm d'in wayarta don gada mamar tace qaryane..,yadda tana shiga d'akin ringing zai shigo sai tayi wayar qarya da rasheeda..... Shigarta d'akin mamar tana toilet alwallar la'asar...,jin motsin ruwa ya tabbatar mata da hakan..., mamar na fitowa alarm na tashi...,da sauri tayi picking tafara magana kamar hakan...... "Rasheeda don Allah kiyi haquri gani nan zuwa...,wlhy na mantane da yau akeyin walima kinga koh mama ban fad'amataba..,amma nashirya gani nan zuwa gada ki wuce kinsan bansan gurinba....,kiyi haquri plx nashirya insha allah....." Wayar takeyi kamar da gsk harda d'an saurarawa kamar dgsk magana akeyimata...,don mamar ta d'auka dgsk ne kawai.....,har mamar zata saka hijab ta kabbarta sallar sai Farha tayi sauri ta aje wayar tamiqe tsaye zuwa gefen gadon tafara magana...... "Mama inason naje wakimar wata qawarmu kuma yr uwarsu rasheedace sosai toh jiya aka kawoman invitation d'in lkchn kina d'akin baba kuma na mance..,yau rasheeda ke tunamani don Allah naje.... ?" Mamar ta kalleta ta juyar da fuska tacigaba da saka hijab nata sannan ta juyo ta kalleta...... "Hmmm ai shi kad'aine aikinki...,da ynx kina gidanki kin rufa ma kanki assiri wazai d'auko gayyatar banxa ya turomaki...,zaman biyar bukin qawayekitayi....,kuma don kince rasheeda ce na aminta da tarbiyar yarinya zan barki saidai kisani wlhy ana tashi koh gidansu gada kikuskura kibita ta ajiyeki nan kidawo gida.....,domin kinsan mahaifinki cike yake dake....,kibar ganin yace yasakamaki ido ba ruwanshi dake...,wlhy komai zai iya akanki...,kitashi kije kuma gada ki d'ad'e....." "Insha allah da wuri zan dawo...." Tatashi da sauri tafita..,Alla Alla takeyi tafita gidan ta kira rasheeda....,ta shaidamata tafito p don gada mamar takira rasheeda asamu mtsl duk da tasan komai.....itama tajamata kunne domin idan akazo nemanta batasan ydda zatayiba dole gsky ta fito....,suka kai qarshe...., Farha tashiga gidansu jamila...,domin jamila iyayenta ba ruwansu da abunda yayansu keyi...,shiyassa tafi qaunar zuwacen ta gyara yadda zatayi kyau...,shigarta take shaidamata inda zasuje da anwar amma bataso asamu mtsl domin walima tacema mama.....,jamilar ta jinjinamata domin farha tayi kyau sosai.... "Amma rolling zakiyi koh.? Sbd wlhy kinyi kyau farha dole ya rud'e mutanen gurin su rud'e...,shima anwar ba bayaba gurin kyau...,wlhy qawata kunyi bala'in dacewa da juna ke kykkyawa shima haka...,dani nasamu gayennan dana zarce tsara ga kuddi ga kyau qarshe ga iya soyayya....." "Tsayanan qawata gada asamu mtslr yabonnan p...,kibari nayi dakaina...ai mai abu maganin abunai....kinga Anwar kinga farha....,qarshe zamu barje luv d'inmu gidan aurenmu ynx haka saura 7days akawo sadakina....." Shewa jamila tayi....,da murna....tace... "Akwai kashe kala kusa kenan domin har naga bukinku za'ayi 'barin kuddid'an gidan Naira fa kedai Allah y kaimu......" Rurin wayarta ketashi dasauri ta d'aga my heart tagani da sauri ta washe baki tayi picking.... "Zuciyar farha ya kake ne...?" Ya amsa mata da "qlau... Hope kin shirya domin zanxo d'aukarki.....?" Tayi murmushi tace...... "Eh kai kad'ai nake jira...,amma ina gidansu qawata kazo nan bayan layinmu zakaga wani gida mai qaton get koh ka tambayi gidan sanusi plastic..., za a kawoka....." Directly cen yawuce domin yasan gidan...., kiranta yayi tafito....,tundaga nesa hankalinshi yatafi domin farha tayi bala in kyau...,jin yayi bazai iya ganinta a cikin motarba...,sai yafito riqe da marfin mota...,murmushi kawai yake tazubawa....,farha