An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
๏ปฟ
Compiled by Umar Dalha
Copied by Bee Been Masoya.
Bee Been๐ Masoya: ๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH๐ญ๐ญ*
๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
ยฉยฎ
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
*I LUV YOU ALL MY FANS*๐๐๐๐๐
*_I'm back masoyana nazo da sabon salon labari mai tsuma zuciya...lbrn yafaru dgsk...saidai akwai salon morewa aciki...da wa'axantarwa domin wa'axin yafi yawa ga wayanda hakan bai faru dasuba suguji sa'bama iyaye..._*
*_Alkhairin dake ciki Allah yabamush bakid'aya..,sharrin dake ciki allah yakaremu dashi....kuskuren dake ciki Allah yayimuna gafararshi....,_*
*_ina neman gyara a inda na kuskure..., Amma ta hanya mai kyau...,idan akaje yiman gyara aka kaucema shari'ar gyara bazanjiba kuma bazan gyaraba..๐
๐ผdomin kunsan an gyara ta sigar fahimta...๐คท๐ผโโidan lbr yafaru dgsk dole saida gyara....,naso yin chikar muradin zuciyata saiga wani lbrn anbani jiya...,don haka Allah yabamu ladar abunda zamu fad'a ciki...._*
*โ
TRUE LYF STORYโ
*
*BISSIMILLAHIRRAHAMIRRAHEEM*
*{BISMILLAHILLAZIE...LAH YADURRU MA'A ISMUHU SHAI'UN FEEL ARDI..,WALAH FEESSAMA'I...,WA HUWAL SAMI'UL ALIEM}*๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป
๐ง๐ง๐ง
Nasadaukar da page d'in gareki..,my luvly
*Zarah katsina {mmn beauty's}* qaunarki gareni babu adadi much luv you dearโค
Page...
โ
1โฃโ
ยฎ *"'ya'ya farha* kiyi haquri kijaye qud'urinki akan abunda bashida umfani gareki...,kidaina biye ma wata rayuwar daba ita bace rayuwa mai kyau...,ni yr uwarkice wadda ba kyason kiga kukana kuma bakyason kiga abunda zai 'batan rayuwa...,'ya'ya don girman Allah kitausayaman ke kad'ai ke gareni a duniyar nan wadda zan duba naji sanyi....kiyi haquri ki kar'bi abunda iyayenmu sukazo dashi nasan gaba zakiyi murna da farinciki 'ya'ya farha kiso *brox abdl-jabbar* nasan zakiji dad'in kasancewa dashi na har abada...."
"Dakataman *iman* ke qanwatace wadda aqalla nabaki shekaru ukku da jin qamshin duniya...mezaisa ki fini hangen abunda ni zanfi ganinshi....mezaisa na kar'bi abdl-jabbar a matsayin mujin aure....,bayan inada wanda nakeso rayuwata shine farincikinah,shine rayuwata ta aminta da shi amatsayin muji....,don haka wlhy bazan iya aurenshiba...,gara namutu dana aureshi......"
*Iman* da sauri taqarasa gabanta tareda riqo hannunta.....hawaye kefita cikin idonta d'aya bayan d'aya...ta duqa da qafafunta qasa tace....
*"'Ya'ya farha* kirufaman assiri gada kiyi silar tarwatsewar rayuwamu kiyarda da qaddara gada ki kafurcema Allah tareda qin yima iyayenmu biyayya kifad'a halaka mafi muni...yaya kinfison duniya tabada musali dake ne a kan son zuciya...?"
*Farha* hawaye ke xuba d'aya bayan d'aya kasancewar ganin qanwarta na zubar da nata qwalla taqara riqa hannunta itama tagoge hawayenta tace......
*"Khadijatul iman* nakiraki da sunanki na gsky..., kinkoh san menene so..,da rashin so....? Idan har da kinsan so toh wlhy bakisan tasirinshi a zuciyar d'an adam ba....,sanin kankine banta'ba son Abdl-jabbar ba dad'ai rana...amma ina yimasa d'aukar d'an uwa maqwafci wanda xumuncin abotar qawancen iyaye ya had'amu...,amma banta'ba sonsaba dad'ai rana domin b shine chikar burinah ba.....amma naso yin biyayyar a farko amma ynx nafasa...bansonshi wlhy bansonshi๐ญ..."
