Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* *37* Bayan ta tashi daga baccin da ya dauƙeta tun bayan Sallar asuba wanka tayi ta shirya cikin wata doguwar riga mai hannun roba purple da ya amsheta ta ɗaura dankwalin a kanta sai ta nufi sashen mammi don gaisheta, da sallama ta sanya kanta ciki ta ga mammin kwance a kan sallayar da tayi sallah ta ɗora kanta saman pillow tasbihi take a hankali tana ta maimaita "Allahumma inni As'aluka husnal khatima, Allahummar ruzuƙnee taubatan nasuha qablal maut, Allahumma ya musalibbal quluub thabbit qalby ala dinika, ya musarrafar quluub sarraf quluubina ala ɗa'atik..!" Abin da ta lura kusan kullum a kwanakin ya zama tasbihin Mammi kenan, a ganganta ta zauna "Mammi...kina lafiya?" Tayi tambayar hankalinta na kan mammin gabaɗaya ganin yanayinta kaman marar lafiya lumshe idanu mammin tayi ta buɗe kan ta ce a hankali "Afeefah je ki buɗe bedside za ki ga wani kwali ki ɗauko" Miƙewa tayi taje ta buɗe ta ɗauko ta dawo tana zama riƙe dashi "Mammi gashinan!" Mammin bata motsa daga kwancen ba don bata jin zata iya tashi tace a hankali "Afeefah ki buɗe ki gani menene ciki?" Buɗewa tayi sai ta ga set ne na dankunne sarka da abin hannu da kuma zobe, daga gani ka san ba ƙarami bane don ma bata san gold ba da sai ta ce wannan ɗin gold ne babba ma don yadda yayi wani irin kyau ga ɗaukar ido. "Set na sarka ne Mammi" "Masha Allah, sadakinki kenan da na yi amfani dashi na saya miki wannan kadarar, ki riƙe a wurin ki naki ne halak malak ban baki tsabar kudin bane don na san ba zai ajiyu ba amma wannan ko shekara nawa zai yi a zaune babu abin da zai yi sai ma darajar shi ya ninku" Rasa bakin godiya Afeefah tayi sai hawaye ya shiga ziraro mata "Mammi kin yi min komai a wannan duniyar ba ni da abin da zan saka miki face Adu'ar Allah ubangiji ya baki lafiya, Allah ya yaye miki wannan ciwo ya kawo mana karshensa mu ga kema kin warke kaman kowa, Allah ya sa kaffara kika yi" "Ai lafiyar ta zo ma Afeefah" Ta faɗa tana rufe idanu jin yadda take jin ciwo mai tsanani a ciki da ma jikinta gabaɗaya. "Mammi...!" Sai ta ga wani irin zufa na karyo mata numfashinta na fita da kyar da kyar har chasbin hannunta na zamewa da kanshi, wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ta da gudu ta miƙe ta fito sai tayi side ɗinsu kaman za ta kifa haka ta tura kofan ta same shi tsaye gaban madubi, ba zata ce ga yadda ta riske shi ba ita dai ta san ta isa gabanshi tare da riƙe hannunshi "Mammi...! Mammi.." "Me ya sameta?" Ya faɗa hankalinshi na tashi lokaci ɗaya, ganin duk ta ruɗe yace "Je ina zuwa" Fita tayi da sauri shi kuwa ya ɗauki boxers kawai ya saka da jallabiya tare da zaran keyn mota kafafunshi ma silifas ce ta wanka ya fice da hanzari, yanayin da ya sameta sai da ya ƙara ɗaga masa hankali haka ya ɗauketa Afeefah na ta kuka suka nufi Asibiti duk ma'aikatan hankalinsu ya tashi da sauri aka karɓeta sai oxygen aka sanya mata sun yi iya kokarinsu har numfashinta ya ɗan daidaitu, Rayyan dai ya kasa aikata komai don ba karamin