Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
..,nabiyun da sauqi saidai har lkch da zafi hakan yasa tanata raki da hawaye...,ana ukkunne bataji zafiba sosai...,sai wani dad'in ruwan datakeji domin suna shiga jikinta dai2... Hakan da jabbar yaga tayi shiru alamar da sauqi ynx...,sai yafita yace yana zuwa...., Zanen gadon yakeson ya changr..,d'aga bargon dazaiyi babu abunda yagani sai jini..., "Subhanallh Iman dole ki wahala wlhy...,dole kiji jiki ashe haka najimaki ciwo da yawa....? Ikon Allah wlhy bansan nayiba...,abunne babu control koh kad'an don wlhy abunda naji har baya misaltuwa rayuwata, ALLAH nagodemaka...,daza'baman abu mafi alkhairi dakayi a rayuwata..,samun Iman wani yankene daga ni'imar duniya ya Allah karayamu tare...." Ameen jabbar...,kwashe zanen gadon yayi ya aje gefe ya shinfid'a wani...,yagyara koh ina dai2...,kwashe kayan barcinsu yayi ya aza gefen zanin gadon wanda za'a wanke....,d'akin Iman yaje yad'aukomata wata doguwar riga mara nauyi ya aje gefen gadon bayan ya fesheta da turare...., toilet d'in yafad'a wanda yasamu iman har wankan tsalki tayi domin har ta d'aura towel jikinta saidai takasa tafiyane.... Murmushi yayi sannan yaqaraso inda take...,ya rungumota yayi kissing nata a goshi....,hakan yasa Iman duqar dakai qasa tayi....hakan yasa yad'auketa sai gefen gado ya ajeta a hankali....,rigar yad'auko yasakamata babu yadda ta'iya domin komai bazata iyayima kantaba sbd koh ina na jikinta ciwo yakeyi...tsayawa yayi yana duban fuskarta had'a fuskarshi yayi da tata fuskar suna kallon junansu...,hancinshi saman nata goshinshi saman goshinta yahad'a bakinshi da nata kuma sai yayi magana...... "Sannu hasken zuciyata...,Allah yayimaki albarka kinsakani farincikin da har nake tunanin bani neba...... *IMAN INASONKI HAR QARSHEN RAYUWATA*....." kissing nata yayi sannan yamtso da pillow d'in kusa da ita yakwantar da ita...,yajawo bargo ya rufeta...yajuya ya kwashi zannuwan gadon yatafi toilet ya wankesu duka..,yayo wanka yafito...,jallabiyya yasaka yashinfid'a sallah Capet ya kabbarta sallah don miqa godiyarshi ga Allah da wannan ni'ima da yasakamashi da ita...,yaqare sallah..,sannan yad'aga hannu roqon Allah zuri'a d'aiyyaba dakuma soyayya mai d'aurewa dashida iman...,qarasawa yayi yatashi ya haye gadon yajawota jikinshi yasanya bargo ya rufesu cikin sanyi da nishad'i..... Basu falkaba har 9:30am shima kiran wayar ummanshi ne yatayar dasu...,har ta tsinke baisamu qarfin d'aukaba...,sbd bayason yad'aga da qarfi sbd Iman dake jikinshi kwance duk ta maqalqaleshi...., jin jikin Iman da zafine yasa jabbar qara ta'ba kanta da jikinta...,duka sunyi zafi sosai Alamar zazza'bi ta kwana dashi....,a hankali yajawo pillow ya d'an janye jikinshi ya azata yajawo bargon yagyaramata....miqewa yayi a hankali ya jawo wayarshi yaduba missed call na umma har biyu...,tym yaduba 9:35.... "Subhanallhi har tym yakai haka bamu saniba....?" Tashi yayi yashiga toilet yad'auro alwallah yayi sallah...,sannan yad'auki wayar tashi yayi fallow domin kiran umma yaji lfy....,kiranta yafara batafi ringing biyuba ummar tad'auka...,gayar da ita yayi....,sannan ta amsa tace.... "Lfy qlau babanah dama nakirane naji Iman lfy take..,naga jiya bangankuba dukanku tunda kukashigo muka gaisa...,ynx kuma gashi har nafita baku fitoba...,dama zan fad'amakane idan xakaje aiki kawuce dani gidan babanku Aliyu toh kuma sai ba'a d'aukaba...,nasamu napape na hawo...,ina bisa hanya ma...." "Eh umma batad'an jin dad'ine tunjiya shiyasa nima bansamu shigowaba...,amma da sauqi sosai....,kuma yau baxanje aikiba sbd gobene tafiyarmu muna shiryawane....,muna gaidasu zanxo d'aukarki...." "Toh yayi sai naqare