Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nufi don haka Adu'a suka mata na samun ingantacciyar lafiya. Abeeha ta dubi Afeefah "Yaya fa?" Shiru Afeefah tayi don bata san me zata ce ba, a lokacin mommyn ta fita daga ɗakin "Yana ɗakinshi Adda Abeeha" Miƙewa zaune Abeeha tayi ta riƙo hannunta. "Afeefah na san zaman ku da yaya babu daaɗi, na kuma san kina tsoron shi da kuma tsoron kasancewa inuwa ɗaya da shi amma wallahi a yanzu babu wanda Yaya zai fi buƙata kaman ke! Mammi za ta yi farin ciki idan kika kular mata da shi at his worst moment irin wannan..." "Ta yaya Adda Abeeha? Mutumin da bai taɓa min kallon matsayin abu mai muhimmanci ba, wanda bai taɓa ɗaukata da kima ko daraja ta mace ba macen ma matarshi?" Tayi maganan cikin sanyi, tun ɗazu yaƙi take da zuciyarta akan Rayyan, tana so ta je inda yake amma tana tsoro ta san yana buƙatar wani amma bata san ta yadda za ta rarrashi mutum irin shi mai dakakkiyar zuciyar da baya bayyana rauninshi a fili ba. "Trust me Afeefah za ki iya, na san kema kin san me ya fi buƙata a yanzu tunda duk waennan abu kin yi going through a rayuwarki... A lokacin da muka rasa Abbu akwai Mammi Dukda bata da lafiya ta tsaya mana dukkanmu har saida muka zama daidai muka amshi ƙaddararmu amma a yanzu bata nan ita da ta fi kowa sanin Ya Rayyan a duniya, na sani a kwanakin nan bacci sai dai idan da allura ko magani hakanan zai yi ta ciwo amma ba zai nuna ba, ba zai yi magana ba ba zai ci abinci ba don Allah ki taimakemu ki kula dashi matsayin ki na matarshi" Kai Afeefah ta gyaɗa ganin Abeehar ta fara hawaye, tun dazu take so taje gareshi har cikin zuciyarta amma bata san me zata yi ba in taje ɗin, Miƙewa tayi tana kallon Abeeha "Ki yi bacci zan kula da komai in shaa Allah" Godiya Abeeha zata yi mata amma tayi saurin ficewa Abeeha ta mayar da idanun ta rufe hawayenta na gangara. Afeefah na barin sashen tayi ɗakin ta wanka tayi saboda yanayin zafi da ake dan yi tayi Sallar isha ta jima tana yiwa Mammi Adu'a tana hawaye kan ta yi shafa'i da wutiri ta nemi riga da wando na bacci jajaye ta saka ta ɗora hijab har ƙasa a kai sai ta fito ta nufi ɗakinshi, sai da tayi knocking ta buɗe ta shiga hasken a kunne don haka ta hange shi kwance kan gadon ɗakin idanunshi a rufe ya ɗan dukunkune kaman mai jin sanyi amma kuma bai rufa ba, kamshin shi da ya kama ɗakin na nan yadda yake ta nufi gaban gadon ta ɗan tsaya a kanshi kaɗan tana kallonshi. Allah sarki mutuwa, in ba mutuwa ba mai ya isa ya jijjiga Rayyan har haka a yini guda har ya rame, fuskarshi dake fari tass yayi wani irin ja musamman kan hancinshi, daga yanayin baccin da yake zaka san ba na farin ciki bane don a baccin ma sai yamutsa fuska yake, a hankali ta ja bargon ta lulluɓa mishi har kafada, sai ta isa wardrobe dinshi ta dubi wani bargo ta zo ta shimfida a ƙasa ta zagaya ɗaya ɓangaren ta ɗauki pillow daya dake cike da kamshinshi zuciyarta na bugawa sossai ta kwanta a ƙasan bayan ta kashe wutan ɗakin, ko motsi tayi sai taji kaman yana nan a kusa