Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daga shi har Sulaiman idanunsu na a kanta. Da kyar ta iya buɗe baki tace "Sannu da isowa Ya Saleem" "yauwa Afeefah" "Ina yini?" Kai kawai ya ɗan gyaɗa mata hakan ya sanar da ita cewa lokacin da ya kamata yayi magana da ita ya wuce. "Yaya Sulaiman ina yini?" Muryarta da ya karye ya ƙara sanyaya yana fitowa a slow, ɗago ido Ryan yayi ya kalleta daidai tana ce mishi shima Ina yini? Ya kau da kai kaman bai gane da shi take ba, daga shi har saleem sun fahimci chanzawar muryarta, shi Ryan kam ma mamaki ne fal ranshi don a yanzu abin da ya sa ya sake kallonta tuna abin da saleem ya gama faɗa mishi bayan ya ɗauko shi daga Airport wai son yarinyar nan yake, in ba janyowa kai raini ba shi bai ga abin ba ya tabbatar a auren ƙauye sun kusa ajiye irin ta. Tsaki ya ja a fili yana furta "Man we talk later!" Ya faɗa cikin muryarshi mai cike da ginshira sai Muryar ya bata tsoro ta tuna ranar da yake daka mata tsawa da hanzari ta ɗago idanu ta sake kallonshi, ya miƙawa Sulaiman tender fingers ɗin shi da kaman zai fidda jini don haske da taushi suka yi musabaha, yana kokarin buɗe mota idanunshi suka sake shige wa cikin nata, daga ita har shi suka yi saurin kawar da idanun ya shige ya ja ya bar gidan. Saleem ya dubi Sulaiman ya ce "Nima kaman zan shiga daga ciki jikina kaman an min duka" Sulaiman na murmushi yace "Ai dole, a huta gajiya mazan fama" Suka yi musabaha kan ya nufi ciki, ya zaci Afeefah ma za ta yi wa Sulaiman ɗin sallama ta biyo bayanshi sai ya ɗan waiga nan ya ga sun matsa jikin motar Sulaiman ɗin yana mata magana a hankali ita kuma tana dariya, tuni duk wani walwalar fuskarshi ta kau, ranshi ya shiga suya bai iya ya shiga main parlorn ba ya bi ta baya ya haye sashenshi, backpack ɗin kawai ya ajiye ko zama ya kasa yi ya dawo jikin Window yana kallonsu, kusan mintuna talatin suka yi suna hira kan ya ga Sulaiman ya buɗe mota ya fiddo wasu ledoji ya miƙa mata. "Ga shi umma wai na kawo miki" Tayi murmushi mai kyau cike da jin daaɗi tace "Allah sarki umma, ka yi mata godiya na ji daaɗi sossai Allah ubangiji ya kara girma da lafiya" Wayanshi ya zaro yana furta "Ko kuma ki yi mata da kan ki ba" Ido ta zaro kan ta yi magana ya shiga ƙiran ummar, bayan ta ɗaga da sallama ya ce "Ummar mu ga Afeefah tana so ta miki godiya" Kaman za ta nitse haka ta karɓa ta shiga gaisheta tana yi mata godiya, Albarka Ummar tayi ta sanya mata kan suka yi sallama ta miƙa mishi wayar tana ɗan tura baki na fushin yadda ya saka ta jin kunya, murmushi yayi "Kar ki sa na narke fah Afeefah" Tayi murmushi Ya miƙa mata wani leda mai girma da farko kin karɓa tayi sai dai da ya matsa ta karɓa ɗin tare da godiya suka yi sallama ta nufo ciki. Da hanzari Saleem ya ɗauko wayanshi ba ta ko kai ga shiga ɗakinta ba ta ga saƙon shi "Menene ke tsakani ki da Sulaiman?" Muƙut haka ta haɗiye wani miyau kaman yana gabanta, da sauri ta shige ɗakin ta ajiye ledar tare da zame mayafinta ta jefa kan katifa ta fara safa da marwa cikin