ci ko bamu ci ba, mun yi karatu ko ba mu yi ba muna lafiya ko babu tun muna zuba ido yanzu wata kenan da ko mun je gidan ba'a bari mu shiga, ga mommy kwance a asibiti saboda damuwa da hawan jini...!"
Dukda maganan da take yi ɗin ya shige shi sossai, damuwa ya nuna a kan fuskarshi sai dai bai tanka ba har ta gama ta cigaba da kukan.
"A wani asibiti take?"
Ya jefa maganan a hankali
"Tana 44 ne, anan muke da file"
Kai ya gyaɗa kan ya katse wayan, Afeefah dake tsaye jikinta ne yayi wani irin sanyi a hankali zuciyarta ke motsawa da wani irin yanayin damuwa ba dai saleem da ta sani ake magana akai ba? Amma ai wannan Muryar ta Sadiqa ce, saleem ne har ya kori mahaifiyarshi a gidanshi? Ko jikinta duka kunnuwa ne ba zata yarda yana cikin hankalinshi yayi hakan ba, Wani irin tashin hankali ne ya zo mata har ta kasa boyewa ta manta waye a gabanta tace
"Yaya Saleem ne cikin wannan hali? Shi ne ya kori mahaifiyarshi da kanshi? Su Samha ne ke cikin irin wannan damu..."
Haɗa idanu da suka yi ya sa maganar ta katsewa idanunta har sun cika da kwalla suna shirin zubowa, gani irin kallon da ya mata ya sa ta saukar da idanun ƙasa, ajiye spoon ɗin hannunshi yayi ya zari wayan bai miƙe ba yana nuna ta da wayan ya ce
"Kika kuskura kika sake hawaye ɗaya ya zubo miki a kan fuska za ki gane ba ki da wayo...!"
Mukut haka ta haɗiye kukan zuciyarta na cigaba da racing cikin mixed feeling ga idanun da ya zuba mata yana jira ya ga zata yi kukan ne ko ba zata yi ba ga damuwar halin da ta ji wai saleem na ciki.
"Mam..mi na ƙiran ka"
Ta faɗa a ɗan tsorace. Kwafa yayi ya miƙe ya fice daga wurin da sauri ta dafa dining ɗin tana jan kujera ta zauna....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*34*
*Don Allah readers ina ɗan so ne in ja hankalinmu a kan wani abu da na fahimta, zan ɗan yi magana ne da miyaun marubuta. A duk sadda marubuci ke rubutu ba duba iya zallar nishadantarwa yake ba ko da kuwa littafin akan nishadi ne, ba son rai ake dubawa ba saboda ba shi ne ake son isarwa ba, duk sadda marubuci ya ɗora alkaminshi a kan Littafi tunanin farko da zai fara shine me ya kamata na isar? Shin wani saƙo ne nake da shi a cikin labarin nan da zan ba al'umma kuma su amfana da shi? Kar mu raja'a ga iya fannin nishaɗi ko soyayya don rayuwa bai taɓa tafiya babu ƙalubale ba... Don haka don Girman Allah mu daure muna karatu ta fuskar ɗaukar darasi don akwai darusa masu yawa da marubuci kan jefa a cikin kowani labari wanda ba sai an fito fili an ce yi kaza kar ka yi kaza ba mu dinga kokari muna fahimtar hakan saboda mu marubuta mu samu ladar ku👏🙏*
****
Da kyar ta iya danne kukan da ke taso mata, tsoron Allah na ƙara rufeta tana tuna irin iko da isan mommy akan saleem ashe har za'a iya samu macen da za ta raba wannan iko da isar cikin lokaci kankani haka?
