Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ma Allah, domin anyi mashi sakayya da wata irinta, jini guda, kuma rayuwa guda. Cen sai yayi nishi mai sanyi tare da farin cikin da ya mamaye mashi zuciya, ya azo hannuwanshi duka biyu ya rungumota daga k'irjinta, domin bayason ya matse cikin nata, ya takura babynshi, domin yanzu hakan da ya shafa cikin yaji alamar cikin ya fara fitowa daga k'asan mararta, domin tayi tuli kad'an. Hakan yasa bai yadda ya matse cikin ba, sai dai k'irjinta da ya cika shima, sai suka k'ara yimashi dad'i aza hannun nashi, sannan ya saita muryarshi yace...... "Farin ciki! Tabbas yanzu na yarda ciki ne da ke, amma me ya sa baki fad'aman tun da wuri ba nayi celebration d'ina ba, sai yanzu?" Farha matsar k'irjin yayi mata yawa, hakan yasa ta yamutsa fuska, tunda tasan ba ganinta zai yi ba tace... "Allah dear da zafi fa, gashi ni bansan me ya sa suke yiman ciwo haka ba yanzu, amma nasan, wannan ajiyar taka mai wuya, ita ke kawo wannan zafin, gashi jiyama wahalar da nasha bansan me zance ba ma akai, sannan nima yau d'innan nasan da wannan ajiyar, domin bansan da ita jikina ba, saboda bana wahalar komai, sai wannan abun da kake yi kullum " K'ara matsarta yayi, wanda sai da tayi k'ara sosai, saboda k'eta yayi mata mai yawa gurin, wadda sai da ta wulk'ita da sauri zuwa gadon. Da sauri Abdul-jabbar ya bud'e idonshi tare da rik'eta, kada tayi k'asa ta sashi yayi hasarar abun da ya dad'e yana nema. Farha dariya tayi sannan ta koma jikin nashi da kashedin cewa kada ya k'ara yimata k'eta.ya amince da hakan, sannan ta yarda ta natsu. Tambayarta yayi "how many month yanzu ga babyn? Saboda naga kamar kin dad'e a yanayin da kike, kuma sai yanzu nake tuno long time da kika d'auka bakiyi period ba, wata nawa suka ce, baby na zai iso?" "Baka duba result d'in ba?" Ga ki, me zan yi da takarda?" Inji Abdul-jabbar. Hannu farha ta d'aga mashi da cewa... "Hud'u da sati biyu, yana nufin wata biyar babu sati biyu " "Haba dear! Wannan wane kalar lissafi ne hakan? Duk don ki ja mani rai ne ko?" "Sorry sweetheart! 5month ne, result yace " "Alhmdllh! Na ma rasa me zanyi anan, bayan gode ma Allah da nayi, wajibi na k'ara da raka'a biyu ta godiya ga Allah, sannan na samu dogaron wannan farin cikin anan " Juyo da farha yayi, tare da jawo da filon da yake kai ya aza farha a saman filon, sannan ya zame k'aramin gyalen da ta d'aura akan nata, ya zuba ma gashin kanta ido, sannan yakai hannunshi tsakiyar gashin nata. Duk da hakan bai ji godiyar ta isa ba, sai da ya matsa da bakinshi a nata, yafara kissing nata. Nantake zance ya chanja tunda hannunshi yakai ga zip d'in rigarta, domin zipping na rigar yayi tare da saka hannunshi ciki yana wasa da dukiyar da suka rena tare. Nantake ko wannensu ya shiga faranta ran d'an uwanshi, ba tare da babban al-amarin ya shigo ciki ba, amma sunsha soyayya a gadon aurensu ta murnar samun d'an jinjirin cikin love d'insu. Kukan Ikram da farha taji a falo, yasata rik'e mashi hannu da ya rungumota tace... "Dear d'iyata kuka take yi fa, ka sakan naji me ke damunta? Kasan batada rigima, naje naji abun da ke damunta " Bai saketa ba, kuma bai daina abun da yake yi ba, domin yaji dad'in kasancewar tasu a wannan lokacin kuma zata katseshi. Hakan yasa bai ko kulata ba, sai ce mata kawai yayi.. "Kijira kad'an" Ya fad'i hakan cikin murya kamar ta mashayi, domin duka jikinshi ya saki baki d'aya. K'ara jin kukan nata, yasa farha rik'eshi da sauri tace... "Dear ka dawo hankalinka, kaji fa Ikram