Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuka tana cewa... "Wayyo Allah nah! Nashiga ukku ni farha, k'anwata cikin gata nikuma koh oho rayuwata, gani kulle ina idda mara amfani domin babuta kaina tunda komai bai had'ani da Anwar ba, ga Iman cikin gatan samun miji nagari wanda ni da kaina naqishi,ynx ga iman tasamu ana tarairayarta cikin jin dad'i da soyayya,gashi ynx sai cigaba sukeyi tarin arziqi shigosu kawai yakeyi,nikuma danida almajira duka d'aya, naga takaina ni farha, nabani danasanin so tsaye saman kaina, ban masan mafitataba, qanwata tazama yaya tah ynx domin komai tafini, tir da kalar son zuciya irin nawa, son zuciya mara amfani,za'ben sharri kabar alkhairi,rashin jin maganar iyaye nagane ba abun alkhairi bane, _YA ALLAH KASHIRYA MAI HALI IRIN NAWA YAGANE CEWA BAYADA KYAU TUN KAFIN YAFARU DASHI_.." Kuka taci mai yawa,wanda intatuno kallon da iman da jabbar kema junansu har wani tsinkewa zuciyarta keyi ta fad'i domin tasan bazata samu irin mai kulawa da ita kamar yadda jabbar yake kula da iman ba,kukanta naqara tsananta babu adadi. Tunda suka tafi farha takasa komai,har tym d'in d'aura sanwa amma takasa komai,rarrafawa tayi hakanan tafad'a kitchen d'in amma su iman take kallo a idanunta....... _Toh farha sai haquri,kece kika sawo ma kanki dana sani duk da kin tuba kin nemi gafara,Amma koma me jabbar yayimaki ke kika saye,domin kin cutar dashi da so farko,ynx kuma koh kallonki baya sonyi domin yana ganin yasamu wadda tafiki._ *Bee Been masoya*๐Ÿ’ž [2/14, 10:03 PM] โ€ช+234 803 932 4068โ€ฌ: ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ* ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง ยฉยฎ Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ โ˜…TRUE LYF STORYโ˜… โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… *_AYSHARTFAREEDA๐Ÿ’•,KARAMCINKI A๐Ÿ’งSO NE DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ’งBA KA'DAN BANE,HAKAN YASA IMAN DA JABBAR SUKACE AGAISHEKI,KUMA SUKA NEMI A SADAUKAR MAKI DA PAGE 'DIN YAU, DON HAKA PAGE 'DIN YAU NAKINE DUKA๐Ÿ˜˜_* Page... โ˜…3โƒฃ9โƒฃโ˜… ยฎ Shigarsu motar, Iman ta kalli jabbar tare da harararshi da gefen ido alamar da zance qasa,saidai zancen na nishad'i ne na masoya, dubanta yayi yace.... "Daga fad'in gsky sai ganin laifi kuma?" "Eh mana,shine har da nunama umma kai bakada haquri kenan, harda cemata wai bazaka iya zuwa batare dani ba" "Gsky nafad'a,gudun gada na cutar da kaina kinji,kuma koh gaban baba zan qara fad'in hakan,domin 2days bazan iya cikasu dai2 ba wlhy in banitare dake Iman.." "Hmmm,sbd bazaka jure ba koh?" "Eh mana" Mota yaja suka kama hanya sai bakin get d'insu mama,fitowa sukayi dukan su,amma iman taqi jiransa da sauri da d'an gudu kad'an tafad'a fallown da sallama, shigarta ciki taga mama da baban zaune suna fira,murmushi tayi tareda da sauri taqarasa gurin mamar tazauna tareda gayar dasu baki d'aya cikin jin dad'in d'a da mahaifa. Suna cikin gaisawa kenan, jabbar shima yashigo tareda sallamar shi,gefen baba yazauna tareda gaidasu duka,suma suka amsa cikin farin ciki,baba yafara magana da cewa...... "Abdul-jabbar ya gidan? Da kuma aikin?" "Alhmdllh baba, kuma dama nazo ne domin shaida maka,sakamakon jarabawar mu ya fito,kuma anyi nasara,ynx hakan kaga text d'inda aka turoman na tayani murna