sannan tace.... "Kataso muje"
Iman tareqe masa hannu tace...
"Kayafeman kuma kacika alk'awalina, kuma wayata na mallakama yaya farha abata, domin inada sak'o da yawa ciki wanda na ajiye domin ita,sauran naka sak'on ka........."
Bata k'arasa ba sai ta sarqe da miyon bakinta, umma da gudu ta kira likitan, amma abdul-jabbar rik'e yake da hannun iman ga gam sai sannu yake ce mata, "nabaki ruwa?"
ta d'aga kai ya jawo d'ayar gorar ya bata tasha sosai, sannan tace barci nake ji, dai² da shigowar likitan yace abata guri ta huta, da alama tayi magana doguwa, suka fita amma banda abdul-jabbar, umma goya ikram tayi sukayo waje.
Kusan awa d'aya Abdul na zaune jinya bai san cewa Iman tayimai nisan kiwo ba, sai sun had'u kuma, hango ruwan da aka saka mata yayi jini na dawowa ciki sa sauri ya rik'a hannunta tare da kiran sunnanta amma da gani barcin yayi nauyi inji shi.
Yafita kiran doctor d'in, suka dawo tare dubata yayi sannan ya cire ruwan yace.....
"Sai hak'uri aboki nah, Itama tabi mamar ta, gidan gaskiya "
"Menene ma hakanan?"
"Hak'uri kuma assabru, kuma sorry duka kagane ako wane yare "
Kameshi abdul-jabbar yayi yace....
"Haba likita daga cewa ka dubata sai kace wai nayi hak'uri, idan bazaka iyaba nakaita wata assibitin a dubata koh da a tsirara zan tafi "
"Toh abokina, nasan kai musulmine mai imani da k'addara mai kyau koh mara kyau don haka ka yarda matar ka ta rasu kusan 30mnt da suka wuce "
Fad'uwa kawai likitan yaga yayi tare da rik'e kai, dai_dai da shigowar umma da farha, umma da sauri ta k'arasa kusa tare da tambayar lafiya?
Doctor yak'ara nuna iman kuma ya fad'a masu ta rasu.
Ai kafin ya k'arasa fad'i, tuni farha tabi sahun k'asa itama a sume, nan take imanin umma yak'aru ga ikram sai kuka take yi, ga rashin iman ga su sukuma a kwance.
Shikenan duk sun mutu sun barta, ya zatayi? 'Dauki likitoci suka kawo, umma koh hawayen ta nema ta rasa,waya ta d'auka ta kira baban don shaidamashi, shikuma............
😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
_Innalillhi wa'inna ilaihirraji'un._
_kullu nafsin za'k'atul maut._
Duk mai rai zai d'an d'ana azabar mutuwa.
Mai kudd'i, talaka, almajiri, mawadaci, yaro, babba, mara lfy, mai lafiya, masoyi da masoyan shi,duka wata halitta zata d'an d'ana azabar mutuwa.
Muji ya rasa matar shi, mata tarasa mujinta, koh uwa tarasa d'anta koh d'an yarasa uwar, idan dai baka ta'ba d'an d'ana zafin rashi ba, toh zaka sameshi wata rana.
*KULLU MAN ALAIHA FAN,WAYABQA WAJHI RABBUKA ZUL JALALU WAL'IKRAM*
Kunga kuwa baza'a bar wani don wani yaji dad'iba.
Ina typing d'innan damuwa feel a zuciyata, hakan yasa nakasa turo shi,amma nasan dad'in hak'urin rashin iman zai sa musamu farinciki gaba.
😭😭😭😭😭😭
★★★★★★★★
💧 *masoya nah da mabiya buk d'ina, sak'o gareku.....*💧
Kusani labarina yafaru da gsk, kuma wayanda abun yafaru da su suna biye da ni, idan nace iman bazata rasa ranta ba, sak'on da nake son isarwa ba zai zoba.
Kusani ni kaina wlhy naji mutuwar Iman domin khadija mutunce, duk wanda yasan rayuwarta yasan ita ta dabance, alokacin da nake rubuta wannan page na mutuwar tata labarin sai yazamo man sabo bisa ga lokacin da aka bani labari, domin ina rubutawa ina zubar da k'wallah wanda hakan yasa yau gabad'aya naji har tsoron posting nake yi wlhy.
