Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"Barkanku da zuwa 'ya'yana, Maraba lale da isowa masarautar Fombina" "Mun gode mama" Suka fada duka da murmushi a sadda ta sake su suka zauna tana rike da hannun Afeefah Dukda bata ma san wacece wace ba a cikinsu amma dai duk sun kwanta mata ganinsu hakan "Sannunku da zuwa" Aisha ta faɗa suka amsa da godiya. Zarah tace "Sannunku dai" Itama suka amsa. "Ni sunana Ammi ku daina cewa Mama akwai mamar taku Fulani Adama za ku je ku kai mata gaisuwa anjima, wannan ita ce Aishatu ƙanwar Sameer Yayanku su biyu Allah ya bani kan ɓacewarshi sai wannan ɗiyar wurin Makama cousins suke da su Sameer ko in ce Rayyan yadda kuka saba faɗa. Ina fata za ku dauke ni matsayin Uwa da kuka yi rashi gabaɗaya. Allah ya gafartawa Mammi ya kai haske makwancinta" Suka amsa da Ameen kan jannah tace "Ni ce Jannah, wannan kuma Abeeha ita ce kanwata Ga Afeefah ita ce matar Ya Rayyan" Ammi tayi murmushi tana kallonta "Masha Allah, Allah ya cigaba da baku zaman lafiya ya kawo zuri'a masu albarka" kunya ya hana Afeefah amsawa "Da ma na kasa haƙuri ne nace dai bara na zo na ganku, Abeeha duk abin da kuke so ko ya shige muku duhu ku kama sa'ade za ta kawo ku har inda nake ku tambayeni kun ji? Ke kam ma sashe na zaki dawo ba da jimawa ba" Suka yi murmushi ta dubi su Aishatu "Sai ku zauna nan duk abinda basu fahimta ba za ku iya fahimtar da su da kuma bayani akan family Dukda sai a hankali za su san kowa" Suka amsa kan ta miƙe ta fice suna mata sai anjima. Yadda su Aishatu suka kame haka dukkansu suka kame sai hirar ya koma tsakanin junansu kawai ita jannah ma waya take da mijinta yayinda Abeeha ke hira da Afeefah suna yar dariya, kaman daga sama sai ga shi ya shigo. Ko Aisha yau ne suka fara ganin juna dashi face to face, zama yayi a one seater ya kame yana kallonsu daya bayan ɗaya, jannah ta fara gaishe shi ya amsa ta mishi murnan dawowa cikin family Abeeha ma ta gaishe shi. Zarah ce ta gaishe shi ya kalleta yana son tuna sunan "Aammm.." "Zarah" "Oh Yeah lafiya ƙalau" Ya kalli Aisha da ta gaishe shi last itama ya amsa, Afeefah ce ta gaishe shi ya ɗan yi shiru kan ya kalleta sai ya miƙe ya nufi ɗakinshi. Abeeha ta miƙa hannu ta mistineta, kallon jannah tayi sai jannah ta harareta dole ta miƙe don sun cika ta da lectures kaman me akan Rayyan tun fitansu gida har hawansu jirgi zuwa sauƙansu magana ɗaya ake babu abinda basu gaya mata ba akan gidan sarauta sai ta tashi ta kama mijinta a hannu in ba haka ba ta ji a salansa. Ruwa ta haɗa a tray da cup mai tsananin kyau ta ɗauka ta nufi ɗakinshi, yana zaune bakin gado dafe da kanshi dake ɗan sarawa ya ji sallamar ta, bai ɗauka za ta shigo ba sai kuma ya ganta unexpected idanunshi masu shiga jikinta ya kafe ta da su yana yawo lungu da saƙo na jikin nata, tana sanye da doguwar riga peach mai roba ya fitar da duk wani shape ɗinta ta ɗaura dankwalin sai ta sako jelar guda ɗaya ya sauka har kan kirjinta tayi kyau sossai barin ma lips ɗinta dake shining na lip gloss. Ruwan ta zo ta ajiye mishi tana ɗan ɓata