tunanin amsar da za ta bashi, sam bata so yayi fushi da ita da kyar ta iya rubuta mishi "Babu kawai kyautatawa ce da suke min shi da ahalinshi" Shiru ba reply, ta san ba wai ya yarda bane kuma kila shirun nan da ya yi fushi yayi, ta kasa zaune ta kasa tsaye haka ta yi ta saƙe-saƙe ita kaɗai, ƙiran Magrib ne ya katse ta jiki a sanyaye ta shiga bayi tayo alwala ta zo ta gabatar da sallah ta zauna nan tana karatu. Sulaiman kasa zuwa office yayi haka kawai yake sake tariyo kallon da saleem ke yiwa Afeefah, ji yayi ko ya je office ba zai taɓuka komai ba yana buƙatar shawara da mahaifiyarshi don tamkar ƙawarshi haka take. "Wash Allah na!" Ya faɗa yana kwantar da kanshi a kan kafafunta, ta sa hannu ta shafa sumanshi "Ya dai likita?" "kawai gajiya ne umma" "faɗamin gaskiya ko dai kai da surkar tawa ne?" Ya ɗan yi shiru kan ya ce "Ina tunanin umma saleem na son Afeefah, ko dai ita bata sani ba ko kuma ta sani tana min wasa da hankali ne" "Saleem shi ne ɗan masu gidan da take aiki?" Kai ya gyaɗa mata "Kuma Baaba ta tabbatar min kaman yarinyar tana shan wahalan gidan aiki haka ne?" Nan ma ya gyaɗa kai fuskar shi babu walwala "Kaman saleem ɗin ne kawai yake taimaka mata, kuma kaman ba ta da kowa don dole ne kawai take zaune gidan" "Ka kwantar da hankalinka Sulaiman, kila ba soyayyar ba ce tsakaninsu sai kyautatawa don ya na tausayinta, kila kuma yana son ta ɗin amma yana tsoron bayyana mata don iyayenshi, zai ma iya yiwuwa ya sanar mata ɗin amma ta ƙi bashi haɗin kai don babu macen da za ta yi kuskuren jefa kanta inda ta san ba'a ƙaunarta ko kuma inda za ta sha wahala" Numfashi ya sauƙe "Umma haka kawai nake jin kaman ba zan sameta ba" "Ka cigaba da kyautata mata domin zuciya tana son mai kyautata mata, idan har matarka ce za ka aureta, ni ma zan so ka sameta don na tabbatar wacce ta iya mallake zuciyar My Son ba ƙaramar nagartaccciyar mace ba ce" Ya miƙe zaune yana murmushi "Umma za ki fara taya autocinki zolaya ta ko?" "Ai gaskiya ne sabon shiga, duk ka bar komai obvious sai gano ka muke yi dubi duk yadda ka ruɗe daga sanin tana da wani saurayin" Ta ƙarasa da dariya. "Duk ba za ku gane bane umma ni dai na yi nan" Yana ji tana cewa "Toh zo ka ganar da mu mana" Yayi murmushi kawai. Allah ya gani shi karan kanshi ba zai ce ga sadda ya fara jin son Afeefah a ranshi ba, kawai dai ya san ta yi mishi kyau ranar da ya fara ganinta, sanyin muryarta idan tayi magana sai yake jin tamkar ƙanƙara ake zuba mishi. Ko da ta bar asibitin bai wani sa hope ɗin sake ganinta ba amma daga ranar da ya je ya isketa cikin fitar hayyaci sai ya ji tamkar an soki zuciyarshi da mashi barin ma da ya gama fahimtar tana shan wahalar rayuwa a gidan, sannan ya san babban burin ta a rayuwa shi ne ta yi karatu ta zama wata public figure da za'a yi alfahari da ita, kaman tana da wani ciwo ne da take jin ba zai taɓa warkewa ba har sai ta yi nasara a duniyar ta, ba ya jin zai iya bar wa saleem ita za su buga wasa ne duk wanda ya iya allonsa ya wanke. A daren da misalin ƙarfe