Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba auren soyayya tayiba..,auren huce takaici...,auren biyayya ga iyaye....,to tayarda da qaddarar daduk ta faru kanka haka Allah yatsaroma....,tajuya ta kwantawarta..,rufe idonta suke amma ba barci takeyiba hawayene ke fita idanunta..,kamar zuciyarta ta 'balle...kukan har yafara fitowa...... Dama jabbar abunda zasucine yaje kitcheen d'in yana shiryawa hakan yasa yayi bedroom nashi da sauri domin ya cire kayan jikinshi.... 'Dauke yake da kayan abunda zasuci a plate...,jin shisshekar kuka natashi da sauri ya tura qofar yashiga ya ajeye kayan a Stoll d'in gefe...., Iman duk ta duqunqune fuskarta kuka kawai takeyi..,har batasan yashigoba...,dasauri yajuya gefen gadon tareda aza qafaunshi duka...,yajawo bargon data rufe fuskarta dashi...,anan taji shigowarshi...,yabud'e bargon baki d'aya.., yasaka hannunshi yariqota gabad'aya tatashi...... "Iman me kikeyima kuka...? Kisani qaddarace Allah yarigada yarubuta hakan zai faru tsakaninmu...,nasan tilas akayimaki domin anyimaki abunda saida akayi aka sanar dake...,nima hakan naji daga baya....,Iman nasan yin aurennan an tauyeki da yawa...,kisaka aranki ni yayankine kamar yadda kika d'aukan farko bazan cucekiba...,kuma bazanyimaki abunda bakisoba zanyimaki abunda zakiso Iman...ke amanatace...,kiyishiru zanxama gata gareki kinji...,fatana kitayani da addu'a kinji...,insha allah xamuga alkhairi mai yawa...." Yaqara jawota jikinshi yasharemata hawaye...,yayi murmushi yace....." Toh kema kiyiman nagani...." Ina Iman ai bazata iyaba domin har ynx akwai sauran duhu ga zuciyarta...,domin zamane zasuyi wanda baya sonta..,sbd zuciyarshi tasan tana gurin 'ya'yarta...., Da hakan yaqaracewa "kiyiman mana koh k'anwata.." Dakyar tayi murmushin...yariqota yace "sauko kici wani abu kafin ki kwanta...." Haka tasauko shi da kanshi yabata duk abunda yakamata ace taci tasha...,saida tafara juyar da fuska amma duka bai qyaletaba saida yaga eh lallai ta qoshin..... Yariqata yakaita toilet yabata brush yace tayi..,ta amsa tayi.... Yafito ya bud'e drower d'inta yaciremata wata rigar bacci mai dogon hannu da dogon wando rigar nada hulla akanta..,ya'aza mata saman gadon ya kwashe kayan yakai kitcheen yadawo...,lkchn itakuma ta fito...yace..... "Kisaka kayan barcinki inazuwa...," Yayi hakan ne domin tasamu damar saka kayan...,yafita zuwa bedroom nashi...,sauri tayi tasaka kayan kuma taji dad'i domin manyane sosai..,haka tacire wedding gown d'in tasaka da sauri..,cltad'auke wayannan domin undiss d'intana ciki..,takai drower d'in ta aje tajawo hijab d'inta cikin kaya tasaka...., takoma baki gadon ta zauna...,sai gashi yashigo,Iman sai kame kame takeyi sbd hijab d'inda tasanya saman kayan barcin..., dariya tabashi yace acikin zuciyarshi.... "Iman kenan! toh menene abun 'boyo anan ai nibanganshiba.., koh d'azun ai d'unkin zamani ya rufamana assiri.,amma ai bakida komai...daina 'boye 'boyenki...,zan haqura har sai kinkai age d'inda nasan zaki iya d'aukata..,domin ynx ai halakaki zanyi sbd ni manyan mata kawai ke iyawa dani koh su sai jaruma...,zan riqe ciwona nata renonki har tym yacika...." Duk cikin xuciya yaketa lissafinshi..,kuma yayi tsaye yana kallonta...,cen kuma yayi ajiyar zuciya yamatso inda take zaune gefen ya zauna...,tana wasa da yatsun hannunta...,yariqo hannun nata tad'ago ido ta kalleshi....,gabanshi yafad'i domin takoma mashi farha sak...,kamar da ake kira masu sai ynx yaganta baki d'aya...,tsoro yakamashi da sauri yasaketa domin gada yafad'a wani yanayinda zai yima d'iyar mutane rauni....,yace a kasale domin abun ya motsa.... "Baki buqatar wani abun...?" Ta girgitsa kai alamar komai