zankiraka....,kagayar da iman d'in kafin mudawo...,kuma tadaina yawan aiki domin lfyrsu sai ahankali...." Murmushi jabbar yayi yace...."toh umma insha'allah za'a kiyaye...." Yakashe wayar yaqara muemushi yace.... "Umma dai har kin aza d'iyarki tasamomaki jika...,toh sai jiya ma mukasan k'ofar aikin inda take....,amma ai koh yau a iya samo abunda kikeso umma..,don nayi aiki babba....." Falkawa iman tayi cikin matsanancin zazza'bi ga sanyi tanaji gashi har ynx da sauranta....,rarrafawa tayi tayo alwalla ta hau daddumar sallah dataga yaqare tayi itama tayi amma takasa d'agawa sbd zazza'bin yayi yawa...,kwance tayi anan.... Jabbar na kitchen yana had'amasu break yadda da tatashi kawai ci zatayi...,qarasawa yayi yazo domin tayar da ita.... Shigowarshi sai yaci karo da ita a saman sallah capet kwance..,alamar har tayi sallah...,da sauri ya matso inda take yariqota...jin jikinta zafi sosai... "Sweet meke damunki naji jikinki da zafi...?" Bud'e idonta kawai tayi tadubeshi kuma sai tarufe idon nata....,gyaramata kwanciyar yayi yad'auki wayarshi yakira doctor habibu....,yafad'amasa madam d'inshi babu lfy in yana free yataimaka mashi yazo yadubata....,yace yana zuwa..... Fallow yaje ya d'auko break nasu yaxo dashi nan yatayar da iman zaune ya had'a tea yabata tareda dankalin daya soya....,amma duka bataci komaiba...,koh tea d'in saboda ya matsamata tasha...., Hakan yayita yimata dubara har yasamu tashanye cup d'in d'aya....qyaleta yayi domin gada tayi amai.... Ringing d'in wayarshi yafara tashi dubawa yayi yaga doctor d'inne...,don haka sai yad'auko Iman zuwa fallown anan ya ajeta kujerar bayan yasakamata hijab yace.... "Ina zuwa.." Fita yayi yashigo da doctor bayan suna dariya harda tafawa...,saidai bansan me suke cewaba..., dasuka matso ciki...Iman ta kalleshi tagayar dashi duk da kunyar da takeji...,domin kanta qasa yake.... Amsawa yayi sannan ya tambayeta me takeji jikinta...? "Kallon jabbar tayi..,sannan tace... " zazza'bine kawai da ciwon kai..." Yafahimci dai maganar jabbar ne domin wahala ta haddasa mata wannan zazza'bin ya bata magani yace tasha ynx...,zuwa anjima komai normal..., Jabbar ya amsa yayimashi rakkiyya..,suka fita.... Dawowa yayi.,yad'auko ruwa yabata maganin...,sai sannu yake yimata...,tana lumshe ido..,don ita har ynx batada bakin magana wlhy domin yarufe bakin tun jiya bata iya cewa komai...,saidai abu d'aya tasani shine mujin nata ba abun wasabane namijine na gsk wlhy...,itama duk qoqarinta saida takasa..... "Sannu my delight haske zuciyar jabbar...,kitashi muje ki futa domin anjima kad'an zanje d'auko umma kuma ta tambayeki bata gankiba nace bakijin dad'i har tabani saqo tace nace maki kidaina aiki da yawa...,sbd ta aza ciwon samun jikane...." "Hmmm ai duk kaine kahanan ai naje naganta..." Dariya yayi yariqota yace...., "Yau kad'ai nake tare dake...,gobe bana nan kuma sai nadawo..,umma kuma kina tareda ita nukuma ai kinga zanyi missing da yawa koh..." Jin zancen tafiyar nan na'batawa iman rai don Wlhy tafison tadinga ganinshi kusa da ita koh ba komai tasamu farincikin ganin jabbar kusa da ita bale ynx dasun zama d'aya..., marairaice fuska tayi...,nan take ya gane nufinta...., Dariya kawai yayi yad'auketa yayi ciki da ita..,a hakan ya kwantar da ita shima ya kwanta gefenta yana shafar suman kanta...,nan take barci yad'auketa shima barcin ya koma....,2:pm dai2 yaji kiran sallah hakan yatashi ya watso ruwa ya changr kaya don zuwa masallaci kuma yasamo masu abun ci tunda bazata iya komaiba...., Koh da farha tatashi tanemi ciwo ta rasa gabad'aya har qarfin jiki tasamu sanadiyyar maganin datasha....,hakan yasa tatashi da sauri tayo wanka tayi d'akinta domin shiryawa....,sallah