girgiza yayi ba duk tashin ciwonta bai taɓa ganin kaman wannan ba, bai zaci za su iso asibitin da ranta ba jikinshi rawa kawai yake yana tsaye daga gefe yana kallonsu a sadda zuciyarshi ke cigaba da bugawa kaman zai fashe, idanunshi sun rine sai adu'a yake yana roƙon Allah akan ya bata sauƙi a ranshi. Ganin ta dawo daidai oxygen ɗin na tafiya a hankali ba kaman daga farko ba da in ta ja kaman ba zata sauƙe ba ya isa gangarta ya riƙe hannunta kawai ya zauna, a jikin gadon ya ɗaura kanshi yana danne abinda yake ji na taso mishi, ina ma da zai iya kuka da yayi ko don samun sassaucin abinda yake ji a ranshi da ma kwakwalwanshi! Ba zai ce ga adadin lokutan da ya ɗauka zaune a wurin cikin wannan yanayi ba chan dai ya ji kaman ana shafa suman kanshi da ɗan hanzari ya ɗago sai suka haɗa idanu tana ta kallonshi, gyara zama yayi yana kirkiro murmushi mai nauyi ya ce "Mammi na! Kin farka? Ya jikin?" Ta sake yin murmushi a hankali ta nuna mishi oxygen na hancinta sai ya cire yana jin yadda take sauke numfashi a kai akai "Mammi ki yi saving energy ɗinki kar ki yi magana kin ji?" Ta sake yin murmushi "Ina so na ji abin da ke bakin ka! Ka ba ni labari...tun jiya na lura kana son min magana amma kana riƙe wa menene?" Shiru ya ɗan yi "Speak up Saraki, yanzu ne kake da lokacin magana da ni anjima kaɗan kila sai dai matarka ko 'yan uwanka" Da sauri ya ɗan kalleta tana ta murmushi, kanshi ya duƙar a hankali ya fara furta "Mammi ki daina irin wannan maganan don Allah" "Toh na daina Saraki!" Ta faɗa tana lumshe ido, hannunshi dake cikin nata ne ya ƙara yin sanyi she can feel the nervousness a cikin tafin hannunshi zata iya cewa yana cikin yanayi ne marar fasaltuwa sai dai da yake namiji ne kuma jarumi yana iya shanye damuwarshi kaman babu komai. Idan Mammi ta tafi ba tare da ya sanar da ita menene a ƙasan Ranshi ba tabbas zai yi nadama mai girma, tunaninsa ya dinga rarrabuwa har yana jin kaman zai zauce idan ya cigaba da zurfafa a cikin muguwar tafiyar rayuwarshi...iya tunanin kaɗai kan karya duk wani guntun karsashinsa. ***** A hankali yake buɗe idanunshi har ya ware su akan Mommy da su Sadiqa dake zaune a ɗakin jugum jugum. "Saleem! Ka farka? Sannu ko mu je asibiti ne?" Girgiza kai yayi yana Miƙewa zaune jikin gadon ya kalli mommy da ita ma take kallonshi a hankali yace "Mommy na tuba! Mommy ki yafe min wallahi...." "Shhhh Saleem na sani, na san ba da saninka ka aikata hakan ba na san baka cikin hankalinka a lokacin da komai ke faruwa, laifina ne wlh laifina ne ka yafe min Saleem son zuciya ɓacinta, hakika na yi amfani da son zuciyata wurin ɗaiɗaita maka rayuwa don Allah ka gafarceni" Ta roka yafiyarshi tana kuka su ma duk su sadika suka shiga bashi hakuri, anan ya zauna yana jin yadda komai ya kasance... Hakika mommy ta yi kuskure Afeefah ce ta faɗo mishi a rai ko tana cikin wani hali yanzu? Ko ya rayuwa yayi da ita? Allah masani ****** "Mammi..!" Ya sake ƙira a karo na biyu ba tare da ta buɗe ido ba tace "Uhmm" "Zan faɗa miki ne, zan faɗa miki