zama Mayya? Taya aka yi ta zama Mayya? Amsar da ta kasa ba kanta kenan har yau bata ma san Shigowar Aunty zainabu ba sai dafa ta da tayi ta ji, ta ɗago kai
"Aunty don Allah ki yi haƙuri ki mayar da ni gidan kawu zan cigaba da juriya ni karan kaina hankalina ba'a kwance yake ba, tsoro nake ji ina tsananin tsoron kar wani abu ya same ki ta dalilina ba zan iya yafe wa kaina ba..."
Kuka ne ya ci karfinta Auntyn ta share mata hawaye
"bawa baya taɓa wuce ƙaddarar shi Afeefah babu wanda ke da ran wani a hannunshi face ubangiji don Allah ki kwantar da hankalinki kin ji? Ba zan taɓa iya sake barinki ki zauna wurin 'yan uwan mahaifinki ba muddin ina numfashi. Tashi mu je"
Tashi tayi suka fice daga gidan suka je aka saka mata maganin ƙuna a wurin kan suka dawo.
Washegari suka sake fita dayake Aunty zainabu yar kasuwa ce tana saya da sayarwa sossai babu wanda bai santa ba a unguwar da ma unguwannin da suke maƙotaka tana saya kuma ta sayar, hatta kayan jikinta in zaki ce kina so ta kan iya cirewa ta sayar miki haka take bata zauna ba, shiyasa take da rufin asirinta a karan kanta makaranta suka je aka yi wa Afeefah interview da kyar aka barta a js2 duk da shekarunta sun wuce ajin, private ce da bai wuci dubu shidda ba termly don haka Aunty ta karbi sample na uniform suka tafi kasuwa ta yanka mata yadi aka ba tela akan zai ɗinka kan su gama sayayya, sayayya sossai ta yi mata da saida tayi ta zub da hawaye tana da sauran gata ashe bata sani ba soyayyar Aunty zainabu ya shige ta tamkar yadda zata so mahaifiyarta.
Da kaya sossai suka dawo niki niki, a ɗakin Aunty zainabu inda Afeefahn take suka ya da zango nan ta sake shirya mata kayanta dama ta cire nata masu ɗan dama suka tafi da su kasuwa aka rarrage mata yadda zai ƙarbe ta duk na gidan kawu zubarwa tayi.
Rayuwa ne mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ta shiga gudanarwa gidan Aunty zee da uncle usman, tun yana tsoro har ya sake barin ma da ya ga Afeefar yarinya ce mai kwazo, natsuwa da hankali ga ibada da son karatu boko da arabi komai na gidan yanzu ita ke yi don babu wani yawa bata bari Auntyn nata tayi komai muddin tana nan, haka a makaranta malamai sai yabawa kwazonta suke don tana da ilimi kuma akwai saka kai, suna ganin ma a karshen shekara za'a iya bari tayi Junior waec ta tafi ss1 in dai aka tafi a yadda take a yanzu, haka islamiyya tana kokari sossai kusan kowa ya san ta a unguwar saboda yadda Aunty zee ɗin ke nuna ta matsayin ɗiyarta.
Sauri sauri ta gama shiri don ta so makara ta fito goye da school bag ɗinta, fuskanta ya fito fess a cikin sky blue hijabin makarantar kyaunta ya sake bayyana na ainihin Black beauty, skin ɗinta har wani sheki yake na samun natsuwa, fararen idanunta take warawa ta inda za ta hango Aunty zee sai dai bata ganta ba, a parlorn ta tsaya ko zata fito daga ɗakin uncle usman ta samu ta mata sallama sai shi ta ga ya fito ta ɗan duka ta gaishe shi ya amsa cikin natsuwa
"Dama uncle ina son yin sallama da Auntina ne ko ta koma bacci?"
