da Apple Ipad ya fiddosu a kwali ya miƙa mata
"za ki yi amfani da waennan kiyi karatunki daga kan gado i promise to help you in all the process exams kaɗai zai kai ki makaranta. Ina fata hakan bai ɓata miki ba?"
Ts saki murmushi hawaye na zuba mata tace
"Har wacece ni da zan ce hakan bai min ba? Ciroma ne fa gabana kuma Sarakin Fombina..! Ni din ban kai wannan matsayi ba kuma ko da na kai ba zan taɓa kin amincewa ba don ni'imace hakan da ban tsammata ba Allah ya bani, wasu na chan ma suna neman yadda za su yi karatun bai samu ba, wasu na chan suna yawo lectures cikin rana, zafi da ruwa ai ni daaɗina ma na samu miji mai gatanta ni... Allah ya saka maka da alkhairi na gode sossai na gode kwarai, na...."
Bakinta yayi saurin rufewa da nashi ya bata deep Kiss da ya sa take jin sanyin na sauka har cikin zuciyarta.
"Babu wannan tsakaninmu girmanki ne Sarauniyata"
Tayi murmushi tana sake godewa Allah.
Janshi tayi suka je ya ci abinci yana bata cike da kulawa har suka gama suka zo suka gabatar da isha kan suka shige cikin bargo yana yi mata setting na system da ipad ɗin yana koya mata yadda zata yi amfani da su tana daga kwance nashe nashe akan kirjinshi.
Washegari da misalin ƙarfe goma ta fito cikin wani Apiligue lace peach da yayi mugun amsarta ta ɗora gyale mai girma a kai tare da alkyabba marar nauyi ta nufi sashen Ammi don miƙa gaisuwa, ta isa parlorn babu kowa don haka kai tsaye ɗakin Ammin ta nufa ta saka hannu zata bude ta ji Ammin na cewa
"Yaya Maudo ni dai ban goyi bayan wani auren Zarah da Sameer ba Dukda na san alkawari ne amma Meyasa Mai martaba zai fara matsawa a yi shi yanzu? Shi kanshi Sameer ɗin ba son maganan yake ba sai kwana- kwana yake ya fi sati biyu mai martaba na Binshi da wannan magana... Ba wai bana son zarah bane amma yaushe har suka dawo suka gama sabo da nan ɗin? Kwata kwata aurenshi ma da Afeefar bai fi watanni takwas ba don Allah ka bashi shawarar a jinkirta ba dai sati biyu masu zuwa kaman yadda yace ba..."
Wani irin faɗuwa gabanta yayi har tana ganin jiri, Dukda tana jin Ammin na cigaba da magana bata iya ta tsaya sauraronta ba don mugun jin da tayi ya daki zuciyarta fiye da zato ko tsammani, a gigice ta juya ta nufi sashensu don gaisuwar ba zata iya shi ba cikin wannan hali ta tabbatar da za'a bincika jininta yayi mugun hawa ko ya zuƙe tas yayi ƙasa tsabar tashin hankali
Yana zaune kawai ya ga faɗowarta don yau din Asabar ne bai fita ko ina ba da kyar ma ya kyaleta ta fita gaisuwar, ganin halin da ta shigo ya sa yayi saurin Miƙewa yana rike kafaɗunta.
"Afeefah! Afeefah menene? Me ya faru?"
Ta kasa magana ma, girgizata yayi
"Me ya sameki? Afeefah!!!"
Da ƙarfi yayi maganan yana bin jikinta da kallo sai dai bai ga komai ba.
"A wurin Ammie ne aka ɓata miki rai? Ko wurin Mama ne? Me ya faru kika shiga cikin wannan yanayin? Ki yi min magana mana!"
Kuka mai sauti ta fashe dashi kaman wacce aka rufe da duka sai ta sake ɗaga mishi hankali ya juya da sauri zai fita ya tambayo uban da ya taɓa ta tayi saurin riƙo hannunshi tana kukan sossai duk ta ruɗa shi.