wanene ni..." Da sauri ta buɗe ido ta kalleshi cikin yanayin jin jiki ta zura mishi idanun a hankali ya cigaba da cewa "Ban manta komai ba, na ƙi faɗa ne saboda wacce daraja da ƙimarta suka zama ƙololuwa a gare ni ta yi fatali da hakan ta ɗauke ni ta yasar tamkar tsumma a cikin al'ummar da ba ni da masaniyar yaya suke bare ya rayuwarsu take, ya al'adarsu take ko ya imaninsu yake, ba tare da ta damu da zan ci ko bazan ci ba, shin rayuwata za ta inganta ko za ta yi lalacewa marar iyaka? kafin na haɗu da ke na zaci uwa masifa ce ga 'ya'yanta ta kan nesanta su da farin ciki ta saya musu wahala, ta kan zama tamkar ginin ƙasa da muddin ɗa ya jingina da ita sai ya faɗi, a maimakon ta kasance garkuwata sai ta zama ita ce a farkon cutar da rayuwata, na kasance a koyaushe bana rufe idanu na buɗe ba tare da na ga sadda take cire hannayenta daga cikin nawa ba tare da tura ni cikin dattin juji...ta tafi! Ta tafi da rayuwata da dukkan farin cikin da ya taɓa wanzuwa cikinsa ta tafi da rai da ruhi na..." Shiru yayi yana cije lip ɗin shi na ƙasa da har su ma rawa suke yi. "Ke ce kika ba ni hope na rayuwa, a kan ki na yarda uwayen ma suna suka tara Mammi kin zame min gata a sadda na kasance cikin wahala, kin ba ni duk wani kulawa da gata ba tare da tsammanin lada ba kin bani kaunar da bata taɓa yankewa ba, kin zame min rayuwa, rahama da kyautatawa da bata da iyaka. Mammi Sunana Sameer..." Lumshe ido tayi a hankali hawaye na sauka mata ya sa hannu ya share mata. A hankali ya cigaba da bata labarin da kafin ya gama jijiyoyin kanshi sun yi raɗa-raɗa, idanunshi tamkar garwashi muryarshi har yankewa yake amma Dukda haka jarumtarshi ta ƙi barin ruwan hawaye ko guda ya diga bisa fuskar shi ko zai samu salama cikin rai da ruhinshi, ba zata iya Miƙewa ba da zata iya da ta rungumeshi ta rarrasheshi da ta nuna mishi komai na duniya mai wucewa ne, da ta tuna mishi da irin girma da darajar da Allah ya ba uwa don kalamanshi sun yi tsauri sossai a kanta, bata san dalilin ta na yin hakan ba amma ta san babu uwar da zata so tagayyarar ɗan ta, ɗan ma mai tarin gata, daraja da martaba irin Rayyan. "Ka zama mai haƙuri da rayuwa! Ka zama mai afuwa Saraki haƙiƙa an cuce ka an kuma ɗauki alhakinka mai yawan gaske amma ina roƙon ka da ka bari komai ya wuce kaman ba'a yi ba, ka yi uzuri ga mahaifiyarka ka waiwayi gida..." Shiru tayi sai ta ɗan yunkura kaman zata tashi ta koma ta kwanta tana shaƙuwa. "Ka min alƙawari Rayyan!" Girgiza kai yayi yana ɗago rinannun idanunshi gareta sai ya ji tana ambaton Allah da salati ɗauke a Bakinta a kan idanunshi, hannunta na a cikin nashi Mammi ta ja numfashinta na ƙarshe da ya tafi da duk wani ƙwarin gwiwanshi, ya tafi da duk wani haske da yake tunanin da shi yake amfani wurin haskaka tarin duhun dake mamaye da shi, gigice wa ya nemi yi sai ya manta da cewa shi ɗin ma likita ne, ya kasa yanke hukuncin cewa ta tafi ya kasa yardar wa kanshi cewa da gaske ta tafi ta bar shi... "Innalillahi wainna ilaihi rajiun..." Shine kalaman da ya fito da kyar