bataso...,yace... "Toh kikwanta ki huta kinga kin gaji koh...?" Batace qalaba ta juya takwanta..,yajawo bargon yace......" Toh kicire hijab d'in koh...,zai takuraki..." Nan tayi magana tace...."ah ah sanyi akeyi..." Yayi murmushi domin yagano metake nufi...,yace... A zuciyarshi..."hmmm iman kenan nasanki p yaushe kika fara abunda kike boyewa.. Kuma.?" Jawo bargon yayi yace "kiyi addu'a ni sallah zanyi..." Yarufe mata rabin jikinta yashafa goshinta ya rage hasken d'akin yafita domin zuwa d'akinshi yad'awo domin bazai barta takwana ita kad'aiba...,domin shi ko ya kwanta ba bacci zaiyyiba gara yayita nafilarshi koh tafi masa....,fitarshi tacire hijab d'in ta qarasa saka bargon har samanta...,nantake barci yatafi da ita... Shikuma alwallah yayi yadawo yashin fid'a sallaya yafara sallarshi...,nandai barci shima yad'aukeshi a abur sallahr sai safe..,sbd angaji da dawa....... ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… 3 days da bukinsu Iman..., Anwar yadawo nigeria...,farha farin ciki ba'acewa komai..,sbd ynx gidan nasu gaisuwa d'ai ke had'ata da iyayen koh yaushe...,gidan yafara isarta wlhy hakan yasa yau tashirya domin Anwar zaixo gurinta...,tanaso ta fad'ama mahaifiyar amma babu fuska..,hakan dai ta daure ta shaidamata...,ta amsa "da Allah yakawoshi lfy.." Kawai tacigaba da aikinta...,farha hidima kawai akeyi ta taron baqo...., tashirya tayi mugun kyau komai dai2 jikinta....,kiranta yayi yashaidamata ya iso tace yashigo..... Yauce rana tafarko da anwar yafara sanya manyan kaya da hulla..,yayi kyau sosai yashigo yazauna domin yau firar arziqi za ayi ata tsiyaba cikin gida ake zaune..... Suka gaisa irin gaisawar masoya..,tamiqe don kawo mashi ruwa kuma tayima mamah magana cewa zasu gaisa... Tashin datayine saida yalasa bakinshi domin arayuwarshi yanason farha..,kuma bazai iya barintaba....wlhy da mahaifinshi bai yardaba da koh tawacce hanya sai ya mallaketa koh don shiga tsara ai farha tayi...,aganka da itama ai burgewane....shi yata'bata kawai ai wata sigace tacikon qara samun jindad'inshi a gurin lalatarshi.... Shiga tayi cikin gidan tashiga d'akin mamahr tasu da sallama..,take fad'amata Anwar na parlor zasu gaisa... Ta amsa datana zuwa..... Farha kayan more rayuwa ta girke mashi nagani nafad'a...,kuma yaci yasha...,amma imaninshi naga farha da bagidansu yazoba dababu abunda zai hana bai latsetaba domin tayimashi kyau sosai.... Shigowar mamar da sallama yakatse firar luv d'insu....,yaduqa har qasa yagaida cikin mutunci...,da ka ganshi kasan ubanshi na zubar da naira...,suka gaisa da fara'ar mamar tabar parlon.....,kud'i yacire bandur biyu na yn 1000 yacema farha takaimata tasaka kati...... Farha nazuwa dasu mamar tace bataso amaida mashi..... Farha bataji dad'iba kuma bazata iya mayar mashiba hand bag kawai tasaka...,tace mashi tana godiya p........ya tashi yadawo kusa da inda take zaune.... "My farha dady ya aminta da aurenmu...,zaizo nema man aurenki 2weeks masu zuwa...,dakyar nasamu ya yarda...sbd banson narasaki.....,dis week nahad'amuna party dakuma birthday d'ina tym d'aya..... Yrda da aurenki da dady yayi ai dole muyi murna......, amma dole kixo domin kece keda gurinfa....." Murmushi tayi hadda zare manyan idanunta duka.,tace.... "Na isa naqi zuwa hidimar my only one..,wadda yashirya domin ni da shi...., saidai tunda nake banta6a zuwa party ba koh da k'awayeneba.....,sbd ba'a barinmu zuwa......" Saida yakai ga riqa hannun nata..,yadubeta da sigar magiya...... "Plx kiyi duk yadda zakiyi ba dad'ewa za'ayiba burinah kawai na ganni dake gurin farincikin rayuwata...." "Insh'allah zanxo..." Sakinta yayi yaqara kashe mata murya..,wanda saida jikinta