tareda samun grade mai girma,sun kaini lavel 12 under road engineering acen abujar promotion d'in yafad'a,ynx next 2 week zanje da takar duna sukace duka.." "Masha'allah Abdul-jabbar,Alhmdllh Alhmdllh, ina tayaka murna domin mataki naqarshe suka kaika,ikon Allah wannan abun sai Allah, domin Allah kad'ai za'a godemawa abdul,mutane dayawa sunayin exam d'in don samun haka amma basu samu ba amma gashi kayi d'aya nan take kasamu,toh mungodema Allah domin shine abun godiya Anan don shine yabaka,Toh Allah yatayaka riqo da arziqi mai amfani,kuma ako ina mutun yasamu kanshi ya kwatanta adalci domin shine dace na gsky.." "Ameen baba, insha'allah zanyi riqo da abunda ka horeni dashi,kuma zan kiyaye haqqoqin sa ako ina, end dis week d'innan zan wuce,amma bada iman zanjeba wannan tafiyar sbd bansan kan wurin da zasu baniba,amma idan naje da kwana biyu naga gurin zan dawo na d'auketa.." "Hakan nada kyau jabbar,saidai da bari kayi har sai ka d'an dad'e gurin kaga yadda aikin yake sannan kazo kaje da ita,sbd kaga farko ne, ba daga kwana biyu ba kuma kaje da itaba, inaga bazaka fahimci komai ba.." "Insha'allah za'a kwatanta yin hakan baba.." Shima baba yaji dad'i sosai,sai dai jabbar fa yafad'i haka kawai,amma bazai juri yin nesa da iman ba. Mama itama tayima jabbar addu'a, sannan suka miqe da iman don basu guri sukayi cikin d'akin mamar, mama tadubi iman cikin kulawa tareda alamar tambaya ga dubin tace... "Iman amma cikine dake koh? Naga kinyi fari sosai gakuma qiba dakikayi anya baki da juna biyu kuwa?" Iman ta done kanta, domin ita tasan bata da komai,kuma bazata iya cema umma basu dad'e ma da fara abun da ke kawo cikin ba,domin akwai kunya tashaida mata sau biyu abun yafaru,hakan saya tayi saurin kare kanta da cewa... "Mama banida komai,domin ban dad'e da qarasa period nawa ba " "Ok toh lallai kwan ciyar hankaline kika samu Iman,domin kinyi kyau sosai,Allah yakawo nagari toh " A zuciya iman ta amsa da ameen,domin kunya takeji sosai,hakan yasa takawar da zancen dacewa... "Mama yaya farha da umma nagaisheki sosai.." "Ina amsawa, sai dai baku samu wata matsalaba kuwa game da zaman ta tare da kuba koh? Domin nasan farha batada mutunci,naso babanku yabarta tazauna anan tunda nasamu lbrn rabuwar aure amma yace saidai ta tafi zamfara ta zauna,shine ummar jabbar tace abarta nan gurinta.." "Eh umma, wlhy bamuda wata mtsala tsakaninmu, domin ynx yaya farha ta changr sosai,nadamar abunda tayi ya shigi jikinta sosai,koh yaushe cikin neman yafiyar kowa takeyi, kuma ni naji dad'in abunda umma tayi mama,domin hakan zaisa taqara gane abunda tayi bata kyautaba,kuma nima zanfi samun kwanciyar hankali domin idan tana cen nasan damuwa zatafi yimana yawa nida ita na rashin ganin juna,domin ynx tana sona sosai,kamar yadda take sona a lkch baya,don haka Allah yasakama umma da alkhairi kawai.." "Ameen Iman,kema Allah yayi maki albarka,yaqaramaku d'anqon soyayya dakeda mijinki,halinki mai kyau ne iman,Allah yabaki 'ya'ya masu kalar halayenki na qwarai, yaqarama mujinki arziqin riqeki cikin salama.." "Ameen mama, Allah yayi muna albarka baki d'aya har yaya farha, domin mama wlhy ta sauya halinta ynx halinta abun koyine ma mama, don Allah kuqara sakata addu'a,Allah ya bata dace naqwarai.." "Toh ameen iman,kitashi kuje koh,naga