"Eh ai tun da ta fito ta ga kin kamalla komai tana komawa ta sake bingirewa da bacci"
Afeefah tayi murmushi
"Toh shikenan na wuce makaranta"
"karɓi"
Ta matsa ta karɓi ɗari biyu da yake miƙa mata
"Sai kin dawo a mayar da hankali"
Ta amsa tana ficewa da murmushi fal fuskarta kaman ba Afeefar da ba da take yawo da tsananin damuwa da hawaye a ko da yaushe.
Ko a makaranta natsuwarta bai kau ba, sam ba zaka ganta tana wasa ba koyaushe littafi na hannunta tana dubawa har ta fara presenting abubuwa a assembly da participating a wasu programs na makarantar, bata da ƙawa har yanzu don duk ajinsu ba sa'annin ta shirin exams ake don haka yau revision ƙarfe sha biyu suka tashi ta nufo gida cikin natsuwa.
Sai dai ta samu babu kowa, ta karɓi key a maƙota ta shiga sai da ta zare uniform ɗinta ta sauya da wasu kananun kaya wando ne da dogon riga da ya zo mata har gwiwa kan ta ɗaura dankwalin ta fita zuwa kicin, abinci ta ɗora musu tana mamakin inda Aunty zee ta tafi don bata ce mata za ta fita yau ba kuma kila wani abu ne dai ya taso a chan cikin dangi, ita dai ta san suna da dangin nesa nesa ta ɓangaren mahaifiyarta amma su ma ba wani karbarta suka yi ba ko daukar ta da muhimmanci Dukda ita kanta Aunty zee ɗin ba ta su take ba abinda ke gabanta ma ya fi karfinta.
Tana sauƙe faten doyar sai ga su sun shigo
"wannan kamshi haka me ake dafa mana ne Afeefah?"
Aunty zee ta leƙo kicin ɗin tana tambaya
Dariya Afeefah tayi
"Aunty faten doya ne fa, amma ya Naji muryarki kaman ta marasa lafiya?"
Tana zama a kujeran tsuguno ta janyo filet ta miƙawa Afeefahn, Afeefah ta karɓa ta shiga saka mata kan tace
"Eh Afeefah ban jin daaɗi ki taya ni murna kin kusa samun kanwa ko ƙani"
Wani irin zaro ido Afeefah tayi kan ta saki ihu tana rungume Aunty zee ɗin sai ta hau hawayen murna, zuciyarta tamkar takarda haka take jinta oh ashe Aunty zee na da rabon ganin 'ya'yanta a duniya?
Ita Aunty zee ture ta tayi tana share mata hawaye tace
"duk na murnar ne? Yanzu na gama share wa uncle ɗinki da ma ɗayar Auntyn taki da suka tasa ni gaba suna kukan farin ciki shine kema za ki fara? Oya ni sa min abinci in ci cikina kaman ana yasa"
Tana murmushi ta ƙarasa saka mata ta dauka mata zuwa gindin bishiyar dake ba da iska mai ni'ima, taburma ta shimfida mata kan ta ajiye mata abincin taje ta kawo mata ruwa tuni ta yi nisa a cin abincinta.
Dukda karatu da Afeefah ta saka a gaba saboda tana son fitowa da sakamako mai kyau a term ɗin don Aunty tayi alfahari da ita hakan bai hana ta jajirce wurin kulawa da Aunty zee ɗin ba, ko tsinke in ta ga zata ɗaga za ta karɓe duk abin da take so ko a hira tayi maganan Afeefah za ta yi kokari wurin ganin ta dafa mata shi tunda uncle usman bai Gaza da gidan ba ko ta wani ɓangare, kishiyar Aunty zee ɗin ta kan zo sossai tun samuwar cikin itama da ita ake haduwa ana ririta cikin Dukda Afeefah dai jininsu bai wani haɗu da matar ba tunda iyakarsu gaisuwa, ko hira Aunty zee ke yi da Afeefah in dai ta sa matar bata amsawa ita dai Afeefah bata damu ba tunda babu abin da ya haɗa su duk kuma a je a zo bata wuce awanni biyar zuwa goma a gidan so bata damu ba sam.