yayi sanyi sosai..,lumshe manyan idanunta tayi...,harsaida yayi kissin d'in hannunta yace... "Muje kikar6o tsarabarki ta jidda.." Yawuce tabishi har gurin motar..,kayane yaketa kwaso mata masu yawa..., da kayan kwalliya...farha bata iya d'aukesu duka saida tasaka almajirinsu ya riqa mata..., Sukayi bankwana sai sun had'u a waya...batabar gurinba saida ya wuce.... Komawa ciki tayyi tabawa almajirin 500 ..,tashiga d'akin mamar tata..,dama taga kayan ita tace akaimata d'akinsu cen a ajiyemata...,mamar naganin shigowarta..tace.... "Suna d'akinki....adaibi duniya sannu...,don duniya budurwar wawa...,gada *so yazamo dalilin hawaye nan gaba*....." Tunda farha taji tagane nufinta sai takama gaban tayi d'akinta....,wai ita ba'a sonta.... Fitarta mama tad'auki waya domin jin lfyr d'iyarta Iman...... *Bee Been masoya*๐Ÿ’ž [1/14, 12:17 PM] Bee Been๐Ÿ’ž Masoya: ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ* ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง ยฉยฎ Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ โ˜…TRUE LYF STORYโ˜… โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… *~ADDU'AR NEMAN TSARI DA ABOKAN GABA...~* *_ุงู„ู‡ู… ุฅู†ูŠ ุฃุนูˆุฐ ุจูƒ ู…ู† ุบู„ุจุฉ ุงู„ุฏูŠู†...ุŒูˆุบู„ุจุฉ* *ุงู„ุนุฏูˆ....ุŒูˆุดู…ุงุชุฉ ุงู„ุฃุนุฏุงุก.._*.๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘} ~โ˜… ุฃุฎุชูŠ ุฎุฏูŠุฌุฉ ุจูŠ ุจูŠโ˜…๐Ÿ’ž~ Page... โ˜…1โƒฃ6โƒฃโ˜… ยฎ IMAN na kwance da wayarta a hannunta bedroom nata...,kiran umma yashigo.,da sauri Iman tad'aga...,tafara da cewa.... "Mamah har naji sanyi danaga kiranki...,domin banida kati wayana.., kuma inason bajiki da yaya farha kuna lfy...?" "Iman muna lfy qlau yakuke..? Hope komai lfy...,?" A fili iman ta amsa da.... "mamah lfy qlau..,kuma banida mtslr komai..,saidai atayimana addu'ar samun qarin alkhairi..." Azuciyarta tace...,yau 1week da aure..,wanda aka had'ani dashi..,banice rayuwarshiba kallon arziqi bazai yiman ba...,sbd banice rayuwarsaba..,iya karsa mugaisa...,yawani yiman tambayar banxa....wai harda wani cewa yakeyi IMAN ba wata matsala koh..., shikenan firarmu dashi..., sannan ace ina lfy..?" Mama taji shiru tayi magana ba a amsaba taqaracewa... "Iman kina nan kan wayar kuwa...?" Hawaye nat xubo mata masu zafi tabud'e bakinta da kyar tace..." Eh mamah inajinki.., netwk ke hana kiji menake cewa amma ni inajinki...." "Toh Iman dama nace bari naji lfyrki...,kuma naji a nasihata baki mance komaiba..? Sbd kinsan kece macce, kece yakamata ace kina saka sonki da k'aunarki a zuciyar mujinki...,inason ki kwashe zuciyar jabbar gabad'aya..,yadaina tunanin yr uwarki..,kisaka soyayyarki dutse a zuciyarshi..,Iman kinsan ni na haifekikoh...? Toh babu wata kunya tsakanina dake..,ni mahaifiyarkice ni yakamata nasanar dake komai..,kasancewarki yarinya nice jigon qarasa tarbiyata ta uwa...,idan abu yashige maki duhu..,gada kiyarda ki fad'ama kowa koh da mahaifinkine..,ni kisameni ki shaidaman zamu war ware komai...., jabbar bayada wuyar kamu kinsan na reneshi nasan halinshi kema nasan naki...,don haka ki zage damtse..,ba ruwanki da baya kulaki kedai aikin sarrafa kanki shine jarinki gidan aurenki...,kamayar dashi tamkar waina ba boka babu malam ...,hijab d'innan da akaceman shi kike zama dashi kiyi cancel d'in zama dashi....,zama bedroom kibarshi sai tym d'in kwanciya...,ke gada kiqara yadda jabbar ya kwana wani guri inba tare dakeba...,idan baki fara wannanba daga yau ki fara..., domin rumaisah tasanar dani komai..,kuma kayan dana aiko maki dasu ki zage damtse kishasu sbd wayannan abun dakika gani zasu sauyaki tamkar bakeba..,kifito kicigaba da dafa abinci da kanki ba ruwanki da baya kulaki shi dakainai