kashe tsohon mijin da kikayi ik'irarin shine za'binki, bayan ya mutu, ya dasa maki ciwon angano ank'i aurenki, shine umma zata sayaman wahala, toh wallahi ba dani ba, zanbi umurninta na zauna da ke a matsayin garkuwa, amma gada kiyi tunanin kinyi auren dad'i, sai dai wahala wallahi, "
Bankad'eta ya k'arayi ya wuce a gurin, Farha hannu ta'aza saman kai tare da rufe bakinta, ai d'akin umma bazai shigu ba, dole komawa tayi d'akinta tana kuka, babu yadda ta iya dole sai hak'uri domin wallahi babu yadda ta iya, dole tayi hak'uri, wata k'addarar kenan da zata risk'eta, kuma a yanzu bakin al-k'alami ya bushe, domin babu wata mafita an riga da an d'aura, ita kuka Ikram kuka, rungumeta tayi tare da saka ma d'akin key, saboda taji wanda zai shigo, ganin farha na kuka yasa ikram itama kuka, ganin abun zai zamar masu ciwo, ga ikram na kuka bayan batasan menene farha kema kuka ba, hakan yasa ta share nata hawayen ta aza Ikram d'in a k'afarta tace......
"Ikeey nah, menene kike ma kuka? Kinga aunty farha na kuka koh? Toh ki daina nima na daina, dama kinga yau zamuje sabon gida koh? Toh kukan murna nakeyi, kuma har da abbanki zamu koma, kinga dole muyi kukan rabuwa da umma koh? Toh ki daina nima na daina, bari na tashi nayi maki wanka, kafin ak'arasa taruwa kiyi kyawonki zamuje sabon gida ko ikeey nah?"
"Eh Aunty farha, kisaka mani janbaki, kuma kisaka mani wannan abun da kika saka ranar "
"Toh zan saka maki yanzu ma, zo na cire maki kaya koh?"
Firar da farha tayi da ikram kad'ai, sai taji komai ya yaye mata a rayuwarta,hakan yasa taci gaba da hidimarta yadda ya kamata, rasheeda murna ta tayata, domin samu namiji kamar Abdul-jabbar, abun farin cikin koh wace macce ne, sai dai sai da tak'aramata nasihar yin hak'uri rayuwarta.
Farha jinta kawai takeyi, amma tasan inda zancen ya kwana, domin tasan ita da rayuwar aure mai dad'i kuma har abada, domin tasan zaman da zatayi koh yanxu bamai dad'i bane, don haka taci alwashin daga umma har rasheeda babu mai k'ara jin sirrin zaman aurenta, addu'a da hak'urin nan shi zata ci gaba da yi kawai, don haka sai ta saki jikinta taci gaba da hidimar gabanta.
Aunty hafsart d'irka mata gyara kawai takeyi,amma da tasani da ta raba kanta da wahala, ita da aka kira ragin maza, ragin ciwo, toh ina wani kadari kuma gareta gidan aure? Amma batason tayarma kowa da hankali, domin abun ya tsaya a haka kawai shine zaman lafiyar, koh yaushe akanta ake tashin hankali, insha'allah yazo k'arshe, koh da Abdul-jabbar zai yanka namanta bazata ce k'alaba, domin tasan hakan shine zaman lafiyar ta.
★★★
"Ango Ango, wallahi nayi bala'in jin dad'in wannan had'in aure da akayi, amma wai Abdul- meyasa aka fasa auren Hisham da Farha?"
