rigar yana shafa duk inda hannunshi ya sauka a fatarta har lokacin kuma yana wasa da wuyanta da harshenshi.
Cikin whisper yake jefa mata magana a cikin kunne bata ma jin me yake cewa don yadda ya rikice haka ya rikitata abinda ta iya tsinta shine
"lets make another baby my Queen..."
Kai ta gyaɗa ya zura harshen cikin kunnenta daga haka basu ma san sun isa gado ba, sossai yayi kewanta rabon da ya ji shi a gajimare tun kan tayi ɓari sai ya ji kaman an sauya ta ne, kaman an kara mata zuma ta haukatashi ta gigitashi a duniyarta sai gashi yana sambatun da bai ma san abinda yake cewa ba ta bashi gudumawa sossai don itama ta yi kewar shi ƙwarai basu sarara ba sai da ya tabbatar bayan ya samu natsuwa itama ta samu ya rungumeta cikin kirjinshi yana sanya mata albarka.
Ta sake shige wa jikin nashi tana murmushin kunya, chadak ya ɗauketa suka je suka yi wanka suka fito cikinta ta shafa
"Yunwa nake ji"
"Afuwan duk na yashe abincin, bari na samo miki wani abu"
Ya faɗa yana kokarin saketa ta riƙe hannunshi
"Just sit bari na ɗauko mana fruit salad da na haɗa ɗazu"
Kai ya gyaɗa ta fice chan ta dawo da bowl mai girma dauke da spoon ciki, hannu ya miƙa mata ta bashi ya ajiye bedside kan ya janyo hannunta ta zauna kan kafafunshi bayanshi jingine da jikin gado ya shiga bata a baki sai da ta ɗauke kai ya mayar da spoon ɗin ta ɗauka ta dibo tace
"Haaa"
Murmushi ya saki ya buɗe bakin ta shiga bashi sai da ta kai spoon na ƙarshe ya kai hannu ya sauƙe towel ɗinta daga sama ɗan tsorata da tayi ya sa ta ɓata mishi lips sai ta Shagwaɓe fuska yayi murmushi, ta juyo gabaɗaya ta raba kafafunta tsakanin nashi tace
"oops lemme help clean your mouth"
Lumshe ido yayi ta kai bakinta ta sude madarar tas za ta janye yace bata isa ba nan suka sake fara ƙoƙarin komawa ruwa ita ta janye tana dariya.
"Ke ko?"
"Me na yi? Ba kai ne ka ja na ɓata maka bakin ba kuma daga taimako sai sai a nemi zarcewa"
Ya janyota ta dawo jikinshi yana murmushi tace
"Yau saura sati ɗaya aurenka ko?"
A ɗan sanyaye tayi maganan, yayi pecking goshinta yana kallon idanunta yace
"Ai ina da aure ni"
Tayi murmushi
"Ba nawa auren ba ina magana kan amaryar ka Zarah
"Wace hakan?"
Ta ɗan Harare shi da fararen idanunta da ya saka shi sakin kyakyawar murmushi tace
"Ka fa san wacce nake nufi ko baka san sunanta ba?"
"What name? Afeefahhh ita kaɗai na sani, Afeefah kamal Its the only name i learned nd i call.." Yayi maganan yana lakace hancinta idanunshi na tabbatar mata da sunanta kaɗai shi ya sani a duniyarshi.
Za Ta sake magana ya haɗe bakinsu sai da ya tabbatar ta manta da maganan wata zarah kan ya zare bakin yana rungume da ita suka yi bacci cikin natsuwa da tarin ƙauna.
Washegari da safe shi yayi mata breakfast don da asuba ma bai barta ba duk jikinta ya mata laushi, bayan ta karya yayi wanka ya shirya cikin wasu fararen kaya da suka amshe shi ƙwarai da gaske ga mamakin ta ta ga ya ɗauko wani alkyabba silver ya saka da yayi mugun yi mishi kyau, baki ta saki tana kallonshi sai ya ɗauko wani takalmi shima silver da ya fi yanayi da na saurata ya saka ya saka hula kan ya zauna ya naɗa rawani.
