Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sauƙar yayi kooking ta ba da sauti tuni suka maƙale juna suna kakkarwa kaman kadangarun da suka faɗa wuta sai salati suke. Ya ce cikin dakakkiyar murya "Menene wannan a hannu na?" Mudi da yake jin yana shiru saleem zai iya fashe kanshi don an sha ce musu idan allurar sojojin ta tashi bata da hankali ana ɓata wa sojan rai sai kisa yayi carab ya ce murya na rawa "Abin kashe mutane" "sunanta na tambaya!!" Ya faɗa a hasale da kuma gaske a mugun hasalen yake, Ishaq yayi saurin cewa "Sunanta bindiga wallahi bindiga sunanta" "Kun dai san ni soja ne, kuma ina da lasisin harbata ko?" Sai kai suke gyaɗawa kaman kadangaru "Buɗe baki za kuyi ku amsa ni malamai" Tuni suka cika ɗakin da "Eh, tabbas! Haƙiƙa hakane!" "To ku buɗe kunnuwanku da kyau ku ji ni, wannan yarinya da Hajiya ta kawo ta nan ko kallon da ya wuce na seconds kuka yi mata bare magana ta fatar baki ba tare da kwakwaran dalili baaaa..." Ya miƙe tsaye ya isa inda suke ya ɗodɗora bindigar kan kowannen su yace da ƙarfi "Toh tabbas sai ya kwana a lahira!!! Ina Fatan kuna ji na da kyau??" Suna zare numfarfashin tsoro da kaɗuwa suke amsawa a tare "Mun gane wallahi mun gane, ba za mu kuskure ba ranka ya dade yallabai" Ya ɗan matsa baya. "Kar ku ga kaman ban cika zama ba, gidannan ko ta wani ɓangare ina da abin ɗaukar video a ɓoye waninku ya gwada saɓa doka ta ya gani..." Yana kai nan ya juya ya fice bayan ya sake nunnuna musu bindigar a Goshi ai da gudu iliya da mudi suka fara rige-rigen isa bayi sai zawo...! Ko magana cikinsu babu wanda ya sake yi a haka baccin dole ya kwashe su dukunkukune da juna. Ya ɗan jima tsaye yana kallon kofan ɗakin nata bayan fitanshi kan ya wuce, yana tsaye a balcony ɗin shi na sama ya ga isar mommy da ita wurin abin ya matuƙar damun shi, ta ya mommy za ta haɗa mace da maza har uku waenda ba muharammanta ba? Tsoro ne ya mamaye zuciyarshi ba zama yake ba yana matukar tsoron wani abu ya sameta ba zai iya yafewa kanshi ba, wayanshi ya fitar ya kira Rayyan. Ringing na ƙarshe ya ɗaga da sallama "Ya aka yi ne man?" "I need your advice, ni ne na kawo lu'u lu'u mai tsananin daraja da ƙima sai na rasa inda zan killace hakan ya sa dole na ajiye a inda ba ni da tabbacin za ta samu tsaro da kular da ta dace da darajar ta, ban gama nazari ba sai na kyalla ido na hango wasu kananun ɓarayi da basu kai ko da shakar numfashi ɗaya ba suna zagaye wannan lu'u lu'u da kallon da ban gamsu ba, idan ba zan iya tafiya da wannan lu'u lu'u ba kuma dole zan tafi wani mataki kake ga ya kamata in ɗauka?" Ryan ya ɗan yi shiru na seconds kan ya ce cikin dakakkiyar voice ɗin shi "Dukkan yanki ba'a rasa ɓarayi kuma ko wani ɓarawo yana da uban gida, idan har kai ne uban gidan wannan ɓarayi kana da dama da ikon gargaɗi mai zafi irin na asalin maza ba mata ba, ina mai tabbatar maka daga zarar sun tsorata da gargadin ka ko kallon hanyar da wannan tagulla take ba za su sake ba" Lumshe ido yayi "Na gode" Ryan ya kashe wayanshi. Ya ɗan sake nazari kan ya saki murmushi ya juya ya je ya ɗauko bindigar ya wuce sashen. Dariya kaɗan yayi tuna yadda suke ta zazzaro idanu suka jike jagwaf da gumin tsoro... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *Don Allah ku yi haƙuri da wannan yau ɗin nan ban zauna ba wallahi* *012* Ta ɓangaren Afeefah anan bakin ƙofa ta ci kukanta har bacci ya sure ta ba tare da ta sani ba, mummunar mafarki da tayi da Aunty zee ne ya sakata farkawa a razane, fitsari ne kaman zai zube mata hakan ya sa tayi single kofa guda ɗaya da ta gani a ɗakin sai ta samu madaidaicin bayi ne, bayan ta gama abinda take ta fito ne ta fara bin ɗakin da kallon tsanaki don wutar a kunne tarrr kaman rana. Matsakaicin ɗaki ne a lailaye yake da farin tiles, fanka da bulbs duk suna aiki daga chan dungu 'yar ƙaramar katifa ce da babu ko shimfidi a kai, sai agogon bango da ɗakin ke dashi, time ta kalla ƙarfe biyu na dare har ma da mintuna ashirin da uku, juyawa tayi ta koma bayin ta yo alwala ta zo ta sake shimfida dankwalinta ta saka hijabinta ta tada sallah, raka'a shidda tayi a sujadar ƙarshe ne ta saki kukan dake dukanta a kirji tana jerowa Allah kirari bayan ta jera sunayen shi masu daraja casa'in da tara ta bi da salati annabi kan ta fara jero matsalolin ta da neman sassauci ta yiwa iyayenta da sauran 'yan uwanta da ta rasa Adu'a ta roki Allah ya kawo mata sauƙin rayuwa ya warware mata matsalolin ta ya kuma cigaba da bata zuciyar karbar ƙaddarar ta a duk yadda ya zo mata. Kusan ƙarfe uku da rabi ta sake kwanciya a wurin sanyin tiles na ratsa ta har wani baccin ya ɗauke ta. Ta makara don tana bude idanunta ta ga haske daga Window, da sauri ta miƙe ta shige bayi tayi saurin yin alwala ta zo ta gabatar da Sallar asuba tana sallame wa bata wani zauna Adu'a ba don tsoron laifi abincin jiya da ya ƙanƙare saboda sanyi ta cuccusa kan ta fito riƙe da plate ɗin ta nufi inda ta ga sun fito jiya. Tsaye bakin kofan kitchen ta ci karo da mommy sanye da hijabi, duk da zuciyarta ya buga haka ta ƙarasa ta zube a ƙasa tana gaisheta. "Sannu isasshiya sai yanzu za ki fito? Ban gaya miki aikin ki shara da wanke wanke bane, sai karfe nawa ake shara a gidan ku?" Murya a sanyaye tace "Ki yi haƙuri" Tsaki ta ja kan ta juya cikin kitchen ɗin "Talatuwa miƙo mata kayan sharar nan da mopping ta ajiye su chan baya don bana son kallonta gangar abincin da yarana za su ci ban san me za ta iya jefawa ciki ba ko jini ko tsoka" Abubuwan sharan wata dattijuwar ta fito mata da su, ta karɓa ta fara share parlorn zuwa dining area daga nan bayan ta gama ta shiga mopping da goge-goge aiki ba baƙonta bane don wannan a wurinta mai sauki ne sossai ma, haka zagi ko hantara duk ta riga da ta saba sai dai ba rayuwar da take fata tayi ba kenan, ba rayuwar da take buri ba kenan tana so ta ga tana karatu tana so ta ga tana hulda da mutane kaman kowani dan Adam, tana so taga ana hira da dariya da ita kaman yadda ta samu gidan Aunty zee, sai dai da kaman wuya wai guguwa da auren nesa. A gefe ta tsaya tana kallon Talatuwa dake ta aikin shirya abincin mutanen gidan bisa dining bayan ta gama ta dubi Afeefah tace mata "Ki zuba turarukan wuta 'yan dai-dai a cikin wanchan abin ki kunna" ta ƙarasa tana nuna mata burner, show glass ɗin ta tafi a hankali cikin natsuwa ta buɗe ta ɗauko ta saka ta kunna yadda aka gaya mata ta koma bakin kitchen ɗin ta tsaya tana cewa Talatuwa ta gama.. "Akwai abincin ki na saka miki a plate ɗinki ki ɗauka kije ki ci sai yaran sun gama karyawa tass sun wuce makaranta ake wanke-wanke" Da to ta amsa kan ta ɗauka ta fice, a hanya ta gamu da Ishaq so take ta gaishe shi amma kaman walƙiya haka ya wuce ta, bata damu ba ta shige ɗakin da yake da sunan nata ta rufo kofan. Ba za ta ce rayuwa a gidan yayi mata tsanani ba, saboda kwata kwata aikinta bashi da yawan da zai dameta, tana idar da Sallar asuba take zuwa tayi share share da su