ga uwa uba gyara makwancin shi, ga iya soyayya da iya kalamai masu tausasa zuciyar mai jinsu, ga biyayya, ga uwa uba ni'ima da Allah ya tanadar mata, wadda wannan shikad'ai yasan iya darajar abun a gurinshi.
Iman na sadaukar da farincikin ta domin ta kyautataman koh da zata cutu, ahakan wazai yimashi yanzu har ya iya gabatar da aikin shi cikin farinciki kuma ya dawo gida a farinciki? Wayannan tunanen ne ke hana abdul-jabbar samun lafiyar zuciyar shi, kullum ramewa yake yi, abinci sai umma ta matsa mashi yake samu yaci, sannan ta k'ara yimashi wa'azi akan girman abun da yake yi, ya saki ranshi da walwallah Allah zai musanya mashi wata wadda tafita insha'allah.
Shi umma mamaki take bashi, "wai wadda tafi iman?"
Shi a rayuwarshi ai gani yake yi soyayya kuma ai ya ajiyeta, kuma bashi ba k'ara aure domin maganinshi zai siyo ya dinga shan abunsa domin yasan babu maccen da zata iya yaye mashi damuwar shi kamar yadda iman ta yaye tashi, hakan kesa kullum cikin damuwa yake, kuma bazaiyyi auren ba, domin babu maccen da zata 'bata mashi rai ga banza wlhy, koh yar gidan ubanwa ce ya mazgeta koh, toh gara ya sanya ma kanshi sanyi.
Wannan Rayuwar tasaAbdul-jabbar ya dawo d'akin umma a 3sitter nan yake barci, kuma nan yake cin abinci, wankan ma wataran a nan yake yi, dama yanzu saboda baya zuwa koh ina, indai ba Basheer yazo ba koh kuma ikram ke tare dashi toh Abdul-jabbar koh firarsa bazakaji ba, shifa shikad'ai yadan yadda yake jin wannan ka d'aicin, domin dukan su ganin yake yi baza su gane komai akai ba.
Hakan yasa baba yin tattaki da ga gidan shi zuwa inda yake, ya kirashi fallow d'in yafara magana da shi kamar hakan.....
"Abdul-jabbar, dama gurinka nazo akan zancen komawa aikin ka, yanzu kusan 3month da rasuwa amma har yanzu baka koma ba? Ance anturo maka text na kakoma aiki kace suk'ara maka 2weeks, toh wai kai da kake namiji zaman juyayin me kakeyi idan kayi imani da Allah? Toh kenan kaima takaba kake yima iman kenan? Tunda kak'i kayi abunda Allah ya horeka da kayi, bari nafad'a maka gaskiya kaji, kasan nafika sanin dad'in aure koh? Ak'alla tun kafin a haifeka nayi aure zama kuma na aminci da matar da ta haifaman d'iyar da kai kake juyayin rasata bale ni, kakoh ga ni yakamata na shiga irin hakan bakaiba mai shaikara biyu da aure, amma gashi na manta komai ina zaune cikin mutane ina walwalata, kuma ba don bana tunawa da itaba, don haka gobe ka gyara ka koma aiki "
"Toh baba insha'allah, gobe zan koma, amma naje da ikram koh?"
"Acen wazai rike maka ita idan zakaje aikin? Kuma wahalar da kanka kawai zakayi domin ni nasan ikram bazata biki ba,domin bata damu da kaiba kamar yadda ta damu da auntyn ta farha ba,don haka kajaye zancen zuwan da ita, amma idan kasamu mata kayi aure sai abaka ita kutafi tare "
"Aure kuma baba? Ni gaskiya aure bance bazanyiba amma ba kusaba "
"Hmmm toh naji, amma kasan nasan matsalar ka koh?"
"Eh na dad'e da samun sauk'in matsalar ai "
"Toh shikenan na gane, Allah yak'ara sauk'i kayi shiri ka koma, kuma don Allah kayi aski mana, ji fuska da kanka kamar wani mahaukaci?"