Idan da labarin nawa ne, kuma nice na k'irk'irashi, toh banga abunda zai sa na kashe iman ba, ni bee bee bani na kashe iman ba, daga Allah ne hakan yazo.
Duk mutun na k'warai zai so ace ya mutu yana cikin soyayyar jama'a da yawa domin hakan babban dace ne, sbd kowa zai fad'i alkhairin ka kuma zai samamaka tsira koh da a shaidun k'warai ne, iman ta cika da imani, domin a tafarki tsira taje lahira, tana da aure, kuma mijinta na yaba halinta, kuma itama tana yaba halinshi,kunga wannan kad'ai dace ne, don haka da ita da mahaifiyarta anayi masu fata da zaton sunyi dace.
A halin yanzu idan kana son iman addu'a kawai zaka bita da ita domin koh tanan ta samu dace mai girma.
*Fatima Aliyu Abbas (Farha)* kuwa kusani itace tabada labarin domin a rubuta shi, wanda a halin yanzu hakan da labarin yak'ara kawowa wannan part d'in,gaba d'aya farha cikin damuwa take.
Masu cewa farha ta sa'bama iyayenta farko, tabbas hakan yake kuma ta nemi gafara, tare da gyara halinta tazama tak'warai,wanda laifinta rashin jin maganar iyaye da kuma mummunar soyayyar Anwar da tasaka ma kanta, wanda kuma sai Allah ya nunamata ishara a hannunta, aka had'ata da wanda gara mazinaci dashi, tasha wahala, tabugi wahala, wahala kuma ta ganta.
Wanda duk yayi laifi, yagane kurensa har yanemi yafiya ba a yafe mashi ba, ai cikar imanin bai kaiba, ansan cewa idan kayi laifi a nuna 'bacin ran abunda kayi, sannsn dga baya a yafeka.
Idan ana yima Allah babban laifi ya yafe idan taubatun nasuha ce, mezaisa za'ayima d'an adam yak'i yafewa? Don haka kowane mai rayuwa ake sonsa da kalmar hak'uri, domin samun zaman lafiya sanadin hak'urinnan, don haka farha tayi laifi kuma ta gyara, sannan mutuwa kad'ai tazamar mata ishara a rayuwa, rashin uwa ba k'aramin jidali bane ga rayuwa, da rashin yar uwa ta jini, anan ku fad'aman waye farha ynx?
Don haka inason a bayanina yan uwa kufahimci cewa.....
*WAMAN K'ADARALLAHU, HAQQAN K'ADDIRIHI*
Babu mai wuce zanen da aka rubuta mashi a *lauhul mahfuz* don haka imani da k'addara khairan wa sharan.
Fatana kubini a cikin littafinnan domin akwai nishad'antarwa gaba, tare da gargad'i mai amfani, insha'allah, akwai duk wata soyayya wadda babu ita a baya gaba zaku sameta, albishirine daga gareni.
Sannan ina taya d'aukacin masoyan iman ta'aziya baki d'aya, Allah yayi mata rahama, yasa mutuwa hutuce gareta da mahaifiyarta da mahaifanmu baki d'aya, muma allah ka gafarta muna laifukanmu kuma kasa mucika da imani.
Nidai d'in ce taku, ta masoya, jinin soyayya, tambarin ruwan soyayya,insha'allah a cikin soyayya zamu wuce😍.
Allah kabarmu da soyayyar Allah da manzonsa, ka kuma barmu da masoyan mu.
Ina cikin alhinin rashin iman, amma kuma ina cikin farinciki, domin nasan ita tayi mai kyau, sai addu'ar Allah yabama Abdul-jabbar hak'uri, da musaya mashi mata wadda tafita.
Akwai show fa👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻
*Bee Been masoya*💞
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
# ;*” ”*;.
‘*;._
, ‘*-;
*:, .;* ORRY!
This is a special SORRY 2 u my fans! Allah 4give all our sin's.
Page...