"Zamu raba hanya dakai wallahi, duk ka k'ara kirana Ango sai munyi 'bacin ran da ni dakai bazamu k'ara gaisawa ba"
"Subhanallah! Abokina, basheer ne fa? A yau nine za'a k'yale? Toh ai nasan bazaka iya ba, domin ni da kai hanta da jini ne "
"Zakaga yadda ake rabasu kuwa, idan akan wannan zancen shegen aungon ne, kai nifa babu abunda ke 'bata man rai kamar wai and'aura aure na bansani ba, kuma shegen d'an iskan mijin da tabari ance cututtuka ya kamu dasu wayanda koh zama ba'ason yi kusa dashi,sannan sun rabu bayan shine wanda takeso, ka ko ga itama ai bazata rasa su ba, kuma bala'in ma ya tsaya nan, ko da ace bata da cutar komai, wani yafara bud'e ledar ta, sannan ni a had'ani da ragi, wallahi ni ko na zauna da ita babu abunda zan iya yimata, kuma bazan iya bata soyayyata koh d'aya ba, zanbi umurnin umma amma wallahi adalci nasan zuciyata bazata iya bawa waccen yarinyar ba, domin babu sonta koh kad'an a zuciyata "
"Innalillhi! Yanzu dama, saboda hakan Hisham yak'i auren farha, shine umma kuma zata d'aura da kai? Toh ai zai iya yuyuwa kaima ta saka maka wata rana, amma kasan yadda za'ayi? Idan hankali ya kwanta ka d'auketa kuje assibiti ka k'ara tabbatarwa, gudun gada 'barna ta afku ba'a sani ba, sannan mu'amalar da ita da kaine Allah bai yanke ba, toh tunda yanzu ta gyara halayenta, kayi hak'uri komai ya wuce"
"Na kaita ayi gwaji? Toh halan angayamaka, ni idan naganta sha'awata tashi take yi da zan nemi wani abu gurinta? Wlhy idan inada sha'awa kusa, toh idan inason na nemi sha'awar na rasa, toh na had'u da waccen yarinyar, nan take zakaga abur ta kwanta, kai koh da nake da mugunyar sha'awa, ba ga matan da wasu suka gama kichaniya saman su suka k'areba suka sako nakeyi ba, ga yarinya wadda nasan idan na rik'ata ni zan bud'e abuta kuma na kulle abuta ba, yooo wadda kasan ta zama taga a gadon wani ai ni batada kadari gare ni, YA ALLAH KAJIK'AN IMAN, iman mace ce wadda ta tara duk wata rahama, hakan nasani jin na tsani koh wace macce, toh da nayi rayuwar aure da farha, gara na koma abuja na auro kareema hakanan, koh banza ita budurwa ce"
"Ah ah Abdul-jabbar, itama kareemar yanzu haka bakasan iya mazan da suka k'are saman kanta ba, domin 'yan matan bariki yanzu sai addu'a, gara farha dubu da ita, domin ita a tafarkin aure ta samu hakan, kuma da tanada ciwon da kai kake tunani wallahi da umma bazata bari a yi auren nan ba, bafad'amaka k'addara ta kawar da komai, ka d'auka hakan shine alkhairi a kanka kawai "
"Naji imamu, a bar zancen kawai"
"Umhmm, ka fahimta koh gada ka fahimta, zansha kallo, domin ni nasan farha da gani irin matan da ke maida tsoho yaro ne,kuma gamu kallo yanzu dai, katashi muje muga yadda gidan yake na G.R.A d'in, tunda umma ta rantse yau zata tare"
"Hmmm! Wallahi andai cutan, kuma banida ikon hanawa"
Suka fito suka kama hanya zuwa gidan, ko da sukaje komai angyara, har anfara zuwa ganin gidan, hakan yasa suka dawo, Abdul-jabbar cikin zullumi kawai yakeyi, domin yasan babu adalcin da zai iya yima farha a zuciyarshi, don haka babu ruwanshi ita tasiya da kud'd'inta.
Da dare aka shirya kai amarya, gida masha 'allah, farha taci kuka, kuka mai cike da alhini, amma kuma addu'a ita tafi yawa a zuciyarta.
Aunty hafsart tabata wasu miyagun sinadarai na bala'i, tace amma sai in zasu kwanta zata saka su, kamar turaren da wasu kayan, kar'ba kawai farha tayi da cewa "toh"
Amma hankalinta baya gareta.
kasan cewar Ikram tayi barci, umma tace abarta sai da safe, za'a kawota, farha bataso hakan ba, domin tasan a daren yau ita zata zamo mai share hawayenta koh da a fira ne, amma kuma bazata iya musu ba, hakanan suka taho.