zai kawo kanshi...,kuma kinsan ance ummanshi zata dawo part guda wanda aka gyaramata koh...,? Toh kicigaba da biyayya Iman zakiga haske......" Tashare hawayenta..., tace a zuciyarta....mamah bazaki fahimtaba jabbar koh son kallona bayayi maganarsa d'aya dani..,ba wata mtsl toh kije ki kwanta..,koh kije kiyi sallah...,toh koh me zanyi ai bazai ganiba..,narasa meyasa koh irin wasar nan da yake yidani gida ynx bayayinta dani...,saidai babu abunda narasa na rayuwa na ci koh sha..,koh yaushe da abinda yake zoman dashi..,yashiga tabani ya wuce...,tun ina tsoron zama ni kad'ai har na fara sabawa...,don haka da mamar tafad'a mata dawowar umma taredasu farinciki yakama Iman wanda saida mamar tafahimci hakan a wayar...... Jin kawai tayyi mamar tace..... "Allah yayimaki albarka Iman yabaki ladan abuda kika zo yi yakuma jawo hankalinshi gareshi...babanku nagaidake....." "Ameen mamah nima ina gaida kowa da kowa har ya'u almajiri๐Ÿ˜Š..., mamah 'ya'ya farha koh kirana batayi gashi ina missing d'inta sosai...." Wani kukan ya kufce mata hakad'ai yr uwarta taqita duk kan jabbar..,shikuma gashi sai ko inkula yakeyi da rayuwarta....,mamar tace..... "Iman ki manta da farha kamar yadda ta manta dake...,kiyi abunda ke gabanki...,kidaina tunaninta kap...,domin inkina kawota kusa dake zaki dinga samun mtsl ga abunda nace....,ai xaku had'u wani lkch kidaina kuka kinji....." Taji sanyi da maganar mamar tata...,sukayi bankwana..,takashe wayar ta ajiye domin zatayi alwallah tayi sallahr la'asar.... Shigarta keda wuya taji tsayawar motar jabbar..,b a fi 3mnt ba yashigo taji shigowarshi d'akin...,kidanta takeyi...,jin motsin ruwa yasashi gane tana toilet...,hakan ya ajiyemata ledodin take away da abunda take buqata duka yafita....,fitarshi keda wuya Iman tafito....,wayarshi taji tana qara domin bai bar corridor d'in d'akinba...,har tasaka hijab d'in sallah sai kuma taji yafara magana saibata kabbartaba...,da alama wanda yakirashi tsokanarshi yayi...,don daji ango yakirashi..,sai jin tayi yana cewa...... "Basheer banson Iskanci wlhy...,wanne ango kuma...? Ai kamar yadda kakirani da angon k'waila kawai kabarshi hakan domin Iman k'wailace wlhy aka kawoman...,da raino bata isa abunda kaike tunanin na gabatar mataba...,kai inda na sha mai wlhy da ynx kajimu assibiti domin zanjimata ciwo waccen alhaki...,shiyasa koh zama bana bari muyi sosai domin akwai abunda nakeji idan tana yiman kalar kallon da farha keman...,toh tsoro nakeji gada gada tasa na afkamata najimata ciwo shiyasa naketa kaucemata...,wlhy jiyama saida nasai maganin 8k akan mtslta sbd in yatasoman ciwon kamar zan mutu....." "Jabbar kadaina shan pill's d'innan zasu halaka ka wlhy suna Illah....,Iman tawuce qwailar dakake kiranta zata iya...,saidai duk da hakan kabita a hankali domin wlhy nasanka....." "Kai wlhy Iman bazata Iyaba zan kashetane kawai amma zan haqura..,kuma bazan iya zinaba wlhy...,har sai ta cika 20 years ranar zamu fara amarcin mu....,don haka kagane.....,yauwa dis week umma zata dawo inason kazo mu d'aukota sbd gyaran wani abun nikad'ai da wuya....." Basheer ya amsa masa tareda jinjina masa..,kuma yace a gaida qwaila..., jabbar dariya yayi ya wuce d'akinshi don watsa ruwa.... Iman da za'a sallah sai sallah tafasu..,domin ita baqin cikin yayimata yawa wlhy...,ajiye hijab tayi takoma gaban dressing mirror tayi tsaye mamaki da baqin ciki yanaso yakasheta....,tamiqe dai2 tadubi kanta sama daqasa tafara cewa..... "Buhun wulaqanci...,shin wai nice qwaila..? Tashin hankali..,dama d'aukarda jabbar keyiman kenan....,? Shiyasa baya zama tare dani...? Toh wallhy zan nunamasa ai nahin sunana *khadija Aliyu Abbas*...,kunya ce gareni