tayi sannan tayi silent kwalliya powder da lipstick kawai kaya tasaka material dunki riga da sket...,amma wlhy har ynx tanajin ciwo qasan jikinta sosai ma...,hakan yasa a tafiya take d'ingishi da qafa...,turare tafeshe jikinta dashi tayo fallow..da niyyar shiga kitchen.... Sallamar jabbar tadawo da ita baya...,ganinshi da leda niqi niqi da alama abinci yayo take away nashi...,dubanta yayi da alamar tambaya...., mezatayi...? Dawowa tayi tazauna tafiyar tatama sai slow..., "Hmm kina ahaka kuma zakije yin wani aiki...?" "Ni lfyta qlau..,kadaina d'aukata ragguwa p...,sbd ni jarumace sosai... Don inda wasune sukasha wahalar danasha sai lahira kawai...." Zancenta dariya yabashi sosai...,abincin yafitar yafara fitarwa kala kala yad'auko plate ya xuba...,yafara bata..., Balaifi taci sosai shima yaci.... Harda cemashi tayi.... "Daga yau nakashe siyoman abinci cikin gida wlhy domin banason abincin yahudawannan...," Bai cemata komaiba agogo ya duba...,tym yayi yaje d'auko umma...,dubanta yayi sannan yazauna gefenta yariqo hannunta yace.... "Haske nah...! Zanje d'auko umma gidan mama daga cen nayo bankwana dasu don gobe tafiyar safe zamuyi...." Miqewa yayi tsaye amma bai saki hannuntaba...,itama d'ayan hannun nashi ta riqe cikin shagwa'ba tace.... "Nima zanje...,sai mudawo tare...." Duqowa yayi har tanajin numfashinshi ga fuskarta yace.... "Ahakan zakije kina d'ingishi su umma da mama sugane an amshi darajarki jiya....,? Ai kawai kibari sai kinkoma normal tukunna dai...,nima banda dolene da babu inda zanje ina tareda Ruhinah manne...,muyi jinyar tare amma kiyi haquri bazan dad'eba...." Turo baki tayi...,alamar zatayi kuka...,yayi saurin zaunawa gefenta.... "Ah ah gada ki hanani xuwa d'auko umma Iman...,kukanki ai matsalane ga Rayuwata..." 'Dago fuskarta tayi tadubeshi ta lanqwashe kanta..,tace.... "Kaje kawai ina gaida su mama idan kaje..." Murmushi yayi yasaka hannunshi yashafo qirjinta...,tareda had'e bakinshi da nata na 3mnt sannan ya miqe tsaye...,ya lumshe idonshi yace.... "Take care my haskena...,ki kwanta warki bazan dad'eba domin tunaninki bazai barni naga kowaba sai ke...,koh umma don itace wlhy...,ga wayarki kiyi fira kafin nadawo....," Miqamata wayar yayi tareda kunna mata ita domin shi yakasheta jiya.... Fita yayi itakuma ta kwanta a kujerar...,yana tafiya yana waiwayenta har tafita....... *вee вeen мαѕoyα*💞 [2/1, 1:06 PM] Bee Been💞 Masoya: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH😭😭* 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 ©® Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* 💋💋💋💋💋 ★TRUE LYF STORY★ ★★★★★★★★★ *_True Love💞 Depends On The Willingness To Give Take And Work On The Relationship...,😍 With The Effort That You Have Shown This Far I Cant Doubt The Undying Love That You Have Shown Me..., I LUV YOU ALL MY HEART❤ MASOYANAH😘_* Page... ★3⃣2⃣★ ® Isar jabbar gurin d'auko mahaifiyarshi...,yayi sallama suna fallow dukansu zaune...,mama da umma alamar fira sukeyi...,yashigo yasamu gefe yaxauna..., suka gaisa da mama...., Cen yaji suna fira amma wlhy baisan kota mececeba...,amma yaji ankira farha ciki...,hakan yasa bai maida hankalinshi ga son jin zanceba domin koh hanyar da zancenta zai bi bayason su had'u...,domin itace macce tafarko da tanunamashi tsana rayuwarshi...., Jin ankira sunan nata dakuma zancen babu lfy tare da ita...,hakan yasashi tashi domin yabasu guri suji dad'in magananar....,wayarshi ya d'auko alamar zai kira masoyiyarshi yayo waje..... Calling nata yafarayi...,nan take tad'auka alamar tafara barci ne...., "Haskenah badai har kin fara barciba...?" "Hmmm...,dole ai katafi kabarni ni kad'ai acikin gida...,kuma umma bata kusa...." Murmushi