Kaman yadda ta ci buri ranar hutu sai ga Afeefah da position 3rd ta yi murna kwarai, haka ta dawo gidan da farin ciki. A tsaye ta samu Aunty zee tana tattare kayan da Afeefah ta wanke da safen don shigarwa ciki sai ji tayi an rukunkumeta
"Aunty ki taya ni murna"
Result ɗin ta miƙa mata
"Masha Allah, Alhamdulillah yarinyana kai ya fara ja Allah ubangiji ya sa ki fi haka ya dafa miki a dukkan lamuran ki, Allah ya nuna mana ranar da wannan karatu zai anfanemu ina fata za ki yi kokarin ci gaba da tafiya a haka next term mu ga First rubuce wannan wuri"
Kai ta gyaɗa tana ta dariya.
****
Aunty zee ce zaune tana ta aikin kallon Afeefah dake yi musu alele don yau da sha'awar shi ta tashi hakan ya sa tana furta wa Afeefah ta hau yi, tana aikin cike da tsafta tana kuma jefawa Aunty zee ɗin hira kaɗan kadan da ya shafi islamiyya da kuma boko da suka koma sati huɗu kenan.
A ranta take raya abubuwa dayawa game da Afeefah ɗin tana da matuƙar buri a kan rayuwar Afeefah yadda take very jovial bata fata nan gaba ko ma menene ya karya ta, tana adu'a yadda ta samu farin ciki ta dawwama a haka haske ya cigaba da bibiyar rayuwarta, bata san me gaba ya tanadar ba amma tana mafarkin ganin Afeefah a kololuwar matsayi cike da kwanciyar hankali, danne tunaninta da ya so juyewa ta yi tana cewa Afeefah
"Wai kuwa kin san kamanninki har ya ɓaci da Yaya Aisha?"
Afeefah ta ɗago ta kalleta yau ne karo na farko da maganar mahaifiyarta ya fito daga bakin Aunty zee ɗin
"Na zaci da babana nake kama don mutane kan ce ina kama da inno(kakarta da ta rasu)"
Miƙewa Aunty zee ta yi ta shiga ɗaki ta ɗan jima sossai kan ta fito da wasu hotuna hannunta, a lokacin Afeefah ta koma kan taburma ta zauna ta bar alelen ya dafu gefenta Aunty zee da cikinta har ya turo sossai ta zauna.
"Jini ne kawai tsakanin ki da inno amma kamanninki tsaff Yaya Aisha ne, kin ganta nan lokacin bikinta ne da babanki"
Karo na farko kenan da zata ga mahaifiyarta sai ta ji zuciyarta ya cika da rauni, hannunta na ɗan rawa ta sanya ta karɓa hotunan da ne Black and White matar da ta kasance mahaifiyarta da bata sani ba zaune sanye da zani da riga tare da Ali goggoro, hawayenta ne suka tsinke ganin yadda matar ta zauna tamkar ta kirata ta amsa, da gaske hatta yatsun hannu da na kafar ta irin na mamanta ne, baƙin fatarsu mai sheƙi, manyan fararen idanunsu, tsinin hancin su, karamin bakinsu da fararen hakwaransu hatta dimple guda ɗaya da maman nata ke dashi a gefen hagu itama tana da shi.
Raɗaɗin maraici ne ya mamaye zuciyarta, in ba mutuwa ta zama dole ba wa zai so maraici? Maraici ma irin nata marar gata da tushe? Maganganun mutane a kan iyayenta take tunawa sai taji kaman yanzu ne ake jefanta mugayen kalamai, tsintuwa da hantara a kan waenda duk duniya idan da za'a ce me take buƙata ayi mata ko da abu na ƙarshe ne za ta zaɓi su yi rayuwa na har abada amma ake mata Ƙazafin kashe su, anya zuciyarta za ta taɓa warkewa? Anya za ta iya yafewa masu alhakinta?