"Sakeni in ba zaki faɗa min abinda aka yi miki ba Afeefah, Sakeni nace in je in ji dalilin da kaina...!"
Da tsawa yayi maganan yana kokarin fusge hannunshi tayi saurin rungumeshi kamkam tana cigaba da kukan da ya ƙarasa cire mishi natsuwa.
"I thought ina da muhimmanci a rayuwarka, a zatona duk wani abu da ya shafeka ya shafe ni Meyasa zaka min hakan? Meyasa Ya Saraki?"
Sakinta yayi yana riƙo fuskarta idanunshi cikin nata
"wa yace miki ba ki da muhimmanci a rayuwata? Kin kuwa san yadda nake jinki Afeefah? Meyasa za ki yi irin wannan tunanin?"
"Ba gashi ba, idan har ka daukeni da muhimmanci ba zaka binne ni ba, ashe aure zaka yi nan da sati biyu? Aure Ya Saraki irin wannan baka iya ka sanar min ba?"
Kukan da take na shaketa ta ƙarasa, sossai fuskarshi yayi Red ainun jijiyoyin kanshi duk suka miƙe kukanta tamkar saukar tafasashen ruwa ne a zuciyarshi shi kadai ya san irin abinda yake ji, a ina ta ji? Zai yi magana ta ture hannayenshi ta nufi ɗaki da gudu tana cigaba da kukan ya riƙe kanshi yana ambaton sunan Allah, bayanta ya bi da sauri sai dai ya tarar ta rufe kofan da makulli hankalinshi ya sake tashi ya shiga bubbugawa yana kiran sunanta cikin damuwa...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*55*
https://chat.whatsapp.com/HUJI7tg9TOU941grP60r4S?mode=ems_copy_c
Kinaneman group din dazaki ringa sarinkayan kitchen cikin farashin sari...tayadda koda kinje kasuwa bazakisamu kasa d farashinmuba snn zaki iyazuwa har hargida kisayi dukkan kayan dakike bukata cikin kwanciyar hankali kokisaya ayimaki delivery zuwa dukkan inda kike afadin Nigeria da dama makotan kasashenmu kikarbi kayanki cikin farinciki da aminci!!!.....kiyi joining a mai nono kitchen utensils and household........gaskiya d amana sune takenmu!!!👏🏻
********
Yayi yayi ta buɗe kofar ta ƙi, har spare key ya ɗauko sai dai dayake ta bar key jikin ƙofan ya ƙi shiga, cike da damuwa ya koma ya zauna a kan kujera hannunshi dafe da goshinshi sama da mintuna goma yana nan shiru kan ya miƙe ya tafi ɗakinshi yayi wanka ya shirya cikin wani jumpha baƙi dinkin zamani, ya saka hula da half cover duk baƙake ya fito kai tsaye ya nufi motarshi su Gaabɗo na miƙa gaisuwa ma babu wanda ya amsawa ganin yanayinshi yasa basu nuna za su bishi ba don kallo ɗaya ya musu suka koma suka natsu.
Tafiya ba mai nisa ba sossai ya kai shi shiyyar da Galadima yake duk a cikin masarautar, parking yayi ya sauka ya nufi ciki hadiman ɓangaren na ta miƙa gaisuwa bai amsawa ko ɗaya ba ya isa babban parlorn Galadiman, ya kuwa same shi zaune suna ma tattaunawa ne da Ameer, ganinshi ya sa duk fuskokin su suka cika da fara'a
"A'ah yau ɓatan kai ka yi ne Ciroma?"
Da kyar ya ɗan sake fuskan ya zauna
"Baba Barka da rana"
"Barka dai, ya iyalin naka?"
"Alhamdulillah"
Miƙawa Ameer hannu yayi suka gaisa kan ya dubi Baba.