yayi da lumshe ido domin ya tuno wani nishad'i na jiya da dare yace...., "Haskenah! Ina missing naki p sosai...,ji nakeyi kamar nayi 1hour dabaroki duk missing naki yakamani...,plx yauma.....?" "Hmmm yauma me..? Wlhy ah ah sanyinah....,bazan iyaba wlhy..." "Ai ba wancen nake nufiba p...,d'ayan dai koh...?" "Naji ni barci nakeji sai kadawo plx..." Dariya yayi yakashe wayar domin jin alamar fitowar umma..., saka wayar yayi aljihunshi ya tako gurin dasuke tsaye...,umma nayyimata magana tareda cewa..... "Insha'allah zanyi qoqarin inje ingani...,amma kuma kusanya ranku sanyi yaran zamaninnan ai sai addu'a..." Umma tawuce gurin mota anan jabbar yafara yimata bankwana gobe xaije exam abuja kuma zaiyyi week insha'allah....,tayimasa addu'ar samun nasara aciki..., Sukayi bankwana yace zai kira baba awaya yafad'amasa...., Umma tashiga mota shima yashiga suka kama hanyar gida..., Shigarsu umma tace zata shiga taga Iman sannan tawuce ciki... Koh da suka shiga iman na toilet alwallar magarib..,shiga yayi d'akin nata yake shaidamata umma tazo ganinta..., Kallonshi tayi sannan ta kalli yadda take d'ingishi kuma yasa umma zuwa toh ita yazatayi.... Shima dariya yayi domin baisan dacewa zata shigoba...,kallonta yayi yace.... "Ki daure kawai kije domin babu yadda za'ayi domin tariga tazo ganinki..." Hijab iman tasaka takwaso juriya ta aza agurin saita tafiyarta domin wani barkono takeji idan ta had'a qafafun cije baki kawai tayi tatafi..,amma wlhy akwai azaba ciki....,ita bazata qara yadda ba kuma tunda abun ciwone dashi....,gashi ya xamar mata miki ynx....." Fitowa tayi tana takowa a hankali...,duk iya qoqarin iman gada ummar tagane saida tagane komai daga yanayin tafiyarta....,iman tazo gefenta tazauna domin bata iya xama qasa wallhy...,ummar riqota tayi tadawo kusa da ita...,azaton umma iman cikine da ita..,amma ganin yanayinta yanunamata cewa ynx jabbar ke amarcinshi domin ynx tafiyar iman ke changrwa...,tagane zazza'bin da jabbar yafad'a na wahala....., "Iman yaya jikin naki da sauqi koh...?" "Eh umma da sauqi sosai nasha magani....." "Toh masha allah...,gobe idan jabbar yawuce akwai inda zamuje insh'allah..." Dad'i iman taji duk da tasan da sauran warkewa jikinta amma wlhy sai taje koh ina ne...., Ummar tawuce part d'inta..,jabbar yadawo fallown anan yake tambayar yasuka kwashe da umma tace mashi normal suka rabu....,dariya yayi sannan yatafi sallah...." Daren yau lfy suka kwanta saidai jabbar bai yarda koh kad'an iman tamatsa daga inda yakeba...,motsi d'aya yace..."meke faruwa haskenah...?" Iman p duk tafiyar daxaiyine yau ke d'aga mata hankali...,hakan yasa duk tayi sukuku...,gyaran kayanshi takeyi amma badon jin dad'iba domin batason yatafi yabarta...,yajawota yayi tana zaune gefen gadon takwanto jikinshi....,yasaka hannu ya matseta qirjinshi sosai yakai fuskarshi jikin qirjinta ya shaqo kamshin dake jikinta...sannan yad'ago zuwa fuskarta.... "Wai damuwar tamenene iman d'ina...,ni ban damuba sai ke..,zaki damu...? Nine yakamata nayita damuwa nida nad'and'ana zuma kuma zantafi nabarta naje wani guri da banida abokiyar d'ebe kewa...,gashi har ynx baki warkeba da aikin danayimakiba...,bale naqara komawa najiyo wani..." Hannunshi yasaka ya xuge rigar barcinta dake d'aure da igiyoyi yakai bakinshi ciki...,lumshe ido iman takeyi domin tanason wannan abun da yake yimata kuma tanajin dad'inshi...hakan yasamu damar rabata da rigar duka..,wasa yakeyi dadukkan halittun jikinta wani feeling nasaukarmashi...,hakan tata wasa da ita har yasamu yarage abunda yakeji...,itama iman taji dad'in wasar domin tanason jabbar yayi kissing nata kuma tanajin dad'in yayi wasa da qirjinta domin iya ynx tafara