Ɗago raunannun idanunta tayi ta Kalli Aunty zee
"Aunty don Allah yaya maita yake? Ya ake yi? Yaya mutanen su ke? Kila baka sanin sadda kake yi in ba hakan ba ta ya zan zaɓi wannan rayuwa akan iyayena? Kila ko cikin fitan hayyacine ake yi ko? Menene ribar yin? Suna yin kuɗi ko Aunty? To me yasa ni ban yi ba? Yanzu wannan pure soul ɗin ni na kasheta ko?"
Duk ta rikice ta rasa me zata ce, kalaman suna zuwar mata ne kawai ba tare da ta san fitan su ba, kuka ne ya kufce mata, kukan da ke fita daga ƙasan zuciyarta na ciwo da raɗaɗi...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ku yi ta Adu'a mu ƙare a haka ina jin karsashin typing, ina jin daaɗin comments ɗin ku Allah ya bar ƙauna*
*005*
Hannunta ta riƙe cike da tarin tausayinta da kuma ƙaunar da take jin tana mata fiye da ƙima ta shiga cewa
"Na san ba ki kashe kowa ba Afeefah, ƙage ne kawai da Ƙazafi irin da jahilai daga cikin al'ummar mu, ƙarancin ilimi yayi yawa ta yadda mutane suke kasa yarda komai daga Allah ne, a ƙarƙarorin mu ne musamman wanda babu addini sossai za ki samu ko tuntuɓe bawa yayi sai an faɗi dalili da silar shi basu yarda cewa komai Allah ne yake yi ba.
Afeefah Kowacce rayuwa akwai ƙalubale ciki ke kuma ta ki kalar ƙalubalen kenan, amma fa na faɗa na sake kar ki saka hakan a ranki saboda babu mai kashewa da raya wa sai ubangiji, duk kuma wanda kika ga ya rasa ransa tabbas lokacin shi ya riga ya ƙare ne ko da sanadi ko babu dole babu maƙawa sai ya tafi, tsakanin ki da su Adu'a ne shine zai ba su tabbacin irin ƙaunar da kike musu. Afeefah mahaifiyarki ba za ta so ta ga kina zub da hawaye ko kin ƙuntatawa kan ki saboda ƙaddarar da ba ke kika ɗorawa kan ki ba, kaman kowace uwa ni ma zan baki shawara ki saka zuciyarki gaba, ki yi Adu'a ki kuma jajirce ki zama tamkar bishiyar gamji sara ko sassaƙa ba su isa su hana ki toho ba"
Jikin Aunty zee kawai ta faɗa tana shesheka da kyar ta lallasheta ta bar kukan kan ta ɗago
"Na miki alƙawari in shaa Allahu Aunty za ki yi alfahari da ni nan gaba, ba za ki taɓa kuka a kaina ba"
"Allah ya amince hajiya ta"
Dariya Afeefah ta saki jin ta kirata hajiyarta wadda babban burinta kenan ta zama shahararriyar 'yar kasuwa don tana so tayi kuɗi saboda wani dalili nata. Ƙaurin kamawar leda da suka ji ya sa ta tashi da gudu taje ta sauke tukunyar alelenta daga kan gano tana furta
"Aunty alele na so yayi mana buƙulu"
Aunty zee na dariya tace
"Hira ta yi daaɗi ba, duba ki ga Allah ya sa bata yi komai ba"
Sun ci sa'a bata yi komai ba sai na ƙasan guda biyu da ledar ya ƙone nan ta zuba musu tare da Auntyn ta zuba na uncle a kula suka zauna suka ci tare suna hirar su gwanin sha'awa bayan sun gama ita ta yi wanke wanke, ko da ta dawo kan taburman hoton Aunty zee ta bata
"Gashi na bar miki, ki ajiye a wurinki"
Murmushi ta saki kan ta karɓa tana godiya.