fuska, fuskar yake ta bi da kallo bayan ta ajiye ta juya zata tafi karab ya riƙo hannunta ya ɗan ja ta tayi baya baya ta zauna bakin gadon gefenshi har suna gogan juna ya juyo ya kalleta ba tare da ya saki hannun ba. "Haɗe ran nan fa?" Yayi magana yana dan ɗage gira guda alamun tambaya, lumshe ido tayi don maganan ta ji shi ne har cikin zuciyarta. Bata san ta narke ba tayi shiru bata ce komai ba. Kuma sai bai ji haushi ba sai ma kyau da ta mishi yadda take yi da fuskan itama kuma ta ji daaɗi da bai mata ihu ba sai ma Ruwan da ya ɗauka ya sha kaɗan ya ajiye yana dafe Goshi da hannunshi ɗaya har lokacin ɗayan na cikin hannunta yana dan motsawa a hankali. "Ba ka da lafiya ne?" Ya ji tambayar nata sai ya buɗe idanunshi da suka ɗan sauya ya kalleta ya ɗaga mata gira ɗaya "Sorry" "Kin san Meyasa ban amsa gaisuwarki ba?" Ta girgiza kai ashe ya san laifin da ya sakata fushin ma. "Saboda ba haka ake gaisar da miji ba madam..." Kan tayi wani magana ya ja hannun nata sai jinta tayi kirjinshi ya rungumeta ta runtse ido tana jin zuciyarta na chanza bugu, a hankali ta sa hannunta ta riƙe shi yayi baya baya ya jingina da jikin gadon ya ɗan lumshe ido. "Ya kike?" Taji maganan daga sama, ita dai ta rasa gane kanshi so yake sai ya zautata ko menene? "Lafiya ƙalau, ina taya ka murnan reunion ɗinka da family... Na kuma ga naɗi Allah ya taya riƙo" Ya yi murmushi kaɗan kan yace "Ameen, thanks" Suka yi shiru, ƙoƙarin Miƙewa take ya matse ta "Your perfume! Yana da daaɗi" Tayi murmushi "Thank you, gashi na mata ne da na baka" Dole ya saka shi dan murmusawa yadda take maganan bilhakki. Sun dan jima haka kan aka kira azahar ya sake ta ta mayar da kanta ƙasa tana wasa da bakin gyalen ta shi kuma yana kallonta. "Kin gama exams lafiya?" Tana mamakin yadda sai an manta wani abin shi kuma sai lokacin yake magananshi "Alhamdulillah" "Meyasa kika shiga toilet da waya kika jefa ruwa?" Ta ɗan zaro ido tana mamakin yadda aka yi ya sani shi kuma idanun yake kallo, haka kawai yaji baya so su daina maganan Dukda kanshi dake sarawa sai yaji in dai magana da ita ne ko za'a kwana kaman ba zai gaji ba, sanyin yanayinta, kamshinta, murmushinta da ma maganarta kashe shi suke. Bayani take mishi amma Bakinta yake kallo har ta gama bai ji komai ba, jin ana shirin shiga sallah ya miƙe ya nufi bayi bai ce komai ba, ta girgiza kai ta dauki tray ɗin ta fito dayake ɗakinshi akwai dan hanya tsakanin shi da parlor da hakan yasa tana gab da bayyana parlor ta ji Zarah na cewa Aisha "Aisha kina ganin Ya Sameer zai yarda ya aureni? Wlh tun ranar da ya cecemu na kamu da son shi da na fahimci shine Yaya Sameer wanda nake da alkawarin aure dashi tun yaranta sai na ji na sake kara sonshi kalleshi kiga yadda yake komai cikin wani irin aji da natsuwa...ba ki ji kishin da Naji ba da na kalli matarshi" Aisha tayi dariya "Zai aureki mana kin taba ganin inda aka yi alkawarin aure aka karya shi a zuri'ar nan? Kuma ai na ga matar tashi tana da sanyi bare ma dolenta ta ga kishiya har da kwarkwarori ma idan yana so sarkin gobe fa take