Kuka sukeyi dukansu zukatansu na bugun ukku ukku kowa baqincin zuciyarshi ya isheshi ba kamar iman da take kuka biyu....halinda iyayensu zasu shiga gefen tayar da alqawalin dasukayi a matsayinsu na aminai na qwarai....,dakuma halin da yr uwarta qwaya d'aya dazata shiga...domin wannan kafiya tata babu inda zata kaita saiga danasani... Koh mutuwar data tsarama rayuwarta...,hakan ita iman take ganin tarwatsewar rayuwarsu mai dad'i yazo...,taqara duqar da guwayyunta a qasa tana kuka tadubi yr uwarta tace......
"Toh ynx ya za'ayi wannan rikitaccen alamari..,kinsan dai ynx balallaine baba ya yrda da abunda kikeso kikafa koh..? Tun farkoh yakama bakyasonshi ki fad'amasu gsky amma baki fad'iba saida abu yayi nisa har kowa yasan da zancen tsayar da aurenku.., a gsky ni banga zaman lfy ba awannan rayuwar..., toh 'yaya farha idan har kin rabu da brox Abdl-jabbar waye kikeso da nashin yayi tasiri a kanki.....?"
"Iman *ANWAR TIJJANI IBRAHIM MILO* nakeso domin duniya gabad'aya babu wanda nakeso kamarshi...shine burin xuciyata shine tsarin rayuwata...."
Jinsunan da farha ta ambata yasaka iman saurin sakar mata hannu tareda miqewa tsaye...tazaro idanunta baki d'aya tace.....
"Innalillhi wa inna ilaihirraji'un....,yaya farha lallai kinsamu mtsl mai girma domin bansan cewa wannan qaramin yaron zai firgitakiba kamar hakan...,domin *ANWAR* natabbata idan xai girmi shekarunki bazai baki shekaru ukkuba a duniya...,domin yarone sosai....,gada qiyar kud'in mahaifinshi takaiki ga shiga halaka....gada rud'in arziqin wani yasaki ga fad'awa halaka...kirabu da masoyinki na gsky wanda kesonki so na har abada tun kina yarinyarki wadda bata mallaki hankalintaba har kika girma yana qaunarki...ynx ki zubar da gsky ki kwashi gsky....ni yr uwarkice wadda keson ganinki hanya tak'warai *anwar* yarone bazai iya sharemaki hawayenkinba wlhy...."
"Dakata *IMAN* kina kiransa yaro a wacce siga yake yaro gareki..? Kingirmeshi ne...?
" bangirmi *anwar* ba,saidai a aure ke kingirmeshi..."
Dasauri *farha* tad'aga mata hannu...
"Dakata Iman nasiharki ta isheni hakan ki adana aburki may b gaba zatayimaki rana...,ynx ni ba zancen kowa xan iya ganewaba....."
*Iman* fitar da idanunta tayu gabad'aya domin jin furuchin yr uwarta mai biyayya mai addini....mai kamala...a yau wai wa'azinne batasonji sbd soyayyar da banga zatayi haske garetaba....a yau tasani tatake saninta....,hakan yasa *Iman*sakin baki tana kallon ikon Allah....
Jin motsin mamarsu dasukaji a gefen d'akinsu yasa *iman* saurin share hawayenta....,hakan itama *farha* sauri tayi tafad'a toilet...,domin halin da suke ciki gabad'aya iyayensu basusan da shiba...,domin *farha* ta hani *iman* da gada tafad'i zancen so takeyi shi *abdl-jabbar* d'in yafad'i da bakinshi yafasa aurenta abashi kud'inshi .....
Mamar taturo qofar d'akinsu a hankali tana kiransu...,karo tayi da *iman* tsaye...
"Auta lfy najiku shiru..banga kunzo d'ibar abinciba...? Ina 'yayar taki take....?"
"Tana toilet alwallah takeyi amma ynx gamunan fitowa..."
