Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi suka fice daga gidan, har suka iso gidan Auntyn nata magana bai haɗa su ba ta sauƙa ta shige yayinda ya juya ya koma asibitin. Bata bari abin ya cigaba da damunta ba ta kintsa gidan tamkar Auntyn na nan ta ɗora girki marar nauyi ta ci ta zuba saura a kula kan ta ɗan kwanta bacci, har ga Allah ta tsame kanta ne saboda gudun abin da zai je ya dawo sam ba zata so wani ya yi kuka sanadin ta ba bare Auntyn ta don haka tana ganin shawarar da ta yanke shine daidai Sai da Aunty zee ta kara kwana biyu a asibiti saboda postpartum ciwon ciki da ya matsa mata amma duk da haka sai damun uncle usman take akan maganan Afeefar har fushi ta yi ta matsa a sallame ta saboda tunanin ta kar Afeefar ta ji an ware ta ko ta sanyawa kanta damuwa, duk da sun shirya da hamdiyya sai dai har aka yi sallamar hirar arziki bai haɗa su ba don ta matuƙar jin zafin abin da ta yiwa Afeefar. Tana sanya kai cikin gidan ta soma kiran "Afeefah! Afeefah!!" Da gudu Afeefah da ke zaune a parlor tana kallo ta fito ta rungumeta tana murmushin ganinta, Auntyn ta ɗago fuskarta sai ta sauke ajiyar zuciya "Afeefah ni kika yasar a asibiti ko?" "A'a Aunty ban isa yasar da ke ba wallahi, na bari ne Aunty hamdiyya ta kula da ku ni kuma sai in kula da gida ba gashi ba gidan ma ya ji daaɗi, da missing ɗin mu da zai yi sai yayi mishi yawa" Dariya Aunty zee ta yi tana girgiza kai, a parlor suka ya da masauki kan a natsa ma maƙota da abokan arziki an fara shigowa barka tuni gidan ya soma ɗinkewa da jama'a nan Afeefah ta shiga jeka ka dawo. Zamanta da hamdiyya na kwanaki shidda ba karamin wahala ta sha ba ta kuma danne zuciyarta, ko Aunty bata bari ta san hamdiyyar tana matukar musguna mata ba ta yadda ko satan kallon yaran ta yi sai ta yaɓa mata baƙar magana, har tsoron kallonsu take Dukda tana jin son su tamkar jini da tsokarta ta sha ɓuya tayi kuka sossai na mummunar shaidar da take dashi don bata tsira ba ranar suna har nuna ta hamdiyya ta saka ake yi saboda kananun maganganu duk Aunty bata sani ba. Auntyn Ta yi matuƙar kyau cikin milk leshin ta yayinda yaran suke sanye cikin kyawawan tufafinsu pink da blue, Afeefah ma cikin leshin da Auntyn ta yi mata musamman na suna maroon ta shirya ta yi mugun kyau Aunty zee har ajiye ta tayi ta zana mata liner a baki ta saka ta saka kwalli ta shafa mata powder sai tayi kaman ka sace ta ka gudu, masu hidima da kitchen ita suke kira tana miƙawa mutane abinci daidai ta zo miƙawa wasu mata kenan da yake ta bayansu ta zo ta ji ɗayar tana cewa "Ni kam dai ina tausayawa Zainabu saboda fa da gaske yarinyar da take riƙo rikakkiyar Mayya ce kuma fa an ce Mayu sun fi zaluntar wanda ya ji tausayin su" Ɗayar ta ce "Ni fa ban san yarinyar ba amma kuma ina da labarin tun tana ciki take cin maita, uban ta ma bai tsira ba haka uwar da ta haife ta, aiko Allah raba mu da irin wannan iri. Haihuwa bata yi rana ba" Wani irin abu mai nauyi ne ya taso ya tsayawa