nasu..shike koyamusu assignment yakuma gyara masu inda suka kuskure...,har suna kiransa da brox jabbar sbd d'aukar dasuke yimashi na yayansu najini..,domin bazasu rabe dangantakar iyayensuba domin akwai kyakkyawar shaquwa da k'aunar juna tsakaninsu wanda kowa nashiga dangin kowa....
Haka suka taso cikin kyakkyawar kulawa...,farha na bala'in son k'anwarta wadda komai tare sukeyi d'aya bazayayi abunda d'aya bayasoba,suyi kuka tare idan d'aya yayi laifi akayimashi fad'a...suyi dariya tare idan d'aya yayi abun farinciki...hakan nasa iyayen nasu jin farinciki duk da baibasu d'a namijiba kuma bai qara basu wata haihuwaba...sunji alhmdllh kuma ga abdl-jabbar nayi musu duk abunda d'a namiji zaiyima iyayenshi domin rabin zamanshi duka gidansune.....
Lkchnda abdl-jabbar yaqare secondary school lkchn ne kariyar arziqi tafad'oma baban farha komai nasu ya tsaya domin shine garkuwarsu har Abdul d'in hakan yasa daya gama secondry bai wuce wataba...lkchn mahaifinshi malam ibrahim bayada komai domin albashin nashi na shigowa bashin abincin dasuka amsa zai cenye kud'in....
Duk da halin dasuke ciki Aliyu abbas bai daina buga bugar dayakeyiba gurin neman kud'in makarantar yaranshiba haka itama binta..har saida komai nata yaqare a hakan suke zaune cikin rufin asirin Allah yaran na karatu....
Watarana gidansu abdl-ake kawo masu abinci...har farha takai primary 5 awannan halin suke....
hakan yasa baba Aliyu abbas yaga yakamata abdl-jabbar yawuce school tunda takardunshi sunyi kyau hakan yasamu yasamamashi wata university nan kaduna yafara..tareda taimakon shi abdl d'in domin yasan ciwon kanshi...,hakan suketa taimakon junansu hardai aka qarasa.....
★★★★★★★★
Rayuwa nagudu kwanakki na gushewa ayau farha taqarasa secondary school d'inta iman na s.s.2...Abdl-jabbar yaqarasa university d'inshi sai service dayakeyi a yobe wanda yana d'aukar long tym bai dawoba.....
Izuwa lkchn duk wani yn matanci gabad'aya ya baiyyana ga farha domin yariyar akwai kyau..farace kuma mai d'an jiki, qirar farha qirace ta azo agani domin ita mai yalwar qirjice ga kyau....wanda baka rabeta da qanwarta saidai iman batayi haskentaba.., totally yaran sun had'u....
Dawowar abdl-jabbar tafarko lkchn ne yaji qaunar farha tawuce ta d'aukar zumunci takai ta abun a yaba...,han yasashi fara nuna mata a wasa....,
Watarana yazo gidansu bayan isha'i kamar tym d'inda yake zuwa fira gurinsu domin shi ba ma abuci son qawayeneba....
Farha tafito d'akinsu domin gaidashi taji yashigo....kallo d'aya yayimata yafara jin changi jikinshi....haka tazauna shinfid'ar tareda yimashi barka da dawowa...suka fara firarsu kamar yadda suka saba...,dare yayi yawuce suma suka koma d'akinsu......
Yadawo gida hnkalinshi tashe domin wlhy son farha yakamashi amma wlhy yakasa fad'amata....Toh waishi ta ina zaifara.....??
Yake tambayar kanshi domin sonta full yake a zuciyarshi....Allah yasa ta aminta dashi kafin yakoma....,shikad'ai ke firarshi ad'akinshi.........
*Bee Been masoya*💞
[12/29/2017, 9:44 AM] Bee Been💞 Masoya: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*_{SUBHANALLAHIE WA BEHAMDIHIE....,ADADI HALQIHIE....,WARIDA NAFSIHIE....,WA ZINATU ARSHIHIE....WAMADADA KALIMATIHIE...👏🏻}_*
*RAMLART REAL DAMBU...congratulation...,inamaki murnar qare buk d'inki.., ☔NAMIJI BA YARO BANE☔ Allah yaqara haxaqa...,bee been kice dai💘*
Page....
★4⃣★
® ABDL-JABBAR IBRAHIM UMAR..., matashine maiji da kanshi ta hanyar gyara kanshi abdl-jabbar shikad'aine ga iyayenshi..wanda sun dad'e basu samu haihuwaba sai gareshi..,kuma sai Allah bai qara basu wata haihuwarba....