Mama ta juya *Iman* tausayin mamar yakamata sai tazauna kujera d'aya dake d'akinsu ta dafe kai sbd tsananin rikicin kukan datayi kanta har ciwo yakeyi....
Fitowa *farha* d'in tayi daga toilet d'in tace "sai kitayi yr wahala....domin wa'azinki bazai kai ko inaba...."
"Allah yasa kigane gsky tunkanda su baba susan abunda kikeyi....."
waiting comments....โ๐ป
~Ummu Ilham~
*Bee Been masoya*๐
[12/26/2017, 9:43 PM] Bee Been๐ Masoya: ๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH๐ญ๐ญ*
๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
ยฉยฎ
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
๐๐๐๐๐
โ
TRUE LYF STORYโ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
*_INA QAUNARKU WRITTERS๐MANYA DA QANANAN MA...SBD QAUNARKU GA BEE BEE๐BA ADADI...ALLAH QARA BASIRA YABARMU TARE..K'AUNARKU LODI LODI_*โค
page...
โ
2โฃโ
ยฎ "FARHA inasonki bazan iya rayuwa babu keba...farha mena yimaki lkch d'aya zaki sakaman da wannan mummunar sakayar...kece mace ta farko da na fara so..,kece zuciya ke mararin samu...zuciyata ta sarqu acikin zuciyarki...banji zan iya haqura dake ba...,innalillhi wa inna ilaihirraji'un...."
Kuka yakeyi kamar ranshi zaifita qirjinshi har wani zafi yakeyi...juyawa yayi ya jawo wayarshi..dake charging gefen gadonshi...,bud'e luck d'in wayar yayi babu wadda yaci karo da ita sai farha tana murmushi a wallpaper d'inshi...wani mashi yaqara sukar zuciyarshi๐wadda saida ya juyar da wayar gefe....yafara dialing wayar farha d'in daya sanyama *my happiness* ringing takeyi ba ad'aukaba..hakan yasa yaqara kira tareda duba agogon d'akin nashi.... 9:30 yasan bata isa barciba haka ringing d'in yaqare batayi picking ba...,ya aje wayar kawai yakoma tunanin 'baqincinkin dazai risqi zuciyarshi ynx.....
Hakandai bai damuba kuma yaqara danna number tata...lkchn daya kira Iman tafito toilet d'insu taduba wayar daketa faman ringing amma farha taqi d'agawa......
" 'yaya farha wayarki na ringing p..."
"Nagani kuma ina sane da ita banida ra'ayin d'auka domin ba shine gabanaba...kallon nan yafiman jin muryarsa dad'i....,keda abun yadama kin iya d'auka domin ni ba xan iyaba wlhy...."
Hakan yasa iman d'aukar wayar...tareda sallama...,lkchn da yaji muryar yayi tsammanin farha d'ince domin muryarsu na kala d'aya yad'aga acikin farinciki.....
"My happiness..."
"Brox abdl iman ce...yaya na toilet idan tafito zan fad'amata kakira..."
"Ok sis dama inason tambayarkine...,shin koh kinsan abunda nayima farha ne tace ynx bata sona....?"
Tayi ajiyar zuciya tareda duba phone d'in tace....
"Koh d'aya babu komai...,kawai rayuwace kasan kowanne lkch za'a iya 'batama mutun har yayi fushi....ni qanwarkuce bazan iya yanke wani hukunciba akan hakan...domin bansan menene soba bansan menene rashinsaba..,domin ban sababa.....amma kanemi sani gareta...."
"Toh shikenan ngd sis ki gaida su mamah saida safe..."
Ta aje wayar tareda juyowa ta miqamata wayar..."yaya farha zaki jawomuna mtsl p...zaki sakamu a wani yanayi na 'bacin rai....,domin xaki jamuna zagi a idon duniya...wlhy idan baki aje wata rayuwa taqaryaba zaki d'auki gsky lkchn da nadama zata xo maki a rikice...."
Tsawa tadakamata tareda miqewa tsaye.....
