ita jibi, domin ni har na kira mahaifinta na fad'amashi a dakatar da auren d'azun "
"Dady........!
Dakata hisham, wallahi nima na haramta wannan auren, idan kuma kayishi bani babu kai, walkahi zan tsine maka, kuma gada ka kirani a matsayin uwarka, sai dai ka changr wata "
"Momy.......! Innalillhi wa'inna ilaihirraji'un!, momy dady kuyiman rai, kufad'aman laifin da aka aikata wanda zai haramtaman auren farha "
"Babu wani laifi, sai don tana tsohuwar matar Anwar d'angidan Alhaji naira, wanda ciwon H.I.V ya kashe da kuma wata cuta wadda koh na kusa dashi zai iya d'aukarta bale wanda ke tare dashi, hakan muka samu labari ga yan uwanka, kuma sai yanzu natuno ranar da mukaje asibiti ganinshi, farha da kukazo da ita tanayi mashi Allah ya isa, don haka aurenka anjuyashi zuwa ga jidda d'iyar k'anwar mahaifinka, jibi da ita za'a d'aura maku aure "
Nan take Hisham ya fad'i somamme a gurin, hankalin uwar itama ya tashi, suka shiga yayyafa mashi ruwa har nufashinshi ya farfad'o.
Shigar farha gida ta isko nasu alhini, na cewa iyayen Hisham sunce amaida masu kayansu sun fasa auren, saboda farha na d'auke da cutar H.I.V da tsohon mujinta keda ita.
Nan take hankalin kowa ya tashi, amma banda hankalin umma domin ita tasan komai, domin kafin Iman ta rasu tata'ba fad'ama umma cewa Farha basu ta'ba had'a gado da Anwar ba, kuma ta yarda da zancen, hakan yasa koh a jikinta, domin mahaifin farha d'in ya d'auka da gaske ne, amma umma tayi mashi bayani, sannan tace har result d'in test d'in farha d'in na hannunta, ta d'auko tabawa baban farha d'in da k'anen mahaifin Abdul-jabbar, suka duba komai lafiya.
Farha taci kuka, domin tasan auren anwar babu abunda ya tsinana mata sai danasani da take ta biyar ta har yanzu, kuma yanzu sunanta ya 'bace a gari idan auren nan ya fasu, shikenan da ita da aure har abada, hakan yasa ta kashe wayarta bayan tayima rasheeda bayanin abunda ake ciki, itama tace yanzu take jin zancen,amma gada ta damu tunda ita tasan koh wacece, Ai Allah na nan, sannan farha tace, ko da ace ta auri Hisham, sunanta ya 'bace ga danginsu da kuma gari baki d'aya, don haka har shi ta hak'ura dashi.
Dasafe umma takira baban farha da k'anen mahaifin Abdul-jabbar, suka zo, tace dama alfarma take nema akan su goya mata baya akan abunda takeson yi yanzu.
Suka aminta da hakan, amma tafad'i nuk'atar ta, umma tafara zancen kamar hakan.......
"Inason gada ad'aga ranar d'aurin Auren nan, domin inason mu nunama duniya cewa farha bata d'auke da matsalar komai, kuma wayanda muka gayyato bazasu ji haushin angayyacesu ba kuma anfasa ba, don haka nakeson A d'aura auren Abdul-jabbar da Farha, kuma don Allah gada kuk'i yadda da abunda na fad'a "
Kawun Abdul-jabbar ya yadda da wannan hukunci, amma baban farha bai yarda ba, domin yasan anshiga hak'k'in Abdul -jabbar sosai, hakan ya d'anyi musu, kuma sai ya hango wani al-amari da zasuji kunya gobe shima ya aminta.
'Karshe suka yanke hukuncin d'aurin auren gobe babu fashi, don haka a cigaba da hidimar buki.
An yanke hukuncin d'aurin auren, batare da Farha ta saniba, Haka Abdul-jabbar, wanda baya yini gidan bale yasan matsalar da ake ciki.