gane wayannan al-amurran me suke sawa aji...amma ashiga jikintane at bataso sbd yaji wahala sosai wanda har ynx da sauran miki...., 'Dagowa jabbar yayi domin yaji kiran sallar assubahin...,dakyar ya'iya rabuwa da iman domin hakan kad'ai a jikinta nasashi jin yagamsu...., tashi yayi domin yayi wanka yashirya 6:am zasu fita dayake sunada yawa...,jirgi zasu shiga..., Iman ma jin yatashi itama sai tayi d'akinta sharp sharp tayi wanka tayi alwallah....,fitowa tayi...,sallah tayi tasaka doguwar riga takama hanyar kitchen karn safe tashirya mai sauqi domin yaci...,nantake taqarasa dai2 da fitowarshi shima..... "Haskenah kice har kin had'a komai...?" Langa'be kanta tayi...,taja hannunshi domin tasan zai iya makara har ayi jiranshi.....,break yayi yamiqe don d'auko kayanshi...,iman itama tabishi d'akin....riqe jikkar tayi tafara kuka.... Nan take jabbar shima yaji duk babu d'ad'i amma babu yrda ya iya dole yakawar da nashi damuwar domin yasamu ta daina kukan...." "Iman menene haka kuma...,ai zan dawo...,kisani nima banason tafiya nabarki..,saidai dukanmu babu wanda zaije da matarshi kuma babu wanda yassan yadda gurin yake..,bale naji har naje dake...,idan har kuka zakiyi sai na'aje tafiyar nayi rarrashinki domin nafi sonki akan aikin daxanje nemo qarin girma dominshi....." Fad'awa tayi qirjinshi ta rungumeshi sannan tad'ago tadubeshi shima idonshi sun sauya...,tace acikin muryar kuka..... "Farincikinah...! Dole nadamu nasaba dakai sosai..,nakai bana iya 2mnt batare dakaiba...,yau gashi har week bazamuyi tareba dole nadamu...." Jawota yayi zuwa gadonshi ya zauna ya'axata a qafarshi...,yakai bakinshi cikin nata na 2mnt sannan ya zare bakin yace.... "Zaki rage kad'aici domin koh yaushe zamu kasance a waya...,kuma gurin umma zaki koma har sai nadawo...,kid'auki duk abunda zaki buqata dana wuce ynx ki rufe gidan har sai nadawo...,kuma nabaki dama duk inda zakije da izinina bale nasan bazaki wuce gida biyuba...,gidan mama da umma..." Duba agogonshi yayi shidda saura kwata...,kafin yamiqe har kiran abokin tafiyarsu yashigo...,bai d'agaba domin yasan zancen tafiyarne..... "Riqa hannunta yayi d'ayan hannun riqe da trolley nashi tana ja...,ido sunyi ja...., _rabuwa da masoyi babu dad'i koh da second ne bale week....😍_ _ALLAH BARMU DA MASOYANMU...,KADA KASA MUDINGA NISA DA JUNA...AMEEN_👏🏻 part d'in umma yashiga sukayi bankwana tayimashi addu'ar nasara...,yafito yazo part nasu ya amshi bag d'inshi yayi kissing iman sannan yafita...., iman hawayen missing kawai akeyi aka koma ciki kwasar kaya zuwa part d'in umma duk ranta babu dad'i....... Bayan iman tarufe part nasu ta d'auki itama tata jikkar tayi part d'in umma da ita...., Ummar naganin iman tayi murmushi domin tasan kuka tayi kenan saboda zai tafi...,hakan baisa tatsaya tambayartaba...,ganinta kawai tayi takai kaya d'ayan d'akin ta ajiye..., fitowarta kenan ummar tace tashirya akwai inda zasuje ynx..... Cema umma tayi toh..,duk ranta babu dad'i wlhy...,itafa missing d'in mujinta takeyi wlhy.... Wucewar iman d'in keda wuya ummar itama tatashi tashirya domin suje da wuri....... *Bee Been Masoya*💞 [2/1, 6:51 PM] Bee Been💞 Masoya: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH😭😭* 💧💧💧💧💞💧💧💧💧 ©® Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* 💋💋💋💋💋 ★TRUE LYF STORY★ ★★★★★★★★★ *_ASTAGFIRULLAHULLAZIE...,MAN LAZIE LA'ILAHA ILLAH ANTA...,ASTAGFIRUKA WA'ATUBA ILAIHIE...