surutu bata ce musu komai don faɗuwar gaban da take fama dashi kaɗai ya ishe ta, ko da suka bar ɗakin kifewa kawai tayi ta saki kukan da bata san na menene ba, ko abinci bata ci ba tayi kuka ta koshi har bacci ya ɗauketa a haka wuraren bakwai na dare.
****
Shafa fuskar ipad ɗin take da ake nuno hiran tana kuka, tana ganin yadda yaronta ya girma ya zama mutum, tana ganin tarin baiwa da nasaba da Allah yayi mishi tana jin guilt na tauye mishi wannan hakki tun daga yaranta, tana tuna yadda ta zame kafafunta daga cikin hannunshi tana tafiya ta barshi a bakon wurin da bai san kowa ba.... Bata ga laifinshi ba don bai zo inda take ba itama kunyar fuskantar shi take ji kaman ta nitse.
Turo kofan aka yi aka shigo, ta ɗaga kai ta kalli Aisha, Matashiyar kyakyawar yarinyar da ke tsananin kama da Rayyan ɗin ta iso gangarta
"Ammi Meyasa kike son sakawa kanki damuwa har haka? Baya nan kullum kuka da tunani ba ki samu cikakken farin ciki ba ya dawo ma baki huta ba? Gashi shi ko ya damu dake tunda bai tako kafarsa ya zo inda kike ba?"
"Aisha bashi da laifi don bai zo ba, baki san me na aikata mishi bane"
"ko me kika aikata mishi uwa fa uwa ce Ammi don Allah tunda ya bayyana cikin koshin lafiya yana ci yana sha kuma babu abinda ke damunshi ki bar wannan kuka haka ki nemi natsuwar ki"
Da lallami tayi maganan, Ammie tayi murmushi mai ciwo sati uku kenan ko kallonta mai martaba bai sake yi ba bare har yayi magana da ita, ta san tayi kuskure amma su saurare ta kan su yanke kowani irin hukunci, tana kuma ganin Aishan bata san zafin dake cikin Abandoning bane ta tashi gaban iyayenta da gatanta shiyasa take wannan magana amma ita ta san dole sai an dauki lokaci Sameer zai sauƙo.
Karfe shidda ya tashi ya watsa ruwa yayi sallah kan ya kira Abeeha ta ɗauka suka gaisa kan yace
"Me kaman Muryar jannah nake ji?"
"Eh Yaya ta zo ne da shirin tafiya akan gobe kawai sai mu wuce airport daga nan"
"Me zai faru idan goben kuka haɗu airport da ita? Mijin yarinyar nan na sakacin barin matarshi sakaka tana yadda take so fa... Ina Afeefahh?"
Miƙewa tayi
"Bari na kai mata tana ɓangarenku"
"Wayanta fa me ya same shi?"
"Ruwa ne ya shiga sai ya ɗauke Yaya"
Bai ce komai ba chan kuma ya fara ja mata kunne akan su tabbatar basu bar komai da zai iya lalacewa a gidan ba tana amsawa har ta tura ɗakin Afeefah da sallama.
"Yaya ta yi bacci fa in tashe ta?"
Ya ɗan yi shiru yana jin ba daaɗi kaman ya ce eh sai kuma yace
"Kyaleta..amma sallah fa?"
Sai tayi shiru ya fahimta don haka yace
"Shikenan! Da safe za mu yi magana"
Ta mishi sallama ya katse wayan ita kuma ta fice daga dakin.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*48*
Washegari saboda tarin gajiyar da ke jikinshi bai iya ya farka ba tun bayan Sallar asuba sai wuraren karfe sha ɗaya, ko da ya kalli time ya san any moment from then sun kusa isa already Mai martaba ya tanadar da duk motocin da za su ɗauko su daga airport da ma masauki har da abin da zasu ci kan ya zauna da su gabaɗaya yadda ya shirya.
