Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. Bayan nan ina yi mana Sallama irin ta addinin musulunci shi ne Assalamu Alaikum warahmatullah" Duk suka amsa, ta ɗan sauke numfashi "Ba gixo ba kuma ba mafarki ba haƙiƙa ni din ce Afeefah kamal wacce kuka fi sani da Annoba ko kuma Mayya a wannan gari, haƙiƙa na jure abubuwa dayawa daga gare ku 'yan uwana, yayyena, Ƙannene na da kuma iyayena. A baya na zama mujiya cikin tsuntsaye Abar kyamata da gudu. Abar tozarta wa da wulaƙanta wa, Abar muzantawa a cikin al'umma saɓanin a yanzu da nake da miji nagartacce nake kuma da surakan girma waenda suka taka rawar gani bisa inganta rayuwata daga Wacce ta sallamar da farin ciki ta sallamar da jin daaɗi zuwa wacce ta zama mai cike da buri da alfahari. Da na zauna nayi nazari da tunanin Meyasa nawa iyalan kuma dangina suka yi min abinda suka yi a baya sai na fahimci babu wani abunda ke damun ahalin wannan gari na mu sai rashin ilimi da sanin daidai. Na fahimci mun samu tawaya da koma baya a wannan ɓangaren iyayen babu bare su tarbiyatar da yara akan daidai, a sadda na sake zurfafa tunanin me zan yi na taimaki al'ummata sai na ga babu abinda ya fi dacewa irin in wayar mana da kai in taka rawa wurin ganin mun samu ilimi har ma muna aiki dashi, in ga cewa wata mace ko wani yaro bai ɗanɗani irin ɗacin da na ɗanɗana ba, in ga cewa yadda rayuwata ta inganta kowa ma a yankina rayuwarshi ta inganta gobenmu mu samu tsatson da za mu yi alfahari da su daga wannan gari namu. Ya ku 'yan uwana musulmai ku sani cewa addinin musulunci addini ne na ilimi. Umarni da neman ilimi shi ne farkon abin da Allah Maɗaukakin Sarki ya umarci Annabinsa (S.A.W) da shi, yayin da ya saukar masa da faɗinsa : اقْرَاْ بِاسْمٍ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ! خَلَقَ الْإِنْسَانَ مِنْ) عَلَقٍ 2 اقْرَاْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ 3 الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ 4 عَلَمَ .[العلق: ٥ - ١] (الْإِنْسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ 5 Ma'ana : (Ka yi karatu da sunan Ubangijinka da ya yi halitta. Wanda ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu kuma Ubangijinka shi ne mafi karamci. Wanda ya sanar da alqalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba). (Alaq : 1 - 5) Addinin musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa akan neman ilimi, domin ba zai yiwu mutum ya bauta wa Allah ba sai da ilimi. Allah madaukakin Sarki yana cewa : فاطر:] (إِنَّمَا يَخْشَى اللَّ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ28) TA]. Ma'ana : (Kaɗai waɗanda suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa su ne masu ilimi) Idan na ce zan kawo muku faɗar Allah da kuma hadisan da suka yi magana akan ilimi da amfaninsa gare mu za mu kwana bamu ƙare ba amma tabbas da akwai ilimi da duk ban fuskanci abinda ya faru da ni a wannan kauyen namu ba, Ajalin mahaifina ya same shi ba tare da na zo duniya ba, mahaifiyata ta rasu bisa rashin kula da rashin zuwa asibiti a yayin daukar ciki zuwa haihuwan