na matsowa ya qarasa bud'e idon bud'e mata gaban motar yayi tashiga....,qamshi taketayi shima yashiga kapin yaja motar saida yace mata.... "My wify I Luv u fa...." "Toooo " Kawai tace mashi suka ja motar sai gidansu..,domin son yakeyi ya shirya sannan su wuce....,sbd ynx 5pm tayi bayaso baqin suzo baya gurin.... Dasauri ya shirya domin bayason abokan harkarshi suxo zancen tafiya yasha kara..... Shima yayi kyau sosai.....,suka miqo hanya zuwa hall d'inda aka d'auka da kud'i masu yawa...., fito warsu mota yazo gurinta...,yasaka hannunshi d'aya ya maqalota..,wanda saida gaban farha ya fad'i...,amma batace komaiba...,a haka suka shiga ciki kid'a natashi.....,saidai hanjin Farha sun d'uri ruwa daganin yadda yn mata da maza ke rungume da junansu..,sai tsoro yakamata...., itako yau tabani...., Ahaka kuma sai tayi shiru.... Ba a fara gabatar dakomaiba saida magariba tawuce...,akayimashi happy birthday tareda happy engagement wanda sai lokacin mutanen gurin sukasan aure zaiyi..,domin sunsan halinshi da abunda yakeyi kuma masu irin aikinshi basa aure...,amma kuma irin maccen dazai aura tana iya changr kowa domin kyaunta kad'ai zaija ra'ayin mutun yabar komai....,inji abokan party d'inshi...... Anci ansha an soye domin gurin kowa da budurwarshi...,Anwar sai kula yakeyi daita....,saidai yawan jawota jikinshi shine bataso....,amma hakan yake tayimata wai gada ace matar dazai aura bata wayeba...,haka gurin ynka cake yawani matseta...,gabad'aya taji hakan ai bai daceba...,sai dai so hana ganin laifi....takasa hanashi........ Sbd hasken gurin da kuma kid'an dake tashi sai watsin kud'i akeyimasu ba adadi... Shiyasa bazaka gane safiyace koh ranaba domin hall d'in yatara abubuwa da dama..... Farha tajawo jikkarta taduba wayarta....8:30 da sauri ta rufe jakar...,tace..... "Nabani Anwar zanje gida...,baba yakusa dawowa..,kuma idan yashigo ban dawoba komai na iya faruwa.....kamayar dani plx......" Riqe hannunta yayi...,"kibari atashi kawai 9 za'ayi closing gashi koh pic bamuyiba kuma donmu aka zo...." "Ah Ah idanranar aurenmu tazo muyi...,amma wlhy banta'ba zuwa party ba don Allah kabarni inbason kakeyi a ynke aurenmuba....." Hankalinshi yatashi domin baya qaunar abunda zai xamo barazana a aurensu hakan yasa yasauko...,yashaidama qawayenshi zai kaita gida domin tagaji zai dawo.... Suka fito hankalin farha akan agogon hall d'in 8:35 duk ta qagu takai gida kafin baba yashigo...,don mama nada sauqi amma wlhy shi hukunci zai yankemata don ynx abu kad'an zai sashi hawa fushi indai kantane..., suka fito suka shiga motar amma farha takasa cewa komai sai ynx take danasanin xuwan... Dai2 nan kiran rasheeda yashigo..,gaban farha ya fad'i.... Da sauri tad'auka..... "Farha kinkoma gida koh kina hanya...,mama takirani amma band'aukaba...,kuma dagani baki komaba...,kuma qilan takira wayarki koh kashe koh baki d'aukaba domin tayiman missed call ukku nakasa d'auka..,kina ina.......?" "Hmmm abun hawa yayimuna wuya amma ganinan zuwa ynx gidan nayo....." "Toh kiyi sauri zan fad'amata muna gidansu momy da aka qarasa amma gakinan zuwa......" Dasauri farha ta kashe wayar domin gara tace babu charging wannan qaddarar party data hau kanta batasan yaxata kwasheba idan babansune yadawo....... Hankalin mamar yatashi domin ace 8:40 farha bata gida...,tunda suke da ita da yr uwarta basu ta'ba kai issha'i basu dawo gidaba koh da gidan ummar jabbar ne kuwa......,tsoronta gada mahaifinsu yadawo zaiga laifinta kuma ita zata gane kurenta...... Farha