ce ke kuka kuma da k'arfi, don Allah ka sakan muje mu gani, kada wani abun ne ya sameta fa" Sai a lokacin ya fahimci me take cewa, saboda ambaton Ikram da tayi da ko wani abun ne ya sameta, shima shi ya d'aga hankalinshi. Da sauri farha ta jawo rigarta da yayi k'asa da ita, tayi saka hannun rigar tare da saka zip d'in rigar ta jawo gyalen da tayi d'ankwali dashi da d'aura ba tare da ta gyara gashin kanta ba tayo falon da sauri. Abdul-jabbar shima rigar tashi yake gyarawa, sannan ya fito. Farha ta hango sadiya goye da Ikram tana rarrashinta, maryam na d'aure hannun nata da wani k'yalen atampa. Da sauri farha tace "maryam meye hakan kuma?" Sadiya tace.... "Aunty Ikram taje kitchen wallahi ta yanka hannunta da wuk'a, wai zata yanka lemu ne " "Subhanallah! Bani ita naga hannun" Fad'in farha kenan da ke shirin duba hannun. Dai-dai nan Abdul-jabbar ya fito da sauri don ganin abun da ke faruwa. "Ayya my Ikey! Wuk'a bata kyauta ba, zata sha bulala, yi shiru, sorry sorry" Farha ta d'auketa tayi part nata, tace ma su sadiya suje part nasu, Ikram sai kuka take yi, jinin da ke zuba hannun nata shine take tsoro. Abdul-jabbar kar'barta yayi hannun farha ya azata saman k'afafunshi, shima yana rarrashinta. Farha d'auko kayan aiki tayi sannan ta saka mata magani ta d'aure hannun ta kar'beta ta bata ruwa, da sweet d'inda take siyo mata ko yaushe. Da haka farha ta d'auki zane da niyyar goyata,Abdul-jabbar ya banko mata wani mugun kallo,sannan ya aza Ikram d'in a kafad'arshi har tayi barci, sai cewa yake yi.... "Tunda ni bani da hankali, zan bari kiyi goyon k'atuwar yarinya ta danne man hancin baby " "Lah-lah! Yanzu ina hancin yake anan, kuma ina fuskar take anan?" "Ni nasan inda suke" fad'in Abdul-jabbar da yake ajiye Ikram a kujerar gadon dake d'akin, sannan yace "zanje d'aki zan dawo idan kin gama jinyar " Farha ta gane nufinshi, don haka dariya kawai tayi masa tare da kashe mashi ido d'aya, ta fad'a toilet tana dariya. Tun daga ranar, ikram ta hidimar ikram ta dawo hannun farha, sai in zataje aiki sannan take barinta gurin sadiya, tare da shaidamata a kula da ita da kyau. ★★★★★★★ Bayan dawowar su umma daga hajji, su farha suka shirya domin zuwa gaidasu, domin a kaduna suka tashi, anan kuma suka sauka. Dukansu sukayi tafiyar don yima su umma barka da zuwa da kuma kar'bo tsaraba inji Ikram da ta bada sak'on a siyo mata baby mai magana, don haka ta matsa a tafi kaduna. Kwanan su 7 da dawowa, su farha suka dira garin. Tunda umma tayi arba da Farha ta gane cewa akwai tsaraba a cikinta zaune, don haka farin ciki bisa farin ciki. Suma farin ciki gurinsu ba a cewa komai, domin su umma sunyi kyau sosai, umma har wani shek'i ake yi. Abdul-jabbar da ya kalli farha sai ya kashe ido da,alamar akwai zance k'asa kenan akan kwanciyar hankalin su umma, farha sai ta kawar da fuskarta domin ya kusa sakata abun kunya a gurin, domin umma zata gane nufinsu da wuri. Bayan an basu tsarabarsu, sannan suka sha fira, suka kama hanyar masaukinsu na nan kaduna, wanda wannan karon Ikram bata yarda ta rabu da iyayenta ba, duk inda sukayi tana cen. Satinsu d'aya, suka kama hanyar komawa, inda suka nemi umma da ta barsu su koma da sadiya, domin zata rik'ama farha wani abun, saboda girman da cikin nata ke yi. Umma ta aminta, domin ko basu ce ba, zata yarda su tafi da ita, sai maryam ta tsaya anan. Itama sadiya taji dad'in hakan, domin tanajin dad'in kyautatawar farha gareta, gashi har school an sakata a cen abujar, ikram itama an sakata wata babbar