gida, kakata shekarun ta ya ja ƙwarai wacce dole a yi mata tsammanin mutuwa a sadda ta tafi haka Goggona ta tafi bisa sakaci da zaman jahilci da dabbanci da ake yi a cikin gidanta, bamu san kan mu ba bare mu nemi sanin hakkoƙin da suka rataya mana, hakkoƙin matayenmu, hakkoƙin iyayenmu bare hakkoƙin 'ya'yayenmu wanda duka sai ta hanyar ilimi za mu sani, na koma wurin Aunty zainabu ta gamu da postpertum wanda ciwo ne da ake samun shi bayan haihuwa duba da bata taɓa ba ga yawan shekaru babu wanda ya fahimci hakan sai da lokaci ya ƙure ta tafi duk ba mu dubi ajalin su ne yayi ba, mun manta Allah ya ce ba zai taɓa jinkirta ajalin dayanmu ba idan ya zo dole za mu tafi. ku sani na yafewa kowannenku da wanda yayi min na sani da wanda ban sani ba duk na yafe muku, a wannan gidauniya tawa tafiyar duk na neman ilimi ne da kuma tsayuwa akan kafafunmu don Allah ina roƙon mazaje da ku bar matayenku da ma ku karan kanku ku nemi ilimi don Allah ba ya ƙarbar uzurin bawa akan rashin sani saboda ya mana umurnin nema. Akwai ma'aikata da za su koyar da sana'o'i ga yara da matayenku su ma ku bar su don zai amfani wannan al'umma tamu, duk lokacin yaye ɗalibai idan yayi zan zo kuma idan Allah ya amince za mu dinga raba kyaututtuka da suka shafi sana'ar da mutum ya koya don ya cigaba daga inda ya tsaya ina Fatan ganin chanji daga gare mu bakidaya na gode" Wasu hawaye suke yi suna tuna abinda suka mata amma dayake tana da zuciya mai kyau dubi Alkhairin da ta nufe su dashi, kawu ta miƙawa mic ɗin don ya taso yana son yin magana, a gaban tarin al'ummar yana kuka ya ba da duk labarin abinda yayi mata da wanda aka mishi ta sanadiyar son zuciyarshi da yadda ilimi ya sauya shi daga mummuna zuwa kyakyawa har ya kara da "An karɓo daga Kasir ɗan Qaisi ya ce, ina zaune tare da Abud Darda'i a masallacin Dimashqa, sai wani mutum ya zo wajensa ya ce masa, Ya Abud Darda' i na zo wajenka ne daga Madinar Manzon Allah (S.A. W) saboda wani hadisi da aka ce min kana faɗa daga Manzon Allah (S.A. W), kuma babu wata buqata da ta kawo ni nan sai wannan. (wato jin wannan hadisin) Sai Abud Dar' da'i ya ce, "Na ji Manzon Allah (S.A. W) yana cewa : "Duk wanda ya bi wata hanya yana neman ilimi a cikinta, to Allah zai sanya shi akan hanya daga cikin hanyoyin Aljannah, kuma haqiqa Mala'iku suna sanya fika - fikansu ga ɗaliban ilimi, don yarda da abin da yake nema, sannan duk wanda yake sama da qasa yana nema wa malami gafara, har ma da kifayen da suke cikin ruwa. Falalar malami a kan mai bauta kamar falalar wata ne a daren goma sha hudu a kan sauran taurari, kuma haqiqa malamai magada Annabawa ne, Annabawa kuwa ba su bar gadon dinari ko dirhami ba, kaɗai sun bar gadon ilimi ne don haka don Allah kar mu raja'a akan boko don shi iya na duniya ne mu nemi lahira kuma mu koyar komin kankartarsa, ko uwa malama ce akan yayanta kar mu saka finafinai ko waƙa gaba mu ta rawa da nishadi da yara mu koya musu abinda zai amfanesu a gaba. Ni a karan kaina misali ne kuma Aya ne ubangiji ya nuna min akan Afeefah" Duk jikin mutanen