tara ya ƙira layinta, ta gama wanke-wanken dare kenan da yau yayi yawa sossai saboda abincin da aka yi kalolin daban-daban, sai duba wayan take ko za ta ga saƙon saleem don gabaɗaya ranta babu walwala, ko da suka haɗu ko kallonta bai yi ba kuma ta sake mishi saƙo babu reply. "Assalamu Alaikum warahmatullah" A natse ya amsa "Wa'alaikissalam gimbiyar mata" Tayi ignoring sunan da ya ƙiratan "Ka koma gida lafiya?" "Da an damu da ni ai da an neme ni, ni da ya zama dole na ba gashi na kira ba. Ya kike?" Har za tayi magana ya katse ta "Wait!! Kina lafiya ko? Ya na ji muryarki duk cike da damuwa da rashin Walwala ba yadda na bar ki ba?" Ta ɗan ja numfashi tana tafiya kwance daga zaunen da take jingine da gini. "Kaina ke ɗan ciwo" "Eyyaa so sorry, kina da ORS?" Ta girgiza kai tana amsawa da "A'a" "Ki sha pcm da safe zan zo in auna jinin ki sai in taho miki da ORS ɗin, ciwon kai bashi da daaɗi musamman ga ke da jininki sauƙa yake kuma kin san ya fi high BP hatsari" Idanu kawai ta runtse bata san me zata ce ba tunda ta riga ta yi suɓutar baki ta ce kanta na ciwo zuwa kam sai ya zo to kuma saleem da har yanzu bai sauko daga fushin ɗazu ba fa? "Kina ji na kuwa Afeefah?" "Eh ina ji, na ce da ma ka barshi in na yi bacci zai daina" "hmmm ke dai kawai in na zo ɗin zan ƙira ki, kwanta ki huta Allah ya baki lafiya" Yana kai nan ya katse wayan ba ya so ta hana shi zuwa haka tayi ta juye-juye har bacci ya sure ta. Washegari tana gama goge-goge ko ɗaki bata koma ba sai ga ƙiran shi, gate kawai ta wuce don ta karɓa da sauri kan saleem ya tashi ya ganta "Sannu da zuwa" "kin tashi lafiya?" Yayi tambayar yana ƙare mata kallo, ita kam ko me ta saka kyau take mishi "Alhamdulillah ya su umma?" "Umma na gaishe ki da jiki ta ce in miki sannu" "Na gode sossai" Leda ya fitar ta zare ido, ko kayan jiya bata buɗe ba saboda damuwar fushin saleem da ita yanzu kuma ya sake ciko leda? Shi kam ba ya gajiya ne? "Hidimarka na yawa a gareni Dr. Na kan rasa kalaman godiya a gareka, wani lokacin sai in ji tamkar ba na kyauta maka don ka fara ƙaunata tun ba ka san wacece ni ba! Ban san ya za ka karɓeni ba a duk ranar da wani ya tare ka ya ce maka Afeefah annoba ce!" Kallon bana fahimtar zantukan ki yake mata daidai saƙo ya shigo wayar ta sanin saleem ne ya sa dole ta buɗe tana ta ƙoƙarin haɗiye kukan dake zuwar mata "Ki sallame shi za mu yi magana" Ta ɗago ta kalli Sulaiman da har lokacin idanunshi ke kanta. "Zan shiga ciki za mu yi magana" "Saleem ɗin ne ya ce ki sallameni?" Ya faɗa cikin wata murya yana ƙara tsare ta da idanu. Ba Ta yi magana ba ta mayar da kanta ƙasa kawai. "Ya za ki saka ni a duhu kuma ki tafi ki bar ni ciki? Me kike nufi a tare ni a ce ke annoba ce? Mutum ya taɓa zama annoba ne Afeefah?" Muryar ta na rawa tace "Kwarai Dr. Sulaiman da za ka iya da ka yi tattaki zuwa Dutsen-wai ka tambayi wacece Afeefah kamal ina da tabbacin bayan nan ko mai sunana aka ƙira maka za ka gudu! Umma ta karɓe ni ne domin itama bata san wacece ni ba don babu uwar da za