aure" "hakane kam duk kishi na shiyasa nake dannewa sanin a auren sarki iya ruwa ne fidda kai kowacce ta iya allonta ta wanke ne, yanzu haka ba za'a rasa ma waenda suka nemi haɗin aure dashi ba ta wurin mai martaba daga bayyanar shi zuwa yau" Sossai maganganunsun ya daki Afeefah, bata san wani irin yanayi ta shiga ba ko motsi bata yi ba sai da ta ji ya buɗe kofa ya fito sai ya tsaya yana kallonta tayi kokarin danne abinda ke taso mata ta fita parlorn ya bi bayanta ya fice masallaci ita kuma kan ta isa dining ma kuyanginta sun karɓa... "Ba Za mu isa kuyi sallah ba?" Ta tambayesu tana danne yanayinta kwarai da gaske don for the First time a rayuwarta taji zafin wani duk abubuwan da ake mata a baya tana kokarin shanyewa kuma tana kokarin ta ga bata tsani kowa ba amma yanzu ji tayi bata son sake kallon Zarah a inda take, har ɗaci ɗaci take ji akan harshen ta maganan son da take yiwa Rayyan ke ta kai koma a ranta... "Kar ki damu yanzu za mu tafi ma ai" Kai ta gyaɗa suka miƙe suna mata sai anjima tace "Na gode sai anjima" Suka fice ta nufi ɗakinta ta samu bakin gado ta zauna tana dafa kirjinta dake zafi zafi, duk ɗan farin cikin da ta samu a tare da shi ya kau. Bata motsa ba sai da aka mata sallama ta ba da izini aka shiga sai ta kalli wata mata ce babbar mace rike da wani tray a hannunta wata kuyanga na binta a baya da akwati "Barka da wannan lokaci ranki ya dade" Nauyi taji na matar tace "Ina yini?" Matar ta kalleta lallai wannan ba tashin masarauta ba ce. "Fulani Faɗimatu ce ta aiko mu shirya ki mai martaba na son ganinku gabaɗaya" Kai ta gyaɗa matar ta shige bayi ta haɗa mata ruwa mai kamshin gaske ta mata iso cikin bayin ita dai ba don su jannah sun ce mata kar tayi musu a duk abinda ake sakata ba da zata ce musu ba sai ta yi wanka ba yanzu tayi wani amma kuma da ta shiga ruwan yadda aka hada shi ya mata daaɗi da ta fito kamshi duk motsinta haka yake tashi. Turaren kolecture suka bata mai bala'in kamshi ta shafa ko ina na jikinta kan ta shafa lotion ɗinta, da kansu suka shirya ta cikin atampha riga da zani da ya zauna mata sossai suka bata gyale ta yafa bayan sun daura mata dan kwali suka hada gyalen da ɗan kwalin suka yi pinning yadda ba zai dinga zamewa ba kan suka ɗora mata wani cream colour Alkyabba da yayi mata mugun kyau kaman ka sace ta ka gudu. Ta kara turaruka Dukda kamshin ma da take ya isheta, kan suka fito gabaɗaya ta samu su Abeeha a parlor "Masha Allah Kin ga yadda kika yi kyau uwargidan Ciroman fombina kuma Yariman matasan fombina?" Sai ta ɗan yi murmushi kadan don uwargida da aka ce ya tuna mata kalaman zarah.. Suka fice gabaɗaya aka musu jagora har babban parlorn mai martaba sun samu kowa na nan na kusa kusa dangi da ya kamata a ce sun sani. Gaisuwa aka yi Mai martaba ya gabatar da Uncle Musa da su Uncle sanusi matsayin dangin Rayyan tunda su suka rike shi tun barin shi gidan har kawo yanzu, yayi musu godiya marar iyaka kan ya nuna su Abeeha matsayin 'ya'yanshi don ya ce a yanzu basu da maraba da su Aisha a wurinshi sai ya nuna Afeefah don Ammi dake gefenshi