Amarya farha a gidan angonta Abdul-jabbar, da tsohuwar zuma ake magani, inji yan karin magana, aka watse aka bar farha ita kad'ai kamar mujiya........
_Toh fa, gamu dai zuwa, zamuji yadda wannan zaman doya da manja zai kaya a gidan Ango Abdul-jabbar da amaryar shi farha._
_Mudai je zuwa nawas.😍_
~Ta masoya~
*Bee Been masoya*💞
[3/13, 12:08 AM] +234 814 230 8036: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*_ASTAGFIRULLAH, ALLAHUMMA AGFIR LANA, WALIL-WALIDEENA, WA LIMAN SABAK'ANA BIL IMAN,WALIL MUSULIMINA, WAL MUSLIMAT, AL AHAYA'U MINHUM WAL AMWAT_*👏🏻👏🏻👏🏻
Page...
★5⃣7⃣★
Bayan an watse, akabar farha ita kad'ai cikin d'aki, tanata rusar kukanta, kukan tausayama rayuwarta, domin tasan ita da kwanciyar hankali kuma sun yi hannun riga, don haka sai ta share hawayenta, domin tasan wahala kawai zata d'auro ma kanta aciki.
Mik'ewa tayi ta cire mayafin jikinta tare da duba yadda tsarin d'akin nata yake, a cikin part d'in nata, da ka shigo k'aton fallow ne mai d'auke da d'akuna guda ukku, a cikin d'akuna biyu, koh wanne da gado da wardrobe nashi,kuma koh wanne d'aki da toilet ciki.
A yanayin gyaran d'akin duka ya nuna na mace d'aya ne ba tare da mujinta ba,sai kuma d'ayan d'akin da ta bud'a, anan taga d'akin baby ne, hakan ya tabbatar da wannan d'akin Ikram ne kenan, domin ga kayan da tasaya mata nan wayanda da a gidan hisham za'a saka su, a d'akin da ikram zata zauna, hakan yasa taji wani farin ciki na kusanto zuciyar ta.
Zaunawa tayi kusa da inda pic d'inta yake da ita da ikram d'in suna murmushi, sannan itama tayi murmushi ta shafa photon tace.....
"Ikram! Albarkacinki, zan juri wulak'anci, zan juri azaba ta gidan aure, insha'allah zan zamo maki uwa ta gari wadda zata zauna da mahaifinki komai tsanani da wahala,ikram inasonki so na har abada, domin ni uwace gareki, bazan ta'ba bari ki zubar da hawayenki ba har abada "
Wannan zancen kawai da takeyi, sao taji gabad'aya batada damuwar komai a zuciyarta, sai wani qwarin gwuiwar mik'ewa tayi tare da murmushi tace....
"Hak'ik'a gidan ya had'u, duk da banga sauran part d'inba, kenan wannan duka nawane, toh Alhmdllh, ni farha wannan kad'ai zaisa nadinga dagewa da addu'a akan lamarin mijin da Allah ya k'addaro zamuyi rayuwa dashi, kuma na k'ara juriya akan abunda zai biyo baya domin ni na janyo hakan tun farko "
Fitowa tayi ta k'ara lek'a fallown babban fallown na gidan baki d'aya, acen ta hango kitchen yake kenan, sannan da wani part thesame nata, amma bata matsa ba, sai ta koma d'akinta ta fad'a toilet don yin alwallah tayi sallah, tare da rok'arma kanta hak'uri da zaman lafiya.
Bayan tayo alwallah, ta cire kayan jikinta da saka doguwar rigar sallah, tafara jero nafil-fili, a ko wace raka'a biyu zata sallame, sannan ta d'aga hannu zuwa addu'oi wayanda daga ita sai mahalincinta suka san me take rok'awa kanta, amma kamar zan iya gano biyu daga ciki.