Miƙewa tayi ta nufi sashen Mammi, ba za ta zuba ido rayuwar saleem ya cigaba da tafiya a haka ba don salim ya cika mutum cikakke ɗari bisa ɗari ya taimaketa a sadda bata da mai taimako bayan Allah, shi ne namiji na farko da ya fara nuna mata so tsakani da Allah ba tare da kyama ko tsoron tabbatuwar zancen al'umma a kanta ba, ya hana hawayenta zuba ya kuma ƙarfafa mata gwiwa akan jajircewa da haƙuri da rayuwa, ta san babu abin da zai saka saleem saɓawa mahaifiyarshi don ya san darajar ta fiye da kowa face sharrin asiri. Abin da ya sake bata mamaki ya ɗaure mata kai shine ta yaya wacce mommyn ta yarda da ita har ta aura mata saleem ba tare da yana so ba ta zama sanadiyar rabuwarta da ɗanta? Sam bata kawo cewa ko alhakinta bane saboda ta san ita ɗin ba dolen su ba ce da su taimaketa da kar su taimaketa duk wannan tsakaninsu da ubangiji ne yo waenda suka zama dolen nata ma basu mata ba sai bare ne za su mata?
Ta saka a ranta son zuciyar mommy ne ya janyo mata wannan wahala da suke ciki, tayi negleting duty ɗinta a matsayin uwa tana ganin dabararta shi zai sa 'ya'yanta su cigaba da zama ƙarƙashin ikon ta alhali 'ya'ya ba ababen iko da gadara bane ta manta Allah ne ke da dukkan iko akan bayinsa kuma shi ne ya san abin da yake fili da na ɓoye.
Ko da ta isa wurin Mammi bata samu Rayyan ba, zama tayi cike da damuwa tace
"Mammi Yaya saleem na cikin masifa"
Ta ƙarasa idanunta na cika da kwallah, Mammin ma ta fahimce damuwar Afeefar don Saraki ya sanar da ita komai kuma tausayin Saleem ɗin duk ya rufeta itama.
"Yanzu Saraki ya gama sanar mini, nayi mamakin yadda aka dau lokaci bai zo ba har ma aka yi auren Saraki saleem ba ya a kusa da shi ashe abin da ke faruwa kenan, laifin mahaifiyarshi ne Allah ya sa wannan abu da ya faru ya zame mata Aya ya sa ta hankalta"
Kai Afeefah ta gyaɗa tana amsawa da
"Ameen ya rabbi, Mammi ina so in taimaki Saleem Dukda ban san me Ya Saraki zai yi ba amma ina so in ba saleem gudummawa kaman yadda ya ba ni a sadda na rasa madafa don Allah ki taimakeni akan hakan"
Ta ƙarasa a karye.
"Me kike tunani Afeefah?"
Mammi tayi tambayar cike da kulawa.
"Mammi ina so ki yi convincing Ya Saraki akan za ki dinga bashi magani yana saka saleem sha ni kuma zan dinga haɗa zobo ko wani kalar drink da ayoyin da mafificin annabin mu annabi Muhammad (SAW)
Yayi mana umarnin amfani da shi don karya sihiri, ko da kurba bibbiyu zai yi Allah zai ba mu nasara kuma ina so zan yi wani abu na sadaka da tawassilin Allah ya dube shi ya dawo dashi hayyacinshi kar mahaifiyarshi ta mutu da damuwarshi"
Sossai Mammi ta yabawa hankalin Afeefah ta kara jin kuma tabbas bata yi wa Rayyan zaɓen tumun dare ba, ta gamsu kuma da shawarar don haka ta tabbatar mata zata bata duk wani taimako da take so.
Afeefah ta ji daaɗi ta koma ɗaki ta fara neman takardar ta da tayi rubutu akan hakan a sadda malaminsu na islamiyyat ke koyar da su, ta kuwa samu bayan dogon bincike Adu'a kawai take a ranta Allah ya taimaketa.
****
Rayyan na fita Asibitin ya wuce kai tsaye ya samu kuwa mommyn na jin jiki yaran sai kuka suke yi, har ranshi tausayinsu yake ji kuma yana jin su ne tamkar su Abeeha, shi karan kanshi a yanzu ya gamsu cewa asiri ne ke dawainiya da abokin shi in ba haka ba ko mahaukaci ai ya san girma da darajar uwa.