★4⃣9⃣★
Ringing d'in wayar baba yaashigo amma tana a silent lokacin, saboda yana gaban k'abarin mama yana jero mata Addu'a da nema mata gafara gurin Allah, ya shafa k'abarin tare da shafe hawayen shi ya fito mak'abartar, duka anwatse shi kad'ai ya rage, don haka sai ya kamo hanya shi kad'ai don dawowa gurin ta'aziyyar.
Fitowar shi kenan, ya k'ara jin _vibration_ na wayar tashi na motsi a aljihunshi, dubawa ya yi sannan ya amsa kiran domin yaga numbr abdul-jabbar ce, kafin ya d'auka gaba d'aya imani ya gama shiga jikin shi domin yasan baya wuce iman itama ta tafi ta barsu.
_Picking call_ d'in yayi, tare da tare da yin shiru, sannan muka yaji ance....
"Iman itama lokaci yayi! idan kun k'arasa azo a d'auki gawar itama a suturta ta,kuma ga yaran dukan su sun fad'i a sume "
Kalma d'aya ta fad'o mashi a bakin shi, domin itace garkuwar shi koh ina, ita kad'ai ke rik'e da nauyin imanin shi yace tare da hawaye.....
*_"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Allahumma ya muk'allibal qulube sabbit qalbe Allah Deenika, Allahumma ya musarrifal qalube wal'absari, sarrif qalbe Ala d'a'atika"_*
Jin zuciyar shi tayi sanyi, yak'ara bashi qwarin gwuiwar yin sauri zuwa gidan nashi.
Shigar shi aka fara yimashi ta'aziyar matarshi, anan ya amsa yace masu zai koma domin kar'bo gawar 'yar tashi, saboda itama Allah ya amshi aburshi, anan mutane nat fara rud'ewa suna kuka, sai Allah yabama baban k'arfin hali da k'warin gwuiwa domin jin hakan yake yi ba wani abu bane yanzu, tun bayan karanta addu'ar da yasan itace dogaron shi, nan take ya shiga basu hak'uri tare da fahimtar da su girman hak'uri da imani da abunda Allah ya saukar, sannan suka kama hanya shi da aunty hafsart k'anwar mahaifiyar su farha don zuwa assibitin kuka kawai takeyi, baba nabata hak'uri da nuni da bazata da wo ba har abada.
Likitoci ukku kan abdul-jabbar amma yayi nisa sosai, hakan yasa suka sanya mashi abun jawo numfashi a hancinshi saboda taimakon rayuwar shi, suka bashi _30mnt_ su gani koh zai samu farfad'owa.
Haka farha itama, nurse nurse suka d'auketa zuwa nasu _saving_ d'in akan ta, sunyi iya k'ok'arin su akan hakan, cikin yardar Allah da taimakon su ta dawo hayyacin ta,sai dai kuma tambayar su take yi...
" wai menene yafaru hakan? kuka taru akaina, nifa daga assibiti nafito, kun wani rik'e ni tare da danne man jiki hakan, lafiya kuwa?"
Nurse d'in d'aya ta taso zuwa gareta tace.....
"Lafiyar ki k'alau,kawai mun dai rik'eki ne amma ke baki san abun da ya faru ba?"
"Eh umma ta kirani a waya nazo, toh kuma nazo kuku ma kun wani rik'eni hakan, toh ku sakan naje naji lafiya kuwa?"
Nurse d'in guda tace, gada a saketa, domin ba cikin hankalinta take ba, kuma bata san me take cewa ba ne baki d'aya, kamar yadda alama ta nuna azancen ta, hakan yasa sukayi mata allurar barci.
Baba da sauri yashigo, ya isko umma a waje zaune ikram sai kuka kawai take yimata, tasaya mata yougout ta saya mata duk abun da zai sa ta daina kukan, amma tak'i ta daina, umma kuma sai rarrashin ta take yi amma ikram tak'i ta daina kukan,wanda umma ke ganin rashi mahaifiya ke ta'ba yarinyar.
Baba hannu ya mik'a ya kar'beta amma tak'i tazo, hakan yasa ya barsu domin zuwa kar'bar gawar ta iman.
Aka dai-daita tare da saka hannun baba, d'aukar gawar kawai ta rage.