"Toh baba" kawai yace, ya mik'e zuwa part nashi ya shirya, saboda yanzu yana shiga tunda aka kwashe pictures nasu a fallown har na bedroom nashi duka babu idan na iman ne, sai dai duk da hakan baya 10mnt ciki zai fito, domin shima yanason ya cire damuwar ranshi koh zai dawo normal.
A hakan ya shirya komai nashi yafita don shirin tafiya domin jirgi zaibi gobe da safe............
*_wash🤦🏼♀ nagaji wallahi kuyi hak'uri, wlhy banajin garau, kiranku da text naku yasa na rubuta hakan, kuyi hak'uri mu had'u gobe_*
~Ta masoya da masoyan~
*Bee Been Masoya*💞
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*Life can give us lots' of beautiful persons, But only one person is enough for a beautiful life...♥*
Page...
★5⃣1⃣★
*AFTER 5Month's*
Rayuwa kenan, komai idan bakayi hak'uri kansa ba, toh kuwa wahala zata gano ka.
Da haka umma keta jan hankalin farha akan ta dinga mantawa da komai, ta daina zaunawa tana saka tunanen abun da ya riga ya wuce, kuma ta d'auketa a matsayin uwa wadda ta haifeta, domin ta d'auki alk'awalin rik'ata amana, kuma tanaso ta manta da mahaifiyar ta bata duniya, domin idan har Allah ya rayata da ita da ikram zata zamo masu gata a rayuwar su.
Hakan nasaka farha jin dad'i, kuma take k'ara sakewa da umman cikin kwanciyar hankali.
A koh da yaushe ikram na tare da ita cikin jin dad'i, domin ita batasan rashin uwa ba, Allah ya bata uwarta a hannunta, duk inda farha zataje suna tare da ikram, kasan cewar yanzu ta d'an samu hutu saboda k'arasa nursing nata, nan da 2month zata fara zuwa aiki.
A halin yanzu bakin ikram ya bud'e gaba d'aya, tasan me take so tasan abun da bata so, hakan yasa suke zama suyi ta firar su a d'aki, idan kaji farha na fira da ikram, sai ka rantse da Allah da babba take fira, amma da kashiga d'akin zaka ga ikram ce abokiyar firar.
Hakan yasa koh yaushe shak'uwace mai tarin yawa tsakaninsu, kuma farha bata barin ikram koh kad'an da damuwa, komai saya mata take yi, hakan mahaifinta na aiko da kud'd'i masu yawa ga umma domin gudun gada anemi wani abun a rasa, shiyasa koh yaushe account d'in umma cike yake da kud'di, ita kuma ta wakilta farha akan kud'd'in, duk abun da babu taje kawai ta siyo.
Tunda Abdul-jabbar ya bar garin kaduna, sau d'aya ya ta'ba dawowa garin da sunan _week end,_ koh yaushe cewa yake yi aiki yayi mashi yawa, amma zai dawo insha'allah.
Ba komai ke hanashi da wowa ba, sai face tunanin iman da yake yi a duk lokacin da zai dawo sukayi waya, zai tambayeta dame dame zai samu? Ita kuma sai tace *"sanyi nah dukan kaina da ruhina, da sassan jikina, a gobe idan zaka dawo na mallaka maka su a matsayi babbar kyautar welcoming naka"*
Toh wa'yannan furucin duka suke saka Abdul-jabbar jin idan yadawo, yasamesu gurin waye? Shiyasa ya zaunawar shi acen kad'ai zaifi mashi farin ciki, Ikram ce yake ji kuma yake gani a yanzu sanyi idaniyar shi, toh ita kuma bata damu dashi ba, tafison wannan munafukar Auntyn tata, toh tun da hakanne, Menene na yayi wahalar dawowa gidan? Umma ce idan sunyi waya ya bata hak'uri zata yar da.