"Kukan nan me zai yi mata? Ko ba ku san Adu'a shi ne makamin ko wani mumini ba? Ko kukan lafiya zai bata?"
Da ɗan faɗa yayi maganan don sun cika mishi kunne, duk shiru suka yi don sun san shi baya ɗaukan nonsense da likitan da ya duba ta yaje yayi magana don anan ɗin ma yana da office kuma yana aiki da nan ɗin Dukda ya fi zama Capital.
Daga nan ya shiga ya duba ta tana bacci ya dawo ya kallesu yana so yayi magana da hankalinsu zai kwanta bai iya ba sai cewa yayi
"Komai zai wuce in shaa Allah"
Daga haka ya zaro kuɗi mai yawa ya basu kana ya fice, yana shiga mota Mammi ta ƙira shi a waya.
"Saraki idan ka samu Saleem ko da a waya ne kar ka yi mishi magana da tashin hankali, ka bi shi da lalama kuma kar ka tsananta magana akan mahaifiyarshi da 'yan uwanshi ka nuna baka damu ba don kar matar tashi tayi yunkurin shiga tsakaninku don akwai abinda nake so kullum ka tabbatar kana bashi yana sha, shi ramin ƙarya a koyaushe ƙurarre ne zai wuce ne kaman ba'a yi ba"
Ya gamsu kuma ya san Mammi wani abin zata sama mishi na karya sihiri ya ji daaɗi don bai san ya zai yi ba, ya tabbatar saleem a gidan ba zasu barshi yayi komai na malamai ba bare yace zai kaishi wurin wani malami. A kan ibada da azkar ne zai tsaya sossai ya ga saleem ɗin ya koma yi don tun da chan ɗin shi saleem ba mai wasa da ibada bane kai duk iya ibadarka idan Allah ya nufa kamun asiri na cikin jarabawarka dole sai ya kama ka sai dai ka samu sassauci saboda ka riga ka yi tawasilli ubangiji shine mai yin komai.
Kai tsaye gidan Saleem ya je Allah ya bashi sa'a ya dawo don yana horn aka buɗe mai gate a mota ya tsaya ya shiga kiran Layin saleem ɗin ringing na karshe aka sada shi dashi, amsa sallamar kawai yayi ya ce
"Ina waje"
Yana kai nan ya yanke wayan kusan mintuna uku sai ga saleem ɗin ya fito, ido kawai Rayyan ya kura mishi don kaman ba shi ba ya ɗan yi duhu kuma ya tara gashi sannan fuskarshi babu walwala haka ya iso ya buɗe gefen zaman banza ya shiga ya zauna.
"Ya kake?"
Saleem ɗin ya tambayi Rayyan yana kallonshi.
"Lafiya ƙalau, ka yi wuyar gani."
Murmushi yayi wani dry smile da babu annuri ciki
"An tura ni Lagos ne wani aiki shine muka tafi da madame fa, inda nake kuma babu wani service na kirki"
Kai Rayyan ya gyaɗa.
"No wonder, ya kowa da kowa?"
"Lafiya ƙalau"
"mu shiga mana in gaishe da mommy kwana biyu ban leƙa ta ba"
Saleem ya ɗan yi shiru don wlh ya manta da ya tura su chan gidan.
"Mommy bata nan sun koma tsohon gidan mu"
"Amma me yasa? Ina haya kuka saka a chan?"
Ya ɗan yi shiru
"Eh, nan ɗin ya ɗan takura mu ne ga iyayen Sabrina sun dawo shiyasa nace su koma chan"
Kai kawai Rayyan ya girgiza duk ranar da Allah ya bashi macen da zata raba shi da Mammi bai san irin hukuncin da zai mata ba don idan bai kasheta har lahira ba sai ya nakasata yadda ba zata taɓa amfani ba har abada.
"Ya Mammi da jiki?"
Saleem ya katse mishi tunanin da yake yi
"Tana ta faɗan kwana biyu baka shigo ba ai, ni kam saleem in tambayeka mana?"