😭_* *~YA ALLAH KAGAFARTAMUNA XUNUBBANMU WAYANDA MUKA SANI DA WAYANDA MA BAMU SANIBA BAKI'DAYA ALBARKAR MA'AIKI {S.A.W}~*👏🏻👏🏻👏🏻 Page... ★3⃣3⃣★ ® Likitoci suka gurfana gurin ceto rayuwar farha...,Allah yabasu ikon shed'arta tadawo..., likitocin suma sunyi mamakin wannan abu domin ba hatsaribane...,wanna dukane na bala'i..., Kiran rasheeda sukayi suka shaidamata cewa yr uwarta na d'auke da ciwon zuciya mai tsanani wanda bai fi 5days da kamataba...,kuma idan ba'ayi hattaraba zata iya rasa rayuwarta ko wanne irin lkch...,sannan suka tambaya wanne irin ibtila'i ne tafad'a haka da har akayimata duka hakan...,?don wannan dukane kuma idan yn fashine sukayimatashi toh marasa imanine naqarshe...,yakamata kisanar da iyayenku idan suna gari....." Rasheeda hawaye nat zubo mata domin tasan Farha ita tasiyoma kanta musiba da bala'i...,"lallai Anwar shine yayimata wannan rashin Imanin kenan...,rayuwa kenan Farha kinganta....,gashi mahaifanki suma sunjuya maki baya nikad'ai naragemaki mai dubanki... Nima danaso dazan qyalekine..,amma babu aminci idan nayi maki hakan sbd inasonki...." Azuciya Rasheeda tace hakan...,doctor yadubeta yace..,kinata tunani kitashi kije kisanar da iyayenku domin sud'auki mataki da wuri...." "Ah ah doctor ynx nikad'ai naragema farha...,domin ita tayi laifinta ynx laifin yajuyo mata....,wannan dukan mijintane yayimatashi...,kuma naje iyayenta sunce bazasuzo ganintaba domin itama ta bijeremasu farko tace sai shi takeso tabar za'binsu dakuma son zuciya....don haka sunce bazasu zoba jiya natafi...." Likitan yajinjina kai yace..., "lallai rashin biyayya ga iyaye ba khairibane gashi da wuri taga sakamako...,amma kizama jigonta gurin nemamata yafiyarsu domin tana cikin wani hali wlhy wanda 'bacin ran nasune yata'bata..,kuma nima zanyi qoqarin ganin hakan na taimaketa gurin ganin iyayen nata...." Rasheeda tayi godiya sosai...,kuma taji dad'i...,kasancewar zataje gida amso abincin da akace idan tafalka aba...,sai ta'bar yr aikin gidansu domin koh jiya itace takwana gurinta..,itakuma takoma gida...,fitowarta gate d'in assibitin acikin motar ta..,ta hango ummar jabbar da Iman napape ta ajesu bakin gate d'in...., Hango iman rasheeda tayi...,tayi bala'in kyau ga haske datayi ga cika datayi...,kamar ba 'itaba....,parking tayi bakin gate d'in tafito...,iman yakira har sau biyu...,sannan tajuyo hangota da iman tayi da sauri tazo suka rungume juna.... " 'yaya rasheeda nan kike aikine...?" "Ah ah Iman inadai da patient ne anan..." Sannan umma tajuyo suka gaisa..., "Dama ynx nake tunanin kiranki domin bamusan gurinba..." "Eh umma nima da zaxanje gidane...,toh sai na hangoku shine natsaya...,muje koh duk da bata falkaba har ynx tun jiya barci takeyi domin takwana 5batayi barciba inji likitan..." "Subhanallh da sauqi dai koh...?" "Eh dasauqi kowanne lkch tana iya falkawa ynx sukace...." Suka kama hanya amma iman p batasan waye ba lfy ba...,tunaninta yn uwan rasheedan ne kawai.... Suna shiga Farha na falkawa...,yr aikinsu rasheeda na riqe da ita tana kuka tanacewa.... "Anwar Allah yasakaman...,kayi sanadiyar dana bar iyayenah...,nabar kowa da kowa dayazama shine gatanah...,amma gashi kaci amanata..,ashe kai fasiqine..,dazama dakai gara zama da mazinaci...." Rasheeda najiyo sautin kukan farha tarugo da gudu..,ta rufemata baki...,kuka kawai farha keyi ga ruwan da aka jonamata a hannu har jini yafara dawowa ciki...., Shigowarsu Iman kenan gabanta yafad'i domin qafafun farha kawai ta hango..,bataga koh fuskartaba....,amma tagane itace...,baki tasaki tasaki tana matsowa zuwa gadon...,rasheeda matsawa tayi gefe riqe da hannunta.....,Iman abun mamaki yabata domin farhace koh mai kama da ita...? Tsaye tayi tana lissafi domin ta bushe ta rame tayi baqi ga kunburin bugunan fuskata tako ina kwancin belt ne..... Farha naganinta ta ambaci sunanta... "Iman...! Rasheeda Iman ne koh gizo takeyiman...?" "Itace farha.." Farha 'balle allurar ruwan dake jikinta tayi taqwace hannunta ga rasheeda ta diro saman gado...,ta rungume iman.....,iya lkchn Iman komai takasayi domin bata yarda farha bace..,jin ta ambaci sunan nata sannan ta yarda...,rungumeta tayi itama ta rushe da kuka.... " 'yaya farha kece kika koma haka...?" "Eh Iman nice..,kinga yadda haqqinku yamaidani koh...,nabar haske nad'auki duhu...,gani yau ina cike da zullumi kaina yabuga yayo d'umi...