ya ratsa harshenshi har ya fita sarari. Ya fi mintuna ashirin a zaune a haka baya iya ko da kifta idanun kirki, kila mafarki yake, kila bacci tayi za ta buɗe idanu kila zai iya ganin kirjinta ya motsa ya cigaba da bugawa kila za ta ja numfashi ta ce mishi wasa take... Shigowar wani likitan ne ya tabbatar mishi da cewa da gaske ya rasa Mammi rasawa ta har abada haƙiƙa ɗaci da raɗaɗin mutuwa ba za su faɗu ba ba kuma za su misaltu ba. A chan reception kuwa Su jannah da Afeefah ne zaune cikin damuwa mai yawa don tunda suka shigo Afeefah bata daina zubar da kwallah ba, ta san mutuwa kuma ta ga mutuwa daban daban bata fata ya kasance a kan Mammi nan kusa Dukda ta san da cewa mutuwar dole ce ga dukkan mai rai, su uncle Musa da iyalan shi da Abeeha ta ƙira ta sanar musu jikin Mammi babu daaɗi duk suna cikin asibitin a lokacin da wannan likita ya fito ya sanar musu da rasuwar gigice wa suka yi suka fice daga hayyacinsu, Jannah ce ta yanke jiki ta faɗi sai jini ya fara fita mata Abeeha kam rasa ma ya zata yi tayi sai da uncle Sanusi ya riƙo ta yana ta maimaita salati ta kankanmeshi ta fara kuka mai tsuma zuciya shikenan sun zama marayu babu uwa babu uba, Mammi ta tafi lallai dukkan mai rai mamaci ne. Afeefah kam ba zata ce ga yanayin da take ciki ba, Dukda ta kaɗu iya kaɗuwa sai dai ko motsi ta kasa yi daga inda take hawayen idanunta ma kafewa suka yi, wata cousin ɗin su Abeehar ce ta riƙe mata hannu sai ta firgita tana kallonta idanunta duk a waje... "Wai cewa suke Mammi ta rasu? Ko kunnuwana ne basu ji da kyau ba?" "Sai haƙuri Afeefah, sai haƙuri..." Wasu irin hawaye ne suka shiga zubo mata masu zafi da raɗaɗi, da kyar take iya maimaita innalillahi wainna ilaihi rajiun.... A lokacin Rayyan ya fito hannunshi na tura gadon da mammin take kai a hankali yana tafiya ne ba tare da ya san inda yake jefa kafafunshi ba, Uncle Sanusi ne da matarshi suka taho da sauri suka saka mishi hannu don kaman zai kifa, idanunshi sun zama wani iri jikinshi na rawa zuciyarshi a bushe haka suka fice yana gaban motar da Mammi ke ciki wacce amblance ce aka dauko ta a baya har cikin gida, a ɗakinta aka sanyata babu wani jinkiri Matar uncle Musa dattijuwar malama da taimakon wasu malamai mata aka yi mata wanka aka yi mata sutura, kan kace mene gidan ya dinke da mutane masu kuka na yi masu yabon kyaun halinta na yi, Jannah dai tana asibiti don ɓari tayi ba tare da ta sani ba. Abeeha da Afeefah banda kuka da du'a babu abinda suke yayinda Rayyan na a parlorn shi a zaune wane mutum-mutumi tasbihi yake yi amma ba zai iya cewa ga abin da yake cewa a ciki ba, Saleem ne ya shigo Dukda ba ƙarfin jiki ya samu ba sai dai labarin mutuwar ya dugunzuma hankalinshi. "Rayyan!" Ya kira sunan. Jajayen idanunshi ya buɗe ya zura mishi ba tare da yayi magana ba "Sannu! Allah ya gafartawa Mammi Allah ya haskaka makwancinta ya sadata da annabin rahama" Da kyar ya iya furta "Ameen" Idanunshi na kan hawayen da Saleem ɗin ke yi ina ma zai iya? Ina ma ya san ta yadda zai nemo hawayen? Ina ma