tashi, kece zuciyarsa ke bege ko wanne lokaci, sai dai kash! Yaya farha duka baki gane hakan ba, domin rud'in duniya da haskenta yasa baki gane gaskiya ba har kika barshi"_
Hawaye suka fara zubowa daga idon farha, domin tafi kowa sanin wannan zancen na Iman, hakan yasa ta share 'yan qwallarta da suka zubo a fuskarta kad'an, taci gaba da karatun nata.
_"ki sani yaya farha, yaya Abdul-jabbar kece yake so bani ba, yazauna dani ne saboda tsananin biyayya da kyautatawata a gareshi, yafara sona ne, saboda yayi rashinki, a haka har sona yayi rinjaye a k'irjinshi, amma kisani sone kawai yaya Abdul keyiman, k'aunar duka taki ce yaya farha, yaya Abdul na sonki har kamar yadda baki tsammani, sannan duk wani abu da zai yi maki shi, zai yi shine saboda tsananin kishinki da kuma begenki, domin nafi k'arfin wata shidda a gidansa koh yaushe kece yake kira a cikin mafalkinshi, wanda na gane hakan nasamo dubaru wa'yanda zasu rinjayar dashi daga barin ambatonki izuwa ambatona, domin nice a gabansa lokacin, naci wuya kafin na sauya begenki a zuciyar yaya Abdul-jabbar ta hanyar sadaukar mashi da dukkan rayuwata, yaya farha gada na cikaki da dogon zance domin nasan kinsan wannan ba tun yanzu ba, sai dai wani sirri nake son bar maki wanda idan har abban Ikram kika aura, kika rik'e wannan sirrin, zaman aurenku zai yi dad'i sannan ke zaki samu mijinki hannu biyu, wanda ina yimaki fatar samun Abban Ikram a matsayin mijin aure yaya farha, wanda nake fatar sak'ona yazo hannunki tun kafin kiyi aure da wani bashi ba, kuma ina neman alfarmar idan Allah ya d'auki raina kuma bakiyi aure ba, yaya farha ki auri yaya abdul, domin nasan Ikram zata samu gata mai yawa a kan hakan, nasan Allah shike rayawa da kashewa, amma ni na dad'e da sanin cewa rayuwata ba mai tsawo bace, domin abun da nake ji nake gani a rayuwar tawa, ni nasan rayuwata bamai dad'ewa bace, don hakan tun daga ranar da kika dawo gida, bayan rabuwarki da tsohon mujinki, nake maki fatar samun miji na gari, kuma insha'allah a yanzu da bana raye, nasan idan kika bi tarihin kalar zaman da nayi dashi, yaya farha zaki samu yaya Abdul-jabbar, ko mai nauyin k'iyayyarsa gareki"_
"Nasani iman, wallahi nasan duk abunda kika fad'a gaskiyane, kuma nayi alk'awalin kasancewa dashi ta har abada, wallahi inason yaya Abdul, amma narasa yadda zanyi ne tun farko da na dawo gidan umma naga kalar rayuwar da kukeyi, tun anan naji sonsa nakeyi, kuma kishinsa nakeyi akan hakan, saboda nasan nawane ya dawo hannunki,amma kuma idan na tuna da babu aure tsakaninmu har abada,saboda aurenki,sai naji na tsani kaina, kuma na tsani rayuwata,hakan kuma sai Allah ya d'auki son Ikram ya sanya man arayuwa, domin nasan jininsa ce ita, Iman baki duniya a yanzu, amma wallahi zakiji dad'i a makwancinki na aminci, da zamowa da mijinki da 'yarki da zanyi, domin zanyi k'ok'ari akan na dawo da soyayyarshi a gareni da hak'uri da juriya"
Share hawaye tayi sannan taci gaba.