Ta farko iyayenta da yar uwarta, domin ina ganin tana hawaye lokacin fad'in wani abu daga ciki.
Ta biyu kuma nemama kanta sauki akan matsalar gidan aure da zata risk'eta, ga wani mugun so nashi da aka azamata tsakanin jiya da yau, domin duk motsi d'aya sai ta tunoshi sau goma, sai dai ta makaro, domin ita tasan bazata ta'ba dawowa ba a matsayinta na da.
Hakan yasa ta dage akan rok'on Allah, domin jarabawa na hawan kanta kala-kala, d'aya daga ciki itace kalmar k'auna ga Abdul-jabbar.
Da wannan addu'ar da takeyi, tayi fatiha, tare da shafa addu'ar, ta mik'e cire kaya da saka rigar barcinta mai kauri ta kashe wutar d'akin, bayan ta rufe d'akin nata da key, sannan ta shiga d'ayan d'akin d'aya ta kwanta hankalinta kwance, tana tuna Ikram yadda zatayi in tatashi bata ganta ba.
Abdul-jabbar, gabad'aya duniyar tayi mashi zafi, don haka da basheer yace zai rakoshi, cewa yayi...
"Tunda auren sonshi nakeyi da zaka kaini gurin wata amarya cen, wallahi ko ina bazan shigaba, don haka kawuce gurin matarka munafuki, sai yanzu ma nake tunanin, koh harda bakikinka a had'ani aure da waccen banzar "
Zaro ido basheer yayi,tare da rik'e baki yace......
"Matarka ce, kuma yar uwarka,idan kayimata adalci kai kaso, ni kaga tafiyata gurin iyalina, na amshi taro mai kyau"
Wucewa basheer yayi, yabar abdul-jabbar a tsaye, shima komawa yayi cikin tsohon gidan nashi, ya d'auki wasu kaya da yake buk'ata ya kama hanyar gidan amaryarshi.
Shigarshi gidan, ya shiga babban fallow, tare da kayan da yake buk'ata, ya bud'e d'ayan part na gefe ya kunna wutar ciki ya shiga.
Shima hankalinshi kwance, domin ko tunanin yadda farha d'in take bai kawo a ranshiba, ajiye kayan yayi sannan ya cire rigar jikinshi ya d'aura towel zuwa toilet yayi wanka da alwala.
Karasa wankan yayi ya fito, yasaka jallabiyarshi da shinfid'a dardumar sallah ya gabatar da nafilar da yasaba kafin ya kwanta, ya k'arasa tare da d'aga hannunshi ga Allah ya rok'eshi buk'atunshi, kamar yadda ya saba.
Bayan ya k'arasa ya cire jallabiyar, tare da kashe tashi wutar ya kwanta, sai dai tunani ya hanashi sakat a zuciyarshi, hakan ya samu da kyar barcin ya ziyartoshi har asuba.
Farha tatashi da wuri, tayi sallah d'inta, tare da karanta alk'ur'ani mai girma, da azkar kamar yadda tasaba a cen gida, ta k'arasa tare da kwashe kayan karatun nata, sai dai kuma 7:00am yunwa take ji sosai, ga kuma kewar Ikram don haka ta d'auki waya tafara kiran Umma, nan take Ummar ta d'auka tare da cewa.....
"Toh kiyi shiru mana, ga aunty taki ta kira, itama takasa jurewa, kinga tunda safe ta wani kira "
Dariya farha tayi sannan tace...
"Umma ina kwana?"
"Lafiya k'lau fatima, ya bak'on wuri?"
"Alhmdullah umma"
"Toh masha'allah, ga d'iyarki yau da kuka ta kwana fa "
"Umma don Allah a kawo man ita, wallahi duk naji babu dad'i, rashinta tare dani "
"Hmm! Uwa da d'iya kenan? Rabuwa da d'iyarki bakiji dad'iba, amma rabuwa damu iyayenki kinyi murna, gaki dad'i aure "
"Ah ah Umma wallahi ba haka ba, ai ko ke nasan kinyi missing d'ina sosai, sai dai idan nace zanzo bazaki barni ba, amma ita ai zaki yarda tazo gurina "
Umma dariya tayi sannan tace.....