Wannan dalili ya sa kawai ya shiga wanka a natse yake komai cikin sarauta da ya bi jiki, ya fito ya shirya cikin manyan kaya mint green ne yadin mai ɗan duhu ya mishi kyau ainun ya feshe jikinshi da turaruka kan ya fito parlor sai karab idanunshi suka sauƙa akan kuyangi har biyar da suke zaune daga chan kusurwan parlorn bai tanka su ba ya shiga kitchen ya haɗa tea ya fito ya zauna tare da crossing legs nan suka fara kwasar gaisuwa kai ya gyaɗa kan ya yi kiran Gaabɗo yana cigaba da sipping tea din yana karkaɗa ƙafafu.
"Wa ya aiko su?"
"Uwargida Fulani Adama ce ranka ya dade ya baka yawan rai"
Ya amsa
Bai ɗago ba idanunshi na kan waya yace
"Duk su bani wuri ba na son ganinsu ka kuma tabbatar basu sake shigowa sashen nan ba"
Da sauri ya amsa ya juya ya kallesu tuni suka miƙe suka tafi ɗin.
Ba'a jima da tafiyan su ba sai ga kira daga mai martaba dole ya miƙe ya nufi sashenshi, a zaune ya same shi shima ya samu wuri ya zauna ya kwashi gaisuwa
"Mamanka ta kawo min ƙararka, Meyasa ka kori kuyangin da aka tura sashenku? Ka dai san ko kai baka buƙata matarka tana buƙatarsu saboda hidima"
"Basu yi min bane ranka ya daɗe"
Murmushi mai martaba yayi
"Toh shikenan zan yi magana da jakadiya sai ta kawo maka wasu"
Shi dai idan ba don mai martaban ba da ba wata da za'a tura mishi shashe amma bai ce komai ba.
"Baƙinmu za su iya sauka cikin kowani lokaci motoci na nan suna jiransu a Airport da Wambai da shi na wakilta ya tarbe su saboda muhimmancinsu"
Ko kan yayi magana aka fara sanarwar Shigowar Mahaifiyarshi Dukda yadda gabanshi ya faɗi zuciyarshi ya chanza bugu hakan bai sa ya ɗago kai ba kanshi na kasa har ta samu wuri ta zauna ta mayar da kanta ƙasa a hankali hawayenta ke diga bisa kan kyakyawar shimfidar parlorn.
Shiru wurin ya ɗauka kan a hankali Rayyan yace
"Barka da safiya ranki ya dade"
Bai jira amsarta ba ya miƙe zai fice tayi saurin ɗago kai tace
"Sameer...!"
Chak ya tsaya yana jin sunan har cikin ranshi sai dai yana tuna ranar da ta mishi umarnin cewa ya manta da ya taɓa amsa wannan sunan, ya manta ya taɓa sanin su a rayuwarshi.
"Kaico na! Kaicon uwar da ɗan ta ba zai iya ɗaga idanu ya kalleta ba saboda wani tabo da ta samar masa mai wuyar warkewa, Don girman Allah ka dawo ka zauna ka saurare ni, Mai martaba ka yi min alfarmar tsayuwa ka ji uzuri na idan kai kana fushi shi yana fushi wani hali kuke so in shiga? Wani hali kuke so ku riske ni a ciki kan tausayina ya darsu a ranku ku ji cewa za ku iya min uzuri? Ni fa uwa ce ni kaɗai na san irin zafin ɗaukar ciki, rainonsa zuwa haihuwarsa da gayya ba zan salwantar da rayuwarka ba Sameer, da gayya ba zan ƙuntaci kaina tsawon shekarun nan ina kuka da hana kaina bacci wurin roƙon ubangiji ya baka ingantacciyar rayuwa da farin ciki ba... Don Allah ku saurareni ko da sau ɗaya ne"
Tausayinta ne ya rufe mai martaba Dukda haushin ta da har yanzu yake cike a cikin zuciyarshi, wlh in bai ce har tunanin sakinta yayi ba yayi ƙarya kasancewarta macen da ya fara so kuma har abada yake jin sonta daban cikin matanshi bai sa yaji cewa zai iya yafe mata abinda tayi mishi ba amma a yanzu tausayinta ne ya fara rinjagayar fushin, kallon Rayyan da bai motsa ba bai kuma ya dawo ya zauna ba yayi yace
"Ciroma samu wuri ka zauna"
A dole ya zauna ko sau daya bai kalleta ba don idan ya kalleta zai iya jin zafi da raɗaɗin shi ya ƙaru kaman yanzu yake tuna yadda ta jefar dashi aka ce zuciyar yaro babu mantuwa a daidai lokacin da yake jin daaɗin rayuwarshi yake kuma da gatan shi ta zabi mayar dashi marar galihu har ma ana kallon idanunshi ana mishi zancen kila shi ɗin shege ne marar uba! Idanu ya runtse kukanta har ranshi yake ji amma baya jin kukan a matsayin uzuri.