😭 narasa kowa gatana adalilin so mara umfani gareni...,narasa hankalina lkchn da yakamata ace inada hankali...,naqi sauraron kowa naqi gane kowa..,gani cikin duhu haske yayayeman bansan ynx hakan a ina natsayaba....,iman naqi gane maganarki lkchn da yaci ace nagane kece jinina ta haqiqa...,nad'aukeki mara hankali nice mai hankali...,gashi ynx ina danasani tun kanda aje koh ina....,nagane cewa rayuwata batada amfani...,sbd naqi bin umurnin iyayenah bayan sunyi tarbiyyata da gata da so da k'auna...,sunsoni sona haqik'a amma sai nasakamasu da butulci...,nasan haqqinsune ke fita tunbanje koh inaba gashi *SONE DALILIN HAWAYENAH😭* Iman kiyafeman kiyafeman naqiki lkchn da yakamata ace nasoki amma nakasa hakan domin son zuciya da rud'anin shaid'an bayan nasan bakiman komaiba...,iman kiyafeni kuma kitaimakeni iyayenmu su yafeni domin nasan bazasu saurareniba koh kad'an.....,hasali kunyarsu nakeji ynx kitaimakaman koh nafita a dajin duhun danake ciki...." Rungume juna sukayi dukansu suna kuka...,iman tarasa gane kan 'yar uwar tata domin dagani bugune ga fuskarta...,wanda gabad'aya ta kunbura suntul...,d'agowa tayi tadubeta tace..... "Yaya me yafaru dake har fuskarki ta kunbura hakan...?" Fashewa farha tayi da kuka sannan tashafa fuskar tace cikin kuka... "Komai ma yafaru dani Iman....,ynx hakan bansan waye yakawoni nanba...,abu d'aya kad'ai zan iya tunawa a rayuwata danasanin auren anwar...." Ganin lbrn zaiyi nisa yasa rasheeda zuwa takama farha domin hannunta jini yakeyi sakamakon allurar data cire..,gashi ynx tafalka...qin sakin iman tayi tariqeta sosai itakuma kuka takeyi mai tsanani damuwa biyu guri guda ga mijinta baya kusa gashi halin da tasamu 'yar uwarta ciki...., Umma zuwa tayi ta kamo Iman ta rungumeta itakuma rasheeda riqe take da farha..... "Haba farha bakida lfy p..,amma sai qara sakamakanki damuwa kikeyi...,ynx nan kika falka...,kibari kisamu relief before kiyi abunda zakiyi...." "Rasheeda waye yakawoni assibitin nan...?" "Nice farha..,kikwanta kifuta duba hannunki jini yakeyi p....." "Rasheeda meyasa kika ceci rayuwata..,? Meyasa baki barniba namutu..,aftr kinemaman gafararsuba....,rasheeda rayuwata batada amfani mudun dangina da dangin jabbar basu yafemanba...,uwa uba shi..,domin shima nacutar dashi....,mutuwata tafiman komai ynx rayuwata....." Umma sakin Iman tayi taje gurinda su rasheeda suke...,ta dafa kafad'ar farha...,nan take farha tajuyo da sauri...,ganin ummar jabbar ce...,sai kuma tadone kanta qasa taqara gunjin kuka.... "Ah ah farha kidaina kuka kibari kisamu lfyrki sannan...,ynx hakan bansan bakida lfyba jiya nakeji shine mukazo dubaki....,kidaina kuka kinji duba hannunki duk jini...,rasheeda kikira likitan yaduba....." Tafiya rasheeda tayi ummar ta riqata...,hakan yasa farha sauka daga gadon tad'uqa tana hawaye...., "Umma kiyafeni...,umma na cutar daku naqi aminta da abunda kukaga shine alkhairi kaina...,Umma kiyafeni kitayani roqon baba da mama su yafeni...,kuma ki roqaman 'ya'ya jabbar ya yafeni....,don nasan bazasujiniba koh kad'an don nasa'ba masu farko....." "Tashi yawuce ni nayafemaki...,kuma suma zasu yafemaki tunda har kinyi nadama...,Allah yayafemu baki d'aya...." Shigowar likitan tasa umma gyarama farha kwanciya ta matsa gurin...,duba hannun nata yayyi yasaka bandeji kawai ya