_"yaya Abdul ya kasance acikin maza masu mugunyar sha'awa, sannan shi mutun ne maison kyautatawa, yana da ra'ayin macce cikakka wadda take da cikar halitta, yanason macce mai sura irin taki yaya farha, a dalilin hakan lokacin da aka kaini gidansa, yake yimani d'aukar ni k'wailace,wadda batasan komaiba, wanda hakan shi ya bak'anta mani rayuwa,nayi yak'i da furucinsa domin nuna masa nima macce ce, nasan cewa yaya farha komai kin fini a rayuwa, domin ke koh a cikin mata daban ce, Allah ya k'eraki k'ira irin wadda yake bawa 'ya'ya mata kyautarta, ni kad'ai zan iya shaida maki gaskiyar ke wacece?,domin ni jininki ce, yaya farha inason idan har yaya Abdul yazama mujinki to zaki samu zuciyarshi cikin gaggawa domin irinki yakeso, kibi hanyar da yanzu ni zan fad'amaki sirrinsa, yadda zaki shawo kan zama dashi,kamar yadda muka zauna acikin so"_
Motsawar Ikram kenan, tare da yin kuka, da sauri farha ta jawota zuwa jikinta, tare da jijjigata ta koma barcin, da ikram jikinta ta k'arasa karantawa, tana lumshe ido, domin yanzu ne aka zo gurinda yayi mata dad'i, kuma sai taji k'aunar Abdul-jabbar na k'ara shiga zuciyarta, hakan yasa taji tsoronsa ya 'bace a zuciyar ta, taci gaba, domin shine page na k'arshe acikin document d'in da tayi zooming nashi.
_" yaya Abdul nada sauk'in kai, yana mugun son k'ananan kaya, yana son a dinga kulashi, ko da shi bai kulaka ba, yaya Abdul mutunne miskili, hakan yasa idan baka dage ba, zaka d'auka shi mutunne mai zafin zuciya, amma baxaka gane ba sai ka kusanci rayuwarshi sosai, yaya Abdul mutunne mai son adinga shagwa'bashi da riritashi a gabanshi, gada fushinsa ya girgizaki, domin zai iya cewa zaiyimaka abu kaza a cikin zafi, amma da ka iya tafiyar dashi komai zai wuce, yaya farha kisaka juriya a zaman aurenki, idan har Allah ya k'addara auren ki da yaya Abdul, domin nasan Allah ke ikonsa, amma nafison ki auri yaya Abdul, domin nasan shine dai-dai da ke, ina wannan rubutun ne tare da hawaye, sai dai kuma ina farin ciki, domin nasan banbar mujina a hannun wata ba"_
Share hawayenta tayi, sannan kuma itama tayi murmushi ta shafa kan ikram tace.....
"Allah yayi maki rahama k'anwata, Allah yasaki a aljanna firdausi, a hakan kad'ai kika tsaya my sistr na amfana, sauran aikin zan k'arasashi da kaina, kuma daga gobe bazan k'ara shakkun yaya Abdul ba, insha'allah "
Rufe wayar tayi, domin babu buk'atar son jin sauran labarin, domin tagane inda sauran zancen Iman ya dosa, don haka bata k'ara duba komai ba, ta kashe wayar, tare da gyara kwanciyar Ikram itama taja bargo ta rufe rabin jikinsu, sai safe kuma.
Safiya ta waye, farha ta tashi domin gyara ma ikram zuwa makaranta, duk da batasan wazai kaita ba, domin shi abban nata ba ganinshi take yi ba, amma bari ta gyara mata idan bataji motsinshi ha, takira driver umma yazo ya ajiyeta.
Gyaramata tayi, tare da shiga kitchen ta had'o mata duk abunda tasan zata nema a makarantar, ta gyara komai nata, sannan ta rik'o hannunta zuwa babban fallow d'in gidan, tana rataye da lunch box d'in ikram a kafad'unta.
Har zata kira umma ko driver d'insu na nan yakai ikram makaranta, kuma sai ta tsaya, domin umma zatayi doguwar tambaya akan hakan, sai ta changr shawara izuwa part d'inshi tayi mashi magana, duk yadda za'ayi sai dai kuma ayi yanzu, domin batasan ya za'ayi da zuwa school nata ba.