"Tabarakallah Masha Allah!"
Ta ambata tana sauƙe numfashi idan ba Allah ba waye? Waye ya isa kera irin wannan jarumi, santalale kuma kyakyawar namiji haka mai zati da kwarjini? Bayan nan kuma ya ɗauka ya bata matsayin miji! Alhamdulillah ta sake ambata bata san ya iso ba sai hura mata iska da ta ji yayi a fuska ta lumshe idanu tana sake buɗewa a kanshi hannu ta ɗaga a dunkule ta shiga furta mishi kirari.
"Ado da kanshi ya sara maka ɗawisu...Barden maza in ka fito yaƙi ya kare, mari babban kifi maganin hadamammu...bangon duniya sun yi iya yinsu sun kasa Huda ka, Allah ya bar mini kai jarumin jarumaina...!
Mai sarauta da halin girma.
Tauraron sarakai jigon Afeefah
Saraki kai gaba kai musu nisa kamo ka sam sam ba su iyawa sarakai duk suna a bayan ka..! Allah ya ja da zamanin Ciroman duk duniya Yariman matasan Fombina...kare ka angon Afeefah"
Sossai yake murmushin da ya sake tafiya da ita ya duƙa yayi pecking goshinta yace
"Duka wannan kirari nawa ni kaɗai Matar masu sarauta?"
"Duk kirarin da zan ma ka wuce nan Sarakina! Allah ya bar mini kai har aljannah"
Ya shafa fuskarta yana kallonta har lokacin cikin towel take ya shafa idanunta da suka sake haske da sheki zuwa lips ɗinta da ya mayar da su cherry Red tsabar yadda ya fitine su ya furta
"Zan fita, ki kula min da kanki har zuwa dawowata kar kuma ki manta da cewa Saraki na ƙaunar ki... Your eyes, your voice, your smile kai komai da komai i just love everything about you"
Ta sauƙo tana gyara towel ɗin ta ɗauko turare ta sake fesa mishi tana murmushi tace
"I love you more takecare, sai ka dawo"
Kaman kar ya tafi haka ya fice ta koma ta zauna tana murmushi.
Yana fita kai tsaye Fada yayi fuskarshi a haɗe ya shiga dogarai suka fara mishi kirarin isowa, karon farko da ya zo fadan tun naɗinshi shi karan kanshi Abeey ya ji mamakin ganinshi haka, a gaban mai martaba ya duƙa
"Barka da safiya Your majesty..."
Sarkin dogarai zai amsa sarki ya ɗaga mishi hannu
"Barka dai Ciroma, ina Fatan lafiya don da ganinka akwai magana fal a bakinka"
"kwarai kuwa Adalin sarki, na zo ne zuwa na musamman a yau... Na zo ne in shigar da ƙara ina kuma fata wannan sarki mai adalci zai yi mana hukunci daidai da tsarin addini bisa adalci irin nashi"
Gaban mai martaba ne ya faɗi, ya riga ya san binciken da Sameer ke yi amma baya so ko ma menene a kawo shi gaban fada shi kuma Saraki Yana so ne duniya ta shaida ta yadda kunyar duniya da mutanen cikinsa kaɗai ya ishe su kan su gamu da na lahira, yana sane yayi hakan kar ma Mai martaba yayi tunanin Afuwa saboda zumunci ko wani abu...
