Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai fatan Allah ya basu zaman lafiya. 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *24* Da misalin ƙarfe ɗaya na dare ta jefar da mayafin kanta tare da dira daga saman gadon tana jan tsaki, me salim ke nufi ne? Babanta ya tabbatar mata shirin da aka yi akan shi ba mai sauƙi bane da zai iya resisting amma me ya faru har yanzu bai shigo ba? Ɗaukan maganin da Gaje ta bata a gefen bedside tayi ta jujjuya "To bai ma zo bama bare in sha wannan ɗin" ajiyewa tayi ta janyo wayanta kaman ta ƙira su Gajen kuma sai ta fasa ta nufi parlor, kasancewar sashen nashi ɗaki daya ne da parlor sai kitchen in har dai ya shigo to ba zai wuce yana parlorn ba sai dai idan a waje zai kwana. Shi kuwa salim tun karfe tara ya shigo gidan yanayinshi baya mishi daaɗi sam, fuskarshi babu walwala haka ya tura kofan da sallama ya shigo, yana taka door mat ɗin ya ji kanshi yayi wani diimmmmm jiri na shirin kwashe shi a hankali ya furta "Subhallah!" Ya tsaya a wurin sama da mintuna biyu kan ya sauƙe numfashi ya nufi three seater ya kwanta hannunshi dafe da goshinshi, duk yadda zai yi ya samu sauki ya yi sai dai wani irin tension yake ji, sai juye juye yake Sabrina da a chan ƙasan ranshi ya san bai damu da ita ba sai kai komo take yi a ranshi, bai san adadin lokacin da ya dauka ba shi ba mai bacci ba shi ba ido biyu ba, ko matse shi zaka yi ba zai ce maka ga abin da ke damunshi ba sai jin Fitowar ta yayi. Ganinshi ya sa ta nufe shi. "Ya salim dama ka shigo? Shine kayi kwanciyarka anan ina chan duk tsoro ya rufe ni?" Bai ce komai ba sai ido da ya ɗan zuba mata. "Ka tashi mu je ka kwanta a ciki idan baccin ne ma" Ta faɗa tana riƙo hannunshi, kasa mata musu yayi haka ya bi bayanta kaman rakumi da akala, a bakin gado ta ajiye shi ta shiga rage mishi kayakin jikinshi, wani sashi na zuciyarshi tsantsar mamaki yake na wannan bushewar idon wani sashen kuma na faɗa mishi ba laifi bane, har ta gama cire mishi kayan shi dai bai tanka ba kuma bai motsa ba, hannunshi ta ja wai tunda ba ya jin daaɗi su je ta mishi wankan, tana tura shi bayi ta dawo da baya ta sha wannan maganin da gaje ta bata don ta tabbatar mata yana kusantarta da maganin babu kuma wani abu da zai gane, babu wacce zai gani nan duniya bayan ita. Tun daga chan cikin bayin zancen ya sauya, ita ce ke jan ragamar komai kaman ba amarya ba har dai ta samu nasara a kanshi Dukda ita ce tayi kidinta kuma tayi rawanta abinda zuciya bata so gangar jiki ko an tilasta ta ba zata ba da abinda ake so ɗin ɗari bisa ɗari ba, shi dai ya san bayan nan bacci mai nauyi ya ɗauke shi tana kwance jikinshi tana zabga murmushin nasara. Washegari da kyar ya iya tashi yayi sallah a makare, yana zaune kan sallaya idanunshi na zube a kanta tana ta baccinta, duk ya rasa me yake tunani ko me yake ji kaman an yi blocking kwakwalwarshi da daidaitacciyar tunani, knocking da ake ta yi shi ya ɗaga shi daga wurin ya nufi kofan ya buɗe Samha ce. "Ina kwana