Ajiye ikram tayi a kujera tare da ajiye lunch box d'in a table d'in fallow d'in, tace ma ikram....
"Kijira nazo kinji"
'Dakinta taje ta d'auko hijab, domin kayan barcine jikinta, dama so takeyi, idan ikram ta wuce sai ta yi wanka, sanyo hijab d'inta tayi, sannan ta taka gidan benen izuwa part nashi, ganin k'ofar sake, ya sata yin sallama har sau ukku, jin ba'a amsa mata ba, sai tayi kamar ta juyo, kuma sai ta tsaya saboda taji an bud'e wata k'ofar dake gefenta.
'Daga idonta da zatayi, sai suka had'a idanu dashi, nan take taga towel ne d'aure jikinshi, sai tayi sauri duk'ar da kai tace......
"Don Allah kayi hak'uri yaya, dama Ikram zataje makaranta ne, bansan wanda zai kaita ba, gashi lokaci yana k'urewa, suna promotion exam ne"
Kallonta kawai yayi hankalinshi kwance, sannan ya tsuke fuska, tare da dafe nad'e hannunshi a k'irjinshi yace.....
"Amma saboda baki da hankali, shine zaki shigo d'akina kai tsaye ba tare da izini ba? Inace ni zankaita makaranta koh? Toh sai ki jira a cen inda aka ajiyeki idan banzo ba, sannan ki yanke hukunci, malama ki dinga tsayawa huruminki, ki daina zuwa inda ba'a kaiki ba"
Iya bak'inciki farha taji bak'incikin maganar tashi, nan take kuma itama sai ta mayar mashi da amsar ta cikin ruwan sanyi tace......
"Da farko ina baka hak'uri akan huruminka da na taka, duk da na nemi izini naji shiru, kuma ai ban shiga ba, sannan na biyu, kasani ni farha daga yau bazan k'ara saka hannuna a lamarin zuwa makarantar ikram ba, Ikram d'iyarka ce, haka nima d'iyata ce, sai dai kasani kafini iko da ita, idan ikram tayi karatu nasan zaka fini farin ciki, idan batayi ba, zaka fini bak'in ciki, daga yau bazan k'ara saka bakina akan zuwanta makaranta ba, kuma bazan k'ara shiga huruminka ba, kayi hak'uri, kuma ni bazan k'ara rik'on Ikram a hannuna ba, daga yau ka mayar da ita gurin umma, ta zauna domin zamanta hannuna 'bacin rai kawai yake sada man"
Da kuka ta bar d'akin nashi, ta sauka k'asa, ikram na ganinta tana kuka, itama ta fara kukan,sannan da farha taga hakan, sai ta daina nata kukan ta rungumo ikram zuwa jikinta tace.....
"Ikee nah! Me kike ma kuka hakan?"
Kallonta Ikram tayi tace....
"bake naga kina yi ba, Aunty Abba ne ya dakeki?"
"Ah ah bashine ba ikram, buge fuskata nayi da nazo wucewa, shine naji zafi nayi kuka, amma ai kinga na daina ko? Toh kema ki daina, yanzu ki bari gobe sai na kaiki school da kaina, domin Abbanki yace babu mai a motar shi"
Ikram ta gamsu da zancen auntyn tata, hakan yasa, ta rik'a hannun nata zuwa d'akinta, anan ta cire mata kaya, sannan ta changr mata wasu, suka zauna a fallown Farha suna kallo.
Tunda Farha ta bar d'akin Abdul-jabbar sai jikinshi kuma yayi sanyi, domin kuma yasan wani tym d'in baya kyauta ma farha, domin ko ba komai tana son d'iyarshi sosai, amma shi bai san dalilin da idan har tazo kusa dashi yake jin ya tsaneta ba, amma kuma yafara gano menene wannan dalilin dake sa yanajin hakan a zuciyarshi, duk lokacin da yaga farha.