"Na zo ne in shigar da ƙarar Makama, Madaki da Fulani Adama bisa laifin zamba cikin aminci, yaudarar masarauta, cin amana, zalunci da kuma kisan kai... Sun cutar da wannan masarauta kuma sun cutar da sarki tsawon shekaru a yanzu kuma sun cutar da abinda bai kamata su cutar ba... A Yanzu kan shari'a tayi nisa nake shaida cewa na yanke alkawarin aure dake tsakaninmu da zuri'arsu don zuri'arsu basu da nagartar amsa sunan sarauta har abada"
Kallon kallo aka shiga yi cike da dumbin mamaki yayinda Makama da Madaki zufa ya shiga yi musu wanka, gabansu ke faɗuwa amma Makama ya dake ya ce
"Wani irin zance kake yi Ciroma? Kar fa ka manta waenda kake zargi da waennan muggan ayyukan ba tsaranka bane kuma iyaye muke a gareka... Daga dawowarka zuwa yanzu har ka isa shiga lamuran da baka sani ba? Ka kiyaye don ba za mu yafe sharri ba ko daga waye kuwa.."
Yayi murmushi ya ce
"Sanin kun taka matsayin iyayen nawa shi yasa na kawo zancen inda za'a yanke hukunci da wasu ne chan. Hmmmm...."
Mai martaba ya katse shi
"Mecece hujjarka na wannan zargi Ciroma?"
"Ina da tarin hujjoji amma kan nan ina so a gurfanar da Fulani Adama gaban fada a kuma gayyaci duka matan Laamiɗo don duk ya shafe su"
Sarkin gida Mai martaba ya kalla tuni ya fice, duk fadan ana zaune shiru kowa da abin da yake saƙawa yayinda su Makama ke zare idanu suna kuma haɗa gumi da tsoron abinda wannan karamin alhakin zai iya yi musu.
"Kaman yadda kuka sani gabaɗaya bana ɗaga kafa a zalunci kuma ko wanene muddin na same shi da zalunci na kan hukunta shi ne daidai da laifin da ya aikata ban cire kowa ba, Ciroma ya shigar da karar Makama, Madaki da kuma Fulani Adama bisa zargin cutar da iyayenshi da matar shi za mu so jin hujjojinshi don yin hukunci daidai da laifukansu idan kuma muka same shi da son bata suna ko wasa da hankalin wannan fada shima za mu yanke mishi hukunci daidai da laifinshi. Muna sauraronka Ciroma"
Gaabɗo ya kalla sai ya miƙe da sauri ya fita, idanu Fulani Adama ta zuba mishi tana jin wani irin tashin hankali na rufe ta, da alama kallon biri take yi mishi shi kuma yana mata kallon Ayaba, a zaton ta ta toshe duk wani hanyar da zai iya sunce mata zani a kasuwa sai ya ke kokarin nuna mata shi ɗin mai zamani ne dole ta kiyaye shi. bata gama tsurewa ba sai da ta ga wasu sojoji mata biyu sun shigo da rahane da aka chanza mata kamanni ko tsayuwa bata iya yi suka gurfanar da ita, zabura tayi sai kuma ta koma yaraf ganin An sake shigo da wani mutumi an yi mishi ɗaurin huhun goro Dukda shekarunshi, azaba duk ya ishe shi ko motsi baya iya yi mai kyau....
"Kai!!!"
Rayyan ya daka wa tsohon tsawa da sauri ya zube ƙasa yana roƙon yafiya cikin kuka.
"Menene alaƙarka da waenchan???"
Ya ɗaga kai ya kalli su Fulani Adama ya ce
"Tsawon shekaru arba'in kenan ina yi musu aiki ba na asiri bane, ina ba su wani magani ne da ya shafi lalata mahaifa, hana ɗaukar ciki da ma zubar da shi idan ya samu... Sai G...gu..ba. A gafarceni Ranka ya daɗe da farko ban so aikatawa ba suka min barazana da 'ya'yana daga baya son zuciya da kudin da suke cika min ya ja ni har na zalunci Sarkin mu mai adalci.... Don Allah a yi min aikin gafara na tuba na bi Allah na bi ku ku yafe min..."
Tsaki Rayyan ya ja ya kalli Rahane
"Faɗi bayanin da kika yi min..."