"Ke dakataman wlhy bazan d'auki iskancin banxaba...yaushe zaki zauna kidinga fad'aman maganar banxa...,bayan sama nake dake ba qasaba..kisani nagaji dajin maganarki ta banza wadda ba itabace abunda ke gabanaba don haka ki natsu kikagane...kina magana ne da 'yayarki *FATIMA {FARHA} ALIYU ABBAS* banason kina yiman magana a matsayinki na qaramata ki dinga ganin komai nakeyi ba a hankalina nakeyinshiba nasan menakeyi iman nasan menakeyi....you know....?"
Iman sakin baki tayi tana kallonta...tunda suka tashi basu ta'ba samun sa'bani tsakaninsuba...,koh a hanyar mkrnt kagansu farha riqe take da hannun iman duk inda zasuje kayansu iri d'aya suke sakawa...gasu kyawawa dasu...wani baya abu ba tare da d'ayaba...farha nada tarin qawaye amma idan ba'a za'ayi komai da qanwartaba toh tafison su rabu da qawar....tun tasowarsu suke cikin gata tun mahaifinsu bayada doguwar wadata.,har Allah yabashi dai2 gwargwado......
Ayau ga farha na shirin ruguza farincikin family d'insu mai dad'i wanda a ynx ankai matakinda kwata kwata bata fahimtar zancen da qanwarta ke fad'amata harda miyagun maganganu...toh Allah kawo sauqi ciki kawai.....
Duban datayimata tareda bud'e fararen idanunta kawai sai hawaye suka biyo fuskarta...,nantake sai kuka takeyi tana fad'i......
"Haqiqa yaya farha kin samu ta'bin aljannu idan kuma ba aljannu bane toh ke ba farhan da nasanibane....,Allah yakawo sauqi...amma kisani wlhy a ynx iyayenmu nake tsoron wani abun yasamesu domin zuciyar dakega mahaifinmu...,zancigaba da addu'a insha allah......"
Kallonta kawai farha tayi tareda duban fuskar datake hawaye da ita...ta ja tsaki kawai tace.....
"Rashin aikinyi kawai..."
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
A wata ranar monday farha tasauka a qarshen titin gidansu domin gada wani yaganta...,an sauketa a mota mai bala'in kyau...,dai2 tym d'in Abdl-jabbar yadawo aikinshi saman mashin d'inshi wanda samarin ynx ke bala'in taqama dashi wato zhonshen...hango saukowarta kawai yayi tana murmushi...abun yayi bala'in bashi mamaki...tareda tsayar da mashin d'in nashi domin ganin ikon Allah....,dama farha tasan tashiga motar wani wanda ba d'an uwantaba ba jinintaba...bakuma mijin dazata auraba....lallai akwai qalubale gabanshi da wuri....."
Takunta takeyi cikin hankali siga ta burgewa duk abunda yakeyi idan yaga farha hankalinshi tashi yakeyi....,gashi bayason abunda zai dameta tuntana qarama...amma wajibi yau yasan laifin da yayimata.....,
Yakai dai2 wani shop na unguwarsu anan ya aje marching nashi tareda..takawa da qafafunshi yabi bayanta...zai iya shiga gidan nasu domin bayada shamaki da gidan tun baikai hakanba.....amma bayason gidan nasu susan da abunda ke faruwa...,gara yaji laifinshi tunda wuri yanemi yafuwar abunda yayimata...tun akusan tashiga get nasu yake ta qwalamata kira ......
"FARHA...! FARHA...!! FARHA...!!!
Don Allah kitsaya kiji abunda zan fad'amaki mana..."
Yabiyota da sauri har bakin get nasu tanajinshi amma tayi banxa dashi..,ganin ankawo get nasu xai iya biyarta har cikin gida hakan yasata zayawa bakin get nasu...,juyowa tayi a fusace tareda d'aure fuska tace.....
"Lfy wai kake qwalan kira kamar wata dai2 kai....? Toh kasani wlhy bazan aurekaba..,kuma idan duniya zata taru saman kaina bazan aurekaba...kasani na girmi ajinka ynx...,domin ni bazan iya rayuwa dakai a matsayin dakake zauneba...,dama ina maka kallon mutuncine sbd babu yrda zanyi..,daga ranar da akace wai anbakani daga ranar nafara shakkun wannan auren ai bazaiyi kyau daniba...,saigashi ynx kuma nasamu waraka domin nasamu dai2 ni.... Idan kanada zuciya katura tsofaffin dasuka kai kud'in aurenka ga iyayena su kar'bo maka abunka kasamu dai2 kai....kasani koh uban da ya haifeni a halin ynx bazai tillastani aurenkaba na d'auka...,kakosan shike iko dani kuma shine gaba da al amurrana..,amma a aurenka bazanjiba..."