ta karɓeni matsayin surka muddin tana ƙaunar ɗan ta" Ranta zafi yake mata, tana maganar ne tana tuna mahaifiyar saleem da kyamatarsu gareta ta wani ɓangaren kuma bata ga laifinsu ba don ba laifi bane mutum ya kare abin da yake so. "Ka yi haƙuri ka tafi Dr. bana so sai ka zurfafa kasan ni wacece in karya maka zuciya, na tafi ciki" Tana kai nan ta nufi ciki ta bar shi tsaye, hawaye take zubarwa ba wai duk cikinsu babu mai nagartar aurenta bane sai dai tana ji babu inda za'a karɓeta matuƙar an san wacece ita! Taɓon nan da bata san mafari ba ba zai taɓa goguwa a tarihin ta ba, tabo ne mai raɗaɗi da har Abada za ta cigaba da rayuwa cikin gangar jikin da ruhi mai tarin buruka suka mutu... Da saleem ta ci karo a sadda ta shawo kwanar ɗakinta ido kawai ya zuba mata ko da ta zo bata tsaya ba kawai ta wuce shi yayi saurin shan gabanta. "Afeefah saboda Sulaiman kike ɓata rai da ni?" Hawaye take yi wadda ta kasa sarrafa su cikin rabuwar murya tace "Ba saboda shi bane yaya saleem" Ta sake yunkurin wucewa ya sake tare ta "Ban gane ba bayan ga idanunki nan suna zubar da kwallah Afeeefa?" Cikin Muryar kuka ta shiga cewa "Ina kuka ne saboda na gaji da yaudara ta da zuciyata ke yi na cewar zan samu farin ciki, ina zubar da hawayene saboda na farka daga mafarkin da bashi da tabbas" Shesheka ta ja tana kallon cikin idanunshi "Ka gaya min Yaya saleem a cikin ku biyu da waye zan dogara? Da Kai da mahaifiyarka ta yi Allah ya isa muddin ka yi min maganar da ta wuce ta minti ɗaya ko da Dr. Sulaiman da bai san wacece Afeefah ba?" Wuce shi kawai ta yi don ta san ba zai amsa ba saboda minti ɗayan ya riga ya wuce hakan ya kara rura wutar zuciyarta ƙarfin kukan ya ƙaru, jakar hannunshi ya bi ta har cikin ɗakin ya ajiye ya tsaya ya zuba mata idanu yana jin kukanta na sukan zuciyarshi, idanunshi suka sauya sossai tausayinta da ƙaunarta suka ninku a cikin ranshi. Samha da ke tsaye jikin pampo ta sake hanci da baki tana kallon su ta kwasa da gudun tsiya ta kamo hannun mommy "Mommy zo zo zo ki ganewa idanunki wallahi Ya Saleem ne ɗakin Mayyar chan..." Mommy har tana tripping garin sauri suka nufi bayan a lokacin suka hangi bayanshi ya fito ya nufi hanyar waje, duk su huɗu suka nufi ɗakin kowa da bala'in da ke cin shi a rai... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *017* 18hours Earlier Kanta a ƙasa tun da Sulaiman ya fita daga gidan tana tsaye ne jikin taga tana kallonsu tun Shigowarshi da ma isowar su saleem da tafiyanshi bayan ya ba Afeefar Abu a leda, bata taɓa sanin haka so yake ba sai da ta faɗa komar Sulaiman zuciyarta yayi mata wani irin nauyi, tsananin haushin Afeefah take ji kaman ta samu bindiga ta harbeta kowa ya huta, a yanzu ma bata san hawaye na zuba mata ba sai da ta ji an dafa ta. Ɗago kai tayi ta kalli Samha sai ta duƙar da kan again tana share hawayen fuskarta "Sameera me ke damun ki haka? Menene ya sameki kike kuka?" "Babu Samha" "A'a Sameerah ina fa lura da ke kwana biyun nan duk kin chanza kaman ba ke ba, kullum kina cikin