yaya?" Kai ya gyaɗa bai ce komai ba. "Gashi in ji Mommy wai in kawo muku" Karɓa kawai yayi ya juya ya koma, ta tsaya tana kallon kofan for seconds kan ta tafi. Shirya abincin yayi kan ya nufi cikin ɗaki ya nufi bakin gadon ya shiga bubbuga hannunta. "Sabreena! Sabreena!!" "Uhmmmm" Ta faɗa cikin baccin tana haɗawa da tsaki "Wai menene?" "Kin yi sallah?" Ta sake jan tsaki kan ta buɗe idanu tare da Miƙewa zaune "Ka san gajiyar da nayi? Ai koyaushe na tashi zan yi Sallar yanzu ka tashe ni sai in yi ciwon kai ai" Da mita tayi maganar. "Ai in sallah bai tashe ki ba yunwa zai tashe ki, ga abinci chan ki fito mu karya" Yana kai nan ya miƙe ya fice yana ji kawai ya gamsu da something is off with him amma ba zai iya pointing menene ba. Sama da mintuna arba'in sai gata ta fito shirye cikin wasu riga da wando masu fadi, yana zaune yana jiran ta ganinta sai ya fara kokarin sanya musu abincin bata hana ba ya saka plate ɗaya zai saka wani ta riƙe hannunshi "Wannan ma ai zai ishe mu Ya salim mun riga mun zama ɗaya ai ko ba haka ba?" Kai ya gyaɗa yana zame hannun nashi ya ɗauki spoon ya saka, ita ta haɗa musu tea tana wani irin murmushi. Tun daga wannan rana saleem sai da ya kwana bakwai bai fita ko ina ba yana tare da ita, wani lokacin haka za su yini duk abinda tace zai gyaɗa kai kuma zai iya yi mata amma ba zai yi magana ba, itama kuma tana abunta da taku ne, ko sau ɗaya basu sauka sun gaida Mommyn ba suna gida ɗaya abinci kuwa safe rana dare daga wurin mommyn ake turo musu, wayanshi ma kashewa tayi kar ma a kira shi don dama ya ɗan samu hutun aiki. Yau mommy na zaune a parlor tana mamakin wannan sabon hali na Saleem kasa shiru tayi ta kalli Sadiqa tace "Yayanku kam duka cikin daaɗin auren ne za'a kwana bakwai muna gida ɗaya bai iya lekowa ya gaishe ni ba? Daga shi fa har Sabrinar tunda aka haura da ita ban ga keyarsu ba" Sadiqa tayi murmushi "Ai za ki musu uzuri Hajiya mommy kin san sabon shiga, amma na san dai duk yadda ake ciki yau kam kila su sauƙo kin san har da gajiya duka na hidima ya tarar musu" Samha dai bata gamsu ba amma ganin mommy bata sake cewa komai ba sai itama ta share. "Amma mommy ba kya tunanin akwai abin da yake damun Sameera? Yarinyar nan duk ta zama kaman ba ita ba don damuwa?" "Toh Sadiqa ya zanyi? Na yi tambayar duniya ta ce babu komai kila ku in kun saka ta gaba zata faɗa muku damuwarta" Sadiqa tace "Wlh ni dai ta ƙi faɗa min ban san ko Samha ba" "kawai karatu ne fah! Kin ga tana ta shirin shiga final year abin babu sauƙi" Ba wai sun yarda ba suka bar maganan, Sameeran ce ta fito ta zauna za tayi magana suka ji motsin takowa kaman ana saukowa daga stairs duk ido suka zubawa staircase ɗin sai ga Sabrina da Saleem suna jerowa idanunshi na kallon ƙasa yayin da take murmushi mai faɗi har tsakiyar parlorn suka zo bai ɗago ba, ganin zai fice mommy ta miƙe tsaye "Saleem" Waigowa yayi ganinsu ya ɗan shafa kai "Oh mommy ashe kuna nan, barka da safiya" Speechless ta zama ta kasa furta ko