Hararshi tayi tajuya zata tafi...qafafunshi duka rawa sukeyi...domin jin kalaman farha dai2 suke da mutuwarshi ynx...da sauri ya riqota hannunshi biyu ya turata ginin dake cikin get nasu..,yariqeta gam....zuciyarshi halbawa takeyi sosai domin jin kalamanta na nuni da ta haukace koh aljannune jikinta domin akwai mamaki wayannan maganganu harda mahaifinta take iqirarin bazai tilastataba....
"Farha kiduba dakyau Abdl-jabbar ne...,don Allah kisanar dani laifin danayimaki nabaki haquri...,kinsan da sonki na saba tun baki kai hakanba...,baki nuna baki sonaba sai ynx da iyayenmu sun kakai qarshen magana....farha kiyi haquri kisoni gada kice baki sona ynx don wlhy zan iya halaka..,kece mace tafarko dana fara so rayuwata....,plz my farha tell me...menayimaki hakan dazaisa kid'auki zafi hakan?"
Kallon riqon dayayimata harda kusan had'a jikinshi da nata guri d'aya shi yasata hasala daqarfi ta dubeshi tace....
"Kasakan..! Nace kasakan mana..."
Yaqyaleta fuskarta yake kallo da bakinta ji yakeyi kamar ya maidata cikin jikinshi baki d'aya koh tafad'amasa laifinshi yanemi afuwan..., taqara fusata tace da qarfi....
"Idan ka haifu ga uwarka Amina da malam Ibrahim kasakeni nashiga gidan ubana...banxa kawai mara zuciya...,wlhy samun sauqinka gareni shine katura kace kafasa auren nawa abaka kud'inka kanemi wata...,don wlhy *Banasonka! Banasonka Abdl-jabbar! Kuma bazan aurekaba koh duniya zata nad'e kuwa bazan aurekaba don bana k'aunarka...."*
Dasauri yasaketa tareda matsawa baya yana kallonta...idanunshi sunyi jawur sbd kalamanta sun hirgitashi nantake fuskarshi tayi jawur sbd bala'i...tunda uwar data kira ta haifeshi ba'ata6a kirantaba anxageta hakaba sai farha da yake iqirarin itace matarshi uwar yayanshi lallai ta d'ebo da zafi domin ta'ba mahaifanshi jidaline duniya babu wanda yafi qauna kamar ummanshi da abbanshi sai ita farha d'in da yasaka aranshi toh tunda batasan girmansuba zai tausa zuciyarshi duk halin dazaishiga saidai yashiga ya qyaleta domin bazai d'auki cin mutunciba wlhy.....
Tawuce fuuuuuu da sauri tareda gyara hand bag d'inta da handouts d'inta ke ciki....,ta bud'e qofar tashiga koh waigowa batayiba bale taga halin da yake ciki.....
Abdl-jabbar riqe kanshi yayi tareda karanta addu'ar da yasani a bakinshi.... *" ALLAHUMMA AJIRNI FEE MUSIBATI HAZA WA HALUFHU KHAIRAN MINHA..* Lallai ina cikin mtsl domin ciwon sonki zai kasheni...,amma wlhy bazan d'auki zagin mahaifanaba akanki....,dole nasama kaina burki akanki wlhy koh da kuwa zan.mutu....."
Hakan yajuya jikinshi babu qwari yabar get d'in....yana was wasi a xuciyarshi anya kuwa farha ce..? Hakan ya d'auki mashin d'inshi sai gidansu.....
Shigarshi gidan rayuwarshi babu dad'i hakan yakama hanyar d'akinshi domin bayason wata fira tashigo zuciyarshi...yashiga d'akin nashi yafad'a gadonshi domin komai ya toshemashi...tunani yakeson yayi amma wlhy baya iya tuna komai sai miyagun kalaman farha akanshi...,hakan yaji qwalla nabiyar fuskarshi domin shi kad'ai yasan baqincikin dayake ciki.....