Kai yaa gyaɗa mishi
"Ya tsakaninka da ubangijinka?"
Ya ɗan yi shiru kan ya kalli Rayyan ɗin
"ban gane tambayar ba, ina sallah biyar a rana yadda aka umurci kowani musulmi"
"na sani, ina magana ne akan nafilfili musamman na dare da na sanka da shi da azumin nafila, yau ka ma yi azkar na safe?"
Numfashi saleem ya ɗan sauƙe kaman abin na damun shi
"A gaskiya na manta rabon da in yi wani azumi da Sallar nafila, azkar ne nake dan yi watarana wani sa'in wani abu ya taso ko bacci ya hana ni amma zan yi kokarin ganin na gyara"
"Don Allah saleem ka gyara, da karatun alqur'ani kar ka manta ko da baka yi a fili ko baka nuna kana yi ba idan ka ji ƙuncin zuciya ka dinga ambaton Allah zai yaye maka ka ji?"
Ya ƙarasa da tausayin abokin nashi, kai ya gyaɗa.
"Ka shiga ciki"
Rayyan ya faɗa don ganin Sabreenar na tsaye tana kallonsu, ba don tsoronta bane baya so ta fahimci ya san matsalar saleem din kuma baya so ta tambayi saleem ɗin abinda ya wakana tsakaninsu don irin su akwai wayo idan baka iya kama ɓarawo ba aka ce sai ɓarawo ya kama ka.
"Gobe zan zo in gaida Mammi"
Kai ya gyaɗa
"Sai ka zo"
Daga haka ya fice shi kuma ya ja motan ya bar gidan.
****
Afeefah yinin gabaɗaya bata zauna ba, musamman Mammi ta ba da aka yi mata sayyayar kayan zobo don ta san saleem na son abin, ta dafa shi ta tace bayan ta gama yi mishi haɗi ta zauna ta yadda idan tana karatun numfashinta zai dinga sauƙa ciki ta fara karanto Ayatushifa
Suratul tauba aya ta goma sha huɗu 14.
Suratul Yunus aya ta hamsin da bakwai 57.
Suratul Isra'i Aya ta tamanin da biyu 82.
Suratul nahl aya ta sittin da tara 69.
Suratul shu'ara aya ta saba'in da takwas har zuwa na tamanin da biyu 78-82.
Suratul fusilat aya ta arba'in da huɗu 44.
Ta Yi su ne kafa bakwai bakwai, ta yi su da tawassilin cewa Allah zai karɓa har cikin zuciyarta babu kokonto don ba'a yi wa Allah kokonto ta yarda da cewa muddin ya yi amfani da wannan ayoyin na tsawon kwana bakwai duk abin da ke jikinshi sai ya kau. Ba sai a zobo ba ko a cikin ruwan miya ko a cikin ruwan tuwo kai duk abu da mutum zai iya ci muddin aka yi ayoyin nan kafa uku uku ko kafa bakwai bakwai da yardar Allah ko niyyan sihirin ne aka yi maka ba zai kama ka ba bare wanda ke cikin jikinka.
A gefe akwai ganyen magarya guda bakwai busassu ta cika farin bokiti surr da kyakyawar ruwa shima ta zauna yi mishi nashi a yayin da Abeeha ke tayata dura zobon a goruna don a sa a frigde. A cikin wannan bokiti mai dauke da magaryan ta shiga karata ayoyin kaman haka:
Suratul Fatiha.
Ayatul kursiyu.
Suratul A'araf aya ta ɗari da shida zuwa ɗari da ashirin da biyu 106-122.
Suratul Yunus aya ta saba'in da tara zuwa ta tamanin da biyu 79-82.
Suratul kafirun kafa ɗaya.
Falak da Nas ƙafa uku uku.
Sai ta karanta wannan Adu'a:
'Allahumma rabannas azhabal ba'as washfi antas shafi la shifa'un illa shifa'uka shifa'un la yugadiru saƙaman' kafa uku.