A, Sabrina ta kalleshi "Kayi sauri don Allah Ya Saleem idan ka dawo za'a yi gaisuwar" Ba musu ya juya ya fice, ta juyo tana murmushi ta zo ta samu kujera ta zauna "Mommy barka dai Fatan kina lafiya?" Ido kawai suka zuba mata, da kyar mommy ta kawo musu uzuri a ranta ta zauna tana cewa "Lafiya ƙalau ɗiyata ya zaman sabon wuri?" "Lafiya ƙalau mommy ai ba wani sabunta da yake duk gida ne kuma yayan yana kula da ni yadda ya dace" Kai mommy ta gyaɗa, samha da Sabrinar take sa'a da ita tace "kin tashi lafiya?" Murmushi tayi "Lafiya ƙalau ƙanwar mu" Harara ta maka mata Sabrinar tayi wani murmushi tana kallon su sadiqa tana jira su gaisheta. Mommy ce ta musu ido duk suka gaisheta ta amsa kuwa hankali kwance ita matar yayansu "Mommy kin ga ya fita yana sauri ko? Wlh Gaje ce bata ji daaɗi ba kuma Bakinta babu taste kwadayi take ji shine na ce ya je ya sayi kayan kwalam sai ya kai musu gidan ya kuma bata kudin magani" Mommy da kanta ya sake ɗaurewa tamau ta zubawa Sabrina ido sabon salo wai gada a kotu yaushe kuma aka fara hakan? "Ah yayi kyau" Abinda ta faɗa kenan, Sabrina ta miƙe "Bari na koma ciki" Tana kai nan ta haura saman ta Barsu da tunanin me ke faruwa? Sai dai babu wanda ya je da nisa saboda mommyn na mata uzuri kuma tana son ta da Saleem ɗin sai suka kama wani hirar daban. **** Yau sunday tun safe Afeefah ke tare da Mammi, hira suke yi kaman 'ya da uwa kafafun Mammin na kan cinyar Afeefah tana ɗan matsa mata take cewa "Mammi yau ƙafafunki sun kumbura dama yana miki haka?" "Yana yi Afeefah, ni kam me ba na gani ne? Yau kam ma na tashi jikin sai a hankali ai ni kaɗai na san me nake ji" Tayi maganan da 'yar haki tana kishingida. "Sannu! Ko zaki ƙara magani?" "Kayya bar zancen maganin nan Afeefah, je ki kira min Yayanku nayi ta gwada layinshi bana samu tun bayan asuba da ya shigo nan muka gaisa ban sake ganinshi ba" Idanu ta ɗan waro gabanta na faɗuwa, Dukda ta san ta inda Sashenshi yake amma bata taɓa gigin shiga ba to me zai kai ta? Yanzu ɗin ma jiki a sabule ta miƙe ta fice daga ɗakin, Abeeha bata nan tun safe taje gidan jiddah za ta raka ta asibiti wai bata jin daaɗi da ko ita zata iya zuwa amma ita har yanzu ganinta baƙuwa a gidan take, ko ba ma haka ba ina zata iya da wannan da ba'a mishi gwanintar? Mutum sai faɗin rai da masifa... Da kyar ta ɗaga hannu tayi knocking kofan parlorn sai dai shiru babu amsa, ta sake yin knocking karo na biyu nan ma shiru, a hankali ta tura kofar da sallama a Bakinta ta shiga yana kishindige very relaxed a cikin kujera, parlorn da hasken shi ba sosai chan chan ba sai tashin kamshi yake, kaman waya yake yi amma ba da wayar da ta saba ganinshi dashi ba gabanshi system ne shima a kunne kaman dai aiki yake yi ya tsaya amsa wayar. Daga ɗan nesa ta tsaya kanta a ƙasa tana jin yadda yake magana wane wani sarki, murmushi tayi a chan ƙasan ranta take raya dole Mammi ta kira shi Saraki don shi komai nashi ya fi yanayi da jinin sarauta, bayan ya gama wayan ya ɗan kalleta