marece yayi.." Miqewa mama tayi, tada'aukoma iman wasu kaya a laida, dagani kasan kayan gyara d'iyar tane ciki, miqama iman tayi tareda cemata.. "Duk abunda ke ciki akwai bayaninshi a paper d'in ciki,sannan gada kiyi wasa dasu suna da kyau, ance in kanada kyau ka qara da wanka, don haka kudd'i nasaka masu yawa nasaya maki domin zaku amfana dasu sosai,gabad'aya nasha ne at ciki.." Godiya kawai iman tayi,tareda miqewa tasaka kayan a hand bag nata suka fito tare. Fitowarsu fallow kenan, sukaga da baban kad'aine zaune, yana duba wasu takardu,sallam sukayi suka shiga,mama ta zauna iman tad'uqa alamar zama, baban yace... "Abdul na waje,ke yake jira kuwuce basai kin zaunaba,kije Allah yayi maku albarka.." "Ameen baba,sai mun wuce.." Fitowarta taga yana waya, da ji kasan abokinshi ne domin dariyar da yakeyi,bud'e mata qofa yayi tashiga tazauna, sannan ya kashe wayar suka wuce. Isarsu gida, koh part d'in umma basu tsaya shigaba suka wuce part nasu, kitcheen iman kawai tafad'a kafin a kira magrib tasa mamasu abunda zasu ci. Jabbar bai hanataba, domin yasan wajibine yin hakan,d'akinshi yashiga domin qarasa duba takar dunshi. shigarshi keda wuya text yashigo mashi, kamar gada yaduba,kuma sai yaga dacewar dubawa,text ne na ana nemanshi gobe tareda takardunshi, dubawar da yayi saida yazauna domin gaban shi yafad'i,bayason tafiya yabar iman wlhy koh da kuwa 2days ne,shida yake tsammanin sai end week gashi sunce gobe,toh ya zaiyi? Hakan dai yakarasa dubawa, ya had'asu guri d'aya,sannan yashiga yin alwallah, fitowa yayi don zuwa masallaci,anan yaduba kitchen d'in baiga iman ba alamar itama alwallar tajeyi kenan. Wucewa yayi batareda yadawo dubataba,itama sallar ce tayi,sannan tadawo ta had'a abincin data qarasa a foodflax takai dining sannan tashiga wanka. Fitowar kenan tana shafa mai shima yashigo d'akin,qarasowa yayi gurinda take tsaye tana shafa mai domin a tsaye take ba zauneba, rungumota yayi tareda aza kanshi wuyanta yana shaqar qamshi wanda baita'ba jinsaba jikinta,hannu yasaka ya rungumota baki d'aya tadawo jikinshi, hakan yasa yazauna dressing chair d'in tare da ita yana kallonsu ta madubin,yace.... "Haskenah,wannan kuma wanne irin qamshine hakan? Domin gabad'aya kin rud'ani fa, zan iya cin wani abun ynx batareda na ganki ba ?" "Hmm wanne qamshine hakan kake ji kuma bayan kasanshi atare dani?" "Wannan wanine nadaban yau kika samoman,don haka koh nagane sirrin tukuna sannan na amsa maki sauran zancen ?" "Ah ah don Allah, kabar ni nasaka kayana muci abinci yunwa nakeji sosai " Murmushi yayi sannan yayi baya yafad'a saman gadon da ita, jin kawai iman tayi an 'balle mata towel ana chakulata tako ina, domin turaren jikinta humrah ce ba notice tare da ita,dole hakan tafaru, matsarta yakeyi tako ina wanda saida iman tafara yimasa kuka sannan yasamu hankalin tuna barinta domin suci abinci. Daurewa kawai yayi, amma wlhy yarasa meyasa daga shigowarshi feeling nashi ya lunku, sakinta yayi sanna tasaka kaya batareda kwalliyar komaiba, amma tako ina iman alhmdllh. Abinci sukaci tareda yin sallahr isha'i cikin jin dad'i da soyayyar mai gamsar da junansu,sannan suka fara fira fallow. Jabbar yarasa ta hanyar da zai sanar da iman cewa gobe fa abuja xaije domin sun kirashi,hakan yasa bai nemi su kwanta da