Sai ta rufe da
'Bismillahi Urkika min kulli shai'in yu'uzika wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfika Bismillahi urkika' shima kafa uku.
Hawaye ne ya sauƙo mata bayan ta gama tsaf, ta sa hannu ta share tana Miƙewa tsaye tayi yakini akwai waraka cikin alqur'ani, ta yi yakinin saleem baya bukatar wani boka ko malami da waennan kaɗai Allah zai isar mishi.
Sossai Mammi ta jinjina mata don bata bar sashen Mammin ba sai bayan isha, zobon duk a fridge na sashen suka shirya wanda ya kai gora hamsin ta ajiye ruwan ma lungun kujaran da Mammi ke zama a rufe.
Sallama tayi wa Mammin zata fita Mammi tace
"Ki bi sai ki ɗauka muku dinner ɗin ku daga kitchen na san Saraki yana chan yana jira don tun ɗazu ya yi min sallama"
Da Toh ta amsa kan ta fice Mammi ta bita da kallo tana murmushi.
A basket yanzu ma ta samu an shirya musu komai da komai ta ɗauka ta nufi sashen, ita dai wannan yanayi da take shiga ta rasa shi don tana tura kofan kamshinshi da ya cika parlorn ya sanar da ita yana ciki kaman kuwa ta chanka daidai don yana zaune kan kujeran dining gefenshi energy drink ne da yake kurba a hankali yana dannan waya fuskan nan babu ɗigon fara'a.
Ajiye basket ɗin tayi tana tsoron yin magana ta yi laifi sai ta fara cire kwanukan tana shirya su a kan dining ɗin, ta tafi ta samo cutlaries da plates ta fito da su taje ta ƙaro ruwa da drinks ta kawo ta fara kokarin ajiyewa a lokacin ya ajiye wayanshi ya ɗaga ido ya kalleta sai ta nemi ruɗe wa garin ajiye ruwan goran sai ya faɗi ya Buge cup ɗinshi na energy drink da ta samu a wurin ya ɓare kan wayanshi... Wani irin zaro ido tayi ta zari wayan ta fara gogewa da hijabin jikinta tana furta
"Innalillahi..."
*Ban yi alkawarin na dare ba amma in har na samu dama za ku ji ni*
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Ɗazu na ɗan leƙa online na ga yadda ake cigiyata har gabana ya faɗi na zaci laifi na aikata wai sai na ga ashe Haihuwa da hanji ake nema ido rufe😅 Za ku dinga haƙuri da ni Weekdays gaskiya don Sai yamma nake samun lokaci ko kuma dare, weekend da kuke samu raɓa raɓa ma saboda babu inda nake zuwa ne kuma ba ni da aikin komai, and ban da saka tsammanin pages biyu a weekdays ba zai haɗu ba, don Allah a rage ambaton Gureenjoh razana nake🤣🤣*
*35*
Baya baya yayi ya jingina da kujerar tare da relaxing, idanunshi har lokacin zube a kanta yana aikin kallon yadda ta ruɗe sai haƙuri take bashi tana share wayan da hijab ɗinta, he is surprise a lokaci daya kuma he's amuse bai taɓa ganin halittar dake tsoron shi irin ta ba, shi ba dogon magana yake mata ba shi ba dukan ta ya taɓa yi ba amma yadda take yi akan wayan sai ya ga kaman cewa yayi zai sa bindiga ya harbe ta.
A hankali ya miƙa tattausan hannunshi ya ɗora a kan nata da ke riƙe da wayan, abin da taji shi ya sakata natsuwar dole ta ɗago ido ta kalleshi suka haɗa idanu, for some seconds ya janye idanunshi ya zare wayan ba tare da ya ce komai ba.
Ita har ga Allah tana mamakin shegen miskilancinshi ayi mutum babu magana ai sai yayi ciwon baki, ganin bai ce mata komai ba sai ma kokarin saka abincin yake tayi saurin ɗaukan spoon ta shiga serving ɗin shi bayan ta tura mai ta juya za ta bar wurin ta ji ya ce
"Ina za ki je?"