ba tare da ya ce komai ba ya ɗauke idanu itama jin shiru ya sa ta ɗago ganin ya gama wayan ta ɗan ƙara taku biyu sai ta rasa me za ta ce. Da kyar ta iya haɗa kalmar sunanshi akan lips ɗinta "Yaya Saraki..." Ɗagowa da yayi ya kalleta ya sa maganar datsewa, bai san ya ɗago ɗin ba don yadda ta kira sunan sossai ya dake shi, bayan Mammi bai yarda ya ji sunan bakin kowa ba amma jinshi a Bakinta sai ya rasa me yake ji ma, haushi ne ko takaici ko bacin rai? Tsam ya miƙe ya nufo ta. Idanu ta shiga zarewa takunshi na tafiya da bugun zuciyarta har ya matso dab da ita yace "Maimaita abin da kika ce?" Shiru tayi ta kasa magana idanunta da suka yi raurau alamun kuka ko wani lokaci ta ɗauke daga kanshi jikinta na tsuma ta ciki, kusan seconds huɗu kan ya ce "Allah ya so ki, da kin maimaita sai na fasa miki baki ke Mammi ce da za ki kira ni Saraki? Wani Yaya Saraki...!" Ya sake maimaitawa yana ɗan harararta. "Me?" Ya faɗa yana dan gyara tsayuwa idanunshi tsamm a tsaye a kanta ko a jikinshi. "Yaya..." Wlh sai ta kasa cewa Rayyan ɗin tayi tsai tsammm sai ma ta fasa kiran sunan da ɗan saurin baki tace "Mammi ce wai ka je!" Ta juya za ta fice yace "Tsaya!" "Ba ni da suna ne? Ko da gini kike magana?" "Innalillahi wainna ilaihi rajiun..." Ta faɗa kaman za tayi kuka chan ƙasa, sarai ya ji ta "Ga musiba tsaye gabanki ko?" Girgiza kai tayi, tsaki ya ja yace "Bar nan" Da sauri ta fice. Sai da ta ganta tsakiyar babban parlor kan ta dafe kirjinta tana sauƙe numfashi, Rayyan na son kasheta da ranta, yaushe ya iya ma dogon magana haka bata sani ba, shi da komai ko oho ne me yasa zai saka ta a gaba yayi ta razana ta! Jiki a sabule ta ƙarasa wurin Mammi "Wai yana zuwa" Zama tayi kawai bata sake cewa komai ba, mintuna basu wuci uku ba sai gashi gaban Mammin kawai ya ƙarasa ya fara taɓa temperature ɗinta, numfashinta baya fita yadda ya kamata hankalinshi tashi yayi, a take yace su tafi asibiti duk yadda Mammin za ta ƙi ya nace ya dubi Afeefah yace ta ɗauko mata mayafi, da sauri taje ta ɗauko duk sai ta shiga damuwa ganin yadda hankalinshi ya tashi, kuma dai a fili Mammin bata yi tsananin da ya kamata ya ɗaga hankalin nashi haka ba, bata zauna ba itama gyalen da ta ɗaura a kanta na Jersey ta warware ta yafa akan doguwar rigar atamphar dake jikinta ta bi bayansu, a gaba ya saka mammin ta buɗe baya ta shiga suka fice daga gidan. Tafiyar mintuna ashirin ya kai su asibitin shi ya sake kama mammin suka yi inda za'a duba ta don ya riga yayi call, tuni suka karɓeta don a yi mata gwaje gwaje a tabbatar da babu abin da ya sake tsananta ko chanzawa. A reception ta zauna idanunta na kan yatsun ta sai adu'ar samun lafiya take yiwa Mammi mata mai kirki da mutunci, macen da ta zame mata uwa kuma garkuwa a yanzu. "Afeefah...!" Da ɗan karfi ta ji an kira sunanta har bata san ta ɗago a razane ba sai... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *25* Sulaiman kaman zai kama hannunta haka ya tsaya gabanta yana kallonta. "Da gaske ke ce? Ashe zan sake ganinki Afeefah? Ina kika shiga? Kin san irin neman da na miki?" Idanunta na sauƙa kanshi ta miƙe tsaye, ganin irin kusancin su ya sa ta ɗan yi taku biyu baya fuskarta a sake tace "Ina nan Dr. Allah ya haɗa ni da mutanen kirki" "Afeefah me yasa ba ki zo office na ba? Me yasa ba ki neme ni ba da mahaifiyar saleem ta kore ki?" Idanunta ne suka cika taf da kwallah a hankali tace "Ban san inda zan sameka bane ban san sunan asibitin ku ba ko in ce ban riƙe ba, ko ma na riƙe ba ni da ko biyar da zan hau abin hawa in ce a kawo ni" Idanu ya ɗan runtse kaɗan ya buɗe da sauri sai ya ga kaman za ta iya ɓace mishi any moment "Ina kika shiga to? Waye ya taimake ki?" "Na haɗu da mutanen kirki sun tallafeni daidai lokacin da na buƙata kuma suna riƙe ni tamkar ɗaya daga cikinsu yanzu haka ina makaranta" "Alhamdulillah!" Zama yayi saboda a lokaci ɗaya daaɗi da baƙin ciki duk suka haɗu mishi, itama ta zauna a hankali ya ce "Afeefah har Dutsen-wai na je nemanki" Da sauri ta ɗago ido suka haɗa idanu ya gyaɗa mata kai alamun tabbaci. "Gidan kawu ka je?" Kai ya gyaɗa cikin nuna damuwa ya ce "Abin da muka tarar ba karamin tsoro ya bamu ba Afeefah, ban so ba, ban san hakan zai kasance ba da ban yi ganganci da kuskuren tafiya da manya na ba" A lokaci daya ta zama very confused sun je gidan kawu? Me suka tarar? Me yasa yaje da wasu?. "ko da ban furta miki ba kin dai san Sonki nake ko Afeefah?" Lumshe ido tayi kalamar na sauka mata wani iri a zuciya. "A lokacin da na samu labarin tafiyar ki i was very disturbed na ɗauka chan gida za ki koma, ko da na koma gida na samu mahaifiyata da labarin ban gama bata ba Abba ya shigo ya ji zancen, dama ya matsu kuma da maganan aurena dole ya haɗa ni da Yayyenshi kuma ya kafa hujja ne da cewa a musulunce ma bai halatta namiji ya fara taran mace ba tare da sanin iyayenta ba.. Dole ta sa muka tafi tare da su ba don na so ba" Hawaye ne ya zubo mata a kan fuska ta ɗan yi murmushi mai yanayi da wani ciwo a ƙasan rai ta ce "Sun ji kunya ko? Na tabbatar ba su amince maka ba kuma ba za su taɓa amince maka ba..! Ka yi haƙuri, da na san za ka aikata hakan da ni da kaina na faɗa maka wacece ni kafin ma ka je" Ya ɗan haɗiye wani abu mai ciwo a hankali yace "Afeefah sun yanke min hukunci mai girma a yanzu haka ina da aure, an ɗaura min aure last week saturday amma har yanzu zuciyata ke take so, ke take marararin rayuwa da ba wata ba. Na haƙura na karɓi auren ne saboda ban san inda zan ganki ba ban san inda zan sameki ba, a ina ne gidan da kika koma? Idan kin ga da takura za ki iya dawowa wurin Umma na tabbatar ita me riƙe ki ce tamkar ɗiyar da zata haifa a cikinta" Rayyan ne ya fito sai idanunshi ya faɗa kan su, a kan hawayen dake bin ƙuncin ta ya ɗan tsayar da idanun kan ya ɗauke kai ya zo ya wuce su kaman bai gane su waye ba, Afeefah da suka haɗa ido ta sa hannu ta share hawayen fuskarta ta dubi Sulaiman "Zan tambayi Mammi zan zo in gaishe Da Umma! Amma batun soyayya don Allah ka