"Ban san ta ina zan fara ba amma na san duk kun san cewa a wannan gida na sarauta aka haife ni amma ban tashi nan ba kasancewar mahaifiyata ta rasu ina da kananun shekaru, na koma wurin dangin mahaifiyata da zama ta yadda duk wani tuggu, makirci ko fuska biyu na gidan sarauta ban sanshi ba, i was a care free person with a pure soul ina rayuwa kaman kowacce mace ba tare da na san akwai alkawarin auren sarkin gobe a kaina ba kasancewar mahaifina Galadima kuma har yanzu gidanmu ke sarautar Galadima, ina da shekaru goma sha huɗu Yaya Maudo ya turo kuyangi na musamman don su fara horar dani zaman cikin masarauta da ma abin da ya kunsa Dukda a lokacin kana da uwargida wacce itama duk jini ɗaya ne tunda daga Makama har Madaki sarautar gidansu ne kuma kun fi kusa kusa sossai don First cousins kuke har gobe idan babu jininka wani daga gidansu yana da damar zama Sarki.
Kana kuma da Fulani Aminatou da aka baka ita daga masarautar Kamaru Dukda Na samu maganganu masu yawa akan masarautar na shigo ne a mace ta uku da shekaru sha shida kachal, kai shaida ne irin wahalar da na sha kafin nayi blending da rayuwar cikinta ban shekara biyu ba ka cike mata huɗu, dukkanmu daga kan Fulani Adama har Fulani Salimah babu wanda ya taɓa ko da ɓatan wata ne, dayawa sun fi damuwa da ita kasancewar ta fi mu jimawa tsawon shekaru kusan goma kuna tare, kwatsam na samu juna biyu an yi farin ciki kwarai kuma babu wanda bai sani ba ana kuma tattalin wannan ciki watanni biyu zuwa uku nayi mummunan mafarki ko da na tashi ciki ya bare duk mun yi bakin ciki amma muka sallamar Allah ne ke bayarwa kuma shi ya karba kayansa abin mamaki sai da na jera ɓari biyar a ƙasa da shekaru biyu, abin ya dame mu duka neman taimako da adu'o'i babu abin da bama yi har na sake samun wani cikin wanda kai ka hana mu fitar da zancen na tafi Mambila ban dawo ba sai da jaririna ɗan watanni har uku kowa yayi mamaki Dukda an zargi hakan don jimawa ta kuma an yi ta kananun maganganu ban damu ba don zuciya ɗaya na ɗauki kowa, abin bakin ciki yaron nan Aliyu na watanni biyar ya ce ga garin ku... Babu wanda ya san halin da nayi going through sama da kai mai martaba Dukda dukkanmu mun san ba haka kawai bane amma muka bar wa Allah kwatsam cikin Sameer ya bayyana wanda daga ni har kai bamu san da zaman cikin ba ma sai da yayi watanni kusan biyar.