badai tsoroba....,lallai zama da hijab yasa jabbar son ganin makwancina har yake yiman iqirari da k'waila...,yaje school yatambayi qawayenah waye Iman..? Banda qaddarar aure datazo nan take babu soyayya....dashi idan nafara turomai tsantsar soyayyata wadda nadaiga ina yinta bansan inda na koyetaba wlhy ko hannu sainace yad'aga zai d'aga.....duk da naji tsoron jiman ciwo dayace zaiyi...,zansan yadda nakare kaina da wannan domin tabbas wancen d'an gske ne daganinshi hero ne shi.....,amma wlhy sai jabbar ya furta da bakinshi cewa ni macce ce wadda zatafi macce yr 23 dayake tunani itace macce.....,to iman zata saitoshi a hanya badon yasoniba badon yafurta yanasonaba saidon yagane kuskuren fad'amani kallamar k'waila da yayi.....tabd'i jam..,inji yarensu baba filloh....,jabbar ka sawo kanka kuma ka sayar kyauta....,zakaga reno wlhy don ni saidai ynx na reneka...,kuma tunanin wata azuciyarka sai bayan raina in xangani....." Qara juya kanta tayi ta murza idonta duka biyu...,tace..... "K'waila K'waila Iman khadija K'waila..., boom zai tashi gidan jabbar daga gobe...,ina gayyatar yn kallo...,don kayan lefena zasu fara aiki...,mama karantarwarki ga Iman zata fara daga gobe...,hakanma kitsaya ni zan qarasa haddacewa har wasu su kwasa..,๐Ÿค™๐Ÿป๐Ÿค™๐Ÿป๐Ÿค™๐Ÿป Iman k'wailah......" Sallaya ta hau domin duba agogo datayi ha 5o'clock tayi batayi sallahr asri ba..,mamaki da surutunta itakad'ai yad'auki lkch...,tayi sallahrta cikin kwanciyar hankali...,tayi addu'ar data saba yi...,ta cire hijab d'inta ta linke da abur sallah...,taduba ledodin daya zo dasu...,tacire abincin gefe tasa a d'ayar ledar kayan kwad'ayi tazube a d'ayar...,it means abincin tayi parking da cin na waje..,nata zata ringa ci...,kayan kwad'ayi kuma dama aminnantane..... Drower d'inta tabud'a gefen kayanta wayanda tatanada don wata rana su takwaso baki d'aya taxubosu saman gado...,tabud'e akwatunanta takwaso kayan kwalliyar lefenta taduba masu rana aka jera dressing mirror...,atampopi ta jaye takaisu cen qasankayan English wear sune a sama.... Malam hijab aikinka yaqare don ranarka sallah koh baqi insunxo...,domin aikin ynx banaka bane na qwailas ne๐Ÿ˜‚.....,da hakan taqare komai tagyara gurin tad'auki abincin takai kitcheen ta a jiye....,tafara shiga store ba wasu kayan miya da za'a sarrafa abinci amma akwai qwai...,dubarar soya breed da k'wai tafad'o mata hakan tasoya burinta qamshin dafa abu kawai takeso yatashi...,ta had'a tea dinta da madara tadawo pallor amma bata cire hijab d'intaba..,sbd gobe plans d'inta zasu fara aiki ba yauba..... Fitowarshi wanka yaqagu yaji inda qamshin suya ke tashi...da sauri yafito..,hangota zaune yayi tana kallo da cup da plate gabanta...,qarasowa yayi...,yace.... "Ah yr qanwata..,bakiga abincin nakawoba halan kikeshan tea da marece..?" "Naganshi har gayacen a kitchen idan kasamu wani bawan Allah mai nema kabashi....,yau kuma nagaji da abincin inyamurai gara nasha tea d'in zai fiman..,wanda yasaba cin abincin mama ai nasaye zai gagareshi ci...,shiyasa naga nawar umma tadawo kusa dani..,kwanon abincina yadawo hannunta...brox gobe asayoman kayan miya da sauransu...,nafara dafawa kafin umma tadawo......" Mamaki yakasheshi shin yaushe iman ta iya surutu hakan ne wai..? Don Iyakarshi da ita gaisuwa saikuma wasa wadda suka sabayi ba mai yawaba domin girmamashi takeyi sosai.... Don d'aukarshi uwa daya uba d'aya dasukayi....yadubeta koh zama bazaiyiba..,yace..... "Wannan aikin ai ynx banaki bane..,kibari tym na zuwa saiki cigaba...,ni zan fad'amaki idan lkch yayi...,ynx kidinga hutawa mana yr qanwata...." "Ah Ah ynx zanyi sbd hutu ai tsufa yake kawowa nikuma banaso natsufa da qurciyata