ajiye shi a gefe Dr. Kai fa ka gayamin irin abubuwan da Kawu ya muku na ba da kunya, taya za ka yi convincing iyayenka su sake komawa irin gidan chan?" "Zan iya Afeefah kawai ki ba ni dama!" Ta girgiza kai "Aurenka fa?" Zai yi magana ta ce "Ka yi haƙuri Dr. Yanzu ba lokacin wannan maganan bane marar lafiya muka kawo" Shigowar Abeeha da Jannah ne ya sa ta ƙarasa share fuskarta ta ƙirƙiro murmushi ta saka, suka ƙaraso kusa da ita "Afeefah ya jikin Mammin?" Ta ce "Da sauƙi sossai amma tunda Ya Saraki ya shiga da ita ba'a fito da ita ba" "Amma Yaya Rayyan ɗin yanzu muka wuce shi a waje yana waya" "Eh shi kadai ne ya fito" Gaisawa suka yi da Dr. Sulaiman yana mamakin jin ana ambaton Rayyan, gidan su Rayyan ta koma? "Afeefah ko zan iya samun Layin da zan yi magana da ke?" Ya faɗa yana kallonta, kallonta Abeeha tayi sai ta ɗan yi murmushi tace mata "Dr. Sulaiman kenan!" Shima ta juya tace "Yayyena ne Addah jannah da Adda Abeeha" Murmushi yayi lallai Afeefah ta samu wurin zama idan har ta sake da ahalin haka sun zama tamkar jininta ya tabbata ba zata iya barin su ta dawo wurin ummanshi ba yadda ya ci buri. "Dr bamu natsu ba har yau bamu samu mun je mun sayi waya ba, bari na baka layina za ku iya dinga gaisawa kan ta samu nata" Godiya sossai yayiwa Abeehar, ta bashi contact ɗinta ya tafi da sauri ta juyi wurin Afeefah tana murmushi sai ta ga damuwa a kan fuskarta, dafa kafaɗarta tayi "Ya dai?" "Adda wai Shima aure yayi last week saturday" Duk sun ji maganar wani iri amma sai suka dinga nuna mata babu komai kila ba rabonta bane ko kuma Allah ya kaddara za ta zama matarshi ta biyu bata san ta cewa Abeeha ba "A yaushe kenan? Aure last week Adda Abeeha kina tunanin ko shekara daya ne zata amince ya mata kishiya a kusa haka?" "Duk ba mu san tsarin Allah ba, mu yi Adu'a kawai duk abinda ya kaddara daidai ne" Ta gamsu amma har lokacin ranta na suya da abinda kawu ya aikata, kenan akwai ɗan sunnar da zai aureta a duniya kenan? Waye zai yarda ɗan shi ya auri irin ta matukar za su bincika asali da tushenta? Bata san Rayyan ya dawo ya wuce ba chan sai ga shi sun fito da Mammi, duk Miƙewa suka yi suna mata sannu tayi murmushi "Duk rigimar Saraki ne amma jikin nan bai kai zuwa Asibiti ba, Jannah ya jikin naki?" "Da sauƙi Mammi, sannu Allah ya baki lafiya" Ta gyaɗa kai. Idanunta ta kai kan Afeefah dake ta murmushin yake "Afeefah kina lafiya? Na ga damuwa a fuskarki" "Babu komai Mammi sannu da jiki" Kai ta gyaɗa ba wai don ta yarda ba suka nufi mota, ƙin shiga motar Rayyan tayi don wlh tsoron ko motsi take a gabanshi, motar Jannah ta tafi suka haɗu su uku suna hirarsu har gida. A babban parlor suka yi masauki don Rayyan ya riga su isa kuma ya shigar da Mammi ciki ko da ya fito a babban parlorn ya tsaya yana nuna su da yatsa "Ba ku parrots ba? To in ga watan ku ta shiga ciki tana damunta da surutu ko wata taje tana saka ta gaba da kukan banza ku ga abin da zai faru" Yana kai nan ya wuce abin shi basu motsa ba sai da