wuriba, hammar dayaga tanayine shi yasashi kashe kayan kallon yad'auketa tareda kashe wutar fallown duka, Iman sai mutsilniya takeyi ya ajeta fa, amma yaqiya saida yakaita d'akinshi. Shigarsu taga traveling bag d'inshi aje gefe,batayi maganaba sbd tasan ba ynx bane tafiyar shiyassa bata damu da tatambayaba, kayanta tacire tasaka na barci tafad'a toilet d'inshi tayo brush da alwallar barci wadda sukeyi duk zasu kwanta. Fitowa tayi,shima taga yashirya kwanciya domin yasaka nashi kayan, shima alwallar yashiga yayo yafito. Zaunawa yayi gefen gadon inda iman take zaune tareda riqo qugunta sannan yace... "My iman gobe fa abuja zan wuce, domin sun turon saqo d'azu bayan mundawo gidansu mama cewa, jibi suke son ganina around 8, toh kinga dole gobe naje domin tafiyar motace xanyi.." Wata zabura iman tayi,domin ita dai wlhy batason su rabu koh na second d'ayane,iya ynx tafison taganta gata gashi domin ita kad'ai tasan tashin hankalin da take shiga idan jabbar baya kusa da ita. Hakan yasa tafara hawaye masu zafi, nan take jabbar yarikice domin hakan yasa yakasa fad'amata tun d'azun, rungumota yayi tareda jawo pillow ya aza kanta gareshi, shima yabi bayanta ya kwanto jikinta yana kallon fuskarta da yadda hawaye kefita ciki, hannunshi yasaka ya tallabo kanta sannan yasaka bakinshi a lashe hawayen baki d'aya, sannan yad'an tsaya yana duba fuskar kad'an,sannan yafara magana cikin *(sexy voice)* yace.. "Kuka kuma? Iman menene abun kuka a tafiyar dazanyi 2 days nadawo,kisani wlhy nafiki rashin son naje nabarki,kinxama wani yanki najikina iman, second d'aya bana iyawa batare dakeba,wlhy da zan san inda zan ajeki babu takura iman xanje dake koh da kuwa umma da baba basu saniba, amma rashin hakan zaisa nabarki gida harnadawo kuma nasan baxan wuce 2 days ba zan dawo sai muje tare, za'a tabbatar dani ne, tareda ganin yanayin aikin aftr sai nazo naje dake.." Iman taji sanyi, daya kira 2 days amma duk da haka tasan zatayi missing nashi ita kad'ai tasan waye jabbar azuciyarta, hajan yasa tasaka hannunta biyu ta rungumoshi daga kwance har cikinshi na ta'bo nata cikin, ta kalleshi tayi murmushi tace... "Bakomai yayanah, Allah yatsare hanya, yakuma dawo man dakai lfy,yabaka nasarar abunda aka samu yazamo mai sauqi,sannan banda kallon matan abuja wlhy.." Wani irin farin ciki yaji, "kai Iman daban kike koh acikin taurari" yafad'a acikin zuciyarshi, murmushi yayi sannan ya had'e bakinshi da nata na tsawo 5mnt, sannan yafitar idonshi sun sauya, domin xaka ita gani sbd hasken fitilar d'akin, yadubeta murya sarqe yace... "Toh zan samu abu tsarabane?" Domin ni narasa tukuycin addu'ar dakikayi mana,amma naji koh da saqo ne a matan Abujar na kai masu..? "Sosai kuwa, tsaraba wajibice a hannun iman, kuma babban saqo zuwaga matan abuja cewa, iman daban take zuciyar jabbar, don haka su matsa baya lizzamin na iman ne ita kad'ai babu wata, don haka gani nabaka kaina fansa ka amshi tsarabarka, wadda zatayimaka guxurin tsawon kwana biyu.." Farin ciki ai bai barshi tsayawa bata amsaba domin kusa yake yaqagu yajishi wani fanni kuma. Hannushi yasaka tabaya kawai yakashe glub d'in d'akin, nan take yaraba iman da kayan jikinta, baisha wuyaba domin santsi garesu,itama ta tayashi cire nashi. Anan suka durmiyar da junansu gogin rahama, jabbar