Ko mai bai shafa ba, da sauri, yasaka kayanshi, domin yasan rashin son ganin farha shi ke son yajama d'iyar cikinshi, d'iyar da yake so, d'iyar da Iman ta haifa mashi, anya zai iya mantawa da alk'awarin iman a kan ikram kuwa?
Da sauri yaja makullanshi, zuwa d'akin da suke zaune, Ikram kawai ya hango zaune tana kallo, da sauri ya k'arasa tare da duk'awa gabanta yace.....
"Meyasa aka cire maki kayan makarantar ikram?"
"Abba, aunty farha tace bakada mai ne a mota, sai gobe ita zata kaini da kanta, idan ka siyo man"
Da sauri yace...
"a ina kayan naki suke?"
"Suna gurin aunty farha ta maida drower, tasakaman wasu"
"Ok kije kice tasaka maki na makaran........"
Bai k'arasa furu cinshi ba, yaji maganar farha d'in,wadda itama batasan da shi ba, kuma batayi tsammanin ganinshi ba, ko kad'an, tafito da cewa....
" Ikram da ke da waye kiketa magana?"
Had'a fuska sukayi, sannan ta kalli k'aramin towel d'in jikinta, da sauri ta koma toilet d'in.
Lokacin da Abdul-jabbar ya ga yadda Farha ta fito, sai kuma ya fara wani zance a zuciyarshi wanda baisan koh wanne iri ne ba, amma shi yasan wallahi ba so sonta bane a zuciyarshi, koh kad'an, amma meyasa jikinshi kuma ke rawa?
Da sauri yace ma ikram....
" kije ki duba ki d'auko mutafi, 8 ta kusa gada kik'i samun exam koh?"
Da sauri ta tafi d'akin, ashe kayan na bis gadonta, d'aumowa tayi, ya saka mata, sannan yaja hannunta da sauri, tare da lunch box nata suka tafi.
Ganin farha da towel a jikinta, sai kuma wani abun yafara motsi zuciyarshi, domin gabad'aya ita yake gani, amma wallahi, bazai iya komai da ita ba, domin tazama ragin wasu, sannan shikuma yazo ya shiga gurin da wani ya qare dashi, shi wallahi bazai iya had'a gado da ita ba, amma gashi ta fara rud'a ganinshi, domin Iman sak.
Driving yake yi yana tunane, har yakai makarantar su ikram, anan ya ajiyeta har sai da tashiga ciki yayi mata hannu ya wuce, gidan umma su gaisa, tare da neman tayi mashi alfarma ya koma aiki abuja, amma tace sai inda farha zaije, inba haka ba, sai nan fa 3 weeks, a haka kullum yake fama da ita,amma tak'i amincewa.
Tunda suka fita, farha ta gyara cikin riga da sket 'yan kanti,wadda koh ina na jikinta zai iya bayyana saboda zaman rigar a jikinta, babban fallow d'in ta dawo ta zauna tana break anan, bayan ta k'oshi ta kwanta kujerar da ke kusa da ita, nan take barci yayi awon gaba da ita, saboda ta gaji sosai.
Shigowar Abdul- jabbar kenan, ya hango ta kwance, tayi wani kwance, rabin jikinta duk sake, nan take kuma sai yaji wani abu ya k'ara d'arsuwa a zuciyar shi.
"amma da wannan tasani fad'awa halaka, gara nayi maganinta da wuri"
Fridge yaje ya jawo ruwan sanyi, yazo dai-dai fuskarta ya tsiyaya mata, gorar ruwan baki d'aya jikinta.
Da sauri farha ta mik'e, tana kallonsa, ta rasa a bun cewa, shikuma kallonta yajeyi kawai, sannan yace.....
"Ke kika jawo, domin nan ba huruminki bane"
"Ok nagode, sai dai kasani d'an adam nada rana, koh da shege ne, kuma kaji tsoron Allah,abunda kake yiman, yafi wanda ni nayi maka "
Tamik'e ta shiga ciki, ta barshi nan tsaye, yana kuma wani tunani.
Dafe kai kuma yayi kuma domin ciwon abun nason ya dawo................