duk ta nuna mishi su dama kuma ya riga ya gaisa da su Uncle kan zaman duk Ciroma yayi introducing nasu. "Ga 'yata Afeefah ita ce matar Ciroma, ina fata za mu cigaba da zama anan cikin zaman lafiya da haɗin kai yadda muke tafiya, ina marabtar ku da shigowa wannan masarauta matsayin 'ya'ya masu daraja, duk wani abu da kuke so za ku iya zuwa kai tsaye wurina dukkanku matsayin uba nake a wurin ku kaman yadda na dauke ku duk 'ya'ya na" Godiya duk suka yi Afeefah dai na matuƙar takure kuma zuciyarta bugawa yake kaman zai fito tana jin idanu sun mata yawa a jiki amma bata iya ta ɗago ba har sarki ya sallami Matan suka fice "Afeefah!" Ta ji muryarshi ya kira sunanta sai taji wani iri, sunanta a bakinshi daban take jinshi chak ta tsaya ya matso har tana jin kamshinshi da ma numfashin shi dake fita a hankali... "Ba na son duk abin da za'a baki a gidan nan ki ci! Idan ma ya baki sha'awa za ki iya fada min in nemo miki amma kar ki ci komai daga kowani bangare a gidan nan ina fata kin gane?" Kanta ya ƙulle ta ɗago ta kalleshi amma ganin idanunshi a kanta ya sa ta ɗan gyaɗa kai. "Ki amsa min da bakinki, bana son jin cewa kuskure ne ko akasin hakan... Ba kuma na so ki fara tunanin dalili hope am clear?" "In shaa Allah" Kai ya gyaɗa ya juya ya koma ita kuma tayi gaba ta samu su Jannah, aka fara raka su sashen Fulani Adama duk inda ta wuce kirari ake mata. A ƙasa duk suka zauna tana kame cikin kujera suka gaisheta ta amsa tana ɗan murmushi "ƴa ta Afeefah sai ga ki gidan sarauta, ina fata za ki ba da haɗin kai wurin ganin an zauna cikin aminci kin ga nan ba kaman normal gidaje ba" Tayi murmushi tace "In shaa Allahu Mama" "Sannan za ki yi haƙuri da tsare tsarenmu anan, duk muma haƙuri muka yi muke zaune lafiya ina fata in kin ji labarin alkawarin zarah da mijinki ba za ki ji haushin mu ba kar ki ga kaman daga dawowanshi ne aka bashi mata, kin san mu anan al'adar mu in aka haifi namiji da shekaru biyu ko uku ko ma biyar daga an haifi mace to za'a yi mishi alkawari wanda sai in mutuwa ce ta karya, kin ganni nan tun ban yi rarrafe ba nake matsayin matar mai martaba haka ma Uwar shi Ciroma amma kin ga duk muna zaune ne lafiya cikin amana da kula da juna" Ta Yi mugun ƙoƙari da ta iya danne hasalan da ranta ke yi tayi murmushi "Eyyaaa Allah ya ba mu ikon zama lafiya na gode". Sai kallonta Fulanin take har suka tashi suka fita ta sa aka bi su da kyautarta na maraba a ƙwarya rufe da faifai... Su Jannah maimaita maganan suke da damuwa ita dai bata ce musu komai ba har suka shiga wurin Ammi suka gaisheta "Afeefah kina lafiya kam?" Ta gyaɗa kai basu jima sossai ba don su Zarah suna wurin suka mata sallama itama kyauta sossai ta basu a ƙwarya suka nufi wurin Fulani Ameenatou kadaran-hadaran suka gaisa ta basu kyautarta suka nufi wurin Amarya Fulani Salimah itama suka gaisa kan suka nufi sashensu alkyabbar kawai take so taji ta cire ta huta gashi ana ta kiran la'asar, suna zuwa kuwa ta zame kayakin tas ta ɗauki karamar riga marar nauyi mai hannun singlet dogo ne sossai silk Brown ta saka yana