Juyowa tayi ta kalleshi kaman ba shi yayi maganan ba hasali ma abincin shi yake ci hankali kwance, ganin tsayuwar ba zai mata ba sai ta nufi kujeran dake nesa dashi ta zauna ta ɗan saka abincin kadan ta shiga ci a hankali. Bai fi mintuna ashirin ba ya miƙe ya bar dining ɗin ta bi shi da kallo har ya shige ɗakinshi.
Washegari kuwa da Mammi ta faɗa mata saleem zai zo har gidan ta shiga kitchen ta musu girki ta sake yin tofin a ruwan abincin da ta shirya musu, a dining ta jera musu ta wuce ɗakin Mammi tana shiga bata zauna ba yana shigowa, a ƙasa ta zauna wurin kafafun Mammin shi kuma ya zauna daga gefenta Mammi ta amsa gaisuwar da ya fara yi mata ta ɗora da
"Ya jiki?"
"Alhamdulillah Mammi, ya naki?"
Ta amsa cikin kulawa.
"Afeefah kawowa mijinki ruwa mana"
Wani irin dukanta kalmar yayi a hankali ta ɗan kalleshi shima ita ya kalla jin wani mijinki da Mammi ta faɗa ya janye ido, ta miƙe ta isa fridge ta ɗauko zobon nan da Cup ta kawo mishi tana ajiyewa ya furta
"Thanks"
Yana ɗan lumshe ido saboda kamshinta da ya shige shi, yana mamakin kalar turaren da take amfani dashi ko yaya ta matso kusa dashi sai yayi perceiving smell din, tsiririn tsaki ya ja.
Ta juya zata fita Mammi ta tsayar da ita
"Ina kuma zaki je Afeefah ba kin zo taya ni hira bane?"
Dukkansu basu yi tsammani ba suka ji muryarshi yana cewa
"Dodonta ya shigo dole ta fita."
Calmly yayi maganan, ta ɗan wara idanunta bata ce komai ba sai da Mammi ta ɗan yi dariya ta yi rau da fuska a ɗan karye tace
"Mammi akwai abin da na manta ne ban yi ba a kitchen shiyasa zan fita fa"
Ya ɗago cup na zobon yana sha suka haɗa idanu da sauri ta fice, ya juya ya kalli Mammi
"wannan yarinyar ta cika tsoro da yin abu a zabure, ko ina haɗiye mutane ne?"
Shi dai da gaskiyar shi yayi maganan yana mamaki kuma.
Dariya sossai Mammi tayi
"Ka haɗiye mutane ai babu zaman lafiya kawai yadda kake ɗaure fuskar ne yayi yawa Saraki, ya kamata ka sakar mata tunda matarka ce"
Bai tanka ba chan ya ɗaga cup na zobon
"Yayi daaɗi."
"matarka ce tayi!"
Ya kalli Mammi yana maimaita matarka a zuciyarshi Mammi har ta haddace kalmar, zai yi magana ƙira ya shigo wayanshi saleem ne, Miƙewa kawai yayi ya fice.
Chan sai gasu sun shigo babban parlorn, Mammi ta fito suka gaisa tana ta mishi magana baya shigowa yanzu ya dube ta yana murmushi mai nauyi yake furta
"In shaa Allah zan ke zuwa Mammi"
"yauwa gwara kam ka zo Saleem, idan ba damuwa ma ina so in roƙi alfarmarka"
A kunyace yace
"Mammi kun wuce alfarma ai a wurin mu sai dai umurni"
"Yauwa toh na gode da wannan matsayi, idan har ba zaka takura ba ina so in dinga ganinka kullum for seven days akwai maganin kariya da Saraki ke sha ina so ku sha tare duk aikin naku ɗaya Fatan mu dai Allah ya kare mana ku ya sa ku gama lafiya"
Suka amsa da Ameen, cike da biyayya da yake da shi tun chan yace
"Na gode sossai Mammi kuma in shaa Allah zan ke shigowa har kwana bakwan"
"yauwa Allah ya muku albarka, ku isa ga abinci chan an shirya muku a dining"
Tana kai nan ta miƙe ta koma sashenta, hira suke ɗan yi kaɗan kaɗan a hankali ya ɗan lumshe ido ya buɗe kan chak ya miƙe yana furta wa saleem
"Ina zuwa!"
