Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kaxo, ga result naku, kuma wannan abun datakeyi ba wata mtsl bace zata daina nan gaba kad'an idan tasamu qwarin jikinta, baqon ne naku yaxo da wahalar da maman nashi sai haquri kawai amma wannan bayada magani sai randa stage d'in dainashi yazo, kuma nace gada abata ruwa sai nazo sbd nasan idan tasha hakan zai faru, a dinga bata ruwan da lemon tsami aciki, idan za'a bata ruwan ad'an matsa lemon tsami kad'an ciki domin kawar da gard'in ruwan hakan zaisa aman yarage, amma babu komai akwai wayanda sukafita wahala sosai, ita somewa kawai tayi, wasu idan suka fara hakan bazasu samu sauqiba har sai sun haihu, Toh ALLAH ya inganta yabada mai albarka " Wani farin ciki ya cika cikin jabbar, wanda banda jikinshi babu kyau daya rungume likitan, amma koh ynx alhmdllh. Duban doctor d'in yayi tareda murmushi ya bud'e result d'in yafara dubawa yayi murmushi yace... "Alhmdllh, Alhmdllh,doctor nagodema Allah dajin wannan result da ganinshi,amma doctor babu wani abu daza'ayi gameda mtslr wannan data keyi? Duba yadda take wahala " Murmushi likitan yayi sannan yace... "Ba wata mtsl,domin zata daina a hankali,kuma anyimata allurorin range aman,ynx qarfin jiki kawai yarage zuwa anjima sai kuwuce gida, sai dai kaima fa ynx sai ka rage yawan ziyara domin kaga baiyyi qwariba za'a iya samun mtsl a yawan takurashi, sbd gaga 3weeks ne da kwanakki sama baiyyi qwariba " Murmushi jabbar yayi tareda godiya, kuma yacire 10k aljunshi yace don Allah yasaka recharge yagode da kulawa. Fitar doctor d'inne, jabbar yakoma gurin iman tareda d'agota jikinshi yace... "My everything mun girma, nauyin jarumtarmu da soyayyar mu ta haifar muna dasamun baby,ina cen nadamu naji menene damuwarki ashe ajiyata ce ke wahalar dake, iman bansan wanne irin farin ciki nake cikiba a ynx, ni na yarda cewa ni mai sa'a ne a duniya, baby nah zai iso lkchn da nake cikin wadata ta, ina murnar qara girma gurin aiki,sai ga murnar qaruwar da nahaifar muna sanadiyar soyayyar damuka gina dashi. Iman jinsa kawai takeyi, domin ita abunda yadameta ya isheta, bacika gane me yake fad'iba takeyi,dubansa tayi da alamar tambaya ta bud'e baki dakyar tace.... " waye ya haihu kake kiran kun samu baby?" "Ban haihuba, amma nakusa haihuwar,domin iman nad'auke da baby nah a cikinta wanda ni nabada ajiyarshi kafin natafi, ynx kuma sai gashi shine yadawo dani domin yace nazo yana wahalar da momyn shi, qarshe dai iman kina d'auke da cikin baby nah natsawon 1month ynx hakan shine silar ciwonki " Wani yunquri tayi, zata tashi da sauri ya riqeta tareda rungumeta,hawaye tafarayi tace... "Toh ynx yaushe zanji sauqi?" "Ance sai yafara qwari nanda yakai 4month koh 3month, komai zai koma normal " Matseshi tayi sannan tatura kanta qirjinshi tace... "Nidai wlhy vazan iyaba,mutuwa zanyi 3days dubi yadda nakoma kuma ni kad'ai nasan menakeji jikina, sannan ace sai nayi 4month zan daina amai? Nidai gsky acire babyn kawai nasamu sauqi wlhy wahala bazan iyaba" "Haba, haba iman, dabakinki kike cewa bakiso acire? Kituna sakamakon k'aunar mune yafito, kuma ai kowa haka yayyi koh? Wannan babyn shine gudan jininmu wanda muke fatar samu koh yaushe mai albarka, insha'allah komai zai zamo normal nan gaba kad'an" Kallonsa kawai tayi,domin bazai gane me takeji bane