goge goge ta ɗauko abincinta daga nan ta tafi, sai wuraren sha ɗaya take komawa dining ta tattaro duk abubuwan da suka ɓata na karyawan ta fitar waje ta wanke ta kawo bakin kitchen ta ƙira talatuwa ta shigar, lokacin ita kuma Talatu za ta fiddo mata da abubuwan da ta bata na rana za taje ta tara su wurin wanke wanken ta rufe ta ɗauki abincin ranar ta ta tafi, sai bayan la'asar za ta fito tayi wanke-wanken haka na dare sai wuraren takwas tara. Ba Ta da abokin hira don talatuwa tsakaninsu ki yi kaza ne kar ki yi kaza ita kuma amsar ta ɗaya a komai to. Su iliya gudunta suke bata sani ba ko sun samu labarin ita ɗin annoba ce oho, bayan Hajiya da suka gamu sau ɗaya 'yan mata ukun ko ganinsu bata sake yi ba, kaman yadda bata sake saka saleem a idanunta ba tun ranar da ya kawo ta zuwa yau da take neman sati uku. Bata sani ba shin rayuwar zai cigaba da tafiya a haka ne ko zai sauya? Shikenan ta sallamar da burin ta na yin karatu kenan?Shikenan ta tabbata Mayyar za ta ci gaba da rayuwa ita kaɗai tamkar a fursuna kenan? Bata da mai bata amsa. Da misalin ƙarfe biyu na dare chan cikin baccinta ta ji kaman ana buga mata ƙofa, a ɗan tsorace ta farka sai ta ji ana ambaton sunanta "Afeefah! Afeefah!!" Tun ranar da ta sanya kafafunta cikin gidan yau ne karo na farko da ta ji sunanta na fita a bakin wani hakan ya sake razana ta, da ta kasa kunne kuma sai ta ji kaman Muryar salim a maimakon ta ji sauƙi sai ta ji tsoro ya sake dabaibaye ta. Me yake yi a kofar ɗakin ta da wannan tsohon daren? Ashe bai ma manta da ita ba yadda tayi tunani? Miƙewa tayi ta nufi kofan wani zuciyar na cewa idan kuma hajiyarshi ta ganshi fa? Allah ya isa fa zata mishi sanadiyarta, sai ta girgiza kai tana dakatawa. "Afeefah saƙo zan baki ki buɗe don Allah, na san kina jina please buɗe ba zan jima ba" A hankali yayi maganan amma ta ji shi tsaff kasancewar dare ne, ta gyaɗa kai tana ba zuciyarta tabbacin saƙo kawai zai bata ya juya ba wani abu bane, da sauri ta je ta buɗe kofan sai suka tsaya chakk idanunshi cikin nata yana ƙare mata kallo kusan seconds biyar bai ce komai ba sai ita ce tayi ƙarfin halin ɗauke idanunta daga kanshi ta ɗan duka ta ce "Ina kwana Ya salim?" Ɗauke idanunshi yayi ya lumshe su kaɗan ya saki ajiyar zuciya mai dan nauyi, matsota yayi sossai ta matsa baya tana kallonshi da manyan idanunta, ya leƙa ɗakin kaɗan kan ya dawo baya, time ya kalla inda seconds ke reading, babbar leda jumbo dake hannunshi ya ajiye mata don baya so ya shiga ɗakin nata ba da wannan dare ba, kai ko da rana ne ma baya jin zai iya kebewa da ita inuwa guda ko don addini da ya haramta hakan. "Ki kula sossai za mu yi magana" Yana kai nan ya juya ya fice, ta bishi da kallo har ya ɓace mata kan ta runtse idanunta tana kokarin mayar da kwallarta ta tura kofar ta rufe, ledan da ya fi ƙarfinta ta shiga ja har gaban katifa ta barshi nan ba tare da ta buɗe ba tayi kwanciyar ta, sai dai duk yadda ta so baccin ya sake ɗaukar ta baccin ya ƙi zuwa, tuni ta buɗe idanunta ledar ta janyo gabanta ta shiga buɗewa a hankali. Da wani bargo mai taushi ta fara cin karo kaman ya san tana matuƙar bukatar bargon don tana shan wahalar sanyi da aka fara shiga, gashi bayin ta babu ruwan zafi wani lokacin hatta alwala da kyar take iya yi, wanka kam ba'a magana in dai tana so tayi sai ta bar ruwan a rana wuraren sha biyu zuwa karfe biyu nan ma da kyar za ta watsa bata gama tunanin ba ta ci karo da kwalin heater, irin wanda ake