Iyayen Abdl-jabbar suna matuqar sonshi....saidai rashin wadata mai yawa na tauyesu ta wani gefen gurin samamashi jin dad'in duniya...amma wadatar zucinshi shine abu mafi burge iyayenshi....
Abdl-jabbar kyakkyawane ajin qarshe domin komai taurin kanki ke macce da kinganshi xakiji ya kwanta maki...akwai tsafta akwai son gayu hakan yasa yake samun yn mata tako ina idan yafita...,irin mutanen nanne masu ko in kula da rayuwar kowa...,hakan yasa bayada aboki..,idan yadawo da mkrnt bayada gidan dayake zuwa face gidansu farha yaci firarshi suyi kallo suyi karatu...yadawo gida domin barcinshi...
Tsarin rayuwarshi na burge kowa...,hakan yasanya babansu farha yake matuqar sonshi sosai...,kuma gashi yana d'ebe mashi kewar yaro namuji dabai samuba...
Rashin wadatarce mai yawa tsakaninsu..,komai na karatun abdl-jabbar yadawo hannun aliyu abbas babansu farha kenan...,duk da shima ba komai gareshiba amma yanada mutanen dayasani dalilin kasuwancin dayayi baya..,suna taimaka mashi....,sbd bayason karatun abdl-jabbar yayi baya domin yanada ilmi mai yawa....dahaka akatayin karatun har abdl-jabbar yasamu ya kammala service d'insa....
Saidai yaqarasa tareda wani al-amari mai rikitarwa domin babu wadda yakeso a cikin mata face farha...,duk da yasan idan yafad'ama mahaifansu zasuyi murna da farinciki...,amma yafison yasamu yarda da amincin farha d'in kafin mahaifan susani...,
Toh amma yana nunamata har ynx bata fahimci komaiba...,koh taya zaiyi..?
Hakan koh yaushe zaije gidansu suyi fira yadawo da zancenshi aciki baifad'amata sonda ke zuciyarshiba...,
★★★★★★★
FATIMA {FARHA} ALIYU ABBAS...,fatima kyakkyawace ajin farko kasancewar fatima ita tabiyo mahaifinta gabad'aya Farace sak ga manya idanu...fatima yr duma dumace itaba siririyaba kuma bamai jikiba tsaka tsakiyadai...farha nada yawan son murmushi don koh magana batayimata dad'iba zatayi murmushi sannan tayi fushin nata...farha nada biyayya koh nace sun samu tarbiya mai kyau gurin iyayensu... Iyayensu nasonsu kamar rai da ajali duk da basu samu d'a namijiba sunsan sune sanyi idaniyansu....saidai farha nada wata d'abi a riqaqqen ra ayi gareta..,domin koh a binci akwai abunda takeso akwai wanda bataso..kuma idan batason abu bazatace batasoba saidai kaga tanaqin accepted d'inshi wannan kad'ai na dagula rayuwar yr uwarta iman....
*KHADIJATUL IMAN* k'anwace gurin farha...,khadija itama tsarinsu d'aya da farha saidai farha tafita haske sosai...itakuma khadija batada jiki kamar na farha amma kuma ba ramarmace...,khadija nada kyau da sassauqan ra'ayi komai ya tari gabanta zata iya kar'barsa taci domin tasan shine wadatar gidansu...,kuma shine arziqinsu tunda a farko ba haka suka tasoba....duk da yadda iyayensu ke nunamasu qauna saidai da alamun sonda sukeyima farha ya girmi na iman domin farha itace ta farko...,saidai mahaifiyarsu nanuna k'aunar iman ne a fili....
Komai tare sukeyi basa rabe kansu gurin saka kaya gurin ma'amala koh wa yasan sirrin kowa kuma kowa na rufe sirrin kowannensu..,wanda iyayensuma basa sani...,sai idan abu yafaru mai nauyi su sanar da brox d'insu abdl-jabbar zaibasu mafita....basa fita koh ina..,hakan yasa basuda qawaye sune abokan junansu...
Lkchnda farha tafara zuwa state university nan kaduna lkchn IMAN ke shirin zana S.S.C.E d'inta hakan yasa suka samu banbancin fita tare.....
At all yaran sunsan kansu ta hanyar gyara kansu...dole kagansu kaji kanaso kuma dole kaji sanyi idan d'aya tace tanasonka...duk da farha tagirmi iman kuma tafita cikar budurci amma duk d hakan ba bayaba...chikar haibarsu daban take da sauran yaya duk da rashin wadata mai yawa koh dake garesu..,hakan iyayensu ke sayamasu suturu masu tsada......