"Baba dama na zo ne akan maganan Zarah da mai martaba ya tayar, idan da hali ina so ka mishi magana Baba a dakatar da maganan nan zuwa gaba duk yadda zan mishi bayani ya kasa fahimtata, na amince mishi ne kawai saboda na san girman alkawarin wannan masarauta kuma ba na so ko kadan a ga gazawarshi ka san yadda su Makama suke... Na ji na amince amma ba yanzu ba kaman yadda suke so"
Galadima ya sauƙe numfashi ya ce
"Sameer da safen nan muka gama wannan magana da mahaifiyarka, ta kirani akan a ja maganan ba yanzu ba duba da baka ma wani jima da dawowa ba abubuwa dayawa baka gama sabo dasu ba, ga matarka da bata rufa shekara ba Dukda ba hujja bace tunda anan muna aurawa namiji ma mata biyu a rana ɗaya amma abin a duba ne zancen naku, Mahaifiyarka ba iya jayayya take da mai martaba ba a wanchan ɓangare kuma akwai Fulani da 'yan uwanta har biyu suna uzzura mishi duba da yarinyar ta isa auren shiyasa abin ya zo a hagunce. Zan gwada yi mishi magana idan ya amince sai a bar maganan for now amma da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa"
Idanunshi ya runtse ya san dama aikin su Fulani Adama ne they will be on his fathers neck har sai sun ga sun samu abinda suke so, shi wlh ba ma zai iya wassafa yadda zarahn take ba Dukda bata dameshi ba amma tashin Hankalin Afeefah shine abinda ba zai iya jurar gani ba a abinda ya shafi auren.
"Baba don Allah a yi min wannan ƙoƙarin, mai martaba yayi rantsuwar ba zai karɓi wani uzuri daga gareni ba muddin ba mai ƙarfin da zai iya haramta auren bane a yanzu duk abinda zan fada mishi gani zai yi excuse nake kawowa na watsa mishi ƙasa a idanu"
"Hakane. Dukkanmu ba za mu so ganin an yi ƙaranta ba don ba girman wannan masarauta bane, zan gwada mu gani"
"Na gode sossai Baba bari na koma"
Ya miƙe Ameer ma ya miƙe suka fito a tare a jikin motan shi suka tsaya yayi shiru.
"Lafiya dai kam Sameer? Ko duk maganan auren ne ya saka ka cikin damuwa?"
Numfashi ya sauke yana fesar da iska daga bakinshi
"Ameer damuwana ɗaya ne tak tashin hankalin Afeefah, bana son zancen auren nan kwata kwata don na san ba zata ji daaɗi ba wace macece ce zata so a mata kishiya? Irin wannan kam ma Gani zata yi kaman don ita ba yar cikin gidan nan bane za'a ware ta ko a ba ni zarah, tunanin sakata a damuwan ya sa ban iya na yi mata maganan ba amma sai gashi ta ji a wani wuri yanzu haka tana chan tun dazu tana kuka ban san ya zan yi ba!"
Cike da damuwa ya ƙarasa maganan.
Kafaɗar shi ya dafa
"Ban taɓa sanin haka rauninka yake ba sai akan Afeefah, kuma gaskiya baka kyauta ba ya kamata duk abinda yake faruwa ta fara sani daga wurin ka zata iya fahimtarka ba wai taji a wani wuri ba da ake maganan kila saura sati biyu...! Yanzu kai za ka kwantar da kai kayi rarrashin ta hanyar da zata fahimceka ko don gaba duba da kaine magajin wannan jaha ta mu ko a rana ɗaya ana iya baka mata a ɗaura bambancinta kawai zai iya zama kana sonta fiye da kowa kuma hakan ma wani makami ne a gareta"
"Dole na Ameer don ba zan samu natsuwa ba muddin tana cikin damuwa, bari na je. Na gode"
Da kallo Ameer ke Binshi har ya shiga motar ya bar wurin, murmushi yayi lallai So So ne hmm idan ba son ba wani abu ne zai taɓa zuciyar Sameer haka? Juyawa yayi ya koma ciki don basu gama tattaunawarsu da Mahaifin nashi ba.