Wasa wasa cikin Aunty zee ya shiga watan haihuwa, ta ɓangaren Afeefah tana nan tana ƙoƙarin karatu ka'in da na'in don 2nd term da suka koma ita ta ɗauki na ɗaya kuma 3rd term nan suna ƙare ta tare da ita za'a zana Junior waec ta tafi ss1, a yanzu hatta turanci ya zauna a bakinta ba kaman baya ba da bata wani jin komai, duk wani sayayyar haihuwa tare suke zuwa saboda a hankali ciki ya sa Aunty zee ɗin ta shigar da Afeefah cikin business ɗin ta, wani lokacin ta kan aike ta ita kaɗai ma kasuwa wurin customers ɗinta kuma ta zo ta raba wa clients ɗinta kayan, asusu Aunty zee ta yi mata ta kan ware ladar ta na kasuwanci ta saka mata ciki duk da Afeefah ta nuna ita bata so, tufafi, karatu da kuma cima sau uku da ake bata ya wadatar da ita. Amma Aunty zee ta nuna hakan shine adalci kuma ko nan gaba zata iya anfani da kayanta idan buƙatar hakan ta taso.
A yau Aunty zee take cika wata tara da kwana tara kuma a ranar ta kwana da labour mai zafi, hankali tashe da asuba suka tarkata asibiti har da kishiyarta da ta zo ta kwanan musu kasancewar tun da abin ya fara mijin ya ƙirata, ta fi kowa shiga damuwa an ƙarbe ta zuwa ɗakin haihuwa sai jiran abin da hali zai yi, duk Afeefah ta fi ruɗewa babu abin da take tunawa vividly sai irin wahalar nakudar da innarta tayi ƙarshe daga ita har babyn suka koma wannan abu ba zata taɓa mantawa ba, duk kuma ta ga mai ciki sai hantar cikinta ya kaɗa a yanzu Allah kaɗai ya san halin da take ciki na tsoro da fargaba duk adu'ar da ta zo Bakinta ita take yi.
Sai Azahar Allah ya taimakesu midwifes ɗin da suka karɓi haihuwar suka fito suna musu albishir na ta samu 'yan biyu mace da namiji faɗin kalar murnar da suka yi ɓata baki ne. Karo na barkatai kenan da Afeefah ta ke kai idanunta kan yaran hakwaranta duk waje, yaran gwanin sha'awa kaman ta Haɗiye su, sam bata san Aunty zee ta farka ba sai ji ta yi tana furta
"Suna ba ki sha'awa ko Afeefah?"
Da sauri ta juyo tana dariya
"Sossai ma Aunty zee, sannu kin farka? Ya jikin?"
Ta ɗan saki murmushi.
"Masha Allah, jiki Alhamdulillah"
Ta furta hawaye na gangaro mata Dukda tana sauƙa sai da ta ji ɗuminsu kan wannan wahalallen baccin ya yi awon gaba da ita amma yanzu da ta farka sai take ganin kaman mafarki, kaman ba'a gaske ba ita ce yau da shekaru arba'in da biyu a duniya kan Allah ya nufe ta da ganin ƙwanta? Har biyu kyautar Allah? Bata san wani irin godiya za ta yiwa mahallicinta ba don ko yau ta faɗi ta mutu ta san ta bar bayan da za su iya tunawa da ita su yi mata Adu'a, bata san daaɗin haihuwar ya kai har haka ba a ganinsu da take kawai ji take kaman ta rabu da baƙin ciki har abada matukar suna kusa da ita.
A hankali Afeefah take kokarin ɗaukar su ta kaiwa uwar, daidai shigowan kishiyar Auntyn
"A'a Afeefah me haka? Sabbin haihuwan kike ɗaga su anyhow? Wa kika tambaya da za ki ɗaga su?"