da tsagu gefe da gefe har wurin gwiwa ta hau gado ta kwanta kawai bata motsa ba. Maganganun da ta riska yau kawai a gidan ta ji ya sire mata, bata san ta fashe da kuka ba zuciyarta na squeezing yana mata zafi ta ma rasa me ke damunta. Ta Yi kuka har tayi bacci a haka sai Magrib ta farka ta dauki hijabi ta saka bayan ta wanke fuskanta idanunta dai har lokacin sun dan kumbura kuma sun yi ja ta fito parlor ta samu su Abeeha suka ɗan yi hira ta ci abinci kaɗan kan ta ce musu za ta kwanta kanta na ciwo daga haka ta shige ɗaki. Abeeha tace "Addah jannah baki kula Afeefah na da damuwa ba?" Tace "Na kula Abeeha ko nima ina taya ta damuwa ace daga zuwa yau an fara mata zancen zata yi haƙuri mijinta aure zai yi, na san zai iya yi probably tunda dama haka tsarin su yake amma kuma bai kamata ana fada mata ba gaskiya." "Gaskiya sai Naji da ma bamu zo ba ni da nake murna, ashe abin da za mu tarar kenan ni haushina ma ko fa gama fahimtar juna basu yi ba." "Dole mu san abin da za mu yi akan hakan Abeeha, ki ji mana ko mu yi amfani da kishin nata ne mu ƙara kusanta su?" Shawara suka fara suna murmushi, Abeeha ta miƙe ta shige ɗaki jannah ta cigaba da zama don ita ce ma take dan iya magana da Rayyan ɗin ba tsoro ba komai tana nan zaune sai gashi kallo daya zaka mishi ka san ya gaji tiɓis. "Sannu da dawowa Yaya" Ya amsa da "Yauwa" Zai wuce tace "Wai da ma kai nake jira ne!" "Allah ya sa lafiya" "Da sauƙi dai Yaya Afeefah ce tun ɗazu take kuka wai kanta na ciwo ta sha pcm ma bai sauƙa ba" Ya ɗan yi jimmm yace "Meyasa baku kira ni ba? Kun san tana da low BP sai ta fara suma ne za ku yi aiki da hankali?" Da faɗa ya ƙarasa ta ɗan duƙar da kai "Ka yi haƙuri" Ya ja tsaki kan ya juya yayi ɗakin Afeefar. Ta saki murmushi ta juya ta nufi ɗakinsu Abeeha na jiranta suka kashe suna dariya har da kwaikwayon masifar shi, shi kam yana shiga.... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* *50* Kai tsayen bakin gadon ya nufa ya kai hannu ya yaye duvet da take lulluɓe ciki, a hankali ya sauƙe hannunshi a goshinta hakan ya sa ta ɗan buɗe ido ta kalleshi sai ta mayar ta rufe, ta sake buɗewa idanunshi a kan wuyanta zuwa kan kirjinta da har saman ke a bayyane, muryarta yaji tace "Ya Saraki!" Sai ta sake mayar da idanun ta rufe, ƙarasa yaye duvet ɗin gabaɗaya yayi ya kai zaune gefenta yana kai tafin hannunshi ya shafa wuyanta da shima ya ɗan yi dumi amma ba zafi ba. "Kuka kika yi? Me ya sameki?" Shiru tayi bata buɗe idanun ba shi kuma bai daina shafa wuyanta da ya ɗauki hankalinshi sossai ba, jin yana ta da mata da tsikar jiki yasa ta kai hannu ta riƙe hannun nashi cikin wani irin murya ta sake kiran sunan nashi "Ya Saraki!" "Na'am Matar masu sarauta." Yadda ya amsan sai da ta buɗe idanunta, sunan ya shige ta har inda bai kamata ya je ba. "Mu je ki gayamin dalilin wannan kuka" Ko motsi bata yi ba, ganin ta ƙi motsawa Ya sanya hannu ya ɗauke ta chadak sai jinta tayi cikin hannunshi bai sake cewa komai ba ya fice da ita zuwa ɗakinshi, a kan shimfidadden gadon shi ya yi mata masauki zai kalleta