Sai da yayi azahar ya dawo ɓangaren ga mamakin shi ya samu abincinshi jere a kan dining kuma ya san bata taɓa bari hadimai su mishi girki ba kenan ita ta fito tayi, ɗakin ya nufa ya murda handle ɗin sai dai a rufe still goshinshi ya dafe bai taba sanin tana da fushi haka ba, ya san kalar haƙurinta lallai ya kaita maƙura.
Dakinshi ya nufa don abincin ba zai shiga ba ya rage kayan jikinshi ya kai zaune yana lissafi.
Wasa wasa har dare ta ƙi bude kofan, ko da ya fita Magrib da isha kan ya dawo ya samu ta ɗauke abincin dazu ta ajiye wani daban, shima bai bi ta kanshi ba ya sake komawa kofar ɗakin yana kiran sunanta amma ta ƙi ta buɗe daren tea ya sha daga ita har shi baccin su rabi da rabi don tunda suka shirya basu taɓa kwana ba tare da juna ba cikin bargo ɗaya skin to skin sai ranar.
Ɓangaren Afeefah Da asuba bayan ta yi sallah ta ɗan yi azkar kan ta miƙe ta saka wani silk fabric gown ta ɗaura dankwalin fuskarta har lokacin da alamun kuka don kukan da ta jima bata yi ba tayi shi a jiya a ƙarshe ta yi finalizing solution ɗinta, ta sakawa zuciyarta haƙuri da juriya don ba zata taɓa hana shi ba idan Allah ya rubuta, haka ba zata saka ya ƙi bin umurnin iyayenshi ba ta riga ta sakawa zuciyarta cewa ko ba jima ko da bai auri zarah ba zai iya yin wani auren don haka za tayi Adu'a Allah ya kawo wacce za su zauna lafiya, za ta kuma yi iya kokarinta na ganin ta cigaba da zama ta farko a zuciyarshi har abada sai dai ba zata ɗauki ya dinga binne ta a komai ba, don yawan fushin nata ma na rashin faɗa mata akan lokaci ne.
Ta zubawa dining ɗin idanu ganin bai taɓa komai ba ta tattare ta nufi kitchen ta saka a microwave don bai lalace ba, kokarin ɗora mishi wani abin take don ta san shi kam ba zai ci wanchan ba kawai ta ji an rungumeta ta baya, daga ita har shi sai da suka sauƙe wani nannauyan numfashi, shiru tayi bata ce komai ba ta cigaba da kokarin aikinta ya ɗaga ta chak yayi ɗakinshi da ita ya sauketa a kan gado yana zama ya riƙo hannayenta duk biyu.
"Boɗɗi am...!"
Idanunta ta kawar yayi murmushi mai sauti ya ce
"Na tuba ki yafe ni Afeefah, ba zan iya jure fushinki ba Allah kaɗai ya san wani hali kika jefa ni daga jiya zuwa yanzu... Please lets talk kin ji?"
Idanunta suka cika da kwallah bai ankara ba ya ji ta fashe mishi da sabon kuka a fili ya furta
"Yaaa Salaam Afeefah...."
Rungumeshi da tayi ya saka maganan yankewa, ya rufeta cikin jikinshi yana shafa bayanta idanunshi a rufe yana jin zafin kukan nata har ranshi.
"Ki yi haƙuri na saka ki cikin wannan hali, it wasn't intentional ban san yadda zan iya fuskantarki da maganan bane but am sorry kin ji?"