wurin yayi sanyi kuma sun gamsu ɗari bisa ɗari da lallai suna da nakasu ta wannan fannin dole rayuwarsu ya tafi a jiɓance, Afeefah da manyan gari a gefenta mijinta ne da ya bata support ɗari bisa dari suka zaga wurin tassss ta yabi kyau da tsarin komai na wurin kuma duk abin bukata akwai. Kawu ta damƙawa wurin ta ce ta bashi amana ya riƙe mata ya kula da komai yadda ya kamata bisa tsari shi dai babu bakin magana don ya rasa me zai ce. Cikin jami'an tsaro masu kula da taron kawai idanunta ya sauƙa kanshi, da sauri ta nufe shi tana kallonshi shima ita yake kallo a hankali ta nuna shi "Sa'adu? Sa'adu Rabi'u kai ne?" Kai ya gyaɗa yana murmushi ya gane ta amma bai zaci zata nuna ta sanshi ba ta juya ta kalli Rayyan ya matso "Ka tuna shi Ya Saraki?" "Wannan police da ya ceceki daga sharrin gurbatattun 'yan uwansa" Za Ta cire zobenta na gwal ya miƙa hannu ya riƙe nata, ya zari kati daga aljihunshi ya miƙa mishi "Ka ƙira ni in shaa Allah kyautarka ya fi karfin kuɗi za'a mayar da kai cikin Kaduna da matsayi mai kyau" Hawayen murna ya fara yana godiya. Ko da aka watse taron suka koma gidan Kawu akan za'a saka date na fara daukar ɗaliban da suka kamata za kuma ta turo waenda za su taimaka mishi wurin fahimtar komai da komai kan a sakar mishi, a tsakar gidan suka samu an jibge kayan abinci babu abinda babu wanda za su iya ma watanni goma zuwa ashirin basu nemi kayan abinci ba, a gefe crouches ne da wheelchair na inna Larai Afeefah tayi saurin kallon Rayyan ya girgiza mata kai yana dan ɗage kafada sai ya juya ya fice ta bi bayanshi Za tayi magana jiri ya ɗan dibeta da sauri ya riƙo ta "Boɗɗi menene? Ba kin ga illar kukan da kika dinga yi ba duk yau kin tarawa kanki damuwa! Kan na ciwo ne?" Ya kai tafin hannunshi yana dafe goshinta hawayen ta sake farawa "Ban san da wani baki zan fara maka godiya ba Ya Saraki... Ko baka faɗa ba na san aikinka ne Allah ya biya ka ya saka maka da alkhairi ka yi min komai Ya Sa..." Hannunshi ya sa ya rufe mata baki yana dan ɗauke hawayen da take zubarwa yace "Kin chanchanci fiye da haka a gareni Afeefah don haka ba komai ba ne, na so ko gidan haya ne mu kama a gyara wannan amma bai samu ba idan ba damuwa za su dan koma Kaduna ko ma su je ganin ɗakin ki a Fombina kan su dawo sai a gyare nan ɗin" Rungume shi kawai tayi ya sa hannu yana dan shafa bayanta kan ta ɗago sai ta sake jin jirin yamutsa fuska tayi, ya shiga mota don bai kula ba itama ta zaci ma stress ne don haka ta koma ta musu bayanin za su je Fombina ko sati biyu su yi za'a ɗan gyare nan ɗin kuka kam kawu har ya rasa hawaye ya rasa bakin godiya a haka suka ɗauki duk abinda za su ɗauka aka adana kayan abincinsu a daki guda suka ɗauki duk wani abu mai muhimmanci, yaranshi maza manyan uku da mata shidda na Inna Asabe uku na Inna Larai biyar suka bar garin zuwa Kaduna. Kai tsaye gidan Mammi suka yi masauki jannah ta turo abinci ko da Abeeha ta gaya mata da baƙi suke ta turo daga restuarant, a masaukin baki aka sauke su suna ta mamaki da santin gidan, Ita dai Afeefah su Suhaila ta ja zuwa