don tunda ya ɗauketan a bazata kallon fuskanshi take tana jin soyayyarshi na shiga jini da bargon ta tayi saurin rufe idanu, bai ce komai ba ya miƙe yaje ya watsa ruwa ya sanya kayan baccin shi ya rage wutan ɗakin kan ya zo ya hau gadon ya kwanta. Duk abinda yake tana jinshi, kwanciyarshi da janyota zuwa jikinshi duk lokaci ɗaya hannunshi zagaye da kwankwasonta ɗayan a haɓarta ya furta "uhmm faɗamin" Da kyar ta iya samo kalmar "Mene?" Ta furta "Abin da ya saka Matar Saraki kuka har ya ja mata ciwon kai" Shiru tayi for seconds tsantsin rigar jikinta da kamshin dake fita daga jikinta har gashinta ya shagaltar dashi a hankali yake ɗan bin jikin nata yana shafawa ba tare da ya sake magana ba. Chan tace "Wai da gaske ku nan tun yaro na ƙarami ake mishi mata? Da gaske sarki ba zai iya zama da mace ɗaya ba?" Shiru yayi, chan ya ce "Wa ya faɗa miki wannan magana?" "Kawai na ji ne a wani labari..." Murmushi mara sauti yayi kishi ne ya sakata kuka kuma ya san tabbas faɗa mata aka yi don wulakanci daga zuwanta an tarbe ta da abin da zai sakata kuka a banza, kwafa yayi bai ce komi ba "Da gaske ne kenan?" Ya ji muryarta na ɗan rawa tayi tambayar. "Shhhh ki yi bacci, za mu yi maganan wani lokaci" Dole tayi shiru, hannunshi yake ɗan bubbugawa a bayanta kaman mai rarrashin 'yar baby har tayi bacci ya sauƙe numfashi yana saƙe-sake mai dumbin yawa har bacci ya sure shi shima a haka. Washegari ko da ya tashi sallah ya san bata yi so bai tashe ta ba, ya gyara mata kwanciya kan ya miƙe ya shige toilet yayi alwala ya fice masallaci, daga nan ya tsaya suka gaisa da su Uncle sun jima suna magana da Saleem da duk yau suke zancen juyawa, sai da gari ma yayi haske sossai ya dawo bai sameta ɗakin ba amma ta gyare tsaf ta saka turare ya tsinci kanshi da murmushi kaɗan kan ya wuce yayi wanka bayan ya shirya yana ma shirin fita ne ya ji sallamar ta. Ya amsa yana mayar da idanu kanta sai ya lumshe su ya sake buɗewa, yarinyar tana fusgar hankalinshi fiye da yadda zai misalta sanye take da wani coffee doguwar riga mai shige da material amma yana da kauri an tattare kirjin ƙasan a sake wane umbrella suna haɗa idanu ta kawar da nata don bata iya jure kallon cikin idanunshi barin ma in yana binta da mataccen kallon nan da ya tsira, gaban kujeran dake dauke da table ta ajiye mishi tray ɗin da ta shirya abincin kaman ka kwace don kyaun da yayi a ido, doya ne dafaffe da sauce na manja kana ganin kifi nasha nasha a ciki da kuma dafaffen kwai cikin Miyar, sai dafaffen plantain da ta musu wani yanka mai kyau, da tea mai kauri cikin mug sai da ta ajiye ta ɗago lokacin ya matso dab da ita. "Good Morning!" Ta faɗa har lokacin bata wani fara'a don ba wani daaɗin zuciyarta take ji ba, hannunshi na dama ya miƙa mata alamun su yi musabaha sai ta sanya nata ciki a hankali, da sanyawar da sauya hannun nashi da yayi zuwa hagunshi da fusgarta zuwa kirjinshi da zagaye kwankwasonta da yayi da hannunshi na daman duk lokaci ɗaya, kirjinta da nashi suka haɗe ta zaro idanu tana kallon shi shima cikin idanunta ya zubawa idanu