ta yara qanana gara nayi tunda na iya...,idan natsufa lkch yaqureman ai....kakawoman zan iya dafawa dakaina inkai bazaka ciba..,sai kaci na inya murai....." Mamaki yakamashi idan yayi cen tayo nan...,ita batasan meyake kiyayewaba...,domin shi yana gujema abunda zai dinga had'asu sosai gada d'igayar ciwonshi tatashi ya falketa...,amma sbd qurciya ita taqi fahimta toh ya zaiyi..,tunda haka Allah yaso dashi dole yayi haquri yabi qurciyar yayimata abunda takeso tunda yace yad'au alqawalin riqeta amana..., juyawa kawai yayi...,yabi hanyar kitchen d'in yad'auki take away..,d'in yayi waje..., kallonsa takeyi tanashan tea d'inta har yafita...... "Hakan dai yafi maka domin har ynx bazaka fahimci Iman ba.....,sai darasin qwaila yabi ta jijiyoyin jikinka.....mudai je zuwa....." ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… Farha tunani kawai takeyi ta yadda zata bullowa xuwan partyn Anwar domin yadameta jiyama yayi mata magana gashi gobe ne za'ayi..,kuma tasan wlhy ynx zatayi wuyar fita amma bari ta kira Rasheeda taji koh zata kareta...,inyasso dataje bazata bari ta d'ad'eba tunda yace 8:pm za'a tashi...,kwata kwata batason 'batawa jabbar raine shiyasa dabazata neme taimakon kowaba wlhy...,kuma bazata jeba..... 'Daukar wayarta tayi tafara kiran rasheeda donji yadda abun zai kasance...,ringing ukku rasheeda bata d'aukaba...,sai a ringing na hud'u sannan ta d'auka..... "Aminiyata ina kika shiga..,inata neman ki tund'azun...?" "Hmm farha ai nad'auka son Anwar yarufe maki idon da ko sanin ni wacece a gurinki...., tunda naga baki gane zancen kowa sai nashi..." "Hmm dama nakiraki don nayi missing naki..,kinsan ynx bana fita koh ina shiyassa baki ganina..,nibansan yazamu qareba idan aka koma school ba...." "Hmm farha duka ke nat sawo wannan mtslr p...,kuma a kullum addu'a nah agareki Allah yasa aurenku ya tabbata da shi domin nasan waye Anwar...,amma may b sanadiyarki ya shiryu domin naga yana sonki...." "Addu'arki ta kar'bu rasheeda insha'allah next to week za'a kawo kud'in auren Anwar gidanmu..,kuma Anwar baida wata mtsl nafahimceshi...." "Ah aminiyata nayi murna hakan yasa nagane cewa Anwar dagsk yakeyi ynx tunda yanace a aurenki....,so sone Aminiyata Allah yanunamuna namu lkchn..." "Ameen..,plz rasheeda inada walima da aka gaiyyaceni...,so muna shiri da yarinyar sosai za'ayi walimarta..,toh nasan baza'a barniba shine nake roqon alfarma..,koh da mama takiraki kice yr uwarkuce tare zamuje..,don Allah...." "Ok insha'allah gada kiji komai saidai zankiraki p sbd farha gada kidad'e har assirinmu ya tonu...,4:pm kikace za'ayi ana qarewa kiyi gida....,next 2morrow insha'allah zanxo nayini musha fira..,tunda gobe busy kike....," "Ok Insha'allah qawata komai zaizo a normal...." Rashida har zata kashe wayar kuma sai tace.... "Farha kinada lbrn su Iman kuwa...?" "Toh eh kuma ah ah sbd ni bana koh gaisawa da ita...,amma inajin suna waya da mama...,kuma naji muryar mujinta shekaranjiya yashigo ni koh muryarsa banson ji....." "Innalillhi farha..! Kinada hankali kuwa...?" Gada qiyayyar jabbar tasaka ki qiyayyar yr uwarki uwa d'aya uba d'aya...., kisani ynx bakida tamkarta koh bayan aurenku...,ki lura ki hankalta..,gada qiyayyar jabbar tajawo qiyayyar Iman zuciyarki...., qarshe hakan yazamo *Dalilin hawayenki* ........" "Hmmm bazaki gane bane Rasheeda..,kawai sai kinjini domin in nashirya zan kiraki na shaidamaki goben don planning d'in namu yadai2 ta......" "Hmm naji farha agaida Anwar da mama......" Suka katse wayar..,hankalin farha ya kwanta domin tasan mamah bazata hanata zuwaba indai rasheeda ce....,hakan tayi ta tsara abun domin bata saba zuwa party ba gashi zataje gobe...,Allah yasa gada tayi qauyanci gurin......... Nace ameen kuma a qare party lfy๐Ÿ’๐Ÿผ..... ~UMMUL ELHAM~ *Bee Been Masoya*๐Ÿ’ž [1/16, 9:12 AM] Bee Been๐Ÿ’ž Masoya: ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ* ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง ยฉยฎ Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ โ˜…TRUE LYF STORYโ˜… โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… *_ุงู„ู„ู‡ู… ุจูƒ ุฃุตุจุญู†ุง...