zai iya cire zuciyarshi ya yasar? Da yayi hakan ko zai huta raɗaɗin da ke gasata wane wuta. "An gama shirya ta ayi alwala a fita gabatar da sallah don samu a kaita makwancinta!" Wannan kalma ta Uncle Mansur ya zama kaman zuban wuta a jikinshi, shikenan fa yanzu ko? Shikenan zai rabu da Mammi rabuwa ta har abada? Saleem ne ya ja hannunshi har zuwa bayi yayi alwala suka fito a tare zuwa ɗakin Mammi aka ɗago makarar aka nufi fita da ita haraba inda kuka ke tashi, kowa idanunshi na kan Rayyan ne da yake ta focusing akan hanyar da yake takawa kar ya faɗi riƙe da gawar Mammi da yayi mata sallama na ƙarshe da qulhuwallahu ahad! A tare da shi aka yi mata Sallah aka kaita makwancinta na gaskiya, shine ya ba da ghdumuwa wurin sakata a rami kuma shi ne ya fara zuba mata ƙasa kan yayi baya baya zai faɗi aka tare shi su Uncle Mansur ne da Saleem, ɗagowa yayi yana kallonsu kila su basa jin abinda yake ji tunda gashi suna hawaye! Har aka gama binne Mammi aka kamo Rayyan zuwa mota baya gane fari ko baƙi don duk wanda zai ji mutuwar Mammi a bayan Rayyan ne.... Innalillahi wainna ilaihi rajiun 😭 Allah ka sa mu yi kyakyawar karshe! 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* *38* "Dakata!!" Wata murya mai amo tayi maganan. Chakk suka tsaya daga ɗora wukan a maƙogoron kawun. "Mecece alaƙarshi da ƙungiya?" Yayi tambayar a kausashe. "Babu mai girma shugaba" "Ku kyaleshi jinin shi bai halalta mana ba" Suman daaɗi ne ya tafi da kawu Dukda azabar da yake ciki, dunkule shi suka yi suka tura cikin buhu aka saɓe shi kaman kayan wanki aka fitar sai haushi suke ji bai musu amfani ba tsabar lalacewarshi, a booth na mota aka saka shi sai da suka yi tafiya mai uban nisa kan suka buɗe booth ɗin suka cilla shi ƙasa suka yi tafiyarsu. Ya fi awa nawa yana mutsu-mutsu ga zafin rana Allah ya kawo wani mai ruwa ya taimake shi ya buɗe buhun sai ya fara tari da mayar da numfashi sama sama, da kyar yake ambatar "Ruwa! Ruwa!!" Mai ruwan ya bashi ruwa a gora ya sha sossai yana sauke numfashi kan ya fara kalle kallen wurin da yake, wani kauye ne na daban "Me ya saka ka cikin buhu bawan Allah?" "Sace ni aka yi 'yan yankan kai ne suka sace ni Allah ya kubutar da ni" Abin mamaki ya ɗauke shi har gidan mai garin garin suna da karamci aka bashi wuri yayi wanka ya wanke najasar jikinshi ya rama sallaolin da suka hau kanshi, har abinci ya ci aka ba shi kuɗin mota ya nufi Dutsen-wai cikin zuciyarshi saƙe-saƙe ne mai yawan gaske ga bakin cikin abin da su larai suka yi mishi ga yadda ya sha jinin jikinshi da abin da ya riska a kwanakin wanda har abada ba zai taɓa mantawa ba, yana isa Dutsen-wai gidan mai gari ya nufa yana neman iso aka mishi iso ya ce "Toh dama na zo ne in sanar kuma in nemi a gargaɗi duk jama'ar garin nan cewa duk wanda ya sake cewa Ɗiyata Afeefah Mayya sai mun yi shari'a har kotun koli don Afeefah ba Mayya ba ce, ita kuma ba Annoba ba ce" "Toh fa da kanka Malam Labaran? Kana lafiya kuwa?" "Lafiyata ƙalau kawai dai na san Afeefah ba Mayya ba ce kuma kar a sake