"Promise me Ya Saraki, ka min alkawarin cewa ba za ka taɓa juya min baya ba, ka yi min alkawari cewa ba zaka sake ɓoye min duk wani abu da ya shafe mu gabaɗaya ba, i felt hurt zuciyana ya kwana yana zafi da raɗaɗin jin zancen aurenka ba tare da na sani ba"
Ɗago fuskarta yayi yana share mata hawayen da hannayenshi biyu cikin karyayyen murya yace
"I promise Afeefah, na miki alkawari in shaa Allahu. Ki yi haƙuri i didnt meant to hurt you that badly dubi fuskar ki yadda yayi looking so tired and pale sbd zubar da hawaye"
Wani hawayen ne ya gangaro sai ya runtse ido yayi shiruu.
Shesheka ta ja ta sa bayan hannunta ta share wani ya sake zuba ta sake sharewa looking cute nd sad at the same moment.
"Ka yi haƙuri i couldnt control my emotions ba laifina ba ne, am jealous kishi nake ji in na tuna nan da kwanaki kadan zan raba ka da wata, za ka shaki kamshinta ba nawa ba, za ka hada jiki da ita.... Am sorry"
Duk ta rasa yadda zata yi bata san tana da irin wannan kishin ba kuma ruwan kaunar da ya zuba mata ya sa take jin shigo da wata duniyar su zai yanke mata wannan ƙauna.
Jikinshi ya janyota zuciyarshi na tsananta zafi ya kasa magana, ita kuma ta zaci shirun da yayi ita ce take ɓata ranshi cikin kuka tace
"ka taya ni Adu'a Allah ya sassauta min abin da nake ji Ya Saraki, am just jealous because I love you, angry because all i care about is you a lokaci guda kuma am scared because am afraid of losing you"
Ɗagota kawai yayi ya haɗe bakinsu don kukan ya gama hawa kanshi, wani irin deep Kiss yake yi mata da tun bata amshi signal ɗin ba har ta amsa, a iya romance ya tsaya sai da ya tabbatar jikinta yayi laushi ainun fatarshi da nata na a manne da juna yana shafa bayanta a hankali suna sauƙe numfashi zai yi magana ta riga shi muryarta chan ƙasa tace
"I wanted to be the only one to tells you I love you, wacce za ta haɗa miyaun baki da kai, touches your skin and feel you inside me sai dai kash! kana naka ne Allah na nashi, Kana da damar auren mata har huɗu tunda kana da halin hakan kuma kana da lafiya, abu daya zan roka daga gareka Ya Saraki kar ka daina so na don Allah zuciyata fashewa zata yi".
Yana shafata tana sake yin lub jikinshi ya shiga furta
"Afeefah ki yarda da ni, babu wata kishiya da zuciyar Ryan zata iya yi miki a soyayya domin ke ɗaya jal ta sani kuma ke kaɗai ta aminta da ki ja ta duk inda kike so, da ke kaɗai ta aminta a matsayin Abokiyar rayuwa ba ni da yadda zan yi ne da babu dalilin da zai sa in amince da batun zarah amma ba zan iya watsawa mahaifina ƙasa a ido ba alkawari ne da aka yi tun ban san kaina ba, amma in har za ki cigaba da wannan kukan komai zan iya yi ciki har da barin wannan gid..."
Ɗagowa tayi ta haɗe lips ɗinsu da kanta sai da ta bashi kyakyawar Kiss kan ta kalli idanunshi hannunta na a fuskarshi shima idanunshi zube cikin nata da suke a rine tace
"Kar ka ce komai, ni da kai duka karkashin ikon mai martaba muke dukkanmu uba ne shi a gare mu da magana kawai zai yi mu cika, sannan aure ba haramun bane idan yana cikin ƙaddararmu ina roƙon Allah ya ba ni haƙuri da juriya ya kuma kawo mana ta gari wacce za mu haɗe kai mu zauna mu kula da kai gabaɗaya, don haka Allah ya nuna mana lokaci ya bamu zaman lafiya gabaɗayanmu"
Ta ƙarasa tana komawa kan kirjinshi ta kwantar da kanta tana mayar da hawayen da suka cika mata ido.