^ ูˆุจูƒ ุงู…ุณูŠู†ุง...^ ูˆุจูƒ ู†ุญูŠุง ูˆุจูƒ ู†ู…ูˆุช ูˆุงู„ูŠูƒ ุงู„ู†ุดูˆุฑ...^ ู„ุง ุงู„ู‡ ุฅู„ุง ุงู†ุช ุณุจุญุงู†ูƒ ุงู†ูŠ ูƒู†ุช ู…ู† ุงู„ุธุงู„ู…ูŠู†...^ ุงุณุชุบูุฑุงู„ู„ู‡ ุงู„ุนุธูŠู… ู…ู† ูƒู„ ุฐู†ุจ ุนุธูŠู…๐Ÿ˜ญ ูˆ ุฃุชูˆุจ ุฅู„ูŠู‡๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป...._*๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… _YABON GWANI YAZAMA DOLE_ *FATIMA AZLAND โคUMFATโค* *_๐Ÿ’งยฉREAL PURE MOMENT WRITTERS ADMN...โœ๐Ÿ’งMUTUNCINKI DABAN NE ALLAH YASA KIFI HAKA DA MEMBERS NAKI BAKI 'DAYA...,BASAI NACE KOMAIBA KIN GANE ADDU'A TAH TA K'ARSHEN.......๐Ÿ˜NACE....,AMEEN AMEEN๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป..., Bee Been kuce๐Ÿ’ž_* Page... โ˜…1โƒฃ7โƒฃโ˜… ยฎ IMAN tatashi da qudurinta..,na yau ita zatayi breakfast da kanta domin yau planing nata xai fara.., qwaila zata fara aiki....,dama zasu kwana d'aki d'aya amma koh yaushe sallahr dare yakeyi har barci yakwasheshi..,toh assubahin idan yaje masallaci baya dawowa d'akinta saidai dasun gaisa zai wuce d'akinshi..,kuma bazai fitoba sai In zai samamata break.., Yau Iman da kanta zata nemi break d'in....,cire abayar datayi sallah da ita tayi tareda cire hijab d'inta ta lunke...,toilet tafad'a domin yin wanka don dama tafison wankan safe koh gida yafi zamemata tsari domin tasaba dashi sbd zuwa school....,fitowa tayi da kayan dataga zasufi dacewa da aikinta...ta bud'asu tayi murmushi.., yau zanga dawace qwailar zancen zai fad'a...,ta ajiye ta koma tashafa cream kad'an..,baki turaren jiki ta bud'e tayima kanta wanka dashi..., d'auko kayanta tayi ta bud'e tana dubawa....,wani sket ne iya karshi ya rufe gwiwarta..., kuma daga sama ya matse..,rigar kuwa samanta duka net ne jiki wajibi duk wanda yasaka rigar a ga rabin qirjinshi waje dogon hannu ga rigar saidai matse yake sbd roba ne.... Iman tayi murmushi sannan ta d'auko brah d'inta tasaka domin zata qarama rigar kyau kuma taqara show d'in mai kallonsu domin zata saka su taso dai dai2...., tasaka kayan duka tayi rolling kanta da qaramin gyale..,bata tsaya yin wata kwalliyaba domin kitchen zata je...tadubi kanta sosai a madubin sannan tace.... "Iman dga ynx nayi hannun riga da kunya...,xanyi yaqin nemo yncina na and'aukar qaramar yarinya kawai don yaga ina kunyarshi....,to zai gane da tantiriyar da yake zaune...,saidai tantirancin shed'ana irin tawaba...,bawata kalar ba....,Iman qwaila Allah yabaki sa'a tafi kitcheen aikinki......" Ah su Iman p ita kad'ai ke firarta a d'aki sai madubi...,da haka tasaka takalminta dai2 yadda tafiyar zatayi kyau tafita...., Shigarta kitchen ta duba komai da komai akwai kuma yasiyo jiya kamar yadda ta buqata...., Tafara tsara aikinta yadda taso..,duk wani abu datasan idan zatayi shi qamshi zai tashi shi Iman takeyi...,nan take komai yasauya domin gidan yad'auka..,cikin kwanciyar hankali ba wani jin tsoro koh kunyar abunda takeyi domin ta aje kunyar a d'akin tafito.... Qarasa aikinta tayi tagyara gurin kamar ba a yi komai acikiba..,tajera abunta a dining ta jawo kujerar ta zauna...,bud'ewa tayi tafara ci...., Jabbar na d'aki qamshi soye soye duk ya dameshi kuma yarasa ta ina yake fitowa hakan yasa yafito domin monday ce akwai aiki..,yanason ya samama