Yadda take maganan zaka zata wani gagarumin abu Afeefar ta aikata don har ta tsorata, da ta kurawa matar idanu sai ta fahimci kaman akwai dalilin maganar nata amma bata wani mai da hankali ba don Aunty zee ta amsa mata
"A'a hamdiyya ai Afeefah ba yarinya ba ce da zata kada yaran baki san ko yanzu ta yi aure zata iya haihuwa ba? Getting to 18yrs ba wasa ba"
"kin ga Aunty sabbin haihuwa ne kuma ji da abin mu muke ko kuda bama so ya taɓa su bare wasu da idonsu idon sabon jini su ke Sha'awa"
Da sauri Afeefah ta mayar da idanunta kan matar, Aunty zee ma ta ɗago ta kalleta
"Me kike nufi Hamdiyya?"
"Gaskiya nake faɗa Aunty, hanyar lafiya sai a bi ta da shekara ba za mu so farin cikinmu ya koma baƙin ciki ba"
Hawaye ne ke kokarin zubowa Afeefah da jikinta yayi wani irin sanyi, bata ankara ba sai ji ta yi Aunty zee ta ɗora mata yaran duk biyu a kan kafafunta
"Afeefah ga su nan ƙannenki ne, ki riƙe su yadda kike so"
Juyawa ta yi ga hamdiyya
"A kan Afeefah za mu iya samun matsala da ke, ba zan taɓa zuba ido ki tozarta ɗiyata a gabana ba, kin ga yau na haife su ko? Kuma na san daaɗin su ko? To wallahi zan iya zaɓar Afeefah sau dubu kan in zaɓe su sau ɗaya. Ki kiyaye kan mu yi uwar watsi da ke a kan 'yata"
"Aunty ni kike yi wa gori a kan wannan mayyar?"
Ko kan Aunty zee ta yi magana Uncle ya shigo, kafin ya tambayi me ya faru Hamdiyya ta fashe da kuka mai ƙarfi tana yunƙurin fita, da sauri uncle ya tare ta don shi mutum ne da baya son abin da zai kawo mishi matsala da iyalanshi, yayi kokari ƙwarai wurin haɗe kawunansu ba zai so ko ma menene ya raba su ba, ban da ma yanzu da suka soma tara zuri'a suke kuma cikin farin ciki tsantsa.
"Me ya faru hamdiyya? Zainab me ya haɗa ku?"
Aunty zee dai komawa ta yi ta zauna sai hamdiyya ce ta kara karfin kukanta
"Ka yi haƙuri ni ce da laifi na zaci da ni da Aunty duk ɗaya mu ke kuma 'ya'yanta za su iya zama nawa amma ashe na yi kuskure, in shaa Allah ba zan sake ba"
"Zainab!"
Uncle ya furta sunan cikin rashin jin daaɗi
"Gori kika yi mata?"
"Amma dai ka fi kowa sanin hali na Usman, ban yi mata gori ba kuma ba zan taɓa yi mata ba don nima babu wayo na bare dabara ta Allah ya ba ni, abin da take shirin shigowa da shi ne ba zan lamunta ba sam"
Hannunshi dake cikin nata hamdiyya ta janye
"jita-jita bai taɓa wanzuwa ba matukar babu kamshin gaskiya, an sha tare ni ana gargadina a kan Afeefah amma na ɗauke kai saboda ganin yadda Aunty zee ke ƙaunarta, abin da nake tsoro an ce suna kaunar sababbin jini to don na ce Afeefar ta yi haƙuri da daukar su har su yi kwari shikenan na yi laifi...? Ku yi haƙuri bari na je gida"
Tana kai nan ta fice uncle bai ce komai ba don shima karo na ba adadi an tare shi an faɗa mishi abubuwa dayawa kan Afeefah amma baya bari ya shige shi, sai dai kuma bai ji daaɗin reaction na zainab ba da sai a bi abin a hankali tunda dai already akwai maganganu kan Afeefar.