damuwa 'yar faɗan nan da kike biye ni muyi tayi duk yanzu bakya yi walwala ta kau daga fuskanki har mommy ɗazu maganan take yi, in baki faɗa min ba wa za ki faɗawa Sis?" Kuka kawai ta sakarwa samhar, sai da tayi mai isarta kan ta ɗago ta kalleta "Samha ko na faɗa ma ba ku da maganin damuwata" "Ko Adu'a muka taya ki ai mun taimakeki bare kila akwai shawarar da zan iya baki, idan ba kya son kowa ya sani ne ma i promise ba zan faɗawa kowa ba". "Samha na kamu da Soyayyar Dr. Sulaiman" Tsayuwa tayi tana tunanin waye Drn Sulaiman sai da yayi clicking a brain ɗinta kan ta yi saurin cewa "Wannan likitan dake zuwa duba Mayyar chan?" Kai ta gyaɗa a sanyaye "Samha kaman soyayya suke da ita" "Amma Sulaiman ɗin bai santa bane ba ko? Ina nufin bai san wacece ita ba rufe shi take kokarin yi ta nuna mishi ita 'yar gidan nan ce?" Samhar ta fada har yanzu tana mamaki, Afeefah ta kai Sulaiman ya ce yana so? "Da alama kam" "Toh me kika yanke?" Ta ɗago jajayen idanunta tace "Dole su rabu idan na cigaba da kallonsu tare zuciyata zai iya bindiga Samha, dole ko in sakata ta rabu da shi ko kuma in san hanyar da zan bi gidansu su san wacece ita! Ko yana sonta ai ba shi zai aurar da kanshi ba ko?" Kai Samha ke gyaɗa wa "Wannan haka yake, shawarar nan yayi kuma ki sameta ki ja mata warning mai girma ta tsaya matsayin ta" A hakan suka yanke don har ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi da Afeefah da safe kuma tana tashi bacci wanka kawai tayi ta fito kaman an ce ta leƙa waje ta hanjeshi tsaye da ita, ko abinci bata ci ba ta zauna parlor tana jiran Afeefar ta dawo don ta lura abin nasu gaba yake, bata gama tunanin ba sai ga Samha da gudu ta ƙira su suka nufi ɗakin Afeefar... *** Tana zaune kanta haɗe da ƙafafunta tana aikin zub da hawaye kawai ta ji an banko ƙofan ɗakin, suka tsaya suna ƙarewa ɗakin kallo kan Sadiqa ta nufi wayanta da ke zaune gefenta "Kutt! Yaushe kika yi waya? Na dai tabbatar ba da ita kika zo gidannan ba" Kayakinta Samha take dagawa tana cewa "Mommy yau dai kam Yaya da kike yabo ya watsa miki ƙasa a idanu duk wa zai saya mata su bargo har da su heather in ba Yaya ba? Dubi ƙwalamar dake ɗakin nan? Mommy anya ba asirce shi tayi ba?" Ita dai tana tsaye tana kallonsu duk da zuciyarta da ke dukan sakwara ta kame bata firgice ba, Sameera ta je ta fusgo ledojin da Sulaiman ya kawo mata tana zazzage kayakin ciki idanunta cike da kwallah. "Shikenan wallahi tambaɗe mana take shirin yi a gida, wani namijin ne zai na kashewa mace kuɗi haka ba tare da ta bashi komai ba?" Sadiqa ce tayi maganan tana ganin turaruka da dogayen riguna masu tsada da mahaifiyar Sulaiman ta bata. Sameera ta katse ta "Ko dai asiri ta yi musu ba yaya sadiqa in tambaɗe wa ne kenan har da Yayanmu kalli wayan nan kalar text messages dake ciki na tsantsar soyayya don tsabar rashin kunya da nuna cewa ta isa dashi ma kin ga sunan shi gatsau tayi saving saleemullahi" A fili ta fara karantowa mommy wasu inda yake tabbatar mata da zai iya jurar komai a kanta kuma zai