Yana cikin wannan hali ummarshi ta turo qofar d'akin tashigo...,domin taji shigowarshi amma baishiga inda takeba kamar yadda yasaba kullum idan yadawo aikinshi.....,hangoshi tayi a gado yana kallon fankar dake juyawa da alama tunani yakeyi.....
"Babanah lfy kuwa kake...? Naga kashigo ba yarda nasankaba...,koh wata mtsla ne tasamu wadda bazaka fad'amunba....?"
Jin muryar ummanshi yasashi d'agowa da murmushi domin gada ta fahimci damuwarshi...
"Ah Umma babu komai kawai nauyin aikin namune keda wuya...,amma mezaisa naqi fad'amaki damuwata umma? Babu komai nagajine kawai...."
"Toh babanah Allah yataimaka yasa ayi cikin nasara...har naji zuciyata tayi sanyi...katashi muje muci abinci koh...?"
Yayi murmushi tareda jin wani sanyi zuciyarshi domin yasan cewa a duniya babu abunda ummansa tafi so kamar taga yana farinciki...da ace taji abunda yafaru a yau da zatafishi baqinciki domin itama tanason farha rayuwarta.....
"Umma zanyi wanka nayi sallah zan fito ynx insha allah..."
"Toh babanah ina jiranka....domin na dafamaka abunda kafi qauna rayuwarka...."
Ummar tafita yatashi jikinshi mace yafad'a toilet d'in d'akin ya watso ruwa yayo alwallah yayi sallah tareda roqama kanshi abunda zai zama alkhairi gareshi.....
Yafita don ganin ummar tashi suci abinci........
โ
โ
โ
โ
โ
โ
*Shin wai ya wannan rikitaccen al-amari yake...?kuma shin menene asalin kan lbrn wannan family guda biyu....??*
*Ku biyo bee bee don warware zare da abawa.....*
*Bee Been masoya๐*
[12/27/2017, 7:56 PM] Bee Been๐ Masoya: ๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH๐ญ๐ญ*
๐ง๐ง๐ง๐ง๐๐ง๐ง๐ง๐ง
ยฉยฎ
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
๐๐๐๐๐
โ
TRUE LYF STORYโ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
โ
*_MASOYANAH JEROKU ZAIYIMAN WUYA WLHY AMMA KUSANI BEE BEE NA QAUNARKU LODI LODI..BUHU BUHU...๐ K'AUNARKUCE KE SANI HAWA TAMKAR FARASHIN MAN PETROL...YNX DA YAYI TSADA...KUNA BINA DA PETROL IDAN NAQONE P๐....GA TAKEN P..๐คธ๐ปโโ๐คธ๐ปโโ๐คธ๐ปโโ LUV YOU ALL๐_*
Page...
โ
3โฃโ
*ASALIN WANNAN RIKITACCEN AL-AMARI*
ยฎ Alhaji Aliyu abbas d'an asalin qaramar hukumar zamfara mai suna maradun...,alh.Aliyu abbas shikad'aine d'a namuji a gurin mahaifansa...,sauran duka matane...,d'akinsu mata biyune shine kawai d'a namiji gidansu har allah ya yima mahaifanshi rasuwa...da yn uwansa dasuke d'aki d'aya suma Allah yayimasu cikawa...kasancewar yazamo shikad'ai namiji sai gadonshi yad'ara nasu...hakan yajamashi qiyayyar yn uwansa baki d'aya sai yazamo shi kad'aine ke rayuwarshi....hakan yacigaba da karatunshi...har Allah ya had'ashi da fatima wadda ake kira da binta..mmrsu farha kenan sukayi auren so da k'auna mahaifan binta suka riqamasa akayi auren cikin nasara..,kasancewar yana yr sana'arsa da kuma kiwon dabbobi da mahaifansa suka barmasu kasancewarsu fulani....
Ba yabo ba fallasa suna zaunensu cikin rufin assirin Allah...binta na sana'ointa na hannu hakan kuma shima yana nashi sana'ar....,suna zaune shekara da shekaru basu samu haihuwaba...,hakan bai dameshiba domin yanason matarshi itama tanason mujinta...