_Ta masoya na dawo gare ku masoya na, acigaba da karatu cikin kwanciyar hankali, katsina tayi dad'i sosai, fatar da ce da nasara d'inku duka an samu alhmdllh._
Ta kuce a kullum......
~Ta masoya~
*Bee Been masoya*💞
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAHðŸ˜ðŸ˜*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com
My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*
*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋
★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★
*UMMY GARKUWA* *(UM-FATâ¤)*
_Nagaisheki kyauta, Allah ya sadaki da abunnan da kike so,ðŸ˜muzo kallon..........umhmmm._
Page...60
'Daki farha ta koma domin changr kayan jikinta, tasaka doguwar riga, abun da abdul-jabbar yayi mata,koh kad'an bai 'bata mata rai ba, sai dai gaskiya takusa fara rama abun da yake yi mata, Domin itama fa yar iskar kanta ce, ta fahimci son da take yi mashi yanzu nason ya mai data matsoraciyya, to bari ta ajiyeshi gefe ta nuna masa iya karta.
Duba agogo tayi taga 10:30 yanzu, ya kamata ta gyara masu abincin rana ita da ikram, domin shi ba ci yakeyi ba,don haka bata damu da ta dafa da shi ba.
Fitowa tayi hankalinta kwance don wucewa kitchen d'in, yana zaune a fallown ko me yake sak'awa? oho, fitowa tayi da doguwar rigar jikinta, wadda itama komai nata a bayyane yake, k'arshe ma babu duk wasu kaya da zasu iya kare jikinta da ga barin fitowar halittar jikinta, domin komai nata motsi yakeyi da ta taka k'afarta.
Hankalin farha kwance, domin tasan me take shirin yi da hakan.
Duba wayarshi yakeyi, tare da wani tunani wanda baisan kanshi ba, d'ago fuskarshi da zai yi, sai saman k'irjin farha da ke motsi cikin riga, Runtse idonshi yayi domin wasu taurari nayi mashi yawo a jikinshi, tsohon miki ya fara tashi da ciwo, k'ara bud'e idon da zaiyi, kuma sai ya kalli mazaunanta da suke nasu motsin, nan ma yayi saurin runtse ido da dafe kai, juyowa farha tayi kamar zata d'auki wani abun a fridge kuma sai ta juyo taga halin da yake ciki, anan farin ciki yafara turnuk'eta, kuma sai ta wuce abinta.
Aiki takeyi, tare da biyar wak'ar da wayar ta, wadda ta kunna a hankali, cikin farin ciki, tare da yayewar tsoron komai a zuciyar ta, domin ta gane Abdul-jabbar a kwai rik'o, gara ta dawo da yafiyarta a hakan, tana haka sai zancen iman ya dawo mata na cewa.....
_"Yaya Abdul, bayada wuyar kamu yaya farha, don haka gada ki damu,kibishi a sannu zaki sameshi a hannunki"_
"Hmmmm nagani kuwa, ashe fad'an nashi na banza ne, tunda baya iya rik'e kanshi anan, domin kuwa nafara gani tun yanzu Iman, mudai je zuwa, idan yace maki k'waila ni kuma zai kirani a ragin maza, wallahi zai gane kurensa, indai ina da rayuwa"
K'ara fitowa tayi zuwa store d'inda kayan girkin ke ciki, don d'auko doya a ciki, tayi masu faten doya, domin Ikram takusa da wowa school, yana nan zaune inda ta barshi, har mamaki ya kamata, domin tasan idan dai zai ganta, toh minti d'aya bazai k'ara ba a gurin, amma gashi ya kasa tashi.
Shiga store d'in tayi ta d'auko abunda take buk'ata ta fito, ta koma kitchen don k'arasa aikinta, ba'afi minti biyar ba k'amshin girkinta ya fara tashi, gabad'aya gidan ya d'auka, rufewa farha tayi ta fito don zuwa d'akinta, a hankali take takawa, tare da jijjiga jikinta cikin k'warewa yadda ba lallai a gane cewa tana wani aiki ba, wucewa zatayi, kuma sai taji ance......