"Hakane farha, Allah yaba ku zaman lafiya, da hak'uri da juna, kiyita hak'uri da duk abunda zaki gani, nasan zakiji dad'insa da yawa nan gaba sosai, biyayya tazamo makaminki a gareshi, nasan zaki ji dad'i sosai farha"
"Insha'allah umma gada kuyi shakku akaina, kuma bazan ta'ba damuwa da duk abunda zai faru dani ba, bale nasan insha'allah komai zai wuce, 'bacin rai ne kawai, ni dai burina a kawoman Ikee na Umma "
"Toh masha'allah farha, bana shakku koh haufi akanki, domin nasan kinsan kanki, kuma d'iyarki, idan su auntynki Hafsart zasu zo zaki ganta "
Sukayi sallama, sai taji wani k'warin gwuiwa akan wayar Umma a kanta, hakan yasa ta kama hanyar kitchen d'in taga ko akwai abunda zata break da shi?
Hanyar fita fallown nata tayi, tare da bud'e key d'in dakin tayi, tare da lek'owa da kanta, ko da motsin shi, amma shiru babu kowa, hakan yasa ta kama hanyar kitchen d'in da zunbulelen hijab nata cikin tsoro, domin iya gaskiya tsoron su had'u itama take yi, don batason 'bacin rai yanzu.
Tashiga kitchen d'in ta duba babu abunda za'ace a dafa yanzu a ci nan take, don haka tafito cikin zullumi, dole tasha tea hakanan koh babu komai domin taji sauk'in wannan yunwar.
Jin ana knocking d'in k'ofa yasa gaban farha fad'uwa, kamar tayi d'akinta tayi shiru, kuma sai ta dawo ta bud'e, tare da lek'a kussuwar, malam bala tagani d'auke da abinci, da sauri ta qarasa bud'e k'ofar fallow d'in, suka gaisa ta kar'bi kayan ya wuce, tayi murmushi tace....
"Allah sarki Umma, dole nayi biyayya da abunda kike so, saboda kinyiman abunda uwa kawaice zata iya yima yarta, Alhmdullh kawai"
Ajiye foodflax d'in tayi akan dining ta gyara zaman kayan abincin tare da d'auko plate ta zuba tata wainar da tayi kyau har tagaji, ga miyar agushi, da dak'walen kaji, zubawa tayi ta d'auka zuwa fallown d'akinta, ta d'auko ruwa da lemo ta ajiye tafara ci hankalinta kwance, ta k'arasa da hamdala, sannan ta mayar da kayan zuwa kitchen ta wanke, takoma d'aki tayi wanka tare da yin kwalliya simple, tasaka doguwar rigar atamfa, tayi shegen kyau.
Farha mai kyauce koh babu kwalliya, bale kuma ita ma'abuciya son kwalliyace, anan kad'ai da award nata da mata zasu bata.
Fitowa tayi babban fallown gidan, tare da kunna kallo don gada tajita shiru, tun da har yanzu su Aunty hafsart d'in basu k'araso ba, ba laifi ta samu nishad'i da film d'inda take kallo, domin indian love story ne, soyayyar ta burgeta, amma kuma tana sha'awarsu ne kawai, domin ita tasan soyayya kuma sai lahira idan ana sake yin wata, domin tasan bazata ta'ba k'ara samunta ba, ga abokin yin soyayyar nata da aka bata, hakan kawai sai taji hawaye na cika mata ido, nan take sai ta tuno da tayi ma kanta alk'awalin cewa bazata k'ara saka rayuwarta a tunani ba, sai ta tsaya sannan zata ga takaici, amma idan bata tsaya ba, ai baza'ayi da ita ba, hakan yasa ta jawo farin cikin dake ziciyarta taci gaba da kallonta.