shiyassa,hakan takan yasa bata cemashi komaiba sai hawaye dake fita idonta,shikuma yana goge mata da hannunshi, yana shafa bayanta. Dai2 nan su umma suka shigo baki d'ayansu har da farha, wadda ta tsaya daga bakin qofa, Iman qowarin tashi takeyi jikinshi amma ya hanata domin ya riqemata hannu yana matsawa ta gefe, mama dubansu kawai tayi, sai tayi murmushi, itakuma umma cewa tayi... "Kai kuma yaushe kadawo? Toh ka saketa mana mutane sunzo ganinta, kabi ka wani daddafeta hakan tanaji da kanta " Qala baice mataba, domin dama yasan umma zatayi hakan, mutun da matarshi a takurashi ta'bata bayan kuma batada lfy, Runtse idonta iman tayi domin iya kunya tajita anganta saman k'afafunshi, bai jayeta jikinshiba saida yaji sallamar babansu iman d'in sannan ya yi dubarar jawo pillow ya ajeta sannan ya tashi yana shafar kai. Gefe yakoma yatsaya, tareda takardar result d'in hannunshi, baba mamakin ganinshi yaka mashi domin yace gada yazo amma sai da yazo, duqawa yayi yagayar dasu baki d'ayan su, sannan jabbar ya miqama baba result d'in yakoma gefe. Farha nace gefe, domin motsin arziqi ma batayi, domin bata mance da haukar da jabbar yakira mataba,bada dad'ewa ba, hakan yasata ciro wayarta tana duba wani abu ciki, duka iyayen basu damu da yanayin da farha d'in ke cikiba domin ynx sunsan shiru aikinta ne, inba ace itaba bazata tamka mutunba. Baba yayi hamdala, sannan yafad'amasu cewa "iman nad'auke da juna biyune" wanda kowa saida yayi murnar jin hakan, iman najinsu amma takasa cewa komai. Farha kuma hawaye nat biyo tacikin idonta wanda bakowa xai gansuba sbd hijab da yakare fuskar tata baki d'aya, kukan xuci takeyi wanda ita kad'ai tasan me take cewa, dubi yadda kowa ke farinciki domin samun jika, da ynx itace hakan yafaru da ita, amma gashi kowa ta iman yakeyi. Ana haka dukansu suka fita domin bawa iman guri tasamu barci, sai akace amma farha ta tsaya gudun gada abarta ita kad'ai, jin hakan jabbar shima jabbar yaqi fita,domin yayi niyyar fita ya changer kaya, amma dagajin ance farha taxauna da iman sai yaqi tafiya, hakan yakoma gefen gadon yazauna, anan yafara kiran abokanshi yana sanar dasu dad'i bisa dad'i, ga aiki ga baby dakuma wadda yafi qauna aduniyya Allah yabasu babyn. Duka fa da gangan jabbar keyi domin yaga farha zaune,harda kiran basheer yayi yace... "Aboki kaga ikon Allah koh? Gashi gaba kawai nakeyi, ga aiki babba kuma ga baby nasamu da k'wailata takawo mana baby, kasan aduniya babu abunda nafi k'auna kamar iman da abunda ke cikinta, idan kacire umma dake uwa, don haka dole naje da matata abuja don samun kulawa " Duk wannan zancen dayake zubama basheer martani ne yake maidawa farha, kamar kuma yasan cewa abun ya hau sosai, domin farha tasan da ita yake, hakan yasata fasa kuka mai qarfi wanda saida iman tatashi daga barcin datakeyi. Dasauri ya daka mata tsawa yace.... "Ah ah don Allah yi waje gada kisa muyi hassarar ribar damuka samu, ba k'aunar uban babyn kikeyiba zaki iya illata babynshi, gada kitayar mata da hankali nashiga wani yanayi " Aguje farha tayi waje tana kuka, iman ta riqe hannunshi tareda zubar da hawayenshi tace... "Hakane yafitar dakakira kayi domin ni? Kasani 'batawa yaya farha kamar ka 'bataman rayuwane, kyautata mata kamar ka kyauta taman ne, yaya jabbar yadda kake d'aukar yaya farha ada a ynx ba