d'aure yace basai an qara wasuba sbd dama data falka zasu cire.... Farha tanemi da likitan yabata sallama domin ta warke don Allah...,yace tayi haquri har xuwa gobe..., fita zaiyyi yayima ummar magana akan yanason ganinta office nashi.... Ummar taje..,iman gefe take kawai tana kukanta ita kad'ai... Likitan yafara magana tareda cema umma.... "Kece mahaifiyar mara lfyr...?" "Eh likita nice..," "Toh don Allah kurabata aure da wanda take aure..,domin takai stage d'inda zuciyarta zata iya bugawa koh wanne lkch...,kuma zai iya kasheta wlhy domin dukan dayayimata shekaranji zai iya sakawa yayi kisa...,toh da ayi ba'aji dad'iba gara tunda wuri arabata dashi...." "Toh insha'allah za'a duba...,kuma gsky ni yr uwar mahaifiyarta ce..,kuma mahaifin yarinyar nada tsauri..,domin tasa'ba mashi farko...,amma xamuyi qoqarin ganin komai yagyaru domin gada tahalaka...." Likitan yaji dad'i...,sosai kuma yace ataimaka mashi da number mahaifinta zasuyi magana....,ummar tabashi tayi godiya tatafi.... Itama riqo Iman tayi suka fito...,domin farha tasamu barci...,suka bar yr aikinsu rasheeda nan gurinta.... Rasheeda tad'aukesu takaisu cen gidansu mamar itakuma tajuya domin zuwa gidansu kar'bo abinci....kuma ta d'auko momynta domin zataga farha d'in itama.... Shigarsu mama tatari Iman datake kuka sosai...da sauri tace.... "Lfy Iman meke faruwane kike kuka hakan...?" Zaunar da ita tayi sannan itama tazauna...,umma tazauna taredacewa..., "Halin dataga 'yr uwarta ne ciki yake damunta...,tun cen take kuka har ynx takasa dainawa...." Mama tariqota tace.... "Haba Iman menene abun damuwa da halin wanda baisan kanshiba....,ai duk abunda kikaga farha tasamu kanta ciki itace tasiyoshi da kud'd'inta...,kuma tasiyo gashinan ribar abun yazamo gareta....,kidaina kuka kidaina damuwa domin ke dabance...,banason kijawoma kanki ciwonkai gashi ance bakida koh lfy....,tunda kikaga muda muka haifeta munsamata ido ai kema kisakamata kawai mugani...." Iman kallon mahaifiyarta tayi ta rushe da kuka....,umma tace... "Ah ah binta farha nacikin mawuyacin halinda tana neman yafiyarku sosai....kuyafemata domin nadama takeciki ynx kuma idan kikaga farha ynx amatsayinki na uwa dole kitausayamata...." " 'ya'ya amina ni idan nayafi Farha...,ai abanza domin mahaifinta bazai qyaletaba..,domin yaji baqincikin bijeremasa datayi...,don haka nake ganin gara nima na haqura da ita duk dako soyayyar dake tsakaninmu ta haihuwa...." Iman qasa taduqa da qafafunta tana kuka tace..... "Mama kuyafema 'ya'ya farha domin tayi nadama..." Tana fad'in hakan mamar ta kalleta kenan sallamar baban suka jiyo...,hango iman yayi duqe tana kuka yashigo yazauna domin ya hango ummar jabbar kuma ga iman na kuka hakan yayi saurin tambayawa tun kafin sugaisa.... Iman juyowa tayi da sauri zuwa gaban mahaifin nata tana kuka...,itace amsar tashi daxata bashi... "Baba kayafema 'ya'ya farha don girman haihuwar dakayimana...,kayafemata tana cikin wani hali gada girman laifinta gareku yasa tafi hakan...." Sai ynx baban hankalinshi yakwanta domin ya'axa wani abunne yasamu jabbar a tafiyar dasukayi...,duk da sunyi waya dashi yace sun isa lfy amma yazaci hakan ne...,ashe zancen waccenne mara jiin maganar..., "Iman menene na nemamata gafara..? Cemaki tayyi tana cikin matsalane..? Ai fatima bataga komaiba da sauran nadama a rayuwarta indai son xuciyane...,tagangashi gashinan...,iman kidaina damar da kanki kinji kisaka biyayyar mijinki gaba da yimasa addu'ar samun nasarar abunda yaje samu...." "Ah ah alhji aliyu kayima girman Allah kayafema Farha kuskurenta...,tunda komai ya wuce...,wanda kakeyi dominshi yasamu sakayya da iman wadda ynx suke son junansu ba adadi...

Chapter 14 of 44