Cikin kuka da tarin nadama marar amfani ta shiga cewa
"Sunana Rahane, ni ce amintacciyar Fulani Adama tun da jimawa amma ba ni na fara yi mata wannan aiki ba mahaifiyata ce da Allah ya yiwa rasuwa, ta bani labari kan rasuwar ta irin son mulki da izza irin na fulani Adama, ta tabbatar min akan mulki babu abinda Adama ba zata yi ba, ta iya makirci kala kala kuma bata bar kowa ba har mai martaba, da fari bayan aurenta da mai martaba ta zaci zata haihu plan ɗin ta kuma tana haihuwa za ta yi sanadiyar mutuwar shi danta ya zama mai jiran gado sai Allah bai kawo haihuwar ba har ya auri Fulani Aminatou anan ta yanke hukuncin muddin bata haihu ba babu mai haihuwa a wannan masarauta har mai martaba kuwa don haka ta yanke hukuncin yin mai gabaɗaya Wai Haihuwa da hanji da taimakon yayanta da ƙaninta suka samu wannan mai maganin sadidan yake bata maganin hana ɗaukar ciki..
A kowani sashe na matan sarki tana da amintacciyar baiwa da take biyan su makudan kudi suke yi mata aikin zuba maganin nan a abinci kowace mace da mai martaba ya aura, tun Fulani Aminatou bata shekara uku ba ta gama da mahaifarta yayinda a fili take nuna tausayi da neman taimako ga mai martaba wanda hakan ya bata matsayi mai girma a idanunshi, Shigowar Fulani Faɗimatu ya zame mata barazana don bata yarda hadimai su mata girki ba kuma idan tana yi bata nisa da bakin murhunta hakan yake bata damar ɗaukar ciki tunda duk abinda ta girkawa mai martaba ma babu maganin, duk ta ɗauka Fulani Adama kan san yadda tayi ta sha wannan magani da take karɓo wa cikin ya ɓare. ko da ta samu cikin farko na yarima Aliyu ta gudu Mambila babu yadda basu yi ba su sayi hadimarta mai rasuwa Hanne ta zuba musu maganin ta ƙi har alkawarin kasheta suka yi amma ta ƙi amincewa bayan sun dawo masarauta suka samu nasarar ba wa yarima Aliyu guba ya ci ya mutu fahimtar za ta iya tona musu asiri itama suka yi ajalin ta.
Cikin Ciroma Sameer ne ya zo musu bazata don ita kanta mahaifiyar bata san da ciki ba sai da ya girma, sun yi duk yadda za su yi sai dai Zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzuru ana shaho sai yayi dole ya zo duniya, sun so kashe shi yadda suka yi wa Yarima Aliyu amma shi ɗin murucin kan dutse ne bai fita ba sai da ya shirya ya zame musu kabewar kan ƙabari bakin cikin mai taushe, daga karshe dole suka sa mahaifiyarshi ta rabu dashi ala dole don babu yadda ta iya tana so wa danta rayuwa.
Fulani Adama ta fi tsanar Fulani Faɗimatu akan duka matan sarki don Cikin lokaci kankani ta lalata wa Fulani Salimah ma mahaifarta ita ce ta zame mata gagara badau bisa kariyar Allah, a farkon aikinta babu asiri babu tsubbu don duk ta fi gane kirsa da makirci amma Makama da ya fi kowa son mulkin yana ganin kaman ko ba jima Ciroma Sameer zai dawo sai ya je yayi mishi asirin da zai saka ya manta komai da kowa, ya mishi asirin da zai ji ko sunan iyayenshi ba zai iya ambata akan harshenshi ba, ya saka mishi tsanar masarauta da sarautar gabaɗaya, Kwatsam sai ga shi ya ɓullo kaman huduwar rana tafin hannu yayi kaɗan ya kare shi sun shiga tashin hankali don basu taba zato ko tsammanin bayyanuwar shi ba tunda an tabbatar wa Makama cewa asirin ba mai karyewa bane don kogi aka jefa aka ba wa tsuntsu wani ya fire sai gashi ya dawo kuma da wata mace.