💧💧💧💧💧
Kamar kullum abdl-jabbar a hakan yake riqe da sirrinshi..,saidai yau yaquduri shaidama farha sonshi a zucigarshi zuwa gurinta...
Yashirya kamar kullum domin shiga gidansu gurin firar dasukeyi...,saidai yau tafiyar ta ranace.... Yayi kyau iya matuqa domin ta ko ina qamshi ke tashi jikinshi....yashiga d'akin ummanshi domin yashaidamata zaije gidan baba Aliyu koh da za a nemeshi....,anan yatarar da mahaifinshi d'akin suna zaune suna fira...,ummanshi na ganinshi tace.....
"Babanah kuma yau sai ina hakan...?"
Yasosa kanshi yace...
"Umma gidansu farha zanje zanyimata assignment da akabasu...,amma xan dawo anjima...."
Sukayimashi Allah tsare tareda cewa su gaishesu....
Kasancewar ynx akwai nisa tsakanin gidansu da dagidansi iman..,sbd masu hayar na suka tayar dasu sai suka matsa wani gurin..,wanda malam ibrhim shine yayi hanyar samun wancen d'in kafin Allah ya yassaremasu nasu...
Fitarshi da buri mai yawa axuciyarshi har yakai gidansu farha...,shigarshi keda wuya yatarar da mama da farha zaune suna kallo kasancewar ynx sunfara samun wadata..,sbd baba aliyu yana kasuwancinshi b laifi sbd baison zama.....
Mama naganinshi tafara murna domin tanasonshi sosai ji takeyi kamar itace ta haifeshi domin bata ta'ba mance karamcin iyayenshi akansu....
"Abbanmu shigar rana akeyimuna yau..?"
"Eh mama farha takirani..,wai batagane assignment d'in dazatayiba nazo na nunamata...,dama kuma inason nazo..."
"Kunfi kusa ai..dama aiki nakeyi zanshiga ciki...,kafin auta ta tadawo...."
Sukayi murmushi dukansu tatashi tashiga ciki....
Yadubi farha d'in yace....
"Yau ina iman d'in tajene halan....?"
Tace..."lesson d'in exam d'insu sukeyi tun 7 sai 6pm suke dawowa..."
Yace "toh Allah yabada sa'a.."
Tace..."ameen"
"Brox chemistry d'innan kwata kwata bangane komaiba kuma yace assignment d'in shine C.A nashi gashi da 6aqar zuciya wlhy..."
"'Dauko nagani..."
Tamiqe don zuwa d'akinsu gabad'aya hankalinshi akanta yake...,farha tayi farha ta kammala abunda yakeso ga 'ya mace...,don haka yau zai shaidamata qudurinshi....,yana hakan tadawo da handouts d'inta da longbook nata...,ta sauko qasan shimfid'ad'ar ledar fallon nasu qarami..shima ya sauka...yana nunamata tana rubutawa tareda yata bayani d'ai bayan d'aya har suka qarasa...tarufe buk d'in tana bashi lbrn abunda ke faruwa school nasu...bakinta kawai yake kallo yadda yake motsi da kuma yadda take sarrafashi...gabad'aya yatafi a kallon qirjinta....
"Brox lfy mekake tunani hakan..?"
"Ke farha..! Ke nake tunani...."
"Brox kuma wani sabon salon firane hakan yau...? Toh kayiman ni kad'ai tunda iman batanan sai nabata lbr...."
Yayi murmushi tareda duba fuskarta...,sannan yariqa hannunta yayi murmushi.....
"Farha kinsan menene so kuwa...?"
Tadubeshi cikin mamaki tunda suka girma bai qara riqa hannunsuba sai yau...tace....
"Eh brox nasan so mana...saidai banta'ba yinsaba...Allah yasa munsamu aunty musha biki..."
Yaqara riqa hanunta duka biyu yace....
"Farha ki fahimceni...ki dubi fuskata..,sonkine kwance cikin zuciyata wanda bansa yazan shaidamakiba..,hope zakiso d'an uwanki...,kuma ki bani answer domin nasamu sanyi zuciyata....."
Hakan dayace sai tayi sauri taqwace hannunta duka tareda rufe fuskarta...ta miqe ta.a murmushi sai d'akinsu tana faman rufe fuska....
Mama taga wucewarta da sauri kuma taga tana murmushi harda rufe fuska sai abun yabata mamaki....
Shigarta pallor d'in saita ganshi zaune yana duba littafin nata....
"Babanmu har anqarasa karatun ne..? Naga qanwar taka tayi ciki...?"
"Eh mama anqare ni wucewa zanyi dama zanbiya kasuwa nadubama baba kaya yadawo cin abinci..."