Afeefah a kirji tana ji na ukunsu na furta "za ki gane ta mana wata baƙa marar kiba ta saka leshi maroon, ai daga kallon idanunta da suke manya kaman kwai kin san za'a ga kurwa da kyau... Allah dai ya hana farin ciki komawa baƙin ciki" Gabansu ta zagayo suka ɗan sha jinin jikinsu ganin fuskarta babu ɗigon walwala idanunta da suka surke zuwa ja ta ɗan zuba musu kan ta ajiye abincin ta juya ta bar wurin. A karshe dai ba'a tashi suna lafiya ba don wata wai aljannunta sun tashi ai sai ta kashe Afeefah Mayya ce! nan fa gidan suna ya kachame dayawa suka shiga kururuwa su ma, da ƙyar aka fita da ita a gidan zuwa maƙota ban da kuka babu abin da take, bata san wani irin tunani zata yi ba duk ta ji kaman ta sallamarwa duniya farin ciki da rayuwarta sai ta tuna Aunty zee da ta yarda da ita take kuma bata kariya don yanzu ma ita ce ta nuna jan ido ta sallami kowa da abin da za'a yi sai ya fi haka, chan kuryar maƙociyarsu ta takure tana kuka sossai bata ji Shigowar Aunty zee ba amma ta ji hannu ya taɓa ta firgita ta yi ta miƙe tsaye tana girgiza kai "Wallahi ni ba Mayya ba ce! Ban san ya ake yi ba don Allah ku yi haƙuri ban taɓa cin naman mutum ba wallahi..!" A rikice take maimaitawa da sauri Aunty zee ta rungumeta tana hawayen tausayinta "Ya isa Afeefah! Ni ce! Auntynki ce, na sani wallahi na sani ke ba Mayya ba ce na yarda da ke" Kuka kawai ta saki mai tsuma zuciya tana yin luff a jikin Aunty zee ɗin. Jiki a sanyaye duk suka dawo gidan, yayinda abin da ya faru a sunan ya tsayawa Afeefar ta yadda ko kuzarin taɓa yaran bata da shi, tsoro take ji kar ta taɓa su abu ya faru haka Aunty zee ta sa uncle usman a gaba tana kuka sossai "Duk laifin matar ka ne usman da bata fara ba da hakan bai faru ba, yaran nan fa kannen Afeefah ne amma ka ga yadda take baya baya da su ko taɓa su sai na yi da gaske take yi! Haba mana ko bata duba komai ba ta duba maraicinta mana wallahi ta ɗauki alhakinta dayawa kuma ni kam ta daina burgeni sam" Shiru yayi chan ya ce "Ki yi haƙuri zan yi mata magana, amma ki dinga dubawa itama hamdiyyar ba don tsanar Afeefah bane ya sa take hakan saboda kare yaran nan ne ganin tsawon lokacin da muka ɗauka kafin Allah ya ba mu" "Wallahi na fi ƙaunarta a kan su, ta cigaba da rayuwa da wannan tsangwamar rayuwarta na cikin haɗari don Allah zan roƙe ka Alfarma don girman Allah kar ka chanza mata kaman yadda ka fara mata, ka dubi maraicinta ka riƙe ta kamar yadda za ka riƙe suhail da suhaila". Hannayenta duk biyu ya riƙe "Ban tsani Afeefah ba Zainabu, in shaa Allahu kuma zan cigaba da iya ƙoƙarina a kanta" "na gode sossai Baban 'yan biyu" Ya saki murmushi ita ma ta mayar masa. Duk su biyun sun mayar da hankali kanta ta yadda hatta shi uncle ɗin kan ja Afeefar jiki ko ma ya bata babies ɗin da take matukar so ta riƙe, yau satinsu na biyu kenan a duniya. Tsaki Aunty zee ta ɗan ja kaɗan karo na ba adadi hakan ya saka Afeefah dake jijjiga suhaila yayinda Auntyn ke ba Suhail Mama ta kalleta