da ita saboda yadda daga bargon har pillown ke fidda azabbaen kamshin shi ga kasancewar ta under roof ɗaya da namiji abin da bata taɓa ba sai take jin ta wani iri da kyar bacci ya ɗauketa. Chan cikin dare sai ta fara jin kaman numfarfashi a ɗan tsorace ta farka ta miƙe zaune sai ta ji kaman daga kan gadon da yake kwance ne da sauri ta miƙe tsaye ta tafi ta kunna hasken ɗakin ta nufi gangar shi. Ya haɗa zufa yayi sharkaf sai juye juye yake kaman mai mummunan mafarki, numfashinshi na seizing kaman mai ciwon asthma hankalinta ne ya tashi bata san ta riƙe hannunshi ba tana jijjigawa "Ya Saraki! Ya Saraki ka tashi..!" Duk ta ruɗe saboda yadda yake yin kaman zai mutu, da karfin gaske ta jijjigashi hakan ya sa ya buɗe rinannun idanunsa ya zuba mata yana sauke numfashi a hankali hankali, hawaye ne ke bin idanunta suna diga a duk inda suka samu zarafi kama daga gaban hijabinta har kan hannunshi dake cikin nata. "Mummunan mafarki kake? Sannu ka ji? Bari na kawo maka ruwa" Duk ta rikice tsabar yadda ta ganshin ya dameta, da sauri ta nufi frigde ta kawo mishi ruwa da kyar ya miƙe zaune ya ɗan yi tapping wayanshi ya kalli time karfe biyu, lumshe ido yayi ya buɗe a kanta tana miƙa mishi ruwan, bai san me yasa ya karɓa ba ya dai tsinci kanshi yana shan ruwan yana jin wani abu dake tsaye mishi a makoshi na sauƙa a hankali, sai kuma ya ji cikinshi na murdawa yana jin amai na taso mishi rabon shi da abinci tun jiya da daddare don ko karyawa bai yi ba rashin lafiyar mami ya riskeshi, ruwan ya miƙa mata tana daga tsaye tana kallonshi har lokacin idanunta na cike da kwalla. Ƙoƙarin sauƙa yake daga gadon ba tare da ya ce uffan ba sai jiri ya kwashe shi ya tafi zai faɗi da wani irin hanzari ta riƙe shi "Ya Saraki baka da lafiya...! Jikinka zafi sossai me kake so in kawo maka?" A karye take maganan, kaman ba zai yi magana ba yana tsaye tana dafe dashi Dukda ya tabbatar in faɗuwar ne ɗan tiny body ɗintan nan bai isa riƙe shi ba a hankali yace "Amai...!" Kalma na farko da ya furta kenan tun bayan Ameen da yake ta cewa in an yiwa Mammi Adu'a. "Amai za ka yi? Sannu mu je bayin ko in kawo maka abu ka yi daga nan?" Shiru ya mata sai ya yunkura zai cigaba da tafiya nan ta gane bayin yake son zuwa da taimakonta ana tafiya ana hutawa suka shiga bayin, sai da ya dafe jikin sink ya kalleta ya kalli kofa. "In fita? Za ka iya?" In ba don halin da yake ciki ba za ta iya rantsewa ya Harare ta, bata ƙara magana ba ganin ya zuba mata idon da suke sake firgitata da bata tsoro ta fice da sauri sai da ta rufe kofa ya lumshe ido. Kai tsaye kitchen nasu taje ta haɗo tea mai kauri ta dawo ɗakin gadon da ya jajjanye bedsheets ɗin ta gyara ta tsaya daga gefe kaman security, ganin ya jima bai fito ba ta yunkura ta nufi bayin tana shirin yin knocking yana buɗe kofan da sauri ta matsa baya, ya kalleta ya dauke kai ganin bashi da ƙarfin jiki ta matso ta kama hannunshi bai hanata ba har suka isa kan couch ya zauna yana jinguwa tare da riƙe kanshi da kaman zai fashe yana cewa "Asshhhh!" Kaman zata yi kuka take jera mishi sannu. Tea din ta ɗauko "Ya... Saraki!" Ta faɗa a rarrabe, ya ɗan buɗe ido ya kalleta yana jin sunan na mishi wani iri har a cikin jikinshi "ka sha tea ka ga cikin ka babu komai sai ka sha magani Don Allah..." Ya lumshe ido kawai fuskar nan tamau, hawaye ne ya zuba mata ta ɗan ja Shesheka sai ya bude idanun yana kallonta ya zubawa hawayen idanu haushi yake ji, takaici yake ji Meyasa shi ba zai yi kukan kaman kowa ba? Meyasa take da arhar hawaye a sadda shi yake nema? Zuciyarshi zafi yake mishi raɗaɗi da kuna yake mishi. Hannu ya miƙa mata don yana da buƙatar yin Sallar isha don bai yi ba kuma ba zai iya samun karfi ba matukar ba abu bane ya shiga cikinshi, da sauri ta miƙa mishi ta koma gefe tana share fuskanta wanda ta rasa me yasa hawayen nata suka ki tsayuwa muddin ta kalleshi sai ta ji suna zubowa tsabar tausayinshi. Kurba bai fi hudu yayi ba ya ajiye, ta dubo magungunanshi ta ajiye mishi ya kalleta tace "Don Allah Ya Saraki ka sha ko zaka samu sassauci...!" A karye tayi maganan yayi shiru "Wanne ne zan cire maka?" Ya sake yin shiru "Ya Saraki...!" "Get out of this room..!" Yayi maganan a kausashe ta girgiza kai za tayi magana ya ce "Nowww!" Da ƙarfi yayi magana yana zaro mata idanu... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* *39* Kuka ta sakar mishi mai sauti ya kawo idanu ya zuba mata yana mamaki a ƙasan ranshi, ganin ta ƙi fita ya sa bai bi ta kanta ba ya ɗauki maganin ya hadiye ya tura mata taje ta ɗauka ta mayar inda ta samu ta sake ja ta tsaya, Miƙewa yayi ya isa wurin Sallarshi ya tada sallah. Bayinshi ta shiga itama tayi Alwala ko kan ta fito ya idar da isha nafilfili yake yi itama ta fara nafilfilin sai uku da wani abu taji ta gaji shima yana zaune ne kanshi da yake jin kaman zai fashe jingine da jikin gado, Miƙewa tayi taje ta kwanta a inda ta kwanta da farko nan ƙasa tana kallonshi zuciyarta cike da tarin tsantsar tausayinshi tana kuma mamakin irin karfin halin da tayi har bacci ya sureta bata sani ba. Karfe biyar da rabi ya buɗe idanunshi ya miƙe yaje yayi alwala, har ya wuce ta kaman yayi fitanshi ya kyaleta sai ya tuna irin kulawar da ta bashi a daren na jiya da irin yadda tayi ta zubar da hawaye akan damuwarshi, ko da Abeeha ce ba zai barta ana sallah tana bacci ba, tsugunawa yayi don bashi da wani ƙarfin magana ya sa hannu ya ɗan ja hijab ɗinta firgigit tayi ta tashi tana kallonshi don baccin dama rabi da rabi ne inda bata saba ba, Miƙewa kawai yayi ya fice bai ce komai ba. Da sauri ta miƙe taje ta yi Alwala ta zo ta gabatar da sallah, bata tsaya doguwar Adu'a sossai ba ta miƙe ta gyara ɗakin tsaf ta share ta saka turaren wuta kan ta fice zuwa babban kitchen, duk abincin da aka ci jiya a wurin makoki order ne daga manyan restuarants yau kuma a gidan za'a girka don haka tana bukatar ganin me zasu yi Dukda ba wasu mutane ne na waje ba kadan da suka Kwana duk na gida ne. Pepper soup ne na cowtail da bread sai tea da suke zubawa flasks flasks