Corridor da zai kai ka side ɗinshi daga nan babban parlorn yayi aiko a gab wurin fitowa parlorn suka yi karab da ita har tana Buge mishi ƙirji, baya baya tayi tana ɗagowa suka haɗa idanu sanye take da wani riga da skirt na lace da bai wani kamata ba amma yayi masifar amsarta kasancewar shi Red colour tayi ɗaurin ture ka ga tsiya, ɗan kunne ne kawai a kunnenta bata saka sarƙa ba sai wuyan nata ya fita fresh yana ɗaukar idanu, ga mamakin ta mugun kallo ta ga yana mata sai ta sake shan jinin jikinta.
"Ina kike tunanin zuwa?"
Tambayar sai ya sakata cikin duhu dama ina take zuwa a gidan da ya wuce wurin Mammi ko Abeeha.
"Ina magana kin yi min banza? Na fara wasa dake ne?"
Da faɗa yayi maganan sai ta matsa baya idanunta na cika da kwallah tace
"wurin Mammi za ni"
"Daga yanzu har nan da kwanaki bakwai ko da wasa bayan gaisuwan safe da za ki je yi wa Mammi ki bari mu yi ido huɗu dake a main parlor sai ranki yayi mummunan ɓaci, wuce ki bani wuri"
Hawayen da take ta riƙe wa na tsoron ne ya zubo mata da sauri ta juya ta koma, bai bar wurin ba sai da ya ga ta ɓace ya ja tsaki mai ƙarfi ya juya ya koma parlorn, inda ya tashi ya zauna yana sake jan tsaki.
"Lafiya kam?"
"Ƙalau, mu je mu yi lunch azahar ya kusa"
Miƙewa saleem yayi suka isa dining ɗin Rayyan yayi serving ɗinsu suka zauna suna ci saleem sai yabon girkin yake har suka gama suna ɗan hira tsakaninsu daga nan suka shiga wurin Mammi ta haɗa su da zobon Dukda sun sha a dining bayan ta basu maganin a cup masu kyau duk su biyu suka sha saleem yayi mata sallama suka fito tsakar gidan.
Suna shirin fita masallaci Motar Abeeha ya shigo gidan tayi parking tana saukowa fuskarta a ɗan washe ta gaishe su, duk suka amsa saleem na tambayarta school ta amsa da Alhamdulillah daga nan ta shigo ciki su kuma suka fice daga gidan, sai bayan sun yi sallah ya zo ya ɗauki motar shi ya wuce gida, shima Rayyan mota ya ɗauka ya tafi duba Mommy ya samu da sauƙi sossai ma akan idanunshi aka bata sallama shi ya biya duk bills ɗin kasancewar akwai mota bai kaisu gida ba sai kwantar wa mommy hankali yayi suka tafi shima ya nufi gidan.
Ita kam Afeefah ɗakinta ta koma ta zauna akan kujerar mirror tana kallon kanta, a hankali ta sa hannu ta dafa saitin zuciyarta da har yanzu bai daina bugawa ba hawaye ne taji suna silalo mata, bata san wani mataki zata ajiye kanta ba a wurin Rayyan tsanar ta yayi ko kuma haushin kusancin ta da mahaifiyarshi yake ji bata sani ba, Meyasa zai saka mata boundry da shiga cikin gidan? Me tayi? Da kyar ta kauda tunanin ta tashi ta fara kokarin shirya wardrobe ɗinta tana janye tunanin, a wayanta ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 40