haka takeba, duk da bansan a wanne hali nazo assibitiba amma tunda na falka nake ganin kukan yaya farha akan ciwon dake damuna, bata barci bata cin abinci duk sbd sanadin ciwon dakake iqirarin soyayyar dakake yiman ne ya haddasa samunshi, toh kasani farha yr uwatace uwa d'aya uba d'aya wadda ita kad'aice gudan jinin damuka fito ciki guda, yaya jabbar inasonka sonda bansan adadin shiba, kuma kasan bazan iya rayuwa babu kaiba, saidai zan iya za'bar ganin mutuwata akan abunda kakeyima yaya farha" Miqewa tayi da alamar fita taje gurin farha d'in, duk da juwar da ke d'ibarta amma zataje gurinta tadawo da ita ciki,kuka takeyi mai tsanani wanda hakan yasa hankalin jabbar tashi sosai. Hanata tashi yayi tareda rungumeta yace........ *Bee Been masoya*💞 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH😭😭* 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 ©® Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* 💋💋💋💋💋 ★TRUE LYF STORY★ ★★★★★★★★★ Page... ★4⃣1⃣★ ® mayar da ita yayi kwance, sannan shima ya bita kwance yayi mata rumfa da jikinshi yace.... "Iman ina zakije?" Shiru tayi tana kallon sa, idonta na zubar da hawaye sosai, domin taji zafin tsawar da yayima farha,hakan yasata juyar da idonta gefe tace.... "My honesty, dama baka yafewa yaya farha ba,ka 'boye man kace kayafeta har abada?" "Ah ah haskenah, wlhy na yafeta, amma kinsan maida martani akaina gsky ne a rayuwata akan farha koh? Domin irin wannan lkchn shine lkchn da yakamata nafara bata amsar tambayoyinta akaina, farha taceman matsiyaci, yau gani cikin wadata, farha taceman batasona, yau gani jikin mai sona, Iman idan ban fad'amata tajiba, yaushe zata san cewa ni jabbar nafi qarfin ajinta ynx? Nayafe abunda tayiman, kamar ciwon da yakamani domin ta, amma mayar da amsar ne ban yafeba dole na fad'a mata ita " "Yaya jabbar! Yaya farha tagane laifinta, tagane kuskurenta na farko, kuma ta nemi afuwan akan laifinta, don Allah kamanta komai da yafaru tunda har kasamu madadin hakan a guna, idan kanason babyn dakake murnarsa samunsa yazo lfy, toh kasama man kwanciyar hankali anan, domin shine cikon samun natsuwata bayan kai" Murmushi yayi tareda kai bakinshi cikin nata ya datse, yasaka hannunshi cikin nata ya matse,sannan yad'ago yakai halshenshi fuskarta ya lashe hawayen da keda saura, sannan yakoma bakinta yad'an samu relief kad'an, sai yaji duk 'bacin ranshi kuma yatafi yadubeta a cikin lumshe idonshi yafara kiran sunanta a natse yace... "Khadijah, wannan kad'ai ya'bata maki rai? Toh kiyi haquri,zan kwatanta mantawa, amma kinsan abune mai wuyar mantawa koh? Toh duk da hakan zan kwatanta yin nesa da farha, domin ganinta kad'ai nasakani jin tsanarta, amma idan bana ganinta may b na mance, kiyiman lamuni iman, kinsan banda nake mai imani da yawa da a lokacin nakashe kaina, amma duka na haqure,sbd tsananin azabar data sakani ciki,amma ynx insha'allah komai zai wuce, idan nasamu baby nah a hannu, amma kiyiman murmushi nagani, inason naje na changr kaya, me kikeso nazo maki dashi?" Murmushin tayi, sannan tace... "Ni banason komai,amma agwaluma nakeso kawai kasiyoman " "Tafd'i! Menene agwaluma kuma? Kuma ina xan sameta?" "Oho nidai tambayata kayi, nabaka amsar buqatata" Dariya yayi tareda d'an shafa cikin nata a hankali har zuwa qirjinta ya matsa kad'an kuma bai