Ita farha taga anata hidimar buki ba'a changr komai ba, har taso ta tambaya amma kuma sai tayi shiru, amma kuma me ake nufi da hakan da ake yi, buki babu mujin aure, koh dai Iyayen Hisham sunce a cigaba da d'aurin auren?
"Toh wallahi koh sunce a cigaba ni bazanyi auren ba, nafasa, bari naje gurin umma naji"
Dasauri tafita zuwa d'akin umma.............
_Toh fa, da wata a k'asa kenan, koh ya za'a kwashe?_
_Mudai je zuwa, cakwakiya on way, auren Abdul-jabbar da farha is returned😊_
*Bee Been masoya*💞
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*_اللهم إني أعوذبك من علم لاينفع...، ومن قلب لايخشع...، ومن نفسن لاتشبع...، ومن دعوة لايستجاب لها._*
امين ياالله👏🏻👏🏻👏🏻
Page...
★5⃣5⃣★
"Umma! Me akeyi haka ne? Umma naga ba'a daina hidimar bukinnan ba har yanzi, bayan kuma kice kika fad'aman cewa, iyayen hisham sun ce bazai aure ni ba, amma naga sai shige da fice akeyi a cikin gidan, Umma wallahi nafasa auren, umma nafasa, wallahi bazan iya auren hisham ba a yanzu, domin ko da sun aminta banida komai, watarana zasuyi man gorin na ta'ba auren d'an iska kamar anwar, umma ku bar zancen aure nan na Hisham bazanyi ba nafasa "
Umma murmushi tayi, sannan ta dawo gurin da farha take zaune ta dafata, tace......
"Farha har abada bazaki k'ara kuka ba akan aure,kuma gorin wata rayuwa ya k'are akanki, sannan ko da zaki fuskanci wata matsala nasan kad'ance akan laifinki na farko, amma shima juriya nakeson kiyi kad'an a ciki, farha aurenki a yau babu fashi, domin za'a d'aurashi yau kamar yadda aka tsara abaya 1:30 na rana zaki zamo matar wani kamar yadda kika quduri niyyar yin shi a farko, bazamuji kunya ba, kuma kema bazakiji kunyar k'awayen da kika gayyato ba, farha ki cigaba da hidimar bukin ki ta yadda ya kama, sai a ynz nagane cewa auren hisham bai kamace ki ba, domin za'a raba hankalin Ikram, kuma sai yanzu na tono da sak'on Iman da tace abaki farha, ki sani a yau za'a d'aura auren ki da ke da Yayan ki, domin kawar da wani shakku a kan mutane"
"Umma yaya kuma? Wanne yayan kike fad'i haka wanda ni farha bansan dashi ba, har zaman aure zai had'amu dashi?"
"Yayanki Abban Ikram kenan, wato Abdul-jabbar "
Wani irin mik'ewa tsaye tayi, tare da dafe kai, da zuciya, hawaye suka yo mata sallama, da k'arfi ta kira sunan umma bugun zuciyarta na k'aruwa....
"Um...um..Umma! Umma kin kuwa san me kike cewa anan?"
Mik'ewa ummar tayi daga inda take, tare da jawo hannun farha d'in, ta'ajiyeta gefen gadon nata, ta dafata tace......
"K'warai farha, shi kad'ai ya dace daki aura a yanzu, kuma sai jiya nagane tun farko shi ya kamata ki aura, domin ku reni maraicin Ikram, domin za'a raba mata hankali idan ko wannenku yayi aure wani guri, don haka farha aurenki da Abdul-jabbar yau babu fashi "
"Innalillhi wa'inna Ilaihirraji'un! Umma baya sona, umma wallahi yaya Abdul baya sona ko kad'an, baya amsa gaisuwata idan nayi mashi, baya son duk wani abu da zanyi da zan zamo kusa dashi, umma baya son ganina koh kad'an, Umma ta yaya zamuyi zaman aure da shi wanda zamu sama maku kwanciyar hankali?"