Jin motsin k'ofa alamar an bud'eta yasakata juyo da fuskarta da sauri zuwa inda taji k'arar k'ofar domin ganin waye?..........
_kuyi man afuwa🙏🏻, wallahi busy nake mai yawa,amma na fara samun saik'in shi, shi busyn ba, kuyi hak'uri da wannan ba yawa, yanxu hakan ina typig ina barci, saboda gajiya._
*Bee Been masoya*💞
[3/14, 7:10 AM] +234 810 918 8883: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
Page...
★5⃣8⃣★
Dum! Gabanta ya fad'i, domin ganin wanda ya turo k'ofar, gyara zamanta tayi, tare da duk'ar da idonta k'asa da sauri, d'an had'a idon da sukayi dashi, gabad'aya jikin farha rawa yakeyi, domin taga yadda fuskarshi take, ta rasa meke sata jin tsoronshi, domin ko ba komai, zai fad'amata maganar da zata 'bata mata rai,ita kuma a yanzu bata burin abunda zai ta'bi rayuwar ta.
Takunsa taji yana k'arasowa gaban t.v dake kunne, hannu yasaka yayi switching d'in t.v, sannan ya juyo zuwa gareta tare da nad'e hannuwansa a k'irji, ya had'e fuska yace.....
"Wasu sunk'i, ni kuma an manna man ciwo da mutuwa kusa dani, toh ki sani wallahi ki dinga nesa dani, domin banason zaman mu na yawaita guri d'aya saboda tsaro, sannan shigowa wannan fallow d'in, na hanashi idan ina cikinshi, ki tsaya a iya inda aka tilastani na ajeki, umhmm! Kina sane da gidana ne ba gidan kowa ba, don haka ki gane nufina "
Farha kamar tayi magana, amma kuma sai wata zuciyar tace "ah ah farha yi shiru, koh kin manta da alk'awalin hak'urin da kika d'auka jiya?"
Nan take sai farin ciki kuma yazo mata, d'ago fuskarta tayi tare da cewa.....
"Yi hak'uri, wallahi bansan da wannan dokar ba, saboda ai ni bak'uwace, kuma bansamu rules and regulations d'in gidan a rubuce ba, da bazan taka dokar zaunawa a yanzu ba,amma tunda yanzu naji wak'a a bakin mai ita, insha'allah zan kiyaye "
Koh kallonsa batayi ba, ta mik'e zuwa d'akinta, shigarta kenan ta share hawayen da batasan da zuwansu ba, jin ana surutu a fallow ne yasa farha saurin share idonta, domin batason kowa yasan damuwarta.
"Wai ina amaryar take ne? haka ake yi? Ango fallow amarya kuma bata kusa?"
Inji wata kakarsu Abdul- jabbar da tazo bukin.
Aunty hafsart rik'e da ikram a hannunta, taga mahaifinta amma bashine take son gani ba auntyn ta farha, tura k'ofar aunty hafsart tayi tare da rik'e baki, ikram da gudu ta fad'a jikin farha tana murna, rungumeta farha tayi tare da cewa.....
"Missing u my luvly Ikeey? Ya kika baro umma?"
"Shine kika zo sabon gida kika barni a cen ni kad'ai,ni ma bazan koma ba "
"Eh nima bazanbar Baby nah ta barni ba"
Dariya sukayi dukansu harda aunty hafsa d'in da ke kallonsu cikin burgewa, zaunawa tayi gefen kujerar fallown farha d'in tare da cewa.....
"Farha, wayace maki amarya na baro angonta shi kad'ai? Ai duk inda yasaka k'afa kema ki saka taki, wannan lokacin shine lokacin da xaki mori amarcinki,farha ki fara renon mijinki da kalar taki rayuwar, domin yanzu da tsohuwar rayuwarshi ta aure zai reneki, ki kusanci mijinki sosai farha, anan zaki fahimci kalar rayuwar da yayi farko da iman, in akwai na d'auka ki d'auka, sannan ki k'ara da naki farha, gada ki bani kunya, yadda kike da diri d'innan, gaki macce har mace,gada ki bari wata ta ribanci zuciyar mujinki kinji, ki daina barinsa shi kad'ai babu kyau "
Farha k'ara rungume ikram tayi, sannan ta kalli aunty hafsat tayi murmushi tace.....