bakinshi yakai qirjin iman wanda har yarasa taya zai kama d'ayan, kamar wani sabon haihuwa, hakan yabama iman dariya sai ta sauwaqa mashi ta hanyar saka hannunta tabashi domin tasan a rud'e yake. Lkchn da hakan yafaru itama sai zancen ya sauya gareta domin imaninta yatafi ga wata kalar wasar da yakeyi da ita, banda take macce maivjuriya wlhy data fara sabbatu,don yaune rana tafarko da ta qarasa gane aure dad'i. Hakan yasa jabbar juyawa zuwa wata qasar don sauke babban nauyinshi, ba musu iman ta taimaka mashi yasamu gamsuwa,itama yataimaka mata tasauke tata sha'awar dasuka d'ibo,koh wannesu daga cikin saida yavar tarihi gurin fitar nauyin,don haka yau babu gori saidai soyayya. Ahaka suka qare,kowa sai maida numfashinshi yakeyi,anan ne jabbar yayi qoqarin jawo iman dake barin jikinshi, yake cemata... "Sannu haskenah,ALLAH yayi maki albarka, sannan A text d'in samun aikina, sunbani mota da kuma gida, wanda shine dalilin xuwana gobe nagani da gsk ne, idan har da gsk ne, iman na mallaka maki wannan motar tawa tsohuwar tunda batayi komaiba" Jin xancen iman tayi asama hakan yasa tayi saurin rungumeshi tana godiya, ahaka suka kwana cikin farin ciki bayan sunyi wanka. Dasafe jabbar yashirya komai natafiya domin fitar safe wajibice gareshi, hakan duk iman tabi tawani maqale mashi sai shagwaba taketa xubawa, haquri yaketa bata, hakan yaga bazai yuyuba yace tad'auko kayanta tarufe gidan takoma gidan umma har yadawo. Hakan akayi kuwa, yashiga yayoma umma bankwana, sannan iman taqara biyoshi fallow d'in dayake babu kowa, rungumeta yayi yana yimata kiss tareda saka hannunshi rigarta daga qasa, hakan dasuke shiyayi dai2 da fitowar farha daga d'akinta xuwa kitchen. Dum!Dum!! gaban farha yafad'i,har cup d'in hannunta nashirin fad'u, dasauri takama cup d'in gada ta tona mata asiri, abunda tagani keta dawo mata domin duk basu hankalinsu gasu tsaye baki qofa kuma, "toh koh me sukeji a hakan?" Tafad'a a xuciyarta. Dagudu takoma d'akin tafad'a toilet tarufe tanata darzar kukanta ciki. Qoqarin takeyi ta manta da abunda tagani takeyi amma takasa mantawa sai hannun jabbar take gani cikin rigar iman yana wani shafe shafe,itakuma tana wani matseshi,kukan qara yawa yayi tace... "Nabani! Koh me yakaini fita har naga wannan bala'i?" Wucewarshi kenan iman tashigo d'akin,don duba yr uwar tata, amma shiru babu ta d'akin, hakan yasa tafara kiran sunanta. Farha naji tayi shiru, domin kuka takeyi,kuma idan ta tambayeta tace mata meyene? Oho, hakan yasa tayi shiru. Iman tagaji da nemanta takwanta gadon tana tunani har kwana yad'auketa sbd rankon kwana, jin shiru farhacta bud'e toilet d'in tafito, ganin iman na barci ta kalleta ta kalli qirjinta cike tace.... "Dole qanwata qirjinki yafi hakan, domin nagani suna samun kulawa sosai,kinyi dace koh nace kinyi gamda katar, gaki asa'a,namu lbrn ai babu dad'in fad'i bale sauraro" Tasamu gefe ta zauna kawai tana tunani baqin ganin da idonta nayyimata yau. โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… Kwana d'aya da zuwan jabbar, iman tatashi da rashin lfy mai tsanani baci basha sai amai wanda yakai tun tanayi da wasa har abun yafara wuce guri, tun ciwon daga ita sai farha ke saninshi har yakai farhar tasanar da ummar aje assibiti domin jiya basuyi barciba sbd aman