"Ah Ah jira kuci abinci sannan kaje..."
Sallamar iman tasa umma juyowa....,ganin tadawo da wuri yau...
"Auta lfy dawuri haka..?"
"Qlau mama kawai anqarasa d'ayan wlhy nagaji shiyasa kawai nadawo gida...,nasan 'ya'ya farha tadawo tun d'axun...."
"Eh toh Allah yataimaka.. kije kizubomaku abinci ga yayankunan najira kuci...."
tagaida Abdl d'in tareda wucewa ciki....shigarta da sauri ta hango farha riqe da fuska...,domin farha ta aza shine yabiyota d'akin....
" 'ya'ya lfy kike rufe fuska nice fa...?"
Sannan tasaki fuskar tareda dafa yr uwar tata...
"Iman sabon al-amari...,amma bazan fad'amakiba sai anjima domin ynx zuciyata takasu biyu..,kuma kibani shawara kasancewarki yr uwata abokiyata...."
"Allah yaji dani alkhairi kitashi muci abinci wlhy yunwa nakeji...mama tace nazubamana zatayi sallah...."
Tamiqe tatashi sannan itama farha tabiyo bayanta...,suka zu a kamar yadda suka sabaci..sukayo parlor farha nashiga sukaci karo ashe bai wuceba...,kawai sai tadake suka zauna aka fara ci...,shima hannunshi yasaka ciki sunaci.....
Abinci sukeci hankalin iman kwance sbd batasan abunda suka saniba...farha takasa d'aga idonta bale suga juna....shikuma burinshi yaga idonta amma taqi...,haka suka qare shi yawuce da zumud'in jin amsa d'inta itakuma suka koma d'akinsu don yin sallah.....
Dare yayi sukayi shirin kwanciya bayan sun gama karatu littafansu na addini dashima Abdl-d'in ke karantar dasu gareshi suka sauke alqur'ani....
Farha ta hau gadonsu kusada yr uwarta takira sunanta......
"Iman yau brox abdl cewa yayi wai yanasona kuma nabashi answer da wuri....,kina ganin yadace nasoshi...? Kuma wace answer zan bashi? domin bansan soba wlhy har ynx....."
"Kai 'ya'ya farha keda ke jami'a bakisan soba...bale ni dake secondry...,amma wlhy naji dad'in wannan abun 'ya'ya..,brox yakai namijin dakowa keso....kuma wlhy kunyi dace ki amsa koh ta wayane kawai...,burinah kiyi aure nima a turani wlhy....."
"Iman Allah shiryaki gaki gaki saliha amma sai iskanci 'boye....,zanyi yadda kikace...,saidai inason brox amma har ynx baicika abunda nakeso ga mijina yakasance yanadashiba....
Nafarko...,yanada ilmin dakowa zai soshi... domin yacika duka biyun..
Nabiyu...,abdl nada kyawon dako wace macce zatasoshi...ga hankali da natsuwa....,
Saidai bayada cikar burin danakeson naga na hau wato....mujina yazamo mai dukiya domin iyayenah suji dad'i...... Amma zanso abdl ahakan sistr........
" Ah Ah 'ya'ya farha kiso brox da zuciya d'aya insha allah zakiji dad'i nan gaba har muma baki d'aya...,ki amsa masa gobe kina sonsa kawai...."
"Insha allah gobe zanyi yadda kikace qanwata...."
Kowa yaja bargonshi ya lullu'be sbd sanyi.......
★★★★★
Ga Takundai...
🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀
*Bee Been masoya*💞
[12/30/2017, 12:07 PM] Bee Been💞 Masoya: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*_{AUZU BIKALIMATILLAHIE..TAMAHTIN MINSHARRI MAHALAQA}→Ya Allah kakaremu dasharrin mutun dana aljani..,wanda muka sani da wanda bamu saniba....ameen y Allah←👏🏻_*
Sweet khadyn khady...,
*HAPPY BIRTH DAY 2 U....MORE YEARS IN ISLAM....🎂🎂🍩🍩🥂🍸🍮🍡🍔🍕🍪🍬🍭ALLAH YAKAWO MAGANIN SANYI WATA SHEKARA DA SAURI☹ DOMIN AKWAI DAMUWA WLHY SORRY🤐...bee been kice kawai....🤸🏻♀🤸🏻♀*
Page...
★5⃣★
® Yadawo gida amma hankalinshi tashe yake....ga alama farha nasonshi amma meyasa bazata fad'amashiba...,gashi yarigada ya furta...Allah yasa wani bai rigashiba..,haka yakwana yanata tunani har safe...