ce mata haka don abin da Mayu suke yi ko a mafarki ba zata iya ba wannan abu ne da ya shallake dukkan tunanin mai tunani." Ya ƙarasa cikin tabbatarwa da jimami. "Dama tun farko tsantsar jahilci da son zuciya ya sa kuka lakaba mata abinda ba shine ba, ashe kenan mutum ba zai taɓa mutuwa haka siddan ba? Har fa tambari kuka buga na cewar tun tana ciki ta cinye ɗan uwanka amma Alhamdulillah tunda ka gane gaskiya kuma kana shirin tsayawa a kanta sai ka yi wa kanka faɗa ka nemi tsari da jahilci don wallahi mugun ciwo ne kuma shi ke ɗawainiya da mafi yawanku cikin wannan ƙauye". Malam liman ne ya jero wannan jawabin, kawu ya gamsu har ya ji jikinshi na ɗan sanyi barin ma da malam liman ya sake nusar dashi akan Allah shi ba ruwanshi, da ya turo mu duniya yayi mana umarnin mu nemi sani a kanshi kafin mu bauta mishi, ba ka da hujjar kare kanka da rashin sani a wurin Ubangiji matukar baka tashi ka nema ba. kan ya dawo gida labarin dawowarshi ya riske su bai damu da zancen mutane ba da wasu ke cewa kila ta cika shi da kuɗi ne wasu na zaton ko don ta auri mai kuɗi yanzu ai dole ya ja ta jiki. Shi kuwa hankalinshi ya fi tafiya ga jan hankalin da liman yayi mishi na neman ilimi Dukda a yanzu wani tataburzun ne gabanshi don saurin da yake zabgawa yana so ya tabbatar babu kowa ne a gidanshi kafin faɗuwar rana. Kaman daga sama suka ganshi ya faɗo Asabe murfin tukunya ce a hannunta sai da ya subuce ya faɗi ƙasa ya tsaya kyamm yana kallonsu "Toh ban mutu ba! Kuma dama an ce sai abu ya same ka kake sanin masu sonka ashe dukkanku maƙiyana ne na tara? Ashe za ku iya bari na in mutu? Toh an gama wallahi gwara in zauna ni kaɗai na da in cigaba da zama da ku don haka kowaccenku ta tattara ya nata ya nata ta bar min gida na sake ku saki ɗaiɗai..." "Innalillahi wainna ilaihi rajiun Malam ka tsaya ka saura..." Ya katse ta da masifa "Babu abin da zan saurara Asabe! dole ku bar min gida a yau ba sai anjima ba kuma ku tattaro yaranku kaf ku fice min daga gida a tabbatar kuma an dawo min da kudade na mugayen banza mugayen wofi" Sai masifa yake ko ya tsaya ya saurare su abin ya mishi zafi rigima fa sossai ya kachame don suma sun ce in zasu tafi ba zasu tafi da yara ba tunda ba da su suka zo a kullin gararsu ba ko hutawa bai yi ba aka sake komawa gaban manya ya rantse shi ya sake su su tafi kuma baya bukatar ko wani ɗa don za su iya saka wuyanshi gabas su yanka tunda suka iya watsar da rayuwarshi alhali yana chan cikin tsaka mai wuya. "Labaran!" Malam liman ya kira shi ya amsa "ka san ko ma menene suka yi laifinka ne?" "Ta yaya? Ina fa chan gaban azzalumai mutanen nan don basu da imani suka ƙi daukar waya alhali ga abin da nace su yi da kuɗina ba nasu ba su kubutar da ni, ba don Allah na so na da sauran numfashi ba da na jima da mutuwa yanzu zaman makoki ake" "Labaran ka yarda kaso mai girma na abin da ya faru laifinka ne" "shiyasa na ce ina so in ji ta yaya?" ***** A ɓangaren Rayyan ba zai ce ga yadda yinin ya kasance mishi ba don baya gane komai, kawai yana so ya