sauke hannunba saida yace... "Nayi missing naku,sannan ga dear baby yanason takura mu,amma babu komai zamu dinga ganawa kad'an kad'an " Riqemashi hannu tayi tareda ya mutsa fuska tace.... "A assibiti muke fa, sannan kowa zai iya shigowa,plx barci nakeji,kuma kaina ciwo " "Sorry zan tafi, amma ba don mutaneba,domin bana tsoron kowa akan matata,sai dai don tayi barci" Iman murmushi kawai tayi, itafa kad'ai tasan me take ji, daurewa kawai takeyi koh magana bata so sosai,sbd shine take amsawa. Miqewa yayi tareda riqe hannun nata yace... "Zan tafi, anjima xan dawo maki da abunda kikeso" Iman murmushi tayi, har yabar d'akin baki d'aya,sannan tajuya don gyara kwanciyarta, nishad'in son mijinta har qarshen zuciyarta.................. _Afuwan banajin dad'i,mutane sun daman koh kad'an ne toh gashi arage fira_ *Bee Been masoya*💞 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH😭😭* 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 ©® Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* 💋💋💋💋💋 ★TRUE LYF STORY★ ★★★★★★★★★ 🌿 *WASU MATAN*🌿 (a wannan zamanin) NA *~RUKEY HAROUN~* *_masha'allah mmn nour, ina ta yaki murnanr k'arasa buk naki, ALLAH yaqara d'auka ka da zaqin hannu, ALLAH yaba da ikon sambad'o mana wani,ya kuma sauke ki lfy._*👏🏻 Page... ★4⃣3⃣★ ® Da sauri jabbar ya jawo rigar shi yasaka tare da, qara jawota jikin shi, duk ya rud'e sosai. "Iman fad'aman me yasa mu cikin naji?" Cen iman ta qara riqe cikin cikin kuka tace... "Marata zata 'balle, wani zafi take yiman, ciwo wlhy " "Subhanall! Iman nine koh? Wayyo nabani, idan cikin nan yasa mu mtsl bazan ta'ba yafuwar kaina ba, nara sa hankali na ne wlhy, ban san inda kai na yaje ba, ina son na k'yaleki amma na kasa, dana tuno halin da kike ciki sai kuma na manta, Ina zuwa kad'an " Da sauri ya fita don zuwa fallow d'auko wayar shi, doctor habib ya kira, nan take ya d'auka tare da cewa.... "Engineer har ka iso kenan?" "Eh doctor, akwai mtsl fa! Don Allah kana assibiti koh gida?" "Ah ah nata shi aiki, gani gaban madam, wani abu ne?" "Eh doctor marar iman ke ciwo, plz ina zan sameka?" "Ok ba mtsl, kujirani kad'an gani zuwa, amma tambayar ta jini bai fara zuba ba koh?" Yajuya yafara tambayar ta, kai kawai ta d'aga mashi alamar babu komai. "Eh tace babu komai, na jira anan koh?" "Eh gani zuwa" Kashe wayar jabbar yayi tare da jefar da wayar gefe, ya jawo doguwar riga ya saka ma iman, ya zauna gefen ta tare da kwanto da kanta k'afafun shi, sai sannu yake yimata, tare da shafa marar a hankali. Jin isowar mota harabar gidan nasu, yasa jabbar saka ma iman hijab tare da d'aukar ta domin bazata iya tafiya ba, yakaita kujerar ya kwanta sai wani lumshe idon bala'i take yi, bud'e qofar yayi doctor d'in yashigo, sannan ya fara yimashi bayanin abunda ya faru. Nan take likitan ya gano mtsl da takawo hakan, allura yayi mata ba don ta so ba,sannan yace a kwantar da ita zai daina ynx nan, suka fita tare, anan yake bashi shawarar yadaina da muwar cikin cen, domin har ynx bai yi qwarin da za'ayi mashi bankar da yake yimashi ba, domin daga kalar wancen ciwon marar sai jini ya 'balle mata , daga nan sai cikin ya fad'o. Sukayi sallama, jabbar ya gode Allah da hakan bata faru ba, kuma insha'allah zai jure har xuwa lkchn da cikin zai girma, duk da wata barazanace a rayuwar shi, bale yau da