7:00am yaqarasa karatun qur'ani dayakeyi da azkar d'inshi dayasabayi tareda jero addu'oin dake zuciyarshi wadda ynx taneman aiki itace farko sanna yrda da amincewar farha akanshi domin babu d'iya maccen datayimashi a duniya ynx sai ita...,hakan yasa duk wayanda ke bashi love request baya dubansu domin yasan inda yasa gaba...qarasawarshi tareda tashi daga gurin dayake sai ya hango hasken wayarshi na tashi...yayi kamar yaqyale domin a zatonshi m.t.n ne gara yayi shirinshi domin yaune za'a fara d'aukar ma'aikata company dayake neman aiki...amma sai zuciyarshi tace abdl diba dai....,haka sai kuma yafasa shiga toilet d'in domin duba wayar dake charging...d'auko wayar yayi tareda duba sender message d'in anan yaci karo da sunan lvly sis..da sauri ya zauna gefen gadonshi yabud'e yafara karantawa kamar hakan.....
_"Brox I LUV U WITHOUT KNOWING HOW...,I LUV U STRAIGHT FORWARDLY...,WITHOUT COMPLEXITIES... SO I LUV U BECAUSE IKNOW NO OTHER WAY..., ABDUL-JABBAR LUV U TOO_
Sanyi dayajine gabad'aya yakamashi..,sai yakoma saman gado yakwanta domin duk ilahirin jikinshi yad'auka... saqon farha yagama mashi komai domin tayi accepted nashi ynx burinshi d'aya samun aiki...duk da shima yasan Allah zaibashi hakan yaketa maimaita text d'in ganin har 1hour hakan yasashi miqewa don shirinshi...,yaso ya maida replay amma wannan saqo yafison gashi gata don zaifi zuwa dai2....
Shiryawa yayi yad'auki takardunshi domin zuwa company da aka nemansu...amma idan kasan farinciki da ka kalli abdl kasan yana cikinshi...,haka sukayi submitting d'in takardunsu tareda interview nasu suka qare...,aka shaidamusu za a nemesu ta wayarsu bayan one week insha'allah...haka yadawo gida dad'i bisa dad'i domin yasan da yafara samun aiki iyayenshi xasu fara jin dad'i...yake shaidama iyayenshi su tayashi addu'a insha allah komai zaizo da sauqi...,suma sukayi murna tareda sanyamashi albarka...suka qara godema mahaifin farha domin shine yasamo mashi hanyar tazuwacen gurin neman aikin....
Fitarshi baitsaya koh inaba sai gidansu farha...,shigarshi yanata zumudin ganinta..amma sai yaci karo da baba da mama parlor suna fira yayi sallama yashiga..,suka amsa mashi yasamu guri yazauna tareda shaidama baban cewa yatura takardunshi yau kuma sunyi interview d'in sunce a sauraresu 1week...mamar farha da baban sukaji dad'i tareda sanya albarka garesu....,ganin gidan shiru yasashi tambayar qannen nashi...,mamah ta shaidamai farha na nan amma iman na school batadawoba...
Hakan yasanyashi miqewa tareda cewa....
"Mamah bari nayimata albishir domin nasan zasuji dad'i..."
Suka sakamashi dariya tareda..cewa "ai kunfi kusa da qannen naka.."
Iyayensu farha namugun so Abdl saboda akwai natsuwa...,wanda hakan yasa baban keda wani buri a zuciyarshi amma sai in Allah yaso hakan....
Abdl-jabbar yatura qofar d'akin nasu tareda bud'ewa....,hango farha yayi saman kujerar d'akinsu T-shirt ne jikinta da sket tana karatun handout d'inta domin yau batada lecture...
Hangoshi tayi da sauri ta jawo gyalen iman dake gefen gado tarufe tundaga kanta har fuskarta...., murmushi yayi tareda qarasowa gurin kujerar shima ya zauna....sunkoyowa yayi dakanshi zuwa kanta..tareda saka hannu ya kar'bi handout d'in hannunta datake karatu..ya aje gefe...,yajawo gyalen data rufe fuskarta dashi amma tariqe....
"Hmm kunyata kikeji ne...? Toh ki ajiyeta domin bazata kaiki koh inaba...don ninan akanki komai zan iya fad'a...,don haka ki d'ago kanki zamuyi magana mai muhimmanci..."
Jin hakan dayace shiyasata d'ago kan nata amma kuma fuskarta rufe..domin bata iya ganinshi....
Yakira sunanta tareda riqa hannunta .....