Babu irin wahalan da ban sha ba, babu irin ciwon da ban yi ba kaman ba zan rayu ba kaman zan rayu har Allah ya kawo min shi duniya, mun yi Adu'a kuma mun sa idanu da tsaro sossai kasancewar ranar da na haife shi kwana BOƊEJO tayi kukan murna Ganguna suka yini dokawa na maraba da sarkin gobe, Dukda hakan sau uku cikin shekaru biyu na Sameer ana poisoning ɗin shi da fargaba nake kwana nake tashi, kullum damuwata kar a samu nasara a kanshi mai martaba na rokeka sau ba adadi mu nesanta shi da masarautsr nan don ba zan juri rasa shi ba amma haƙuri da Adu'a shi kace mu cigaba da yi ba zaka iya nesanta da shi ba, kowa ya san Sameer ya taso ne kaifi ɗaya ga zuciya da jarumta, tun yana ƙarami ya san menene sarauta kuma ya san makiya da masoya Dukda haka bai tsira ba yana da shekaru huɗu ya ci poison da ya kwashi wattani tara bai san wanene a kanshi ba har mun fidda tsammani Allah ya sauko mishi da waraka ya farka, tsakani da Allah tun daga sannan na saka a raina cewa zan nemi hanyar bullewa don samun ya tsira da rayuwarshi, a haka na yanke kaishi ƙasar Hausawa na san namiji ne zai iya rayuwa kuma zan dawo in ta mishi Adu'a har karshen numfashi na.
Wannan decision da na yanke daga ni sai Drivern da ya kaini wanda kusan amintaccen gidan mu ne da kuma kuyangata Kande da na san har abada ba zasu taba faɗa ba idan ba ni ce na faɗa ba, saboda in tseratar da rayuwarshi ya sa...."
Katse ta yayi yana jin gabaɗaya mood dinshi na sake sauyawa zuciyarshi kaman akan wuta
"Hakan ya sa kika yi mai gabaɗaya da rayuwata wai HAIHUWA DA HANJI ko? Kika kashe ni da raina Ammie... Har yau ina tambayar kaina me nayi da na chanchanci hakan ashe wannan ne dalilin? Idan ba don mutanen kirkin da na haɗu dasu waenda suka zama ba ni da tamkarsu a sanadiyarki ba zan iya cewa gwara na mutu da irin rayuwa cikin tsananin duhu da na yi a baya don bashi da maraba da rayuwa cikin ƙabari, Mahaifina da irin darajar shi da ƙimarshi an kalleni an ce min shege marar tsatso sau babu adadi wasu in ji wasu ban ji ba babu wanda ya fi tsaya min sai da aka hana ni aure saboda wannan dalili, kullum ina wurin likita ban taɓa bacci lafiya na tashi lafiya ba shine rayuwar da kike tunani ya inganta mini?"
Hawayen da ya tarar mishi a idanu ya mayar ya miƙe kawai ya fice daga sashen, Ammie dake kuka sossai sai ji tayi mai martaba ya dafa kafaɗunta ya ɗaga ta sama sai kawai ta rungumeshi tana ci gaba da kuka mai tsuma rai.
"Haƙiƙa kin yi kuskure amma har da laifina ciki, na sani ina da tarin makiya na ciki da waje, na san irin ciwon da kike ji a duk sadda kika rasa cikin ki na kuma san me kika yi facing a rasuwar yar ki ta fari Dukda mace ce, duk jinyar da Sameer yayi tare muka yi kuka amma ban yi tunanin nesanta ni dashi bane ba saboda bana son ya tashi a rago, na so ya san idan ya rayun ma cikin wuya da tsanani abinda yake gabanshi zai fi hakan, na so ya goge ne barazana ya zame mishi tamkar kuda da zai iya bugewa da tafin hannunshi ta inda na so kaina kenan na mance raɗaɗin da uwa za ta iya ji a sadda aka cutar mata da rayuwar da, amma Faɗimatu da sai ki tuna da idan rayuwarshi ya lalace fa? A wanchan wurin da kika ajiye shi zai iya zama ɗan daba, ko ya zama dan ta'adda ko dai ya faɗa wani mawuyacin halin da zai karar da rayuwarshi cikin mugun yanayi wanda duk alhakin zai iya zama a kanki ne!"