daga nan ta wuce wurin Abeeha ta samu idanunta biyu suka gaisa take tambayarta jikinta ko da Abeeha ta tambayi "Ya Yaya Rayyan?" Bata wani damu ba ta ce "Ya fita masallaci" Murmushi Abeehar tayi ɗan kaɗan Allah sarki ta je ta kulan dashi kenan. Shi kam daga masallaci mota ya ɗauka ya fice asibiti su jannah sai ganinshi suka yi, da sauri ta sauƙo ta zo ta riƙe shi zata fara kuka ya rabata da jikinshi ya ja hannunta zuwa bakin gadon ta zauna. "Menene na kukan? Uhmm? Lafiyar ki ya kamata ki yi focusing a kai mun riga mun yi rashi, haƙuri kuma ya zame mana dole ki bar kukan nan" Kai ta gyaɗa tana share hawayen dake silalo mata, bata jin tausayinsu kaman yadda take jin nashi don yana maganan ne kana jin yadda ɗaci dake shimfide bisa zuciyarshi ke hauro wa har kan harshen shi. Ya gaishe da matar uncle Mansur dake ɗakin ɗayar cousin ɗinsu ya gaishe shi ya amsa suna ƙara yi mishi gaisuwa. Sai da yaje wurin bills aka tabbatar mishi mijinta ya biya komai ya dawo ya nemi da su zo su koma gida tunda ta ji sauƙi, tattara wa suka yi ya ɗauko su har gida ya shiga ciki ya duba Abeeha a lokacin Afeefah bata nan, ko da zasu fara kuka ganin juna faɗa ya hau su dashi dole suka yi shiru ya gaisa da iyayen da suke ciki kan ya miƙe ya nufi sashensu har lokacin kuma kanshi kaman zai rabe amma juriyarshi ya hana shi kwanciya. A tsakiyar parlorn suka haɗu ta fito daga ɗakinta sanye da doguwar riga mai faɗi sai karamin hijab da ya shiga da kayan, ganin shi ya sa ta dake tare da danne tsoron ta ta furta "Ina kwana Ya Saraki? Ya jikin?" Da ɗan hanzari tayi maganan ganin zai wuceta. "Lafiya" Ya amsa kan ya wuce ya shige ɗaki, zama tayi don ta san kila yanzu wanka zai yi sai da ta ɗauki awa kan ta miƙe ta nufi dining ta haɗa mishi tean ta ɗauki bowl ta dibi pepper soup ɗin ta haɗa a karamin tray ta nufi ɗakin, ya yi wanka manyan kaya ne a jikinshi kaftan baƙar yadi mai taushi da ya sake fito da ainihin hasken fatar shi sannan ramarshi ma ya bayyana, a kan couch yake zaune yanzu ma yayi relaxing sossai idanunshi a rufe, waya ya gama yi da likitarshi bata nan ta samu labarin rasuwa hankalinta ya tashi roƙon shi take akan ya samu ya zubar da hawaye yayi leting damuwarshi fita ko kaɗan ne in ba haka zai iya samun matsala ya dai mata shiru ne amma bai san ko zai iya ba yana son yin shima ko zai samu sassauci amma taurin ranshi na dayawa, kuma hakan na da alaƙa da training da ya samu a farkon rayuwarshi. Shigowar ta bai sa ya buɗe idanu ba har ta ja ɗan table ta ajiye mishi tray ɗin ta tsuguna "Ya Saraki..!" Har ranshi ya ji sunan, bai san Meyasa duk ta kirashi hakan sai ya ji kaman an kirashi ba kuma dole zuciyarshi take motsawa ta wani ɓangaren kuma sai yaji kaman Mammi ce ta ƙira shi, dole ta sa ya buɗe idanu ya kalleta ta sauƙe nata ƙasa don ba zata iya jurar kallon cikin idanunshi ba ko a yana ƙalau ma bare yanzu da suke a birkice. "Ga abin kari nan na kawo maka, Don Allah ka ci ka samu ka sha magani." Idan dutse ya tanka to ya tanka, jin shirun yayi yawa