Anan suka yanke hukuncin aura mishi zarah da haɗin Bakinta na daga ta aure shi sarki yayi murabus za su kashe shi su kashe sarkin sai su karbi sarautar har dan Zarah ya girma, kwatsam ta fahimci Fulani Afeefah na da juna biyu, hankalinta ya tashi ta aikeni wurin mai maganinsu inda ya bani magani na kawo sai dai duk abinda aka bata bata ci har sai da Fulani ta yi mata wasu maganganu da suka raunata zuciyarta ta sha fura, a cewar mai maganin sai bayan sati ma zata yi ɓari kar ma a zarge ta tunda da wayon ta ba zata bari a lokaci ɗaya ta zubar da cikin ba dayake Allah ba azzalumin bawan shi ba akwai rabon kamatan dumu dumu bisa laifukanta sai cikin ya ɓare a ranar dole aka san me ta ci kuma a ina ta ci inda daga ranar Ciroma Sameer bai bar su sun shaki iska ba.
Ya kama ni aka dinga min horo iri iri bai bar ni ba sai da na faɗi komai na kuma kaishi wurin mai maganin aka kama shi... Ku yafemin don Allah ku yafe min na tuba wallahi umarni kawai nake bi don tsira da rayuwata"
Cikin kuka mai tsuma zuciya ta ƙarasa.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..! Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Abinda ke tashi kenan a fadar duka matan sarki kuka suke yi mai tada hankali yayinda mai martaba ya runtse ido yana jin hawaye na sulmiyo mishi, ashe kashe mishi yaro suke niyyar yi shiyasa take kanainaye shi da kissa da komai take cusa mishi son auren Zarah da Sameer? Ya gode Allah da ba'a yi auren ba da ba zai yafe wa kanshi ba.
"Wallahi na yi nadama tun ba yanzu ba amma tsoron hukuncin Fulani Adama ya sa na kasa daina basu magani, yarana sun mutu duk a gobara na auri mata sama da biyar duk suna gudu su bar ni don na kasa basu haihuwa, tun mutuwar yarana na yi nadama amma ban san yadda zan yi ba a gafarceni"
Tsohon ke fada. Fulani Aminatou tace
"Allah ya isa! Allah ya isa tsanina da ku duka wallahi Allah ko da ni kaɗai ce zan yafe muku ku shiga aljannah ba zan taɓa yafe wa ba"
Fulani Salima ma Allah ya isa take jerawa cikin kuka mai ciwo, mai martaba hawaye kawai yake yi haka Ammi dake jin mutuwar yaronta ya dawo mata sabo.
"Babu aure tsakaninka da Zarah har Abada Ciroma, ku kuma wannan kaɗai ya ishe ku tsoron Allah, wannan kaɗai ya kamata ya ishe ku ishara.... A tube musu duk wani rawanin zuri'arsu ku kuma shaida na yanke igiyar aurena da Adama a dibe su a kaisu kurkuru mafi azabtarwa na wannan masarauta kan a yanke musu hukuncinsu.... A tabbatar basu samu natsuwa ko kwanciyar hankali ba"
"An gama ranka ya dade"
Sarkin dogarai ya zube ya amsa kan wasu majiya karfin suka shigo suka saɓesu ko damar magana ba'a basu ba, kunya da dana sani marar amfani na rufe Adama komai ya kare mata a lokacin da bata yi tsammani ba.