ɗakinta ta musu wanka ta duba cikin tsarabarsu da ta musu na musamman ta fidda kaya ta saka musu suka haɗe babban parlor aka ci aka sha kan kowa ya nemi makwanci don sun gaji, sai da ta tabbatar sun yi bacci ta watsa ruwa ta shirya cikin wani Red kayan bacci da yayi mata kyau sossai marabarshi da babu kaɗan ne ta nufi ɗakinshi... Yana jingine da gado yana jiranta suna haɗa ido suka Sakarwa juna murmushi mai ƙayatarwa, yanga tayi ta mishi Dukda kunya dake ɗawainiya da ita barin killer looks da yake binta da su har ta iso gadon ya fusgo hannunta ya manna ta kirjinshi yana matse ta a lokaci ɗaya suna sauƙe ajiyar zuciya a tare A kunnenta ya raɗa mata "Kina kashe ni da raina Gimbiyata" Ta ɗan ɗago bai tsammata ba ta haɗe lips ɗinsu kaman jira kuwa ya mirginata kasanshi ya mata rumfa yana bata wasu kisses da suka sake matar da ita a kaunarshi hannunta na yawo bisa bayanshi zuwa keyarshi tana mishi susa, gasping air yayi ya raba lips ɗin suka yi murmushi mai sauti ya sake mayar da lips ɗin yayi mata kyakyawar Kiss Ta raba fuskansu tana shafa kanshi hancinsu haɗe da juna suna musayar numfashi ta ce "Na gode sossai Na gode kwarai haƙiƙa Allah ya wanke min zuciya ya ba ni mijin marainiya, ya ba ni kai ba tare da wayo ko dabara ta ba a koyaushe ba ni da abin faɗa a gareshi sai Alhamdulillah. Ina roƙon Allah akan duk ranar da za ka haɗu da shi, Fuskarka ya zama mai annuri da sheki fiye da yadda yake a yanzu, ya rabautaka da karɓar kyawawan sakamakonka a cikin tafin hannunka na dama sannan ya ce "I am pleased with you" ya haɗa mu gabaɗaya a aljannah madaukakiya ya ba ni dama da ikon Zama shubagar matayenka a aljannah. Ina ƙaunarka Ya Sameer...Ina ƙaunarka Ya Rayyan ina matukar sonka Ya Saraki" Hawayen dake zuba mata yake bi a hankali da harshen shi yana ɗaukewa cikin wani salo zuciyarshi ƙal yayi fixing gaze ɗin shi cikin idanunta "I love you. love you more than anything Afeefah, ban taɓa jin son wani abu yadda nake jin naki ba, I love you more than myself. I will always love you. I will love you till the end of my time. No words can express how much love i have for you. I will alwavs be here for you no matter what kin ji? Babu abinda zan miki da zan ji yayi yawa you are my favorite girl nd my only blessing" Daga nan ta dafa chest dinshi sai ya koma kwance ta dane jikinshi da kanta ta shiga gigitashi abinda bata taɓa sakewa tayi ba ta yi shi a ranar ta goge mishi hadda sai gashi yau ma yana yi mata kuka don ta gama da rayuwarshi in dai ta fannin ne. Washegari sun tashi da mummunan labari don Uncle Usman ya rasu labarin ya kaɗa ta don faɗuwarta kawai suka ji hankalinsu ba karamin tashi yayi ba barin ma Rayyan a hannunshi ya ɗauketa suka tafi asibiti don duk abinda za su yi sun yi matsayin shi na likita ya kasa farkar da ita yana jin panic akan ciwon Mammi amma bai san Meyasa duk abinda ya shafi Afeefah na fitar da ragwantakanshi a fili ba, tsoro da fargaba ya sa ya manta yadda ma ake aikin likitacin sai a asibitin ne aka samu ta farfado nan suke samun labarin tana da shigar ciki kuma razanar da tayi har ya fara barazana ga ɗan cikin nan ya saka aka yi mata allurar bacci don ta huta sossai. 