maƙalawa jikin bokiti ɗin nan a kunna ta ɗora shi kan bargon tana ɗan murmushi, ta sake mayar da hannunta ciki ta zaro hijabai ninkakku har kala huɗu kuma duk za su iya kai mata ƙasa Brown, Ash, purple da onion colour su ma gefe ta ajiye su, ta sake mayar da hannu ciki ta zaro kananun catons na biscuit da wasu small chops dai waenda za su dan kwana biyu basu lalace ba daban daban masu ɗan yawa, har da su five Alive kananu catons uku. Ganin abubuwan dake ciki sun kare ta ɗaga ledan domin matsarwa don ta sake kallon sayyayarta sai taji da ɗan motsi a ciki, ta buɗe gabaɗaya ta ci karo da ƙaramin kwali jikinshi da zanen waya, buɗewa ta yi ta ci karo da karamar Villion mai kyau da tsari Dukda keypad ne amma sossai ya mata kyau, fuskar wayan ne yayi haske alamun a silent yake saƙon akwati na SMS ya bayyana tare da sunan. "Saleemullah" Sai ta saki murmushi karo na farko ta buɗe saƙon. "Ba ki yi bacci ba?" Numfashi ta sauƙe kan ta shiga reply don ta iya sossai a wayan Aunty zee da ma wasu 'yan ajin su na islamiyya lokacin da take zuwa makaranta ta amsa da "Eh, Na gode sossai da saƙon ka duk abinda ka saka a ciki kaman ka san ina da buƙatar su" Bata ajiye wayan ba ta ƙurawa screen ɗin ido chan sai ga reply ɗin shi. "Na kasa samun natsuwa da tunaninki zuciyata ita ta lissafo min duk abin da zuciyarki ta raya tana da buƙata. Kin ga ko zuciya bata ƙarya" Ta karanta saƙon ya fi sau abin da ya fi sai ta rasa amsar bashi, bata motsa ba har wani saƙon ya sake shigowa daga gareshi. "Na san baki jin daaɗin yadda kike zaune amma kiyi haƙuri zan yi iya ƙoƙarina in ga na yi settling komai, za ki yi karatu har sai kin ce ya isa, ga wayan nan zan dinga yi miki saƙo ki tabbatar kina yi min reply, duk kuma abin da kike so do not hesitate ki sanar da ni zan kawo miki. Akwai full qur'an a memory ɗin idan kin ji kaɗaici ki rage lokaci da shi kin ji?" Tana murmushi a lokaci ɗaya idanunta na zubar da kwalla ta rubuta "Wallahi samun mai irin zuciyarka sai an tona Yayana, na gode na gode Allah ubangiji ya ba ni ikon saka maka" Ta tura tana murmushi "Never mention my dear, ki kwanta kar ki makara da safe byeee" Ta sake sakin murmushi kan tayi reply "Allah ya ba mu alkhairi Soja Mai kirki" Dariya yayi daga ɓangaren shi ya rubuta "Au akwai marasa kirki ne?" "Eh mana, abokin kan nan Dukda gaskiya ya faɗa amma in a wrong way, su ne suke ɓata muku suna ake yi muku kuɗin goro" Ya girgiza kai yana cigaba da murmushi "Ryan kenan! Haka Allah yayi shi, oya sleep Good night" Bata yi reply ba sai lumshe idanu da tayi razanannun idanunshi da yake zare mata su da sautin dakakkiyar muryarshi suka dawo mata kaman yanzu yake yi, da sauri ta buɗe idanun gabanta na faɗuwa ganin ita kaɗai ce sai ta saki murmushi a hankali ta maimaita sunan "RYAN" tana lumshe ido. 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *013* Sabo ne mai ƙarfi ya shiga tsakanin su ba na wasa ba ta sanadiyar wannan text message da suke yi wa juna, yana matuƙar wuya ta sanya shi a idanu amma baya yini ya kwana ba tare da sun ɗauki mintuna masu ɗan dama suna exchanging SMS ba, sai dai idan inda yake babu network, idan kuma tana aiki ne wayan na maƙale a kunnenta tana sauraron karatun alarammar Prof Isa Ali phantami wato sheikh Abba zari'a yana matuƙar yi mata daaɗi har ta roki Saleem da in zai zo ma ya taho mata da alqur'ani ta cigaba da koyo don yadda yake karatun daidai da 'yan koyo. Yau ya kama Lahadi kusan duk iyalan