★★★★
Farha a yanzu rayuwa takeyi mai dad'i, domin ta fara manta komai, da ita da d'iyarta kuma k'anwarta kuma abokiyarta Ikram cikin k'oshin lafiya suke, wajibine idan ka gansu kaji suna burgeka, domin farha da Ikram idan ka gansu zaune suna wasa dole abun ya baka dariya da farin ciki, hakan yasa umma na bala'in son tajisu gida, domin suna d'ebe mata kewa, ga uwa uba k'aunar da take yima farha d'in yanzu.
Kasancewar yanzu baba daga gidan umma ake kai mashi abinci, yasa koh yaushe farha itace girkin gidan, kuma ita ke gyara komai, saboda talatu tayi tafiya zuwa garin su, shiyassa komai ya koma hannun farha na gidan, domin bazata iya bari umma tayi komai ba, ita kuma gata zaune.
Wanda yasan farha 5month da suka wuce, toh a yanzu bazaka shaidata ba, domin mai hali baya changr halinshi.
Farha ankoma ma aikin gayun nacen baya da aka bari saboda ibtila'in rayuwa, yanzu kuwa mantawa ma takeyi da tata'ba sanin wani anwar cen abaya, domin gayu take sha naji da fad'i, sai dai na yanzu yasha bamban da nabaya, domin yanzu cikin hankali da natsuwa take yin abunta, babu wulak'anci, babu girman kai, babu dogon buri, sai dai mutuntawa da mutunci ga kowa, ga kunya da karamci da Allah ya sanya mata a rayuwar ta, hakan sai yasa kyawonta na yanzu tafi na da fitowa, kuma yanzu anfi samun doguwar wadata, domin gidan babu abunda zaka nema karasa na more rayuwa, hakan umma ke tule masu kud'd'i taje ta siyo masu kayan jindad'i da kuma nasakawa ita da ikram, wannan ne yakawo changing launi da kamani na su farha d'in domin basu cikin k'unci na rayuwa.
Baba yayi murna da jin dad'in ganin yadda farha ke rayuwarta cikin kwanciyar hankali, hakan sai Allah ya mantar dashi wani rashi da yayi, domin yaga bayan da aka barmashi yasamu kulawa da kuma cigaba a rayuwa,hakan yamanta komai kuma shima yana kawo nashi gudumuwar a cigaban gidan hakan yasa kowa ma yafara mantawa, amma banda Abdul-jabbar, don har yanzu da sauranshi acikin juyayin rashin mata.
Farha na kiyaye duk wani abu da tasan cewa, zai had'ata da Abdul-jabbar, domin tasan yanzu a duniya , babu mutumen da yafi tsana kamar ta, domin ganin yakeyi itace farkon fara nakkasa zuciyarshi, shiyasa koh yaushe da wancen halin na farko yake dangantata dashi, koh me zatayi wallahi baya ganin farinta, kuma idan dai sai yayi mata magana wallahi sai dai gada yashigo gidan nasu, hakan yasa ya sallama mata ikram d'in gabad'aya, idan dai Ikram na kusa da ita, in batazo inda yake ba, bazaya kirata ba, sai dai ko menene yazo dashi ya a jiye mata nan.
Bayan rasuwar Iman da kwana ukku suka had'u, ta gayar dashi sannan tayi masa gaisuwar rashin da sukayi, amma kallo d'aya yayi mata ya amsa
gaisuwar, bai k'ara dubanta ba,sai dai yayi masu addu'a daga cikin zuciyar shi.
Da wannan farha tagane cewa, Abdul-jabbar k'arshene a komai na rayuwa, yadda tayi tsammaninsa ba haka ta ganshi ba, domin rik'o gareshi ga rayuwarshi, sai itama ta kama kanta da sha'aninshi.
Yau dukansu suna fallow suna kallo tare da firarsu kamar yadda suka saba, Ikram na wasarta ta hau kujerar dining d'in ta fad'o, bakinta ya buge sai jini.
Kukanta da farha taji da sauri ta mik'e tsaye domin d'aukota, koh da ta duba bakin nata jini ke fita, nantake farha ta rud'e da sauri tace....
"Nabani umma! Bakin ikeey ta jimu wallahi, wayyo!"