makarantar da sai d'iyan manya ke kai yaransu. Idan suka je tun 7:00 sai 6:00 domin har islamiyya aciki ake yi masu, ga manyan malamai k'wararru a makarantar, hakan yasa tayi zarra a garin abuja. Kwanakki na tafiya, cikin farha na girma, sai dai yanzu da yakai 8 month sai farha ta d'auki hutu, saboda kunburin da k'afafunta nayyi. Hakan yasa hankalin Abdul-jabbar ya tashi, ya tilasta mata zama gidan duk da bata yin komai, sai fita motsa jiki da sukeyi a harabar gidan ko yaushi. Duk wani abu da ya kamata sadiya ita ke kula da komai, sai dai farha ta zauna daga nesa tana bata umurnin yadda abincin mijin nata zai kasance, domin bata son kowa ya saka mata hannu akan hakan, amma dole yanzu ta dinga tsayawa tana gani, tun da bata iya dogon tsayi. Cikin farha yayi girma, wanda sai dai ta d'inka dogayen riguna ba dai zane ba, domin cikin nata kowa kira mata twins yake saboda wani girma da yayi. Tunda Abdul-jabbar yaga yadda farha ta zama, komai sai da kyar, sai ya rage nuna nacinshi akanta, domin yasan idan yace yana so, zata aminta ta bashi, amma kuma zata wahala sosai.don haka sai ya daina zak'ewa sosai, sai dai wasannin da ya saba yi da ita, idan zai fita, ko idan ya dawo kafin yayi wanka, wanda suma yasan k'arfin hali ne kawai take yi, domin bata son barinshi da k'ishirwarta ko kad'an. Bayan farha ta daina zuwa gurin aiki, sai dai bata daina yin waya da k'awayen aikin ta ba,kuma sun shaida mata, da taji alamar na k'uda, basai ta je asibiti ba, zasu zo su kar'bi haihuwar da kansu gida, ako yaushe haka suke fad'amata. Tunda watan haihuwar ya shigo, sai cikin gabad'aya yayi dawo k'an mararta ya tsaya, hakan yasa ko tashi bata son yi, domin ita kad'ai tasan me take ji. Tunda cikin ya shigo month nashi, ko yaushe Abdul-jabbar cikin yima farha waya yake yi idan ya fita office, burinshi yaji komai normal. Wanda har dariya farha ke yimai, tare da ce mashi ta haifi twinx, sai daga baya yake gane cewa wasa ne. Kamar kullum yau haka yau farha ta tashi, domin gyara Ikram da kuma duba yadda aikin ke gudana. Tunda farha ta tashi, sai take jin ba a yadda tasan kanta ba, yau take jin kanta ba, bata fad'ama kowaØŒ sai wata nurse yar uwarta, itama don taji abun ya wuce gurine, gata ita kad'ai cikin gida babu kowa, hakan yasa ta nemi taimako, domin abun ya fara wuce guri. Sistr farida, ita ta kasance da farha tun da ta kirata, sai dai har yanzu haihuwa shiru, kusan 3hour farha na abu guda. Farha ta hana a sanar da Abdul-jabbar domin tasan zai rud'e sosai.sister farida tace.. "Sistr idan abun nan yak'iya fa, wajibi a fad'amasa mu wuce asibiti, domin kusan 2 hour fa amma har yanzu 2 c.m kike fa, kuma idan baki kai 4 c.m ko 5 c.m ba, wallahi haihuwa bata iso ba " Farha da ko magana a halin yanzu ta kasa, ta nuna mata hannu da ta kirashi, domin ko c.s ne ta yadda ayi mata, domin wahalar ta yi mata yawa, tana iya mutuwa take gani. Farha d'in ta nuna mata wayar, tare da ambaton sunan da ta rubuta mashi, nan take ta kirashi. Tunda yaga kira ya san cèwa da matsala.hakan yasa bai tsaya komai ba, ya kamo hanyar gida aguje kamar wanda bai san akwai hatsari a hanya ba, sai sauri yake yi, amma gani d'ewar tafiyar yake yi. Da wannan gudun ya iso gida ko rufe motar bai yi ba ya fad'o gidan....... *Bee Been masoya*💞 [4/22, 4:22 PM] 💖HASKEN MASOYA💞: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH😭😭* 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com ©® Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* 💋💋💋💋💋 ★TRUE LYF STORY★ ★★★★★★★★★ *ALLAHUMMA IHDINAS SIRA'DAL MUSTAQEEM* ðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ Page..79 Da gudu Abdul-jabbar ya shigo gidan.Dai-dai da fitowar sister farida tana k'walawa sadiya kira domin kawo ma farha ruwan Lipton domin k'ara samun kuzari, da alama lavour ya iso kusa yanzu, tunda har farha ta kai 4c.m. Karo sukayi da juna, sannan wanda sai da sistr farida taji tsoro. A rud'e yake shi yasa bazai gane hakan ba. Kallonta yayi sannan ya tambaya cikin rud'u. "Yaya take ne?" Sistr farida tace "to da sauk'i, insha'allah nan da 30mnt, ina saran zata haihu,domin yanzu ta kai c.m d'inda baby zai fito, amma yanzu akwai saura, domin an sanya mata drip, insha'allah komai normal zai je. Yanzu ma lipton nake so a kawo mata domin ta samu k'arfin yin nishi" Abdul-jabbar da sauri ya nufi k'ofar shiga d'akin. Sistr farida tace "ah ah! Da ka bari ta haihu sannan ka shiga, domin yanzu kaima ba zaka ji dad'in ganinta a hakan ba " "Haba sister! Ai samun natsuwata shine; naga halin da take ciki, kada ki manta, matata ce fa, don haka zan shiga muyi wahalar tare, burina taimakon ki akan mu, naga ta fita lafiya " Murmushi sistr farida tayi, sannan ta matsa ya shiga ciki.hango farha yayi kwance da ruwan nak'ud'ar a hannunta sai matsar fuska take yi, tana juyar da kai alamar azaba da rad'ad'i. Da sauri ya isa gurin ya rik'o hannunta, sannan yace.... "Farin ciki na sannu! Allah ya rabaku lafiya " Shi kad'ai ke zancen shi, domin farha bata san yanayi ba, domin bata shaida wanda ke kanta iya lokacin. Sistr farida ta shigo da cup d'in lipton a hannunta.Abdul-jabbar ya d'ago kan farha, sistr farida ta bata ruwan lipton d'in da ke da d'an zafi, domin samun kuzari. Ba'a fi 10mnt ba, nak'uda ta taso, wanda banda zufa da juyar da kai babu abun da farha ke aikatawa, domin abun ba na wasa bane. Hakan yasa farida yunk'urin taimaka mata, duk da Abdul-jabbar ya k'i fita daga d'akin, k'arshe ma kan na farha a saman jikinshi ya dawo, hannunta d'aya cikin nasa ya dumk'esu, sai zufa su ke yi, ita gumin azaba ke fita, shi kuma gumin azabar tausayin sahibar shi dake sha, wanda bata gane komai. Lokacin da wani mugun nishi ya taso mata, sai da tayi k'ara mai k'arfi, tare da sakin dukkan hannayenta daga jikin Abdul-jabbar, tayi wani nishi mai k'ara, wanda sai da taji mutuwarta tafi mata wannan azaba. "Alhmdllh!" Abun da sistr farida ce kenan, fara 'bullowar kan baby. da kanta ta taimaka ma farha,gurin k'arasa ciro babyn k'ato guda,wanda batayi mamakin ganinshi a hakan ba, domin farha ta sha wuya sosai, hour 8 tana abu d'aya. Fitowar baby, sai farha itama tayi k'arfin halin cewa "Alhamdulillh" Sannan taji wani barci mai dad'i ya d'auketa, hakan yasa Abdul-jabbar gyara ma farha kwanciyarta, sannan ya juya karbar new baby nashi mai shegen kyau da girma. Bayan sister farida tayi duk wani taimako da nurse ko likita ke bama duk wani wanda yayi labour.haka tayima farha, Abdul-jabbar ke rik'a mata har suka tsaftace gurin da ya lalace, sannan ta d'auki new born babyn nasu tana gyarawa, anan itama ta tabbatar da cewa; baby boy ne aka samu. Farha banda barci babu abun da take yi, domin ba zata shaida Abun da ta samu ba, saboda ta dad'e tana neman barci, amma bata samu ba, sai yanzu da suka rabu lafiya. Bayan natsar da komai, sannan Abdul-jabbar sai kiran waya ya tashi, duk inda ya kamata ace sunsan sun samu k'atuwa, sai da Abdul-jabbar ya fad'i.Rungume yake da baby nashi, sai murna yake yi yak'ara zama babba, uban 'ya'ya biyu, wanda ko wannensu