ganin tana ta yamutsa fuska ya saka Afeefar katse shirun nasu "Aunty lafiya kuwa?" Ta sake jan wani tsakin karo na barkatai kan ta furta "Wlh Afeefah ciwon ciki ne ke ɗan matsa min tun haihuwar nan kullum sai na yi shi kaman ƙa'ida" "Sannu Allah ya ba ki lafiya, babu maganin da suka ba ki a asibiti?" "Akwai fa ina sha amma kaman bana sha" "Sannu" Haka tayi ta jera mata duk ta saka kanta a damuwa domin sam bata so taji wani na ciwo a gidan sai gabanta yayi ta faɗuwa fargaba ya bi ya rufeta har sai an furta mata yayi sauƙi. Shigowar Uncle da karbar babyn da yayi daga hannunta ya sa ta yi musu sai da safe ta shige ta bar su nan parlor. Chan cikin dare sai ta ji kaman ana motsi da ƙarfi, sai kuma ta ji bugun kofar ɗakinta a razane ta farka tana salati jin Muryar uncle ya sa ta dirko da hanzari ta zo ta buɗe kofar "Afeefah ki zauna da yaran nan idan sun yi kuka ki ba su madara zan kai Auntynki asibiti ciwon ciki ya tasar mata sossai" Tuni ta rikice hawaye har sun fara zarya a idanunta. "Toh uncle" Ta faɗa tana bin bayanshi, shi ya riƙo Aunty zee da ke tafiya da kyar Afeefah na ta bin su tana share hawaye har zuwa kan babur ya hau ta kwanta jikinshi suka fice tana ta jera mata sannu da Allah ya bata lafiya. sai da taje ta rufe kofa kan ta dawo kan yaran ta zabga tagumi cike da damuwar ciwon Auntyn. Yaran sam ba su da rikici daman, tun tana tagumi har bacci ya sure ta a kansu ƙiran Sallar farko da kukan suhaila su ne suka farkar da ita, ta tashi ta haɗa musu NAN1 ɗin su da ake basu saboda abinci ya ishe su, ba zallar nono Auntyn ke ba su ba, sai da ta saisaita ya zama da dumi cikin tsafta ta fara ba su don suhailar na koshi sai suhail ma ya tashi bayan ta gama ta fice taje tayi alwala ta zo ta fara sallah sai da ta idar tayi Adu'a ciki har da roƙon Allah ya ba Auntynta lafiya kan ta miƙe ta bar sallayar zuwa tsakar gida. ƙoƙarin ɗora musu breakfast ta fara a natse take aikin Dukda hankalinta rabi na ga su Uncle da suke asibiti rabi na ga 'yan biyu kar su farka bata ji kukansu ba har ta gama haɗa abinda zata buƙata ta ɗora kan ta shiga sharar tsakar gidan. Ta gama haɗawa tana ƙoƙarin kwashewa kenan ta ji ana bubbuga kofa ba irin bugun hankali ba, jikin kofar ta isa sai ta ji kaman surutai dai ba na mutum ɗaya ba, bata buɗe ba ta shiga tambayar waye ne? "Ki buɗe mana ai za ki gani!" Muryar hamdiyya da ta ji ya sa ta buɗe kofar sai dai me za ta gani...! 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *Jama'a kuna manta cewa na rubuta True life story a jikin labarin nan, Meyasa na yi kyauta ne kam? Saboda ina so mu ƙaru da ilimin dake ciki, na tabbatar daga page 1 zuwa yanzu kun zaƙulo darusa masu dumbin yawa kuma ko ban kawo gyara ciki ba kun san amsar hakan. Wallahil azeem ban ƙara komai a labarin Afeefah ba, ban ce babu ƙari ba akwai amma sai a gaba yanzu duk abinda kuka gani a gaske ne ban chanza komai ba, please bear with me🙏* *007* Wasu gungun matasa ne ɗauke da makamai