ya d'an d'ana yadda ni'imar mai ciki take,amma zai daure. Komawa yayi ciki, yayi mata sannu, domin abun ya lafa, d'aukar ta yayi, sai toilet domin tsalkake jikin su, izuwa yin sallar magariba,anan yace ta kwanta yana zuwa, tea ya had'o mata tare da tayar da ita yabata a baki sannan yace ta kwanta, shikuma yafita don saita fallow d'in da kuma cin abinci, sannan ya zauna yin wani aiki nashi. ★★★★ Ahaka rayuwar tayi ta tafiya, idan jabbar baya gari, iman na gidan umma, duka kulawar ta ta rataya hannun farha, duk da pant farha ke wanke ma iman, sbd cikin ynx ya girma ba ko mai take iya waba. Acikin wannan lokacin ne farha ta nemi da a taimaka abarta takoma makaranta domin zaman ba wani umfani zai yimata ba, ga rasheeda har tafara aiki. A hakan sai iyayen suka ga dacewar yin hakan, mahaifinta shi yayi mata komai, sai dai Nursing school tashiga domin tun farko under healt ta fara karantawa a university d'in su,hakan ya sanya ta koma mkrnt tare da kulawa. kafin tafita zuwa mkrnta sai ta tabbata iman bata buk'atar komai sannan zata fita, wannan kulawar kawai da takeyi ma iman yasa iyayen ynx suka fara k'aunarta ba kamar umma ita dake tare da su tana ganin halayen kowannensu. iya ynx tasan cewa jabbar koh kallon banxa farha bata isheshi ba, hakan yasa ummar bata tsaurara mashi ba domin tasan cewa ynx farha ba zama take yi ba, shima kuma baya koh gari sai in ya shigo. Farha na tafiyar da karatun ta yadda ya kamata, tunda farha ta fara zuwa makaranta koh yaushe cikin shiga ta alfarma wadda hijab take sakawa har k'asa, tare da niqab a fuskarta, tun da take zuwa school d'in ba ruwanta da kowa koh yaushe ita kad'ai take zaune tana karatunta, duk gefen da tasan zata had'u da maza tana kare kanta domin ta had'u da izina babba rayuwarta, hakan yasa ta qudurin kare kanta da kowa ma, suma mutanen sai suka d'auka koh matar aure ce, shiya sa basa gigin yimata magana. Hakan yayi mata dad'i domin burinta kenan a rayuwar ta. Kamar kullum yadda take zuwa makaranta haka tashirya yau ma ta shirya zuwa school d'in bayan ta gyara komai da komai da tasan iman zata nema idan bata nan. Fitowarta kenan d'akin umma don shaida mata tafiyar ta, tayi mata addu'a da nasiha a kan karatu gada a tsaya wasa, farha ta amsa da godiyar nasiha, kuma tayi alqawalin kare kanta da komai, sannan ta fita. Farha tazo murd'a qofar fita, sai taji an rigata bud'ewa, tsayawa tayi tare da jiran mai shigowa, d'ago fuskarta da zata yi, sai suka had'a ido da jabbar zai shigo, da sauri tayi baya domin gudun gada ya mangajeta ta fad'i. Shi mamaki ma abun yabashi, sbd ganin shigar tata da tayi kamar ta Allah, inji shi a xuciyar shi, shigowa yayi ba tare da ya kalleta ba tun dubi na farko, sai cewa yayi tare da wucewa..... "Allah yasa shigar ta Allah ce, ba ta 'boyon kurwa ba in an fita " Farha k'ala bata ce mashi ba, domin tasan manufar shi,kuma Allah shine mafi sanin rayuwarta ynx, wucewar ta tayi batare da ta damu da mtslr shi ba. Shigar shi fallown tsit babu kowa ciki yasa jabbar gane suna ciki ne dukan su, ajiye jikkar shi yayi saman kujerar fallown, da sauri ya fad'a d'akin umma d'in tare da sallama, ganin shi sai yabama umma mamaki domin baiyyi 2 weeks da komawa ba , hakan yasa ta amsa sallamar shi tare da tambayar sa lfy hakan? Jabbar murmushi yayi tare da