k'aunarsu yake yi. Hafsart matar hafiz, tunda akayi waya aka sanar dasu, ta kwaso mayafinta da sauri ta fad'o gidan da murnarta. Sai ta rik'a aka k'arasa gyara abun da ba a k'arasa gyarawa ba, ita ta aza ruwan zafin da za'ayi ma baby wanka, sannan itama farha aka d'aura nata, duk da barci take yi har yanzu. Komai ya lafa, gidan ya dawo tamkar ba anan akayi labour d'inba, sannan farha na tashi abinci ta fara kiran a kawo mata, sannan taci ta iya takawa toilet gurin wanka. Alhmdllh! Domin haihuwar ta zo da sauk'i sosai. Saboda farha ta haihu ko k'arin da ake yima mata, ita ba'a yi mata shi ba, duk da zamowar babyn k'ato guda barakallah, amma ita komai normal, sai wahalar labour da tasha, wanda kuma dole ne, tunda ba'a haihuwa banza. Sister farida ta k'arasa yima farha Alluran da ya kamata tayi mata, domin ta k'ara samun k'arfin jiki, sannan ta rubuta maganin da ya kamata, a siyo mata da baby shima kanshi, domin dukan su sunsha wuya, sannan tayi sallama da su, don komawa gidan ta itama. Sistr farida, ta sha mamakin irin k'aunar da Abdul-jabbar ke yima family d'in nashi, ta dad'e a rayuwarta, tana mamakin irin wannan kulawa da yake yi da matarshi, babu kamar gurin labour d'in, wanda duk lokacin da azabar ta murd'a ma farha, har wani rik'eta yake yi, shima kamar yayi kuka. Bai samu natsuwa ba, har sai da farha ta sauka lafiya, sannan ya samu relief, kuma k'aunar ta juya a babyn sak. Abdul-jabbar Alkhairi ya k'unsa ma sister farida, mai yawa, amma tace bazata kar'ba ba.Abdul-jabbar ko sauraronta bai yi ba, har ya kaita k'ofar gidan nasu, ta shiga ya samu yara ya turasu da kayan da aka bata.Turamen atafa ne manya guda ukku, da turare guda biyu manya, da set d'in man shafawa da sabulu, sannan da kud'i I5k a wata farar takarda a nad'e, wannan duk tukuycin k'ok'arinta ne da ta yi. Bayan ya dawo gida, sai ya tare a d'akin farha, wanda kowa ya watse, ita kad'aice zaune a gado, tana kallon babyn da ke ta famar tsutsar hannunshi, alamar yunwa ya ke ji. Ikram duk ta wani tattare ko ina kada a ta'ba masu babyn su, wanda hakan ba k'aramar dariya ya bama Abdul-jabbar ba. Babu yadda bai yi ba, taje gurin aunty sadiya ba, ya gana da farha, amma yarinyar nan tak'i tafiya. Juyawa yayi yace ma farha.... "Zanzane d'iyarki fa, ko ki ce mata ta tafi" Kallon Abdul-jabbar farha tayi, sannan ta zaro ido duka waje, alamar jin tsoron zancen da ya fad'a. hakan yasa ko kallon gurin da yake batayi ba, ta k'ara gyara kwanciyarta a filo tana kallon Ikram da baby, wanda shi kawai take kallo tana dariya. Abdul-jabbar dubara ta fad'o mashi yace... "Ikram ki kira aunty sadiya,sai ta d'aukar maki babynki ku tafi dashi d'akin ku ko?" Da sauri Ikram taje tana murna, dama sadiya ita take jira, ta fito ta bata abinci kuma tayi mata wanka ta kwanta, domin dare ya fara yi, gashi gobe akwai school. Wanka tayi mata, sannan ta bata abinci, sai tace su je su kwanta. Ikram tace ai bata san hakan ba, domin cewa akayi gurinsu baby zai kwana, don haka Aunty sadiya taje ta d'auko mata babyn ta.kuka take yi sosai, har farha najiyo kukanta, kuma sai taji shiru alamar tayi barci. Fitar Ikram, Abdul-jabbar ya d'auki babyn ya matsa kusa da farha yana cewa.... "Ki shayar damu, wallahi yunwa muke ji, duba kiga yadda yake shan hannu" Farha kallonsu tayi, sannan ta juyar da fuskarta gefe, alamar babu. Abdul-jabbar ajiye babyn yayi, sannan ya jawota da kanshi, ya matse jikinshi, ya bud'e rigar tata da ya zamo ba wuyar bud'ewa zasuyi ba, domin rigar kawai ce jikinta, sannan