Rayyan ya dubi Afeefah dake kuka ya girgiza mata kai a hankali yace
"Na gode Afeefah. Na gode kwarai ta sanadiyarki asirinsu ya karye idan baki manta ba duk ayoyin da kike yi wa Saleem a tare muke sha Dukda ban san da zaman wani asiri a jikina ba, Kin ba ni babban dama ta sanadiyarki na samu faɗa wa Mammi abinda ta jima tana son ji na wanene ni kafin mutuwarta. Ba zan taɓa manta wannan taimako naki ba na gode"
Ammi ta rungumeta tana kuka. A haka aka watse zaman fadan mai martaba sai riƙe shi aka yi zuwa sashenshi tuni Rayyan ya maƙala mishi ruwa don ba karamin hawa jinin shi yayi ba.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*58*
Alhamdulillah komai ya cigaba da tafiya normal bayan nan, ta cigaba da lectures ɗinta cikin kwanciyar hankali kuma tana samun duk wani kyautatawa daga zuri'ar na mijin nata kaman yadda shima yake kara samun kusanci da iyayenshi, Mai martaba ya sha jinya kan ya warke ya tara matan yayi ta basu haƙuri a ganinshi komai ya faru ne sanadin aurenshi da suka yi, sun nuna haka ƙaddarar su take sai dai Fatan Allah yayi musu sakayya akan Adama, Zarah da bata san komai ba sai da aka warware daga farko ji tayi duniyar yayi mata zafi damuwa yayi mata yawa ta tattara ta koma wurin mahaifiyarta da dukkansu har yan uwanta kunyar abinda mahaifinsu ya aikata ya sa ba sa iya ko fitowa, Ammi bata neme ta ba haka Aisha don tunda har ta yi niyyar auren Rayyan ne don ta cutar dashi su ma suka ji ba za su iya cigaba da hulda da ita ba amma Aisha tayi kuka kaman ta mutu, ta ɗauki zarah kaman 'yan biyunta ne bata zaci hakan daga gareta ba.
Maganan yanke hukunci sai da suka yi wata biyu suna cikin na uku garƙame cikin azabtarwa kan aka yankewa Fulani Adama hukuncin kisa ta hanyar rataya, Makama da asirinshi ya dawo mishi ya haukace damuwarshi kawai a barshi yayi ta tafiya ji yake kaman kwakwalwarshi zai fashe idan bai shiga duniya ba dukan da yake yiwa Madaki yasa aka raba musu ɗaki, shi Madaki da sauran hadiman an yanke musu life imprisoment iyalan su sun yi kuka kaman ba gobe amma bahaushe ya ce tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan yi wa dukan tsiya.
Soyayya tsakanin Saleem da Aisha yayi nisa don har ya turo mai martaba yace za su yi fixing rana sai a haɗa da na Ameer da ya kasa komawa da Abeeha dake shirin gama makaranta, Jiddah dai da tayi mugun kewan su sai dai a haɗu a yi ta waya. Yau ya kama ana ya gobe Afeefah za ta gama First semester examination ɗinta kuma Rayyan ya tabbatar mata a satin za su fara shirin tafiya Kaduna don ta matsa mishi sossai akan komawa ga su Suhail da kuma su kawu Dukda shi baƙin cikin kawun bai taɓa wankuwa mishi a rai ba sai dai bai hanata ba don haka mai lalle ta nema Ammie ta turo mata har sashenta.
Tana zaune da dogon wando da wani shirt Black na ma Rayyan ɗin ne daga ganin girman da yayi mata amma ta fi jinta comfortable ciki, ta ɗaura Black dan kwali a kanta an gama lallen kafa da hannun duk an saka leda su Aisha na gefe suna ta hirar su da ta shafi rayuwa har jan ya kama aka cire mata sai aka zana mata baƙi a bayan hannun don ta ce jan kawai ya isa a kafafun yarinyar kwararriya ce kuma lallen ya mugun kamawa yayi maroon sharrr kaman ka sace kafafun in ka gani, Rayyan ne yayi sallama ya shigo duk suka mishi sannu da dawowa daidai an gama baƙin kenan ya tsaya yana kallon hannun kan ya ce
"Wai tunda na bar ku kina nan wurin zaune?"
Ta karkata kai fuska a ɗan Shagwaɓe tace
"Kwalliyar kenan sai wahala duk yunwa ma nake ji babu hannun cin"
Ya kalli hannun nata sai ya nufi kitchen, Aisha da Abeeha suka kwashe da dariya suna tafawa
"Sai da ke Matar mijinta"
Aisha ta faɗa tana dariya.