"Sai da na bar wurin na fara wannan tunani mai martaba, haƙiƙa na yi ragon azanci wlh nayi nadama daga lokacin bayan kwana biyu da dawowar mu bana iya ko runtsawa gashi kana cikin halin ciwo da damuwa na tura driver sai dai ya dawo ya ce min bai same shi ba duk inda ya duba bai ganshi ba, daga ranar Adu'ata ta koma a kanshi na roki Allah kar ya bar min shi rayuwarshi ta tabarɓare na roki Allah da yakinin zai dubi zuciyata ya raya min shi har ma na samu cikin Aisha ban yi wani farin ciki ba, itama babu wanda ya san cikinta don kowa ya san ina jinya bana zuwa ko ina bana rabo da hijabi da chasbaha sai haihuwarta aka ji, nayi hamdala ganinta mace barazanar ta kuma ya zo min da sauƙi. Don Allah ka gafarceni ranka ya dade! Na tuba"
Ya ja ta suka zauna ya riƙe hannunta.
"Na yafe miki Faɗimatu na yafe wlh, wannan damuwa da kukan duk ya dameni ya hanani sukuni..."
Yayi maganan yana share mata hawayen fuskanta, numfashi mai nauyi ta sauƙe.
"Saura Sameer...!"
Ta faɗa da wani yanayi.
"kar ki damu zai sauƙo ne a hankali, don ma rayuwarshi bata lalace ba Alhamdulillah"
"Ya baka labari?"
Kai mai martaba ya gyaɗa nan ya shiga bata labarin abin da ya faru kabb yadda Rayyan ya bashi labari, tayi kuka sossai ta yi wa Mammi Adu'o'in da bata san iyaka ba, taji kaunar jannah da Abeeha tun kafin ta gansu taji cewa sun samu uwa har sai itama kasa ya rufe mata idanu in shaa Allahu yadda bata bar yaronta yayi maraicin uwa ba suma ba zasu yi ba.
Ta roki mai martaba da ya bata riƙon Abeeha har tayi aure ya ce
"wannan na ga yaron ki ne Fulani..! A yanzu kam bana tunanin zai amince bamu san gaba ba"
Mai martaba ya ce
"Amma ya kike tunani batun Zara'u kuwa? Kin san a yanzu da ya bayyana za'a saka mana ido ne a jira a ga me za mu ce tunda yarinya dai ta riga ta isa aure, kina ganin zai karbi auren?"
"Ranka ya daɗe kai ka karance shi tun daga dawowarshi zuwa yanzu na dai san shi tun yana ƙarami da kafiya da taurin kai ban san ko ya chanza a hakan ba amma zan roki wani alfarma, ko da ya amince Don Allah batun jiyan matarshi da ka bani labari a barshi a rufe kaman yadda shima ya roke ka, mu ne kadai ke da alhakin sani a yanzu labarin na fita babu kananun maganganu da ba zaka ji ba, hakan zai iya zame mata barazana a zamanta cikin masarautar nan"
Ya gamsu kuwa, su basu wani damu da jiyanta ba don sun yarda Mammi bata mishi zaɓen tumun dare ba kuma tunda ta gamsu da ita suma sun gamsu.
Miƙewa Ammie tayi
"Zan je na zaɓi kuyangin da zan tura musu da kaina, kuma zan tabbatar da cewa ba'a samu kuskure a hakan ba"
Ya gyaɗa kai
"Ki kwantar da hankalinki da fushin shi zai sauƙo with time musamman idan macen kirki yake dashi na tabbatar ba zata barshi ya cigaba da fushi dake ba nima kuma ba zan barshi haka ba"
Tayi murmushi ta gyaɗa kai kan ta fice.