sama da seconds biyu kan ya furta "Good Morning Caramel Queen..!" Ya faɗa yana bin smooth and silky skin ɗinta da wani irin kallo, kanta ta mayar ƙasa. Ya zame hannunshi dake kwankwasonta ya kai kan fuskarta da ta sako 'yar gashi kaɗan gaba ya ɗan shafa gashin da yatsa ɗaya yana mayar dasu gefe ya furta "Ya ciwon kan?" Ta kalleshi ta kawar "Alhamdulillah na ji sauƙi" "Har yanzu fushin ne?" Tayi shiru, ya ɗago haɓarta ya hura mata iskar bakinshi ta lumshe idanu, tana jin tender nd soft palms ɗin shi na wasa da tafin hannunta. "Talk!" Ta sauke nannauyar numfashi tana jin salon shi na kasheta, zamewa tayi tana zare hannunta "Abincin ka na sanyi" Haka kawai he doesn't like this silent treatment of hers. Zama yayi bai ce komai ba ta tura mishi abincin ya fara ci da bismillah ta juya ta fice, bayanta ya bi da kallo har ta rufo kofar ya sauke numfashi a lokaci daya yana tunanin wanda ya fada mata batun zarah shi da ko za'a shaƙe shi ma bai san kamannin zarahn a idanunshi ba, salon kishin ta kuma ya tafi dashi har yana dan murmushi wai ita tana fushi hmmm Misalin karfe sha ɗaya dukkansu suka fito don sallama da su Uncle Musa da zasu koma da Saleem, ita jannah na nan akwai wani taron Matasa da aka haɗawa Yariman na Matasa kuma Ciroman fombina wanda zallar al'ada suke son fitarwa a wannan gagarumin taron za'a yi shi a jibi sai gata sai ta wuce itama ta bar Abeeha da har sun fara batun neman transfer don Rayyan ya rantse ba gidan da zata je ta zauna kuma ba zata zauna hostel ba. Tun tahowarsu ya zuba mata idanu magana yake da Afeefah matsayin ɗan uwa da 'yar uwa yana kuma bata ƙwarin gwiwar zaman cikin gidan amma tahowar Aisha ya ɗauki hankalinshi har bai san kuma me yake cewa ba, Afeefah ta juya ta kalli wacce yake kallo haka ta saki murmushi ta juyo tayi waving "Ya Saleem ya dai?" Cike da dariya shima ya ɗauke kai ya mayar kanta "An tafi da ni ne, kanwata za ki taya ni yaƙi" Dariya tayi lokacin Rayyan ya ƙaraso inda suke har lokacin Afeefah na murmushi yace "Me yayi muku daaɗi haka?" Idanunshi a kan matar tashi da murmushinta ya tafi dashi ainun. "Sirri tsakanin yaya da kanwa" Inji Saleem, ta ɗan waro ido ta kalli Saleem tace "Gwara ka kiyaye aka hana ka babu ruwan Afeefah" "Da fa gaskiyarki, Yayanmu barka da fitowa" Ya juya yana miƙawa Rayyan hannu da kaman yanzu ne suka haɗu cikin ladabi. Murmushi Rayyan yayi yana girgiza kai wanda ya shagaltar da Afeefar a kallonshi don murmushi ne da bata taɓa gani yayi ba, murmushi na mishi kyau ainun barin ma fararen hakwaranshi da suka bayyana suka haske fuskar tashi. Gaisuwar da su Aisha ke musu ya sa ta dawo daga duniyar shagaltuwarta sai dai ganin kallon da zarahn ke yiwa Rayyan ya sa taji duk mood ɗinta ya chanza, shi kam Rayyan ko kallonsu bai yi ba ya amsa Uncle Musa ke yiwa Saleem magana akan su wuce kafin su yi missing flight dole duk suka yi wurin motar ya dubi Afeefah "kanwata za mu yi magana fa" Ta gyaɗa kai kawai suka yi sallama suka fice cikin motocin alfarma wanda da Rayyan suka tafi, su matan su uku

Chapter 31 of 40