Kafin ya wuce ya nemi a kaishi inda yaran ke kwance, aka fara kai shi gurin da aka kwantar da farha, anan yaga barci take yi sai ya fito zuwa d'ayan d'akin.
Shigar shi dai-dai da falkawar Abdul-jabbar cikin wasu kalamai masu tsuma zuciyar wanda yake kusa dashi.....
"Haba iman! Ai bamuyi hakan dake ba, kin tuna ranar tafiyar ku? Ceman fa kika yi zaki shayar dani k'auna ta har abada, iman kintuna faranta zuciya ta da kikayi kafin kifita part namu, iman ki tayar dani kice mafalki nakeyi ba gaske bane zancen da wancen likitan ke fad'i, Iman! Iman!! Iman!!!..........."
Dasauri yacire abun da aka sakamashi a hancin shi ya mik'e zaune.
Likitocin suka shigo da sauri, sannan baba shima yazo ya rik'a Abdul d'in yace masu su dakata zaiyi magana dashi.
"Abdul-jabbar! Duba da kyau ka ga nine baban ku, ka natsu kaji me zance maka, ka tsaya kayi shiru kaji wani abun abdul "
Ya natsun amma bai daina kukan ba, sannan ya dubi baban da Alamar tambaya tare da cewa....
"Yauwa baba, iman na nan raye koh? Likitan bai san aikinshi ba, mu d'auketa mu kaita waje su dubata, baba inada kud'in da zasu nemama iman lafiya koh da zanje zindir kuwa "
"Kaine ka halicceta?"
"Ah ah baba"
"Waya halicceta?"
"Allah ne "
"Kasan sadda aka busa mata rai?"
"Ah ah baba?"
"Toh idan hakane wanda ya halicceta, yafika sonta, Iman dai rik'o Allah ya baka, kuma yace kabashi aburshi, koh zaka ja da ikonsa ne ya dawo maka da ita?"
"Ah ah bani da iko akan hakan, sai dai ina jine kamar bata rasu bane ciwo ne kawai "
"Toh ka jaye shakku,kasaka imani da hak'uri a zuciyar ka domin kaima baka san lokacinka ba, ni da kai yanzu mataki d'aya muke, sai dai ni nafika saboda ni naga rayuwa iri-iri abdul, kuma nayi imani da hakan k'addarawa ce ta uban giji, kuma jarabawa ce yayi muna yaga zamuyi imani da ita koh kuwa ah ah, toh ka d'auki hak'uri kawai babu wani haya niyya a rayuwar ka, kai namiji ne wanda ya kamata kararrashi mata akan hakan amma kuma ace mata zasu rarrasheka Abdul? Toh kayi hak'uri kasan Allah yace..........
"ولمن صبروغفرإن ذلك لمن عزمالأمور) سورةالشوراى،
Kuma yace...
واستعينوا بالصبروالصلاةان الله مع الصابرين) سورةالأنفال،
Duka kaga Allah yana nuni ne akan hak'uri akan duk wata rayuwa da tafad'a ma mutun toh yayi hak'uri akan ta koh a taimakone, koh a wata jarabawa, koh neman halak, koh hak'uri akan abun da mutun ya rasa.
Kuma Allah yak'ara da cewa acikin *suratul zumar...*
" انمايوفى الصبرون اجرهم بغيرحساب)."
Kaga kenan ladar masu hak'uri da k'addara ba kad'an bace, domin Allah zaiyyi masu saka mako yace mai girma, Abdul kad'auki hak'uri rayuwar ka, nasan munyi rashi rashi mai girma, tsakaninka da iman yanzu addu'ace mai girma saboda girman soyayyar da ke tsakaninku, ba kuka koh hauka ne zai ceceta ba, koh kuma kai ya kawo maka farin ciki ba, ah ah addu'a shine sakayyar soyayyar ka gareta, nasan kowa zai damu da rashin mutanen arzik'i, toh dama Allah bai cika barin irinsu iman a duniya ba, domin a nuna girman adalcin rayuwa.
Iman da mahaifiyarta mutane ne da duk wanda yayi rashinsu zai damu, amma kuma idan ya tuno aikin alkhairinsu a duniya zaiji sanyi a zuciyar shi domin yasan sunyi dace na k'warai.