"My farha...! Kitayani farincikin samun abu biyu..., Nafarko samun sonki gareni...Nabiyu kuma yau nayi interview d'in fara aiki insha'allah...ina burin nanda shekara kizamo a hannun damata...,domin ni banason mu dad'e ban mallakekiba...,sone nakeyimaki na har abada nadad'e da sonki farha banji zankai 2years ban samekiba insha allah ina fara aiki kece farkon mallakina...,hope kema zakiyiman kalar sonda nakeyimaki domin muqarfafa zumuncinmu....."
"Congratulated broz ina tayaka murnar samun abubuwan guda biyu...,kuma ina fatar samun aikin da arziqi mai yawa..kuma insha'allah zakasamu yadda kakeso...,saidai sai kayi haquri dani domin kasan ban iya soyayyaba takace farko dole sai kana koyardani zan iya....."
Yayi murmushi tareda qara riqa hannun nata...
"Farha nah insha'allah zaki fini qwarema domin nima ai banta'ba soyayyaba..,gareki zansan zafinshi dakuma sanyinshi har kibani gurin kwana...."
Dasauri tarufe fuskarta kuma...qamshin turarenshi shine ke bimata hanci har yanasa tanajin sonshi nad'an qara shiga....
"Hmmm farha kidaina kunyata inason mugina soyayyarmu ta hanya mai kyau da inganci sannan su abba da baba su sani..., domin ke tawace insha allah nasan bamuda mtsl da iyayenmu zasu ji dad'in hakan damukayi....."
Murmushi takeyi...hakan yasata d'aga fuskarta takalleshi...,shikuma lumshe mata idanun nashi shanyayyi yayi...,da sauri tajuyar da kanta domin abunda taji jikinta yayi wato sanyi tareda jin baqon al-amari jikinta duk ya mutu sbd kallon da yayimata....,
Gane abunda yayimata yasashi yin murmushi amma bai saki hannun nataba...,d'ayan hannun nashi yasaka ya d'auko handout nata...,yace...
"juyo muyi karatun koh..? Nima ayi dani..."
Batace komaiba kuma bata juyoba...suna hakan iman ta turo qofa da sallama tashigo...,sai suka burgeta irin yadda tagansu da alama soyayya akeyi....
"Toooh ashe kune at ciki...bari naje d'akin mamah nachangr kayana nayi sallah inkun qarasa firar nadawo..."
Iman nafita yadubi farha yace.... "Iman tasan komai kenan..."
Farha ta gyad'a kai alamar eh....
Yace... "Shiyasa nakeson sistr iman domin akwai wayewa da wuri kinga har ta fahimcemu p......"
Murmushi kawai tayi tace.... "Zata dai tonamaka assiri gurinsu mamah ba..."
"Shikenan kowama ai sai yasan jabbar nason qanwarshi farha....kinga sai su fahimchemu kawai su fara shiri...next month subani ke kawai cen muqarasa love d'inmu da karatunmu inda zasu kaimu...."
Murmushi kawai take yimashi...hakan yasashi miqewa don ankira sallahn magrib..ya sunkuyo tareda cewa....
"Fad'aman wani abu dazai zama garkuwata kafin nakai masallaci.."
Rufe fuska tayi tace mashi "I LUV YOU.."
"LUV YOU TOO MY FARHA..."
yafita d'akin nasu bayanshi ta zubama ido tafiya yakeyi cikin sigar burgewa...sonshi na nan zuciyarta...,wanda tafara daga daren jiya zuwa ynx....,tacire gyalen datasaka takoma takwanta a kujerar tana jiran qanwarta tashigo.....
Iman nashigowa d'akin da sauri..,domin taji fitarshi...,tafad'a jikin yr uwarta tace....
" 'Ya'ya farha kinga yadda kukayi kyau kuwa...,wlhy wani farin ciki duk yakamani domin da waya garan koh..,wlhy dasainayimaku pic... 'Ya'ya farha nayi maki murnar samun brox jabbar domin rayuwarshi rayuwace ta burgewa..,ni nasan wlhy ya iya soyayya mai inganci...daganinshi wlhy zai bar tarihi a zuciyar masoyiyarshi 'ya'ya farha kema wlhy nasan kin iya luv kidinga kashe brox yasan akanshi aka fara..,amma kuma an iya..."
"Innalillhi Iman ina kika iya wayannan surattan banxar..? Eh lallai soyayya kikeyi a 'boye cen school d'in taku babu wanda yasani kenan...,toh lallai ke yakamata ayima aure baniba ma...,wato har kinsan a kashe mutun da kalam luv...toh koyaman naji sbd ni bansan komaiba...."