jajirce har sai ya ga sun samu cikar burin su na kasancewa karkashin inuwa daya. "Ya isa haka sadiqa" Mommy ta faɗa jiri na kwasarta ta samu wuri ta zauna, har Dishi Dishi take gani saboda yadda kanta ya sara ashe salim zai iya tsallake maganar ta? Yanzu idan da basu lura da wuri ba tayi amfani da wannan dama ta kashe mata shi fa? Da gaske maita na tafiya da aljanu? Ai kuma duk inda Aljanu suke akwai asiri kenan dai tun farko ma asiri ta mishi ta sa ya kawo ta matsuguninsu? "Lallai saleem! Ni yaron nan zai nunawa ɗan yau ne shi? A kan mace? Macen ma Mayya marar galihu da tushe haɗe da asali mai kyau? Allah ya isa na a banza ya ɗauke shi? Ni saleem...?" Sai ta kama hawaye, hankalin Afeefah ne ya tashi ganin mommyn na mishi hawaye bata son masifar hawayenta ya taɓa shi ko ta wani ɓangare da sauri ta isa gaban mommyn ta zube a kan gwiwowinta "Don Allah Hajiya ki yi haƙuri kar ki mishi kuka, wallahi yana jin maganarki yana kuma tsoron fushinki, Ni ce mai kuskure ni ce na nemi ya sayamin kar ki yi fushi da shi domin fushinki bala'i ne a tare da shi..." Tauuuu sadiqa ta ɗauke ta da mari "Kin san hakan amma kike hure masa kunne ya saɓa mata? Kin san abin da ɓacin rai daga gareshi zai iya ja mata?" Samha da ta janyo jakar da saleem ɗin ya shigo ya ajiye mata ta zazzage komai na ciki tana cewa "Wallahi yarinyar nan so take ta raba mu da ɗan uwanmu Mommy, kalli uwar tsarabar da ya kawo mata a ɓoye ko ke bai kawo miki irin hakan ba bare mu... Farraku take shirin yi mana daga karshe ta sa ya kora mu daga gidan nan" "ƙira min saleem sadiqa" Da wayan Afeefar ta ƙira shi, ringing ɗaya ya ɗaga a hankali ya kira sunanta sai ta duƙar da kai hawaye na gangaro mata jin muryarshi. "Yaya Salim Sadiqa ce Mommy ke son ganinka" Runtse ido yayi da ƙarfi gabanshi na faɗuwa, bai shirya ba! Bai shirya tashin hankali a yanzu ba ba yanzu ba da yake jin son Afeefah yayi mishi yawa a zuciya. Da sauri ya juyo kan motar dama bai yi nisa ba ya dawo wani irin parking yayi ya sauƙa ya nufi sashen Boys quaters ɗin yana Adu'ar Allah ya sa kar mommy tayi mata wani abu, sai kace-nace ya same su suke yi ana ta maida magana, Afeefar na tsugune kaman mai neman gafara tana kuka. Gaban mommyn ya je kusa da Afeefar shima ya duƙa kawai ba tare da ya furta kalma ko guda ba. "Saleem" Ta ƙira sunanshi ya amsa ba tare da ya kalleta ba "Ɗago saleem ka kalleni, ka ɗago ka tabbatar min da kai ke tura duk wani saƙo da na gani wayar yarinyar nan, da gaske kai ne kake son wannan marar cikakken asalin?" Ya runtse ido wani irin nauyin Afeefah yake ji kaman yayi yaya, baya so baya kaunar ta ke jin furucin ɓatanci daga ahalinshi zuwa gareta musamman mahaifiyarshi. "Mommy ni ne, Son ta nake kuma aurenta nake Son y...." Wani irin mari ta ɗauke shi da shi, karo na farko kenan da ta kai hannunta jikinshi don shi yaro ne mai tsananin biyayya a gareta. "Maimaita!" Ta daka mishi tsawa ya sake cewa "Mommy ina ƙaunarta, kuma aurenta nake buri" Wani marin ta sake dauke shi da shi, ba shi kaɗai ba