'Yan uwanshi sun yi rawan gani da su Sulaiman aka sallaci uncle Usman aka kai shi makwancinshi dogon takarda da ya roki sulaiman rubuta mishi ya ba Rayyan akan idan ta dawo daidai sai a bata. Kwanan ta biyu kan ta dawo cikin hayyacinta tayiwa su Suhail kuka ba na wasa ba don maraici babu daaɗi ta kuma yi alkawarin rike su fiye da ƴaƴan cikinta har illa masha Allah. A kwana na huɗun suka juya Fombina, anan ne Kawu suka san basu ga komai ba baki sake suke bin irin girma, tsaruwa da ma kyaun masarautar irin mulkin da ake shimfidawa ko a mafarki basu taɓa mafarkin halartar irin wannan wuri ba sai gashi wacce suka raina ta zama sanadiyar da ake zube musu, sun yi kuka kaman me don sashe na musamman aka sauke su mai martaba da Ammi suka tura ake musu hidima wane wasu masu kuɗi. Ammi da mai martaba kaman su hadiye Afeefah jin labarin cikinta, soyayyar mijinta kuwa ya ninku fiye da yadda yake jinta a da su Suhail sun zama 'yan gata don a take aka tsara musu dakunansu Mai martaba ya sa aka cike musu wardrobes da kaya Ammi ma ba'a barta a baya ba don abinda za ta yiwa jikokinta shi take musu har ma sun Fara ƙiran Afeefah da Ammah Ryan kuma Abbu, school na musamman ya saka su masu musu hidima ma daban aka ware don Afeefah laulayi mai wahalarwa take. Satin su Kawu uku suka koma bayan Rayyan ya saya mishi babban waya an hada su da goma sha tara na arziki suka koma, gidan su ya zama daga cikin gidajen da suka fi kowanne kyau a garin ɗan daidai kuma a kayace sai ya tuna akurkin da suka warewa Afeefah take rayuwa lallai Allah ya nuna musu ikonshi sun tuba har sun rasa bakin tuba, a kuma satin da suka koma aka fara gudanar da aikin gidauniyarta. Sai ga kujerar Umura da Rayyan ya biya musu har da su Mai martaba za su tafi da su Abeeha, sun yi murna barin Afeefah da bata taɓa zuwa ba za dai tayi kewan yaranta cikinta na wata huɗu suna gama second semester exams suka chale ƙasa mai tsarki ranar da ta fara ganin ka'aba tayi kukan da sai da tayi zazzabi bata taɓa ganin abu me kyau da natsuwa ba irin shi duk rayuwarta, ta zube wurin ta yiwa iyayenta da yan uwanta da ta rasa Adu'a har sai da miyaun Bakinta ya kafe, sun yi sati uku chan sayayyan baby kuwa kowa yi yake ba Ryan ba ba Ammi ba ba su jannah ba, daga Saudi sun tsaya kaɗan a Turkey sun yi sayan kayan ɗakin su Aisha ana dawowa Nigeria Aka fara hidimar bikin su. 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* *Wannan shafin naki ne Uwar Ɗakin Damisa namu angon Nyla Ƙani ga Didi kuma Uban Didi. Nana Halima ko na ce Leemar's delicious mai abincin 'yan gayu...Allah ubangiji ya ƙara miki basira da hazaƙa ina godiya ƙwarai🥰* *FINAL PAGE* *60* Zaune suke a cikin ƙayataccen hall ɗin da ake shan hidimar bikin Autan Mammi da Autar Ammi waenda duk yanzu suka zama shalelen Ammi kuma angwayen ma duka 'ya'yanta, Ryan na zaune bisa wani table riƙe da hannun Afeefah sun yi azabbaben kyau cikin outfit ɗinsu na Soire