Ahaka yasamu cigaban kasuwancinshi.., yana kai masara garuruwa ana sara idan yanoma hakan Allah yabashi rufin assiri...alokacinne kasuwancinshi yakoma kaduna baki d'aya...hakan yaga zai dinga dad'ewa idan yaje..,toh sai yad'auki binta suka koma cen kaduna da zama...,yasamu haya suka zauna kafin yasamu halin nashi...
Komawarsu kaduna sai Allah ya had'ashi da wani maqwafci na qwarai wato malam ibrahim..,kasancewarshi dattijo na qwarai kuma a girme ya girmi Aliyu abbas....,hakan sai suka kasance tamkar yn uwa...
Idan Aliyu abbas zai nemi shawara koh wani abu makamancin zaman takewar rayuwa malam ibrahim yake nema....hakan matan nasu suka qulla qawance na har abada wanda idan Aliyu abbas yayi tafiya binta gidan malam ibrahim cen ne gurin zamanta kasancewarta ita kad'ai agidan..,zataxo suyi firarsu tareda yn shawarwarin datake bata a matsayin wadda ta girmeta nesa ba kusaba...zama sukeyi na amana.....
Malam ibrahim nada yaro qarami Aqallah zaikai shekara bakwai wato Abdl-jabbar wanda suke kira da abba domin sunan mahaifin mahaifiyarshine wato Amina....
Abdl-jabbar nada shiga zuciya domin kasancewarshi kyawawa kuma mai hikima...qaramine amma idan yayi magana zakasha mamaki idan ya furtata...,hakan yasa Allah yahad'a jininsa da mutane da dama...,tun yana qarami mutane keson d'aukarshi....,duk da mahaifinshi bayaso saboda bakin mutane.....
Aliyu abbas nabala'in son abdl-jabbar wanda hakan ya karkato dashi ixuwa son haihuwa ynx...wanda burinshi baifi ace shima yasamu yaro kamar abdl-jabbar ba domin yanasonsa so mai tsanani....,hakan yasa yafara roqon Allah yabawa binta ciki koh yaga jininshi a duniya...,hakan har yafara nunama binta ra'ayinshi akan hakan...kasancewar ynx shekarunsu ukku da aure babu wani motsi.....
Watarana yadawo kasuwancinshi yake fad'ama malam ibrahim cewa...
"Yaya malam..! Wlhy ina cikin mtsl...wato haihuwa nakeso naga nasamu kuma Allah bai baniba...,shine nakeso naji koh da wani taimako da za a samu gameda hakan...?"
"Eh Aliyu nikaina kaga har ynx d'a d'aya gareni..,amma ina saran samun wasu gaba insha'allah domin nima na dad'e bamu samu haihuwaba amma akwai maganin da aka ta'ba bani akan mtsl kamar wannan...insha allah zan shirya zuwa gombe cen gurin yn uwana fulani na kar'bo maka maganinnan kuma insha'allah koh a gurin waye mtslr take insha'allah za'a samu waraka....."
Aliyu abbas yaji dad'i sosai sbd burinshi yasamu wannan waraka...,kasancewarshi shi kad'ai bayada yn uwa idan yasamu d'iya zasu zama sanyi idaniyarshi..,yayi godiya tareda neman abunda za a bayarwa...malam ibrahim yaqi amsa kuma yanuna baiji dad'in zancenshiba nacewa zai bashi wani abu domin ai sunxama yn uwa ynx....
Anyi hakan da watanni akafara umfani da maganin da akace dukansu zasusha before suyi sex..,hakan kuwa suketayin umfani da maganin har tsawon watanni shiru dai babu lbr...,koh malam ibrahim abun yabashi mamaki...,hakan suka sanyama sarautar Allah ido....