"Kee! Don Allah tsaya nan!"
Kamar ta wuce, kuma sai ta tsaya tare da yowar baya taji menene uzurinsa?
"Wai ke har yanzu baki da hankali ne? Ki duba yadda kike fitowa duka jikinki sake, amma baki damu ba, sai wata hauka kikeyi, toh kije ki samu wasu kayan ki saka, sannan ki saka hijab, domin idan don ni kikeyi? toh bansan kinayi ba, don haka ki gyara rayuwarki,domin ni bana ra'ayin macce wadda sai da ta k'are rayuwarta a wani guri, sannan ni a d'aura man, kin gane nufina? "
Murmushi farha tayi, domin ta hango cikin idon shi, ai wanda baisan makwancin mazan ba zai fad'ama hakan ya yadda, amma ba ita ba da tasan lungu da sak'on 'ya'ya maza, duk wanda ya zauna da anwar, ai zai iya fahimtar koh wanne namiji, k'arshe kuma shi da ke wannan zancen ai an bar mata sirrinsa a hannunta, toh me zai kuma fad'amata ta yarda, kallon sa kawai tayi, sannan ta ce.....
"Ina ganin a gidan aure akace an kawo ni? To idan dai hakane, kenan gidana ne, zan iya zama a yadda naso, ai a gidan umma ba haka nake zama ba, nan kuma naji ance gidan aure na ne, ni a rayuwata, idan zanyi abu, zanyi shine, basai wani ya ganni yaji sha'awata ba, sanin na gama rayuwar aure na da wasu mazan ne yasa na d'auki jikin nawa ba'a bakin komai ba, nake sakinshi yadda ya kamata, don haka kadaina damuwa, kasancewar ka namiji wanda macce irina bata baka sha'awa, ya kamata ka daina damuwa akan duk yadda na fito, domin kaine ka jik'an jikina, kuma zafi akeyi ina buk'atar nasha iska "
Juyawa zatayi ta wuce, ya wani jawo rigar tata da k'arfi, da nufin ta dawo baya, kawai sai rigar tata ta zame, saboda robace da anja zata tafi,k'irjinta d'aya sai da ya fara bayyana, farha taji kunya sosai, amma kuma sai ta dake tayi tsaye tana kallonsa.
"Subhanallh!"
Kalmar kawai da abdul-jabbar ya kira kenan a zuciyarshi, a fili kuma yace.....
"Ke wacce marasa hankalice? Ni kike fad'ama magana son ranki?"
Yana fad'in hakan yana kallon rabin k'irjin farha, dake bud'e, koh a jikinta, duk da taji kunya kuma cikin jin kunyar take, amma bata gyara rigar ba, kuma itama kallonsa takeyi tare da karance fuskarshi tsaf, sannan tace......
"Ikon Allah, yaya Abdul nifa ban shiga huruminka ba, kuma ni ban fad'amaka abunda bakai ne ka fad'aba, ka tambayeni ne, ni kuma na baka amsa, to menene laifina kuma?"
"Kije ki saka hijab shine nufina, ko kuma ki zauna d'akin naki, domin bazaki zo kina bayyana tsiraici anan gurin ba domin ba kasuwar sayen shi bane"
Jin kamar k'aurin abinci na tashi, da sauri farha ta juya domin zuwa kitchen, amma da k'arfi ya rik'ota, ita da shi duka sai da jikin su ya samu wani sauyi, dama farha akwai sha'awa kusa, nan take jikinta yafara rawa, shikuma wani shocking akayi mashi cikin jikinshi, da sauri ya sake ta, sannan yace.....
"Wallahi ni da gidana, baki isa ki tsallake abunda na shinfid'aba, dole kije ki saka hijab, domin ni ba d'an iska bane, haka kawai ki tayar man da bala'in da banida maganinshi, domin ke bakida magani na, ko kina dashi, wallahi gwara na mutu a hakan, da na nemeshi gurinki, domin bakida wannan damar yanzu, domin kin bama wasu"
"Hmmm! To naji, abinci zan duba, sai naje na changr wasu ko?"