"Farha duk wannan abun da yake yimaki, ya samo asaline da kalar kuskuren da kika aikata a baya wanda yazamo sanadiyar son da yake yimaki ya rage, amma bawai baya sonki ba, ina yimaki albishir da cewa, nice na haifi Abdul-jabbar, kuma ni nasan wane kalar so yayi maki a baya, wanda idan za'a lunka son da yayima iman goma, toh naki zai kai ishirin, farha Abdul-jabbar yaso Iman ne a dalilin kyautatawar da take yimashi, sannan iman na damuwa da damuwarshi, wanda bata bari wani abun ya 'bata masa rai koh kad'an, hakan yasa tayi zarrah a cikin zuciyar shi, Abdul-jabbar namiji ne wanda bayada wuyar kamu a rayuwa, Abu d'aya nakeso nasanar dake shi farha, gada ki yarda kuskurenki na baya ya sake afkuwa a wannan lokacin, domin danasanin yanzu, babu magani tare da ita, Amma ina son ki share hawayenki na tamayeki zance na k'arshe wanda idan kika amsaman zan yanke hukunci na k'arshe, kuma ki fad'aman tsakaninki da Allah cewa zaki fad'aman gaskiya har cikin ranki bazaki 'boye man ba, shin Farha kinason Abdul-jabbar, so na gaskiya a yanzu?"
Saboda tsananin firgita da tsoron tambayar umma sai da farha ta'aza kanta a cinyoyin umma tare da fashewa da kuka, Umma tayar da kan nata tayi, wanda sai da suka had'a idon da farha d'in ido da ido, da sauri farha ta d'uk'ar da kanta, nan take taji wani shauk'in ya kamata a ziciya domin sai yanzu wani sirrin ke shirin fitowa a zuciyarta, wanda umma ta nemi sanin ainahin gaskiyarta akan hakan, umma k'ara cewa tayi.........
"Farha lokaci na k'urewa, ki fad'aman inajinki "
'Duk'ar da kai tayi k'asa domin kunya tace cikin da rufe baki.......
"Umma inason yaya Abdul-jabbar tun da dad'ewa, komai nasa nayimani kyau, yana burge ni, sai dai kuma banta'ba tunanin zai aureni ba, domin nasan banida wata hanya wadda ita zata sakani da ya aure ni, hakan yasa nakawo Hisham a zuciyata domin kawar da hangen nesa na akan abunda bazai dawo gareni ba, domin nayi kuskure a baya, amma ki sani umma na dad'e da sonsa a zuciyata, sai dai ina tsoron wulak'ancin da zan fuskanta a zaman auren mu da shi,amma umma tunda kuka yanke hukuncin hakan akaina,wallahi ko da zan mutu a sanadin zama dashi, zan zauna kuma zanyi masa biyayya iya gwargwadona, umma ki tayani da addu'ar jure wulak'ancin kuskurena a gareshi"
Tunda farha tafara magana, umma ke murmushi har farha ta k'are zancenta, share mata hawayen tayi da hannunta sannan tace........