datakeyi,saidai umma tace Allah yaraba lfy kawai domin tasan cikine, saidai kuma abun ya faskara domin iman tafara galabaita sbd amai. Abu kamar wasa, farha nashigowa d'akin bayan tafito kitchen samama iman abu mai zafi taci, domin umma tace assibiti zasuje ynx, iskota tayi kamar barci kamar rashin motsi, ta'bata tayi tareda kiran sunanta amma shiru, ta'bata tayi kuma shiru, qara farha tasaki tareda kiran sunan umma. Lokacin ita kuma tana shirya wane, da sauri tafito domin ganin waye ne, kuma lfy? Qarasawa tayi d'akin taga iman kwance alamar ba motsi,dasauri taqarasa ta riqota, kiran sunanta tayi amma shiru, a rud'e tace.... "Farha d'ebo man ruwan fridge da sauri" Farha na kuka takawo, umma zuba ma iman tayi a fuska da xuciya, saiga shaid'a tadawo da sauri, farha riqeta tayi tareda sakamata hijab su tafi, anan ma takoma suma. Rud'uwa kam ynx sun rud'e sosai,hakan yasa farha d'aukar waya don kiran mahaifin nasu tashaidamashi. Dasauri yad'auko mota aka d'auki iman sai assibiti..... _Toh iman Allah kawo sauqi, gada jabbar yadiro ta sama, mubani ๐Ÿคฃ_ *_nima saida nayi typing komai yagogeโ˜น saida nayi sabon typing, abun zar ciwo a xuciya, amma dayake masoya nayi alqawali dole naciki_* *Bee Been masoya*๐Ÿ’ž [2/14, 10:04 PM] โ€ช+234 803 932 4068โ€ฌ: ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง *SO NE......* *DALILIN HAWAYENAH๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ* ๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ž๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง๐Ÿ’ง ยฉยฎ Khadija bee bee Khadijabeebee@gmail.com My wattpad user name.... *khadijabeebee......* My Facebook page.... *beebeenmasoya* *I LUV YOU ALL MY FANS* ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ โ˜…TRUE LYF STORYโ˜… โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…โ˜… *_ALLAHUMMA LAH TADA'ALANA ZAMBAN ILLAH GAFARTA...,WALAH HAMMAN ILLAH FARAJTA...,WALAH DAINAN ILLAH K'ADAITA....,WALAH HAJJATAN MIN HAWA'IJ DUNYA WAL AKHIRATU ILLAH AQDAITAHA YA ARRAHAMAR RAHEEMIN._* *_AMEEN YA ALLAH_*๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป Page... โ˜…4โƒฃ0โƒฃโ˜… ยฎ Isar su assibiti, aka kar'bi iman emergency,domin suma kawai takeyi,data falko zatace "ruwa" da anbata kuma sai amai tsananin wahalar aman sai yajawo sumar. Abun yana bawa iyayen tsoro, domin Iman wahala takeyi sosai,gashi jiya kad'ai da yau duk ta rame nan take. Tunda Jabbar yatafi sau d'aya yasamu yin magana da Iman, sbd isarshi garin abinci kawai yasamu yaci a gidan abdul-hafiz barcin gajiya yakamashi, domin shi yayo driving dakanshi. Wayewar garin ne,kafin yafita cen office d'in da ake nemanshi yaji gabad'aya bazai iya fitaba sai yaji Iman yata kwana, Kiran wayar yakeyi amma banza ba'ayi picking ba,sai yashare,domin a tunaninshi iman barci takeyi kawai. Aftr sun qarasa tantance abdu-jabbar tareda mallaka mashi gida da dan qareriyar mota sabuwa _civic 301_ tareda shaida mashi aiki kawai zai fara, domin inda suka bashi shine babba gurin,sun dad'e suna neman mai kalar karatun amma basu samuba sai gashi Allah yakawoshi,sukayi masa fatar alkhairi da horo da riqe amana sai sunjishi. Bayan yadawo masaukinshi ne shida abdul-hafiz,wanda ynx shine abokinshi domin gurin aikin su d'aya, saidai kowa da inda yake aiki. matar