Lkchn da sukacika 4years da aure lkchn ne binta tafara rashin lfy mai tsanani wadda dukansu basu ta'ba tsammanin ciki bane domin wahalar ciwon tayi yawa....,hakan suka d'ugunzuma zuwa assibiti dukansu...,bincike ya nuna binta na d'auke da ciki har wata hud'u....murna gurin Aliyu da malam ibrahim ba acewa komai....suka dawo aka cigaba da rainon ciki....,aikin komai binta bata iyawa saidai Amina tashigo tayimata komai takoma gida....,
kasancewar malam ibrahim primary yake karantarwa hakan sai yake zuwa da Abdl-jabbar kullum...itakuma taji da aiki......
Cikin binta ya isa haihuwa...watarana sai tatashi da naquda mai sauqi..,nantake Allah yakawo haihuwar ya macce kyakkyawa kamar mahaifanta....
Dasauri mmn abdl tazagaya kiran nurse d'in unguwarsu dama tazo taje tadawo...akazo aka gyara baby da mai haihuwa...nan take tafara shaidama malam don yakira aliyun yafad'amashi....
Murna ba acewa komai duk da yaso ace namijine farkon haihuwarshi amma koh ynx alhmdllh bakomai Allah ya rayamasu *fatima* sunan mahaifiyarshi kuma sunan matarshi...yasanyamata....
Farinciki da murna ba acewa komai...yashaidama yn uwan binta da iyayenta domin sukad'ai ke gareshi yn uwa don yn uwanshi bazasu amsaba koh yafad'amasu.....
Ranar suna yn uwan binta sunxo domin mahaifinta yace tayi jegonta gidan mujinta..,tunda sun samu masu taimaka masu...akayi buki aka qare yn uwanta sunkoma da murna domin sunga binta cikin wadata da yalwa...kayan barkarta duka masu kyau dakuma yarinyarta..wadda suke kira da *{FARHA}* farinciki kenan....
Zama mai dad'i sukeyi itada aunty amina domin sunan datake kiranta dashi kenan....,koh yaushe farha na gidansu malam ibrahim...,domin abdl-jabbar cewa yakeyi qanwarsace..,kuma bamai ta'bata sai shi...,duk gidan da take yana cen...mkrnt kad'ai ke rabashi da ita....
Farha na girma tana qara wayo domin koh barci takeyi dataji muryar abdl xata falka tayita miqo hannu ya d'auketa...,tun ana hanashi har yakai basa hanashi ita....shike renonta koh yaushe...hakan yasa iyayen ke qara shaquwa tsakaninsu.....
Farha nada shekara biyu aka yayeta...domin tuntana shekara d'aya da wata biyar taso yayenta amma mmn abdl tahanata...duk da farha ta iya tafiya ga baki amma saida tayi shekara biyu a nono.....
Har farha tayi shekara ukku mamarta bataqara samun cikiba...,saida tayi ukku da rabi sannan taji alamun ciki jikinta hakan yasa farha takoma gidansu abdl-jabbar zama sbd suma suna buqatar hakan.....
Ba adad'eba ta haifi khadijatul{IMAN} wadda taci sunan mahaifiyar binta shine suke kiranta da iman wadda gareta babansu yasan cewa lallai ya d'ebo gadon gidansu kenan...d'iya matane arziqinshi..,toh Allah yarayamashi su shiriya ta addinin musulunci...suka cigaba da renon yayansu a kyakkyawar kulawa....
Hakan kowanne mutun zaiyi tsammani farha da abdl-jabbar da iman uwarsu d'aya uba d'aya duk da iman batayi haskensuba...amma zaka d'auka gida d'aya suka fito.....
Farha nada shekara 6 tana primary 1 abdl-jabbar kuma yana shirin zana j.s.s exam..inda iman koh shirin sanyata ba ayiba domin ynx takeda shekara ukku cikin ta hud'u...amma tamatsa hakan babansu yasakasu dole guri d'aya da ita..aka sakata nursery1..hakan yake kaisu a mashin d'inshi kafin yawuce gurin aiki....
Prvtschool yasanyasu mkrntar masu hannu da shuni domin yanason suyi ilmi mai yawa...,suzama abun alfaharinshi koh da bai samu 'ya'ya mazaba suxamo sanyi idanuwanshi...,hakan yata jajircewa tareda mahaifiyarsu gurin ganin sun samu karatu mai yawa....
Abdl-jabbar kullum shine lesson
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 44