kallon Anwar ma takasa shikuma sauri yakeyi domin yasan akwai mtsl bayason abunda zai dameta koh kad'an...,gudu yakeyi ga duhun dare...,domin akwai nisa..... Tuuuusss sukaji motar tayi sakamakon qusar da tayar tataka...,chak motar ta tsaya...., farha idanu ta bud'e domin batasan menene ke qaraba kamar halbin bindiga kuma shi ya tsayar da motar..., fitowa yayi yaduba...,tayar tayi faci...., "innalillhi wallahi muntaka qusa tayar ta sache...,gashi gurin tsit koh mota baka hange...,bari nakira wani cikin abokaina sukawo muna mota......" Aza hannu farha tayi akanta ta fashe da kuka tace..... "Nabani wlhy baba zaiyiman hukunci mai muni domin nasan yadawo banida wata dubara ynx qaryata taqare...." Kuka takeyi kukanda saida Anwar yakashe wayar dayakira akawo mota....yabud'e motar yashigo yajawo hannunta yana lallashi tayi haquri ynx zasu kawo suwuce...,ba abunda zai faru..... Umma takira rasheeda domin har ynx bataga farha ba...koh gidansu tawuce..... Takira rasheeda ta d'auka suka gaisa...,ta tambayeta farha...,saida gaban rasheeda yafad'i domin ynx batada mafita illah tawanke kanta....,ta shaidamata tund'azun suka rabu...,ita tawuce itama ta wuce..,....gaban mamar farha d'in yafad'i taqara tambayarta toh lfy wayarta a rufe...? Itama rasheedar tace takira ynx bata zuwa.....a haka suka rabu mamar sai safa da marwa takeyi..., toh ina farha tajene hakan....?" Tana cikin wannan halin baban yatsaya da motar shi yashigo gidan....,nan hankalinta yaqara tashi domin batasan ya za a kwasheba idan yatambaya ina farha d'in take domin wajibine ya dawo azo ayimashi sannu da zuwa indai suna gidan..... Shigowa yayi yatararda ita a pallor tsaye tana safa da marwa....., "Lfy kike kai da kawo haka...,?" Juyowa tayi da fargaba...,tace..... "Dolene nakasa zama farha tafita tun la'assar gurin wai walimar yr uwar qawarta rasheeda amma har ynx batadawoba itakuma qawar tace tund'axu suka rabu amma gashi 9:30 bata dawoba....." Shima baban hankalinshi yatashi domin abun tad'aurar mashi kai....kuma yasan bazata ta'ba zuwa gidan jabbar ba gurin ummarshi tunda cen mahaifiyarshi take ynx...,toh cenne kawai gurin zuwanta...., lallai farha shashanci tazo dashi kenan..,nasan maganinta kawai...,burina a ganta....yakira wayarta kashe again....,wucewa yayi part d'inshi amma yakasa gane komai..... Farha kuka takeyi na tashin hankali Anwar na lallashinta...,domin zama gurinma had'arine dashi sbd za a iya kashe mutun ba asan anyiba...,yaqara kiran wanda yakira yakawo motar yashaidamashi yana hanyane..... Anwar shima yaji duk baiji dad'iba domin bayason abunda zai 'bata ran farha...,don ita wata garkuwace gareshi hakan yasa bayason abunda zai 'bata rayuwarta..... Farha ta rigada ta sad'aqar cewa duk hukuncin da zaizo kanta shikenan zata d'auka domin ita tajawo ma kanta wannan qaddarar gashi hakan zaisa hukuncin mahaifinta yazamo wajibi kanta.....tadubi Anwar tadubi agogon motarshi 10:08 ta fashe da kuka tace...... "Anwar mahaifina zuciya ke gareshi dana san hakan zai faru gareni da banyarda nazo partyn nanba domin duk abunda nashirya ya ruguje...,gashi son zuwan zai zamo *dalilin hawayenah!