"Aunty har kinsa naji kunya wallahi, tare fa muke dashi, yanzu, kinsan yadda zuwan namu auren yazo, dole sai a hankali, domin kunya bazata bari nan take a fara bayyanar da doguwar tarairaya ba, amma nan gaba kad'an aunty sai kinsha mamaki, farha fa ce "
"Nasani,kuma nasan jininmu bazai ta'ba bari wata maccen tafishi a gidan aure ba, tun daga gyaran jiki har gyaran makwanci, don haka turaren da nabaki, ki dinga using dashi, idan ya k'are zan k'aro maki wani, domin inason ki zama star a rayuwar aurenki, ki zarce iman a zuciyar shi, wanda sai dai ya bita da addu'a, saboda yanzu ke ce tashi "
"Insha'allah zan kiyaye"
"Toh mu zamu wuce,amma ki fito ku gaisa da kakar abdul-jabbar, saboda yau zasu koma "
Fitowa tayi, suka gaisa, ta kawo masu ruwa da drink,suka sha suka wuce, anan aka bar ikram.
Farha dad'i kawai take ji, na ganin Ikram, domin zata rage kewa da yawa.
A part d'inta, yinin ranar suka wuni, sai dai idan Ikram nason wani abu, farha ta bi ta baya, ba ta fallow ba, tayi abunda takeso a kitchen da sauri sai ta fito.
Kwana ukku yau da aurensu, farha bata k'ara ganin Abdul- jabbar ba, sai dai taji tashin mota da dawowar motar, A dalilin hakan yasa Ikram ta fara kukan son ganinsa, amma babu dama domin saboda farha, shiyasa itama ya hak'ura da ganinta.
A wani daren laraba, Ikram tayu barci, farha ta tuno da wayar da Umma ta bata ta Iman da tace a bata, saukowa tayi ta bud'e drower d'inta cikin hand bag nata ta d'auko wayar ta kunna, ta gama searching, tafara shiga gurin da document yake, taga an rubuta......
*"RAYUWAR AUREN IMAN DA ABDUL-JABBAR"*
Tasamu gefen gadon ta kwanta, tare da gyara kwanciyar ikram, itama ta jawo pillor tare da fara karantawa kamar hakan...........
_Masoya toh fa, sai hak'uri, domin wallahi busy nake, kuma ina shirin tafiyane, shiyasa zaku d'an jini shiru, amma idan nasamu chance zaku dinga ganin posting koh babu yawa, domin mu k'arasa da wuri, kuyi ma bee been ku afuwan da small page da zaku dinga gani daga gobe, har ranar monday insha'allah_
_ku sakamu addu'a, zuwa lafiya, dawowa lafiya, katsina on top,👍🏻 ranar friday._😂
*Bee Been masoya*💞
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAHðŸ˜ðŸ˜*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
_so mai sonka, kabar wanda baya sonka, yi da mai yi da kai, ka share wanda ya share ka, duniya ce, Allah ka karemu da sharrin shaid'an, da miyagun k'addarori, da musibar zamani._
Page..59
*"RAYUWAR AURE NAH, NI DA YAYA ABDUL-JABBAR"*
_"Sak'ona nasan zai isa gareki yayatah, nasan ko ina raye ko bana raye, watarana dole zakiji hakan daga bakina, domin ko da baki samu sak'ona a wayata ba, zaki iya samunsa rubuce, domin na rubuta na ajiyeshi akanki yaya farha"_
Gyara kwanciya farha tayi tare da juyawa gefe d'aya, ta k'ara zooming d'in text d'in dai-dai, sannan taci gaba.
_"yaya farha, kece wadda yaya Abdul keso, kuma kece wadda zuciyarsa keso, kece first love
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 44