"Idan Allah yabani aron rayuwa farha kin k'are kuka har abada, ni zan zamo maki uwa wadda zakiyi al-fahari da ita, kuma idan ina rayuwa, kuma d'a zai ji maganar uwarsa, toh farha kinsamu yayanki a hannu, kisani Abdul-jabbar zai bi umurnina kamar yadda kema kika bi umurni na, don haka farha bazakiyi kuka ba har abada, sai dai nasan zaki d'anyi hak'urin wasu abubuwa a kanshi, domin shima zancen zai iskoshine kai tsaye, zuwan hakan zai iya yimaki duk wani abu na rayuwarshi, sai dai inason ki 'buye naki son kada ki yarda yasan nauyin sonki a kanshi wanda kika fad'aman domin zaki sha wuya da yawa idan yasani, burina shine ki kyautata masa iya gwargwadon halinki, nasan yanzu ke ta daban ce farha, nasan a kwalliya bazan k'araki da komai ba, ki sani kinfi iman kyau da komai na halitta a jikin macce, nasan zaki iya jawo hankalinshi da ya manta da komai, ki zama macce wayayya wadda iliminta zai fara yimata amfani a d'akin mijinta na yanzu, banida shakku a kanki farha, nasan zaki amso kambun soyayyarki da wata rahama da Allah yayi maki, Farha bazan k'araki da komai ba, domin duka nasan kin sansu, sai dai zan iya ce maki kiyi hak'uri a rayuwar ki ta zaman aure, shine k'arshen zancena dake, ban ta'ba jin ina jin farinciki a rayuwata ba kamar yanz ba, Farha Allah yayi maku albarka dukan ku, ya jik'an Iman, ya raya Ikram kuma, yanzu zan baki wayar Iman da tace a baki, nasan yanzu zatayi maki umfani akan hakan "
Gabad'aya fargabar auren Abdul-jabbar gareta kuma ta kauce, domin dama tasan dole sakamako zai biyo bayanta gurinshi, a hakan zata iya samu ta wanke zunubinta a fuskarshi, insha'allah zata d'auri niyyar zama dashi a duk yadda ya so, don haka sai taji wani bak'in ciki nata ya wanke da ga nan, harda murmushi tayi, domin zata fara d'aura aniyar koma menene a tun nan gidan nasu.
Umma wayar ta bata, sannan tace gada ta 'bata lokacinta gurin duba komai aciki, sai bayan ankaita ta natsu sannan ta fara, sannan tace taje taci gaba da hidimar ta, tare da sanar da rasheeda auren yadda ya juya, su k'arasa hidimarsu, ta amsa ta koma d'akinta tare da kuka kuka, farinciki farinciki.
★★★★★
Hisham kwana yayi yana kuka, ya nemi number Farha ya rasa, ya tura text yak'i shiga, yanason fita amma kuma babu dama domin zazza'bi ya hanashi koh motsi, gashi ance za'a d'aura aurenshi da jidda d'iyar k'anwar mahaifinshi, wallahi da ya aureta, gara ya bar k'asar baki d'aya.
Daurewa yayi ya tashi ya saka rigarshi domin zuwa gidan mahaifanshi, domin ya k'ara neman afuwar su akan hakan, tunda da sauran tym, amma yaje yayi kuka, yayi hauka basu yarda ba, sai ma cewa mahaifiyarshi tayi za'a kar'bo kayan auren da aka kai, anan hisham yace yayafe mata, wallahi baya so, domin yayi kyauta bazai kar'ba ba.
Mahaifiyarshi tace....
"Toh ita jiddar dame za'a kawota gidan naka?"
"Sai a sai mata wasu"
Ya fad'i haka domin su bar zancen.
*1:00pm*
Mutane dank'are k'ofar gidan Alhaji Aliyu Abbas, anata halartar d'aurin auren.
Abdul-jabbar na gidan basheer, domin a nufinsa shi bazaije d'aurin auren ba, basheer ya zaunar da shi yayi tayi mashi wa'azi da nasiha akan abunda yake yi bai kamata ba, domin koh ba komai yanzu farha baya kamata yana yimata hakan, tayi kuskure kuma ta gane kuskurenta, k'arshe d'iyar cikinsa, tayi mata rik'o na aminci, tun mahaifiyarta na raye, har Allah yayi mata rasuwa, amma duka itace tare da ita, yanxu wahalar da farha tasha ta ikram koh shi bazai jureta ba a matsayinsa na namiji,sannan basheer ya k'ara da cewa.....
"Abdul-jabbar, nasan irin cin mutuncin da farha tayi maka a baya, wanda koh ni danake abokinka nakanji zafin hakan, amma kuma wallahi tunda tayi nadama sai naji tana burgeni, kai nifa badon nakai sadaki da kayan aure ba a lokacin, wallahi ni zan aure Farha, kuma dole kai zaka bani ita, tunda k'anwarka ce, amma kuma sai gashi narigada na saye sameera, toh tunda har hakan ne, don Allah Abdul ka d'aure kawai mu ziyarci d'aurin auren, tare da yimasu fatar khaira ciki, kai kuma Allah ya baka macce wadda tafi Iman ko.......