Abdul- hafiez akwai kirki, domin tunda ya iso gidan abinci kala kala take aiko mashi dashi bisa umurnin mijinta, hakan yasa jabbar yadaukesu duka masu mutunci, idan yazo da iman wayanda tasani agarin. Ayinin ranar hakan, haka jabbar yaqare tunaninshi a neman wayar Iman ba'a d'agaba, sai tunaninshi yabashi toh yakira umma yaji koh lfy? Duk da ai dasafe yasamu umma d'in take cemashi lfy qlau kowa yake, amma bari ya nemeta yaji. Itama wayar ta umma ringing takeyi ba'a d'agaba,duka haushi yakamashi,gashi yanason yaji muryarta sosai amma kuma kowa shiru, hakan tunaninshi yajuya akan ya juya kiran gurin baba koh yanada lbrn gidan? Hakan kuwa akayi,domin kira d'aya ba'a d'auka ba, gana biyu ne baban yad'auka tareda sallama yakira sunanshi.... "Abdul-jabbar ya kake? yakuma aikin? Hope ansamu dace koh?" "Eh baba alhmdllh, duba da yanayin gurin ba wata mtsl shiyassa zanbar dawo wa sai jibi, sbd akwai abunda zan qarasa kammalawa domin sun bani gurin zama da abun hawa" "Alhmdullh, hakan yayi kyau kuma munji dad'i, amma ai kabari ka kammala komai sannan kadawo " "Toh baba insha'allah zan bari, amma koh lfy su umma suke? Nakira wayar koh wannensu shiru ba' a d'agaba?" "Da sauqi za'ace, domin iman ne batajin dad'i amma da sauqi sosai muna assibiti, basai ka tayar da hankalinka ba domin akwai sauqi sosai " Gabanshi yafad'i,Dum! Dum!! wanda saida ya miqe tsaye saboda razana, shi dama yasan ba lfy ba, tunda yaga iman kwana da yini bata nemeshiba yasan akwai mtsl, dasauri yace..... "Subhanallh! Baba don Allah da sauqi jikin? kuma meke damuwarta ?" "Da sauqi abdul,kuma zazza'bine" "Baba inason naji muryarta, don Allah akai mata muyi magana " "Toh ynx tana barci, amma idan tafalka zan kiraka da kaina kuyi magana,kakwantar da hankalinka kayi abunda kaje yi, da sauqi jikin" Amsawa kawai jabbar yayi,amma wlhy jikinshi yabashi cewa iman batada lfy ne sosai,hakan yasa gabad'aya yakasa sukuni. Daren ranar yadai kwanta kawai, yadda yaga daren haka yaga safiyar, yajira baba yakirashi yabata amma shiru ba bayani, hakan ya quduri kamo hanyar abuja zuwa kaduna,yabar ma abdul-jabbar sauran abunda za'a qarasa gyarawa a gidan nashi,yakamo hanya zuwa gida. Isowarshi bai tsaya koh inaba sai assibitin dayasan dama nan zai iya samunsu. Adai2 lkchn likitoci sunyi taimakon dayakamata suyima iman tareda gwaje gwajensu da test kala kala wanda yakamata,domin tanajin jiki sosai tun shekaran jiya abu d'aya akeyi sai yau akasamu komai yadai2 ta,ansamu aman ya tsaya saรฑadiyar ruwan dasuka sanya mata. Farha ita ke kwana gurinta,duk wata d'awainiyya da ita ita keyinta, hakan yasa iyayen suka barta ta dinga kwana da zama gurin yr uwar tata,hakan yasa ynx suna gaisawa da iyayenta cikin jin dad'i domin sun gane farha tayi hankali, ga nadama mai natsuwa tazo mata, surutu idan bai shafetaba bata saka kanta ciki. Jabbar yad'an wahala kafin yagane room d'inda aka kwantar da iman, domin numbers ga d'akunan kuma baisan koh wanneba,sbd bai tambayaba don bason yakeyi a gane cewa ya isoba, burinshi yaga halinda iman take ciki,domin baisan wanne ciwone tare da itaba. Fitowar farha kenan daga shop d'in assibitin, taje sayen recharge card sbd zata kira rashida tashaida mata rashin lfyr iman. Sanye take da dogon hijab tajawo fuskar hijab d'in daga