gidan suna a gida in ka cire salim da rabon shi da gidan ma an kwana biyu, da zazzabi ta tashi tana jin sanyin hunturu dake busawa na Huda jikinta, kasancewar koyaushe hannunta na ruwa ne ko tana bakin pampo kuma sossai bazarar ya shiga hakan ya haifar mata da mura da ta ɗan kwana biyu dashi, a maimakon ya ragu ma na safiyar yau worst ga ciwon kai mai tsanani da take fama da shi ko idanunta bata iya buɗewa da kyau, a hankali kuma karo na ba adadi ta ɗago su da kyar ta kalli agogo kusan ƙarfe tara na safe ko shara bata yi ba gashi babu wanda ya leƙo ta bare a yi mata uzuri, lallaɓa wa tayi ta miƙe tsaye atishawa na ƙwace mata da ƙarfi ta ja hanci tana dafe kai haka ta sauƙa ta zari hijabai har biyu ta sanya saboda yadda a ɗaki ma sanyin ya isheta bare ta fita waje, a hankali take tafiya har ta isa main parlorn gidan daidai kofar kitchen ta hadu da Talatuwa. "A'a yanzu kenan zan tafi biɗar ki, na gama abin kari tuntuni ina son fitarwa kuma ba'a yi shara ba. Lafiya kam?" Ta ja hanci tana ɗan dafe kanta dake juyawa "Wallahi mura ne ke damu na sossai, kaina kaman an ɗora min dutse" "Ashhaa! Sannu Allah ya baki lafiya, idan Hajiya ta fito ki gaya mata za ta baki magani. Yanzu ki je ki kwanta bari ni na yi sha...." "Ta Yi mene? Kwanciya ta zo yi gidan ne da masu gida suna kwance itama tana kwance?" Sadiqa ta katse musu zancen da gadara. "Wai na ga bata jin daa..." "Kinga Talatuwa ba dake nake ba, ki je ma ki fara shirin ɗorawa friends ɗina abinci za su shigo babu jimawa, ki tabbatar abin da za ki dafa zai ishi cin mutane shidda zuwa bakwai... Ke kuma" Ta juya ga Afeefah "Ki wuce ki je kiyi aikin ki, kuma ki tabbatar tana gamawa ba'a ajiye mana kwanuka a mawanki kudaje suyi ta bi ba" Kai Afeefah ta gyaɗa bata ce komai ba ta wuce ta ɗauko kayan sharar ta duƙa don fara wa, da ƙarfi ta runtse ido jin kanta kaman zai biyo ta ya faɗo haka ta cigaba da aikin cikin dauriya irin nata, Sadiqa dake tsaye tana danna waya rashin maganan yarinyar ke matukar bata haushi ta ja doguwar tsaki kan ta juya fuuu tayi ɗakinta. Afeefah ta gama sharan tana mopping kenan ta ji zuban kaya bisa saman kanta, baya baya tayi Allah ya taimaketa ta dafe jikin dining table, ta ɗago rinannun idanunta ta zubawa Samha da ta watso mata kayan... "Ni ki daina kallona, kurwata kurrr... Wa ma ya sani ko naman wanda ya fi ƙarfin ki kika ci ya tsaya miki a wuya. Ki gama abin da kike ki wanke min kayannan sameera ta aiki Ishaq kuma ina da bukatarsu babu jimawa". Bata jira amsar Afeefah ba ta wuce zuwa ɗakin Sadiqa, dukkansu biyu suna zaune ne Samha ta isa tace. "Allah da gaskiyar ki Aunty sadiqa yarinyar nan ta samu wuri har wani iyayi take kaman ta Allah, muka cigaba da zuba mata ido babu wanda ya san me gaba za ta haifar kin ga har wani fresh tayi ta kara kyau" Sameera tace "Ni na fi tausayin Yaya Salim don daga ganin yarinyar nan wallahi green snake ce, bana tunanin idan da Mommy bata ɗauki matakin da ta ɗauka kanshi ba zai rayu har yau, gwara mu kasheta da aiki ta yadda zata gaji ta gudu" Sadiqa tace "Toh ai yanzu sai mu ci ɗamarar hakan don na ga mommy ta fara mance zancenta, kin ga idanunta kuwa? Wlh muddin yarinyar nan ta samu rana ba karamin shanya za ta yi ba". Suka cigaba da tattaunawa akan Afeefah da idan an matse su ba za su iya faɗan laifinta guda a gare su ba amma da yake amfani da zancen mutane ya riga ya zama jinin ɗan Adam sai ya zamana kawai da gaske Mayya ce a gare su kuma