ta ɗaga ido ta kalleshi yana lumshe da idanun abin shi. "Don Allah dai ka ci Ya Saraki! Ko babu daaɗi ka lallaɓa ka ci ko kaɗan ne a yanzu ba mu da wani majingina bayan kai, ko da ni bana buƙatarka su Adda Abeeha suna da buƙatarka bare ma dukkanmu kaine bangon mu a yanzu ba za mu so ganin komai ya same ka ba a wannan gaɓar da bamu warke raunin tafiyar Mammi daga rayuwar mu ba.." Muryarta ya shiga rawa hawaye ya shiga silalo mata. Sunan Allah yake ƙira a hankali "Ya Allahu!" Kalaman sun dirar mishi da wani rauni da baya tunanin ya taɓa jin irin raunin zuciyarshi na rawa sossai, yadda ta furta cikin kuka ya sa yaji idanunshi kaman za su iya kawo ruwa muddin ta cigaba da irin waennan kalaman cikin sanyin murya da Salon karya zuciya. "Ki je zan ci!" Ya faɗa a hankali, bazata taji kalaman kuma hakan ya sakata jin daaɗi tunda ya yarda zai ci ta miƙe ta kawo mishi magungunan shi kusa kan ta fice sai da ta fita ya buɗe idanu ya zubawa kofan da ta rufe sama da seconds goma kan ya ɗauke ya mayar kan abincin, ya kuwa sha pepper soup ɗin mai yawa ya sha tean tare da magani ya ajiye ya miƙe ya koma kan gado ya kwanta don jiri yake gani a cikin maganin akwai na saka bacci ko da bai so ba dole baccin ya ɗauke shi dama ya saba ko da zai sha da daddare baya iya bacci amma in da rana ne yana yi ba tare da mugun mafarkin shi ba. **** "Malam Labaran Haƙƙin uba zuwa ga 'ya'yansa yana da matuƙar muhimmanci musamman a musulunce, wannan haƙƙi yana tattare da nauyin kulawa, tarbiya da tabbatar da rayuwa ta gari ga 'ya'ya ciki sun haɗa da: Samar da halal ɗin haihuwa wannan ba sai na yi dogon jawabi ba na san ka fahimta ya kasance an samu wannan yaro ta hanyar aure kaman yadda addini ya tanadar. Alhakin samarwa yaro suna mai kyau da ma'ana wadda bai sabawa Addini ba. Ciyarwa da sutura uba na da nauyin ciyar da 'ya'yansa da matansa daidai gwargwadon iko, hakanan da saya musu sutura da tufafi daidai gwargwado. Ga babban wato ilimi da tarbiya, koyar dasu abubuwan ibada sallah, azumi da sauransu. Samar musu da ilimin zamani da horo da zai sa su zama masu amfanar da kansu da al'umma. Ka ga tarbiya a kan hali ba karamin alfanu yake da shi ga yaranmu ba dole ne akanka ka basu horo a kan gaskiya, amana, girmama manya da kyakyawar mu'amala da mutane. Suna da alhaki akanka na basu kariya da tsaro hakan ya haɗa da hana su mu'amala da miyagun abokai ko dabi'u kaman su shaye-shaye, fasikanci da sauran su. Malam Labaran uba kan zama abin koyi ga ɗa wajen addini, hali da mu'amala ina so ka yi nazari a iya tunanin ka matsayinka na uba kuma miji me ka sauƙe a cikin waennan?" Inna Larai ta numfashi "Wallahi malam liman ina ga bayan hakkin farko na samar da su ta hanyar aure babu abin da Malam Labaran ya sauƙe ciki ko haihuwa aka yi mutumin nan baya ragon suna." Inna Asabe da kanta ke ƙasa tace "Mun samu tawaya sossai saboda rashin ilimi da rashin sani gashi mun lalata rayuwar 'ya'yanmu" Malam Labaran yayi shiru jikinshi a sanyaye kenan shi fa Allah zai kama da