Abdul-jabbar kazamo cikin ،الصبرون wayanda zasu so ladarsu tazamo بغير حساب nasan ka karanta kuma kasani domin kai ba jahili bane, nasan rud'ine na rashi, ya mantar da kai, inason a yanzu katashi muje da kai a d'auki gawar matar ka,kayi mata wanka da kanka, ka suturta ta, kuma kayi mata addu'a kamar yadda addini ya tanadar, a raka ka kakaita makwancinta, shine cikar imanin ka da soyayyar ka gareta"
Abdul jabbar ya share hawayen da suka zubo mashi, sannan ya kalli surukin nashi kuma baba gunshi ya k'ara tambayar shi....
"Baba da gaske iman kenan ta rasu?"
"Eh Abdul Iman ta rasu, kuma nasan kai mai imani da k'addara ne, idan ka tuno da ayoyin da yanzu na jawo maka wayan da Allah da kanshi yayi bayani akan hak'uri domin yasan rashin wani abu ga bawan shi ba k'aramar musiba bace, shiyasa ya saukar da ayoyin sakamakon masu hak'urin, ka daina shakku ka tashi kazo muje gida tare a rufe matar ka da kai, Abdul-jabbar na hore ka da ka karanta......
*_"INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN! 3×_*
*_ALLAHUMMA AJIRNI FEE MUSIBATI HAZA, WA HALUFNI KHAIRAN MIHA3×_*
*_ALLAHUMMA INNI AUZU BIKA MIN ZAWALI NI'IMATIKA, WATAHULI AQIBATIKA, WAMIN FUJA'ATI NIQ'MATIKA,WAMIN JAMI'I SAKHA'DIKA_*
Abdul ka karanta yanzu sannan mu fita "
Karantawa abdul-jabbar yayi, nan take yaji kamar anzare mashi k'aya daga cikin jikin shi kuma sai yaji wani k'arfin imani yazo mashi, nantake yace abashi ruwa yasha.
Baba ya mik'o mashi ruwan sannan ya rik'oshi zuwa gurin likitocin, yace su rubuta mashi maganin da zai sha, domin zaije dashi ya rufe matar shi.
_Doctors_ d'in suka tausaya mashi, sannan suka bada maganin da zai sha domin kanshi ya k'ara samun hutawa akan rasa shi da yayi na wani lokaci,suka tambaye shi,koh yanajin wani abun?
Abdul bai masan me zaice da su ba, domin baya son zance koh kad'an, baba ne ya amsa masu da cewa zasu dawo, domin akwai patient tasu anan zasu dawo.
Fitowa sukayi gurin mama daketa faman jijjigar Ikram da tafara barci, ga mutanen da ke gurin sunata yimata ta'aziyar rashin da tayi.
Abdul-jabbar na ganin ummar tare da ikram kuma sai yaji kamar wani abun zai dawo mashi sabo, hakan sai ya dafe kanshi tare da karanta addu'ar da yayi d'azun, kuma sai yaji sanyi.
Motar assibiti aka saka gawar sannan suka kama hanya harda aunty hafsatu , umma kuma aka barta ita da ikram da farha a assibiti, kuma tabada sak'on akawo mata abincinta da kuma kayan ikram d'in kafin a sallame su, tunda ita har ynz, gashi sunce suna ganin kanta kamar ya samu mtsl ma, toh ina zancen komawa gida nan kusa.
Isarsu gida aka sayo lakkafani aka yima iman wanka kamar yadda addini ya tanadar, Abdul-jabbar shi yayi mata wankan, tare da sakamata kayan ta, sannan ya zauna kusa da kanta yafara jero addu'a kamar yadda ake yima koh wane mamaci,yafara da salatin annabi, da kabbara sannan yaci gaba da cewa......