idan bata bar gidan ba za ta iya raba ɗayan su da rayuwarshi, haka kuma duk wanda ya nuna mata tausayi to fa shi za ta fara lamushewa. Zaune yake cikin mota da alama abu yake dubawa don hankalinshi duka ya tattaru ne ga wayan hannunshi, sanye yake da wani grey trouser mai taushi ya haɗa ta da cream Color shirt da yafi yanayi da gashin mage tsabar taushinsa, high neck ce wuyan don idan da zai ja daga sama zai iya rufe har hancinshi da rigar, Dukda wani irin sanyi da hazo da ya cike sararin samaniya motar dake kunne cike take da sassanyar iskar Ac ya haɗu da ni'imtacciyar kamshin shi da ma flavours da yake amfani da su na motan suka ba da wani kamshi na musamman. A hankali sautin waƙan Alex Warren ta ordinary ke tashi, tsaki ya ja a karo na barkatai a ranshi yake shirin fara masifa don baya ƙaunar bata lokaci sai ga wayanshi ya shiga ƙira, Bluetooth na kunnenshi ya ɗan danna. "Allah Saleem zan yi tafiyata ka san na tsani ɓata lokaci" Duk da a hankali yayi maganan alamun muryarshi ya nuna ya hasala kuma tabbas zai iya tafiya ɗin don saleem ya shiga masa lokacinsa. "Afuwan mutumina wallahi sai yanzu na tuna inda papers ɗin nan suke, suna ɗakina kuma kyakyawar ɓoyo na musu babu wanda zai san inda suke ban zaci boss zai tambaya bane da na taho da su, please help me ka je ka dubo min" Shiru yayi saleem ya marairaice murya "Please help a soul ba ni da mai min sai kai, ka ji Autan Mammi?" Da magiya ya ƙarasa hakan ya sa Rayyan ɗan murmushi "Don dai kai ne..." "Eh taimaka pls" Ko kan salim ya gama maganan ma ya ja motar cikin natsuwa yana sauraran kwatancen da saleem ɗin ke mishi na inda safe ɗin da ya ɓoye confidential files ɗin yake, Saleem ya bashi wahala don ya fi hour yana neman su a office nashi na nan head quater don mance inda ya ajiye yayi sai daga baya ya tuna da kyar. Daga waje Ryan ya ajiye motar shi ya sauka ya shiga cikin gidan da ƙafa cikin tafiyar shi mai cike da ɗumbin ƙasaita wane saraki hannayenshi duk zube a aljihu, waƙa still yake ji a Earpods ɗin kunnen nashi saidai sautin na fita ne da sanyi ba mai hayaniya ba, kamar ko yaushe a murtuke fuskar nan sai kace wanda aka zagi iyayenshi har ya shige, bai nufi ma main parlorn ba ta kofar baya ya zagaya ya haura stairs da zai sada shi da ɗakin salim, a jikin kofan ya tsaya ya duba inda suke ajiye key ya ɗauka ya buɗe ya sanya kanshi ciki don duk sun san inda ɗayansu ke barin spare key incase of emergency, dulum ɗakin don komai a kashe ya kunna wuta ya wuce uwar daka direct wardrobe da ya mishi kwatance ya je ya buɗe, kaya ne a jikin hangers ɗin ya ware bangon ya bayyana gefe wani keypad ne da ba zaka ce akwai wani abu da zai iya buɗuwa ba ko da an danna. Wasu numbobi ya saka sai ga wardrobe ɗin ya dare, ya turo wani box waje nan ma ya saka wasu lambobin sai ya budu bai tsaya ma duba me ke ciki ba ya zaro files ɗin ya buɗe don tabbatar da shi ne ko ba shi ba, su ɗin ne kuwa yana ƙoƙarin scanning dilim nepa suka ɗauke. Ɗakin ne yayi duhu sossai ba zai iya scanning haka ba sai ya nufi balcony door yana dan tsaki ya buɗe ya tsaya daga saman ya fara scanning yana forwarding to salim dake online yana jira har ya gama, yana ƙoƙarin mayar da wayan aljihu ya ɗan ɗago sai idanunshi suka faɗa kan ta, har ya juya ya ɗan dakata ya sake waigo wa ya kalli ƙasan ba fuskarta yake kallo ba irin aikin da take yi a sanyin yake gani a ranshi yana raya 'Mutane are heartless' Ya dai san babu ɗiya

Chapter 7 of 40