laifi? A hankali yace "Toh malam liman wani hanya za mu bi mu gyara abin da muka ɓata tun farko? Hakikanin gaskiya ina samun abin da zan iya rufawa kaina asiri da gidana amma son zuciyata ya sa nake kyashin sayowa in kawo, kowa ta kanshi yake kaman rayuwar bariki hatta sutura wannan na manta rabon da in saya ma kowa a gidan, Dukda ina kallonsu da suturu da ma wasu ababen ƙawa amma ban taɓa tambayar ina suka samu ba sai ma fata nake in ga nasu in kwace ko in sace...kaico kaico da wannan rayuwar jahilcin" Hawaye ne ya zubo mishi don sai a yanzu yake fahimtar irin illar da jahilci yake dashi, ga yaran duk sun lalace ya tabbatar babu mai auren su a tunaninsu Afeefah ce ba zata auru ba saboda yadda tayi tambari a garin sai gashi ta auri wanda kaf kauyen basu da kamarsa, haƙiƙa yayi matukar nadamar abubuwan da yayi tayi a baya na tsantsar rashin ilimi. "Hanya ɗaya ne jal kuna raye lokaci bai ƙure ba, ayi Adu'a a nemi yafiyar waenda aka zalunta babban hanyar shine a nemi sani akan addini." Nasiha ya cigaba da yi musu mai ratsa jiki sai gashi duk jikinsu yayi wani irin sanyi, inna Larai dake fama da azabar kafa kawai ta kama kuka, lallai Allah mai girma ne kuma baya abu kan kuskure hassada da bakin ciki akan rayuwar Afeefah ya ja ta jefa kanta da kanta ga halaka. Anan aka saka kawu Labaran mayar dasu dakunansu, inda ya nemi zai dinga zuwa daukar karatu masallacin da malam liman ke koyawa kowani bayan Magrib haka zai yi kokari ya ga ya sauke duk wani hakkinshi amma bai san inda zai ga Afeefah ba. "Za ta zo ne! Dole zata neme ku don ku ne dolenta" Kanshi ya duƙar ba tare da ya yarda da zata zo ɗin ba don su kaɗai suka san irin cutarwan da suka yi mata. **** Samha ce zaune da Abeeha bayan Magrib tana ɗan janta da hira yayinda jannah ke kwance akan gado idanunta a lumshe Afeefah tayi sallama ta shigo ɗakin. Idanu suka hada da Samha, sai tayi kaman bata santa ba ta ɗauke kai ta nufi wurin jannah "Addah jannah sannu, ya jikin? Akwai abin da kike bukata ne?" Ta girgiza kai "Babu, bacci ma zan yi yanzu ki huta da zirga-zirgan nan haka please tun safe kece nan ke ce chan baki huta ba" Afeefah ta ɗan murmusa kadan Dukda ta gajin iya gajiya rabon da tayi irin wannan wahalar ma tun Dutsen-wai, ita ce kitchen ita ce kaiwa mutane abinci da sauran dai duk wani zirga-zirga da za'a rike mutum a gida a yayin hidima ko ta aure ko ta mutuwa. "Shikenan Addah jannah, Allah ya kara sauƙi... Adda Abee Allah ya bamu alkhairi wanka zan yi na kwanta" "A huta gajiya Afeefah sannu" Tayi murmushi kawai ta juya ta fita. Samha da ta zuba mata idanu tun shigowarta gabanta na wani irin faɗuwa tana sake kallon irin sauyawar da tayi da kyaun da tayi ga kamshi kaman wacce ta tsumu ta tashi cikin arziki ta miƙe tsaye tana kallon Abeeha "A..Abeeha wanchan ba Afeefah ba?" "Kin santa ne?" Abeeha tayi tambayar kaman bata san labarin komai ba. "Afeefah Afeefah...!" Sai ta rasa wani kwatance zata yi da Abeeha zata gane "Afeefah dai wacce ta fito daga wani kauye wai shi