suna ƙoƙarin Hankaɗa hamdiyya su rufta mata ai da wani irin hanzari ta mayar da kofar ta rufe jikinta na wani irin ɗaukar tsuma, hankalinta sai ta ji yayi wani irin tashi tsoro da fargaba suka rufe ta, ko kafafunta ta kasa motsa su daga inda take tsaye... Ƙuuuuu haka cikinta yayi wani irin ƙara a sadda ta ji kukan uncle haɗi da maganarshi daga bakin kofan "Ki buɗe ki ba ni yarana...! Kin riga kin cuce ni kin raba ni da uwarsu rabuwa ta har Abada a yanzu ba zan iya sake ɗaukar raba ni da su ba, in kuma su ma kin cinye kurwarsu ne kaman uwarsu nima duk ki haɗa da ni ki cinye Afeefah..." Sossai yake gunji daga jin muryarshi zaka san baya cikin hayyacinshi ne. Tsurewa ta yi tana jin kaman ta zauce ko kunnuwanta ba sa ji da kyau. Tamkar sauƙar aradu ta ji wani da kaman yanzu ya iso a gigice yana furta "Da gaske ne Usman Zainabu ta rasu?" 'Zainabu ta rasu!' Ko kan kalaman su gama shiga kwakwalwanta sai ji tayi uncle na amsawa "Zainabu ta tafi ta bar ni. Sai da aka gargaɗe ni amma na ƙi saurara saboda ta ba ni yaƙini a kan yarinyar, ashe ba haka ba ne kai duniya...! Ashe wanda ya maka rana za ka iya masa dare? Afeefah ta yi mana shigo shigo ba zurfi, lafiya ƙalau muka kwanta da zainabu daga ciwon ciki farar ɗaya muna zuwa asibiti sai ga kiran hamdiyya take sanar min ta yi mummunar mafarki a kan zainabu, sai na sanar mata muna asibiti bata da lafiya ta tsorata tace gata nan zuwa Dukda dare ne haka ta bi gidan wani malami ta taho da shi akan mafarkinta mai muni ne Afeefah ta gama cinye kayan cikin zainabu ashe da gaske ne! Duk irin taimakon da malamin nan ya so bata ya gaza haka likitoci suna gani ta ce ga garin ku..." Hamdiyya ta chafe cikin kuka "in ba aikin maita ba menene wannan? an riga an cinye mata kurwa, sai da na faɗa wlh sai da na gargadi Aunty akan mayyar yarinyar nan.." Gayyar mutane bayan waenda hamdiyyar ta zo da su suka sake cigaba da taruwa suna hayaniya akan tabbas ita ce mayyar ai dama daga Dutsen-wai ma gudu wa ta yi saboda yunkurin kashe ta da Ƴan uwan wadda ta kashe last suke kawai a kasheta. Ƙafafunta sai suka gaza ɗaukarta, ta zube yaraf a ƙasa, hawayen da suke zuba tuntuni sai suka ƙafe kamar rijiyar da aka yi wa yaso. Zuciyarta na raya mata cewa da gaske ita ɗin annoba ce, da gaske ita ɗin mayya ce. Tana ji jama'a na maimaita lafiya ƙalau ta kwanta ciwon ciki ya turniƙe ta cikin dare daga isa asibitin su sai mutuwa. Hujjar da suka kafa kenan suna ƙara tunzura shi wasu na ta faɗan abubuwan da ita karan kanta da ake yi wa ƙagen bata san yaushe aka yi ba, ina ma da bata biyo Aunty zee ba? Ina ma da bata zo ba! Ina ma da bata biyo ta ba! Da gudu ta miƙe tana komawa cikin ɗaki gunjin wahalallen kukan da ta fashe da shi haɗe da ƙara na bala'i na cika ilahirin gidan ba wai don gudun rayuwarta da mijin antinta ke ta iƙirarin ita ma sai an kasheta ta bi matarsa ba sai don rungumar mutuwar a karan kanta, tana so a yau ta kawo karshen komai tana so tayi mai gabaɗaya da