party wanda english party ne duk mazan shigar suite suka yi matan english dress, Farin suite ne jikinshi da baƙin shirt daga ciki bakin takalmi da baƙin hankey da ya ɗan leƙa bakinshi daga aljihun, gashin shi ya sha gyara ainun fuskarshi sheki yake kowa ya ganshi ya ga cikakken namijin da yake cikin kwanciyar hankali da jin dadi. Tana sanye da wani doguwar riga na tsadadden sugar lace da ya bayyana cikinta da ya taso yayi mata kyau ainun, ta saka gyale da ya tafi da kayan tayi wrapping kanta ta sha make up da ya matuƙar zama mata wanda mijin nata ke ta bacin rai akanshi don kishi ya sa ko motsi tunda suka zauna basu yi ba su Saleem sun ta kiranshi ya ƙi zuwa sai Sulaiman ne yake representing ɗin shi, gabansu Suhail da Suhaila ne shigan ryan shine irin na Suhail haka Suhaila ma irin na Afeefah sai suka ba da wani kyau mai ma'ana. Zarah ce da yanzu ta sake saboda janta da su Abeeha ke yi a jiki kuma tayi tuban gaskiya ta zo ta ja su Suhaila don tana kaunarsu su ma kuma sun sonta, Afeefah ta kalli Ryan "Ya Saraki..!" A Shagwaɓe tayi maganan ya kalleta "Matar Masu Sarauta ya aka yi?" Yayi maganan yana ɗage mata gira tace "Eyyaa dubi ana yi wa Adda Abeeha barin kudi in je in manna kaɗan mu yi hoto?" "Wanda kuka yi kan ku zo nan ya isa ba za ki shiga cikin maza ba" Ta ɗan ɓata rai har ma nadamar Kwalliyar take ji yadda ya kasa ya tsare dama bikin duk ya hanata wani hidima yadda ta so cin uwar sabada sai dai ta ga su Samha na yi don duk Fombina suka zo har Sadiqa da ake hidimar aurensu tare sun zabi su zo nan in za'a ɗaura aurenta sai ta koma tunda sai an ɗaura na Saleem an kai mishi matarshi zai ba da nata. Har su kawu sun zo bikin da Inna Asabe sun bar inna Larai a gida, kawu ya sauya ƙwarai natsuwa ta shige shi haka Inna Asabe da inna Larai babu wannan rawan kan da son zuciyar sam sam sam. A bikin ne ma take samun labarin Sabrina da iyayenta inda ta kwaso HIV da ya kasa warkewa ga talauci da yayi musu katutu ita Gaje garin zuwa boka nema mata waraka ta faɗo daga tsauni sai gawa aka ɗauka Yaya ne ya zo neman tuba wurin mommy kuma ta yafe musu. "Assalamu Alaikum warahmatullah" Wata ƙawar Aisha ce ta yi musu sallama, Afeefah ta kalleta da mamaki don ta kula yarinyar na ji da uban ta wani ne tun fara bikin sai rawar kai take bata zaci Rayyan zai wani kula ta ba sai ta ji ya amsa, a take wani abu ya taso mata zuwa wuya wato ita ce bata da kishi shi ya hanata tashi saboda maza ita kuma tana kallonshi yana magana da wata macen. "Yayanmu barka dai, mun jima muna kallon irin kokarin ka akan rayuwar matasanmu a koyaushe His Excerllency ba shi da zance sai taka gaskiya samun shugaba irinka abin alfahari ne in kuwa da irin ku rayuwar matasanmu ba zai taɓarɓare ba" Ya san mahaifinta Gomna ne mai ci a yanzu don haka yana martaba gidansu sai ya ɗan murmusa "Thank you" "idan ba damuwa ga wannan na jima ina so na baka ban samu ganinka ba Its a small gift don Allah kar ka ce a'a" Ta ajiye wani karamin paper bag tayi murmushi ta juya ta wuce. Kaman an ce ya kalli Afeefah ta haɗa gabas