"Haba 'ya'ya wlhy ni banta'ba soyayyaba...,kawai dai kinsan idan kana zaune da mutane mabambanta kuma kana shiga cikinsu zaka qaru da wani abun...,kinga school d'inmu har matan aure nazuwa sbd gyara exam d'insu..,toh nikuma kinsan akwai shiga mutane anan in aka fara fira sunayi nakan kashe kunne naji...tunda bansan inda zanjiba..gareki ne kekuma 'ya'ya bakison mutane shiyasa komai bamu saniba gamu zaune kawai...,ga kyau ana shaidamuna ga diri amma komai bamu saniba..."
"Iman kenan menene ranar zama da mutane kata surutu...,kenifa bakowa nake iya zama nayi fira dashiba...,sai kakai irin mutumen danakeso....ke iman rashi totally baiyiba...,ni da ace arziqi garemu wlhy ni da sai anga bubud'awa domin sai kakai irin wanda nakeso zan fira dakai...ke ynx bamuda shi ma bandamu da kowaba a school d'inmu bare munadashi...kedai Allah yayimuna arziqi mudinga shiga waccen mufita wannan...."
Nan take Iman ta changr fuska..ta miqe jikin yr uwar tata....
"Wlhy 'ya'ya farha raina arziqin da Allah yayimaki kawai shi ke had'ani dake...,kituna munada suturar da duk inda muka shiga za a kallemu..,sannan mu masu surace mai kyau wadda kowa zaiyi murna da farincikin kasancewrshi taredamu...,munada lfy gamu cikin gata uwa da uba na raye..,sannan iyayenmu nayimuna duk abunda mukeso muci mai kyau musha mai kyau karatunmu mai tsa'bta duka school namu damukayi prvt ne da akwai da babu iyayenmu zasu biya muna...,amma duka har ynx kina ganin akwai wayanda sukafimu gata a duniya..mumafa munfi wasu wasu sunfimu dogaro ga Allah yafi komai domin watarana zai wadatamu muma..."
Miqewa tsaye farha tayi tareda riqe hannun qanwar tata....
"Haba Iman d'ina daga magana kuma sai fushi..? Toh zauna kinsan banison 6acin ranki iman insha'allah baxan qara cewa hakanba kuma inason brox jabbar sosai...."
Sukayi murmushi tareda zaunawa iman takalli yr uwar tata tace...."Allah ya tabbatar da alkhairi toh.."
"Ameen.."
★★★★★★
Soyayya mai qarfi ke shiga tsakanin farha da abdl-jabbar..., saidai abdl-jabbar yafi farha nuna soyayya qarara domin koh wacce rana idan bai shigo gidanba zai kirata susha soyayyarsu wadda koh dare da hakan suke kwana..,iman najin dad'in hakan domin yr uwarta tafara maida hankalinta gurin d'an uwansu...ynx koh ina suke suna tare maqale a waya..,wanda tarubutamashi my love..💖shikuma yasakamata my happiness💞 soyayya mai gamsarwa sukeyi wanda farha takai bata jure rashin jinshi....,hakan shima idan sunyi waya dole ne yazo yaganta....
Iman sunqarasa neco d'insu..,ynx tadawo gida koh yaushe tananan jiran takardu...,hakan yasa Iyayensu suka fara fahimtar wani abu tsakanin abdl-jabbar da farha..,mamah takasa haqura ta risqi autar tata domin shan lbr domin wannan irin kallo da yarancen keyima juna nabata mamaki....,
"Iman wai meke tsakanin 'ya'yarki da abdl...?"
Tayi murmushi tareda komawa kusa da mamar tata...tace...
"Mamah gada kice ni nafad'amaki zamuyi fad'a 'ya'ya farha...,wlhy soyayya sukeyi tsakaninsu...,ynx sunfi wata biyu a hakan..."
Mamah tayi dariya domin tadad'e d fahimtar hakan don koh ganin farha tayi ance za aje gidansu abdl-jabbar d'in sai tace batajin dad'i domin gada taje su had'u aganesu....,"toshikenan ai abun yayi kyau Allah had'a hankullansu...zan sanar da babanku kawai..."
💧💧💧💧💧
Abdl-jabbar yafara aiki a federal ferma ba laifi yanasamun albashi mai d'an qarfi..,domin yasamu lavel 5 agurin aikin kuma ba laifi yana rage wahalhalun mahaifinshi...domin ciki yake sayamasu abinci dakuma abunda ba a rasaba....,hakan zaisai kayan make up masu tsada yakaima farha..,tareda sayama iman nata....