Ta isa sashen kuyangi da kanta ta nemi kande ta nuna mata jikokinta ta zaɓi guda biyu da kuma ɗiyar wata Kuyangarta sa'ade ta tura su sashen Afeefah da sunan sune nata amintattun kuma ta tabbatar ba zasu cutar dasu ba, bata ma isa sashen ta ba ta samu labarin isowar baƙin masu muhimmanci.
Ko da isowarsu Rayyan na tsaye a harabar masaukinsu inda ya tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata kuma masauki ne mai kama da apartment da babu wanda zai takura wani komai da komai akwai intact, hannayenshi harɗe a kirjinshi ya zubawa motocin idanu kawai yana so yayi tozali da ita ne ko zai samu sassauci, yadda yaji kewanta musamman a yau da ya san tana zuwa gareshi Allah ne kadai ya sani, kaman kuwa ta sani ita ta fara buɗe side ɗin da ke fuskantarshi ta sanyo kafa waje ta sauƙo, lumshe idanu yayi yana jin wani chill abu na ratsa shi daga inda yake tsayen, sanye take da wani 2 in 1 Abaya fari da ja da ya mugun amsarta.
Gyalen mai bakin lace ne sai ta kawo lace ɗin Goshi kan ta zagaye sauran ya bar dankunnayenta Red colour fashion waje amma wuyanta ruff yake a rufe, hannunta jan jaka haka takalmin kafarta ma Red ne sossai ya shagala da kallonta sam bata lura dashi ba, ta riƙe kofan Jannah ta sauƙo tana tsokanarta akan ta rufa mata asiri kar a ga Gimbiya na buɗe mata kofa a zane ta ita kuma tana dariya tayi mishi kyau kwarai zuciyarshi sai motsi yake, da kyar ya iya kawar da kanshi ya mayar kan su Uncle Musa kan ya nufe so ba tare da ya bari ya sake kallonta ba don urge na jin ta jikinshi yaji yana ji kallon kawai ya mishi kaɗan, yana so yaji ni'imtaccen kamshinta a hancinshi, yana so yaga tana kallonshi da wannan tsoron a idanunta mai maiƙo idan ta tara hawaye, yana so yaji tana mishi magana a karye cikin tsoro da ya zama Shagwaɓa ko jan hankali a wurinshi amma duk ya bar wa anjima.
Fuska a sake ya tarbe su, ita kuma sai da ya isa ya ɗan yi hugging Saleem kan ta yi noticing ɗin shi gabanta na ta dukan tara tara don tunda suka shigo gate ɗin masarautar ta rasa natsuwa, kanta har lokacin ya kasa dauka da ita ce matar magajin wannan masarauta mai girman gaske da ƙawa, mai tarin kuyangi, dogarai, bayi da hadimai. Mai dumbin tarihi motocin da aka dauko su ma kawai abin kallo ne sai dai ta ji jikinta ya sake sanyi ƙalau ganin ko kallon inda take bai yi ba.
Gaabɗo ya kalla da sauri ya zube ƙasa
"Allah ya baka yawan rai!"
"Yi wa Uwar ɗakin ka iso zuwa sashenta"
Yayi maganan yana dan kallonta sai suka haɗa idanu, kanta ta mayar ƙasa Gaabɗo ya matso ya zube gabanta don kallon da ya mata ya faɗa mishi ne wacece a cikinsu.
"Lale Maraba da Uwar ɗakina Zinariyar masarauta mai daraja fiye da tagulla.. Maraba da hasken Masarauta mai haske tamkar farin wata... Sannu da isowa Gimbiyarmu Gatan Fada! Gimbiya mai rairayi cikin gaskiya...maƙi gani sai dai ya kau da idonsa hasken rana kike hannu baya karewa.. Allah ya ja da zamanin hasken zuciyar Ciroman duk duniya!"