da yamma kudu da arewa, idanunta har shekin kwalla su ke, hannunshi dake cikin nata ya ɗan murza don ta kalleshi amma ta ɗauke kai sai ma ta miƙe chadak ta nufi waje, da sauri ya bi bayanta yana dan kiranta amma bata waiga ba dab wurin mota ya riƙo damtsen hannunta a hankali ya janyota bayanta ya sauƙa kan kirjinshi yana dan lekan fuskanta yace "Tsaya mana Boɗɗi fushi kika yi?" Fuskarta babu walwala ta janye tare da Juyowa ta kalleshi "No, Meyasa zan yi fushi?" "Me yasa kika fito to ina ta magana kin ki kulani?" Ta kalleshi "Gashi na kula ka, ina jinka" Numfashi ya sauke "It seems kin gaji mu tafi gida" Ta juya ta nufi motarshi bata ce komai ba, numfashi ya sauke yana ɗan shafa gira ya nufi motar tuni ta buɗe ta zauna ya shiga shima drivern shi ya ja suka nufi ɓangaren su tunda akwai tafiya sossai, hannunta ya riƙe ta zame tare da juyawa tana kallon Window. "Akwai abinda ya faru ne? Ko na miki ba daidai bane?" "Babu, me kuwa zai faru?" "Ta ya zan sani Afeefah na ga kina fushi" Ta ɗan bashi side eye tana sake juyawa "Ni ba fushi nake ba" Lip dinshi na kasa ya ɗan lasa har ga Allah bai zaci wai kishi take ba a hankali yace "Ok" Ya kalleta sai ya ga ta sake haɗa rai ya sauke numfashi har suka isa ta sauƙa tun kan ya zagayo ya buɗe mata. Ɗakinshi kai tsaye suka nufa don suna shiga parlorn ya riƙo hannunta, bata ga amfanin make up ɗin ba bayan hotunan da suka yi musamman nata dashi da yayi kyau ainun hannunshi kan cikinta yana murmushi yalwatacce ita kuma tana kallon hannun nashi tana murmushi wanda har ta mayar wallpaper to bayan shi bata ga amfanin adon ba. Wanka ta shiga bayan ta goge Kwalliyar shima ya kwaɓe ya bi bayanta, tana tsaye shower ta ji ya manne da ita yana bin wuyanta da tafiyar tsutsa, zamewa take har ta gama ɗauraye jikinta ta fice ta bar shi ya bi bayanta da kallo, bata wani tsaya drying kanta ba ta duba shirt din shi ta saka don tana jin daaɗinsu sossai ta zame towel ɗin tana bottuning shirt ɗin da iyakarshi rabin cinyarta ya fito ɗaure da towel a kugunshi da wani irin kallo yake binta ganin ta nufi bakin gado ya isa ya kama hannunta "Kina so ki yi mura ko?" Bata tanka ba yaje ya ajiye ta gaban madubi ya zaro hand drayer ya shiga busar mata da gashin cikin kulawa. Miyau take hadiyewa tana bin ginannen jikinshi dake bayyane da kallo, ganin zai kalleta ta ɗauke kai yayi murmushi ajiye drayer ɗin yayi ya duƙa sossai yana shunshunar wuyanta da baya rabo da kamshin da yake masifar so, a yanzu har da lips ɗin shi yake goga mata zuwa sajenshi da ya sa duk numfashi na kwace musu barin ma shi da yake a kunne, hannunshi ya mayar ta gaban rigar nashi dake jikinta ya fara unbottuning saman shirt ɗin yana sauke wahalallen numfashi mai rikitarwa. "Ya Saraki ka bari, bacc..." Hannun da ya tura cikin rigar ya sa ta ɗauke numfashi ganin zaunen ba zai kai su ba ya ɗagata chadak zuwa gado yana ƙarasa unbottuning shirt ɗin, tun tana resisting har ta sallamar suka rikice a duniyar masoya sai da komai ya kamallah ta zame za ta sauƙa ya dawo da ita

Chapter 39 of 40