Hakan dayakeyi yasa duka ynx iyayen sun gane cewa akwai soyayya mai qarfi tsakaninsu...sukaji dad'i sosai.....
Albashinshi nafitowa yana rage wani abu ciki domin son yakeyi zuwa next year yanada farha hannunshi....acikin kud'in yasayi mashin d'in zamani dashi wataran yake kai farha school duk da batason ana ganinta a mashin amma batason sa'bamashi..amma kamarta da yn jami'arsu kemata d'aukar d'iyar masu kud'd'i sbd takunta da wankanta...domin school d'in kowa nason ace qawarshice koh kuma budurwarshi....amma duka farha bata bada damaba....
Shiyasa idan yakawota aget suke tsayawa gada aga abunda ke ajeta.....
Ahaka dai aketa wannan soyayya...,shi yana yima farha soyayya taji da fad'i itama tanayimashi soyayya da zuciya biyu .... Domin tanasonshi iya matuqa amma kuma da yanada abunda yafi hakan da sonshi ya wucenan a zuciyarta......
Oh nie bee bee nace farha rayuwarki tayi..,kuma batayiba domin sannu bata hana zuwa saidai adad'e ba akaiba....,Allah katsayar da zukatanmu gurin da akajemu...,ka yayemuna dogon buri....ameen👏🏻👏🏻
~Ummul Ilham~
*Bee Been masoya*💞
[12/31/2017, 2:51 PM] Bee Been💞 Masoya: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*_YA HAYYU YA QAYYUM...BIRAHAMATIKA ASTAGISU...,ASLIHLIE SHA'ANIE KULLAH...WALA TAKILNIE ILA NAFSIE 'DARFATA AINIE....AMEEN ALLAH AMEEN....👏🏻👏🏻_*
Page...
★6⃣★
® Mamah ke shaidawa baban farha d'in cewa akwai soyayya mai tsanani tsakanin 'ya'yansu fa..., baban ke nuna mata ai yasan hakan tun aftr 1month baya yadad'e dasanin hakan...,amma yabarsune yaga koh shi Abdl d'in zai tuntu'beshi amma tunda baiyi maganaba shi zanji daga bakinshi ya abun yake....
2days da hakan yaje har gidansu domin ganin malam dabayada lfy sosai..,yakai mashi magani tareda gaidashi...fitowarshi keda wuya suka had'u da abdl d'in...nan yake shaida mashi anjima yazo yana nemanshi...
Dare nayi kuwa abdl bai sa'ba lkchn da yabashiba...,da wuri yaje.,kohda yaje baban baya nan bai dawo masallaciba...,hakan yaxauna sunata fira da mamah da iman...farha nacikin d'akinsu kwance...
Babah yadawo yake shaidama abdl su had'u d'akinshi... Acen kuwa suka zauna shi a kujera shikuma abdl a qasa yazauna suka gaisa cikin girmamawa...,babah yafara magana kamar hakan.....
"Abdl-jabbar naji wani lbr gurin mahaifiyarku nacewa dakai da qanwar taka akwai fahimtar juna tsakaninku..toh shiyasa naga yakamata nafara ji daga bakinku shin dgsk ne koh kuma shaquwarce tayi yawa domin nasan yadda kakeson qannenka...., dgsk akwai soyayya ta aure tsakaninka da qanwarka....?"
Abdl-jabbar yad'aga kanshi yadubi baban nasu yace....
"Eh baba akwai soyayya tsakaninmu kuma inason farhane domin na mallaketa a matsayin mata idan kun yarda da hakan...'
Babah yayi murmushi domin babu abunda yakai mashi wannan zancen dad'i a rayuwarshi..,domin yana d'aya daga cikin burinshi dayaso yacika akan hakan....amma bayason ya takura kowa daga cikinsu amma tunda hakan yafaru babu komai Allah ya tabbatar da akhairi kawai.... Afili kuma yacema abdl....
" Toh abdl-jabbar Alhmdllh Allah yasa wannan shine mafarin shigarmu aljanna baki d'aya..zanji daga bakin yr uwar taka sannan zanje nayima 'ya'ya malam maganar insha allah adaidaita komai..."
"
Toh babah ngd Allah yaqara arziqi da wadata mungode..."
Yamiqe yafita yakoma pallor da murnar da batada adadi domin babu abunda yakaimashi farinciki kamar ace yau farha mallakinshice ta halak...,domin koh yaushe da ita yake barci da ita yake tashi domin idan suna tare jin yakeyi kamar yayi abunda baidaceba...saidai yana tsoron gada ya wuce guri..,yayi haquri har Allah ya mallaka mashi ita hannunshi....,bai dad'e
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 44