ya ɓace Abeeha da Jannah suka tafa suna sheke wa da dariya, Afeefah na murmushi. "Mutum yayi ta muzurai kaman a filin daga yake" Jannah ta faɗa, Abeeha tace "Ai ke baki ganin komai tunda yanzu kin bar gidan nan da sauƙin ki" Jannah ta girgiza kai "Kema kin san babu wani sauƙi wlh sai dai in ban yi wani abin ba Ya Rayyan bai game shi ba ya je har gidan auren nawa ya zane ni tsaff" Ita dai Afeefah bata ce komai ba idanunshi kawai take gani, a hankali ta ɗan yi murmushi tana girgiza kai. Jannah bata tafi ba sai dare, sun sha hira sun ci sun sha, kuma sai da suka cika Mammin da surutu don yana fita daga gidan suka yi ɗakin suna bata labarin gargadinshi tana dariya ta dubi Afeefah "Afeefah ke ce me kukan banza kenan? Me aka yi miki za ki zo ki min kukan?" "Ba ayi komai ba fa Mammi" "Afeefah ki faɗa min damuwarki wlh ina hangar damuwa a tattare da ke" Kanta ta duƙar Mammi ita uwa ce, uwar ma ta wannan baudadden mutum ai dole ta san expression na kowa. Abeeha tace "Mammi Dr. Sulaiman yayi aure shima ashe" Mammi ta kalli Abeeha kan ta kalli Afeefah tace "Auren ne ya dame ki ɗiyata? Kin ga fa duk abin da Allah ya hanaka ba rabonka bane wanda kika ga kin samu shi ne rabon ki, in shaa Allahu za ki samu miji na nunawa sa'a" A hankali tace "Mammi ba auren shi bane damuwata" "Toh menene Afeefah?" "Mammi bana tunanin zan auru, Musulunci ya yarda a auri mace don kyaunta, dukiyarta ko nasabarta, sannan bincike a aure kaman dole ne a musulunci akwai dangi na ƙwarai da za su je bincike a kaina su yarda su bar ɗan su ya aureni? Mammi kin ji abinda su Sulaiman suka samu kawu suna yi a kan layi? Kin ji abinda aka fada musu a kaina daga shigar su kauyenmu?" Hawaye ne ya tsinke mata ta fashe da kuka tana jin ciwon Taɓon ta da bata tunani har Abada zai gogu. Jannah da Abeeha har sun fara tayata hawaye don idan ka ji yadda take maganan za ka san abin na mata ciwo kwarai da gaske.. "Afeefah zo nan" Mammi ta ƙirata, Miƙewa tayi ta isa kusa da ita Mammin ta ɗora ta akan kafaɗarta tana shafa mata kai. "in shaa Allahu Afeefah sai kin auri mijin da kowa sai ya ji sha'awar kasancewa ke, nagartaccen namiji kuma mai tarin ilimi da baiwa na musamman, kawunki ko mutanen garinku ba su isa sun shafe abin da Allah ya rubuta ba, ko kin manta Allah da kanshi ya faɗa mana yana fitar da mummuna cikin kyakyawa ya kuma fitar da kyakyawa cikin mummuna? Ba fa a suffa ko sura ake magana ba ana magana ne akan hali da ɗabi'a. To ki sa a ranki mijin da Allah ya zaɓa miki yana nan kuma idan lokaci yayi za ki aure shi ba makawa kar ki wani damu kanki kin ji?" Kai ta gyaɗa cike da gamsuwa "Na gode Mammi" "na ƙara ji sai na Buge bakin godiyar" Murmushi duk suka yi don da wasa tayi maganan. ***** Hajiya Hussaina tun fa tana tunanin abin na Saleem da Sabrina wasa ne har ta fahimci da gaske ne, domin yau tana zaune a parlor Sabreenar ta sauƙo ta ɗan kalleta tace "Sannu Mommy" Bata jira ta amsa ba ta wuce kitchen ta samu Talatuwa na

Chapter 15 of 40