ya d'auko babyn yace.... "Akan me bazaki bashi abincinmu ba, idan bakiyi hankali ba, har ni zaki shayar ba shi kad'ai ba, don haka ki kar'beshi ki bashi " Farha yamutsa fuska tayi tace... "Babu komai a cikinshi fa, har yanzu abincin bai zo ba, kuma wallahi zafi nake ji, ka barshi har zuwa gobe" Bai ko saurareta ba, ya jawo babyn ya kara a bakin nonon nata, yark'e da kanshi, nan take babyn ya kama yana ja, kamar an koya mashi. Farha sai cije baki take yi, saboda babu komai a nonon kuma ja babyn yake yi da zafi, Abdul-jabbar saboda k'eta har wani k'ara matsawa yake yi, wai babyn yasha. Farha ta gano k'eta kawai yake yimata, don haka sai ta yi sauri cije mashi hannu tace ya barta ta bashi da kanta, sannan ta kar'ba tana bama babyn nono tana kallonsa. Abdul-jabbar ya rufe mata ido, yace... "Ki daina kallar man yaro, saboda naga ba ki damu dashi ba, muma kuma a daina kallon mu " "Eh waya ce ku wahalar dani to?" "Kwad'ayi ne ya kaiki wahala, wanda gashi inata murna kin bani beautiful boy mai kama da ke" Fad'in Abdul-jabbar kenan tare da dariyar k'etar maganar da yayi, sannan ya juyo yana kallonta, ita kuma jaye babyn tayi wanda barci yake yi, sannan ta juyar da fuskarta gefe, tana turo baki. Abdul-jabbar na ganin hakan da sauri ya kar'bi babyn ya ajiyeshi gefen su, sannan ya rungumo farha da sauri, tare da saka bakinshi kunnenta yana cewa.... "Wasa fa nake yi maki, ai dole na biya wannan k'ok'arin da kikayi, dama jira nake yi ki k'arasa bashi abincin, nima sai kiji dani, nayi maki sannu da abun alkhairin da kika sama mana, kin bamu baba Aliyu, kincika burina na samun baba na, ko nace; Allah ya cika burina da yabani baba a tsak'en jikin masoyiyata. My farha ina godiya fa, kinata cika buri na, gashi a k'ark'ashin soyayyar mu da k'aunar mu, mun samu beautiful boy, nayi mashi hud'uba da sunan baba, na saka mashi; *ALIYU (HAIDAR)* ina fatan hakan zai yi maki dad'i?" Tureshi tayi jikinta, domin har wani shafe-shafe yake shirin yi a saman rigarta ta kalleshi yana wani lumshe ido tace.... "Anya kuwa, Aba Ikram lafiya kake? Duka ko 24hour banyi ba, da fitowa tsaka mai wuya, amma sai wani shafa ta kake yi, kamar wata mage, ko tausayina ma baka ji, kuma yanzu wani sanyin kake nema again " "Kin ta'ba ganin wanda ya k'oshi da dad'i? Ai banda ma nasan halin da kike ciki, kuma bazan iya zuwa gurin ba, da sai nace a koma ruwa tun yanzu " Yana fad'in hakan yana dariya tare da shirin k'ara rungumota yace "baki fad'aman taki shawar ba, akan sunan baby na ba?" "To me zan ce, bayan yanzu ka kira shi da babyn ka, duk yadda kayi dashi ai naka ne.amma da shawara ce akan my Ikey; wannan nice gaba, don mugun son da nake yi mata ko......! " ko meye? K'arasa mana naji " "Ni dai barci nake ji, wallahi ka barni na huta hakan, Allah yasa umma ma tace na shirya mu koma gida, ko zan dinga barci " "Wallahi ki jaye wannan zancen, domin babu inda zaki je, saboda idan na yarda, aikin da nake yi a yanzu zai samu matsala, saboda idan dai nayi winning gareshi, to na samu girma babba, wanda nake burin nakai gareshi, don haka ki daina cewa hakan, kinsan umma na iya yadda, kuma tace sai kin je, wanda ni kuma za'a cutar dani " "To ka barni nayi barci na" "Ban gama ganin ku ba" "Sai ka d'auki babyn kuje kuyi fira, ni kuma sai na huta ko?" Dariya yayi, sannan ya matso da babyn kusa da ita, ya mik'e zuwa toilet don yin wanka da alwallah ya fito, ya yi nafilar godiya ga Allah, sannan yayi shirin barci da farin ciki, yaje ya rufe ko

Chapter 42 of 44