rayuwarta wai haihuwa da hanji... bayi ta shige kai tsaye babu wani tunani ko shawara ta zaro piya-piya da su ke ajiyewa saboda sauro ta buɗe tare da kafa bakinta a kai tana kuka me tsanani da dugunzuma zuciya, ƙwatt! ƙwatt!! ƙwatt!!! haka maƙogoronta ke ba da sauti a sadda ta ke haɗiyewa tana jin ta yi sallama da rayuwa kaman yadda mamanta, babanta, kakar ta, innarta da ma Aunty zee suka yi. Lallai an yi mata mummunan zato da ba za ta taɓa wankuwa ba a duniya, ta gaza! Ta kasa rayuwa kaman kowa, a yanzu wa zai dauke ta kuma? Wa zai yarda wani nasa ya aure ta ko ya raɓe ta? Mutuwa ita ce abu mafi sauƙi a gare ta kaman yadda ta yankewa kanta. Kururuwa da take ji a nesa bai sa ta sauƙe kwalbar fiya-fiyan ba sai da ta ji an yi wani irin wurgi da kwalbar ya tafi ƙasa yana tarwatsewa kwatankwacin yadda rayuwarta ta tarwatse. Dishi Dishi take gani jiri ya diɓeta sai taji an tare ta sun tafi a tare suuuuu ƙasa. *** A kafa su ke takawa sanye cikin uniform kasancewar assignment da aka ba su a cikin Anchau sun gama shi kuma a lokacin ne suke shirin barin garin zuwa cikin Kaduna, Zaratan matasa ne biyu sanye da khakin Sojoji daga yanayin tafiya da tsarin zubin halittarsu zai tabbatar maka da waennan ɗin ko a cikin Sojoji zaƙaƙuran ne, da wani irin ginshira suke tafiyan kowannensu na da kalar nashi kyaun, haiba da tarin kwarjini abin da ya bambamta uniform ɗin nasu abu ɗaya ne, shi wadda ya fi cin maganin fuskan nan tamau daga damtsen hannunshi akwai wani farin bandage da aka zagaye ƙarshen uniform ɗin dashi a jiki akwai zanen plus ➕ Da jan tawada wadda zai tabbatar maka da wannan ɗin Medical soldier ne. "Ko wanchan taron na me?" Na gefen da bai kai haske da wani irin ƙasaitar wanchan ɗin ba ya faɗa cikin natsuwa. A sace ya ɗan kalli wurin ya watsar kaman ba zai yi magana ba cikin halinshi na i don't care ya furta "How would I know Saleem after all tare mu ke da kai?" Wadda aka ƙira da Saleem ya sake kallon taron a lokacin da suka tunkaro su sossai "Ko ma menene Rayyan ba na tunanin lafiya..." Ko ya tanka sai ma kanshi da ya mayar ƙasa yana ci gaba da takunshi cikin ƙasaita da isa kaman yadda yake a halittarsa. Ihu da ƙarar da ya ratsa kunnuwansu haɗe da furta kalaman "sai mun kasheta yau za mu ga karshen maita" Da jama'ar wurin suke ta furta wa wasu ma ɗauke da makamai ya sa Saleem taka birki yana riƙo hannun Rayyan da yayi kaman bai ji ba. "Guy akwai matsala, we cannot neglet our duty ba za mu ga ana shirin ɓarna mu kama hanya mu wuce ba" Ko ya tanka sai birkitattun idanunsa da ya kai wurin yana nazarin situation ɗin fuskar nan babu walwala ko na miskala zarratin. Bai yi magana ba har Saleem ya isa ga mutanen, yana tsaye daga gefe da farko jama'ar sun so yin gardama amma jin ya kira akan a turo squad kuma ya zaro bindiga ya sa aka fara watsewa uncle da hamdiyya dai sai kuka da Allah ya isa suke yi, a mayar da maganan da ake ne ya ji abin da ke faruwa. "Wait here!" Ya faɗawa Saleem kan ya