cewa.... "Umma lfy qlau, kuma hutu na samu na 3weeks wanda nake fatar kafin na koma Allah ya sauki iman lfy, ynx haka yau nake son fara sayayyar haihuwar tata, na baby kuma zanyi bucking duk abun da aka samu daga baya za'a cika, daga yau zuwa gobe umma duk abun da yaka mata ayi sai a sanar dani " "Toh alhmdllh, amma sati ukku basu yi yawa ba? Tun da naga ai da saura haihuwar, idan kuma ka tsaya tym d'in ba'a haihuba ai hutu naka zai qare koh?" "Insha'allah, umma iman bazata wuce 2weeks ba,kamar yadda Doctor habib ya fad'aman, kuma idan ina cen hankalina koh yaushe yana nan, umma wlhy koh yaushe bana samun barci sbd tunanin yadda nake ganin iman hakan kesa duk tym d'in da na tuno yadda tayi kumburi sai naji kamar na amsar mata ta huta " "Abbanah kenan, Koh wacce macce ai sai ta wahala kafin takai ga nata d'an, ka koh ga addu'a kawai zaka dinga yima iman, ka daina tayar da hankalinka, d'iya kuke so kuma dole sai kun wahala, ALLAH dai ya rabasu lfy " "Ameen umma" ya ajiye kudd'i masu yawa gaban ta, sannan ya miqe zuwa d'akin da iman take. Shigar shi ya tarar tana barci, ta wani cika sosai, ga k'afafunta duk sun kunbure, fuskarta kawai zaka gani kagane iman ce, domin cikin gaba d'aya a jikinta yake, ynx kuma gaba d'aya yafito. Sanye take da doguwar riga, ta shinfid'e cikin nata, sai barci sukeyi, Alamar akwai sauqi a jikin nata sai dai sbd nauyin cikin yasa iman komai bata iyawa. Duk'awa yayi dai2 inda kanta yake, tare da shafa cikin nata, yakai bakin shi a la'b'ban ta ya tsotsa sannan ya d'ago ya kalleta ya qara shafa cikin nata, sannan yace.... "My lovely baby, kana wahalar da momy, gashi ka changr kamanni momyn ka, gashi kasaka dadyn ka acikin maraici mara misaltuwa, rabonshi da yaji lfyr ku har ya manta, gashi da yr banzar qishirwa mai yawa, wadda maganinta sai momynka amma kuma ka hanamu sakewa koh? Toh Allah ya kawo ka lfy, idan.kafito dady zai yimaka bulala biyar sbd ka ta kura shi, ka takura momyn ka" Iman cikin barci take jin wani sauti, wanda ta d'auke shi a mafalki mai dad'i, hakan yasa bata so bud'e idon ta ba, domin gada ya 'bace mata. Jin hannu a saman k'irjinta ya sa tad'an motsa kad'an kuma sai tafasa, jin anqara riqa nonon nata d'aya cikin sigar da tasan wanda ke yi mata hakan yasata bud'e ido da sauri. Ido hud'u suka yi da juna,iman ta qarasa bud'e idon nata don qara tabbatar da abun da take gani, lallai ba mafarkin da tasaba yi bane shi dai ne jabbar d'inta, miqewa take son yi amma yakasa barin ta sai kallon ta yake yi cikin sigar tausayi, sannan ya yi mata murmushi, itama ta mayar masa tare da riqe hannun shi d'aya, qarasa hawa gadon yayi tare da riqata ta tashi zaune a hankali ya rungumo ta jikin shi, ita kuma ta'aza kanta qirjin shi, sannan yace... "Momy baby, kin ganni a bazata koh? Wlhy barci bana iya wa sosai sbd ganin halin da na barki, hakan yasa na dage akan nasamu hutu nazo na kula dake na wani lkch kad'an, wanda nake fatar Allah ya sauke ki kafin cikar lkchn iman " "Ameen yayanah kuma mujina, k'arshe uban 'ya'yanah, kai kenan kadamu bare ni da nasan me nake ji,gashi na takura kuma na ta kura wasu, domin duka wahala ta yaya farha ke yin ta, duk da wanka ita ke riqaman, ai koh kaga babyn ka ya wahalar damu da yawa kuma ya takura mu daga ciki har da kai ma" "Hmmmm! bazan ce komai ba, domin