" dakata malam! Banson sai'bi, tashi muje don 1:30 zasu d'aura "
"Tab! amma zamu biya ka sauya kaya koh? Domin bazan jera zuwa d'auri aure da kai ba da k'ananan kaya "
"Kai shegene wallahi, naji tashi muje "
Suka biya gidan nasu, yabi ta baya ya shiga part nashi ya d'auko wasu sababbin manyan kaya yasaka, tare da saka hula, da agogo, ya fesa turare ta koh ina, ya fito fallow d'in.
"Ka ga angon kareema abuja, kai wallahi kayi kyau sosai, bala'i! Sai kace d'aurin auren naka? Yoooo koh ango ai sai haka koh? Nasan d'an ard'o d'innan wallahi bazai kaika komai ba, fari akwaishi, zati akwaishi, k'arshe kuma k'arfaffen mamiji wanda zai iya da mata goma d'ai rana, ina zai kai ga jarumina?"
"Kai wai basheer, wane d'an iska ne kai? Mata goma na kaisu gidan uwar wa, kajiman munafuki, too ni tunda narasa iman k'arfina ya k'are akan koh wace macce, don haka wallahi ka daman da iskancinka, koh d'aurin auren ban zuwa tunda ba na k'anen ubana bane "
"Muje,Allah yabaka hak'uri aminina, amma idan mundawo akwai wani sirri fa "
Suka fita, gidan nasu cike da 'yan biki da masu hidimar zuwa ganin d'akin amarya, motoci har sai kaji mamakin ganinsu, domin kala kala, mata kala kala, a unguwar abun fa zar sha'awa.
Suna kaiwa bakin unguwar su farha, mutane chin jim a unguwar, d'aurin auren aketa halarta, parking d'in motar sukayi daga nesa sannan suka tako da k'afa zuwa gurin abokansu da suka gani anata gaisawa da farinci, tare da yimashi murna kuma, duk d'aukarsa saboda tana k'anwarsa shiyasa hakan.
*1:35pm*
Aka d'aura auren....
*FATIMA(farha) ALIYU ABBAS*
DA
*ABDUL-JABBAR IBRAHIEM.*
Ambaton sunan angon ne yasa wasu da yawa shakkun amma ai ba sunan bane a invitation card d'in da aka gayyace su, wasu suce kuskurene, wasu kuma wayanda suka san Abdul-jabbar d'in suce, "Aure ikon Allah"
Duk wannan abun da akeyi, karar lasifika d'in bata kai ga kunnen su basheer ba domin suna waje sosai, sai da wani makad'i ya buga gangarshi bayan an tofe fatiha, yace....
"ALHAMDULLIHI, AN 'DAURA AUREN, *FATIMA DA ABDUL-JABBARU"*
Anan Basheer yayi saurin kallon Abdul-jabbar, shima zaro ido yayi tare da alamar tambaya ga basheer.
"Dama sunan Angon Abdul-jabbar ne?"
"Ah Ah Hisham ard'o yake, amma ya hakan ta faru?"
"Malamin ne yayi kuskuren halshe, amma kuma ai su baba nanan ai sai su gyara mashi "
"Hmmm! Ina ganin babu kuskure fa, kaine dai Aka d'aura auren nan dakai, wai Allah yayi auren mara kwabo kenan"
"Wai basheer kai wane irin mahaukacine? Tayaya za a ayi hakan?"
Kafin ya rufe bakin nashi, mutane da yawa sukazo sunata yimashi barka da arzik'i da kuma sanya alkhairi, da sauri abdul-jabbar ya cire hular kanshi, tare da isko wani d'an uwan mahaifinshi da yazo yake tambayar sa da cewa......