haye katangar gidan da ba shi da wani tsawo chan chan, bai buɗe kofan ba sai yayi cikin gidan yana dube dube, motsi da Sheshekar da ya ji ne ya saka shi kai kyawawan idanunshi wurin sai suka sauƙa kan kwalbar fiya-fiya a take warin ya shige cikin hancin shi da wani kalar hanzari ya fusgo madarar ruwa da ya gani nan cikin ɗakin Auntyn kasancewar ta mai jego ya fasa guda biyu ya isa gabanta ya sanya hannu yayi wani irin wurgi da kwalbar ya haɗe da gini ya tarwatse... Sulalewa take ƙoƙarin yi a lokacin da ya ɗago madarar yana shirin bata, bashi da zaɓin da ya wuce ya sanya hannunshi ɗaya ya tareta suka kai ƙasa ita tana ƙoƙarin sumewa shi kuwa ya sauƙa a kan gwiwowinshi, kanta ya ɗago da take ta kokawar numfashi ya kafa madarar tare da matse hancinta sai da ta kwankwadi mai yawan gaske kan ta sake yunkurowa tayi gaba wani kalar amai na kwace mata, tana gamawa ya sake dura mata ɗayar ta sake kwarara wani aman ko idanunta bata iya buɗewa alamu sun nuna ta jima da ficewa hayyacinta haka ya sanya hannu ya ɗauko ta zuwa waje, Fitowar shi da isowar motar Sojoji lokaci guda sai ciki aka sanya ta ya shiga tare da barin Saleem wurin suka fice a guje kaman yadda suka saba. Da gudu Uncle da hamdiyya suka shiga suka ɗauko yaran da ke ta kuka suna rurrungumesu a lokaci ɗaya suna ta tsinewa Afeefah, Saleem dake tsaye ya iso gangar uncle ɗin "A komai ya kamata ku dinga adalci da tunani, ƙage ko sharri ba abu bane mai kyau shin kun taɓa jin maita ko a addini? Ko kun taɓa ganinta ta yi maitar?" "Wallahi billahi na rantse da Allah idona idon Afeefah sai na sa an kasheta gwara ku gaya mata tun daga inda ta tafi ta san inda dare ya mata, sam Shigowar ta rayuwarmu bai mana rana ba" Hamdiyya ta karɓi zancen "ba kai kaɗai ba ai gwara mata mutuwar ta da dawowa unguwar nan tsinanniya" Juyawa kawai Saleem yayi ya bar gidan suna ta zaginta da kwashe mata albarka wasu mata na shigowa ana ta kokarin mayar da magana ai dama an gargadesu. BAYAN WASU AWANNI A hankali ta shiga ƙoƙarin buɗe idanunta da suka matuƙar yi mata nauyi tana jin yadda kanta yake wani sarawa, a tunanin ta za ta tsinci kanta cikin ƙabari ne kaman yadda ta jima da sallamar da rayuwarta wa mutuwa sai kuma ta ga akasin hakan. Idan ma tunanin ta ya bata daidai kaman nan ɗin ɗakin asibiti ne take ciki duba da yanayin tsarin ɗakin da kuma ƙarin ruwan da ke shiga jikinta ta canular dake ɗaure a hannunta. Tunanin dalilin mutuwar tata ne ya bijiro mata kaman ana haska mata majigin rayuwarta... "Aunty zee ta rasu" Daram! Haka zuciyarta ya buga zuruf ta miƙe zaune kaman ba jiri ne ke walagigi da rayuwarta ba, hannayenta ta sa duk biyu ta toshe dukka kunnuwanta don ji take kaman ana maimaita mata kalaman na rasuwar Aunty zee da speakern da ya fi komai ƙara a duniya. Tamkar zautacciya haka ta saki wani irin ƙara da ya shigo da nurses har uku ɗakin da gudu da ma an ba su aikin kula da ita kar ta farka ta sake yunkurin cutar da rayuwarta. Shigowar su da