Matseta yayi a jikinshi kawai bai ce komai ba, sun jima a haka don bacci ne ma ya ɗauketa shi kam bai iya yayi baccin ba damuwar da ta shiga ya tsaya mishi ainun ya san ba komai bane sai zallar soyayyar da take mishi, lumshe ido yayi kawai sai ranar da take ba Mammi da Abeeha labarinta ya faɗo mishi the way she was deeply hurt nd depressed anya ta chanchanci raba farin cikinta guda ɗaya jal da wata? Yayi adalci kenan idan ya iya haɗa jiki da wata mace ba ita ba? Numfashi ya sauke mai nauyi ya mirginata kwance ya ja mata bargo kan ya sauka ya dauki shirt ya saka ya nufi kitchen.
Breakfast ya samar mata bayan ya gama ya kai har kan gado ya ajiye kan ya shiga shafa kanta zuwa fuskarta cikin tattali da kulawa har ta buɗe ido, murmushi ta mishi ya mayar mata
"Tashi ki ci abinci Boɗɗi"
Miƙewa tayi zaune tace
"Brush tukuna bakina babu daaɗi"
"Ba dole ba na tabbatar through out jiya baki ci komai ba"
"kaima ai na ajiye maka baka ci ba i was disturbed"
"Toh ba fushi kika yi da Sarakinki ba..!"
Yayi maganan cikin muryarta ta saki dariya ya ɗauketa zuwa bayi tare suka yi brush suka dawo tana bashi yana bata har suka koshi.
Wanka ma tare suka yi abin su yana ta takalarta tana ture shi, suka fito ta shirya shi kan suka je ɗakinta ya taya ta shiryawa.
"Bari na je nayi gaisuwa na dawo"
"Ki bar gaisuwan nan babu inda zaki a sake bata miki rai a banza"
Idanu ta ware
"An taɓa fushi da iyaye ne Ya Saraki? Iyaye musamman uwa ita kaɗai ce take mantawa da kanta yayin da take yiwa danta Adu'a ita a wurinta idan danta yayi nasara itama ta yi, Na san ka rasa Mammi ka kuma tabbatar babu zafi da ciwon da ya kai na rashin mahaifiya. Ciwo ne da baya taɓa goguwa har abada, zaka yi fata za ka yi adu'ar ko da ganinta sau ɗaya ne a yayinda kasa ya rufe idanunta a sannan kuma babu halin hakan, Uwa garkuwa ce ga dan da ta haifa, Ya Saraki in na ce maka ga kalar kukan da nayi na maraici ba zaka yarda ba, duk raɗaɗin da zan fada maka akwai ba zaka fahimta ba wani lokacin Allah ya sanya albarka daga bakinsu kawai kake nema ba zaka samu ba, Allah ya umurcemu da kyautata musu iya iyawa a sadda suke raye ni ka ga ban samu wannan damar ba, ko sanin su ban yi ba tsakanina da su Adu'a ashe ba zaka amfani wannan damar ba? Don Allah Ya Saraki ka sake tunani akan hukuncin da zuciyarka ke aikatawa, Allah ya sasanta tsakaninku cikin sauƙi"
Shiru yayi ganin kaman zata ɓata mishi rai ta tashi ta fice tana ce mishi sai ta dawo ya bita da kallo kawai bai ce komai ba.
Sashen Ammi ta fara zuwa suka gaisa ta ɗan jima suna hira da Zarah da Aisha kan ta wuce sashen Fulani Adama.
"Barka da safiya Mama!"
Tana hakimce ta amsa idanunta na scanning Afeefar ciki da bai kallon da ya sa taji duk ta tsargu kan ta amsa.