*_"Allahumma innaha qad nazala bika, wa'anta khairun manzuli biha,faqirun ila rahamatika,wa'anta ganiyyun an azabika._*
*_Allahumma sabit inda mas'alati mand'iqaha,wala tabtilha fee qabriha bima la d'aqata laha beeh_*
*_Allahumma agfir laha,warham ha,wa'afu anha,wa afeeha, wa'akreem nuzulaha,wa was'an madhalaha,wagsilha, bi ma'in,wa saljin,wa baradin,wa naqqiha minal had'aya,kama yunaqqassaubul abyadu minal danassi."_*
Ahaka Abdul-jabbar yazauna gaban gawar iman yayi ta nema mata gafara gurin Allah,sannan aka d'auketa zuwa gurin sallah, akayi mata kuma aka d'auketa zuwa kaita gidanta na gaskiya, wanda tasamu jama'a da yawa da kuma shaidun halaye na k'warai, hakan duk yak'arama Abdul-jabbar natsuwa yaji kamar babu komai a rayuwar shi, ya d'auko ta wakkali ya azama kanshi, amma kuma da nauyin addu'a ciki, aka rufeta kowa ya watse ya tsaya qabarinta yayi mata addu'a sannan ya miqe tsaye baba na jiran shi su wuce, anan ne hawaye suka zubo mashi don tunawa da shikenan ya bar iman sai in sun had'u gidan gaskiya.
_YA ALLAH MUMA KA DATAR DAMU DA DACE NA GSKY, ALLAH KA RABAMU DA IYAYENMU DA MAZAJENMU LAFIYA, ALLAH KABAMU SHAIDU NA K'WARAI A RAYUWAR MU TA DUNIYA, DOMIN SHINE SHAIDAR LAHIRA,ALLAH KASA MUCIKA DA IMANI._
Dawowa sukayi anan aka fara yimasu gaisuwa, tare da tausayawa akan su, domin kowajji labarin zai yimasu addu'a domin sunga jarabawa.
Da marece aka tashi gurin ta'aziyyar baba yace Abdul-jabbar yaci abinci, yasha magani ya kwanta zaije assibiti yaga jikin farha d'in ya dawo.
Yabi umurnin baban amma kuma ba abinci ba, domin baya shiga koh kad'an sai dai yasha ruwan tea don yasha magani.
Hakan dai yasha ruwan tea d'in da aunty hafsart d'in ta kawo mashi, yasha magani amma banza barci baisan dashi ba wallahi,gashi basheer yayo mashi waya yana hanya kuma wayar yanzu baisan inda take ba, domin koh son ganin wayar ba yayi.
★★★★
Farha ta falka, sai yanzu a hankalinta take, kuka take yi wanda batasan yaya yake zuwa ba, umma goye da ikram tana na barci, zaunawa tayi gefen farha ta fara magana....
"Farha kefa musulma ce, kuma nasan zakiyi imani da k'addara mai kyau da marar kyau, rayuwa ce hakan kowa zaiji wannan tambari da bintu taji da iman.......
" mama kuma.......?"
Farha bata bari umma tak'arasa fad'in abun da taso fad'iba ta katseta, domin bataji rasuwar mahaifiyar tata ba, itama umma ta manta da farha batasan da rasuwar ba, don haka umma takasa amsa mata tambayar tayi shiru itama tana hawaye, sannan tace.....
"Eh farha gara kiji duka, sai kiyi imani gabad'aya, domin koh yaushe ne sai kinji zafin rashin fad'amaki, eh hakan mamarki har ta riga iman rasuwa "
K'ara tasaki tare da dafe kanta takoma a inda ta fito, wato somewa kenan.
Lokacin da ta fad'in somen ne, lokacin baba ya shigo da kayan ikram a hannunshi, umma ruwa ta d'auko masu sanyi ta kunbulama farha, domin batako tsaya kiran likitocin ba.
Ta dad'e bata falko ba, sai da baba yaqara watsa mata ruwan sannan tayi ajiyar zuciya tare da kuka mai tsanani.
Umma tayi danasanin furta mata mutuwar, baba yace ai gara da kika fad'amata, domin itama musulmace, yadda kowa yayi imani da k'addara haka itama tayi, sannan ya juya ga farha d'in itama ya fara yimata nasiha kamar yadda yayima abdul-jabbar, sai dai ita yak'ara mata da nuni da rashin mutuncin da tayi baya, yace mata.....