Dasauri umma ta taso don dubawa, don ita farha d'in bata dubaba ta rud'e da ganin jinin, umma ta duba sannan tayi dariya tace....
'Diyar taki karambani ne da ita, ke kuma d'an banzar rakin tsiya, toh bakomai bane d'an bugewa ne, kitashi ki wanke mata bakin sannan sai a duba"
Da sauri farha ta d'auketa zuwa toilet, anan tayita wanke mata bakin nata, da anbata ruwan saita shanye, amma jinin fita yakeyi a bakin nata, anan farha taga jinin yak'i tsayawa bale taga gurin da taji ciwon.
K'ara fitowa toilet d'in sukayi, kuma Ikram d'in tak'i daina kuka, sai kiran bakinta takeyi, umma tamik'a hannunta ta kar'beta, amma wallahi tak'i zuwa, hakan farha d'in ta d'auketa don zuwa asibiti a dubata, domin jinin zuba yakeyi sosai yak'i tsayawa, gashi kuma bata da kayan aikin anan.
Goyata farha tayi, sannan ta d'auko gyalenta tare da handbag tata tafito da sauri.
Rolling d'in mayafin kanta tayi, sannan ta gyara goyon da tayima ikram d'in, gabad'aya bayan rigar farha jinine, da sauri tace....
"Umma sai na dawo"
"Kijira na kira dan ladi yakaiki mana "
"Ah ah umma bazan iya jiranshiba, kinji yadda take kuka, kuma gashi bakin jinin bai tsayaba, zan hawo napape kawai kiyi mana addu'a "
Juyowar da zatayi, taji tayi karo da mutun, kukan ikram ya hana farha jin motsin bud'e k'ofar, d'ago fuskar da zatayi, idon farha a cikin na Abdul-jabbar, nan take tajawo baya domin ya wuce sannan ita ta wuce, har zai wuce kuma sai yaji kukan ikram sosai na tashi ga jini yagani yana fita a bakinta, nan take cikin rud'ewa ya ajiye jikkar hannunshi yace.....
"Ikram meke faruwa hakan?"
Farha komai bata ce mashi ba, domin ko da ta amsa mashi k'yaleta zaiyyi,koh bak'ar magana, garama tayi shiru ta qyaleshi, wucewa farha tayi da ita da sauri zata fita yace cikin tsawa.....
"Amma dai kinji ina tambayar menene ya sameta koh? kuma kikayi shiru saboda gaki mai muzanta mutane ta koh wace hanya ba "
Farha taji bak'in cikin kalmarshi a gareta, amma kuma sai ta danne tace....
"Sauri nakeyi, domin inason nakaita asibiti, saboda jini ke zuba bakinta sosai, fad'uwa tayi "
"Hmmm sai ki bani ita nakaita koh,tunda na dawo?"
Farha ba musu tayi alamar sauke ikram ta bashi, domin tasan d'iyarshi ce kuma zaifita iko da ita sosai, juyo da ikram d'in tayi da alamar ya kar'beta, amma Ikram tak'i zuwa, domin duk yadda yaso tazo, wallahi tak'i zuwa gurinshi, hakan da Ikram tayi, shi yak'ara saka Abdul-jabbar jin kunya, amma kuma sai ya dake, domin baita'ba danasanin abunda zaiyima farha, domin baison ganinta koh kad'an.
Umma jin kukan Ikram na tashine, yasakata fitowa daga kitchen d'in, anan taga rikicin dake faruwa.
Tsaye tayi tana kallon ikon Allah, da sauri tace.....
"Abbanah, menene hakan? Kaduba bakin yarinyar nan jini ke fita sosai, kuma gashi ta fad'ine ba'asan inda jimuwar ta tsaya ba,kuma menene na jayayyar zuwa asibiti yanzu? Ita tasan mutane da yawa, domin gurin zuwanta ne kullun, kaikuma yanzu kashigo garin zakaji wuya kafin aganta,don hakan ka kaisu kawai asbitin a dubata, tunda tak'i yarda ka kar'beta "
Gabad'aya Abdul-jabbar yakasa musu akan zancen umma, hakan yasa ya juya domin cika umurnin kaisu asbitin.