๐Ÿ˜ญ* mahaifina bazai ragaman ba......" "Kiyi shiru farhanah babu abunda zai faru da yardar Allah...,ynx kiyi shiru kawai....." Yajawota qirjinshi yana lallashinta..,hakan yasa tad'an tsakaita kukan.....hasken motar ya hango da sauri ya saketa yafito da ita motar...,yana qarasowa ya bud'e mata motar suka shiga baya gabad'ayansu...,ciro hijab d'inta tayi a jikkarta tasaka...,aka ja motar sai unguwarsu...... Tunda mahaifin farha yadawo yake kiran wayar duk wanda yasan farha zata iya zuwa gurinshi amma tsit....,haka mahaifiyarta itama sau biyu tana kiran rasheeda....,har iman takira ta shaidamata.....,tunda Iman taji takasa koh zama burinta aji inda take...dayake jabbar na d'akinshi itakuma tana d'akinta...,hakan yasa abunda tayi niyyar yiwa jabbar takasa kuka kawai takeyi ita kad'ai.....,kuma batason jabbar yasan da zancen abunda tafara zai dawo baya..,gara tayi shiru ta qyaleshi....,tayita addu'a domin tanason yr uwarta..... 11:00 dai2 farha tafad'o hirgice cikin gidan...., mamar naganinta kawai tayi tsaye hirgice..... Miqewa tayi tsaye tana yimata wani kallo..... "Gidan ubanwa kika fito a cikin tsohon darennan maqaryaciya wadda batasan ciwon kantaba...,.....?" Kuka farha tafarayi tareda duqawa da guwayyunta qasa tafara cewa...... "Mama don Allah kiyi haquri motarmu ta lalace a hanya sai ynx muka tsira...,mama kiyafeman gada baba yaji....." Jin kawai tayi anyanketa da mari guda ukku masu kyau wanda bataganin komai don azaba...,hakan yasa ta duqe tariqe fuskarta...... "Don uwarki kitashi kikoma inda kika fito..,mun sallama ma duniyarke kiyi yadda zakiso da ita...,duniya ita kikeso da qyalqyalin cikinta hakan yasa kika bijirema buqatarmu toh kitafi cen ki qarasa aburki domin bazaki 6ataman sunaba da abun kunya...." Dasauri mahaifiyarta ta riqeshi...,tace da sauri...... "Ah ah baban Iman gada fushi yasa mu aikata abunda bashine yakamata muyiba...,don Allah don girman darajar haihuwar da mukayi musu...,kayi haquri idan taje ynx ina zataje...,darene p....?" "Inda tafito kuma inda tabaro wanda suke tareda ita wanda ya ajeta ynx a mota shi nakeso tabishi cen suqarasa iskancin dataga shine dai2 gareta...." Mamar tadafe baki da sauri..... "Farha maza kike bi kenan..? Har kinsan kibi namiji inda yake kenan..?" "Wlhy mama banta'ba bin mazaba....,koh ynx qaddarace...,ba kowabane Anwar ne...,shi yad'aukoni motar ta lalace sai ynx yasamu aka kawo wata muka wucikke....." "Kibi anwar qanen ubankine..? Har akawoki qofar gidanku da music acikin mota..,da daranane da nasha zagin duniya....,don haka da azagan akan d'iyar dabatasan girmanaba gara nayi sunan bani tare da ita......" "Kayi haquri baban Iman don Allah sukenan garemu..,kuma idan mukayi hakan ai bamusan inda abun xai tsayaba...,kayiman adalci ka tausayaman ka changr wani hukuncin ba wannanba...,albarkacin zaman mu ba sa'bawa tsakaninmu da biyayyar danake yimaka......" Jikinshi yayi sanyi...,amma wlhy da niyyarshi ya sallamata kawai cen ta qarasa....,hakan yasashi zaunawa kujerar parllorn...,cikin fad'a yace...... "Na haqura zan qyaleta tazauna...,saidai nanda kwana ukku wlhy aure zanyimata...,assabar mai zuwa zan d'auramata aure daduk wanda nasamu koh da kuwa almajirine koh kuma takawo wanda takeso acikin kwana biyu...,domin idan har zatasan tabi namiji toh gara na turata auren cen su had'u......." Miqewa tayi ta bud'e idanunta gaba d'aya ta aza hannu saman kanta....tafashe da kuka wannan hukunci hakan dame yayi kama....... Mamarma saida gabanta yafad'i...,aure kamar na yr tsana....., "Ehh hukuncina kenan koh takawo wanda takeson acikin kwana biyu...,koh na auramata d'aya daga cikin wanda naso almajiri....,koh kuma tsoho...,sai taji dad'in zaman....... Kuka farha ta rushe dashi tabani yau ta lalace taga takanta party yazamo mata halaka gashi yazamo *dalilin hawayenta!