ji an daina ko magana a gangarshi ya ji shiru na ratsawa don ya samu damar gamsar da kanshi cewa da gaske ya rasa mace ɗaya jal mafi muhimmanci a rayuwarshi, wacce ta cire shi daga wahala ta bashi so da kauna ta raine shi fiye da yadda ta raini 'ya'yan da ta haifa da cikinta, ko gaisuwa aka mishi sai dai ya gyaɗa kai don baya magana, idanunshi har tsoro yake ba wa wasu idan ya buɗe, An yi an yi ya ci wani abu tun safen har dare ko ruwa bai yarda ya sha ba don raɗaɗin da yake ji daga zuciyarshi har akan harshen shi baya tunanin zai iya cin wani abin don cikin nashi ma jinshi yake a cushe, ganin yana shirin yi wa kanshi illa ya sa Sulaiman yi mishi allurar bacci don daga ƙarshe numfashi wahalar fita ya fara mishi. Su basa yarda da wani zaman makoki daga yinin da aka binnetan duk na waje suka watse, Afeefah tsabar yadda ta kasa yarda cewa Mammi ta tafi a ɗaki ta cigaba da zama hakan ya mata hijabi da haduwa da mutane dayawa ciki har da su mommy da Saleem, don Saleem yayi niyyan kwana a tare da Rayyan mommy ta sanar dashi yayi aure ai, ya shiga tsantsar mamaki ya kuma ji babu daaɗi a lokaci guda, yana mamakin yadda Rayyan yayi aure cikin kankanin lokaci alhali shi bai taɓa ji Rayyan ya furta sunan wata macen a matsayin buduruwa ba, ya kuma ji ba daaɗi yadda bai kasance tare dashi a bikin ba amma ya mishi Fatan alkhairi ya ɗauki su mommy suka koma gida don har yanzu a tsohon gidansu suke har shi, ya ce ba zasu koma chan inda ya zauna da Sabrina ba wani zai saya musu don bai san me suka binne ciki ba. sai dare ta fito ta nufi ɗakin Abeeha dake kwance rib da zazzabi, a gangarta ta zauna tare da rike hannunta "Afeefah da gaske Mammi ta tafi ko? Idan na je ɗakinta ba zan ganta ba ko? Yanzu shikenan ba mu da uwa ba mu da uba?" Ta danne hawayen da ke shirin ziraro mata tace "Haka Allah yake lamarinshi Adda Abeeha, dukkan mu da muke rayuwa a yanzu kwananmu ne bai kare ba idan ya ƙare dole za mu tafi" "ba za ki gane raɗadin da nake ji ba Afeefah" Ta girgiza kai "Duk wanda za ki ji Adda Abeeha na ji shi, kar ki manta ko da aka haifeni ba ni da uba, ban kuma buɗi ido na tarar da mahaifiyata ba sai a hoto kin ga ko zafi da raɗaɗin maraici na fara dandana, shi ne tun a cikin cikin mahaifiyata har zuwa zanin goyona. Adda Abeeha ku gode Allah kun rayu da iyayenku har girman ku..." Kuka ne ke shirin kwace mata amma ta dake ta danne. "Don Allah ki daure ki daina yi wa Mammi kuka haka! Mu bita da Adu'a shi ta fi buƙata a halin yanzu" Matar uncle Sanusi dake ɗakin tace "maganar Afeefah gaskiya ce Mahaifiyarku Adu'a take buƙata Abeeha ba kuka ba ita ai tata ta yi kyau! Allah ya sa jinyar da ta sha ya zama kankarar zunubanta ne" Suka amsa da Ameen. "Mommy ya Adda Jannah?" Afeefah tayi tambayar a sanyaye. Matar uncle sanusi tace "Ta farka amma tana under kulawar likitoci don ɓarin ya zo ne bagatatan ga cikin ya fara girma, ta dai ji jiki kam sai dai Allah ya kawo na moro suna chan tare da su mamanku" Ta fahimci da su matar uncle Mansur take

Chapter 23 of 40