Koh kad'an farha tsarin bai yimataba, domin ita yanzu, bata k'aunar wani abun da zai dinga tayar mata da hankali bayan tasamu natsuwa a rayuwarta, hakan dai tayi hak'uri da bi bayanshi da ya fita.
Wani had'e fuska yayi, sannan ya shiga motar ya zauna, ita kuma kwance goyon ikram tayi ta bud'e bayan motar tashiga ta rungumata.
Tsaki yaja sannan ya tayar da motar suka tafi...........
_kuyiman Afuwan da wanna, Wallahi banida lafiya, kunnena ke ciwo sosai,har ya kunbura, nadai daure nayo wannan, kusani addu'ar ku, Allah yabani sauk'inshi._
_Amma da sauk'i kuma, domin har naci Abinci yanzu, kuma gashi nayi typing, ngd ngd_
*Bee Been kuce,❤ Ta masoya*💞
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
_Enter PIN code..._
_Enter PIN code...L,_
_Enter PIN_ _code ...LO_
_Enter PIN_ _code...LOV_
_Enter PIN Code_ _LOVE....._
_wait......_
_PIN Accepted......_
_Welcome_
_;^ U ^; to v my HeArT❤masoya nah...._
*_Addu'ar ku Allah ya amsa, yabani lafiya sosai, ina godiya masoyanah, sak'onku nak'ara sakani azma wlhy, Allah ya barmu tare👏🏻_*
Page...
★5⃣2⃣★
Shigar su asbitin, da sauri farha ta bud'e k'ofar tafita da ikram, koh ganin inda take takawa batayi bale ta tuna da wanda yakawo su.
Fad'awa tayi G.O.P.D da sauri domin ganin wanda zai duba mata ita, hango doctor hisham tayi daga nesa, da sauri ta matsa tare da yimasa magana cikin damuwa....
"Doctor barka da yamma, ya aikin? Doctor please yarinyata, please yarinyata jini ke zuba tun d'azun daga fad'uwa "
A rud'e farha ke jero mashi gaisuwar, da kuma bayanin, k'ar'bar ikram yayi domin ya duba da kyau amma kuma tak'i aminta taje sai kuka take yi, yace tabarta su shiga office d'in sai ya dubata.
Farha tashigo shima ya shigo office d'in, a saman jikinta yafara duba ikram, hak'orantane na sama suka d'atsi la'b'banta na k'asa wanda saida hak'orin ya fasa le'ben yashiga sosai, dubawa yayi tare da wanke gurin sosai yasaka magani, sannan ya rubuta magani yace kawai taje pharmacy ta kar'ba basai ta biyaba inji shi.
Farha tace "Ah Ah doctor, da wannan kad'ai ma kayi mana taimako, amma inada kud'd'in sayen maganin kabari kawai mungode sosai, gashi duk na rud'e farko, amma gashi yanzu har tafara barci, wallahi mungode sosai "
"Babu komai sistr farha, sai dai naga rud'ewar taki tayi yawa sosai, sai kace wadda batayi training d'in aikin likitaba, wannan _so simple with you_ fa, amma duk kin rud'e _dear?"_
Murmushi tayi sannan tace....
" Oga hisham, tabbas nayi training akan aikin likita, kuma nafara sanin komai,tunda gashi next month zaku d'aukeni aiki idan nayi nasara, Amma a ciwon Ikram bazan gane damuwarta ba domin a rud'e nake ganin jinin jikinta na zuba, amma ai kaga yanzu normal nake, kuma nagode "
"Sister teemah kenan, kina dai ji da babyn nan sosai,toh Allah yasa zaki iya bani mallakin ta "
"Ita ikram d'in oga hisham? Ai Ikram sai ni mahaifiyarta ke iyawa da ita, domin duk wanda ya areta guna wajibi ya dawo da ita "
Sukayi dariya dukansu, farha ta gyara d'aukar Ikram a kafad'arta, tare da cewa.....