"Wanne d'aurin aure ne haka akayi?"
"Aurenka ne aka d'aura yanxu, dama baka sani ba?"
Gumi ya garwaye dukkan jikinshi, tare da lank'washe hular hannunshi, makullan mota ya k'wace a hannun basheer, da sauri yayi gurin mota, kallonsa kawai ake yi, domin sun aza babu lafiya wannan saurin hakan, bashee da sauri yabi bayanshi, amma ina har ya figi mota a guje............
_Toooh koh ina zaije kuma hakan?_
_Toh Abdul-jabbar Allah ya tsare hanya._
*Bee Been masoya*💞
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*_Love is the greatest gift when given. It is the highest honor when received._*
*_I love you all💖_*
_masu zancen cewa idan k'anwa ta rasu, yayarta na iya auren mijinta?_
_Ehh, idan da ace k'anwar na raye a duniya, toh babu auren su har abada, amma da yake bata raye, Auren nasu bai zama haramun ba._
_Sai dai abunda yasa da yawa a al-ada suke ganin hakan bai dace ba, toh susani, shan nono d'aya kad'ai ya haramta aure, sai kuma idan ka auri yaya koh k'anwa, idan d'aya na raye, ba'a had'a auren su, amma idan babu d'aya duniya, toh yar uwar bata haramta gareka ba._
_Don Haka masu biyoni da tambaya prvt, su sani auren Abdul-jabbar da farha bai haramta ba._
_Bayan wannan, sauran Allah adda sani.😊_
Page...
★5⃣6⃣★
Gudu kawai yake yi na bala'i, domin yanason ya tabbatar da abunda yaji ba gaskiya bane, kuskurene.
A guje yayi parking d'in motar a k'ofar get nasu, domin bayada tym d'inda zai iya shigowa da motar ciki, saboda rud'u har baya ganin gaban shi.
Mutane dank'are gidan nasu, hakan yasa gaba d'aya duk ta inda yawuce shi ake kallo, domin ganinsa akayi hula a hannu, bayan sunsan a yanzu shine angon amma kuma sunga sauyi fuskarshi, abokan wasar shi sai gud'a suke saki daga shigowarshi, domin abun yayi masu dad'i.
Fad'awa yayi d'akin umma babu shiri, yafara kiran sunanta.....
"Umma! Umma!!
A ina kika shiga?"
Fitowa tayi daga toilet nata, alamar alwallah tayo, zatayi sallah, murmushi tayi sannan ta samu guri ta zauna, shiko ganin wanna abun ya zama gaskiya sai ya saki hular tashi k'asa tare da zaunawa kujerar bayan shi ya dafe kanshi.
Ummar zaunawa tayi gefen gadonta, sannan ta kalleshi da kyau tace.......
"Ka kirani da k'arfi nafito, kuma kayi shiru har da rik'e kai, koh duk hidimar ce ta kawo hakan?"
'Dago fuskar tashi yayi da sauri yace.....
"Umma, ai dole na rud'e, umma dole na dafa kaina domin har yanzu ban dawo a mafalkin da nake burin ace ya zama k'arya ba, domin banason tabbacin gaskiyarshi, Umma su baba, da baban gombe, sun samu matsala gurin d'aura auren nan, sunana kawai aketa kira sa'banin sunan mujin amaryar, sannan na tambayi baba k'arami na gombe,yace man wai nine aka d'aura dani, Umma ki fad'aman gaskiya, dama ana yima maza auren dole?"