Duk sai ta rikice ta rasa ma me zata ce ta gigice ta kamo hannun Abeeha ta riƙe.
"Barkanka dai!"
Ta faɗa cikin rawar murya, Abeeha da Jannah sai dariya suke danne wa don tuni Rayyan ya jagoranci su Uncle sun shige ciki, yadda Afeefar duk tayi wuri wuri ne na rashin sabo ya saka su dariya shi dai cikin ladabi yayi gaba suka bi shi wasu dogaran suka ɗibo kayakinsu har zuwa sashenta.
Kuyangin na zaune sai ga su duk zubewa suka yi suka fara miko gaisuwa ita Afeefah kuka ne kaɗai ya rage bata yi ba, Jannah ce tace
"Wacece shugaba a cikin ku?"
Suka nuna sa'ade
"Nuna mana ɗakin uwar ɗakin naku tana so ta huta"
"An gama ranki shi dade"
Ta miƙe don da suka zo suka sanar da mahaifiyar Ciroma ce ta turo su Gaabɗo bai hana su ba kuma shi ya nuna musu ɗakunan masu Ɓangaren ɗayan suka kaita yayinda Abeeha da Jannah suka shiga daya don su yi wanka su dan huta.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*49*
Bayan sun yi wanka suka fito parlorn, sun samu an jere musu abinci gashi nan kala kala suka zauna Afeefah na shirin serving ɗinsu ɗayar hadimar tayi saurin karɓa
"Ranki ya dade duk wannan ba aikin ki bane"
Shiru tayi tana kallon ikon Allah har ta gama serving ta koma chan gefe ta zauna.
"Ni kam ina ganin ikon Allah"
Sai lokacin ta tanka, Jannah tace
"Ina baki labari kina ganin wasa nake yarinya, kin san ina karanta royal stories sossai wannan kadan kika gani"
Abeeha tace
"Ni fa in na samu irin gidan nan miƙe kafa zan ko wanka sai an min"
Jannah ta maka mata Harara
"Daaɗi na dake ragwantaka, kar ki sa in miki adu'ar aure inda za ki ɗora tukunya lamba goma"
"Allah ya kiyaye ya kyauta wlh"
Ita dai Afeefah dariya take musu chan tace
"Ni dai kin san Allah duk waennan abubuwan basa burgeni, ni fa na fi so in yi rayuwata ba takura amma yanzu duk jina nake wani iri wlh"
"za ma ki saba ne yarinya"
Suna yar hirar su har suka gama suka dawo cikin parlor.
"amma fa sashen nan naku wlh ya haɗu ƙarshe, ni kayakin nan ma na kasa tantance irin masifar tsadarsu ji kujera kaman bread tsabar taushi"
Abeeha tayi maganan Afeefah tace
"Kema kenan da kuka saba yawace yawace har kasashe ni ko da na shiga bayi sai da nayi kauyanci, wai ni Afeefah ce cikin masarauta har wani zube min ake a ƙasa abin nan ya kasa fita a raina"
Jannah zata yi magana sai suka ji sallama.
Dukkansu kofan suka mayar da hankali wata doguwar matsakaiciyar macece mai cike da kamala ta shigo sanye da rantsatsen alkhyabba fari tass daga ka ganta ka ga mulki fuskarta dauke da fara'a bayanta wasu 'yan mata biyu ne sanye da dogayen riguna suma kyakyawa don duk ruwan Fulani garesu.
Kallo daya suka yi mata suka hangi kamanninta da Aliyu kan ma suyi magana kuyangin ta sun zube suna kirarin da ya sa suka fahimci wacece Dukda Sameer suka ji ake kira.
Dukkansu suka yi yunkurin kaiwa kasa don gaisheta tayi saurin rike Abeeha da Afeefah ta ɗago su kan ta ɗago jannah duk ta rungumesu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 40