gaba,cikin natsuwa take tafiyar ta, jabbar hango farha yayi daga nesa tana qarasowa, kuma tabbas yasan itace duk da rufe rabin fuskarta datayi,amma wlhy bazai iya tambayartaba saidai yabita daga baya, hakan tawuce shima yabiyota daga baya. Shigarta d'akin,taga Iman nason tashi amma takasa, dasauri tariqata tareda cewa... "Menene kikeso iman?" Tanuna mata Ruwa takeso da yatsanta, farha tace... "Toh kijira xan kira doctor domin yace idan kin falka gada abaki komai sai yazo" Kallont kawai tayi,sannan farha tagyara mata zama tace tana xuwa. Dai2 fitarta sukaci karo da jabbar, wanda saida jikinta yabugi jikinshi,d'agowa tayi da sauri domin ganin waye yayimata hakan? Dubanshi tayi da sauri dashirin mayar da magana,amma kuma sai takasa ganin wanda yayimata hakan, gefe tajawo tareda matsamashi hanya yawuce, sai cewa yayi.... "Mtswww!Mara hankali,duk yadda akayimashi magani watarana sai haukar ta motsa" Yawuce ciki da sauri, farha runtse idonta tayi, domin iya muzanta ya muzantata, kuma da qeta yayimata wannan dukan domin taji banka'dar da yayimata sosai, amma kawai ta share tatafi aiwatar da abunda tayi niyyar yi, takira likitan sannan takoma reception tazauna tasaka kati takira rasheeda domin bazata shiga d'akinba sai yafito ciki. Shigar jabbar da sauri yaqarasa gurin iman, duk tayi baqi ga rama datayi, nantake hankalinshi yatashi, zaunawa yayi saman gadon daga gefe ya rungumota yace.... "Haskenah, haka kika koma amma aka rufeman ba a fad'aman ba? Subhanallh! Iman jiya kawai ne at bamu tare fa, menene kedamar manke haka Iman?" Kallonshi kawai tayi talumshe idonta, domin itama batasan mtslrtaba, kawai ganinta kawai tayi a nan kwance, hawaye nat fara cika idonta wanda data rufe idon zai xubo amma kallon jabbar ya hana turufesu,hannunshi yasa ya runtse idon tareda saka hannunta d'ayan hannun nashi ya tare hawayen. "Har abada bazan bar d'ayan hawayenki ya zuba ba idan muna tare, fad'aman meke damunki?" "Nima bansaniba, amma nasan ina amai tun shekaranjiya daga nan banqara sanin inda nakeba,ni kabani ruwa nasha maqoshina zai cire " Dasauri yad'auko robar ruwan yabud'e yabata, tasha ruwan sosai domin takusa shanye roba sannan yajayemata ya ajiye gefe,taji dad'in ruwan sosai,saidai ina bazasu tsayaba,domin d'agowar da jabbar zaiyi gabad'aya ruwan sun dawo mashi jikinshi, bai damuba sbd ganin yadda take kakarin aman kuma babu komai cikinta, tsoro ya kamashi sosai sunan iman yake kira,hawayen wahala ke zuba idon iman riqe kawai yake da ita yarasa me zai yimata, kwantar da ita yayi kawai yana dubanta. Suna hakan kawai sai yaji turo qofar d'akin, d'aga idonshi yayi sai yaga doctor ne, hakan yasashi miqewa gefe amma bai saki hannuntaba, suka gaisa da doctor d'in sannan doctor d'in yace... "Amma abokina wani abun akabata taci koh?" "Ah ah doctor ruwa ne kawai nabata ynx, domin tace tana buqatarsu, wai don Allah meke damunta ne hakan? Doctor kasanar dani nasamu natsuwa " "Da alama kaine Ogan nata koh? Domin naga damuwar tayi yawa sosai, ga kuma kasha wankan amai a jiki " "Eh likita nine, don Allah kasanar dani meke damun iman? Domin shine farkon abunda nakeso naji " "Toh Alhmdullh ba mtslr komai tare da ita sai alkhairi, dama inajiran mahaifinta yazo nabashi result naku amma tunda gaka

Chapter 19 of 44