"Eh idan takama dole ayi masu shi, domin gada su halaka, sannan zancen aurenka da farha, babu zancen rud'ewa, domin nima da sanina, hasali ma nice nan na yarda da hakan, domin farha ita ta cancanci ka aura, tunda ita yar uwarka ce, kuma ita naga dacewar zamanku, koh don Ikram"
"Um.....Um...mah! Umma don Allah kuyiman rai, Umma inada wadda zan kawo koh gobe kike so a d'aura auren mu wallahi na aminta, idan kuma batayi maki ba, na yarda a d'aura aurena da duk wadda kikeso, amma ba farha ba, Umma bazan iya zama da ita a matsayin mata ba, domin bazan iya yimata adalci ba, Umma wallahi bana son farha yanzu kwata-kwata "
"Idan kuwa baka son farha, toh nima mahaifiyarka bana sonka, kuma kadaina d'aukata a matsayin uwa "
"Ummmah! Innalillhi wa'inna ilaihirraji'un! Umma ni d'anki ne wanda bai ta'ba sa'ba maki ba, idan da abunda zai sa'ba maki gudun sa yakeyi, amma a yau ni kike kira da ba d'anki ba, akan wata,wadda batason d'an naki a farko? Umma kisani fa, banine nasaka ma zuciyata tsanar farha ba, itace da bakinta da mugun halinta ya siyo wannan, sannan yanzu Umma shi wanda aka hana mashi aurenta ai ba a kyauta ba a matsayin ku na manya, za'aga rashin girman ku a nan ai "
"Waya fad'amaka hakan? Ai sune suka k'i auren nata, saboda wani dalili nasu na rashin tabbatar da gaskiya, toh hakan ma da yafaru Alhmdllh, domin ni naji dad'in hakan, kuma sai yanzu natuno da alk'awalin da na d'aukarwa iman, kuma a yau na cikashi, don haka banason jayayya zancen ya tsaya nan, batun ta'batamaka rai a farko, yanxu kuma ta gyara, domin farha na sonka a yanzu, sai dai itama ta girgiza da jin d'aurin auren naku, idan kaima irin kuskuren da tayi baya zaka aikata? Toh ga fili ga mai doki, domin ita nata iyayen shareta kawai sukayi a rayuwa, kai kuma wallahi babu ni babu kai a kan zaman auren ka da farha, kasani a yanzu inason farha so na hak'ik'a, akwai abunda ubangiji ya hango a gareni na rashin 'ya mace ya d'auke mahaifiyarta ya bar mani ita a hannuna, a yanzu zan iya rabuwa da kai, amma ban rabu da farha ba, domin ita amanace a gareni, kaga zancen wata tak'i d'ana bata taso ba, domin itace d'iyar tawa, daga k'arshe inason kasani a sabon gidan da ka gina, acen za'a ajiye farha, kuma kaga ikram hankalinta bazai rabu guri biyu ba, domin na farko, bazaka rabata da farha ba koh da a wani gurin tayi aure, yanzu kuwa kaga shikenan 'yarka ta dawo gida, daga k'arshe nake cewa Allah yabaku zuri'a d'ayyaba, kuma wallahi daga d'akinnan gada na k'ara jin wani zance a bakinka kawuce cen sabon gidan, abun da babu idan aka d'auko kayan ta daga gidan hisham sai ak'ara saka mata"
"Hmmmm him...!"
Shi kad'ai Abdul-jabbar yaja yamik'e ya fita d'akin, zai fita kenan sai ga farha zata shigo, a gefen corridor d'in da ke had'a d'akin umma da waje, karo sukaci da juna harda jikinsu sai da ya daki juna, shi tunanin duniya ya hanashi ganinta har sukaci karo, ita kuma waya takeyi dat is why bata ganshi ba.
Gane wanda sukayi karo, sai hankalinta ya tashi, shi kuma hannunshi yasaka biyu ya tureta har tana kusan fad'uwa, sanna ya kalleta yace.....
"Ki sani ansaya maki wahala, domin bana d'aya daga cikin masu sonki, farha bana sonki koh kad'an!kuma kisaka a ranki, babu ranar, idan kina murna da aure nah da zakiyi? Toh ki daina ki fara hawaye,kuma kishirya kuka, azaba domin babu wani d'igo na sonki a rayuwata, banza wawiyya ragin ciwo ragin maza, zan zauna dake nima a garkuwa kawai, amma gada kiyi tunanen cewa a wata manufa, domin nasan abunda ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 44