Abeeha tace
"Ku tashi mu tafi yanzu bai wuci abinda zata ci ya je nema mata ba kan ya dawo ya kora mu ko su makanta mu gwara mun yi ta kanmu salin alin"
Afeefah na ce musu su tsaya ko ta kanta basu bi ba suka tarkata suka tafi sai gashi ya dawo hannunshi rike da wani plate.
"Duk ka kora min 'yan hirar Ya Saraki..."
"Dama wani amfani suke dashi a gareki idan ina nan? Babu so Haaa ki ci abinci"
Murmushi ta saki tana bude baki ya saka mata Nan-bread guda biyu da ya sanyo a plate ɗin da curry chicken da ya zuba a gefe, da hannunshi yake bata yana tabbatar da bai ɓata mata jiki ba har ta ƙoshi ya bata ruwa ta sha kan ya shiga duba lallen.
"Kin yi wa lallen nan kyau ainun Boɗɗi na"
Tayi murmushi tana sake kallon lallen
"Ko kuma shi ya min kyau dai ko Ya Saraki?".
"Wai dama baki sani ba?"
"Mene?"
"Ado biyayya yake miki, Kwalliyar da kanshi ke kike mishi kyau ba shi yake miki kyau ba.."
She's just blushing don bata gajiya da sauraron dadadan kalamanshi yana ɗan wuya ya sake bakin don haka idan ya sake yana zubowar tana amfani da damar ta adana a cikin zuciyarta ta yadda ko baya nan in ta tuna fuskarta kan zama ya cika da tarin murmushi.
Washegari kuwa aka kai ta paper yadda aka saba motoci biyu har gaban exams hall su jira ta gama a dawo da ita gida, yau ko da ta fito bata gansu ba, daga jikin hall ɗin ta tsaya sai ta ga call nashi tayi picking ya ce mata ta taho yana kallonta fuskarta cike da fara'a ta nufi motar nashi don a yau da kanshi ya zo ɗaukar ta.
Idanunshi da ya zura mata tun tahowarta ya lumshe a sadda ta yi masauki gaban motar kamshinta mai sanyi da natsuwa na ratsa shi
"Hey Assalamu Alaikum"
Ta furta a hankali tare da miƙa mishi hannunta ya ɗan murmusa kan ya miƙa nashi ya shigar cikin nata yana kallon tsakiyar idanunta ya furta
"Wa'alaikissalam warahmatullah"
Cire hannunta ta so yi sai ya gimtse yana mata kallon baki isa ba kuma ai dariya ta ɗan yi, ya miƙa hannu gefenshi ya zaro wani rose Red nd green dake fidda sassanyar kamshi ya miƙa mata.
Da hannu ɗaya ta karɓa ta kai hancinta tana lumshe ido fuskanta ɗauke da murmushi tace
"and this?"
"I am bribing you a ban dama in fitar dake outing”
Dariya ne ya ɗan kufce mata
"seriously? Ai na zaci saurayi da buduruwa ne ke fita date ba mata da miji ba"
Tayi tambayar tana wara fararen idanunta a kanshi ya kai hannunshi ɗaya kan kumatunta ya shafa
"Babu laifi a hakan.... Afeefah ki na da kyau fiye da duk wani abu mai kyau, kina da daraja fiye da duk wani abu mai daraja a kullum soyayyarki ƙara yawa take a zuciyar Ryan, I will always love you again and again...kullum sabunta kanshi soyayyar ki ke yi so i have to be very caution"
Tayi murmushi mai cike da tarin alfahari tana sake shinshuna kyawawar furen dake hannunta.
Motar ya ja suka fice daga makarantar.
"Kin ce za ki yi sayayyar su Suhail should we start with the shopping ko mu je ki sha ice cream?"
Tayi murmushi tana sake
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 40