Dutsen-wai?" Abeeha tace "kila kama dai, wannan Afeefar kaman sister take a wurin mu kuma ita ce matar Yaya Rayyan" Wani irin kallo Samha ke mata zuciyarta na bugawa da ƙarfi ko a mafarki ta ganta zata gane ta, Afeefah ce ta koma haka? Wait Afeefah ce take auren Rayyan? Rayyan fa! Kwakwalwarta ya kasa ɗaukar wannan zance za ta yi magana Sameera ta shigo "Samha mu tafi tun dazu Yaya Saleem ke faɗan mun ajiye shi" Bata tsaya jiranta ba ta fice, Abeeha tace "Ki je kar yayi faɗa, mun gode sossai fah sai da safe" Ta ɗauki Jakarta ta fice zuciyarta fal mamaki da saƙe-sake to ko bata gane Afeefar bane? Kai dole in sun zo gobe ta nunawa mommy da su Sameera ita ko ita ce bata gani da kyau ba haka ta danne maganan ta kasa yi da kowa har suka bar gidan zuwa gidansu akan gobe ma zasu shigo. Ita kam Afeefah ko tsayawa tunaninsu bata yi ba dama damuwarta Saleem ne kuma fahimtar ya dawo daidai hankalinta ya kwanta don haka bata da wani issue da su, wanka tayi ta nemi cotton peach kayan bacci riga da wando dogo ta saka sai da tayi isha ta yi shafa'i da wutiri ta miƙe ta kashe komai na ɗakin ta ɗauki wayanta ta fito gabanta na faɗuwa, rabon da su hadu tun safe da ta bashi abin kari don da rana yana parlorn waje da su Saleem so a chan aka kai musu abinci basu haɗu ba, bata san ma ko ya ci ko bai ci ba haka dai ta nufi ɗakin tayi knocking tare da tura kofa ta shiga, kallon wurin yayi sai suka haɗa idanu yana zaune akan gadon kafafunshi biyu na cikin bargo bayanshi na jingine da pillow ramarshi ya sake fita ainun. Ɗauke kai yayi chan ƙasan ranshi yana mamakin yadda a yanzu take shigo mishi ɗaki don tsabar neman magana ya kore ta kuma ta mishi kuka bai sani ba ko tare aka gina musu ɗakin ne oho, abin da ke damunshi ya dameshi don haka bai kula ta ba har ta ɗauko bargo ta shimfida inda ta shimfida jiya taje ta ɗauko pillow ta zo ta ajiye sai ta matsa kusa dashi "Ya Saraki sannu! Ya jikin? Kana bukatar wani abu ne?" Ya buɗe ido ya kalleta ta ɗauke kai kaman ba zai amsa ba sai taji ya ce "Da sauƙi" Daga haka bai sake magana ba taje ta ɗauko ruwa ta zo ta ajiye a bedside ko zai buƙata, wayanshi ta gani a kan couch taje ta ɗauko tazo ta ajiye mishi gefen ruwan kan taje ta kashe wutan ta zo ta kwanta ta bar shi da mamakin ƙarfin hali irin nata... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* *Ina Editing ashe ban gama ba bacci ya ɗauke ni. Ku karya da wannan* *40* Ya jima zaune yana kallon figure ɗinta cikin duhun ɗakin kan ya zame ya kai kwance yana sanya pillow a kirjinshi, idanunshi a lumshe sama da awannin da ba zai iya lissafawa ba har bacci ya ɗauke shi a haka ɗin, chan cikin baccin shi ya fara jin abin da yake ji muddin ya rufe idanu da sunan baccin dare ji yake kaman zai mutu, kaman an saka abu ne aka danne mishi kirji numfashinshi ya toshe juye juye yake ya haɗa zufa sharkaf sai numfarfashi yake fitarwa sama sama. Cikin baccinta ta soma jinshi a hankali ta buɗe idanu sai dai jin yadda yake yin yasa bata san ta miƙe ba

Chapter 24 of 40