har su sadiqa sun tsorata basu taɓa tunanin za ta iya kai hannunta jikinsu ba don ita Allah yayi ta da tsananin son yaranta, hawaye take yi ta sake cewa saleem ya maimaita "Mommy... Mommy da gaske zuciyata ta kamu da Soyayyar Afeefah da ba na tunanin ko wani hukunci za'a yi min zai sa ta fita daga ciki, mommy kila sai kin cire zuciyar gabaɗaya daga kirjina za ki daina jin harshena na furta kalmar ƙauna zuwa gareta..." Wani irin kuka Sameerah ta fashe da shi, a yanzu ta yarda ta yarda ba wani asiri don tabbas abin da take ji a kan Sulaiman shi ke azabtar da Saleem tunda har zai iya mayarwa mommy magana sau uku, Mommy ta sake ɗaga hannu zata mareshi sadiqa ta riƙe hannun tana hawaye "Mommy ba shi za ki daka ba ga Mayyar da ya kamata ki kassara chan, wallahi Afeefah sai kin bar gidan nan ba za ki tarwatsa mana gida ba" Afeefah dai ta rasa yanayin da take ciki, wani irin ƙauna da tausayin saleem ne suka sake mamaye zuciyarta ko tunanin inda za ta nufa in sun kore ta bata yi, damuwarta saleem idan suka raba su basu mishi adalci ba, shi ya cancanci bautar ta na aure har mutuwa. "Saleem!" Mommy ta kira shi karo na ba adadi muryarta har yanzu da wani irin mamaki, idanunshi da suka sauya ainun ya ɗago ya kalleta tamkar ba soja ba wani irin rauni ya bayyana karara a fuska da idanun nashi. "Saleem!!" Ya amsa a hankali "Saleem!! Sau nawa na kira ka?" A hankali yace "Uku" "Wannan ba aikin hankali bane na asiri ne, amma ko da asirin ai ka san matsayi na a wurin ka ko? Ka san ni wacece ko?" "Mommy ke mahaifiyata ce kina da darajar da babu wanda yake dashi a wurina duk faɗin duniyar nan. Kin isa da ni kuma na san za ki so farin cikina! Mommy a yanzu ba na jin ina da wani buri da zai haifar min da farin ciki kaman Afeefah, ban san sadda sonta yayi min wannan kamu ba don ba ya shawara kan ya shiga wallahi ina sonta! Ba zan iya rarrashin zuciyata ba don so bai san rarrashi ba..." "Afeefah Allah ya isa tsakanina da ke! Allah ya isa" Mommy ta faɗa tana kuka. A lokacin hawayen da saleem ke danne wa suka gangaro ya ɗago ya kalli mommyn zai yi magana ta daka mishi tsawa a kan ya mata shiru "Aure kake so zan ɗaura maka aure da yar ɗan uwana Sabreena da take sonka tun bata san kanta ba, amma soyayya, magana ko zancen aure tsakaninka da wannan yarinya saleem har Abada, ko bayan raina ne Allah ya isa ban yafe ba! Wallahi wallahi sai na iya tsine maka ka sake shiga huldar yarinyar nan ko a hanya kuka haɗu ban yafe ba ka mata ko da sannu ne... In har ni na haif...haifeka Saleem sai dai in kana da wata uwar za ka iya" A razane yake kallonta, ta share fuskanta ta dubi Samha "Je ɗakina ki ɗaukomin akwatin da ya fi kowanne girma" Da sauri ta tafi, Sameera zuciyarta ne ke tsitsinkewa a yanzu tsoro ne ya rufeta, wlh tana iya jin irin abin da saleem da idanunshi ke runtse yake ji a yanzu, gabaɗaya jijiyoyin kanshi sun mimmiƙe girgiza kai take yi "Mommy don Allah ki dakata! Ki tsaya kar azabar yayi mana yawa... Ki barta don Allah ko bai aureta

Chapter 10 of 40