abu nane, sai dai wlhy serious na yi missing naki, kuma ynx na dawo insha'allah duka wahalar ki ta dawo hannu nah, bana burin wani yaqara saka hannun shi ciki, ni na siyo abuna kuma ni zan tallafi abu na, ke da ace wannan cikin ya dawo guri nah da wlhy nayi farin ciki, domin nasan xaki samu sauqi, jinakeyi kamar na d'auke miki shi iman " "Allah dai ya raba mu lfy, idan na haihu ni bazan qara yin wata ba, d'ayan ya isheni wlhy, da nasan haka ake ji a d'aukar ciki da ban yi........" "Da baki yi me ba?" "Ba komai ya wuce ynx, mu had'u next d'ai koh?" Yaga ne me take nufi, kuma ya tausaya mata sosai, domin da ganin yadda yanayin jikin iman yake kasan cewa tana qoqari sosai, akwai wahala, hakan yasa ya langa'be kansa tare da marairaice mata alamar gada suyi hakan fa, tace bazata qara yadda ba, bayan tasan a tafkin qoramar ni'imar ta ya dogara ynx, murmushi iman tayi tare da kashe idon ta d'aya, ta langa'be kan itama, sannan ta nuna mashi cikin nata da yatsa alamar akwai wuya kawo wanin shi. Jabbar ya matso jikin ta sosai, tare da jawo wayar shi aljihu ya fara basu selfi, iman na kaucewa amma ina sai turo bakin shi yake yi a nata yana sakin plash tako wace siga, hakan yasa iman riqe mashi hannu tace... "Menene haka plz? Ka duba yadda nake, amma kake ta d'au kata a munin ciki, haba dear idan ka'ajiyeshi yayi maka menene?" "Kika sani koh idan na dinga ganin shi, idan kin haihu na dinga safsauta maki gurin zuqar ni'ima ta, domin danaga yadda kikayi farko, ana biyu sai na dinga d'aga k'afa, toh wannan pic d'in da kika gani, zan ajiye ma d'an love d'in mu, koh 'yar love d'in mu ta gani, momy da dady sun zuba soyayya kafin su kawo mu duniya, kinga wannan ai tarihine babba, kuma insha'allah zasu gan shi, domin mu yaran mu 'yan soyayya zamu ta kawo wa duniya " "Allah ya kawo su lfy, amma ni zan dinga hutawa amma, don planing zaka kaini na 5yrs ayi man " "Haba sweet, ai tsarin iyali ba'a gida naba,domin su nakeso, bakiga ni nikad'ai bane? Toh zan kawo dozen insha'allah da iman kuma " Murmushi sukayi, ya ajiye wayar shi tare da yin setting d'in video camera fuskar su ya ajiye, kamo kan iman yayi yasaka bakin shi a nata, yafara kissing nata halshen shi qasan nata, itama nata saman nashi, hakan kawai ya sauya kamannin jabbar, amma kuma bai zure ba domin baya son ya kawo mtsla rayuwar su, domin yasan iman a halin ynx burinta bai fi ta haihu ba. Hakan ya d'an mammatse ta sbd ya rage zafi, shaf jabbar ya manta da gidan da yake ba gidan su bane, bai gano hakan ba sai da ya buge wayar shi daqafa har ta fad'i sannan ya ankaro, sakin iman yayi domin gudun gada umma tashi go ta kamashi, bayan yasan halin da take ciki, hakan yasa ya saita kanshi domin samun natsuwar shi. Jabbar yafi 3 hours d'akin nan, domin umma bata ta'ba tsammanin yana gidan ba, domin babu alamar motsi. Farha ta dawo school domin dama text kawai nakkaita, kuma anqarasa bata tsaya yin komai ba tadawo gida, direct d'akin su ta nufa, domin fitsari ya koro ta, ba arziqi ta fad'o d'akin,ganin jabbar tayi zaune iman rabin jikinta a jikin shi,yana matsa mata koh ina nata domin kun burin da tayi takejin koh ina nata ya tauye, shiyasa yace ta bari yayi mata, ba musu ta yar da har wani runtse ido take yi sbd dad'in tausar, hakan yasa yana tausa yana rad'a mata

Chapter 20 of 44