" mungode zamu wuce "
_"plz wait sister farha, dama akwai maganar da nakeson muyi dake amma narasa ta inda zan kama,kuma nasamu cikakkiyar gaskiya akan zance da kikayiman akwanakin baya nacewa ke matar aure ce,ashe ba haka abun yake ba, inason ki bani dama domin kawo maki ziyara har gida, muyi maganar data dace akan hakan "
Murmushi farha tayi, domin tasan yarigada ya ganota akan zancen da tace mashi ita matar aurece kuma ga diyarta nan Ikram, sai dai duk da ganewar tashi sai ta juyar da zancen da cewa.....
"Bakomai ina jiranka, sai dai Allah yasa kayi nasara oga, domin ni yanzu ba kowanne namiji ke gabana ba, saboda halinku sai ku bayin Allah, amma bank'i amsa gayyatarka ba, sai dai ina yimaka fatar sa'a "
"Ah abun sa'a ne kenan? Toh ai irinku da kalarku dace ake nema kawai, amma kisani kin had'a duk abunda koh wace macce yaci ace tanada shi, domin tun ranar da nad'aura wa'yannan idanun nawa,nagane lallai farha ba basira kawai ke garetaba, harda basirori masu yawa gareta, kuma ita ta dabance, amma wannan duka zancen, Abun adanawane da tanadi gareni har lokacin da fatar nasara d'in ta hau kaina, sai dai inason abani dama ta k'arshe wadda zankira waya Anjima"
"Nabaka dama oga, sai najika "
Tunda farha tafito motar Abdul-jabbar, sam ta manta da shi, hakan yasa da yagaji ya shigo G.O.P.D d'in yanata tambayar inda zai ganta, acen wani lebura yace mashi ga office d'in nan, tura k'ofar da zaiyi yaje muryar doctor hisham na cewa.....
"Ah ah gaskiya, ni ban yarda kibiya kud'in maganin Ikram ba, nine nan zan sayamata koh nawane, bale 5000 da bawani abu ba, Ai ummar Ikram da Ikram sun wuce hakan "
Dariya sukayi dukan su, farha natsaye bakin k'ofar fita,shikuma Oga hisham yana daga baya ya had'e hannuwanshi duka yana murmushi.
Turo k'ofar da akayine da k'arfi ya saka farha firgita, tare da ja baya tayi tsaye, Oga hisham kuma kallon ikon Allah yakeyi domin shi baisan wannan mutumenba, kuma gashi bayada Alama da mahaukata sai dai tsantsar gayu da kyawon jiki, hakan yasa shi saurin tambaya.....
"Malam lafiya kuwa,zaka shigo ga wuri amma koh sallama babu, kamar ba d'an musulmai b ?"
Kallonsa kawai Abdul-jabbar yayi sannan ya juya ga farha cikin fushi....
"Malama amma kinsan kinmanta dani a waje koh? Don haka idan zancenki na banza zakiyi, kina iya mik'oman yarinyar sai ki tsaya ki k'arasa abunda kikazoyi, kai kuma ni ba talaka bane da zaka sayama yarinyata magani kyauta don ka fahimta "
Nantake doctor Hisham yagane cewa kenan shine uban wannan yarinyar dake tare da farha? Toh idan shine mahaifinta, Toh yaya yake da farha d'in? Gada ace shine mujinta na farko, toh koma shine menene na wannan hucin? bayan sunrabu yanzu? Da sauri doctor Hisham ya yace....
"Sorry Abokina, ina baka hak'uri akan laifin da nayi maka na rik'eta, bansan cewa tare kuke da ita ba, sistr farha kuje, zan kiraki mu k'arasa zancen "
Ya juyawarshi yakoma sit nashi ya zauna.
Abdul-jabbar k'ala baiceba domin yabashi hak'uri, bayada tacewa, domin itace keda laifi ai, tabarshi waje ga driver d'inta.
Farha hanya takama ta waje, sannan ta share hawayenta da suka zubo mata a ido kad'an, shima bayanta yabi, sannan ya bud'e motar ya shiga.