"Amma ba ki kyauta ba zainab, na sani kina kaunar Afeefah kasancewar ta marainiya kuma abin tausayi amma kuma sai ki duba kokarin hamdiyya wurin ganin ta bai wa jininki kariya, tun fa jiya tana tare da ke ko runtsawa bata yi ba, ko da kika sauka kika fara bacci haka ta koma gida ta dafo miki ruwan zafi ta biya ta sayo kayan tea saboda kar ki tashi da yunwa babu abunda zai taimaka miki, ai gyara kayanka baya zama sauƙe mu raba"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Idanunta ta mayar kan Afeefah dake hawaye sossai, rabon da taji raɗaɗin zuciya tun ranar da uncle ya amince ta zauna da su sai yau.
Yanzu ko da tana cin naman mutum wani bala'in ne da rashin tausayi haɗe da rashin imani zai sa ta ci naman waennan talikan da isowarsu duniya kenan? Me zai sa ta cutar da 'ya'yan wacce ta rungumeta ta cicciɓota ta zaro ta daga cikin bala'i da ƙuncin rayuwa?
"Afeefah..."
Auntyn ta ƙira sunanta a hankali sai kuma ta kasa magana duk suka yi shiru tsawon lokaci kan nurses suka shigo, hakan ya tilastawa Afeefah barin ɗakin kai tsaye fita tayi daga asibiti ta tsare abin hawa ta faɗa mishi inda za ta, gidan Hamdiyya ta nufa don ta tabbatar a chan za ta samu Uncle usman da ma ita karan kanta hamdiyyar.
Hasashenta ya tabbata don kuwa ta same shi tare da hamdiyyar yana ta kokarin bata baki tana tuburewa, maganganu take gayamishi cikin ɗaci da nuna kaman shi ne ai ya zaɓi ya ba Zainabun ciki har ta haifi 'yan biyu tana mata gori.
"Haba hamdiyya kema kin san da mutum shi ke ba kanshi haihuwa da yanzu mun tara yaran da bakya zato saboda Zainab macece mai kaunar yara, tun aurenmu na shekara duk inda taji magani muddin bai saba shari'a ba nema take amma da Allah bai turo ba ba gashi yanzu ta haihun ba? Ba'a cire rai daga rahamar ubangiji kema kuma ya san dalilin da ya jinkirta naki namu Adu'a ne kawai da neman zabin alkhairi daga rabbissamawati".
"A'a Usman ai ka fi ƙaunar Zainabun idan da Zainabun ta haihu tun farkon aurenku da baka auro ni ba, silar rashin haihuwar ne ta saka ka kara aure ba don kana so na ba kuma ta haihun ai..."
sallamar ta ya katse musu maganar duk suka mayar da hankali kanta.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*006*
"Uncle, Aunty hamdiyya don Allah ku yi haƙuri, ban zo da niyyar wargaza zaman ku ba, na sani Auntyna ta faɗa miki magana ne saboda irin ƙaunar da take mini amma ni na san gaskiya kika faɗa, don Allah ki koma asibitin ki cigaba da kula da ita da jariran ni zan koma gida zan cigaba da jira har lokacin da ya kamata a ce na ɗauke su ɗin"
Cikin wani kalar sanyin murya take maganan, idanunta har lokacin ba su daina zubar da hawaye ba. Uncle ɗin tausayinta ya ji yayinda hamdiyya ta taɓe baki ta ce
"Toh ai shikenan, ni ba na yi magana ba ne da wata manufa kawai dai ina kare yaran da yanzu ne muka fara morewa wanzuwar su ba za mu juri dare ɗaya a yi abincin meeting da su ba"
Uncle ne ya katse ta
"ya isa haka, ki tashi ki koma asibitin. Afeefah tashi mu je in sauƙe ki a babur na"
Miƙewa ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 40