"Farha iyakar abun kenan, kinga yanzu daga ni sai ke at duniyar, kuma nasan kin d'auki darasi tun kafin aje koh ina, toh rayuwar kenan, kuma ki daina wahalar da kanki da yimasu kuka, domin su sunsamu dace na k'warai,don haka kowa ake son yazamo na k'warai sai yaji dad'inshi lahira, wannan mutuwar wa'azice gareki farha, don haka kiyi koyi da yar uwar ki koh kema kinyi dace na k'warai"
"Ah haba alhaji Aliyu! Menene hakan? Kadubi halin da take ciki fa, kuma kana k'aramata wani ciwon, ai koma menene kana bari har taji sauk'i sannan a yishi, kuma abunda ya wuce ya wuce, kabarmu muji da ikon na Allah da yayi mana kuma"
"Ai umma jabbar gara tun anan taqare kukanta, shiyasa na fad'amata duka domin ta had'a bak'in cikin da nasihar da nayi mata guri d'aya su zauna.
Farha kuka umma ma haka kukan takeyi, shi ma kukan ke shirin fito mashi domin zancen kawai yake fad'amata amma yasan farha abur a tausayamawa ce, hakan yasa ya qara jawo imanin shi yafara tausasa zancen shi gareta tare da rarrashinta da yimata nasiha, haka umma itama tayi mata nasihar har suka samu abun ya rage.
Baba yanemi da abasu sallama suna son suwuce gida da ita hakanan saboda tafiyar akwai wuya, cen su dinga bata magani har taqarasa warkewa.
Da safe aka sallame su, suka koma gida, akaci gaba da amsar gaisuwar, sai dai farha rashin lafiya takeyi mai tsanani, kuma bata iya minti d'aya ba tare da Ikram na gefenta ba, ga ciwo kuma ikram bata yarda da kowa sai ita, koh anso a kar'beta domin ta samu sauk'in ciwon bata zuwa gurin kowa bata cin abincin hannun kowa sai na farha.
Haka Abdul-jabbar koh abinci baya iyaci, duk ya rame yayi wani kalar, sannan ya kasa komawa gidan shi, domin bayason ganin koh k'ofar part nasu domin ganin yakeyi iman zata fito ne.
★★★★★
Aftr 7 days da k'are amsar gaisuwa su umma suka koma gida, sai dai Abdul-jabbar ya kasa komawa part nashi, da yashiga da sauri zai dawo part d'in umma ya zauna, yayita karatun alqur'an, hakan na rage mashi kewa, domin iya yanzu yayi imani da k'addara kuma yasan iman bazata dawo ba.
Sai dai kuma yanzu wata mugunyar shak'uwa tak'ara shiga tsakaninshi da ikram domin komai zaiyi sai da ita, amma ita kuma tafison ta ganta da Aunty nata farha.
*Bee Been masoya*💞
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*_MY ZULAIHEART RANO😘 K'AUNAR KI GARENI GARENI BA KA'DAN BACE, ELHAM DA NA GODIYA,KUMA TANA ALFAHARI DAKE, ALLAH YA BARMU TARE😍 Bee Been💞 kice._*
Page...
★5⃣0⃣★
Rayuwa kenan! Komai mai juyi ne, idan Allah ya jarabce ka, bakayi imani da shiba toh duka kai rayuwar ka sai a hankali.
Haka Allah mai girma da buya, ya nufi Abdul-jabbar da hak'uri, tare da k'arfin d'aukar alqur'ani abun share hawayen bayi da kuma wanke masu zukatan wa'yanda duk wani bala'i ya fad'amawa.
Cikin ikon Allah, A yau Iman da mama ke cika 40 days da rasuwa.
Tun da akayi rasuwar Abdul-jabbar bai koma gurin aiki ba, sbd baya jin dad'i sosai, yau ciwo gobe lafiya, hakan kuma yana da nasaba da rashin iman a rayuwar shi, duk da yayi imani da k'addarar Allah a kanshi, toh shi kuma sabo wani abu ne da ke dad'ewa jikin bayi, koh yashirya da niyyar komawa sai kuma yaji bazai iya ba, domin idan zai koma da kalam iman da take yimashi yake samun k'wari gwuiwar aiki,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 44