Iman abun kari ya wuce office....,fitowarshi kenan ya hango wata zaune a dining..., shakku ya kamashi domin baquwa tunda safe a gidansu...,kasancewar Iman bayanta tajuyo tanata hidimar break d'inta kuma taji fitowarshi amma saitayi kamar batajishiba...,hakan yayi tsaye yana saqe saqenshi...,cen kuma sai yayi sallama yashigo...,d'agowa tayi da cup d'inta a hannu tana cin wani abun..., ta amsa mashi sallama.... Jabbar daskarewa yayi sosai..,domin abun na shirin d'aurar mashi kai...,shin Iman ce koh kuwa watace....amma kuma ai ga fuskarta nan jikin ne at bai ganeba..., qara d'agowa tayi tace.... "Brox ina kwana...,?" Kafin ya ams saida miyon bakinshi suka tsaya sannan yace..."lfy qlau..." "Bissimillah ga break..." Shin shakku zaiyi koh koh tambayarta xaiyi yaji shin itace...? Gabad'aya kallo ya koma sama p....,Iman tafara gane yafara shakku ne..,hakan yasa ta qaracewa.... "Nace fa bissimillh...,baka amsaba..,koh da yake na mance kace ba ynx kakeso na fara abincin dazakaciba...,dama kuma nawa kawai nayi sbd bana qara cin na inya murai..,In zaka ci kuma nasauko maka dashi nan qasa gada kace qanwarka rowa ne da ita...." Duk maganar da takeyi jabbar ba cika gane me take fad'iba yakeyi..,domin mamaki yakusa kasheshi...,dama Iman haka take take zama cikin hijab...? Dubi yadda tafito don Allah wazaice yr 18 years ce...,wlhy da farko na d'auka farha ce ke yiman gixo ashe ba hakaba...,sai da tayi magana nagane cewa Iman ce dai..... Bai qarasa mamakiba Iman tasauko daga dining d'in zuwa inda yake da plate da cup d'inta a hannu..., takowa tayi a hankali cikin sigar burgewa ta jawo centr table d'in ta azamashi gabanshi... Innalillhi mamakin qanwa zai kashe 'yayanta..., Iman dama nada cikar haiba kamar haka...,shin wai wannan qirjin natane ko na kantine ta sawo...,domin ai bai ta'ba ganinshi garetaba...,qugun da yake ganin bazai iya d'aukarsaba shine yake hange cike cikin sket...,koh dai shima qarashi tayi...? Yanata tambayar zuciyarshi yama kasa cewa komai...,jin maganarta da matsowa kusa da inda yake yadawo da hankalinshi.... "Brox kaci koh kad'an ne don Allah naji dad'i yayanah ya aminta da kalar nawa karin...,kuma kaga tym yaqure...,idan kace zaka tsaya neman abinci zakayi late p...,kuma ni qanwarka amanarka bazanji dad'iba..,plx my brox....." Tashin hankali wani juya murya tayi kamar ana kad'a sarewa takira my brox d'in...,jabbar fa yarasa gane kanshi...,tsan tsar mamakine koh tsantsar gid'imace...,shi babu abunda yafi bashi mamaki..,yadda yaga surarta qirjin nata shine abu mafi bashi mamaki....,idan dai har natane...,toh ya akayi bai ta'ba ganinshiba iya zamanta gidan kap baita'ba ganinshiba..,haka kohda take gida idan yaje ba ganin shi yakeyiba...,amma wai yau shine yake gani tumbul a qirjinta tab ana zaton wuta a maqera sai ta leqa masaqa...,tashin hankali sabo...., Jin maganarta kuma a kalar wancen yanayin yadawo dashi tunanin da yakeyi...,domin kap jabbar yafara soke kanshi tun kapin aje koh ina p..... "Brox shikenan.,dama ni nasan baka damu daniba...,baka d'aukeni a matsayin qanwar da kake kiranaba...,idan ban mantaba kai kace da bakinka zaka riqani amana...,zaka so abunda naso amma duka kamanta alqawalinka......" Fashewa tayi da kukan kissa kap shagwa'bar daba tata'bayiba ta tsiro da ita..,duk da dama saurin kuka gareta...,kukan irin mai tsuma zuciya...,nan take jabbar ya saita kanshi da tunanen da yakeyi....ya ce da sauri..,domin tsoron ta'bata yakeji...,irin yadda yake matse xai kashe Iman wlhy kuma yasan bazata iyaba...,gara yabita ahakan har sai takai shekarun da yad'iba.,zaiyi haquri kawai...,don bai yardaba har ynx ace wannan cikar jikin ta

Chapter 7 of 44