๐Ÿ˜ญ* baban wucewa yayi d'akinshi....,mamar ta riqata ta zauna kujera...... " farha fad'aman gsky wani abu yashiga tsakaninki dashi wanda kuke tare...,don nasan yadda zanyi da wuri....,ina nufin kinbashi budurcin naki tun ynx...?" "Wlhy mama banyi abunda kike tunaniba hassali hakan baita'ba shiga tsakaninmuba..,kuma bazanyiba...." "Toh inma kinyi imma bakiyiba...,gashinan son zuciya zaisa ayimaki abunda bakyaso...,ynx gashinan kinjama kanki...,ke nassani ni kinga wucewata......" Farha da gudu tafad'a dakinsu...,ga gajiya da tarin rankon sallah gakuma tarin fargabar abunda zai faru....,wayarta tacire cikin jikkar takunna....,kiran Anwar yashigo...,sauri tayi tad'auka tana kuka tace....... "My Anwar ankusa rabamu domin zuwa partynka yajamani hukunci mai tsauri...,idan baka turo iyayenka nanda kwana biyuba toh babanah zai auraman duk wanda yaso....,kakoh ga mun rabu har abada...,kuma rashin aurenka zaisa yazamo *dalilin hawayenah๐Ÿ˜ญ* na har abada domin sonka yahanani yrda da za'bin iyayenah....." Shiru yayi kuma yace..... "My farha koh gobene yace wlhy zan aureki...,kidaina kuka shirye nake da aurenki koh tawacce hanyace...,zamuzo da dady gobema don gobe zaixo......" Farinciki da kuka farha keciki....,sukayi sallama tashiga toilet yin alwallah tayi sallah ta kwanta don babu barci a idonta yau....... Tab farha and'ebo da zafi kuma....Aure da kwana ukku..? Rikici ba gayu kenan...,auren fuji'a za ayi kenan.....,gamu gani dai...๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ *Bee Been masoya*๐Ÿ’ž [1/18, 11:57 AM] Bee Been๐Ÿ’ž Masoya: ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ* ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง ยฉยฎ Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ โ˜…TRUE LYF STORYโ˜… โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… *_TRUE LUV ISN'T ROMEO AND JULIET...,WHO DIED TOGETHER...... IT'S GRANDMA AND GRANDPA WHO GREW OLD TOGETHER.......?_* โคโคโคโคโค *_Wooo๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€ ๐Ÿ’งBee Bee๐Ÿ’ง LUV YOU ALL MY SWEETHEART MASOYA MY BUK P๐Ÿ˜‰...._* Page... โ˜…1โƒฃ9โƒฃโ˜… ยฎ Dawowar Umman jabbar gidan sai farinciki yaqara cika Iman domin taqara samun hanyar qarasa plan d'inta....,kasancewar ynx koh yaushe tanacen...,acen take wuni sai idan yadawo sai tayo gida domin umman bazata bartaba..., ganin hakan ma dataga yakusa dawowa sai tayo part d'insu da sauri ta sauya shigarta...,haka kawai zata tsiri wani aiki a gidan...., Iman akwai tsafta domin koh ina na gidan zata gyarashi amma baxata shiga d'akinshiba domin bai bata iziniba...,itama bata ta'ba sha'awar shigaba...,saidai shi yashiga d'akinta kuma a tsaye zaiyimata maganar da zaiyi yafita..,koh su had'u a parlor kujerarsu nesa da juna...., shi jabbar duk yanayin hakane don kare kainai daga fad'awa yanayin da zai jimata ciwo...,hakan yasa yake jajjayemata sai tacika age d'inda yasan zata iya d'aukar rayuwar aure...,kuma alokacin zai cika alqawalin da ya d'auka naganin ya mayar da iman macce cikakka amma ynx ina akwai saura..... Hakan da iman taga ynx yana qara jayemata sai ta 'bullo da wata dubara ta bazata yi komaiba sai in yana parlor...., Kamar kullum yau tunda tayi abincin rana takaima umma d'in bata sake yinwaniba sbd ba ci yakeyiba...,iyaka dai taga yasha coffee in yana kallon news hakan yasa taji yau zata dafa indomie taci...., bata tashi fitowaba saida taga yana zaune...., sannan ta sanya wasu miyagun kaya....,wato rigar samanta net ne wajibi kaga rabin qirjinta baki d'aya domin saman komai ana