Tafi 5mnt kafin ta shiga motar, sai da taji dama ta mik'amasa Ikram itakuma tashiga napape, amma sanin zata musgunama ikram idan tatashi bata gantaba zatayi kuka, hakan yasa tashiga motar tana share hawayen bak'in ciki wanda batasan ya zatayi maganinshi ba, a yanzu.
Isowarsu gida, farha koh d'akin umma bata shigaba domin tarin damuwar datake ciki, kuma wadda ta manta da ita tun bayan wasu lokutta, amma a yanzu dole ta kawar da ita ta hanyar yafe ikram a rayuwarta, idan dai akan ikram ne? Toh yau zatayi yak'i da zuciyarta akan abun dake ganin shine dai-dai da kwanciyar hankali a zuciyarta insha'allah.
Umma shigowar Abdul-jabbar kawai taji, amma bataji tasu farha ba, fitowa tayi domin jin ya basu dawo ba har yanzu? Abdul-jabbar ya shaidamata sun dawo suna ciki, umma cikin mamakin wucewar farha d'akin ba tare da ta shaidamataba, hakan yasa da sauri ta shiga d'akin nasu don dubata.
Hango farha umma tayi zaune tana sharar hawaye, ga Ikram na barci alamar ta samu sauk'i sosai, shigowa tayi tare da zaunawa gefenta ta dafata tace.....
"Farha lafiya kika dawo kika zauna kika sanya d'iyarki gaba kina kuka?"
Tayar da fuskarta tayi, idanunta cike da hawaye wanda ta runtse idon suka zubo tace.....
"Umma Ayau zanbar gidan nan nakoma gidan Baba insha'allah, domin zan maida ikram hannun mahaifinta, na fahimci zaman Ikram hannuna ba alkhairi bane a rayuwata, domin koh yaushe idan ina neman farinciki, toh a sanadin zamanta hannuna bangaji da jin gori da tunanen bak'in ciki a rayuwata ba, don haka umma zanjawo hak'urin rashin Ikram a rayuwata nasanya juriyar rashinta tare dani, na baiwa mahaifinta ita, nikuma nayi nesa da dukkan rayuwarshi, narok'eki da Allah Umma gada kiga laifina akan hakan, domin hakan shine kad'ai zai kawo zaman lafiya A rayuwata, domin A yau kad'ai rashin mahaifiya ya dawo mani sabo "
Kuka takamayi mai tsuma zuciya, tare da aza kanta bisa kafad'ar umma d'in tana kuka, nan take ran umma ya'bace, domin tagane yadda zancen yake, kuma abun daga Abdul-jabbar yataso, amma kafin taganshi bari tafara jin menene silar hakan?
"Farha dama har yanzu baki d'aukeni a matsayin mahaifiyar data haifekiba? Toh kisani babu inda zakije,kuma babu zancen maidamashi da Ikram A hannunshi,domin Kece kad'ai kikafi cancenta da kirik'e Ikram a hannunki domin dake tafi sabawa, amma barni dashi, kishare hawayenki, ninasan hukuncin da zanyanke akan hakan, kuma kina tare dani har ranar da zakiyi aurenki kihuta, insha'allah Farha bazaki k'ara kuka a rayuwaba, indai kina tare dani Alk'awalin da nad'auka sai yacika insha'allah, kitashi ki wanke fuskarki, sannan kici abinci ina zuwa kinji "
Share hawayen kawai farha tayi, Amma kuma damuwa damk'e a zuciyarta domin tarasa menene zai kawo wannan k'iyayyar ta yanzu da Abdul-jabbar ke yimata, ai koh don darajar Ikram a hannunta yaci ace ya yafe laifinta da tayi mashi farko, ya kalli girman karamci a rayuwarshi, amma abu kusan shekara nawa yak'i ci bale ya cinye, gaskiya tasan tayi laifi farko, amma dazaiyi tunani anan shine yanzu ai tana k'aunarshi sosai, mezaisa kuma yayita yimata hakan yanzu, gaskiya da tace bazatayi aureba, Amma yanzu dole
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 44