"Ke kuma kikasan hakan, ba ki changr ba, ki daina zuwa inda duk zamu had'u"
"To da haka gara ka ce na koma gida, domin dole na fito neman abinci, amma anjima kad'an zan kwashi kayana sai na koma gidan mahaifina da zama, kayi hak'uri "
Da sauri ta wuce kitchen d'in, shi kuma ita yake kallo, har da fara fassara surar jikin nata.....
"Tirk'ashi! ga macce har macce, amma kuma sai Ahankali k'asan nan, wallahi tsakanin jiya da yau na rasa gane kaina, Anya tsohuwar zuma na magani kuwa? Yarinyar cen nason ta karya mashi lagon rayuwarshi, gata kalar tsarinsa, gata ta tara dukan halittar da yake so, farha dama haka surarki take da kyau? Da ace yadda surar taki take, haka gidan sanyinki yake wallahi, da banida matsala, amma ya na iya sai hak'uri, domin kishin dake zuciyata yabawa shekara hud'u baya, idan na tuna nine na reneki saboda abunda nake gani gareki, amma banine na fara saninki a matsayin mace ba, hakan na sa naji natsaneki, amma farha kin chanchanci a yafe laifinki, domin kin rik'i Ikram kamar ke kika haifeta, wayyo Allah! ni Abdul ya zany?"
Jin motsin wucewar ta yasa shi d'agowa, da kanshi, yadda rigar ta take kafin ta wuce, haka ko yanzu take, gabad'aya ya rasa me zaiyi, domin yadda mazaunanta suke yawo a kwanyar kansa, sai yaji danasanin zuwanshi fallow d'in, wajibi gobe ya bar garin nan, domin wallahi bazai iya ba, yarinyar nan kashe shi zatayi, gara yaje cen inda baya ganinta, da ace yana sha'awar mata biyu gidanshi da ya auro kareema, sai dai gabad'aya ganin farha komai ya kwance mashi, domin yanzu hakan mararshi ciwo takeyi.
Mik'ewa yayi tare da duba time, da sauri ya fita domin d'auko Ikram makaranta.
Farha tashiga d'aki tare da dariyar k'eta, ashe haka yake da sauk'in kai? Ita batayi tsammanin haka ba, lallai zata qara daga yadda take, insha'allah sai tadawo farha d'in k'urciya, sai tadawo farha d'in farko, domin wauta zata yita d'urawa a gidannan har sai ya maidata inda ya fitar da ita, wato zuciyarshi, changr kaya tayi, tare da saka wasu riga da sket, suma dai babu sanya aciki, domin material ne amma wallahi, ya kar'bi jikinta, k'irjin farha ya tsaru a cikin rigar domin sun taso ta yadda ba'a tunani, sket d'in ya bud'e daga k'asa, amma daga saman k'ugunta matse yake, sharp nata ya fito ta yadda ba'a tsammani dai farha tayi, juyawa tayi ta madubi taga kanta, tace......
"Wawww! Auntyn Ikeey ba laifi fa"
Jin hon d'in motar shi, ya shaida mata dawowar su, da sauri ta fito bakin fallown babba ta tsaya, ikram da gudu ta rugo ta rungume farha, haka itama tayi mata, suna murna dukansu, itama sai ta koma ita tanata hajujuwa da ita.
Shigowa yayi da lunch box na Ikram ya ajiye a dining, ita kuma ta sauke Ikram, taja hannunta zuwa changr mata kaya, ta zo taci abinci.
Gabad'aya farha yanzu fallown d'akinta bayada rana, domin babban dai da ake cewa gada ta zauna, acen takeyin komai yanzu.
Fitowa tayi da ikram zuwa dining, anan ta zuba masu abinci suna ci, fitowar Abdul-jabbar ya hangosu a dining d'in farha na bawa Ikram abinci, sai yaji wani d'an farinciki a zuciyarshi, amma kuma sai yayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 44