gani...,sannan Iman komai bata sakaba rigar kawaice jikinta hakan zaisa duk motsin da zatayi dole qirjin budurwa ya motsa...,rigar qaramace kuma guntun hannu..., wando tasaka iya gwuywarta qwafrinta duka sake yake wandon roba ne dole yakama ta tako ina...., nad'e gashinta tayi ta jawo gyale qarami ta d'aureshi..., ruwan turare tasakarma kanta.,sannan taduba madubi taqara ta juya tayi wata shegiyar dariya tace..... "Wooo Iman zakiyi kashin kai...,don kuwa wlhy koh shehu imamu sarkin cin tazbaha yaganki dole ya miqe bare wanda ke d'aukarki ke yarinyace kuma yaga akasin hakan...,brox kagani kuma qwalelenka...,sai kakai limit d'inda kad'aukarwa kanka...,nidai yaqina kagane cewa Iman ba yarinya bace...,inkasoni ingada kasoni nasan dai ni ba yarinya bace irin yadda kad'aukeni...,kunya kuma nakaita gefe na aje sai watarana kuma...." Taqara fesa turare tayi waje...,kallonshi yakeyi bai damu da yad'ago ya dubetaba cup d'inshi a hannunshi yana sha...., wucewa Iman tayi one by one har takai bakin kitchen d'in...,baiyi niyyar d'agowaba amma turaren dayaji tabarmashi a parlon ne yasashi d'agowa da sauri..., hango qarasa shigewarta yayi kitchen d'in bai ganta gabad'ayaba hakan yasa yaji yanason yaganta kuma yaji me zatayi ynx cikin daren nan...., aje cup d'inshi yayi shima yayi hanyar kitchen d'in don yagani da kanshi..., Hangota yayi ta duqa a drower qasa kome take d'auka...,miqewa tayi kuma a ta samar.... Jabbar sumar tsaye yayyi..,ganin qugun Iman kawai yasashi shakku da yawa...,ya dskare wlhy abun mamaki injishi a cikin zuciyarshi...,sauri yayi daga inda yake tsaye yayi qarfin hali yakoma inda yake zaune...,mamakin yau yagirmi na kullum kallon news yakoma son kallon wadda ke kitchen...., Iman kwata kwata batasan yazo gurinba har yakoma...,hakan yasa tadafa indomie d'inta da dafaffen qwanta guda biyu tafito...,qamshinta tashi kawai yakeyi.... Mai makon ta aza a dining sai ta d'auko aburta tayi hanyar d'aki.., juyowar da zatayi...,anan jabbar yamiqe tsaye da sauri ganin abunda ke gaban iman har wani motsi sukeyi..., iman bata damu datayimashi maganaba domin tasan saqonta yaje inda taso yaje...,kafin tawuce da sauri yasha gabanta...... "Qanwata rowa kenan zakiyiman...?" Murmushi tayi tace... "Ah ah p..,abinci idan nayi ba ci kakeyiba...,toh bale wannan jagwalgwalo...,kawai kabarshi ni zan dinga dafamuna nida umma kai kuma kadinga cin wanda kake sayowa...,kuma kace haqqin ciyarwata na akanka to nayafemaka..,ni xan dinga nawa kai kayi naka...,ka matsa na wuce brox...." "Ah ah luvly qanwa...,kiyafeni ynx zanci plx.,wannan qamshi haka yawuce ni...." "Sanin baka damu da shiba da wadda keyinshi shiyassa nadafa na mutun d'aya...." Murmushi yayi domin kuma ta burgeshi yr wannan tsiwar tata....,amma ba abincin ne burinshiba..,abubuwan dake motsi jikinta yakeson yaqarema kallo don shakkunshi yafita....,koh maganar basheer gsky ce.....,? Iman taga bashida niyyar bata hanya ta wuce sai tadawo parlon ta zauna shima yazo kusa da inda take yazauna...,amma ba ita yake kalloba koh abincin datake ci shi burinshi tayi abunda zaisa ya leqo kanshi a rigar yaga shin ba kayan kantine tasakaba...., hakan yasa nashi plan d'in fara rugujewa nacewa bayason ta'bata amma dole p yafara yayema kanshi tunani akan wannan abun dayake kwana yake tashi dashi.....,ynx kusan 1week kenan yanaso yagane gsky amma tsoro yakeji gada ya bayyana kayan kantine tagane nufinshi kuma babu riba.... Hakan dai wata zuciyar ta tunatar dashi matarkace

Chapter 8 of 44