"Lafiya ƙalau, shi mijin naki kam isar shi ta kai ya share sama da watanni a Masarautar nan bai taɓa zuwa inda muke ba sai dai mun haɗu a hanya ko? Uhm ko da shike ba ke ya kamata na yiwa zancen ba mai martaba ne ya ɗaure mishi kugu dole"
Shiru tayi don bata san me zata ce ba, kiran hadimarta tayi
"Ke Rahane kawo mata abin taɓawa"
"Ai mama da ta barshi yanzu na karya kenan na fito"
"Dama na lura baki taɓa cin komai na ɓangaren nan ba, ashe kema baki daukeni uwa ba kenan... ai shikenan sai gaisuwar ma a barta kawai Allahn da bai bamu 'ya'yan ba yana sane da mu, na ji labarin babu abinda bakya ci a sashen Faɗimatu nan ne ba zaki ci komai ba? Yayi kyau"
Bata san Meyasa take mata maganganu haka ba, duk sai ta rikice ma tana tuna gargaɗin Rayyan akan kar ta ci komai na gidan kuma dai tana cin na Ammi, wani zuciyar yace ta gudarwa kanta matsalar Fulani Adama ta ci kawai ai Rayyan ba zai sani ba kuma ma kindirmon da aka kawo mata fari tas kwance a ƙwarya yayi matukar bata sha'awa don haka ta janyo ta dauki ludayi ta shiga sha, sai da ta sha dayawa ta ture tayi godiya kan ta miƙe ta bar sashen.
Yinin ranar suna tare da Rayyan yana sake nuna mata ita kaɗai ce tauraruwar zuciyarshi yana cika ta da kauna don ko girkin rana da dare ma ba ita tayi ba, bayan sun gama cin abincin dare tana kwance kanta akan kafafunshi suna ma kallon wani movie ne yana wasa da gashinta ya shiga jin hannunshi na jikewa musamman in ya kai ga goshinta, shafa goshinta yayi yana kiran sunanta ta amsa
"Lafiya kike zufa haka? Duk irin Ac dake aiki a parlorn nan?"
Tace
"Nima ban sani ba kawai dai cikina ke dan murda min kadan kadan ba sossai ba"
"Mp ne? Amma ai bakya ciwon cikin priod pain tashi mu gani ko mu tafi asibiti?"
Ta girgiza kai
"Ba wani sosai bane ba fa zai daina Yaya"
Ganin ta ƙi tashi ya sa ya kai hannunshi yana shafa mata cikin a hankali.
Mutsu mutsu ta fara duk ta kasa kwanciya wuri guda ita kaɗai ta san azabar da take ji wanda rashin son tada mishi hankali yasa take ta daurewa, yana kula da motsinta sai gani tayi ya ɗagata ya kai hannu ya kunna hasken parlorn tarrr, ganin idanunta ya tabbatar mishi da ba ciwon wasa take ji ba.
"Tashi mu tafi Asibiti"
Ya miƙe yana riƙo ta bata yi musu ba ta miƙe tsaye sai dai abin da taji yana bin kafan ta ne yasa tayi saurin kallon wurin shima ganin yadda ta razana sai ya kai idanunshi wurin.
"Jini??"
Yayi maganan a ɗan rikice kaman kuwa ana jira su gani cikin nata ya shiga kartar da bai yi ba da farko, damke hannunshi tayi tana jin azabar na shirin kasheta tuni ta fita hayyacinta a rikice ya ɗauketa suka fice daga parlorn da gudu Gaabɗo ya je ya buɗe mishi mota ganin yadda suka fito ko tukin ba zai iya ba yana rike da ita a baya yana shafa cikin yana mata sannu sai juye juye take tana zub da hawayen da bata san suna ma zuwa ba, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba jinin da bai san daga ina ba kuma na me na ta wanke su sai sannu yake maimaita mata kaman ya taya ta kukan a haka suka isa asibiti aka yi emergency da ita don har ta fara sumewa.
A masarauta kuwa Ammi na zaune da su Aisha aka kawo musu labarin dukkansu hankalinsu ya tashi suka miƙe tsaye suna tambayar
"Me ya sameta?"
Babu wanda ya san amsar sai kiran me martaba da Ammi tayi tuni ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 40