fara fusge-fusgenta kusan lokaci guda rirriƙeta suke kokarin yi amma kaman mai tashin aljannu sai wani irin ihu take mai tafe da gunjin kuka mai taɓa zuciyar mai saurare don kowa ya ji kukan ya san ba na wasa bane "Ku barni na mutu! Don Allah ku bar ni na mutu ba zan iya rayuwa ba! Ku sakeni....! Ku sake ni na ce!" Duk ta haukace kuma yawan su bai sa sun iya natsar da ita ba.. "Will you shut up and stay still?? Giyar wake kika sha ne?? Hauka kike yi ne??" Kalaman suka fito cikin wani irin amo da ya amsa duka ɗakin... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *008* "Karen hauka ne ya cije ki? Ko stupid lunatic brain naki hauka yake karanto miki?? Are you stupid?? Ki kashe kan naki oya take this..." Muryarshi mai cike da fushi haɗe da zafi ya cigaba da sauƙa wane aradu bisa kan su ba ita kaɗai ba hatta nurses da suka san shi sai da suka sha jinin jikinsu a take, wani irin shiru ne ya ratsa ɗakin kan takun sawayenshi suka amsa ya isa ganganta riƙe da scapel (aska irin ta likitoci) ya damƙa mata a hannu ya fusgo ɗayan da karfi har canular ɗinta na fita daidai jijiyar Wrist ɗinta ya sa yatsarshi babba. "Nan! Nan kawai za ki katse ki mutu idan sha'awar wutan Jahannama ne yake ɗibarki, ba mutuwa kike ƙaunar yi kafura ki tabbata cikin azabar Allah ba? Oya yanke mana!!!" A zaune take amma sai da tayi wani tsallen tsoro saboda tsawar da ya daka mata sai da ya kaɗa 'yar hanjin ta. "Haba Rayyan, yarinya ce don Allah ka bita a hankali mana ka ga yadda duk ka firgitata?" A zafafe yace "Za ta ci kashi ne salim? Muddin ba za ta ci kashi ba to tabbas babu zancen yaranta a lamarin ta sai tsagwaron iskanci da ƙarancin ilimin addini... Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci mafi sauƙi ga bawa a duk sadda ƙaddara ta ruro wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye ne?" Ita dai bata san a wace duniyar take ba don tsabar yadda take kaɗuwa bata sani ba a farke take ko a sume ya juyo da figitattun idanunsa da basu yi mata kala da na mutane ba ya zura mata "To bari ki ji, idan ma ba ki sani ba ki sani idan ma kin sani danne sanin kika yi to gidahumar kwakwalwarki ta tuna kuma ta yi hadda wutar Allah ya fi gaban wasa, kar ki zaci wannan wuta da kuke girki da shi duk zafi da raɗaɗin na wannan duniyar, duk irin hatsarinshi da in ya ɗan taɓa ki za ki ihu sai da aka wanke shi sau dubu saba'in kan aka jefo mana" Kanshi ya dafa yana wani jan tsaki mai tsawo saboda rabon da yayi magana haka ya manta, amma dole ya ƙarasa don zuciyarshi a tunzure take ji yake kaman ya faffalla mata maruka wa ta fi shiga cikin damuwa da zata kashe kanta? "Tabbas duk wanda yana musulmi ya kashe kanshi da gangan ya fita daga musulunci kuma zai mutu ya kuma tashi ranar gobe a kafiri... Ƙarbar kaddara mai kyau ko marar kyau na ɗaya daga biyar ɗin cikacikan musulunci. Ki yi gaggawar tuba domin a yanzu haka kin nunawa ubangiji ba ki da cikakkiyar imani ki kuma gode Allah we were

Chapter 4 of 40